Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na ce Ubangiji na gode
maka da kasa uwata ta haife ni tare da ubana da ka
jarrabe ni da maraici ma ba ka jarrabe ni da na
uban ba sai ka rufa mion asiri ka zaunar da ni tare
dashi.
Ka kuma sa shi ya so ni bai ta6a yarda da
shawarar mugaye na ya bada rikona ga wasu ba,

58
na shafa a fuskata. na gyara zamana a bakin
gadona.
Da wa ki ke wadannan maganganun? Tayi
tambayar a fusace na ce da wanda ya tsargu tunda
ni dai ban ambaci sunan kowa ba, ina zaune a
gidan ubana kuma to ai babu wanda ya isa ya hana
ni 'yancin yin magana, haka kawai in mutum yaga
abinda nake yi ban yi mishi ba to kowa yaje gidan
ubanshi mana.
In da gaskiya cikin lamazin ai cewa aka yi kije
a kai ki wurin naki. don ki huta gorin da ake yi
miki to sai kuma ki dawo mana yau?
An dawo din sai kiyi abinda za ki yi na ce babu
abinda zan yi sai gori babu kuma mai hana ni.
Muna cikin haka sai ga Isiyaku ya shigo da
saurinshi, murmushi yake tayi alamar yana cikin
farin ciki, na kalle shi na taya shi murmushin dona
in zolaye shi, na ce mishi yaya na gan ka da
jallabiya har da bagaruwa da dabino, ko
makwabcinku Alhaji Madugu ya dawo ne?
Yaja wani mummunan tsaki kafin ya ce na
rantse Anti Mero da gangan kike yi, Alhaji
Madugu da ko katangar gidanshi bai yarda
taba ba shi ne zai dawo Umra ya bimu da tsaraba
irin wannan? Yaya Mubarak ne wajen mu goma ya
Daiwa ya shiga lissafa min yaran na gidaje daban-

59

daban, na ce Ubangiji ya karba musu badar da
suka yiwo, addu'o'in da suka yi mana ya karba
mana ya ce amin.
Dadi mai yawa ne ya kama ni don kuwa ba
karamin kewar Mubarak nayi ba, dan sauki-saukin
abin ma shi ne Mansur ya rage min kewar tashi da
ba karamar waiala nasha ba.
Za ka share zauren nan ne? Isiyaku yayi
murmushi cikin yanayin nokewa, gaskiya kiyi
hakuri Anti Mero gida zani inyi wanka, in sa
kayana zan je in raka Yaya Mubarak sallar Juma'a,
na ce to babu laifi sai kun dawo.
Na koma daki na zaro tsintsiyar zaburi na nufi
zaure don in kara kalelece zauren saboda in yazo
ya samu wurin cikin tsabta tunda nasan
saukowa daga Masallaci nan zai zo.
Ina sharar zauren ina lissafin rabon Mubarak da
gida a zuciya, na ce kwana ashirin da uku daidai,
kwanakin sun tafi da yawa al'amura masu dama
sun faru a bayanshi ga shi dama mun dade babu
wata mu'amallah a tsakaninmu tun kafin tafiyarshi
hidimar kasa, ko da dai shi ba mai hira ba ne balle
in ce zamu baiwa juna labarai masu yawa.
Ni kam zan yi kokari in koyi ba shi labarin
abubuwan da aka yi baya nan, ina cikin haka sai
kawai naga wata gabjejiyar kafa ta tako cikin

60
zauren, in daga ido don ganin mai kafar bakon
Babah Lantana na gani yau ma ya dawo, ko me ya
kawo shi kuma oho?
Wani lallaus an faffadan murmushin da ya sake
bayyanar min da hakoran gwal dinshi yayi min,
nan da nan kuma ya sake kifta min ido wai signal
yake yi min, nai maza na sake banka mishi wata
irin uban harara kamar dai yanda muka yi da shi
wancan karon.
Ya wuce cikin gidan ya bar ni ina tunanin maza
suna tafiya Masallaci don yin sallar Juma'a shi
kuma ya shigo gidan mata zai zo ya nade kafa
yayi ta zuba zance.
"Me ya kawo ka gidannan yau kuma? Tayi
mishi tambayar bayan ta mike tsaye ta tsura mishi
idanuwanta tana kallonsa, "Kai ke kam Hajiya
Lantana ba ki iya karbar bako ba, to alheri nazo
miki da shi."
"Ai ba ka da shi ne ko ka ambace shi an ganshi
a farko to sai ka biyo bayanshi da wani sharri."
To babu laifi, duk abinda ki ka ga dama ki
gaya min ni naga abin ki nasa rai a kai."
Ya gyara zama kan tabarmar
mishi, na shigo gidan da nufin wucewa in je in yi
wanka, idona ya kai kan sunkin kudin da ya tura
mata tare da fadin "Ungo wannan rike naki ne ki
da ta shimfida

61

Soma taba su, in maganar da na zo miki da ita ta
samu karbuwa a wurinki to wannan din ba komai
ba ne illa somin-tabin alherin da za ki samu a
wurina"
Ta zuba mishi ido tana kallonshi ba tare da ta
taba kudin ba, ai sai kayi min bayani naji in da
zancen naka ya dosa, sannan in naga za su ciwo in
taba, ai babu abinda ban sani ba a hali irin naka
baka fidda kwabo matukar ba ka hango yanda
za' ayi ya jawo maka sisi su zo tare ba."
Na shiga wankananabar su suna maganganunsu
ban jin abinda suke fadi saboda bayan gidan a
lungu ne na kuma rufo kofa, wanka mai kyau sosai
na tsaya nayi saboda a yau ina matukar dokin
saduwata da Mubarak.
A wannan lokacin na riga na zama budurwa na
kai munzalin yan matancin sosai nayi sha shida
da yawan mutane musamman Mansur sunan da
suke kirana kenan yanmata, ban san dalili ba sai
pake jin zuciyata ta soma so da begen kalmomi
masu dadi tsakanina da wanda nake ganin ya dace
yayi min hakan.
Ko da dai shi Mubarak bai taba furta min wata
magana ko nuna wata alama ta gane na kawo
wannan lokacin ba, a wannan lokacin ina ganin zai

62
gane hakan ko daga irin tarbar da nake shirin yi
mishi.
Kullum a Makaranta kawayena ba su da wata
hira wadda ta wuce ta samarinsu da irin kalamansu
masu dadin ji da sanyaya zuciya, amma ni ba ni da
mai furta min irin wadannan kalaman, dan dama-
dama ma Mansur.
Ga shi kuma kusan kowa ya ganni zai yaba
kyakkyawar halittar da aka yi min gani da tsabta
gani da gyara, ga ni da ado daidai gwargwado ga
shi kuma a wannan lokacin auren yara kan faro ne
daga sha biyu sha uku sha hudu in ta dan yi tsayi
sha biyar ko mu abinda yasa muka kai sha shida ba
a damu ba don muna Makaranta ne, amma shiru ba
ni da kowa.
Na fito daga wanka daidai Nalami ya fito da
Wasu soyayyun kaji daga cikin wata leda da ya
shigo gidan da ita, gashi nan komai dan
kankantanshi. Yana ganina sai ya canza maganar
yana fadin da hannuna na soya miki ita don dai
kiji-kiji dadi ki tuna da girkin maza, ban sake
kallonsu ba na wuce na bar Babah Lantana ta fara
yagar wata cinya tana ci.
Kwalliya sosai nayi na sanya kayana,
maimakon ma in zauna a cikin gidan sai kawai na
fito zaure na zauna ina sauraron isowarsu, ana

63
cikin haka sai ga Mansur ya shigo da dardumarshi
a hannunshi alamar ya dawo ne daga Masallaci.
"Barka da Juma'a. na daga ido na kalle shi
nayi murmushi har an sauko? Ya taya ni
murmushin an sauko ranki ya dade, na sunkuyaar
da kaina kasa ban cika son kana kirana da irin
wadannan sunayen ba, kana sa ni ina jin wani iri.
Yayi maza ya tsuguna a gabana ya zuba min
ido yana kallona, me za ki ji don nayi miki addu'ar
ranki ya dade? Ai bar ni kawai in ce miki ranki ya
daden, ko na dan ji sanyi a raina, kin san yanda ki
ke a'wurina kuwa?
Ai kallonki nake tamfar wata tauraruwa in ban
da kin takura ni kin hana bakina furta miki
kalmomin da yake son furta miki da kin sha
magana.
Tsuke fuskar da nayi yasa shi yin maza ya
canza maganar da tambayata, amma dai kwalliyar
nan da ki ka yi ba unguwa za ki ba na zo na tsare
ki da magana? Nayi maza na ce mishi a'a, cikin
zuciyata kuwa fadi nake yi ina son jin irin
wadannan kalaman amma ba daga bakinka ba.
kwalliyar taki ce na ganta ta zama ta
To ai kwalliyar taki ce na ganta ta zama ta
musamman ta bambanta da irin kwalliyar da ki ka
saba yi kullum wannan din tana da wani abin da
take nufi ta kara miki kyau tasa ki kin zama

64

budurwa ta sosai-sosai da ganinki kuma an san ke
din babbar yarinya ce mai daraja taimake ni ki
gaya min gaskiya kwalliyar nan saboda wa ki ka yi
ta?
Kalamanshi suka yi dalilin da na ce mishi
saboda kai, yayi maza ya ce ke bari zance
Maryamu, kar, ki zuga' abin nan da ba a fadan
sunanta ta hau kaya donni ki ka yi? Na ce, uhh,
don in ganki in ji dadi? Na sake cewa uhh.
Sai naji ya ce, To in dai donni ki ka yi da gaske
don in gan ki in ji dadi saboda kina tattalin farin
cikina to bani izini kawai in je gida in shaidawa
Babana don yazo wurin Mahaifinki ya gabatar da
zancena a wurinshi.
Maganar tashi ta firgita ni ba abinda nayi zaton
zai fito-daga bakinshi kenan ba, don haka na dago
ido da nufin kallonshi, kafin in san irin amsar da
zan ba shi, abin mamaki Mubarak na gani tsaye a
bayan nashi cikin wani irin yanayi, ga dai kwalliya
ta burgewa' yayi amma kuma fuskarshi takai
matuka wajen daurewa alamar bacin rai mai yawa
a tare dashi.
Gabana yayi matukar faduwa, na firgita da
ganin nashi nayi maza na sunkuyar da kaina kasa,
ban san yanda a ka yi ya shigo cikin zauren ban ji
motsinshi ba.

65
Ban san me Mansur ya gani ba da yayi dalilin
da ya waiwaya cikin sauri, ganin Mubarak a tsaye
bayan nashi ya sa shi hanzarin mikewa tsaye tare
da mika mishi hannu.
"Assalamu alaikum, barka da dawowa." Suka
vi musabaha bai sake tsayawa ba ya wuce ya tafi
Kusan minti biyu zuwa uku Mubarak yana tsaye
kallcza kawai yake yi, ba tare da ya ce uffan ba
jikina sai rawa yake yi, ji na nake tanfar na aikata
wani zunubi.
Cikin zuciyata sai tunani nake yi in ya tambaye
ni me zan ce mishi? Ina cikin wannan zullumin ne
sai kawai naga ya juya ya tafi ba tare da ya ce min
komai ba, tafiyar tashi a sani cikin wani irin
yanayi da na kasa jin dadin raina, jimawa can dai
na wartsake na ce oho.
Na mike na nade tabarmata a nufi cikin gida,
har lokacin Babah Lantana tana ta da bakonta,
sai dai ga alama sallama suke yi saboda na ! shi
yana cewa, to sai yanda ta yiwu, ko me a ke ciki
zan turo in ji bayani, ko kuma in zo da kaina, ta ce
to duk wanda a ka yi. Nayi mamaki a raina yanda
a ka yi bhirar tasu ta kasance sabanin ta ranar da ya
fara zuwa gidan.
Ina kwance a kan gadona zuciyata ta ca takai
kawo cikin sake-saken al'amura, naji wani mai

66
sayen kwalla yana tambayar akwai kwalla ko
tangaran ko tasoshi? Da sauri naji Babah Lantana
tana cewa babu sai gado mai rumfa in kuna saye,
yayi maza ya ce muna saye mana, ai mu duk wani
abinda zamu samu amfani a kanshi saye muke yi.
Nayi maza na mike a tsakiyar gadon don ganin
gado mai rumfar da Babah Lantana ke shirin
gado mai runfar da Babah Lantana ke shirin
sayarwa tunda naji ta ce ya shigo.
Ina daga zaunen najiwo ta tana kakkarya gadon
Innata, Asabe tana tayata, 'wannan gadon ma ai
tuni ya kamata in rabu da shi in canza na bari har
wannan shegiyar ta zo tana yiwa mutane
goshinshi.
Ba ma a yayinshi fa Babah, ta ce ch ai in suka
saya kauye suke kaiwa ko kuma su yankę shi su
maida shi na familin mai Rarfe.
Sai da suka fitar da shi zaure suka soma
cinikinshi sannan nabi baya na kalli mai sayen
nace mishi, kai Mallam gadon ba na sayarwa ba
ne, mai gado ya kalle ni ya kalli Babah Lantana ya
dan yi turus alamar rudewa.
To ko dai tayin da aka yin ne bai yi miki ba?
Babah Lantana ta ce, yau naga fitina, kai Mallam
ba ni kudina ka ji na sallama maka. Na ce in ka
saya ma banza ka saya gadona ne da na gada a

67

wurin Mahaifiyata, ban saida shi ba kuma ai babu
mai sayar da shi ko kuwa?
Yayi maza ya gyada kai tare da fadin in dai
haka ne kam babu shi na ce a to, na leka na kira
wani yaro na ce mishi gudu kaje ka kira min
Isiyaku, yaron ya tafi da gudu, ni kuma naja na
tsaya a Rofar gida ina kunkuni, to an zo da gado
gidanmu ne balle a jawo gado a ce za a sayar ayi
canji?
To ku sasanta dai sai mai gadon ta gaya mnin
kudin gadon in biya, na kalle shi cikin natsuwa na
ce mishi amma ai nace maka ba na sayarwa ba ne
za ka bar wurin nan ko sai na kira yaran can sun
rakaka? Sum-sum ya kama banva ya bar wurin.
Babah Lantana tayi kwafa ta kama gado zata
mayar ciki na ce a'a ai tunda ya uto ba zai koma
ba a zo a sayar da shi bana nan, katifar ma don dai
ba zan bar Babana ya kwanta a kasa ba ne da na
shiga na fito da ita na hada su.
Ai sai ki fito da itan kawai ta ju ya ta shiga
gida Isiyaku ya iso na ba shi gadon na ce ya hadu
da yara su kaui shi gidan Yaya Dijah.
A wannan lokacin ne Babah Lantana ta rasa
yanda za ta yi da ni a dake dai ba zai yiwt ba in
zagi ne ba zai gamsar da ita ba, tunda nima nayi
rikan da bana rama zagin amma ina komawa gefe

68

in yi kunkunan da bata jin abinda nake fada wanda
nasan yafi komai bata mata rai.
Ga shi ta fito da gado da niyyar sayarwa ta
karbi kudin wai-ita zata yi canji na kwace gadon
na tura wa Yaya Dijah: shi babu kuma yanda zata
yi dani, ina jin ta tana rattabawa Babana bayani na
karya da na gaskiya don dai ta samun ya sa baki
cikin maganar bai ce mata komai ba.
Takaicinshi ya kama ta, ta kalle shi cikin
yanayin bacin rai tare.da jan tsaki kai kam ai gaya
maka magana ma ba ta da wani. amfani sai ayi a
gama kana ji ba za ka ce komai ba, kayi wani gum
da baki kamar na mai cin najasa.
Bai ce komai ba nima ban ce tha cikin zuciyata
dai ccwa nayi in ma kin yi ne don ki:cuci wani to
kanki zai koma.
Ban sani ba ko takaicin labiane yake yawan
damunta ko kuma ta mantá ne:cewar dasa
hannunta: cikin shirun na Babaha yasa naji ta tana
mita ita kadai' a dakinta, a ce maigida duk abinda
aka yi a gidanshi ba zai ce komai ba, sai yayi gum
da bakinshi kamar na mai bubu? To ina zance? A
hankali na buda baki na ce babu, sai dai nasan bata
ji ni ba.
Tsaraba mai daraja sosai Mubarak ya aiko min
da itya, sai dai hakan bai sa da muka gamu da shi a

69

hanya na daga ido na kalle shi ba, balle in je ina
kula shi saboda na gaji da yanda yake tafiyar da ni
ba kuma zan lamunci miskilanci da jan aji irin
nashi ba.
A wannan lokacin mu'amallata da Ahmad
Mubarak sai ta kara ja baya sosai mafi yawancin
lokaci ko yana dan murmushi ya ganni daure
fuska yake yi, ko yayi kamar bai ganni ba, nima
bana kallonshi in ba a kan kuskure ba.
In na san yana gida ma bana zuwa sai in bari
sai baya nan in yi maza in je in gaida Umma in
dama abin da zan yi mata ma in yi mata ina ganin
ya dawo zan yi maza iu îta in bar gidan.
Umma da kanta ta ganc mun yi 'yar tsama ni
dashi don sau biyu tana tambayata ni me ke faruwa
ne tsakaninki da Ahmad Muuarak Maryamu? Ina
jin ta soma irin wadannan tambaycin sai kawai in
gudu in barta.
Sai dai irin wannan zaman da muke yi da shi
bai sa ya canza komai ba na daga abubuwan da ya
saba yi min kowane lokaci a cikin yi min aike
yake, kayayyakin bukatar rayuwa irin su mai,
sabulai, na wanka da wanki, under wears, audugar
al 'ada, kudi babu abinda ba ya baiwa Isiyaku ya
kawo min.

70
Ana cikin haka watan Azumin Ramadan ya iso,
don dama su Mubarak sun yi umrarsu ne a watan
Rajab, Isiyaku ya turo yazo ya tambaye ni me da
me nake so a kawo min? na ce yaje ya gaya mishi
bana bukatar komai har cikin zuciyata ban jina
kamar ina bukatar wani abu nashi a wannan
lokacin tunda abinda nake so yayi min bai yi ba
abinda nake nema a wurinshi ban samu ba.
Babu wata alama kuma da take nuna zan samu
yanda nake so din a wurinshi, to ana me zai yi ta
hidima yana ta dawainiya dani bayan shi ba sona
yake yi irin son da nake yi mishi ba, in taimakona
wake yi don kyakkyawar mu'amallar da yayi da
Innata a shekarunsbi na kuruciya to ya kyautata ya
taimake ni a bayanta har na kawo munzalin da
nake ciki & yanzu.
Don haka na gode ya bari haka, in don tausayi
ne ma dai to na gode yanzu nayi girman da shi bai
lura ya gane ba, don haka ya bar ni kawai in ci
gaba ni kadai in ma wahalar ce in shata kawai. A
yanzu abinda nake so ya so ni ne kawai irin son da
nake yi mishi, soyayyar da zata rikida ta zama ta
8ure, aroma ba kullum a ji tausayina ba.
A duk lokacin da irin wadannan abubuwan
suka dawo a cikin raina zama nake yi in yi ta kuka

71

wani irin kukan da sai nayi na gaji kawai nake yin
shiru.
Ban san dalili ba cikin zuciyata babu abinda
nake so irin aure, ban sani ba kowace yarinya ta
kevo munzalin da nake abinda take ji ke nan ko
kuwa ni don ina tare da Babah Lantana ne? matar
da kuliu:burinta ta cutar da ni ne in kaga bata yi
min hakan ba to abin ya gagara ne kawai.
Sannan kullum hirar kawayena ke nan
samarinsu da ranar aurensu, sai na samu kaina
nima a irin wannan yanayi da matsayin sai dai
kuma na kasa sakin zucivata in so wani ban da jin
dadin wata magana in dai a hakin wani ta fito ta in
da nake so ta fito din kuma abin ya gagara, to ya
fita mana ko zan samu in saba da wasu irin sabon
da nayi da shi in so su irin son da uake yi mishi ko
na rinka jin dadin kalamansu.
Gaya mishin da aka yi bana bukatar komai shi
ne yayi dalilin da ya gangaro da kanshi yazo har
kofar gidanmu sai dai yau ma cikin rashin sa'a tare
da Mansur din yazo ya same ni, sai dai maimakon
ya juya ya tafi bayan tafiyar Mansur din kamar
yanda yayi wancan karon tsayawa yayi ya tsare ni
da ido yana kallona, yayinda ni kuma na sunkuyar
da kaina kasa nayi kamar ban san da tsayuwar tashi ba

72

Ni me ke tsakaninki da wannan ne? a hankal1
na ce wa'? Yayi shiru ya ci gaba da kallona ba tare
da ya sake cewa komai ba, saboda sanin da yayi
nasan wa yake nufi, na mike tsaye a hankali cikin
natsuwa tare da karkade jikina a sakamakon
zaman dirshan din da nayi a kasa sanda nake hirar.
Cikin natsuwa na kalle shi na ce Mubarak, ya
ce uhh, ya amsa ba tare da ya buda bakinshi ba
watakila bai ji dadin yanayin da na ambaci sunan
nashi a ciki ba.
Na sunkuyar da kaina kasa kafin nace mishi
yau ne ka ga ya dace ka tambaye ni abinda ke
tsakanina da Mansur? Ya sake cewa uhhm, ba tare
da na dago ido na kalle shi ba, nace to ai ka
makara, na juya na shiga gida na bar shi a wurin
yana tsaye.
Na hau gadona na zauna a dalilin na kasa
kwanciya jikina sai faman bari yake yi, yayinda
Zuciyata ke ta faman harbawa a dalilin sanin da
nayi na batawa Mubarak rai. Hankalina yayi
matukar tashi na kasa jin dadin al'amarina.
Tsawon lokacin ina cikin wannan hali kafin
naji zuciyata tana rarrashina tana bani hakuri
kalamai masu karfi take gaya min, ya zama dole in
zama jaruma a kan lamarinshi in har ni kadai ce na

73

ke sonshi shi tausayina yake ji to ya tafi ya bani
wuri mana kawai ya gani ko ba zan rayu ba.
Ya tafi ya bani wuri mana ya bar ni tare da
masu sona irin son da nake bukatar ayi min a
yanzu, ya tafi ya bani wuri mana ya bar ni in yi
harkokin rayuwata menene na tsare ni da
tambayoyi? Na mike cikin kuzari saboda jin da
nayi zuciyata ta gamsu da abinda na aikatan naje
na debi ruwan sanyi nayi wanka na dawo na zauna
goge jikina ina shafe shi da man shafawa na
10.0-6 man da Mubarak ya saban min da shafawa.
Wani abin takaicin shi ne duk wani abinda ke
kewaye dani shi ne don haka na tsayar ma raina da
cewar cikin matakan da zan dauka na kamewa
daga gare shi har da daina yarda da hidimomin da
yake yi min.
Ina cikin wannan halin sai ga Isiyaku ya shigo
dauke da wani katon kwali shake da kayayyakin
amfani na hidimar Azumi, ba zan iya cewa a
mayar mishi ba don kuwa yana da girma da kima a
wurina.
Na karba na ajiye, Mansur ma ya kawo min
nashi na sake hadawa daga gidan Yaya Dijah ma
ta aiko da sako guda biyu, na Babana da nawa. Ina
jin Babah Lantana tana gayawa Baba wai in ban da
kar ta ce ya mayar wa Yaya Dijah da kayan kamun

74
AZumin da ta kawo mishi ace bata kyauta ba da ta
fada don kuwa ba a kan son ranta ta bada nashin
ba, tunda abinda ta bashin bai kai wanda ta ba ni
yawa ba.
A watan Azumin kullum na kan shiga gidan su
Mubarak ne da safe in je in gaida Umma in kuma
rike mata Alkur'aninta muje wajen jin Wa'azin
Tafsir din da ake yi a babban Masallacin
Juma'armu in a ka tashi sai na rakata gida kafin in
zo gidanmu in yi alwala in yi sallah, in hau gadona
in kwanta in yi bacci.
Ba na farkawa sai karfe uku da rabi, sai in yi
wanka in yi alwala in yi sallar La'asar in kama
shirye-shiryen abin buda bakina wanda nake yi da
dan dama don bani kadai ba ce, 'yan Almajiraina
guda biyu da muka yi matukar sabo sai Isiyaku da
Mansur da kuma Babana da kullum nake daidaitan
dawowanshi daga wurin Tafsir tunda na dare yake
zuwa in ba shi abinda nayi ya zauna yana ci, ni
kuma ina gefe ina jiranshi sai ya gama in karbi
kwanon ya wuce ya shiga gida kafin in bi
bayanshi.
A haka har Azumin yazo karshe muka shiga
kwanaki goma mafiya daraja kwanakin neman
daren Lailatul Kadri daren da AIkur'ani mai

75

girma ya ba mu labarin cewa darajarshi tafi ta
watanni dubu, haka alkairorin da ke cikinshi.
Ubangiji yasa mu dace, kullum abinda Umma
ke fadi ke nan in taji Mallam yana ta nanata fadin
alherin daren 'Lailatul kadri ni kuwa sai in ce
mata anmin Umma.
A wannan lokacin zan iya cewa ban taba
samun kaina cikin hali na kunci da farin ciki
lokaci daya ba irin wannan karon, ina cikin farin
ciki saboda alkhairori da suke ta zuwa min daga
wurare daban-daban.
Kusan kullum gari ya waye sai an zo min da
sako na kayan sallah daga wani wuri. Yakumbo
Halima da ba wani karfi ne da ita ba ma atamfa
'yar Holland ta dinka min a dalilin wai na zama
budurwa, Yaya Dijah tsalelen leshi gami da
takalmi da Jaka da gyale.
Umma atamfa da leshe itama da takalmi da
Jaka da gyale mahadin takalmin duk da dai tace
wai da kudin bankina ta saya min amma dai nasan
alherin Umma bai kwatantuwa a wurina.
Mansur yayi min kala biyu masu kyau shima
tare da takalmi da Jaka tare da gyale, sai kuma a
ka kawo min na Mubarak, Isiyaku ya aiko ya kawo
min. Na zauna ina kallonsu suma kala biyun ne sal
dai shi komai nashi daban ne da na saura, bai taba

76
mancewa da wani abu ba in dai har aiken zai yi
min yadika ne masu kyau masu laushi kala biyu
mai ruwan madara da kuma baki na rike su a
hannuna ina kallonsu ruwan da suke yi ya kara
tabbatar min da darajarsu.
An yi musu adon zare a wuyansu kalan zaren
ya dace da kalan takalma guda biyu da ya saka a
cikin kayan kenan kowanne da mahadinshi gyale
biyu sai kayan shafa da under wears ga kuma wani
dan karamin akwati mai dauke da wata 'yar sarka
mai dan madaidaicin 'yan kunne da zobe a wata
yar takarda kuma wasu siraran wararai ne da
agogo babu yanda za ayi a kushe hidimar Mubarak
in dai zai yi ta matsalarshi guda daya ce ita ce ta
ban san in da yasa gaba ba.
Kuncin da nake ciki da takura kuma shi ne na
tasa ni a gaba da Mansur yayi in bar shi ya tura
iyayenshi wajen Babana magana ta wuce tsakanina
da shi har yaje ya hada ni da Yakumbo Halima, ita
kuma ta kira Yaya Dijah ta gaya mata cewar lalle
ne ta gaya min in bar Mansur ya tura iyayenshi
wajen Babana ayi maganar aurena in kuma ba shi
nake so ba to in turo wanda nake son daga nan
zuwa watan Sallah in har ba so mu nuna mata ba
ita ta haife mu ba, amma ina amfanin wannan
zaman da nake yi a gidanmu?

77

Shi karatun boko ai ba dole ba ne wurin 'ya
mace, na Addini kuwa na same shi daidai
gwargwado a gidan mijina ma kuma zan iya yi
tunda neman sanin addini ne shi aure ai suturar 'ya
mace ne.
Yanda naga Yaya Dijah ta dauki maganar da
karfi na tabbatar zai yi wuya a ce watan Sallah
yazo ya wuce ba tare da an titsiye ni na fitar da
mijin ba, to ya ya zan yi? Ba da sunan Mansur din
zan yi shi da yake son a bada sunan nashi ko kuwa
wata hikima zan yi da Mubarak zai san abin da
nake ciki?
Cikin hanzari na kawar da wannan tunanin
saboda sanin da nayi cewar ba zan taba nuna mishi
wani abu

Please Login or Register in order to submit comment