Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba'a koya miki tarbiyyar girmama navgaba da ke ba."

Amatullah tace "ai tarbiyyar kala-kala ce, wani shi ba'a koya masa tarbiyyar yadda zai girmama kansa ba ma, bare har wani ya girmama shi."

A fusace ta matso tace "don ubanki da wa kike?"

Amatullah tace "ba dai ubana ba."

Ta d'aga hannu zata kai mata mari Amatullah tayi saurin ri'ke hannunta, Baba mero da ta shigo kitchen d'in tace tace "sunhanallah, menene haka kuma yake faruwa?"

Cikin 6acin rai Saudat tace "wai ni yarinyar nan take son kawowa rainin hankali? Neman zagi na fa take."

Duk da Baba Mairo taji duk yadda sukai sai ta juya gurin Amatullah tace "me yasa zaki yi mata rashin kunya? Ai dai kin San ba sa'arki bace ko?"

Amatullah tace "Baba tun wuri na zo zanyi girki ta hanani, a gabanki Ammar yace yana jin yunwa, na zo na tarar sai yanzu zata d'ora abinci kuma don zan had'a musu tea sai ta hana? Haka take so yaran su zauna da yunwa?"

"Ko me ta yi bai kamata kiyi mata rashin kunya ba tunda ba sa'arki bace, kar na sake ganin irin haka ta faru a gaba."

Jiki a sanyaye Amatullah ta amsa da "to." Ta juya ta fita daga kitchen d'in.

Baba Mairo ta maida hankalinta gurin Saudat dake tsaye har lokacin tana huci tace "Saudatu abinda ki kai baki kyauta ba, ina jinku tun d'azu yarinyar nan ta zo zata yi girki kika hana ta, ta ha'kura ta koma d'aki, yanzu sun dawo suna jin yunwa ba'a d'ora abincin ba, kuma had'a musu tea sai ya zama laifi tsakani da Allah?

Da kin barta ta dafa ai kema hutunki ne, kuma idan kika kwantar da hankalinki zaki mori Amatullah sosai, saboda bata da 'kowa.

Yanzu idan mahaifin yaran nan ya sami labarin abinda ya faru me kike tunani? Ai idan kina da wayo da yaranma zaki sake samun fad'a a gurin iyayensa da shi kansa mai gidan.

Don Allah kar irin hakan ta sake faruwa."

Har ta gama bayaninta Saudat d'in bata kula ta ba, sai juyawa da tayi ta ci gaba da aikin girkin da ta fara tun d'azun.

Ita dai Baba Mairo ta wuce ta had'owa yaran tea ta fita ta kai musu parlour suka sha.



*_Ku yi ha'kuri da errors ciwon kai ne ya hana ni editing._*


*Ummu Aisha*
[8/29, 2:27 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*


*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, Wasila Abdu Unity Bank, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 19&20*

Da farko Amatullah tayi niyyar sanar da Uncle abinda ya faru tsakan inta da Saudat amma sai Baba Mairo ta zaunarta tayi mata nasiha sosai har ta ha'kura, amma ta tabbatarwa Baba Mairo da cewa duk abinda zatai mata ita akan kanta zata jure, amma kar ya shafi yaran, don inda tayi musu abu to ba zata iya kau da kai ba.

To kuma da yake Allah ba azzalumin sarki bane ranar sai ga Bashir ya dawo gida da wuri, sa6anin abinda ita Saudat ta ji a gun Baba Mairo cewa sai bayan magriba yake dawowa d'azu da ta tambaye ta.

Har ya shiga d'akinsa don yin wanka babu wanda ya san da dawowarsa a gidan, a lokacin ne ita kuma ta fito daga d'aki zuwa kitchen ta sauke abincin da ta girka, tana cikin juyewa a warmer ya fito daga d'akinsa.

Ganin babu kowa a parlour sai ya nufi d'akin yaran don ganin me ya hana su fitowa parlour kamar ko yaushe.

A kwance ya sami Ammar yayi pilo da cinyar Amatullah, sai Muhibba da ke zaune kusa da Amatullah itama ta yi jigun kamar wadda take cikin damuwa.

Da sauri ya 'karasa inda yaran suke, ya tsugunna a gabansu, ya ta6a jininsu duka ya ji babu zafi saibya tambayi Ammar "my boy me ya same ka?"

Yaron yace "Abba yunwa nake ji."

Da mamaki ya kalli Amatullah yace "baici abinci bane?"

Ta amsa masa da "eh, ba'a gama ba."

"Akan wane dalili za'a kai har yanzu ba'a gama girkin ba? Waannan ai sakaci ne, sai ku zauna da yunwa da gangan Ga 'kananan yara kuma?"

Kafin Amatullah tace komai Muhibba tace "sabuwar Aunty ce bata gama ba, kuma ta hana Yaya Amatu had'a mana tea sai Baba ce ta had'a mana."

Da ido ya tsare Amatullah, sai tayi saurin sunkuyar da kanta, don ta riga ta yiwa Baba Mairo al'kawarin ba zai ji komai a bakinta ba.

A fusace ya mi'ke zai fita sai Baba Mairo ta dakatar da shi da cewa "don Allah kar kayi mata magana, sai taga kamar yaran na son shiga tsakaninta da kai ne tun yanzu, sannan lokacin da abin ya faru a kan idona akai komai, kuma nayi mata nasiha, na nuna mata kuskurenta, ta kuma fahimce ni.

Ba zan so daga zuwan yarinya kun fara samun sa6ani da ita ba, sai na zama babbar banza a tsakaninsu, kuma ko Hajiya idan ta ji ba zata ji dad'i ba."

A tausashe yace "shikenan Baba Mairo tunda kin sa baki maganar ta wuce, amma fa ba zan d'auki yiwa yara horon yunwa ba, ko da Habiba ce da ta haifi yaran."

Juyawa yayi ya fita, sai ya same ta tana jera abinci a dining, tana ganinta tayi masa sannu da zuwa fuskarta cike da fara'a duk da zuciyarta ba haka bane.

Ta yaya mijinta zai dawo daga gurin aiki bai neme ta ba ya fara tafiya gurin 'ya'yansa? lallai sai ta dage akan mutumin nan in ba haka zata kwaahi ba'kin cikinsa ba kad'an ba.

Dining d'in shima ya nufa ya ja kujera ya zauna yana tambayarta "wai sai yanzu aka gama abincin rana?"

Sai ta amsa masa da cewa "wallahi barci ne ya d'auke ni ban san lokaci ya ja ba, sai da na tashi."

Yace "to su yaran da suka dawo daga makaranta me suka ci?"

Cike da kisisina tace "na had'a musu tea sun sha."

A lalace ya kalleta cike da mamakinta wai ta had'a musu bayan yanzun nan Muhibba ta gama sanar masa da farko hana Amatullah had'a musu tea d'in tayi sai Baba Mairo ce had'a, amma don babu Allah a zuciyarta zata yi masa 'karyar banza.

A fili kuma sai yace "tea d'in me kike ganin zai yi musu maganin yunwa? To gaskiya ki sake tsari don ba zan yarda da barin yara da yunwa ba, in kuwa ba haka ba da wuri za'a ji tsakaninmu da ke."

Cikin sunkuyar da kai kamar mumina tace "kayi ha'kuri yau ma akasi aka samu, amma insha Allah irin hakan ba zai sake faruwa ba."

Lokacin da take zuba musu abincin a plate sai ya ga abincin bashi da yawa sai yace "wane abincin yaran za su ci kenan?"

Kai tsaye ta bashi amsa da "yana kitchen bari na kira Amatullah ta d'aukar musu."

Kallonta ya ci gaba da yi sannan yace "ba haka tsarin gidan nan yake ba, tare muke had'uwa mu ci abinci gabad'aya, don haka rana tsaka ba za'a canza tsarin ba."

A take fuskarta ta sauya zuwa damuwar da har ya fahimta, sai ya ce idan kina ganin ba zaki iya kuma min da yara ba babu dole sai na maida ke inda na d'auko ki."

Cikin dauriya tace "amma ai kasan ban san tsarin da kuka saba ba, kuma kai da ya kamata ka sanar da ni baka sanar min ba, don nayi gaban kaina kuma sai ya zama laifi?"

Sai yace da kar6ar gyaran kikai kai tsaye ba zai zama laifi ba, amma fuskarki ta nuna baki amanna da maganar cin abinci tare da su ba.

Abinda nake so ki sani, a kaf duniyar nan bayan iyayena 'ya'yan sune abu na biyu masu muhimmancin a gare ni, babu wata mace da zan aura ta na zauna lafiya da ita matu'kar bata 'kaunar 'ya'yana.

Ina sanar da ke wannan ne don ki gyara idan kina son tafiyarmu ta d'ora da ke."

Yana gama fad'ar haka ya mi'ke ba tare da ya ci abincin ba ya kira yaran duka har Amatullah suka fice daga gidan.




*_A yi min afuwa yau ma babu editing_*


*Ummu Aisha*
[8/29, 2:27 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, Wasila Abdu Unity Bank, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 21&22*

*_Not edited_*❗

Suna barin gidan basu tsaya a ko ina ba sai wani lafiyayyen restaurant, order yayi musu kowa ta za6i abinda ransa yake so aka kawo musu suka ci, sannan su kaiwa Baba Mairo take away suka koma gida.

Basu samu Saudat a parlour ba, babu wanda ya bi ta kanta, kowa ya kama sabgar gabansa.

Ita kuwa tun lokacin da suka fita ta kasa cin abincin saboda 6acin rai, ta tashi ta koma d'aki, ta d'auki wayarta ta kira Zainab 'kawarta.

Tana d'agawa ko sallama bata tsaya yi ba tace "Zainab akwai matala."

"Wacce irin matsala kuma daga zuwanki?"

"Yaransa sune matsalata Zainab, sannan ga wata shegiyar yarinyar 'yar Yayansa da take zaune a gidan."

Nan dai ta kwashe komai ta sanar da ita.

"Na fa fahimce ki, amma ina so ki gane ke ce mutum ta farko da zaki haddasawa kanki matsalar Saudat, da farko dai kin fi kowa sanin da ya akai auren nan, daga zuwa bai kamata ki nuna halin ko in kula akan 'ya'yan da ba.

Kamata yayi ki nunawa yaran kulawa da soyayya, ta yadda ko da daga baya kin sauya musu idana an gaya masa ba zai yarda ba.

Shi komai na duniya da kike gani da siyasa ake bi kafin a cimma buri, ita kuma yarinyar da kike magana akai ina gani matsalata mai sau'ki ce, ki dai jira zuwa lokacin da zaki kafa kanki kivsamu fada a gurinsa."

Dogon numfashi ta sauke tare da cewa "anya zan iya? Zainab kin San yadda nake jin haushin yaran nan kuwa? Kar ki manta fa mahaifiyarsu ita ce ta zame min shanmaki tsakaninta da farin ciki na tsawon wasu shekaru san...."

Saurin katse ta tayi tun kafin ta 'karasa fad'ar abinda za ta ce da cewa "me yasa ba zaki fahimci manufata bane Saudat? Ni kaina ba buri na bane ki zauna yiwa wata 'katuwa bautar 'ya'ya, amma komai na duniya sannu-sannu ake bi.

Kina tunanin za ki samu damar shiga zuciyar Bashir kiyi kane-kane alhalin kina njna halin ko in kula a kan 'ya'yansa?

Idan kina tunanin yiwuwar hakan ya kamata ki daina, babu namijin da zai so ki alhalin kin fito fili kin nuna bakya 'kaunar 'ya'yan da."

Sun dad'e suna magana kafin su yi sallama duk da ko kad'an Saudat d'in bata tunanin zata iya amfani da shawarar Zainab d'in na baiwa yaran kulawa da ta bu'kata.

Bata San lokacin da suma dawo gidan ba, sai da ta fito, abin takaici ta tarar babu wanda ya ci abincin da ta girka har Baba Mairo, cike da takaici ta kwashe komai ta zubar a dust bin, anan ne ta tarar da ledar wani restaurant a ciki alamun take away aka yi.

Washegari dole ta tashi da wuri ta d'ora breakfast sannan Jere gabad'aya akan dining har yaran duk da ta d'ebarwa Amatullah, don tana ganin ba zai yiwa ace komai sai an daidaita ta da sauran yaranba.

Tare da yaran suka fito don yi musu rakiya kamar yadda ta saba, sai Uncle ya umarce su da su taho su karya.

Gabad'ayansu suka nufi table d'in har Amatullah, sai dai abin mamaki ta kai hannu zata ja kujera don ta zaina Saudat ta dakatar da ita da cewa "naki abincin yana kitchen."

Uncle Bashir ne yace "kamar yaya?"

Ba tare da ta nuna alamun damuwa ko wani abu ba ta amsa masa da cewa, gani nayi kamar Amatullah tayi girma da zama a tsakiyar mu, in dai zancen gaskiya ne bai kamata ta dinga cin abinci a cikinsu ba."

Ajje cokalin dake hannunsa yayi, ya dubi Amatullah dake 'ko'karin juyawa tare da dakatar da ita, sannan ya maida hankalinsa kan Saudat yace "akan wanne dalili kenan?"

Sai ta bashi amsa da cewa kawai dai gana nayi bai kamata ba, Amatullah fa ta fara girma, muma ko Muhibba ce ta kai shekarunta ai ina ganin abinda ya kamata kenan."

Cike da takaici ya sake cewa "akwai wani banbanci kenan tsakanin ita Amatullah da Muhibban da kike gani?"

Ai kai ma kasan akwai banbanci, Muhibba fa 'yar cikinma ce, Amatullah kuma 'yar d'an uwanka......"

Saurara na gaji da jin wannan shirmen naki, ko Habiba da ta haifi Muhibba bata ta6a nuna banbanci ko a tsakaninsu ba, muma ke ma ba zan d'auki hakan daga gare ki ba.

Ba zan gaji da gaya miki ba cewar idan har kina son zaman lafiya da ni ki kyautata mu'amalarki da yaran nan dukkansu, don ni duk abu d'aya nake kallonsu."

Yana gama magana ya ajje cup d'in hannunsa ya bar gurin da tissue a hannunsa yana goge bakinsa, ya umarci Amatullah da ta zauna ta ci abincin a cikin 'Yan uwanta.

Wannan abu ko ba'a fad'a ba ya 'konawa Saudat rai, itama kasa 'karasa zaman cin abincin tayi ta tashi ta shiga d'aki zuciyarta cike da takaici.

Ita kuwa Amatullah zamanta tayi ta ci abincinta ta 'koshi ko don ta 6atawa Saudat d'in rai, ganin yadda take nuna alamun bata 'kaunar ganinta a gidanqq.

Kusan tun daga wannan lokacin rashin jituwa ya 'kara shiga tsakaninsu, ita Saudat tana ganin Amatullah tana neman hanata sakewa a gidanta, yayin da ita kuma Amatullah take ganin si taje ta nuna mata ita ba kowa bace a gidan, duk da kasancewar duk abinda tayi mata bata kula ta saboda kyakkyawar tarbiyyar da ta samu ta girmama na gaba da ita.

A kwanakin kuma Hajiya ta matsawa Bashir akan tana so ya mayar da Baba Mairo guda tunda yanzu akwai mace a gidan.

Duk da hukuncin Hajiyan bai yi masa dad'i ba haka ya mai da ita.

Ita kuma sai take ganin kamar wannan wata dama ce a gareta ko kuma lasisin da zata yi duk abinda taga dama.

Abu na farko shine ta mai da Amatullah kamar wata 'yar aikinta, duk wani aiki na gida ta sakar mata tun daga shara, wanke-wanke, girki da kuma ragamar kula da yaran don tace ba zata iya ba tun da ba bauta ta zo ba.

Matsala ta farko da aka samu itace Uncle ya aan d'and'anon girkin Amatullah, tun yana kara har ya gaji ranar da daddare djk gidan suna parlour ban da Amatullah da yanzu ko yaushe tana d'aki, kamar yadda matar gidan ta bata umarni.

Ba wai ta zauna bane d'in bin umarnin Saudat d'in sai don Hajiya da kafin tafiyar Baba Mairo sun dad'e suna magana a waya, kuma tayi mata kyakkyawan gargad'i akan kar ta ji wata 6araka tsakaninta da Saudat d'in.

Kuma itama Baba Mairo nasiha sosai tayi mata da ta tashi tafiya tace duk abinda zata gani tayi ha'kuri kar ta tanka wata rana sai labari.

Uncle dake zaune da computer a gabansa ne ya dubi Muhibba da ta gama home work da aka basu a makaranta yace "kirawo min Amatullah."

Tashi yarinyar tayi don amsa umarninsa, yayin da Saudat ta ji ranta ya fara 6aci, don har ga Allah ita fa bata 'kaunar kusancinsa da Amatullah, duk da cewa babu abinda hakan zai haifar, sai dai tana jin haushin yadda ya damu da yarinyar.

Tare suka fito ri'ke da hannun juna, suka samu guri suka zauna, sai ya ke tambayar Amatullah dalilin da yasa yanzu bata fitowa parlour kamar kowa.

Sai ta bashi amsa da cewa tana duba littafan isalamiyyarta ne, sai ya maida hankalinsa ga Saudat yana tambayarta "wai me yasa ne kika sakarwa Amatullah ragamar girkin gidan nan?"

Da mamaki ta ke kallonsa tace "kamar Yaya?"

Ya ce "kamar yadda na fahimta, yanzu kowane lokaci ita take girki a gidan nan, bayan ga ki matar gidan kina zaune me ya janyo hakan."

Wani kallo yayiwa Amatullah tare da cewa "sharri za kiyi min, son ki had'a mu ko me kike nufi?"

Da mamaki yace "sharri kamar yaya? Kina tunanin Amatullah ce ta sanar da ni?"

Sai ta bashi amsa da cewa "to dama idan ba ita ba wa zai gaya ma?"

Ya ce to " kin yi kuskure, babu wandabya sanar da ni da kaina na fahimta, saboda tun kafin ki shigo rayuwata nasan d'and'anon girkin Amatullah."

Wani mamaki ne ya kama ta, tambaya take yiwa kanta ya d'and'anon girkin Amatullah? To me hakan yake nufi?





*Ummu Aisha*
[8/29, 2:27 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, Wasila Abdu Unity Bank, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Last Free page 23&24*

Duk da yadda Saudat take 'ko'karin ganin ta 6oye abinda ke ranta game da yaran, hakan bai hana Bashir fahimtar akwai matsala ba, saboda idan tana zaune babu mai ra6arta, alamun basu samu fuska daga gareta ba.

A 6angaren Amatullah kuwa gabad'aya hankalinta ya koma Kano, amma abu d'aya da ke da'kusar da ita sune su Muhibba, tunaninta idan ta bar gidan bata San wane irin zama za suyi da Aunty Saudat d'in ba.

Saboda fahimtar da tayi mata irin matan nan ne masu tsananin son kai da son isa.

Duk yadda ta so komawa gida dole ta ha'kura ta danne, musamman da ta san shi kansa Uncle d'in ba lallai ya yarda da 'kudirinta ba.

Har fargabar tafiyarsa Kano Weekend take, domin 'ka'idar ne sai ta yiwa yaran horon yunwa, abinda yake mugun wahalar da Ammar kenan.

Ga fad'a da tsawa da takewa yaran, d'an kuskure kad'an yaro zai yi, ta rufe ido tai ta zazzaga masa masifa idan Uncle baya nan.

A haka suke rayuwa ba tare da ya san halin da yaransa suke ciki, ba, tun da idan yana babu wata kyara ko tsangwama da take nuna musu, duk da bata shiga harkarsu.

Tun da aka kusa hutu yaran suka fara ro'konsa ya kai au Kano suyi hutunsu a can, cikin sa'a ya amince ba tare da ya ja musu rai ba.

Kowanne a cikinsu murna yake, yayinda Amatullah tafi kowa murna don ta 'kudurce a ranta in dai suka koma Kano ba zasu dawo ba, gabad'ayansu.

Tun daga lokacin kowannensu ya matsu su gama exams su tafi, don ji suke kamar su jawo ranar.

Abin tsautsayi ana saura kwana biyu tafiyarsu yaran suka dawo daga makaranta, kowa ciki fal yunwa, amma sai suka tarar ba'a gama abincin rana ba, son tun ranar da Uncle yayi maganar Amatullah ke girkin gidan ta dawo yi da kanta, amma sai lokacin da taga dama.

Amma da ya kasa ha'kuri ga fara yiwa Amatullah Kukan yunwa, cikin damuwa ta fito kitchen don ta ro'ki Saudat ko tea ne ta had'awa yaron, cikin sa'a ta tarar bata kitchen d'in.

Cikin sauri ta had'a tea d'in ta shiga d'aki ta kaiwa yaron, ya kar6a ya fara sha.

Ita kuma sai ta shiga toilet don yin wanka. Yana gama sha ya fita da cup d'in don mayarwa kitchen, sai ya tarar da ita tsaye a gaban gas tana duba abincin da ake dafawa.

Juyowa tayi tana kallonsa tace "wannan cup d'in me akai da shi?"

Yace "tea masha."

Sai ta zare masa ido tare da cewa "uban wa had'a maka Tea d'in?"

Tuni jikin yaron ya fara rawa yace "Yaya Amatu ce."

A fusace ta nufi inda yake tsaye yana ''ko'karin ajje cup d'in, ganin yadda ta nufi shi yasa jikinsa ya fara rawa, kawai sai cup d'in ya su6uce daga hannunsa."

Tana zuwa ta kama kunnensa tace "shegu masu cin tsiya, uwarku ta sanar muku da cin abinci kamar jakuna, wallahi ni ba zan d'auki wannan iskancin ba.

Ta saki kunne tare da tura shi gaba, yaron ya fad'a kan fasashshen kofin, wanda hakan yayi dai-dai da tsaiwar Amatullah a gurin.

Yaron ya fasa 'kara saboda fasassun glass d'in da suka yanka shi, Amatullah tayi kansa da gudu, tana kiran sunan Allah.

Da sauri ta kama yaron zuwa d'akinsu tayi toilet da shi, don wanke masa inda ya 6aci da jini, a jikinsa.

Ita kanta Saudat sai jikinta ya d'auki rawa ganin da gaske Amatullah ta ga lokacin da ta tura yaron, tuni fargaba ta cika ta, saboda bata San matakin da uban yaron zai d'auka ba.

Cikin sauri ta nufi d'akinta ta kira shi a waya ta sanar da shi cewa Ammar ya ji ciwo da fasashshen cup.

Hankalinsa ya tashi sosai, a take ya nufi gida, yana shigowa a parlour ya tarar da ita cikin damuwa, sai yayi tunanin damuwar ciwon yaron ne.

Tare suka shiga d'akin da ita, idonsa akan Amatullah da suke kuka tare da Ammar d'in, da sauri ya 'karasa burinsu, ya d'ago yaron yana duba raunikan da ya ji a hannayensa duka biyu sai gwiwoyin 'kafarsa.

'D'ago shi yahi daga jikinsa da nufin kai shi asibiti, da sauri itama Saudat ta rufa masa baya, taje d'akinta ta d'auko hijab ta fito.

Ganin yana 'ko'karintan tayar da motar tayi saurin shiga suka tafi asibitin tare.

Anyi masa dressing d'in raunikan sai magani kashe zugi da aka bashi, suka taho gida, Saudat na zaune a 6angaren mai zaman banza rungume da Ammar a jikinta.

Zuciyarsa cike da farin cikin yadda take nuna kulawa ga gidan jininsa, sai yake tambayarta "a garin yaya ya fad'a kan kofin?"

"Wallahi ina kitchen ina girki ya shigo da cup d'in a hannunsa zai ajje, ban san a garin yaya ya yarda shi har ya fashe ba, na juyo da niyyar yi masa magana na ganshi ya fad'a a kai."

Jinjina kai kawai yayi tare da cewa "tsautsayi ne Allah ya aiko, sai dai Allah ya kiyaye gaba."

"Amin." Zuciyarta fal murnar rufuwar asirinta.

Da suka koma gida ma haka tayi ta hidoma da shi, kamar gaske, wanda hakan sai dad'i yake yiwa uban, bai ba don Allah take ba.

*Note* _(Sau da yawa zaka ga mace tana azabtar da 'ya'yan mijinta, musamman wad'anda iyayensu suka rabu sanadiyyar mutuwar aure, ko kuma uwar ta mutu ta bar yaran._

_Magana ta gaskiya wannan al'amarin yana d'aure min kai, ke bakya tunanin 'kaddara da ta raba wannan uwar da 'gatanta keme zata iya zuwa ta raba ki da maki 'ya'yan?_

_Ya kamata mata idan barci muke mu farka, shi d'a da dukiya ba'a yi musu mugunta, son Allah ne kad'ai ya san wanda zai amfane su, sannan sai da yawa za kaga yaran da suka sha wahalar rayuwa daga baya sai su zo su zama wani abu, naki 'ya'yan da kika fifita za su zama a 'kasansu._

_Don Allah idan barci muke mu farka, duk wanda Allah ya 'kaddaro zamansa tare da ke Ubangiji ya fi ki sanin dalilin da yasa ya 'kaddara hakan._)
*_Allah ya bamu ikon gyarawa Amin._*

___________________________________________________

Tun lokacin da suka gansu a gaban Hajiya murna ta cika su, musamman Amatullah da ta fisu hankali.

Hajiya na yi musu

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment