Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabbatar ba zaki yi abinda kika san zai cutar da ni ba."

"Dama ba wani abu nake bu'kata daga gareni ba face ina son ki amince ki auri Bashir."

A razane ta d'ago kai tana kallon Hajiya, fuskarta d'auke da bayyanannen mamaki.





*Ummu Aisha*
[8/29, 2:27 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 13&14*

Wani irin farin ciki marar misaltuwa ta ji ya mamaye zuciyarta, tambaya d'aya take nanatawa kanta dama zata samu cikar burinta? Ta dad'e da fad'awa tarkon soyayyarsa, ganin yadda suke nuna soyayya da kulawa da juna shi da matarsa wannan ya sa ta bata ta6a tunanin samun matsayin zama matarsa ba, amma sai gashi lokaci d'aya al'amarin ya zo mata a bazata.

Cike da jin kunya tace "na amince, ko wani kika za6ar min ba Yaya Bashir ba ba zan amince, don ba zan ta6a watsa miki 'kasa a ido ba."

Maganarta ta yiwa Hajiya dad'i sosai, ta dinga saka mata albarka.

A ranar ta kira Bashir ta sanar da shi, godiya sosai yayi mata, duk da ko kad'an bai ji dad'in za6in Hajiyan ba, don har ga Allah shi a tsarinsa baya son mace mai 'kiba, ya fi son dai-dai misali, wadda ko abin gudune ya taho zai sungumi kayarsa.😃

A washegari ta sanar da Alhaji Babba halin da ake ciki, shi kansa yayi farin ciki da al'amarin, tun da akan idonsa yaran gidan su Saudat suke tasowa, ya san tar biyyarsu.

Shima baiyi 'kasa a gwiwa ba, ya sanar da mahaifinta halin da ake ciki, ya kuma nemi izinin zuwa neman aure.

Na take ya amince, ya kuma bada ranar da za'a je d'in.

Cikin 'kan'kanin lokaci magana ta kankama, don a ranar da aka kai kud'in aure basu bar gidan ba sai da aka saka ranar biki.

Kasancewar mahaifinta ya san Bashir mutumin kirki ne da duk wani uba zai so had'a zuri'a da shi, shiyasa komai ya zo musu a sau'ka'ke.

Tuni Hajiya ta bawa Aunty da Hauwa da Mamin Amatullah umarnin fara had'a lefe, bayan ta yi magana da shi, ya turo kud'in da za'ayi amfani da su.

Sai shirye-shiryen biki ake, yayinda angon ko garin ya 'ki zuwa, don shi sam Saudat bata yi masa ba, ya dai kar6i batun aurenta ne saboda yadda Hajiya ta nuna ta yaba da tarbiyyarta.

Shi a tsarin rayuwarsa sam baya son mace mai 'kiba, yayinda ita kuma ta kasance 'yar lukuta.

Ko gidansa turo da kud'i yayi ta hannun Haidar don ayi masa 'yan gyare-gyaren da ba za'a rasa ba.

'Bangaren Habiba kuwa ko yaushe yana waya da Umma don jin halin da take, sannan yana tura musu kud'i saboda bu'katunta na yau da kullum.

Ganin yadda lokaci ya ja sosai bai zo ba, ga biki yana ta 'kara kusantowa yasa Hajiya yi masa magana akan rashin zuwansa, dole wanna satin ya daure ya shigo garin.

Amarya Saudat tun da ta sami labarin zuwan angonta garin ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda farin ciki.

Bai samu zama da Hajiya sai da daddare bayan an fito daga sallar Isha ya shiga gidan, zama yayi a kan d'aya daga cikin kujerun parlour'n sannan ya risina ya gaida ita da cewa "barka da yamma Hajiya."

Ta amsa da "barka dai."
"Mun same ku lafiya?"
"Lafiya 'kalau, ya ka baro yaran?"
Suna nan lafiya, suna ta cewa a gaida ke."
"Ina amsawa. Sai kuma na jika shiru, alhali ga maganar aure har tayi nisa, sannan ita kanta yarinyar baka ta6a zuwa gurinta kun tattauna ba."

Cikin sunkuyar da kai yace "kiyi ha'kuri Hajiya, wallahi aiyuka ne suka sakko ni a gaba kwanan nan, shiyasa bana samun damar zuwa gida."

"To shikenan Allah ya taimaka, yanzu gobe in Allah ya kaimu sai kayi 'ko'karin zuwa gidansu Saudat d'in."

Yace "Allah ya kaimu." nan suka koma wata hirar ta daban, kafin tasa sabuwar mai aikinta mai suna Azumi ta kawo masa abinci.

Washegari da yamma ya je gidansu Saudat kamar yadda Hajiya ta umarce shi, an yi masa tarba ta girma, don sosai aka karrama shi.

Duk da ba wata hira suka yi ba zuwan nasa yayi mata dad'i, bayan gaisuwa babu maganar da ta sake shiga tsakaninsu sai ma wayarsa da ya d'auko daga aljihu ya maida hankalinsa a kanta har na wani tsahon lokaci, kafin daga 'karshe ya mi'ke tare da ciro kud'i daga aljihunsa ya bata, tare da cewa duk wani abu da take bu'kata na biki ta yiwa Haidar magana, sannan yayi mata sallama ya tafi.

Tabbas bata ji dad'in abinda yayi mata ba, amma bata nuna ba ko a gida, haka taci gaba da al'amuranta kamar babu abinda yake damunta.

Sai zuwa dare ta kira Zainab 'kawarta ta sanar da ita duk abinda ya faru, amma sai Zainab ta kwantar mata da hankali da nuna mata duk abinda zai yi yanzu lokaci ne, ta 'kara ha'kuri ta shiga daga ciki, lokacin ne zata baza mulkinta son ranta.

Wannan shawarar itace ta saka ta cire damuwar abin daga ranta ta ci gaba da harkokinta da shirye-shiryen biki kamar yadda suka fara.

Saura kwana goma biki aka kai lefe na gani na fad'a, don sosai sukai 'ko'karin ganin anyi komai na burgewa ganin yadda Hajiya ta kasa 6oye yadda take son auren, kamar wannan ne aurensa na farko.

Duk wannan hidimar da ake su Amatullah basu sani ba, tunda Uncle bai sanar da su ba, gashi ita ba waya ba, bare taji a gurin wani daga gida, saboda har yanzu Uncle bai yarda ta ri'ke waya ba, yace sai ta shiga tertiary institution sannan zata ri'ke.

Bashir bai sake zuwa Kano ba sai ana gobe d'aurin aure, ya zo ranar juma'a da daddare, washegari Asabar da misalin 'karfe goma na safe jama'a suka shaida d'aurin auren Bashir Yusuf da umaryarsa Saudat Aminu.

Labarin d'aurin auren yana shiga gida zuciyar Saudat ta cika da murna da farin ciki, ko babu komai yau burinta ya cika, ta zama mallakin mutumin da ya sace zuciyarta tun bata gama sanin menene son ba.

Anci gaba da shagul-gulan biki daga duka 6angare biyun, itama Amarya a ranar tayi nata yinin bikin, da yamma kuma aka mi'ka Amarya gidan mijinta wanda ke kusa da gidansu.

Washegari 'yan biki kowa ya koma inda ya fito.

A ranar lahadi da daddare Bashir ya shiga yake sanar da Hajiya cewa gobe litinin da safe zai koma gurin aikinsa, amma Hajiya tace bata san zancen ba, sai dai ya tasa matarsa a gaba su tafi.

Wannan al'amari sam baiyi masa dad'i ba, amma haka ya bi umarninta, yana komawa gida ya sanar da Saudat da cewa ta shirya gobe za su koma porthercout, kuma fitar wurin za suyi, son jirgin 'karfe shida na safe za su bi.

Tana shiga d'aki ta kama rawa saboda murna, sai dai abu d'aya da ta tuna ya rage yawan farin cikinta shine yaransa da suke can, ta tabbatar ba zasu bari su sake ita da mijinta yadda take bu'kata ba.

Amma duk da haka zuciyarta ta raya mata zata ji da al'amarinsu.





*Ummu Aisha*
[8/29, 2:27 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, Wasila Abdu Unity Bank, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 15&16*

Bayan barin Bashir gidan a lokacin Hajiya ta kira Baba Mairo a waya, bayan sun gaisa ta sanar da ita batun auren Bashir, sannan ta 'kara da ro'konta akan don Allah ta saka ido akan zaman Saudat da yaran, ba don bata yarda da ita ba, a'a, sai don idan taga kuskure ta gyara musu, sannan kar ta bari a sami matsala daga yaran, don tana kyautata zaton daga gurin Saudat d'inma ba za'a sami wata matsala ba.

Bayan sun gama magana ta nemi da ta bawa Amatullah wayar tana so suyi magana da ita.

Nan Baba Mairo ta juya ta fuskanci Amatullah dake zaune a akan kujera ri'ke da littafin Bulugul Maram tana karantawa, ta mi'ka mata wayar tare da cewa "gashi Hajiya tana son yin magana da ke.

Ajje littafin tayi akan hannun kujera ta koma kusa da Baba Mairo ta kar6i wayar ta kara a kunnenta tare da sallama, bayan Hajiyan amsa ta narke murya cike da shagwa6ar da ta saba yiwa Hajiyan tace " Hajiya nayi kewarki."

Daga d'aya 6angare Hajiyan ta amsa da babu wata kewa ta da kikai, kin san zaki kewar tawa kika gudu kika barni?"

A shagwa6e ta 'kara cewa Allah kuwa nayi kewarki, kawai dai na dawo ne saboda su Muhibba ba zasu ji dad'in zaman ba, babu Aunty babu ni, kuma kinga shi Uncle idan ya fita office tun safe baya dawowa sai magriba."

Hajiya tace "eh, kin kyauta kam da kika koma, tun da ko ba komai zaki d'ebe musu kewa.

Yanzu haka magana nake son yi da ke shiyasa nasa Mairo ta baki wayar, a jiya an d'aurawa Uncle d'inki aure kuma a g......"

Cikin mamaki Amatullah ta katse ta da cewa "aure kuma?"

Hajiya ta amsa mata da cewa 'kwarai kuwa, kuma a gobe idan Allah ya kaimu za su taho tare da amaryar nan gurinku.

Abinda nake so dake Amatullah kar naji an sami wata 6araka daga gareku ke da 'yan uwanki, ku zauna lafiya da ita kiyi mata biyayya kamar yadda ki kaiwa Auntynki itama matar ubanki ce.

Sannan ki sani duk abinda ki kai da shi 'yan uwanki za suyi koyi, na tabbatar itama ba za'a sami matsala daga gareta ba.

To ina so kema kar naji wani abu ya 6ullo daga gare ki." Duk da maganar auren bata yiwa Amatullah dad'i ba haka ta yiwa Hajiya al'kawarin insha Allah ba za'a sami matsala daga garesu ba.

Suna gama wayar ta mi'kawa Baba Mairo wayarta zuciyarta cike fal da takaicin Uncle d'in nata, yanzu tsakanin da Allah da can da Aunty take 'kalau bai tashi 'kara aure ba sai yanzu da yaga bata da lafiya? Idan auren ne ya jira mana har lokacin da zata warke.

Wannan damuwarce ta sa ta ji karatun da take ya fita daga zuciyarta, sai ta rufe littafin tayi komawarta d'aki, tana shiga ta wuce toilet tayi alwala tayi shafa'i da wuturi sannan ta kwanta zuciyarta cike da tunanin irin zaman da za suyi da sabuwar Aunty tasu.

Da 'kyar barci ya d'auketa a daren.

Har da asuba da ta tashi bata qdawo cikin walwalarta ba, Baba Mairo na kula da ita bayan sunyi salla tayi mata nasiha sosai akan auren har sai da taga hankalinta ya kwanta ta rabu da ita suka fito don gudanar da aiyukan gidan kamar yadda suka saba tun bayan dawowar Amatullah garin.

Zuwa 'karfe bakwai na safe sun gama komai, an shirya yaran cikin uniform don tafiya makaranta. Amatullah ta sakko su a gaba don raka su buss stop d'in school buss d'in makarantarsu ke tsayawa don d'aukar yara.

Fitowarsu daga gidan tayi dai-dai da fitowar su Uncle daga cikin taxi d'in da ta kawo su daga airport, Amatullah turus tayi tana kallonsu ta kasa motsawa.

Yaran na ganin mahaifinsu suka kwasa da gudu gurinsa da murnar dawowarsa, cikin farin ciki ya shafa kan kowannensu, sannan ya ri'ke hannayensu ya nufi Amatullah dake tsaye guri d'aya.

Tana ganin sun nufo ta tayi saurin 'karasowa gare shi tare da yi masa sannu da zuwa, sannan ta dubi Saudat da zuciyarta ta cika da mamakin kasancewarta amayar Uncle d'in nata.

Haka kawai jininsu bai had'u ba, don duk had'uwar da suke da ita a gidan Hajiya magana bata ta6a had'a su ba, don haka kawai ita dai bata kwanta mata a zuciya ba.

Kamar ba zata kula ta ba, sai kuma ta daure tayi mata barka da zuwa kamar yadda ta yiwa Uncle d'in, sannan ta kama hannun yaran suka tafi tare da da cewa "Uncle zan raka su buss stop."

Wani kallo Saudat d'in ta bita da shi cike da mamakin ganinta a nan, don har ga Allah bata yi tunanin ganinta a gidan ba.

Tunaninta ta Yaya zata yarda ta zauna da wannan budurwar don kawai tana 'yar yayanshi? Wannan abu ne da sam ba zai yiwu ba, suma sauran yaran don babu yadda za tayi da su ne tun da shine ubansu.

Jikinta a sanyaye ta bi bayan Bashir d'in zuwa cikin gidan, inda Baba Mairo ta tar6e su da murnarta.


___________________________________________________


'Yan uwan Habiba kuwa ba 'karamin mamaki batun auren Bashir ya basu ba lokacin da labarin ya same su, don gani suke kamar ya nunawa duniya cewa a yanzu Habiba bata da sauran amfani a gurinsa tun da bata da lafiya.

A yanzu haka zaune suke a gaban mahaifiyarsu, dukkansu yaranta, suna tattauna maganar, kuma ba kowa ne ya had'a wannan gangamin ba sai Adda Jamila da tafi kowa jin zafin auren, cikin fusata Adda Jamila tace "ni zan kira Bashir d'in muyi magana, dole na sanar da shi cewa bai kyauta mana ba, ita kuma baiyi mata adalci ba.

Zuwa yanzu ya nuna mana lafiyarta kawai yake bu'kata ba wai....."

Umma ta katseta da cewa "me yasa baki da ha'kuri ne Jamila? Nace muku yaron nan ya sanar dani cewa saboda yaransa ya amince da auren yarinyar nan ba don wani babu ba.

Kuma ko babu komai ya kamata a kar6i uzirinsa, tun da har zuwa yau bai ta6a nuna gajiyawarsa da al'amarin Habiba ba."

"Amma Umma fisabilillahi idan saboda yara ne ina wannan yarinyar Amatullah da suke ri'kewa, sannan naga mahaifiyarsa ta bashi mai aikinta saboda kula da yaran, shi dai kawai yana bu'katar aure ne."

Babban yayansu mai suna Yaya Labaran da tun da aka fara maganar bai saka baki ba sai a lokacin yace "idan yana bu'katar aurenma ai ba laifi bane.

Shi 'karin aure ai ba zai zama laifi ba, tunda yana da halin ri'ke ko mata nawa yake aure, abinda baku sani ba ni kaina tun watannin baya nake bashi shawarar ya kamata yayi aure, amma ya 'ki.

Idan baiyi aure ba haka kuke so ya zauna? Ko kuwa ita Habiban kuna da tabbacin lokacin da zata warke, ko kuma don kar ya 6ata muku sai yayi ta zama haka babu mace? Wannan zancen banza kike yi Jamila, kuma da nasan dalilin taruwarmu a nan kenan da ba zan 6ata lokacina na zo ba."

Yana gama maganar ya mi'ke yayi tafiyarsa.

Gabad'ayansu da kallo suka bi shi har fita, sannan suka sauke ajiyar zuciya, Adda Kubra wadda itace Habiba take bi a haihuwa tayi magana da cewa "gaskiya maganar Yaya abar dubawa ce, Bashir yayi 'ko'kari ko ma nace yana kan yi, saboda a zamanin nan da wahala a sami namijin da zai ri'ke al'kawari haka, bai juyawa Habiba baya ba duk da larurar da Allah ya jarrabe ta da ita.

Sai nake ganin muma adalcin da zamu yi masa mu kawar da kai a kansa, don yayi aure ba wai yana nufin baya sonta bane, ko da tana da lafiya idan lokacin yin aurensa yayi dole sai yayi, kar ki manta duk yadda mai aiki zata kula masa da yara ba kamar matar da take zaman aurensa ba, mu dai fata d'aya da za muyi Allah yasa matarsa ta kasance mace ta gari.

Sannan ita Amatullah da kike magana nawa take? Duka-duka yarinyar nan bata cika shekara sha bakwai ba, to ta Yaya za'a bar mata d'awainiyar kula da yara.

Mu dai mu ci gaba da yiwa 'yar uwarmu addu'ar Allah ya bata lafiya."

Gabad'aya suka amsa da Amin, dukkansu sunyi amannna da maganar ta, wannan yasa dole Adda Jamila ta ja bakinta tayi shiru ta bar maganar.





*Ummu Aisha*
[8/29, 2:27 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, Wasila Abdu Unity Bank, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 17&18*

Lokacin da ta dawo daga rakiyar yaran bata sami kowa a parlour'n ba, sai ta shige kitchen kai tsaye ta zuba abinci ta fito ta zauna ta fara breakfast, har ta gama babu wanda ya fito.

Sai da ta shiga kitchen da cup da plate d'in da tayi amfani da su, tana cikin wankewa ta ji alamar bud'e 'kofa.

Bayan ta gama ta fito ta had'u da Uncle sanye da wasu suit ash colour a jikinsa, sa6anin sanda ya zo sanye da shadda, hannunsa ri'ke da brief case d'insa ta zuwa office, tambayarta abinda suka girka na breakfast yayi, ta gaya masa, sai ya zauna a dining ya umarce ta da ta kawo masa shima ya karya.

Lokacin da ta kawo sai ta tarar da Saudat itama ta fito, ta sauya shigarta daga riga da zani na atampa zuwa wata doguwar rigar shadda, abinka da mai 'kina sai taga tayi wani shirim a ciki.

Ajje musu abincin tai ta juya zuwa d'aki don yin wanka, ta barsu a gurin suna karyawa.

Da ta gama karyawa ma batai sake fitowa ba sai ta sami guri tayi kwanciyarta, d'in dama ta saba da hakan, tun da yanzu ba wani gurin take zuwa ba, ita ba 'kawaye ba bare ta dinga kai musu ziyara.

'Kawarta d'aya ce Shukurat 'yar gidan Maman Ganiya ce, suna mutunci sosai don tare ma suke d'aukar karatu da daddare a gurin Uncle, to itama iyayenta basu barta tayi S.S.C.E a porthercout ba, garinsu aka maida ita, kuma har yanzu bata dawo ba.

Barci ta sha sosai har wajen sha biyu na rana, sannan ta tashi ta wanke fuskarta ta fito parlour'n, sai ta sami Baba Mairo zaune ita da Saudat suna hira.

Abin mamaki Saudat na ganin Amatullah ta ja bakinta tayi shiru, kuma ta had'e fuskarta, Amatullah na ganin haka ko kula ta batai ba, ta yiwa Baba Mairo sannu ta wuce kitchen ta barsu a gurin.

Nan da nan Saudat ta sha'ka, don tana ganin wannan rainin hankali ne Amatullah d'in ta zo da shi, in ba rainin wayo ba tayaya tana kallonta zata wani share ta ta shige kitchen kamar na uwarta?

Tabbas dole ta gyarawa yarinyar nan zama a gidan nan kafin ta sa a maida ita gida, don ita sam ba zata d'auki wannan rainin ba.

Tana ta sa'kawa da warwara ta ji 'kamshi girki na tashi a kitchen alamun girki ake, ai kuwa ranta ya sake 6aci, ta tashi ta nufi kitchen d'in tana tunanin ba zata d'auki wannan rainin ba, ita da gidanta wata 'yar yarinya ta dinga abinda taga dama a ciki ita kuma ta zuba ido tana kallonta.

Daga bakin 'kofa ta tsaya tana kallon Amatullah dake juya kayan miyar da take soyawa a cikin tukunya tace "me kike yi a nan?"

Ba tare da ta juyo ta kalle ta ba tace "abincin rana na d'ora."

Cikin isa tace "wa ya baki umarnin d'ora abincin ranar? Ko kuwa nace miki ni ba zan iya d'orawa bane? Bazan d'auki halin nuna isa da gadara ba, nan gidan mijina ne, don haka ko d'orewar zaki ya kamata ki nemi izinina"

Ajje ludan hannunta tayi ta juyo ta kalle ta a cikin ido sannan tace "nayi tunanin haka kyautatawace a gare ki, sannan ko babu komai kya huta gajiyar hanya da kika kwaso, amma tunda bakya so Allah ya baki ha'kuri, kawai sai ta kashe gas d'in, ta sauke tukunyar daga kai, taje ta tari ruwa a tap ta wanke kayan miyar da ta fara soyawa ta wanke tukunya ta kife tai ficiwarta ta barta tsaye a kitchen d'in cike da takaicin mataki da Amatullah d'in ta d'auka.

Da ta fito ko a parlour'n bata zauna ba tayi shogewarta cikin d'aki taI zamanta.

Bata dad'e da zama ba, Baba Mairo ta shigo d'akin, kallonta take cike da tausayi, don duk abinda ya faru a kitchen tana jin komai, kuma tabbas indai haka Saudat d'in zata gudanar da al'amuran gidan to za'a samu matsala, amma ko a fuska bata nunawa Amatullah ta san abinda ya faru ba ta ce "yaya kika fito daga kitchen d'in baki d'ora girkinba? Kin San lokaci ya ja, yanzu sai ki ga yaran sun dawo suna kiran yunwa."

Amatullah ta amsa mata da cewa "yau ba ni zanyi girkin ba."

Da mamaki tace "waye zai yi?" Kamar bata San yadda sukai ba.

Ta amsa mata da cewa "matar gidance za tayi, tun da na d'ora tace bata bu'kata, shiyasa na ha'kura na fito."

Baba Mairo ta amsa da "to ai shikenan, Allah ya taimaka."

"Amin." Cewar Amatullah daga haka ta gyara kwanciyarta, itama Baba Mairo sai ta samu guri ta kwanta ko zata d'an runtsa.

Duk cikinsu babu wadda ta sake fita, ita Baba Mairo ma barci ne ya d'auketa, ita kuwa Amatullah idonta biyu bata bu'katar fitar ne shiyasa tayi kwanciyarta.

Lokacin dawowa a yaran nayi suka shigo kowanne goye da school bag a baya, tashi tayi ta sa suka cire uniform tai musu wanka ta shirya su cikin kayansu sannan ta samu guri ta zauna.

Ammar ne da Sam bashi da juriyar yunwa yace "Yaya Amatu abinci zan ci yunwa nake ji."

Dubansa tayi sai tace "ka je gurin sabuwar Aunty ka gaya mata, sai ta baka."

Gabad'aya yaran da kallo suka bita, tun da sun san su dai basu da wata sabuwar Aunty a gidan.

Fahimtar basu gane wa take nufi ba yasa ta ce musu "wannan ta d'azun da suka zo da Uncle ai itace Auntyn ku je gurinta zata baku abincin.

Ganin yaran sun 'ki tafiya yasa Baba Mairo dake saurarensu tace wa Amatullah "
ke ya kamata ki raka su ai, tun da yau tazo gidan nan basu saba da ita ba."

Kama hannunsu tayi duk su biyun suka fito daga d'akin tare, abin mamaki suna shiga kitchen d'in Amatullah ta ga tukunya a hannunta alamar lokacin zata d'ora girki.

Amma sai ta dake kamar bata me take ba, tace "Aunty Saudat ga su Muhibba sun dawa daga makaranta wai yunwa suke ji."

Wani kallon she'ke'ke ta juyo tayi mata sannan tace "sai su jira yanzu zan d'ora."

Cikin 'karfin hali ta sake cewa "Ammar baya iya jurewa yunwa, yanzu sai ya fara yiwa mutane kuka."

Ai da jin haka sai ta ajje tukunyar hannunta ta juyo gaban Amatullah tace "to gani ki bashi ya ci, tun da kin ce baya jure yunwa."

Bata sake kulata ba ta wuce inda suke ajje flask ta ta6a taji akwai ruwan zafi a ciki, sai d'auko kofuna guda biyu zata had'awa yaran tea, amma ga mamakinta sai cewa tayi kar ki kuskura ki ta6a min wani abu a kitchen d'in nan, naga wani tashen rashin kunya kike ji da shi to wallahi zanyi maganinki, kuma fita ki bani guri.

Itama amatullah da ranta ya fara 6aci tace "idan kinga na fita daga kitchen d'in nan wallahi sai na sama musu abinda zasu sa a cikinsu, kin hana ni dafa musu abinci da wuri, sannan kuma ki ce ba zan had'a musu tea ba?"

"To ki had'a d'in mu gani, tunda ke

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment