Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wani qaton bakin gilas wanda: ya mamaye rabin fuskarta. A, Kai tsaye za ka lye. kiranta da ‘first Lady’ saboda haduwarta. Tana fitowa daga motar ta dubi yarinyar
’da ke tsaye, cikin wata irin murya mai kama da rada rada ta soma magana cikin harshen turanci.
“jeki shigo da su.”
Yarinyar ta amsa da ‘okey Tare da juyawa da sauri ta wuce ita kuma ta nufi cikin gidan nata tana wani irin taku, da wata irin faskekiyar waya a 'hannunta. ;
Dillaliya da ta gaji da ruwan bala’i sai kuma ta yi shiru tana tunanin mafita, can dabara ta fado mata ta
Ciro ‘yar qaramar wayarta baby Nokia ta lallatsa lambar Hajiya Kande ta kara a kunne; tun kafin ta
soma magana ta ji an bude wata qaramar kofa yarinyar. Tace come and enter
Dudda Dillaliya ba ta san abin da ta ceba, amma ta fahimta ta hanyar yi masu nuni da hannu da yarinyar ta yi, don haka ta zabaura ko kallon Saude ba tayiba tayiciki, don haka itama tamike da sauri ta bi ta
Kan Saude ya yi masifar daurewa lokacin
da ta shiga cikin harabar gidan, gabanta ya shiga wata rugurguza da bugawa mai tsanani, yarinyar ta yi masu jagora har zuwa wani qaton ginin bane hawa hudu, wanda tamkar da gilas kawai aka yi shi, dama da hagu duk iri daya ne, suka nufi Bangaren dama suka tattaka wata matattakala wadda ba tafi hawa shida ba, sannan suka ratsa ta wata Kofa mai fadi, anan ma mace ce tsaye qikam kamar an kafe ta, tana sanye ita ma da bakaken suita jikinta, sai da ta sa wata ‘yar na’ura ta daddana a jikinsu sannan suka ‘ wuce cikin kofar da za ta sada ka da qaton falon gidan. Saude ta bi matar da kallo a zuciyarta tana fadar, ikon Allah yanzu ita kuma wannan aikinta kenan”
Kamshin rom freshner da turaren wuta dan Maiduguri shi ya dakar masu hanci su duka hakan ya tabbatar masu da sun iso falon, qaton gaske wanda aka zagaye da kujeru saiti uku, kuma kowane
kalarsa. Kai batun ma in tsaya in, labarta muku haduwar falon duk wani bata lokaci_ne na barwa mai karatu ya yi image dinsa a zuciyarsa.‘Yarinyar wadda zan iya kira da Ingozi ta yi» masu nuni da cikin falon suka tafi suka zauna dirshan a ‘qasan kafet din duk da kujerun da ke zube kamar a cikin store. Yarinyar ta juya ta tafi abinta tabar. su nan
zazzaune kamar masu zaman gaisuwa,; sai :rarraba
idanuwa suke ba Sauden ba na Dillaliyar ba, wadda sai ka ce ba ta taBa zuwa ba.
Tun suna tsammanin fitowarta har .suka soma . cire rai da za ta fito, don sun share fiye da awa biyar a zazzaune suna zare namujiya, sanyin AC sai kada su yake suna faman karkarwa. Tuni sun gama’fidda rai da fitowarta, ga gajiya ga wata~ masifaffiyar yunwar da ke kwakwalarsu, sai faman gyangyadin gajiya suke. , Kamshin turarenta shi ya farkar dasu; gaba daya Suka wartsake suna daidata nutsuwarsu,. idanuwan Sande na zube a kan matar wadda ta nufo inda suke tana lallatsa faskekiyar wayar da ke-hannunta,*Allah mai halitta abin da Saude ta iya fada kenan a zuciyarta, saboda yanda ta ga tsabagen kyau kwance a jikin matar, wadda ba za a kira ta da doguwa ba ba kuma gajeriya ba ce, sai dai a kira ta da tsaka-tsaki. Ba ta da qiba sosai, amma kuma ba ‘siriri ba ce sosai dai tana da jiki daidai-daidai.
1page is missing
A yanzu ma takalmi ne mai tsini a kafarta, sai dai babu gilas yanzu a fuskar tata.
Ta karaso cikin falon ta fada kan kujera ta dora kafa daya kan daya ba tare da ta dago ta kallesuba
idonta na kan wayar hannunta ta rinka amsa: masu gaisuwar da suke ta faman kwarara mata
Duk azaton Saude za ta basu hakurin shanyar dasu da ta yi amma sai taga kwata-kwata ma hankalinta baya kansu yana kan wayar dake hannunta ne
falon ya dan dauki shiru, Dillaliya na nazarin ko ta fara. Maganane
Cak matar ta mike wadda ba zata haura shekara talatinba
ba, muryar nan tatat kamar mai rada ta soma magana.
‘Ki yi hakuri baiwar Allah ina da abin yi yanzu haka kikaga nazo nazauna dan insaurareki dama na lura kamar akwai wani important issue ne shi yasa na ce aje a shigo da ku, yanzu banida lokaci inada apointment da karfe sha daya.’ Tana maganar tana taflya. ’
Dillaliya ta fara bada hakuri cikin rawar murya tana fadar, “Ki yi hakuri ranki shi dade, wailahi na dan saurara ne ki fara magana kada in fara kiga kamar na yi rashin da’a a gabanki, dama ba wani
abu ba ne yar aikin da kika ce kina so CE na kawo miki guda tun wancan watan‘ lokacin da mukazo ni
Da Hajiya Kande taya ku murnar cin nasarar lashe zabe kika ce kina san yar aiki guda mai nutsuwa za ki Kara shi ne na tsaya na binciko miki na kawo miki
Matar ta dan dakata daga tafiyar da take ta waigo a hankali, ta daura dara-daran idanuwanta kan Saude tana qare mata kallo sama da Kasa, tamkar wadda ta ga wani abun kyama a tare da ita, ta dauke kanta tana ‘ latsa wayarta cikin rashin kulawa ta ce, “Is okey. ”
Ta dan karkace tasa hannunta saman hannun
kujerar ta janyo sai ga wata ‘yar loka, shake da kudi bandir-bandir yan ‘ dubu-dubu, ta zaro masu yawa ba tare da ta Kirga ba ta cillawa Dillaliya tana fadar, “Ki hau mota, sai da safe.” ‘ Ba tare da ta~ saurari godiyarta ba ta yi gaba abin ta, dad'i ya kashe Dillaliya ta tashi jiki na Bari. tana fadar, “Ke kuwa kin yi nasara Saude, da ta dauke ki don Hajiya Kande ce min ta yi ta kawo mata yara ‘yan mata sun fi guda talatin tana cewa ba su yi mata ba, don haka saiki kula ni dai kin ga tafiya ta.”
Ta mike ta bar Saude na zare namujiya, zuciyarta na faman kaiwa da kawowa, a yanzu ma kukan ya gagare ta' saboda tashin hankalin da take ciki yanzu ya fi gaban kwatance, tunaninta daya yanzu wace irin rayuwa ce za ta yi a gidan da ba ta san kowa ba?
Wane irin‘ qalubale ne yanzu kuma za ta fuskanta? ' Ta Iumshe idanuwanta Kirjinta na barazanar ‘
fashewa, ga‘ bacci, ga yunwa, ga gajia, ga uwa-uba fargaba da tashin hankali da suka‘ dabaibaye zuciyarta. Tana nan zaune tana muzurai ta ga wata dattijuwar mace ta shigo falon sai dai ita da ganinta Bahaushiya ce wadda shekarunta ba zasu wuce
arba’in ba. Ta dubi Saude cike da kulawa kafin tace, “Ki taso muje in nuna miki masaukin ki.”
Saude ta yunkura ta mike tana jin tamkar za ta. kifa saboda rashin kuzari. Ta wata hanya ta ga sun bi ta cikin falon sai ga su sun flto wani Karamin bedroom shi daya, ba wasu karikitai a cikinsa sosai, ‘ karamin gado ne kwara guda mai kyan gaske kwanciyar mutum guda, sai wardrobe dinsa a gefe, shi kenan sai kafet da ke malale a dakin mai laushi.
Matar ta juya ta dubi Saude tana fadar, ‘Nan shi ne dakin da Hajiya ta ce a sauke ki da fatan za kiyi . farin ciki, don gaba daya ma’aikatan .gidan nan masaukinsu a waje yake sai ga ki ke daga ~zuwan ki anwareki, natayaki murna." ‘
Saude dai ba ta ce komai ba don ita abin da ke cikin zuciyarta yafi gaban wannan. Ta zauna gefen gadon wanda ya sha lallausar shimfida ta ci. gaba da bin dakin da kallo, wanda take ganinsa ‘tamkar wata
aljannar duniya. Matar ta sa kai ta fice saboda ganin hankalin Saude baya kanta.
Ba ta jima da fita ba sai ga ta ta dawo hannunta riqe da plate da ke rufe, tare da pure water ta ajiyewa Saude ta juya ta fice. Jikin Saude har rawa yake wurin saukowa ta bude plate din, ta kafe idanuwanta saman abincin. Shinkafa ce jaloup babu ko wadatar kayan miya a cikinta. Saude ta sa cokali ta soma ci, sai dai bakinta ya gaya mata dan ba ta yi tunanin
shinkafar za ta yi dadi a yanda ta ganta ba.
Hannu ba ka hannu kwarya haka ta rinqa cin abinci, lokaci guda ta kawar da shi, sannan ta dauki ruwan ta fasa ta shanye shi tas. Tana sauke ledar ta saki wata‘ nannauyar gyatsa, idonta ya soma lumshewa ta yunkura ta haye kan gadon ta kwanta. Tana kwanciya wani barci mai nauyi ya dauke ta.
Ba ta sake motsawa ba sai lokacin da ta jiyo ana ta kiraye-kirayen sallar Asuba, ta yunkua ta mike tana faman zazzare idanuwa can ta hango wata kofa jikinta na rawa ta nufe ta, ta bude ta tsaya sororo ‘ tana kallo; 'an qawata wurin da kayan qawata bandaki. ‘ ' ‘ Da sauri Saude ta maida ta rufe dan ita a zatonta wani dakin hutawa ne, ta dawo ta zauna tana san yin
sallah amma ba ta san inda za ta kama ruwa ba, balle
, ta dauro alwala. Da ta gaji da zama ne ta koma ta
kwanta. ‘ Sai dai a yanzu ba barci take ba. idonta biyu, tana kwance tana tunani, wai ita ce yau a kwance saman
lallausan gado irin wannan, ko a mafarkinta bata taba tunanin hakan ba. Fargabarta guda yanzu yanda ta ga matar gidan da ganinta tasan bata da mutunci, dan tunkan su hadu wani irin tsoranta ya mamaye zuciyarta‘ Tana nan kwance tana juyinta, ita kanta ba ta san awannin da ta kwashe ba, ta ji motsin ana shigowa dakin ta yunqura ta tashi zaune tana kallon mai shigowar.
Matar Jiya ce ta shigo da sallamar ta, a yanzu ma hannunta na dauke da plate da cup a sama sai ruwa guda daya a dayan hannun ta ajiye, Saude da ke kan gado ta amsa mata sallamar ta tare da gaishe ta, ita kuma matar ta dan zuba mata idanuwanta kafin ta ce“Yau dai kin yi kwanciyar kadaici k0 ya ki ka ji gidan namu?”
Sande ta yi murmushi ba tare da ta tanka ba, matar ta Kara gyara zama tana fadar, “Kin ga dai matar gidan sai kin yi takatsantsan dan ba ta da kirki, yanzu dubi duk dukiyar mai gidan nan amma abincin su daban na masu aiki daban.
Haushi ya kama Saude a duniya ita akwai ta da surutu da naci amma ba ta iya gulma ba, dan haka cikin qosawa ta dubi matar tana fadar, ‘Don Allah inane bayan gida in je in kama ruwa har yanzu ban samu na yi sallah ba ”
Matar ta ce, ‘Wane bayan gida kuma bacin wancan.”
, Saude ta waro ido tana fadar, “Yanxu wancan kewaye ne?” Matar ta yi murmushi tare da fadar,
“Taso muje in nuna miki yanda za ki yi amfani da 'su
Saude ta yunkura ta mike ta bi bayan matar. Daya bayan daya ta rinqa nuna mata yanda ake amfani da komai da yake kwanyar tata a bude: take, a
take: ta dauka, don haka suka fito, matar ta tafi ita
kuma ta haye saman gadon ta janyo plate din ta bude, soyayyan dankalin turawa ne da kwai sai ruwan tea dan tsururu mai kama da fitsarin godiya. Dadi ya kama Saude yau za ta yi karin kumallon ‘yan gayu. Ta tisa dankalin tana ci tana faman santi a zuciyarta yanzu dama wannan shi ne rayuwar da masu aiki ke yi a gidajen da aka kai su aikatau? A gaskiya suna morewa don ita in dai za ta rinka samun abinci mai rai da motsi irin haka, to ai ba aikin da za,a sata a ,ciki batayiba bayan ta kammala sannan ta kwashe kayan ta ajiye gefe ta mike ta nufl bandakin ta dauro alwala ta tayi sallarta. Tana gammawa ta kishingida saman kafet din aiko nannauyan barci ya dauketa saiji tayi matarnan tazo tana tashinta ki tashi hajia nason ganinki
A falo yanzu nan da minti biyar Hajiya zata sauko ta ki gana da ita.”
‘Yan cikin Saude su kai wata masifar juyawa, alamun tsoronta ya bayyana a fili qarara. Matar ta-yi murmushi ta mike tana fadar.
“Hajiya na da matukar kwarjini a idanuwan kowa, ki dake ki fltO yanzu dan kar ta riga ki fitowa ki samu matsala.”
Ba ta jira abin da Saude za ta ce ba ta juya ta fice, ta yunkura da hanzarinta ta nufi bandaki ta wanko fuskarta da bakinta jikinta sai faman rawa yake tamkar wadda za ta gana da Azara’ilu ta fito falon, Wanda yake tas-tas tamkar ba a shigwarsa saboda tsabar gyara.
Saude ta raba daga qasa ta zauna zuciyarta na barazanar fashewa, don ta san yau za ta wuni anan ba ta fito ba. Sai dai da mamakinta ba ta kai minti biyar da zama ba ta jiyo Kamshin turarenta mai kwantar da hankali, zuciyar Saude ta tsananta bugawa da sauri-sauri, tamkar ana buga ganga, da Kyar ta iya daga kai kadan ta dan saci kallonta.
Sanye take da wata dakekiyar shadda baka ‘yar Mali, dinkin riga da siket sun bala’in kama ta, an yi mata aiki da jan zare da fari da kuma kore, kwalliyar nan da gani ta kanti ce, tun daga hannuwanta zuwa qafafuwanta da wuyanta gwala-gwalai ne sai daukar ido suke takalmi ne baki mai masifar tsini a Kafarta.
A yanzu idanuwanta rufe suke da baKin gilas din da . ya mamaye mata fuska,‘da makullin mota rike a hannunta tana kadawa, ta qaraso ta zauna saman daya daga cikin kujerun da ke baje a falon ta dora
Qafa daya kan daya tana kadawa Saude ta zube tamkar mai shirin yi mata sujjada. Asma ta taBe baki tana yatsina fuska tamkar wadda
ta ga abun Kyama ta daga mata hannu.
“Ya isa bana san yawan gaisuwa, ya ya sunan ki?” . ~ Muryarta na rawa ta ce, “Sande.”
Ta yamutsa fuska tamkar ba .za ta sake magana ba can ta ja fasali kafin ta ce, “Malama Saudat na san dai kin san nan k0 gidan waye a qasar nan aka kawo ki ba ki da bukatar sai na maimaita miki?”
, Ta dan yi shiru tamkar wadda maganar ke mata ‘ wahala kafin ta ci gaba, “A dan jiya zuwa yau nasa a , dan yi mini binciken ki a bugi cikin ki dan a fahimci idan kina da yawan surutu. Is oke zuciyata ta nutsu da na dauke ki aiki, ni dai ba mazauniya ba ce ‘yar siya ce ba ni da time din kaina ma ballantana na wani, kullum cikin sabgogina nake;
Don haka na ce a samo mini yarinya mai nutsuwa wadda _zata kula da maigidana. za ki tsaya ‘yar aiki a sashin maigidan, idan ki ka gaza kula da shi kuma zaki fuskanci fushina. Aikin ki shine zaki rinqa kula da abincinsa, abin shansa,
gyaran sashinsa, wurin hutawarsa. Ki nutsu ki fahimci abubuwan da yake so da wanda baya so akwai lokutan da baya san magana, ki nutsu ki fahimta kar ki kuskura ki rinKa cika shi da yawan
magana, baya san yawan kallo koda yaushe yana bukatar abu mai sanyi kusa da shi Yana cin abinci sau hudu a rana, yana shan fruits
da daddare around 12:am kuma yana shan coffee, yana tashi daga barci qarfe bakwai, yana motsa jiki a lokacin da ya farka yana gamawa zai sha tea, sannan ya tafl ya watsa ruwa. Yana karyawa da misalin
Qarfe goma na safe.
‘ Wannan shi ne tsarinsa, da fatan za ki kula, duk yan aikin da na daukar masa rashin fahimtarsa ne da basayi kesa inakorarsu. Ayanzu kece damata ta qarshe daga ke idan ki ka kasa kula da shi ba ' buKatar a Kara kawo masa wata, don haka ki tsaya ki nutsu ki fahimce shi ban san sakarci, idan kin yi aiki irin yanda yake so ni zan rinqa biyanki nera dubu ashirin duk wata. Da fatan kin fahimta?”
Saude ta daga mata kai a sanyaye, amma . a kasan zuciyarta ta yi masifar karaya, don ta san ba ma zata iya ba yaudarar kanta kawai ta yi da ta amsa. '
Asma ta yunkura ta mike ta dubi matar da ke tsaye wadda da alama ita ce ma’aikaciyar sashinta, tace “Ki ba ta kayan ta saka, aikinta zai fara daga
[1/22, 10:28 AM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/24, 9:31 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*

*CHAPTER 15*

gobe qarfe biyar na yamma, ina da taro a Hotel sai na
dawo." Ta juya ta fice abin ta babu maganar mayafi
Matar ta mikawa Saude wata leda tana fadar, “Wadannan
su ne kayan da za ki saka.”
Saude tasa hannu ta karbi kayan jikinta a sanyaye.
Matar ta yi wani takaitaccen murmushi tana fadar, “Ya na
ga farawa da iyawa har kin yi la’asar, haba Saudat kar ki
karaya mana ki batawa Hajiya rai kin dauke ni matsayin
Auntynki ki yarda da abin da zan fada miki, ki sawa zuciyar
ki za ki iya abin da aka saki da kuruciyar ki ai babu abin da
zai gagare ki-Maigidan ‘mutum ne mai saukin kai yanayin
rayuwarsa irin ta Turawa ce idan dai ki ka nutsu komai zai
zo miki da sauki, kin ji?”
Saude ta daga mata kai alamar eh sannan ta karbi kayan ta
koma Bangarenta ta fada kan gadonta da. kayan zuciyarta
na barazanar
fashewa.
Tsawon Iokaci ta dauka tana saka da warwara, , sannan ta
yunkura ta tashi zaune ta zazzage kayan daga ‘cikin ledar
tana daddagawa. Suite ce baKaKe riga da siket sai ta cikin
fara, ta tsaya tana kallon
kayan sun burge ta sosai, ta linke su ta maida a leda.
Ta yunkura ta sauka daga kan gadon ta janyo abincin da
Aunty ta kawo mata ta bude
Tuwon shinkafa ne da miyar agushi, Saude ta zauna ta ci
abincinta sosai ta gama ta mike tayo alwala ta dawo ta yi
sallah sannan ta koma ta
kwanta.
Sai dai fargabar da ke zuciyarta babu abin da ya canza
yinin yau haka ta yi shi, ba kuzari a jikinta tana tsoron abin
da zai iya faruwa idan ta kasa yin abinda Asma ta sanya ta
ba ta san irin hukuncin da za ta yanke mata ba qila ma ta
iya kashe ta kawai.
'Zuciyarta ta kara tsinkewa wasu irin hawaye masu zafi
suka taru a idanuwanta, watakila ajali ne ya kawo ta gidan,
tasa hannu ta goge ‘yar kwallyar da ta tarar mata ta juya
daga gefen da take ta lumshe idanuwanta, amma ba barci
take ba.
Washe gari Saude na zaune a qasa gefen gadonta, tana
tunanin da ya zame mata jiki, zuciyarta ta lula duniyar
tunanin Hamid da irin kulawar da ya. ba ta a rayuwa. K0 a
yanzu ba ta fidda rantaba tana ji a jikinta za ta koma gida ta
same shi, tana ji a jikinta shi ne mijin da zai aureta su yi
rayuwarsu cikin kulawa da Kauna.
Aunty ta turo kofa ta shigo tare da sallama, Saude ta bude
idanuwanta tana amsawa. Aunty ta tsaya daga bakin kofa
tana fadar, “Ya na gan ki anan zaune, k0 kin manta ne yau
ne ranar da aikin ki zai soma?”
Saude ta kalli tace Na sani Aunnty ba ta ce sai Karfe
biyar ba?”
Annty ta yi wani takaitaccen murmushi kafin ta ce “YallaBai
ya yi tafiya zuwa qasar China sati ukun da suka wuce, don
haka yanzn za ki tashi ki fara gyara masa Bangaren shi ki
zauna har ya iso.” Ta wurgowa Saude makullai tana fadar,
“Ungo
wannan sune makullan bangaren sa.”
Saude ta cafe lokacin da bugun zuciyarta ya tsananta,
Annnty ta juya tana fadar, “Ki tashi ki shirya ina falo ina
jiran ki na raka ki Bangaren nasa.”
Saude ta taKarKare ta mike ta nufi bandaki ta dade a tsaye
zuciyarta na faman kaiwada komowa, sannan ta daure ta
watso ruwan ta fito, ta zauna bakin gadonta ta ciro kayan
daga cikin ledarsu ta sanya kamar yanda Aunty ta nuna
mata, ta mike tsaye siket din bai Karasa isowa kasa ba ya
dai wuce gwiwoyinta, sannan ta janyo hijabinta ta sanya
sannan ta kawo takalmin da ke cikin kayan ta saka wanda
yake sawu-ciki, sannan ta fito ta samu Aunty zaune tana
jiranta tana fitowa suka jera suka fita. ~ '
Gaba daya suka fita daga wannan shashin, suka . nufi daya
Bangaren wanda ke hagu. Aunty ta karBi makullin ta bude
sashin suka shiga, komai na sashin irin na wancan ne, babu
abin da ya bambanta. Aunty ta mika mata makullin tana
fadar.
“Ga shi ki goge komai ki gyara,idan kin gama. Ki zauna har
ya iso, da ya iso ki karbi jakarsa ki kawo masa abu mai
sanyi kin ji?“ Saude ta daga mata kai ' alamar eh.
Sannan ta juya ta tafi ta bar ta tsaye tana faman bin
katafaran falon da kallo. To ta ina ma za ta fara? Ita dai a
iya ganinta ba ta ga abin da ya yi datti ba, ta taBe baki
sannan ta fara takawa saman matattakalar ‘ ‘ benen ta
shiga cikin falon, kai tsaye wani qaton falo ne ta fara shiga
wanda, har yafi na farkon haduwa da tsaruwa.
Idanun Saude suka sauka saman wani makeken hoto
wanda yake jingine a kasan gefen bango, ta danci gaba da
bin hoton da kallo. Wani kyakkyawan namiji ne ajin qarshe
wanda shekarunsa ba zasu‘ wuce talatin da biyar ba, kallo
daya za kai masa ka tabbatar ya hadu tamkar wani
Balarabe, yana rungume da Asma sunyi murmushi'su duka,
sun yi * masifar kyau, dama duk kyan Asma bata kai
mutumin ba, duk da yana namiji, don shi kalar kyansa yafi
kama da na Larabawa saika rantse Balaraben Saudiyya ne
Saude ta wuce a hankali ta shiga zagaye falukan sashin da
bedroom din dake ciki, ita kanta tana ,tausayin kanta
saboda sashi~sashin dake ciki sun kai
goma, haka ta dauko mofa da tsintsiya da tawul da .bokiti
ta fito ta shiga gyaran sashin,‘
Sai da ta gyara ko’ina da ina ta goge tare da kunna bona
bonar da ke falukan kowacce ta zuba turaren 'wuta a ciki,
sannan ta dauki room fresner ta dinga feffesawa a ko’ina
da ina, ta Kara gudun A.C sannan ta rurrufe ko’ina kamar
yanda Aunty ta fada mata, ta dawo falon qasa ta zauna
gefen kujera tana faman zare na mujiya, sanyin A.C na
ratsa ta. A take tamkar ta kwanta saboda tsabar gajiyar da
ta yi.
Misalin Karfe biyar da ‘yan mintina Saude ta ji an turo Kofar
falon ta zabura ta tashi tsaye kirjinta na wani masifar
bugawa da qarfl da qarfi. Shi daya ne ya shigo yana sanye
cikin shigar Kananan kaya, sai wani yaro da ke bayansa
wanda ke sanya da suit, yana rataye da irin jakar
ma’aikata.
Ahmad ya tsaya yana watsa mata wani irin kallo
wanda ya Kara hautsina mata‘ yan hanji, muryarta da rawa
ta fara fadar, ‘Sannu da zuwa
‘ Shut up! You are very stupid, get the hell out of here
Jikin Saude ya hau Bari ko’ina na jikinta rawa yake ga shi
dai ba ta san tsiyar da ya fada ba, amma yanda ya kwatsa
mata tsawa, ya tabbatar mata da korarta yake don haka jiki
na Bari ta gifta zata wuce, Ahmad ya kara daka mata
tsawa.
“Wait, na ce ki tsaya.”
Saude ta ja ta tsaya, sai faman kyarma, take, don yanda ta
ga tsantsar Bacin ransa ta tabbatar zai iya
kai mata duka cikin bacin rai yace hope baki dai hau min
sama ba?"
Saude ta yi shiru tana faman rawar murya, yaja wani dogon
tsaki ya wuce ciki, jikin ta yana rawa ta wucc, sai faman
harde qafafuwa taka , har tabar falon.
A tsaye ta samu Asma sanye da wata doguwar riga milk
colour, ta dora dan qaramin mayafi saman kanta wanda ya
tsaya iya wuyanta, gilas dinta yau a hannu yake tare da
makullin mota da alama fita za ta yi. ‘
Saude na shigowa ta tsaya tana kallonta, cikin tsantsar
takaici take kallonta, jikinta ya qara yin la’asar tana shirin
dukawa ta gaishe ta ta ji saukar wani mahaukacin mari' har
sau biyu, dama da hagu,
* wanda yasa sai da ta kifa cikin takaici Asma ke fadar.
“Ashe ke dakikiya ce ban sani ba sakarya, jaka ce keba?
Dube ki, dubi abinda da ke jikin ki, yanzu da wannan bakin
abun ki ka shigar masa ne? Oh! Kin gama dani, amma kin ci
sa’arsa da ya kyale ki da kin gane baki da wayo, don na
tabbatar yau k0
' ruwa ba zai iya hadiya ba.” Ta ja tsaki mts! Ta juya ta dubi
Aunty wadda ke« tsaye tace, “Rabi maza Id debo mata
kayan shafawa da turarurruka, ta cire wannan bakin abin ta
shirya, ki tabbatar ta koma ta ba shi hakuri, Wallahi
idan ki ka sake yaqi amincewa da ke zama ‘yar aikinsa na
rantse miki sai kin fuskanci fushina kin ji na rantse.”
Ta'Karasa maganar da karfi, sannan ta juya ta yi gaba abin
ta.
Wasu irin hawaye masu zafl suka biyo kuncin Saude, wayyo
Allah wannan wace irin rayuwa ce ta samu kanta a ciki?
Au'nty ta dafa ta muryarta a . sanyaye. .
“tace kizo mu je, kada dan

Please Login or Register in order to submit comment