Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki Dr. Ahmad ya rufe matashi
da’wani zazzafan marin daya rudarda ita, ya nuna mata
hanya.
‘get out stupid girl Bace' min da gani bagidajiya kawai.”
Saude ta dafe kunci cike da kaduwa ta juya simisimi ta fice
Tana fitowa daga falon tamkar wadda aka zungura ta fashe
da kuka mai ban tausayi, ta kifa kanta akan kujera tana
kukan ta babu mai lallashinta, ita kanta bata san tsawon
lokacin da ta dauka ba sai dai ta jiyo motsin mutane alamar
za a tito.
Ta zabura ta boye: bayan kujera tana jin su sàida suka
gama fita gaba daya, sannan ta fito cike da tsoro. Kai da _
ganinta kasan tana‘cikin tashin hankali dan bata san irin
hukuncin da zai yanke mata ba yau, duk da bata ga
laifinda‘tayi’masa ba, ammata lura ya dau zafi da * ita ta
qara fashewa da kuka Ya Allah Ka fidda ni tausayin kanta
ya kama ta.
Ita dai batayi sa,ar zuwa duniya ba tunda tazo batasan
masoyanta ba duk inda ta shiga da.
[1/24, 10:13 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/25, 9:29 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*

*CHAPTER 17*

masu Kin ta take haduwa, a duniya yayanta ne kawai ya
taBa sonta, sai kuwa Hamid, mutum na farko da ya nuna
mata qauna da soyayya ita kanta duk da ba ta san meye so
ba, amma ta san tana san Hamid dan ta san wahalar da
take sha gidan su ta linka ta nan gidan sau goma, amma
kullum burinta ta samu ta bar " gidan ta koma gida k0 ta
hadu da Hamid dibta kuIlum addu’arta kenan musamman
idan ta zo kwanciya bacci.
“Wayyo Allah ya Ubangiji gani gare Ka
Jin alamun taflyar da ta yi, ya sa ta saurin dago kai. Dr. ne
ya dawo daga rakiya, gaban Saude ya yi
Wata mummunar faduwa ta yi saurin ja da baya tana ba shi
hakuri, da kukanta dan gani take dukanta zaiyi Dr... ya ja ya
tsaya cak yana kallonta ya ma rasa
me zai mata ya huce haushinsa, ya lumshe idanuwansa
lokaci guda ya bude ba tare da ya yi magana ba ya matsa
da niyar isa inda take ashe bai sani ha ta ajiye tiren kayan
abinci a gun «
Sai dai ya ji ya yi karo da wani abu, ya fasa wata ‘yar
siririyar qara ya durkusa, ya rike babban dan yatsansa,
wanda tuni har ya soma zubar da jini abin ka da lallausar
farar fatar da hutu ya jika, hankalin
Saude ya yi masifaffan tashi, tayi kan shi tana _ fadar ~
‘Wayyo Allah na shiga uku na lalace "ta rike kafar tana
kuka, ‘Wallahi ba da gangan na ajiyeba
Na rantse da Allah ” ya runtse.idanuwansa ba tare da yace
da ita komie ba “ta rasa yanda za ta yi ta kalli kan kayan
abincin ashe, da yar qaramar wuqar yanka cake da ita ya
‘yi karon harta yankeshi hankalinta ya qara masifar tashi
yanda ta ga jini na zuba ba wai kadan ba; ta rude ta cire
himar din » kanta tasa hakori ”ta"yaga shi ta yagi kadan ta
daure masa dan yantsan Dr ya bude idanuwan shi da Kyar
yana kallonta yanda tabi ta gigicc ta rude fada take, ‘Sannu
Wallahi bada gangan na ajiyeba, ganin yanda ta fita
hayyacinta yasa ya nemi fushinsa, ya rasa. Ya'sake lumshe
idanuwansa sbaoda radadin da qafar kemasa yce ‘Dauko
min wayata in kira likita. ” .Hankalin, Saude ya: qara "tashi
da taji an ambaci likita, ashe abin mai girma 'ne. Ta. sake
rushewa da :kuka ita ko yau ta san hukuncinta mai girmane
taje ta dauko masa wayar ta rankwafa ta mika masa, ita ta
zauna daga gefe tana 'kallonsa
Hankalin ta ya kara tashi tsoronta daya kada ’ jininsa ya
qare, don ta ji ance jinin mutum na Karewa mutuwa zai yi,
ta sa hannu ta gage hawayenta cikin muryar kuka ta “ce“K0
in kawo ‘maka gishiri ka barbada tunda jinin yaqi tsayawa?”
Dr. ya waro ido yana maimaita gishiri kuma?
Saude ta qara marairaicewa “Don Allah in kawo maka kada
jinin ka ya qare.” Yanda ta yi maganar a shagwabe shi ya
narkar da zuciyarsa ya ji har cikin tsikar jikin shi. : Ta sake
langwaBe kai “In kawo?”-. Bai san lokacin da ya daga mata
kai ba, Saude ta zabura ta mike da gudu ta fice, Dr. ya raka
ta da manyan idanuwansa masu saurin daukar hankalin‘
yan matan zamani ‘
Meke son faruwa da ni ne? Ya tambayi kansa. Tambayar da
ba shi da mai amsa masa. Saude ta dawo da sallamarta, ta
durkusa ta mika mesa gishirin, ya lusmhe idanuwansa ba
tare da ya yi magana ba, ta ce, “In barbada maka?" '
Ya daga mata kai alamar eh, ta durkusa ta ‘ ‘warware
danrin' sannan ta soma barbada masa gishirin, inda naman
ya Bantale, bai san lokacin da
ye saki qara ba ya rike hannunta saboda azaba. » ‘
Saude ta watsar da gishirin cikin’ ta rike qafar tana fadar,
“Yi hakuri don Allah‘da zafi ko?”
Ya girgiza mata kai alamar a’a, ita kanta ta san ya fada ne
kawai. Ta rankwafa kanta ta shiga hura masa .da iskar
bakinta , tana yi tana sharar kwalla yau Allah kadai ne zai
crce ta a gidan. '
Wani irin‘ tausayin; yarinyar ne ta kama kowace Kofa ta
'jikin sa tausayinsa da ya gani Karara a idanuwanta ya
narkar da zuciyarsa, ya ji tamkar yasa hannu . ya shafi
gashin kanta wanda kana kallon shi kaga gashin Fulani‘: ta
daure shi tamau kamar gammo a kanta, ya Kara laushe
idanuwansa a hankali. ;*A haka har likitan yazo ya same su,
ta yi saurin , share hawayenta tare da gaishe da likitan ya
amsa cikeda kulawa sannan suka gaisa da Dr. ya zauna
yana fadin garin yaya haka? Dr cikin sanyayyar muryar shi
ya ce ‘Tsautsayi kawai likita yace to allah ya kiyaye gaba .”
Ya fada yana kallon shi cikin kulawa ya
Janyo yar akwatin‘sa ta duba marasa lafiya, ‘ saude ta miqe
da hanzarinta, Dr ya, dubeta. . ‘
Yace ina zaki kuma
Cikin sarkewar murya irin ta wanda ya gaji da kuka ta ce,
“Zan fita ne ba zan iya kallo ba.”
Ya zuba mata idanuwansa yanda take maganar yaf8 komai
daukar hankalinsa, ganin bai ce komai ba yasa ta juya ta
fice ita kanta ta soma tsarguwa da kallon da yake mata yau,
wanda ta kasa hada shi da irin Wanda ya saba yi mata a
da.
Kai tsaye Saude ta wuce daya Bangaren, tana shiga falon
ta yi karo da Dillaliya a rabe gefen kujera ita kadai sai ka ce
munafuka. Saude ta karaso da azamarta cikin doki ta zauna
tana fadar “A’ a Dillaliya kece yau a gidanmu, sannu da
zuwa, ina wuni?" Dillaliya ta watsa mata wani kallo mai
kama da
harara, kafin ta ce“Ina ne gidan naku? Lallai samun
wuri tusar asuba, ashe ke nan har gidan
, ya zama naku, kai gaskiya ne, an zo birni an asha jar
'miya ai dole a mance mafari.
To idan kin manta bari in tuna miki gidanku na Katsina, a
Katsinar ma qarshen gari inda k0 wutar nefa ba ta wadaci
unguwarku ba, gidanku na nan gidan qasa an masa faci da
buhu yana nan yanda ki ka bar shi kuma za ki koma ki
same shi munafuka an samu wuri an Bade sai juya
mazaunai ake ke da
matar gidan baku da bambanci, fata ta murje anyi * kilin
To ki sani kin kusa komawa gida,'dan an sa ranar auren ki
wata biyu yau saura wata guda, keda Garba Gurgu, yana
nan yana jiran ki."
Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa ta ji ‘ tamkar
ta dora hannuwa aka ta rusa kururuwa, saboda tashin
hankali da kaduwa. Ta kifa kanta da kujera ta saki wani irin
kuka mai ban tausayi.
Dillaliya ta’ tabe baki tana fadar, “Kuka kama yanzu’ ki ka
fara ni kam ina amsar albashin ki zan wuce yanzun nan
don tun safe nake nan a jibge kamar kayan wanki, ungo
wannan nataccen saurayin ki Hamid ya ce a kawo miki.”
Da sauri Saude ta dago kanta don ganin abin da take mike
mata. Wata doguwar ambulan ce, ta sa hannu ta karBa jiki
na rawa.
Dillaliya‘ ta ce, “Har na shiga mota ya zo da kansa har
tasha ya kawo mini, ya gama ni da Allah ,in kawo miki,‘ ke
kin san in bacin ya biya ni kudi masu kauri ai ba zan kawo
ba.
Saude dai jujuya takardar kawai take, tana jin wata irin
soyayyar Hamid na mata yawo a zuciya, jin bai manta da
ita ba shi ya mantar da ita kukan da take.
Ta mike cike da dokin san ganin abin da ke cikin *‘ambulan
din, Dillaliya ta dube ta, ‘Gidan wa za ki ai ba mu gama ba,
kiyi maza ki tattaro mini abin da kika tara ko‘kina nufin haka
nan ki ka zauna ki ka
saki baki da ciki kina ta kwasar dadi ke da ki ka iya cin
dadi.”
Cikin sanyin jiki Saude ta ce ‘Ki yi hakuri Dillaliya wallahi
ban ajiye komai ba, tunda na zo babu abin da aka ba ni.”
Dillaliya ta cce“Ke dalla tashi' can har sai an ba ki keba ki
iya ‘yan tattare-tattare ba, duk dan wani abinda kikaga anyi
sake dashiki tattaraki boyeba
Saude ta ce “Subhanallahi! Haba Dillaliya sata fa kenan?”
Dillaliya ta ce “Ke gafara can sakarya ai idan ba ki sata kin
Boyeba bikinki yazo ke za a bari da abin kunya, idan ko kin
sata kin bada an boye miki ai kin san abin da ki ka yi ”
Wani inn takaici ya kama Saude wai a tura mutum sata
yanzu idan‘ yar tace ta sanya ta? Cikin sanyin muryarta ta
ce, “Bari in shiga Dillaliya ki gaida gida ki gaida su ‘Yar
Baba da Inna Laure da Baba na gode
Dillaliya ta hayayyako mata cike da masifa “Idan ubanki ya
ba ni kudin motar ba saiki tilasta ni na gaishe su ba,
munafuka, mutuniyar banza, ai duk kyan gawa dai cikin
Kasa za a turbune ta sai mu ga qarshen jin dadi da kyau.".
Saude dai ba ta kula ta ba ta fice abin ta, tan shiga
bangaren ta, ta fada kan gadonta ta zauna zaman
Dirshan ta balle ambulàn din ta zazzago abinda ke ciki
Wasu kudi suka fado yan dari bibbiyu rafa guda tare da yar
qaramar wayar saluka
Saude ta shiga jujjuyawa cike da mamaki ta qara
zazzagawa saiga wani zobe ya fado tare da wata yar
takarda da aka cika da kyakkyawan rubutu ta zubama
rubutun ido dukda batasan abinda aka rubuta dinba amman
rubutun ya burgeta ta dauki zoben nabazurfa dan sirir tana
jujjuyashi shima zoben ya birgeta ta zura zoben a dan
yatsanta qarmi na hagu
Zuciyarta ta kwadaitu dason sanin abinda ke rubuce a cikin
takardar
Ta linketa da kudin ta boye sannan ta dauki wayar tana
lallatsawa dukda bata iya wayaba amman zuwanta
gidannan ta iya kunnawa da kashewa da kuma amsa kira
sbd akwai wayar tarho da akasa a dakin don kiran gaggawa
Saude ta kunna wayar tana qara jujjuyata wayar na
kunnuwa kira na shigowa dukda batasan lambar wayarba
amman zuci yarta ya bata hamid ne don haka hannunta na
kyarma ta daga kiran ta kara wayar a kunne tareda sallama
Wani sanyin dadi ya bugi zuciyar hamid lokacin da siririyar
muryarta ta daki kunnensa muryar da har ya fiddah rai da
sake jinta a duniya cikin doki dajin dadi yake magana
Amin wa,alai kumussalam ya habibati saudat nasan zuwa
yanxu saqona yaxo gareki hakane?
Murmushin dake fuskarta ya qara qawatuwa kafin tace
hakane yaya hamid dillaliya ta kawomin dazu ashe baka
mance daniba yaya hamid?
Hamid yace wat? Haba sudat ai idan har zan iya mancewa
dake to wlh zan iya mancewa da kaina saudat soyayyata
gareki ta gaskia ce kuma ta ginu ne tun daga lokacin dana
fara ganinki kuma inhar ba daina numfashi nayi ba sudat
bazan taba barinki ba sainaga kin taka wani matsayi a
rayuwa na miki wannan alqawarin
Cikin farin ciki dajin dadi saude tace na gode yaya hamid
Yayi wani murmushi wanda har saida ta jiyo sautinsa yace
gaskia saudat dina ta fara girma haka bakinki ya bude ?
Murmushi kawai tayi bata tankaba hamid yace saudat
nasha wahala lokacin dana dawo na iske bakyanan wlh
saida nayi tamkar zan haukace kamin in samu insan inda
aka kaiki amman bansan ko waccce anguwa bace ba a cikin
abuja saida na biyo ta hannun wannan matar yanxu ya kike
ganin za,ayi don muna cikin matsala fa
Saudat an fada miki ansa ranar aurenki? Saude tace eh an
fada mini
Toya kike gani abuja zanzo in sameki ko ko ya za,ai ?
Cikin kidima saude tace ina?
Ka rufamin asiri masu gidan bazasu bariba
Saidai kawai ka bari inna samu dama kawai na gudo
Hamid yace to yaushe ?donni nanda sati daya jirginmu zai
tashi zuwa qasa mai tsarki aikin hajji birina kafin satin duk
yaddah za,ai ayi kawai a daura mana aure don wlh saudat
ina tsoron in rasaki
Saude taja‘numfashi kafin ta ce, “Insha Allahu Yaya Hamid
duk yanda zan yi kafin satin zan yi ba za ka rasa ni ba da
yardar Allah.”
' Dadi Ya kama Hamid nan ya ci gaba da jan ta da hira, su
kan Su ba su san sun ci lokaci ba sai da suka
jiyo ana kiran sallar Magariba.”
Hamid ya ce “Lah! Saudat kin ga kin shagaltar dani mun ci
lokaci har haka, bari in je in yi sallah zan kira ki zuwa dare
kin ji sweaty na?”
Dariya kawai ta yi shi kuma ya kashe wayar, wani sanyin
dadi ya cika masa zuciya. Ta murgina ta sake mirginawa
cike da shaukin soyayya kusan sai nace ban taba ganinta
cikin irin wannan farin cikin ba ‘ ’ “”
Washe gari Saude na cikin shirin tafiya aikinta,
ta ji karar wayarta, ta matsa inda ta Boye ta ta dauka ta
kara a kunne tare da rairo sallama
Hamid ya amsa tare da gaishe ta, ta amsa ba sai dai ta
maido masa da gaisuwar ya amsa suka gaisa sosai, can ya
nisa kafin ya ce“Kin san me wai ashe jiya yayanki yazo
gidanku, ban sani ba sai daga baya na samu labari?”
Cikin zakuwa Saude ta ce, ‘Kai don Allah Yaya hamid yanzu
yana ina don Allah?” ~
Hamid ya ce“Nima abin da yasa na baro Kaduna ke nan
cikin daren na zo Katsina, amma sai na samu wai matar
gidanku ta sa mahaifinku ya yi masa korar kare, suka dinga
watso masa kaya waje cikin daren ya bar Katsina, amma ya
barma maqotanku saqo baki
Saudat ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya ji take
tamkar ta shake kanta saboda baqin ciki
Hamid ya ce, “Ai kuma nifa ba wai na fada miki ba ne don ki
tayar da hankalin ki ba, ki yi hakuri tunda ya dawo yanzu
wata rana ma , zai sake dawowa, don wallahi tallahi na
yarda da Kaunar da ke tsakanin ku na san in har yana da
rayuwa ba zai mance da rayuwarki ba Saudat ki yi haquri
don Allah kin ji?" Haka dai ya yi ta lallashinta sannan ya
kashe wayarsa.
Saudc ta qara fashewa da kuka mai cin zuciya
dama she Yaya Rabi’u yana raye? Ashe ‘dama bai mance
da niba? Shin kowace irin rayuwa yake yi a
Lol labari dai nata tafiya cikin kwanciyar hankali kuma ta
wani barin sai nake ganin kamar Dr Ahmad nason ya fada
tarkon sofa idan ya fara son saude ya kuke ganin zata kaya
tsakanin asmau da sauden hamid da saude da kuma garba
gurgu da saude kai akwai rikici fa mu tara donjin ci gaban
wannan qaya taccen labarin idan naga comment sosai
zanci gaba anjima idan kuma kukaqi to sai gobe kenan
naku har kullum
Admin Dboy🤔
[1/25, 9:29 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[1/25, 10:39 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*

*CHAPTER 18*

1page is missing
Gaban Ahmad ya yi wata mummunar faduwa cikin sanyin
jiki yace, “Lafiya kuwa me ke damun kine? Tamkar ba zata
tanka masa ba saboda yanda kukan yake. neman Kin
tsayawa, sai da ya sake‘ maimaita mata tambayar, sannan
ta samu ta tsaida
, kukan cikin shakakkiyar muryar da ta gaji da kukan
Tace
“YallaBai me yasa rayuwa take zuwa da abubuwa marasa
dadine irin haka? YallaBai me yasa rayuwata kullum ba na
ganin haske sai duhu a cikinta? Me yasa rayuwa ta kullum
take neman rugujewa ne saboda wahala?” YallaBai shin .....

Kuka ya ci Karfinta ta kifa kanta a kan cinyarta ta ci gaba
da raira abin ta. Wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyar
Dr. Ahmad, ya durqusa gabanta a hankali har tana jiyo
kamshin turaren da ke fatar shi.
Muryarsa a sanyaye ya kira sunanta ‘Saudat Wanda ya sa
ta dago kanta da sauri don bata taBa
zaton ya san sunan ta ba, kuma yau ne karo na farko da ya
taBa kiran sunan nata. Ya ci gaba da magana, ‘Saudat k0
me rayuwa ta
' bada hakuri aka a karba, ki karBa' duk abin da rayuwa ta
zo miki da shi ki rungume shi, sai ki ga Ubangiji ya taimake
ki a duk inda ki ke, yawan kuka ba zai kare ki da komai ba
sai ma ya haifar miki da . wani ciwon. Kalle ni Saudat.” Ya
fada da siririyar » murya, ta dago da jajayen idanuwanta
tana kallon ,
shi, ya mika lallausan hannun shi yana goge mata hawayen:
“Ki daina zubar da hawayen ki irin haka, alhalin
ba ki tanadi mai share miki shi ba.”
Saude ta’ yi saurin janye fuskarta cike da jin kunya da
nauyi, ya dan razana tare da fadar “Oh am sorry Ya mike ya
ciro hankicif daga cikin aljihunsa ya mika mata. Ta karba ta
soma share hawayen ta gama ta miKa masa ya karBa ya
mayar aljihu, sannan ya ce
“Tashi mu je ciki, kin ci abinci kuwa?”
Shiru ta yi don rabonta da abinci tun jiya don haka ba musu
ta mike, suka nufi falon kai tsaye
Suna shiga ta nemi gefen kafet ta zauna bai tanka
‘ba Ya wuce kai tsaye wurin firij din da ake aje kayan
gwan'gwani ya bude ya ciro wani qaton cake tare da
~ lemo guda da fresh milk ta kwali, sai chips a wani
Qaramin plate wanda ya ji dafaffen kwai da madara
' ga shi ya dauki sanyi.
Ya nufo inda Saude take zaune ya ajiye mata a gabanta,
sannan ya ja gefe ya zauna saman kafet din yana'
fuskantarta, da hannu ya yi mata nuni da ta ci, ba musu ta
sa hannu ta dauki milk din ta fasa, ta bade cake din ta rinqa
hadawa tana ci. Cake din * ya yi mata wani masifar dadi
don sai ta ce tunda take “ ba ta taba cin abu mai dadinsa ba
ita kanta ta yi
mamakin wanda ta cinye, don chips din kasa cin shi ta yi
don ba ta saba cin irin shi ba.
Ta daga madarar ta shanye tas, don sai da ta ji babu wuri a
cikinta, duk abin da take yana zaune yana kallonta tana
gamawa ta mike da niyar tattara
kayan, ya daga mata hannu.
“Bar shi kawai za a tattara.” Kallon shi kawai ta yi sai dai ta
gaza magana.
Don haka shi ya katse shirun ta hanyar fadar, “Kije kawai ki
huta', kin'ga kin sha kuka kada kan ki ya yi ciwo, kin ji?’ '
Saude ta amsa da to a hankali, sannan ta juya zata tafi
hartakai bakinkofa tajiyakira sunanta ta' waigo tana
kallonsa. Tamkar wanda aka matse bakinsa aka ce dole sai
ya fadi abin da yake son fada ~ ya ce, “Please kar ki sake
yin kukan nan don Allah.”
Saude ta daga masa kai alamar to, ya ce, “Kin yi alkawari?’
Da kai kawai ta amsa masa, sannan ta . juya ta fice
A yanzu mamaki yake ba ta ba ta taba tunanin yana da
tausayi da jin Kai irin haka ba, ashe dama yana da
kyawawan halaye irin haka ya Boye su, Allah Sarki, ko da
yake ai rayuwarta abin tausayi ce ga duk wani mutum mai
imani. _ ' .
Ta zauna bakin gadonta ta janyo Wayarta miss ‘ call biyar
ta gani, ta san kuma duk aikin Hamid ne, ‘ Allah Sarki
soyayya. Ta ajiye wayar karkashin
Kanta ta kwanta. Hirar ta da shi jiya cikin dare ta dawo
mata tamkar yanzu ‘suka yin ta, ta yi wani ”murmushi tare
da yin wani juyi
. Da safe misalin Karfa takwas ta nufi Gangaren Dr Ahmad
da mamakinta yau kwance ta same shi cikin falon Kasa,
saman doguwar kujera da News paper a hannunsa yana
dubawa, yana sanye da wando three quater wanda ya wuce
gwiwarsa sai
bakar singileti a jikinsa. Saude ta durkusa tare da ‘ ”gaishe
shi.’
Ba tare da ya dago kansa daga karatun da yake ba ya amsa
mata gaisuwar. Saude ta mike ta soma aikinta kamar yanda
ta saba, sai da ta kammala tsaf sannan ta soma turare
falon da turaren wuta, kamar wadda aka cewa dago kanki,
karaf su kai ido hudu, ‘gaba daya idanuwansa da
hankalinsaya tattara su a ‘kanta.~
‘ ’Saude ta ji ta yi wata masifaffiyar tsarguwa, cikin
basarwa irin ta gogaggun maza ya‘ yi
mata alamar kira dakansa, jikin Saude ya Kara yin sanyi ita
dai ta fara tsorata da irin kallon da yake mata, ba yanda ta
iya haka ta ajiye bonar din ta nufl
: ' inda yake ta dan durkusa kusa kadan tare da fadar, _
“Ga ni‘ Yalla Bai.”. Idonsa na' kanta kamar mai san
karantar wani abu cikin idanuwanta ya ce“Ya kamata a
tsaya da aikin
nan haka a kawo mana abun karyawa k0 ke ba ki soma jin
yunwa ba ne?” Yadda ya yi maganar cikin "salon nuna
tausayinsa a kanta shi ya ba ta mamaki
Saudat ta sunkuyar da kanta qasa‘ tana kallon yatsun
hannunta, sannan ta amsa, da to muryarta a sanyaye, bai
tanka. mata ba har ta mike ta fice daga falon, ya koma ya
kwanta ya dora hannun shi guda a kan shi ya lumshe
idanuwansa komai yake tunani? Oho.
Saude ta karBo break din ta kawo da sallamarta ta ajiye
masa. tiren kayan abincin a gabansa tare da fadar, ‘Ga
abincin. ”
Dr. Ahmad ya yunkura ya tashi zaune ya sauko daga kan
kujerar ya zauna a gabanta tare da harde qafafuwa tamkar
wani karamin yaro ya ce, “Zubo mana. ’ Saude ta yi saurin
kallonsa tana san tambayarsa shi da wa amma kwarjinsa
ya hana,
don haka ta sunkuyar da kanta. Ta dauko ' plate biyu za ta
zuba Dr. ya sa hannu ya janye dayan yana fadar, ‘Plate
guda za ki zuba mana.” Ba ta musa ba ta dauki saving
spoon ta , debo soyayyar agada (Plaintain) tare da alalar
nama da kwai sai soyayyar da nama cikin dankali ta zuba
su kowane gefe da gefe a tsakiyat plate dim sai ta zuba
wata hadaddiyar miya kadan sannan ta tura plate din a
gabansa ta rufe kulolin, sannan ta dauki
kofi guda biyu ta zuba kunun madara da gero tasa ‘cokula
ta miqa masa.
Dr. Ahmad ya zuba mata manyan idanuWansa da dan
murmushi a fuskarsa ya ce, “Sannu.’ Ba ta amsa ba saboda
yanda ta ji nauyin yanda ya mata sannun,
kamar ba yallaBan da ta sani ba. . Da kan shi ya matso da
plate din a gabanta shi
ma ya matso tare da miqa mata kofl guda na kunun Gaban
Saude ya yi wata mummunar faduwa ta yi
saurin matsawa tana girgiza masa kai alamar a’a. Dr. ya
hade fuska tare da fadar.
“Karbi mana meye haka?” Yanda ya yi maganar cikin tsawa
ya sa ta saurin mika hannu ta karBa.
Ya ce “To sa hannu mu ci maza.’ Ta yi saurin kallonsa
idonta 'ya ciko da kwalla ta gaza yin magana, Dr. Ahmad ya
girgiza kai cikin damuwa ya ce “Abincin ne ba zaki ci ba shi
ne za ki yi kuka?”
Ta yi saurin girgiza masa kai,alamar a’ a Ya kada kai cike
da damuwa ya mike ya koma kan kujera ya kwanta ya
lumshe idanuwansa ba tare daya yi magana ba. ~
Wani irin abu yayi wa Saude tSaye a zuciya, shin wai ita me
ya maida ta ne? Yanzu abincin ma da zai ci sai ya wahalar
da rayuwarta a kansa, abin da yake mata ya soma ba ta
tsoro. Ji take tamkar ta mike ta
bar masa falon, in ya ci ma k0 bai ci ba ruwansa. Bude
idanuwansa da' ya yi shi ya katse mata tunanin
take cikin sanyayyar muryarsa ya ce “Na takura ki k0? Ki yi
hakuri kina iya tafiya kawai. ’ ‘ Gaban Saude ya yi wata irin
masifar .faduwa cikin muryar kuka ta ce“Ka yi haquri dan
Allah ’ Ya dauke kansa kafinn ya ce “Aini banyi fushi ba.” ‘ .
. Damuwar da ta gani qarara a fuskarsa ne ta
Narkar da zuciyarta, ita kanta tana mamakin kannta -.
yanda hankalinta ke tashi idan suna tare bata san lokacin
da bakinta ya bude ba sai dai ta ji tana ‘ fadar
“Ka yi hakuri yanzu ai zan ci.”
A hankali ya dago yana kallonta, ta ta" sunkuyar da
idanuwanta kasa, wani takaitaccen murmushi ya yi tare da
saukowa daga kan kujerar ya: zauna gefenta. Da kan shi ya
dauko kofi din kunun ya mika mata, ta sa hannu ta karBa
cike da jin nauyi ta soma sha, dadin kunun ya ratsa mata
kwanya ashe haka yake da dandano a baki, tun tanajin
nauyi har ta dake ta ci sosai tana cire hannunta yana cire
nasa.‘ a
Ta dan zuba masa idanuwanta, ya daga mata gira, alamar
ya aka yi? Shiru tayi “ta kwashe kayan ta dawo ta gyara
wurin da sukaci abincin sannan ta qarasa inda yake zaune
yanacikin karant
jaridarsa, ta dan durkusa. _ “Zan tafi Yallabai ko akwai wani
abin da~ ka ke so?” '
Dr. Ahmad ya dago da kansa ya kalle ta a nutse~ kafin ya
ce, “Me yasa za.ki tafi nan ba falo ba ne? Me yasa ki ka
kasa sakin jiki?” Saude ta yi shiru ba tare da ta iya cewa
komai ba Dr. ya girgiza kai tare da fadar samu guri ki zauna
ina san mu yi magana.’ Ba musu ta samu gefen kujerar da
yake zaune ta

Please Login or Register in order to submit comment