Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji labarin kin tsaya kin saurari matsiyacin yaron nan na rantse da Allah sai
na lahira ya fi ki jin dadi, ‘yar iska tambadaddiya.’ Ta sa qafa ta haure ta sannan ta wuce
Saude ta dauki bokitin tallarta tasa kai ta fita, tana faman sharar kwalla. Rayuwa kenan ita dai ta san ba ta daga cikin wadanda sukai sa’ar rayuwa a duniya.
Tana tafe tana sharar kwalla tana zancen zuci, ba ta ankara ba sai dai ta ga mutum a gabanta, wani irin kallo yake mata mai cike da mamaki muryarsa a sarkake ya ce Lafiya Saudat, wace irin shiga ce wannan laflyarki qalau kuwa?”
' Saude tasa hannunta guda tana goge hawayenta, ta soma magana cikin kuka.
“Lafiyata lau don Allah ka yi hakuri ka flta daga rayuwata na roqeka.”
Hamid ya girgiza kai yana fadar, “Impossible, wallahi abin da ba zai taBa yiwuwa ba kenan, sai dai idan har son ki zunubi neto na ratayawa kaina alhakinsa, amma ba zan taBa barin ki ba.”
Saude ta tsaya da kukanta tana kallon shi kafin
ta ce, ‘Me yasa ba xaka rabu da ni ba, k0 kana san jefa zuciyata ne cikin bala’in da ba zan iya flta ba? . Wannan kukan da ka ga ina yi duk ta dalilinka ne.” Hamid ya ce “Na ji na dauka, amma don. Allah ki yi hakuri ki bani kadan daga cikin labarin ki ni
nayi miki alkawarin taimaka miki da duk wata gudun mawar da kike buqata."
Hawayen da suka tsaya da zuba daga idanuwan saude suka Ci gaba da zubowa tana sharBar majina kana ta fara magana.
“Kamar yanda ka sani sunana Saude, tunda na . tasona bude idanuwana na ganni tare da Yayana,shine uwata shi ne ubana shine komai nawa. Bai barin nayi kuka , kullum burin shi ya samamin farin ciki da gatan da na rasa a rayuwa,
Ni kuwa burina kullum in matsa masa in sanya shi yimin abinda baidai konyinsa
Hamid ya ce, “To yanzu yana ina shi Yayan naki?
‘ Saude ta Kara rushewa da kuka kafinn ta ce . an raba ni da shi, su suka raba ni da Yayana.”
Ya ce, ‘Su waye?’
Muryarta na rawa cikin kuka ta ce, “Baba da inna Laure.”
Hamid ya ja wani numfashi mai nauyi yana jin yanda take ta faman kuka da shashsheka tausayinta mai tsanani ya shige shi, muryar shi a sanyaye yake magana.
“Ina mahaiflyarki da mahaifinki su ke?"
Saude ta ce, “Ban san inda mahaifiyata take ba,
Ban taBa ganinta ba, wannan kuma da ka gani shi
ne mahaifina, Inna Laure kuma matarsa ce ‘yar Baba ita kuma qanwata ce
Hamid ya sake sauke wani nannauyan numfashi ya fahimci yarinyar tana cikin matsala, ya zuba mata idanuwansa farare tas cikin sanyin muryarsa ya ce, “Ki yi hakuri Saudat na fahimci irin abin da ki keji a zuciyarki, ki kwantar da hankalin ki insha Allahu na yi miki alqawarin taimaka miki da dukkanin karfina in dai ina raye sai na daga darajarki a duniya, sai kuma na wanzar da murmushi a idanuwan da Yaya ya bari cikin hawaye.”
Ya dan qara numfasawa kafin ya ce “Ki je
" 'lallar ki dawo, zan zo da daddare in same ki wurin tallarki za mu yi magana, amma don Allah ki daina kukan nan haka nan kin ji?”
Saude ta daga masa kai tana goge hawayen da
ke fuskarta, ya dan tsura mata ido da murmushi a kumatunsa ya ce, “To dan yi murmushi mana beauty
*Dukda batasan abindayace ba,ammatayi murmushin kuma kalmar beauty din ta yi mata’ dadin sauraro a kunne. Sai da ya ga tafiyarta
sannan shima ya juya ya tafi zuciyarsa na raya masa abubuwa masu yawa.
Da yamma likis Saude ta dawo daga wurin tallarta Laure ta jibgo uban wanki, sannan tace ta ' dora sanwar tuwan dare. Saude ta duka a gun ta yi kukanta har ta gaji sannan ta ja ruwa ta dora sanwar ta dawo ta ci gaba da wankin.
Ana gama sallar Magariba Malam Bala ya dawo gidan, Laure ta shimfida masa tabarma a
tsakar gida ta kawo masa fura da mafici ta zauna gefensa.
Malam Bala ya bude furar ya soma sha, sannan
ya dubi Laure yana fadar, “Wai ya suka yi da yaron nan ne Laure?”
Ta taBe baki tare da furta, “Uhmm! Malam kenan, ai yaron dan iska ne takadari kana ganinsa kamar na kirki suna hira da ‘Yar Baba ya nemi taushe ta cikin zaure Allah ya rufa asiri yarinyar nan ta yi ihu, na kwaso da gudu na raka shi da bakin wuta har waje, mutane na ta bani hakuri suna fadar in kyale shi ai ni’wannan abu ya ci min zuciya wallahi har kuka na yi.
Yanzu dan kawai an gan mu talakawa matsiyata shine za a shigo har cikin gida a ci zarafin mu. Kai Malam wannan abu da me ya yi kama?” .
Tunda ta fara zancen ‘ya’yan cikin Saude suka fara juyawa wani irin gumi ya shiga tsatstsafo
mata, take juwa ta kwashe ta, sai dai ta ganta zaune a gefen bokiti.
Malam da tunda ta fara zancen ya hau sallallami, ai sai ya rufe furar yana fadar, “Wai harni za a ciwa mutunci a garin nan Laure na rantse miki da Allah sai na yi kararsa kotu, kuma ta addinin Musulunci.”
Laure ta ce ‘Aa, Malam abin ai duk bai kai na kotu ba wurin mahaifinsa za ka gobe tunda sassafe ka kai qararsa ka ce ya jawa dansa kunne ga abin da ya yi maka in ba haka ba za ka sa hukuma ta
(shiga tsakaninku.”
Bakin ciki ya cika malam Bala ya zabura ya
mike ya suri buta ya nufi bandaki.
Laure ta tabe baki ta raka shi da harara a zuciyarta tana fadar sauna kawai. Ta yunkura ta mike ta dubi Saude da ke 'zaunc ta ce, “Toke kuma tsohuwar munafuka kin zauna kin kasa kunne kina sauraran jama‘a sai ki tashi ki dauki tallar gyadar ki tafl idan kin dawo kin qarasa wankin tunda cinikin na yauzu ne."
Saude ta lallaba ta mike tana jin tamkar za ta
fadi ta dauki tallar ta ficee, kuka maya gagareta idanuwanta sun yashee babu komai cikin zuciyarta sai duhu. ' ‘K0 minti goma bata yi da zama ba ta hango shi ya nufo inda take; yau sanye yake cikin manyan kaya, ‘na wani lallausan yadi milk colouz; mai hasken gaske dukda a'cikin duhu ne amma bata kasa ganin shekin yadin ba, kansa yana sanye da hula baka yasa bakin takalmi a Kafafuwansa, tun kafin ya Karaso kamshin tuiarensa ya daki hancin Saude ta lumshe idanuwanta, sai a lokacin wasu
hawaye suka tarar mata ’ Hamid ya yi mata sallama tare da durKusawa gabanta, muryarsa a sanyaye ya ce “Sannunki yan matana barka da Kokari.” '
Saude ta bude idanuwanta tana kallonsa. hawayen da suka taru a kwarin idanuwanta suka ziraro ‘ ‘ Hamid ya mike tsaye ya ciro farin hankicif
Dinsa daga cikin aljihu ya miqa mata, Saude ta girgiza masa kai don ta san k0 rike hankicif dinma kadai ta yi sai ya yi dauda, to balle ta goge fuska dashi wai sunan wani wai shi ‘
Danduwala.
. Hamid ya sake mika mata hankicif. din yana fadar :‘Wallahi sai kin goge garama ki karBa kawai” ‘
' Jim yanda ya yi saurin rantsuwar ne yasa Saude
ta amsa ta goge hawayen, ya ce, “To bani abuna”
Ta yi wani dan taqaitaccen murmushin da bai , wuce kan labbanta ba ta ya qara goge fuskar shi da shi sannan ya saka a aljihu yana fadar.
“Wannan tafiyar yau ba ta ki ba ce wurin Baba nazo don haka ni kin ga taflyata."
Bai jira abin da za ta ceba ya juya ya tafi abinsa zuciyar Saude ta qarasa karyewa ta kifa kanta saman kayan tallar tana rera wani irin kuka mai cin zuciya. .
Hamid ya karasa Kofar gidan da qarfin zuciyarsa ya aiki yaro ya yi masa sallama da Malam Bala. Yaron bai jima da fitowa ba ya ce ga ‘ shi nan zuwa, sai ga Malam Bala ya fito da alama masallaci za shi saboda an fara kiran sallar Isha’i, yana ganin Hamid a qofar gidansa ya ja ya tsaya yana fadar.
“Malam laflya?”
Hamid ya durKusa har qasa yana gaishe shi. Malam Bala ya ce“Kai dakata ban san rashin kunya ka ji har ni za ka dauka mutumin banza da WOfl, to ka je komai ka yi dan kanka ka, Allah ya isa tsakanina da kai, duk da ka gan ni talaka ina da wadatar zuci.”
Mamaki ya kashe Hamid ya dago yana kallon
Malam muryar shi cike da rudani ya ce Don girman Allah ka yi hakuri Baba wallahi ban san abin
da nyi ba wanda kake fadarsa a yanzu« Malam Bala ya ce ‘Ai dama ba zaka san abin da kake; fada a kansa ba, tunda ka ci idon dan akuya ' amma abin da nake so da kai anan shi ne ka tashi ka ba ni Wuri kar in sake ganin ka gifta k0 qofar gidan nan, kuma zanje in samu mahaifin naka ya yi maka tsakani da‘ ya yana mutumin banza kawai’ Yana gama fada ya juya zai tafi, Hamid na kiran ‘ Baba don Allah ka saurare ni, amma bai kula shi ba , ya yi gaba Wani abu ya tsaya zuciyar Hamid, ya lallaba . ‘ ‘ya mike jikinsa ya yi masa masifar sanyi ya nufi ’ inda Sande take zaune tana faman raira kukanta. ‘ ‘ « Tausayinta ya lullube shi ya kura mata ido ' na wani dan lokaci kafin ya soma magana muryarsa a ' sanyaye ya ce“Ba zan hana ki kiyi kuka ba Saudat, « dan zubar hawayenki ya zama dole na fahimci abin da aka shirya mana, amma don Allah ki yi haquri kamar yadda na dauki alkawari’n taimaka miki ba . zan fasa ba Saudat da yardar Allah sai na ga rayuwarki ta inganta, kar ma Wannan abun ya dame ki ki yi hakuri kinji share hawayen ki karma ki Jawa kan ki
. ciwon kai” ' Ya samu ya lallasheta ta yi shiru sannan ya tafi zuciyarsa na faman saqe-sake ‘
Washe gari da sanyin saflya Malam Bala ya shirya ya nufi gidan Alhaji Bashir saboda yanda Laure ke ta faman ingiza shi. A kofar gidansa ya same shi zaune saman mota da News paper a hannunsa yana dubawa.
Malam ya yi masa sallama, Alhaji Bashir ya dago tare da amsa masa cikin sakin fuska ya miqa
. masa hannu su kai musabaha. Malam Bala ya ce
‘Dama Alhaji wajen ka nazo.”
Alhaji Bashir ya ce, ‘To mu shiga daga ciki k0?”
“A’a daga nan ma ya isa, Kara na kawo maka.”
Alhaji Bashir ya ce, ‘Kara kuma tawa?”
Ya ce ‘Danka Hamid na kawo maka qararsa ka ja masa kunne dan kuwa ya shiga har cikin gidana zai keta mini haddin‘ ya shi yasa na zo wurinka na kawo maka kashedinsa, don kar naje in dauki mataki kaga anatare babu dadi,don haka nazowurinka kai masa kashedi da iyalina.”
Alhaji Bashir da ya nutsu yana kallonsa mamaki ya dabaibayeshi muryar shi a sanyaye ya ce, “Lallai ka haifi yaro ba ka haifl halinsa ba, don Allah ka yi haquri Malam in dai nina haifi Hamid ya gama bi k0 ta gefen gidanka kayi haKuri don Allah, don Annabi.’
Malam ya ce, “To ni dai kashedi na kawo maka
ka ja masa kunne.’
Alhaji Bashir ya ce, ‘Insha Allahu.” Sannan ya juya ya Lafi buzun-buzun.
Alhaji Bashir ya sauke wani gwauron numfashi, sannan ya yunqura ya nufl cikin gidan zuciyarsa a cunkushe ya shiga falon gidan, babu kowa a falon sai Hajiya Hanifa tana tsaye tana goge-gogenta a falon, yana shigowa ta tsaya da aikin da take tana kallon maigidan nata bakinta na fad'ar.
“Latiya dai k0 Alhaji?”
Muryarshi ba dadi ya ce, “Ina yaron nan yake?”
Hajiya Hanifa ta ce, “Yana dakinsa ka san ai bai farka ba yanzu.” Alhaji Bashir ya ce tado mini shi maza-maza.
Jikin Hajiya Hanifa na rawa ta nufi kofar dakin Hamid din. ta kwankwasa masa yana kwance nannad‘e cikin bargo yana Sheqa barcinsa, saboda rashin baccin da ya samu jiya.
Ya bude idanuwansa tare da yunkurawa ya mike, yazo ya bude kofar, Hajiya ta dube shi kafin ta ce “Ka je Abbanka na falo yana jiran ka Ya amsa da. to, sannan ya juya ya koma ciki ya nufi bandaki ya wanko bakinsa da fuskarsa sannan ya fito ya dauko jallabiyarsa ya sanya ya fito
Alhaji Bashir yana tsaye inda yake har Hamid ya qaraso yana qokarin dukawa ya gaishe da mahaifin nasa, ya ji saukar wani gigitaccen mari ya ratsa .
Kunnensa ya dago da sauri yana kallon sa, cikin Bacin rai Aihaji Bashlr ya soma fada“Ni zaka dauka dan iska k0 Hamid dama abinda. ka koyo kenan a qasar wajen da na tura ka. Ni zaka jawa; abin fada a cikin garin nan. To baka isaba., maza ka tattara yanaka-yanaka ka koma Kaduna, yau
ba sai gobe ba ka je ka kula da kamfanina tunda aikin gwamnatin bai zama dole ba, ba zaka zauna nan ka ja mini abun kunya ba, dama shi yasa da aka ce ka je ka nemi yarinyar nan Zainab kaqi saboda ba ka gaji da barbada ba, ka yi daidai ka kyauta tashi ka ba ni wuri.’ Jikin Hamid ya yi matukar yin sanyi ya miqe a sanyaye tare da fadar, “A yi h akuri." Ya juya ya koma dakinsa ya kwanta, tunani ya addabi zuciyarsa ‘ya rasa hanyar da zai bi ya taimaki yarinyar nan, ya ‘ lusmhe idanuwansa yana jin wani abu na masa
yawo.
Ya san fushin mahaifinsa yana fushi da shi ya yi kwana uku, tabbas kuma dole ya tafi Kaduna tunda ran mahaifin nasa ya Baci, ya lallaBa ya mike ya cire jallabiyar da ke jikinsa ya fada bandakin da ke cikin dakinsa.
Saude ta dawo daga tallan safenta ta iske Laure Zaune itada Malam Bala suna tattauna magana!
Hamid, ta a jiye bokitin wainar ta 'bama Laure kudin, ta karba tana kirgawa sannan ta ,dubeta tana fadar.
“Jeki ga wake can ki kai markaden alala.”
Saude ta amsa da to, sannan ta wuce Malam Bala ya dubi Laure yana fadar, “Kin ga na ma mance, Malam Garba ya fada min za"a kawo kayan sa ranar yarinyar nan gobe
Laure ta cc, “Ai garama a gaggauta Malam mu kawar da yaran nan mu huta.” ‘
Iya abin da da Saude ’ta ji kenan ’ta fice tana jin tamkar za ta kifa saboda tashin hankali da fargaba. Haka ta je ta kai markadan ta dawo ta dafa alalar duk Laure na zaune tana kallonta, ta gama ta zauna ta Kirga mata a bokiti, sannan ta dauka ta tafi
Hamid da ke kokarun sanya jakarsa a mota ya hango ta ya rufe motar da sauri ’ ya nufo ta da murmushi a fuskarsa ya ce, “Ranki shi dade barka da
fitowa.” Saude ta waigo tana kallonsa kafin ta gaishe shi
da dakusasshiyar muryarta. Hamid yargyara tsayuwa yana fadar. “Dama ke nake jira ki taho mu yi magana da tun dazu na Hamid ya ce ‘Kinga wannan fitowar wallahi Kaduna zan tafi yanzu yanzun nan mahaifina ya tura ni amma karki damu kwana uku kaWai zan yi in
dawo saboda maganar ki, akwai wata hukumar kula da haqkin mata zanje ofiss din su a kan maganar ki
Saude ta daga masa kai alamar eh ya yasa hannu cikin aljihu ya Ciro kudi masu yawa ‘yan yan naira dari biyar biyar guda ashirin ya miqa mata yana fadar ‘Ga wannan ki riqe ki yi amfani da su kafin in dawo.”
Saude ta zaro idonta wadanda suka ciko da hawaye, ta girgiza masa kai alamar a’a, Hamid ya hade fuska yana kallonta ya ce “Karbi na ce mana me ye haka?” ‘
Ganin yanda ya hade fuska yasa Saude ta sa hannu ta karBa tana fadar, “Na gode.’ Ya zaro wata waya cikin aljihunsa ‘yar qarama mai kyau ya mika mata.
“Ga wannan ki riqe ta hannun ki zan rinka kiran ki mu yi magana.”
Saude ta karBa ya juya yana fadar, “Sai na dawo.” Saude ta juya da niyar taflya su kai ido hudu
da ‘Yar Baba tana tsaye tana kallon su, suna hada ido ‘Yar Baba ta ja kwafa tana kada kai ta wuce 'Hankalin Saude ya yi masifar tashi wasu zafafan hawaye suka biyo kuncinta ta ji tamkar ta zubar da kudin saboda firgita, cikin tsoro ta je tallar yau ta dawo cike da tsoron irin hukuncin da za ai mata. Haka ta shigo gidan ‘tana faman sanda kamar munafuka a tsakar gida ta samu Laure da dillaliya
suna zaune. Ita iyan tana kan tabarma, ita kuwa dillaliya tana kan kujera ‘yar tsugunne. Saude ta durkusa tana gaishe da dillaliyar sannan ta mikawa Laure kudin tallar nata, ta karBa ta sake mika mata hannu.
“Ba ni sauran wanda kwarton naki ya baki
Jikin Saude na rawa ta ciro kudin da wayar ta mika mata, Laure ta shiga jujjuya wayar a hannunta da kudin tana taBe baki ta dubi dillaliya tana fadar.
“Duba ki ga fa.”
Dillaliya ta karba tana gani, ta dago tana kallon Laure tana fadar, “Amma ni sai nake ganin kamar wata banza ce ta sauko muku daga sama, kawai ki yi kwance-kwance kinada abun duniya idan ma yaudara ce ta kawo sa ke dai me ya dame ki ita ta jiyo.”
Laure ta ce, “Hmm! Dillaliya kenan ba zaki gane ba yaron fa da gaske aurenta zai yi ba wai da wasa ba.”
Dillaliya ta dan yi shiru kafin ta ce, “To yanzu ya ki ke ganin za a yi?”
Laure ta ce, “Gaskiya na fara tsora ta da lamarin nan karfa danhakin dakaraina yazo yatsone maka ido. Shi yasa na kira ki kawai ki dauke ta ki tafi da ita AIKATAU cikin gidaje har zuwa lokacin bikinta shekara guda za a sanya ranar daurin aurenta sai ki taho da ita kawai kin ga na yi maganin takadaranci k0 ba haka ba?” Dillaliya ta ce, “AI ko kin kawo shawara Laure, Abuja ma zan tafi da ita gidan wani sabon dan Majalisa, mai tashen kudi, wata kawata ce ta yi min maganar kai masu ma’aikata gidan, don haka ta shirya gobe zan zo in dauke ta da sassafe mu tafl, duk wata
kina da dubunki biyar zan rinka karBo miki na albashinta.”
Dadi ya kama Laure ta ce “Allah ya kai mu Kawata, tun Asuba ma zan tasheta.”
Dillaliya ta ce, “Amma kina ganin ba za mu samu matsala da mahaifinta ba?”
Laure ta ja wani gajeran tsaki tana fadar, “Ke kuma da sokawa zance wuqa kike wannan qotan wake san ya shi a lissafi ai sai yanda na yi da shi.”
Dillaliya ta ce “To shi kenan babu matsala ‘yar
uwa. ‘ . Duk labarinsu Saude tana jiyo su daga daki tana zaune saman simintin dakin kanta na jingine da bango, wasu irin hawaye ne masu zafin gaske kebin kuncinta. Wayyo duniya ita dai ta san ta zo duniya a rashin sa’a. Haka ta ci gaba da rera kukanta babu mai‘lallashinta.
Washe gari Karfe takwas kamar yanda dillaliya ta
fada ta zo cikin shirinta Laure ta tiso qeyar Saude a
gaba, ta hada ta da dilla'iyar tana faman zuba mata kashedi.
‘Kl kulada aikin da za,a baki kuma banda dan hali, dan wallahi kika sake ki ka yo abin da za a koroki ki ka dawo min lokacin dawowarki bai yi ba wallahi saina shake ki kin mutu kin ji na fada miki, kuma kinsan zan iya
Ta zaro naira dubu cikin kudin da Hamid ya ba ta, “wanda ta kwace, ta mikawa dillaliya tana fadar.
“Ga wannan kiyi kudin mota.” Dillaliya ta karBa ta tisa Saude gaba suka tafi.
Sai a lokacin wasu hawaye masu zafi suka samu damar zirarowa daga idanuwanta, tana ji tana gani suka nufa tasha cikin‘ yar qaramar motar nan Kurkura.
Suna sauka dillaliya ta kama masu motar Abuja suka “ hau, dama. saura mutum uku, aka samu wani namiji
yakarasa cikon na ukun direbaya dauhanyar Abuja.

ALHAMDULILLAHI MASHA ALLAH _
Sai mucewa matafiya Allah ya kaisu lafiya. .

Mu hadu a littafi na biyu
Donjim yaddah wannan lbrn zaici gaba da kaYAwa
[1/19, 5:14 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[1/22, 10:28 AM] I love my mum: *YAR TALLA*

BOOK 2

*CHAPTER 14*

TUNda suka fara tafiyar Saude ke raira
kukanta, a hankali har sai da suka kusa
kawowa Suleja, sannan wani bacci mai
nauyi ya dauketa Ba ita ta farka ba sai da ta ji
Dillaliya na tayar da ita, Saude ta bude ido ta ga har
sun kawo tasha, mutane na ta fita, sannan ita ma ta bi ayarin masu fitan
Tun da suka sauka tasha Saude keta faman zare na-mujiya, ta zo garin da ba nata ba, za ta iya rantsewa tunda take ko gidan Mutum Daya bata taBa zuwa ba, to balle ta tsallaka Kano k0 wani garin da ke kusa‘ da su, amma yau ga ta cikin ‘Abuja tsamo-tsamo. Ikon Allah. .
Dillaliya ta tsaida musu tasi tasha suka shiga, Saude dai na biye da ita da idanuwa sai faman waige-waigen idanuwa take. A hankali ta ga sun shigo cikin rukunin wata unguwa wadda kai tsaye za a kira ta da G. R.A
Unguwar shiru ba ka Jin motsin komai sai kukan tsuntsaye da haushin karnuka ga manyan shuke shuke da suka sa titin unguwar tsakiya, kowane gida ka kalla ka san na wani kusan ne, gaba daya babu gidan da bana wani babban mutum ba a unguwar.
Saude na cikin kallon jerin gidajen ta ji Dillaliya na fadar.
“Nan za ka ajiyemu.”
A hankali Saude tabi kofar gidan da aka ajiye su
din, wanda za ta iya rantsewa tunda suka taho gidaje
kadan ne suka kai shi kyau da tsaruwa. Saude ta zuro qafafuwanta ta fito kamar yanda ta ga Dillaliya ta yi, ta tsaya ta biya mai tasi din sannan ta yi gaba Saude ta bi bayanta. Kai tsaye katafaren gate din gidan suka nufa makeken gaske mai kama da Kofar shiga gari, ga wasu manya-manyan shuke-shuke da suka zagaye gidan gaba daya. Dillaliya ta tsaya tana latsa wata ‘yar karamar na’ura da ke like a bangon gidan. ' Wani irin tsoro da faduwar gaba suka bugi Saude anya kuwa, ba tahowa akai da ita a saida ita ba, don tana da yakinin wannan ba gida bane sai dai k0 wata ma’aikata ta sarrafa naman mutane Ba ta gama tunanin ba ta ji qarar tura gate din take ta yi ido hudu da wasu manya-manyan qarti har hudu, bakikkirin da su majiya qarfi, sun bude qofar, suna qokarin shiga suka ga wata bakar mota
yar dunkulalliya mai daukar hankali ta ratsa ta
shiga cikin gate din
Dillaliya ta janyo hannun Saude da niyar su shiga, qartin nan suka yo kansu da wata irin masifaffiyar tsawa wadda tasa ‘yan cikin Saude
juyawa gaba dayansu,fitsari ya fara kwace mata a wando, ita kanta Dillaliyar ta firgita, don cikin rawar murya take fadar.
“Ku yi hakuri wurin matar gidan muka zo ni ce wadda na taBa zuwa da Hajiya Kande, wan,,,,,,
“Shut up! I don ’t speak Hausa.” ,
Tuni ‘yan cikin Dillaliya suka juya, .don ita dai k0 zo in kashe ki da Turanci ba ta sani ba, ido ya ' raina fata ta dubi Saude tana fadar.
' ‘ “Me suke cewa?”
Cikin muryar kuka Saude ta ce, “Ban sani ba nima.”
Dillaliya ta harzuka “Yanzu ashe duk makarantar da ki ke zuwa asarar kudin tara kawai ake baki san komai ba?’ ‘
Saude dai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mutanen nan suka maida kofa suka rufe suka bar su nan tsaye,
Dillaliya na ta faman saukewa Saude kwandon masifa, don ba ta iya Turanci ba. Kunji fa rashin‘ kunya.
A hankali motar da ta shigo cikin gidan mai bakin gilas' ta faka a qatuwar harabar da aka tanada dan ajiye motoci, aka bude gidan direba da hanzari, wata ‘yar budurwa ta fito cikin shigar suite baqaqe da gani ba zata wuce shekara talatin ba
, Tana fitowa ta bude gidan bayan motar tare da ja gefe ta kama, wata kyakkyawar mace ta fito, mai
masifar kyau kai ka ce Balarabiya ce k0 Baturiya saboda tsananin kyau da hasken fata Tana sanye cikin shigar wani danyen leshi mai kyan gaske, wanda tsadarsa ta tasamma dubu dari da wani abu, an yi masa dinkin riga da siket matsatstsu irin dinkin matan manya na Legas, dan qaramin mayafi ne saman kafadarta wanda ta dora shi kawai ta yi a gefen kafadarta, kanta an kafa mata wani masifaffen dauri mai kama da daurin inji, qafar nan tana sanye cikin wani masifaffen takalmi mai tsinin gaske da ‘yar Karamar post din su a hannunta Idonta na sanye

Please Login or Register in order to submit comment