Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai mai alherin ne
kullum a gare ni.
Da sauri ya tambaye ni me ki ke so in yi miki
Maryam? Gaya min shi ko menene shi zan yi miki.
Na sake sunkuyar da kaina kasa sosai kafin na
soma ce mishi, ni din budurwa ce nafi zaton daren
yau shi ne dare na bankwana a tsakanina da kai,

118
don haka nazo wurinka ne in yi maka kyauta daa
abinda nake ganin tanfar naka ne.
Muryata ta soma rawa jikina ya soma kaduwa,
hawaye suka soma gudu daga idona suna zuba
shar! Shar!! Shar!!!! Gaba daya hankalin Mubarak
ya sake tashi, ya tsunduma cikin wani hali da ya fi
kama da kidima.
To menene na wannan kukan? Me ki ke so in
yi da ki ke wannan kukan yanzu a gabana? Na ce
ki gaya min kawai ko menene zan yi miki shi, kiyi
shiru. Nace kiyi shiru.
Kwan! Kwan!! Kwan!!! Muka jiwo
kwankwasa kofar falon nashi, lokacinne na san bai
shigo ba sai da ya kulleta da sauri ya mike wajen
kofar ya bude.
Me ke faruwa ne Ahmad Mubarak? A hankali
naji Umma tana yi mishi tambayar, me ki ka gani
Umma? Ta dan yi shiru kafin ta ce mishi ji nake
kamar ba kai kadai ba ne. Ya sake cewa me yasa
ki ka fadi haka Umma?
Ta canza tambayar da tambayarshi to me ka ke
yi har yanzu idonka biyu? Bakin ciki ne ya dame
m Umma, ina bakin cikin raba ni da Maryam da a
ke son a yi.
Rabuwa kam ai an raba ka tunda gari na
wayewa za a daura aurenta, kai dai kayi hakuri

119
Kamar yau ne za ka ga ya wuce wata rana kuma ai
sai labari, ko ma ka kwanta kar in sake Jin ka a
waje, ya ce mata to.
Ta juya wurinta shima ya maida kofar ya kulle
ya dawo har lokacin ina durkushe a inda ya bar ni
ya sake kai guiwowin nashi kasa ya sake
durkusawa kamar yanda dama yayi muka fuskanci
juna.
Da gaske ne Babana zai raba mu don haka nake
so in yi maka kyauta ta alfarma don ta zamo
girmamawa ga al'amarinka da ke cikin zuciyata.
Yayi ajiyar zuciya mai karfi kafin ya tambaye
ni mecece kyautar taki Maryamu? Ban kalle shi ba
na ce mishi 'BUDURCINA' yayi matukar kaduwa
da jin kalmar da na furta, don kuwa sai da hakan
ya bayyana a fuskarshi, ban yarda mun hada ido
ba na ce mishi karbi budurcin kawai a wurina bani
da sauran bukatarshi bada shi zan je gidan nashi ba
shi yasa nazo' yanzu don in kawo maka shi.
Mubarak ya zama tanfar wani mutum-mutumi
sai faman bari yake yi tanfar wanda yayi wanka da
ruwan sanyi a cikin sanyin hunturu, da kyar ya
buda baki ya soma yin magana, a'a kar muyi haka,
ba sai kin yi min haka ne zan san ina da matsayi
mai girma a wurinki ba.

120
in kin bar shi a nan ma nawa ne, ai nawa i
Maryam zan kuma karbe shi ai ke tawa ce naa
kuma yi sa'a kin gane ke din tawa ce, kar kiyi
gangancin bada shi ga kowa.
Na dan dago kadan na kalle shi a rikice kwarai
yake bakinshi ne kawai mai jarumtakar furta
kalmomin da yake fadin. Ba ka sona? Da sauri ya
soma fadin ina sonki mana Maryamn, ina sonki, ya
ya ma za ki ce bana sonki? Ina sonki, ina son ki,
ina sonkki.
Ina jin ya fara furta irin wadannan kalmomin
na soma cire kayan da ke jikina ina ajiyewa a gefe
dai-dai da dai-dai, kan kace meye wannan sai gani
na zama daga ni sai 'yar shimin da ke jikina wacce
bata ma gama sauka kasa ta cinyoyina ba, itama na
saki hannayenta kirjina ya bayyana na maida
hannayena baya don balle rigar nonon shima in
ajiye shi a gefe.
Da sauri Mubarak ya taso yana fadin uh'uh
Maryam uh'uh kar muyi haka wannan kam ba zan
barki ki cire ba, ya miko hannu da nufin hana ni
cireta, a wannan lokacin kaduwar da yake yi takai
duk inda takai, kar muyi haka Maryan maida
rigarki jikinki kiji abinda zan gaya miki.

121
Yayi maza ya mike ya shiga wata kofa da ke
cikin dakin zuban da naji ruwa yana yi ya fahimtar
da ni ban daki ne.
Kusan minti biyar kafin ya fito yanayinshi ya
sauya daga yanayin da ya shiga bayan gidan, a ciki
can gefe ya koma ya nemi wuri ya zauna ya soma
yi min magana a hankali, shiga kiyui alwala za ki
dan ji sanyi a cikin ranki.
Kaina a sunkuye na ce mishi uh'uh kar kiyi
tunanin bana sonki ko kin fi ni shiga cikin wata
damuwa duk wami abinda ki ke zato a kan wannan
al'amarin na shigo abinda yafi haka, ina sonki fiye
da duk yanda zuciyarki take iya kwatanta miki,
son naki kuma zan iya cewa yana daga cikin
dalilan da suka sa ba zan iya yin hakan da ke ba,
don kina da girnma da kinma mai yawa a wurina.
Mahaifiyarki tana dashi, iyayenmu mutanen
kirki ne, yin hakan kuma ba zai rage min komai ba
na daga ciwonki da nake ji cikin raina, hakika na
sani an zalunce mu ko kuma in ce ana shirin
zaluntarmu tunda har yanzu ban tabbatar da daurin
auren ba, ina sonki ne ba don sha'awa ba, ina
sonki ne ba don kaina ni kadai ba, ina sonki tare
da girmamawa da mutunta duk wani al'amari naki.
Don haka ba zan so mu aikata wani abin da zai
taba mutuncinki ba, don haka mu kara hakuri da

122

Juriya da jaruntakar da zamu kai ma cimma nasara
kar mu sanya sabon Ubangiji a cikin lamarinmu,
ko kin ta6a jin inda darajar mutanen da suka gama
rayuwarsu ta duniya suka koma ga Ubangijinsu ba
su taba aikata zina ba a ranar Alkiyama?
Ina yi mana fata da addu'ar shiga cikin irin
wadannan manyan mutanen da muyi haka
Maryam gara mu kama hanya mu bar garin ni da
ke muyi tafiyarmu zuwa can wani wuri muyi
zamanmu su neme mu su rasa, sai komai ya lafa
mu dawo kin ga lokacin komai ya warware sai a
sake gabatar mishi da maganarmu.
Ban ce mishi komai ba ban sake daga ido na
kalle shi ba, saboda kunyarshi da ta kama ni, girma
da darajarshi da kimarshi suka yi matukar karuwa
cikin raina, zuciyata ta kara tabbatarwa tare da
sakankancewa cewa tabbas Mubarak mutum ne
mai girma da daraja wanda bai nuna son kai kan
abinda yake so.
Bai saurari yardata ko rashin yardar ba ya
mike yana fiddo kaya a cikin wardrope dinshi da
yawansu kayan mata ne gaba dayansu kuma sabbi,
sunkin kudi ya dauko yana kokarin adana kudin a
jikinshi yana yi min bayani muje in kai ki in da za
ki zauna in kuma zauna tare da ke in tsare

123
mutuncinki har kafin wannan maganar ta lafa sai
in...
Bai kai Rarshen maganar ba muka ji ana buga
kofar dakin nashi da karfin tsiya, tare da hayaniya
mai yawa, alamar dai mutanen da ke dukan kofar
ba mutum daya ba ne ko biyu adadi ne na Jama'a
masu yawa.
Gabana yayi mummunan faduwa nan take
kuma jikina ya dauki rawa nayi matukar tsorata,
tsoro kuma matsananci irin wanda ban taba jin irin
shi ba a rayuwata saboda gane muryar Babah
Langana da nayi a cikin masu maganganun nan.
Wayyo! Wayyo!! Jikina sai rawa yake yi.
Mubarak ya zuba min ido yana kallona cikin
tashin hankali saboda shima a tsorace yake amma
duk da haka kokari yake ya rarrashe ni ya kwantar
min da hankali kan irin tsoratar da yaga nayi.
Kai ku bar dukan kofar nan haka ina ganin
kamar babu kowa a ciki, wata daga cikin matan da
ke wurin ne suka fadi haka.
Babah Lantana tayi maza ta ce, a'a ai babu
maganar bari a tunbuke min kofar gaba daya sai
na shiga na gani da idona na gaji da iya shegen da
ake yi min ina kallo duk wanda yayi a baya bai
ishe shi ba sai yayi a yau dinnan na daren aurenta
masu bugun kofa suka ci gaba saboda a umarnin

124
da Babah Lantana ta basu ga dukkan alama kuma
so suke su tunbuke kofar dakin da gaske.
Kai haba wane irin hauka ne wannan? Umma
ce ta iso wurin take yin tambayar kai ku bar
wannan abinda ku ke yi in ba so kuke ta jawo
muku abinda zai dame ku ba.
Me zai dame su? Ai in abinda danki ke yi bai
dame shi ba wannan ba zai dame su ba tunda shi
da yake kwana da matar wani bai ji tsoro ba sa
masu tun6uke kofa? Mero ai matar wani ce tunda
gari na wayewa za a daura aurenta in kuma
takamarka iya shege to bari in gaya maka, shi
mijinta ya fi ka sanin kan tsiya don shi wannan in
yaga dama zai iya kasa tsiya a tire ya saida ita
saboda saninta da yayi.
To ta shafe ku ku kadai in ji Umma, kai ku
kauce ku bani wuri in yi magana da shi, in kuma
bata ciki to zan yi maganin rashin mutuncinki, za
ki gane ba ki da wayo zan nuna miki ke din
mahaukaciyar tsohuwa ce sau uku kenan kina
kulla mishi irin wannan sharrin, to daga yau ba za
ki sake ba.
To in aka same ta a ciki fa? Uwar banza mai
daurewa danta gindin yayi lalata da matar aure.
Da kyar a ka shiga tsakanin Umma da Babah
Lantana ba don yawan mutanen da ke wurin ba da

125
ba karamin gwabzuwa suka yi ba don kuwa su
dukansu biyun majiya karfi ne.
Umma ta matso kusa da kofar ta jijigata ta ji ta
a kulle kana ciki ne Ahmad Mubarak? Da sauri ya
amsa mata da eh Umma, ina ciki. To zo ka bude
min kofar mana don wannan azzalumar taji kunya
ta gane kai ba irin abinda take zato ba ne.
Ya mike ya nufi bakin kofar duk da sanin ina
cikin saboda ta ba shi umarnin budewa, ina ganin
ya kama hanyar fitar jikina ya kama rawa kar-kar-
kar saboda sanin da nayi bude kofar yana nufin
Babah Lantana tana da mutanenta su ganni.
Masharranciyar mata kawai wacce ta rasa
wanda zata tasa a gaba da cuta sai marainiyar 'yar
mijinta, ai kin ji kunya za kurma ki kara jin kunyar
tunda baki da aiki sai na kullawa 'ya'yan Jama'a
sharri ba kin haifa ba ke ma?
Bude kofar Ahmad Mubarak ya sake cewa to
Umma abinda na tabbatar kuwa shi ne shima ba
son bude kofar yake yi ba, iyaka dai kawai ba zai
iya bijire mata ba ne.
Kar wanda ya shigo min daki, kar wanda ya
matso min nan in baso yake ranshi ya
abinda naji ya fara fadi kenan daga bude kofar
tashi, ga dukkan alamu kuma kashedin nashi ya
126

shige su don ban sake jin wani yana yunkurin
shiga ba.
Uhun yasan ba shi da gaskiya yasan in an shiga
za'a fito da ita ne shi yasa yake wannan zare idon,
Babah Lantana ce mai fadin hakan.
Ke matsa ni ki bani wuri ja' irar mata kawai da
tun zuwanta unguwar nan take haddasawa Jama'a
da 'ya'yansu fitintinu iri-iri da sharri daban-daban
sai ya koma miki kanki.
Babah Lantana ta ce eh fadi duk abinda za ki
fada naji ba kuma zan bar nan wurin ba sai an fito
min da ita sai an fito min da ita kin daurewa danki
gindi yana lalata 'ya'yan Jama'a, wannan dai ya
isa haka wanda a ka yi a baya ya isa na hana kumna
tunda nayi mata miji zata je gidanshi ta zauna a
can sai kuma ki sake neman mishi wata tunda da
saninki yake yin komai.
Ban sani ba ko Mubarak yayi yunkurin yiwa
Babah Lantanan wani abu ne naji Umman tana ce
mishi a'a-a'a kyaleta a kanta sharrinta zai kare ba
dai kin iya hawa kan laifin 'ya'yanki ki hango na
ya'yan wasu ba ai kina da shirin shan mamaki.
Kai Mubarak gaya min gaskiya kawai kasan
inda Mero take? A natse ya ce mata eh, da sauri ta
sake tambayarshi tana ina nc? ban ji yayi wata

127
magana ba kafin na sake jin Ummanshi ta tambaye
shi tana wurinka ne?
Ya ce mata eh Umma, tana wurinka fa ka ce?
Ya sake cewa eh Umma, da dukkan alamu Umma
ta firgita kwarai da jin da tayi Mubarak ya amsa
ina cikin dakinshi.
Ahaha, da kin ce bata ciki gashi tana ciki kin ce
ke danki na kirki ne gashi ya bayyana miki cewar
yafi na kowa lalacewa kin ji kunya kin ji kunya
abinda Babah Lantana ke gaya mata ke nan.
Da kyar ta iya buda baki ta ce mishi to fito
musu da ita, kan ya ce komai sai Babah Lantana ta
sake café zancen da fadin to ba dole ba, ba dole ba
ma ya fitowa mutane da matarsu ba, matar mutane
ce fa ya samu yana tur...kai tir da wannan baki
naki kin girma ba ki san kin girma ba?
Ke kin san kin san, kin girma da ki ke daure
mishi gindi yana lalata 'ya'yan Jama'a shiru
Umma tayi bata tankawa Babah Lantana ba to fito
musu da ita ta sake ba shi umurnin, in fito musu da
ita Umma? Bata tsaya ba shi amsar tambayar tashi
ba sai kawai naji shigowarta.
Kan ka ce meye wannan sai gata tsaye a kaina
hannu da sakata kama ni ta jawo ni muna isowwa
falon muka gamu da Mubarak ga dukkan alamu

128
biyo ta yayi yaga abinda zata yi kar ki ba su ita
Umma muna gamuwa abinda ya fara cewa ke nan.
Na roke ki kar ki ba su ita yana nata rokon
nashi saboda ganin alamar ba za ta saurare shi ba,
tana jin haka ta saki hannuna ta juyo gare shi a
fusace tau! Tau!! Tau!!! Wasu irin zafafan marika
ta sakar mishi a jere cikin sauri har guda uku.
Jikina ya sake daukan wani rawan kar-kar-kar
na kara tsorata wani irin matsanancin tsoro ban
taba ganin dan gata kuma shagwababben da irin
Mubarak ba, amma ga abinda Umman tayi mishi a
yau a kaina kuka sosai na kama yi yayinda
Mubarak ya kai guiwowinshi duka biyu kasa kiyi
hakuri Umma bata saurare shi ba ta sake kama ni
muka yi waje ta dankawa Babah Lantana ni a
bannunta, to yi waje ku bani wuri.
Yanzu kuwa kin taba ganina a gidanki in ban
da yau? Kin taba ganin kafata ta tako cikin
gidanki? Gidanki ai ba gidan zuwa ba ne, gidan da
uwa ke daurewwa danta gindin ya rinka lalata
'ya'yan Jama'a? ai kukan karya ki ke yi.
Duk abinda Babah Lantana ke fada Umma ba
ta ce mata komai ba kuka kawai take yi sai dai ban
san asalin dalilin kukan nata ba na ganina a dakin
Mubarak ne ko na tausayin al'amurana ne oho.

129
Babah Lantana ta damko ni tamfar zata karya
kashin hannun nawa saboda tsananin rikon da tayi
min bayan kuma ni ko nuna alamar jayayya ban yi
ba.
Muna tafiya sauran Jama'a suna biye damu a
baya duuuw! Ita kuma tana bayani duk da daren ba
mai boye sirrin magana ba ne, tun bata isa komai
ba yarinyar nan take bin maza, nan in da ku ke
kallonta babu irin lalacewar da bata sani ba in a
kan namiji ne babu kokarin da ban yi ba a kanta
abin ya faskara, a ce yarinya kamar wannan ta iya
bin namiji har gidanshi taje kwanan gida? Ai kuwa
randa ta rika akwai magana kenan, ni wannan tana
da aiki ko in ce mijinta yana da aiki in ba a dace ya
zamo irin ta ba.
Ga dauke-dauke ko bera bai fi ta sata ba, ni fa
yanzu da lalita nake yawo saboda duk inda zan
ajiye zata dauka tanfar mai wankin ido take tayi na
kudi tayi na naman miya, bani da halin in motsa a
gidana sai tayi min ta'adi bani da sakat.
Bayanin nata ban sani ba ko ya gunduri. wasu
daga cikin Jama'ar tata ne naji wata mata daga
bayanmu ta fara cewa ba a yi wa da irin wannan
tonon asirin Lantana musamman ma da yake ke
din uwarta ce ba a bakinki ya kamata a ji
wadannan kalmomin ba ai tsakaninki da ita

130

addu' ar ce Ubangiji ya shirya mana musamman
ma kuma da yake yau din nan shi ne darenta, na
karshe a tare da ke zata gidan mijinta gobe kamar
yanzu fa ita din matar aure ce tana can a gidan
mijinta.
Cikina ya bada wani irin mummunan sauti na
kulululu! Saboda jin da nayi ta ce, gobe kamar
yanzu ni din matar aure ce ina gidan mijina.'
Addu'a ya kamata ki dage kiyi tayi mata na
Ubangiji ya shiryeta ta bari fiye da haka ai anyi an
kuma bari kawo ki ka gani yana rayuwa yana da
kuskuren da ya aikata lokacin kuruciyar wanda in
da za a sake dawo mishi da kuruciyar tashi a
yanzu ba zai maimaita wancan abin ba don ya
gane bai yi wa kanshi daidai ba.
Wata can daga gefe ta sake cafe maganar itama
maganar take yi shi sabulun wankan aure ma wani
irin siddabaru ne da shi saboda sabulu ne mai
albarka wanke dauda yake yi yayi tas, ya wanke
duk wani mugun hali ya zama mai kyau mara
hankali ta zama mai hankali kiga an kai yarinya
daki ana tsoron al'amarin ta sai kuma kijita shiru
ta zauna sai wanda yasanta yasan kuruciyarta
shine kawai zai san ta taba yin wani abu.
Babah Lantana taja wani mummunan tsaki
wato nan duk bayanin nan da nake yi muku

131
haushina ku ke ji da sauri dayar ta ce ba haushinki
ba ne muka ce kiyi mata addu'a ta sake jan wani
tsakin to da addu'arta zan ji ko da ta nawa
ya' yan? Gaba daya suka hada baki wajen cewa
aiya kin yiwa wani addu'a kin yiwa kai ne don
kuwa ita addu'ar yana daga cikin sharadin
karbanta in ka yi wa kanka ka hada da sauran
Musulmi baki daya da kuma za ka bar yiwa kanka
ma ka koma ba ka da aiki sai na rokarwa
al'ummar Musulmi ko wani dan uwanka to kai ma
da kaga biyan bukatunka cikin sauri.
Babah Lantana ta ce, ai sai kuyi tayi ina jinku
wannan dai babu abinda zai sa in zauna ina bata
lokacina kan wannan ba don ni kadai ni nasan irin
abinda ta guma min iyaka dai tunda zaman namu
tare yazo karshe shi kenan magana ta kare, zata je
gidan mijinta nima ta bar ni in zauna da nawa
mijin lafiya a gidana, aniyar kowa kuma ta bishi,
kowa yayi shiru yana jinta babu wanda ya sake ce
mata wani abu.
Muna shiga gida naji ta kai min wani irin
wawan dukan da ban zata ba sai da na kife a kasa
saboda tsananin buguwan da nayi nan take kuma
ta biyo ni ta sake dannewa tana duka tana fadin
har a daren ranar auren naki ma sai kin je kwanan
gida duk wanda ku ka yi a baya bai ishe ku ba sai

132
kin sake kai mishi kanki a yau saboda ki samu
kaiwa dan uwana kazantarku ko?
Tana yi tana duka tana mintsini tana bugun kai
a Rasa, ga kuma bayanin da take yi fatanki da bai
wuce ki sa mutanc su zage ni su ce ban iya tarbiya
ba, toaniyarki zata biki dadin abin kuma shi ne ba
ke kadai ba ce a gidan ga yar uwarki nan Asabe
ita ce gaba da ke ko da yake ba sosai ba ne amma
sai ki tsallaketa tana kwance kije wurin iya
shegenki tana kallo babu ruwanta saboda bata gaji
wannan tsiyar ba.
Mafi yawancin mutanc suka fusata da dukan da
Babah Lantana ta rufe ni da shi fadi suke yi haba a
ina ake wannan abin amarya kuma ayi mata duka
tun a wurin sakun lalle take burin dukan yarinyar
nan a ka hanata shi ne yanzu ta fake da wannan
abin tayi mata irin wannan nagazawar.
Aka kwace ni da kyar daga hannun Babah
Lantana a ka kai ni daki a ka zauna da ni na
makure wuri daya cikin tsananin takaici da bakin
ciki ga masifar 6acin ran auren dolen da tasa ayi
min ga bakin cikin azabar da ta gana min ga
wulakantani da tayi wurin mutanen da ba su sanni
ba, babu ma kuma abinda ya hada ni dasu balle su
san sharri ta kulla min na maganganun da ta fadi a
kaina.

133
ina zaune ina kuka yayinda mutane a tsakar
gida suka yi cincirindo suka zagaye Babah
Lantana suna sauraron karin bayanin da take yi
musu a kaina na game da mugayen halayena sai
kawai naga wata mata da ban santa ba ta fado
cikin dakin tana shigowva tasa hannu caraf ta
damke hannuna.
Nayi kamar in kurma ihu saboda tsananin tsoro
don nayi zaton ko bayanin da Babah Lantanan ke
yi musu ne ya kara fusatata har taga bari tazo ta ja
ni kawai zata kai ni a sake yin rubdugu a lakada
mini wani uban dukan.
Sai naga tayi maza na dora dan yatsanta a baki
tare da fadin shhhhi alamar kar in yi wani motsi
mai karfi da zai jawo hankalin Jama'a gare mu
don haka na mike cikin nutsuwa ina biye da ita
sannu a hankali cikin hikima da kulawa ta fitar
dani daga cikin tirmitsin Jama'ar nan ta nufi kofar
gida da ni.
Muna fita waje ta kalle ni cikin nutsuwa ta ce
min kama hanya kiyi tafiyarki kin ji yarinya,
wannan fitinar tayi yawa je ki abinki babu wani
abinda zai same ki sai alheri shi da ai na kowa ne
babu mai yi mishi sharri sai wawa.
Zuba mata ido nayi ina kallonta a tsorace gani
nake tanfar wani sharrin take so ta sake kulla min

134
don gani nake tanfar duk wani wanda yakc tare da
Babah Lantana mugu ne sai naji ta ce min, ke fito
da ke nayi fa don ki samu kiyi ta kanki, yi maza ki
bar wurin nan tun bata ankara ta gane ba kya nan a
cikin gidan nan ba.
Kallon da nake yi mata cikin tsananin tsoro ne
wata kila ya sa ta maimaita cewa yi ta kanki na ce
don ki samu ki kubuta daga sharrin wannan
muguwar ja'irar, ta sake maimaita kalmar shi da
na kowane babu mai muguntarshi sai wawa, jeki
duk inda ki ka ga yayi miki daidai kin ji wata rana
in kina raye sai kiga kin bada labari.
Ina jin haka na gane da gaske tayi nufin
taimakona ban sake tsayawa wani 6ata lokaci ba
yankawa kawai nayi a guje duk da kasancéwar
lokacin, lokaci nc na nisan dare ga kuma duhu.

TIRKASHI!

Ku biyo ni mu sake bin 'yar gidan Mallamn
Habu Mai Tumatir cikin littafinmu na uku don
muji da ta yanka da gudu a cikin nisan dare da
duhunshi ina ta dasa?
Me kuma ya faru bayan haka? Meene karshen
maganarta da Babah Lantana da kuma auren
Alhaji Nalami?

135

Fatan alheri gare ki dukkankuu na gode da
kulawarku kan harkar rubutuna na gode, Ubangiji
ya sakawa kowannenmu da alherinsa ya kuma
sada nu cikin Aljannarshi ta Firdausi domin
rahamarSa, Amin summa Amin.

Taku,
HAFSAT CHINDO SODANGI
6/7/1434
5/5/2014


36





































































An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment