Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wadda suke fashin zuwa gida, kasancewar yanayin aiki ya saka su zama a kudancin 'kasar nan.

Sunyi abubuwa da yawa saboda sallah, sunyi cake doughnut da kuma dambun naman kaji, saboda ba'kin da ke shigowa gidan da sallah, sannan sun bar naman kaji wanda za suyi pepper chicken da shi gobe idan Allah ya kai mu, sannan da yamma Aunty ta fara had'a miyar da za suyi abincin sallah gobe, Amatullah kuma ta d'ora musu girkin bud'a baki saboda suna yin azumin arfa.

Kafin lokacin sallar magriba Amatullah ta had'a komai, ta gyara gurin kamar bata yi komai ba, tun farko ta samu wannan training d'in daga gurin Maminta, kuma daga baya da ta koma porthercout hannun Aunty Habiba itama bata barta ba, don kowane lokaci Mami tana nunawa Habiba kar ta bar Amatullah ta sangarce, dole ta koyi aiyukan gida kasancewar ta 'ya mace.

Ai kuwa zuwa yanzu ta fi kowa jin dad'in hakan, don sau da yawa Amatullah itace take kusan duk aiyukan gidan, gashi Allah yayi ta mutum ce da sam bata da 'kiwar aiki.

Tun da suka sha ruwa Amatullah ta kasa moruwa, don yau kam ta sha aiki, ga wahalar azumi, don dama Amatullah akwai raki in dai akan azumi ne.

Washegari tun 'karfe hud'u suka tashi suka shiga kitchen, Aunty suyar funkaso ta d'ora ita kuma Amatullah sauran naman kajin da suka ajje tun jiya wanda za' ayi pepper chicken da shi ta d'auko ta fara 'ko'karinta had'awa don dama tun a jiyan sun soya.

Cikin hukuncin Allah da wuri suka gama komai, zuwa 7:30am sun gama komai har sun yi wanka, lokacin ne kuma Uncle Haidar ya shigo da kuloli biyu wad'anda aka zubo waina da sinasir wanda aka bada order saboda sau'kin aiki.

Tare suka tafi masallacin idi da Uncle Bashir wanda ya fito cikin wata d'anyar shadda fara tas da ita, tasha d'inkina tazarce, da hula akansa, ba 'karamin kyau yayi ba, ko don bai fiye saka dogwayen riguna bane oho.

Uncle Bashir d'an gayu ne na nunawa, mutane da yawa suna mamaki idan akace musu shine mahaifin Muhibba, don a yanzu ne yake ganiyar cin lokacinsa.


___________________________________________________


Tun bayan sakkowa daga masallacin idi suke ta kar6ar ba'ki, har yamma, sannan Aunty ta samu sau'ki, don ita Amatullah tun azahar ta gudu gidan Hajiya, saboda gidan tun hantsi ya fara cika da jikokin gidan, kowa ya zo yiwa tsofi gaisuwar Sallah.

Kasancewar babbar sallah, akwai aiki yasa su Amatullah basu sami danar yawatawa ba sai bayan sallah da kwana uku, sun zagaya 'yan uwa sosai, inda basu samu zuwa ba kuma washegari suka je, daga nan kuma aka fara shirin komawa, saboda makarantar yara da kuma aikinsa shi kansa Uncle d'in da zai koma don dama hutun sati d'aya ya d'auka.

Lokacin da suka je sallama da Hajiya ta idar da sa'kon Alhaji na kar ya manta da maganar dawowar Amatullah Arewa don zana S.S.C.E d'inta anan, don Alhajin ya ce sam bai yarda da zana jarrabawarta a kudu ba, inda shikuma Uncle d'in yace insha Allah ba za'a samu matsala ba.

Haka su kai sallama da kowa suka tafi zuciyarsu cike da kewar gida da mutanen gidan.

Tun da suka koma kowa ya maida hankali kan al'amuransa kamar koyaushe, Amatullah yarinyaya ce da sam bata wasa da karatunta daga na boko har na islamiyya, don duk da suna kudu hakan baisa Uncle yin sakaci da karatunsu na addini ba ita da sauran yaran, kullum da daddare suke zama yake koyar da su da kansa, wanda hakan ya ja hankalin wasu musulman da suke ma'kwabtaka da da su, suma suke tura nasu yaran, sai gidan ya zama kamar wata islamiyya duk dare.

Zuwa yanzu Amatullah ta kai izifi hamsin da biyu a Al-qur'ani, kuma tana had'awa da sauran littattafai.


*TASHIN HANKALI*

Sanye take da uniform riga da skirt, skirt d'in coffe colour ne, da tsayinsa bai wuce gwiwarta ba, sai riga milk colour mai dogon hannu, sai hula itama kalar coffe da ta d'ora a kanta, duk da cewa a 'ka'idar uniform d'in nasu babu hula, itama sai an tashi daga school take sakawa, 'kafarta sanye cikin takalmi toms ba'ki da farar safa, sai school bag dake rataye a gefe kafad'arta ta hagu, tana tafiya cikin yanayin gajiyawa.

A 'kafar block d'insu ta tsaya dake cikin estate d'in na N.N.P.C quartz, buga 'kofar ta fara yi, sannan ta sa hannu ta tura ta shiga da sallama.

Yanayin da ta ga parlour'n ba 'karamin fad'ar mata da gaba ya yi ba, komai a hargitse gashi hatta TVn dake falon an fasata kwatsa-kwatsa, parlour'n dai babu kyaun gani.

Tana tsaye ta kasa gaba ta kasa baya don mamaki sai ga Aunty Habiba ta fito daga kitchen hannunta ri'ke da fasasshe jug na tangaran, ga jini yana zuba a hannunta, gashin kanta a hargitse.

Yadda Amatullah taga tayo kanta gadan-gadan, ya 'kara tayar mata da hankali, cikin zafin naman da bata san tana da shi ba ta fita waje da gudu, cikin sa'a ta ja 'kofar ta rufe Auntyn a ciki.

Tana fitowa ta fashe da wani irin kuka mai tayarwa da mai sauraronsa hankali, ko ba'a fad'a ba ta fahimci cewa Auntyn ta had'u da matsala ne na ta6in hankali.

Tambaya d'aya ta dinga nanatawa a cikin zuciyarta a garin yaya hakan ta faru, tunda ta san lafiya 'kalau suka rabu da Auntyn da safe, har tana yi musu fatan alkahairi.

Tunanin sanar da Uncle na ya d'arsu a zuciyarta don haka ta mi'ke da sauri zuwa gida na uku da suke ma'kwabtaka da su, da sallama ta shiga parlour'n duk da kasancewarsu ba hausawa ba, amma musulmai ne.

Maman Ganiya dake kitchen ta le'ko tana amsa sallamar, sai taga Amatullah, bayan ta gaida ita ta nemi da ta taimaka mata da aron waya, za tayi kira.

Kallonta matar tayi cike da tuhuma sannan tace "wa zaki kira?"

Kai tsaye ta bata amsa da cewa "Uncle zan kira."

Tambayarta ta sake yi da cewa "ina wayar Auntynki da ba zaki kira shi da ita ba?"

Nan take hawaye ya fara zuba daga fuskarta nan ta labarta mata halin da ta dawo daga makaranta ta sami Auntyn ita kanta ba 'karamin rud'ewa tayi ba da jin abinda yake faruwa.

Take ta bata wayar tace "ba hana ki wayar nake son yi ba, sai dai ina gudun ko wani abu ne ya faru tsakaninki da Auntynki zaki fad'awa mutane gida shiyasa, kinga ba zan so ace ni na baki aron waya ba, in wani abu ya faru za'a ga kamar ni nake zuga ki.

Kar6ar wayar tayi ta saka number Uncle ta kira, har kiran ya katse bai d'aga ba, ta sake kira bai d'aga ba, sai a kira na uku ya d'aga shima don ya ga mai kiran ya'ki ha'kura ne.

Amatullah na jin an d'aga kiran cikin muryar kuka tace " Uncle don Allah ka zo gida Aunty bata da lafiya."

Nan take hankalinsa ya tashi, musamman jin yadda Amatullah ke kuka ya san al'amarin ba 'karami bane.

"Me ya same ta?"
Itace tambayar da ya jefowa Amatullah, amma Maman Ganiya da ke kusa sai ta girgiza mata kai, alamar kar ta gaya masa, don haka sai tace "ni ban san me zan ce maka ba, amma dai bata da lafiya, kazo ka ga yadda take yi."

Yace "to shikenan gani nan zuwa yanzu."

Tare da Maman Ganiya suka koma gidan, ita dai Amatullah kasa shiga ciki tayi, sai Maman Ganiya ce ta shiga, amma itama da gudu ta fito don da gudu Aunty Habiba tayo kanta duk da a yanzu babu wani makami a hannunta.

Suna tsaye a waje cirko-cirko Uncle Bash ya iso gurin hankali a tashe, tambayarsu yake me ya faru, amma Amatullah ta gaza bashi amsa sai kuka take, Maman Ganiya ce tayi 'karfinta halin ce masa "ka shiga ciki Maman Ammar babu lafiya."



*Ummu Aisha*
[8/29, 2:27 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 9&10*

Babban abinda yake bashi mamaki sun kasa ce masa ga takamaimai abinda ya same ta, sai dai su ce bata da lafiya, kuma gasu tsaye a waje sun kasa shiga cikin gidan bare su taimaka mata.

Ganin tunanin ba zai amfana masa komai ba yasa ya bud'e 'kofar ya shiga, sai dai shima tun daga bud'e 'kofar ya fuskanci akwai matsala. Kafin ya samu damar wani tuna taiyo kansa tana wani irin 'kugi, cikin zafin nama yayi caraf ya ri'ke duka hannayensa biyun.

Ganin yanayi da take ciki baya bu'katar 'karin bayani, duk da wannan ba'kon al'amari ne da bai ta6a faruwa da ita ba.

A iya zamansa da Habiba ko aljanu bai ta6a ganin ko jin labarin ta tayr ba, bare wata rana ayi tunanin al'amari irin wannan zai iya faruwa da ita.

Yadda taiyo kansa haka shima cikin dakiya irin ta maza ya isa inda take da nufin kamata, a take komawa ta harmutse a tsakaninsu, har sai da Maman Ganiya dake tsaye daga ba'kin 'kofa tare da Amatullah ta shiga ciki don taimaka masa.

Amatullah da har lokacin take sharar hawaye ya kira ta d'auko masa abinda zai d'aure hannunta, da sauri da shiga d'aki, nan da nan ta fito da wani d'an 'karamin mayafi daga gani na Muhibba ne ta mi'ka masa, cikin nasara Allah ya bashi sa'ar d'aure hannayenta suka biyun.

Da wannan damar yayi amfani ya samu ya kaita mota, sannan ya tafi da ita asibiti, ya bar Amatullah a gida saboda kar yaran su dawo daga makaranta au tarar babu kowa.

Cikin gaggawa likitocin suka kar6eta, don ganin irin halin da take ciki.

Bayan kamar awanni uku likitocin da ke tare da ita a d'akin da aka shigar da ita suka fito, likita d'aya ne ya bu'kaci Uncle da ya bishi office yana aon magana da shi.

Kusan a tare suka shiga office d'in, sai bayan likitan ya zauna ya nunawa masa gurin tare da umartarsa da ya zauna.

Sai da ya d'auki biro da takarda yayi 'yan rubuce-rubucensa sannan ya d'ago ya maida hankalinsa kansa.

Sai da yasa hannu ya zare glass d'in fuskarsa sannan yace "maganar gaskiya a yanzu dai bamu gane menene ainihin matsalata ba, sai dai daga nan zuwa gobe muna saka ran dawowar babban likitan 'kwa'kwalwa na asibitin nan daga tafiyar da yayi, sai ya duba ta.

A yanzu haka mun yi mata allurar barci, kuma zamu ci gaba da yi mata ita har zuwa lokacin da zai iso, don ba zai yiwu a barta haka ba, ko don wannan doke-doken da take.

Godiya sosai Uncle yayi ga likitan, duk da har lokacin a tashe ya ke, tashi yayi ya fita daga office d'in likitan, sai ya d'auko wayarsa da ke aljihu ya kira Hajiya, tun suna gaisawa daga muryarsa ta fahimci a cikin tashin hankali yake.

Tambayarsa ta fara yi da "me ya faru najiuryarka haka bashir?"

Cikin wani rauni da ya 'kara a zuciyarsa saboda jin muryar mahaifiyarsa yace "Habiba ce bata da lafiya Hajiya, yanzu haka muna asibiti."

Itama cikin yanayin damuwar tace "sunhanallah, me ya same ta?"

"Wallahi Hajiya lafiya na fita office na barta, amma d'azu sai ga Amatullah ta kira ni a waya tana kuka, wai nazo ta dawo gida ta tarar Auntynta ba lafiya.

Ina dawowa na same ta cikin yanayi na ta6in hankali."

Hajiya tace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un! Ta6in hankali kuma?"

A sanyaye yace "wallahi kuwa."

"To yanzu me likitocin suka ce?"

"A yanzu dai sunce basu gane komai ba, amma gobe in Allah ya kaimu babban likitan 'kwa'kwalwa na asibitin zai zo, sai ya duba ta."

"To Allah yayi mana ji nagari, ita kuma Allah ya bata lafiya."

"Amin." Ya amsa a sanyaye, da haka su kai sallama.

Mahaifiyar Aunty Habiba ya kira itama ya sanar mata da halin da suke ciki, sannan ya ro'keta da ta taya su da addu'a.

A lokacin yayin tunanin komawa gida ya duba halin da yaran suke ciki musamman amatullah da ya bari tana ta faman kuka, amma sai da ya fara le'kawa d'akin da aka kwantra da ita ya ganta sannan ya tafi cike da tausayin ta.


* * * * *


Bayan tafiyarsu asibitin da kyar Maman Ganiya ta samu ta lalla6ata ta daina kuka, da farko so tayi ta tafi da ita can gidanta, amma sai ita Amatullah d'in ta 'ki, saboda tana son zama ta gyara gidan son muninsa yayi yawa saboda fashe-fashen da Aunty tayi.

Ha'kura tayi ta koma gida, son lokacin dawowar yaranta daga makaranta yayi.

Ita kuwa Amatullah gyaran parlour ta shiga ya, sai da ta tsince duk wasu abuwa da suka fashe cikin takatsan-tsan, saboda tsoron karta yanke.

Sannan ta d'auko tsaintsiya ta share parlour'n tsab ta sake mopping, daga nan sai ta koma kitchen, shima sai da ta gyara shi, sannan ta d'ora abinci mai sau'kin dahuwa saboda yaran gab suke da dawowa daga makaranta.

Cikin lokaci kad'an ta gama girkin sai ta koma d'aki ta cire uniform tayi wanka ta sauya kaya, dama tana cikin rlfashin sallah.

Tana 'ko'karinta fitowa parlour yaran suka shigo d'akin da sallama, bayan ta amsa musu sai ta tsaya sai da yayiwa musu wanka, ta sauya musu kaya sannan suka fito parlour'n tare.

Abincin ta zubawa kowanne a cikinsu suka fara ci amma ita ta kasa ko lauma d'aya, Ammar sai tambaya yake ina Umminsu, sai Amatullah tace "sun fita unguwa ita da Uncle."

Shi kuwa Ammar yana kano tun tahowar sallah basu taho da shiba, don Uncle Haidar ne ya hana saboda sha'kuwar dake tsakaninsa da yaron.

Bayan sun gama ci ta kwashe komai ta gyara gurin, tana kitchen tana wanke kwanukan da suka 6ata Ammar ya shigo kitchen d'in yana tambayarta "Yaya Amatullah me ya sami TV? Na zo zanyi kallon catoon naga ta fashe.

Nan take wani hawayen ya aake cikowa a idon Amatullah, ta faki idonsa ta goge, don Ammar yaro ne mai matu'kar wayo, idan ta fahimci tana kuka zata sha tambaya a gurinsa.

A sanyaye tace "nima ban sani ba Ammar, ka jira idan Aunty ta dawo daga unguwa sai mu tambaye ta."

Sai yace to kawai ya juya parlour yaci gaba da al'amuransa.

Sai gab da lokacin sallar magriba Uncle ya dawo gidan come da damuwa, dukkansu a parlour ya same su, Ammar yana ganin ya rufe 'kofar bayan ya shigo ya fara tambayarsa ina umminsa.

Cike da tausayawa ya bashi amsa da cewa "bata da lafiya tana asibi ana yi mata allura, ko na kaika gurinta?"

Cike da alamar tsoron yaron yace "a'a zan zauna da Yaya Amatullah a gida sai ta dawo."

Daga haka bai 'kara cewa komai ba ya shige cikin d'akinsa, sai da yayi wanka da alwala ya shirya cikin jallabiya sannan ya fito.

Duk a zaune ya same su a parlour, Amatullah da Muhibba sanye da hijabai Ammar da alwalarsa suna jiran ya fito ya jasu jam'i kamar yadda suka saba.

Bayan sun idar da sallar ta gabatar masa da abinci, sai ya tambaye su da cewa "kowa ya ci?"

Har Amatullah tace amsa masa da "eh," sai Muhibba ta sanar masa Amatullah bata ci ba, nan ya zaunarta a gabansa sai da ya ga ta ci sannan ya rabu da ita.




*_Yau ban samu damar yin editing ba, don Allah kuyi ha'kuri da errors da kuka gani a cikin rubutun._*


*Ummu Aisha*
[8/29, 2:27 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 11&12*

Washegari likitan ya zo kamar yadda aka sanar da shi, tun da ya zo yasa akai wasu gwaje-gwaje da hotuna, sai zaman jiran sakamakon a ke.

Bayan kwana biyu kuma yayarta da Aunty Hauwa yayar Uncle Bashir suka zo, don al'amarin ba 'karamin tayarwa da mutane hankali yayi ba.

Tun da suka zo babu abinda suke yi sai addu'ar Allah ya bata lafiya, kamar yadda a can gida aka dage da addu'o'i da saukar Al'qur'ani akan Allah ba bata lafiya.

Cikin sati gudu duk sakamakon da ake jira sun fito, sai dai abin mamaki duk iyakar binciken likitocin sun kasa gano abinda ya same ta, saboda komai nata lafiya yake.

Wannan ya sa Alhaji Babba cewa a taho da ita gida, a gwada a nan kuma ko Allah zai sa a dace.

Dole suka tattara gabad'aya har yaran suka dawo kano, don nema mata magani a nan.

Duk mai imani idan yaga Habiba sai ya tausaya mata, mace 'yar gayu mai son kwalliya da 'kwalisa amma a wannan yanayin.

Da farko an kaita wata babbar cibiya ta magungunan muslinci, inda suka fara bata magungunansu, cikin hukuncin Allah sai akai nasara ta daina buge-buge da kai duka ga duk wanda ya zo kusa da ita.

Bisa bincikensu sun tabbatar da cewa sihiri ne akai mata, kuma iya karatunsu Aljanun da aka turo mata sun 'ki yin magana, sai dai idan anayi kaji tana wani irin 'kugi, amma babu magana.

Kusan watanni uku ana abu d'aya amma babu nasara, dole suka fantsama neman magani, duk inda suka ji labarin wani mai magani zasu je gurinsa, amma amma sau'ki dai shiru har yanzu ba'a dace ba.

Tun tuni mahaifiyarta ta nemi alfarmar tafiya da ita gida don kula da ita, kuma aka bata dama, su kuma yaran gabad'aya suna hannun Hajiya.

Ganin neman magani ake babu alamar nasara ya sa aka matsawa Bashir da ya koma wajen aikinsa, dole ba don ya so ba ya amince.

Sai dai an sha ta'kaddama da shi, don dagewa yayi kai da fata sai ya tafi da yaransa, su Hajiya kuma suka ce ba zai yiwu ba, shi kuma ya dage akan cewa da wanne zai ji, da rashin mahaifiyarsu ko kuma da rashinsu?

Dole daga 'karshe aka amince masa tafiya da su, sai Hajiya ta ce Baba Mairo ta shirya ta bisu saboda kula da yara, nan da nan kuwa ta fara had'a kayanta.

Lokacin ne kuma Alhaji Babba yace ba za'a koma da Amatullah ba, tunda yanzu an shiga second term, dole ta zauna a gida a samar mata makaranta ta fara zuwa sai tayi S.SC.E d'inta a nan.

Haka kuwa suka had'a ya nasu-ya nasu suka koma suka bar kowa da kewarsu musamman Amatullah don ma an bar Muhammad a Kano yanzu ma ba'a tafi da shiba, don Hajiya ta hana.

Haka lokaci yaci gaba da tafiya, zuwa yanzu su Amatullah har sun fara jarabawarsu. A 6angaren Aunty Habiba kuwa sai dai godiyar Ubangiji domin babu wani ci gaba da aka samu, sai dai duk da haka basu karaya ba, duk ind a suka ji labarin wani mai magani sai sun je.

Wani mai magani ne da suka je gurinsa ya tabbatar musu cewa duk wadda tayi sihirin nan macece, kuma saboda mijinta tayi, kuma asirin bashi da makari sai dai idan auren ita wadda ta sa akayine ya mutu, to tabbas haukar zata koma kanta, ita kuma Habiba ta warke.

Wannan magana ta girgiza iyaye da 'yan uwan Habiba, amma sai mahaifiyarsu ta hana gayawa kowa, har Bashir, saboda ba kowa ne zai yarda da maganar ba, sannan basu da tabbacin wadda ta aikata wannan mugun aikin, sai suka ci gaba da yin addu'ar Allah ya tona asirin ko wacece, ita kuma Habiba Allah ya bata lafiya.

Lokacin da Amatullah ta gama jarabawa cike da d'oki ta tattare kayanta ta koma porthercout, don dama duk hankalinta na can saboda 'yan uwanta.

Suma yaran ba 'karamar murna suka yi ba da dawowarta don sunyi kewarta sosai.


___________________________________________________

Kullum burinsu su wayi gari su ga Habiba ta warke amma Allah bai nufa ba, zuwa yanzu shekara guda kenan da faruwar al'amarin.

A wannan tsakanin ne kuma su Hajiya suka matsawa Uncle da maganar aure, da farko ya so ya 'ki maganar, amma ganin yadda ran mahaifansa yake neman 6aci akan maganar ya sa ya ha'kura.

Musamman da ya tuna wayar da su kai da Baban yayansa Yaya Mukhtar wato mahaifin Amatullah, yayi masa nasiha sosai, da nuna masa fa'idar kar6ar 'kaddara kowacce iri ce, sannan ya 'kara da cewa "wannan auren da ake so kayi ba don komai bane sai dan kare mutuncinka.

Ka ga dai ita matarka bamu san lokacin da Allah zai bata lafiya ba, kuma ba zai yiwu mu zuba maka ido muna kallonka haka ba, sannan ba rabuwa muka ce kayi da ita ba, tun da 'kaddara ce Allah ya aiko mana gabad'aya, don baza mu ware kanmu ba.

Ko ba don komai ba ma saboda yaran nan ya kamata kayi aure, ko zasu samu wadda za su kalla a kusa da su a matsayin uwa, ita kuma sai mu ci gaba da nema mata magani da kuma addu'ar Allah ya bata lafiya.

Sosai Bashir ya kar6i shawararsa duk da ba wai don yana so bane, sai don nuna biyayya a gare su.

A ranar ya kira Hajiya ya sanar da ita, ya amince zai yi auren, amma shi bashi da za6i, duk wadda suka ga ta dace da shi, su za6ar masa.
Ai kuwa tayi murna da jin wannan magana sosai, nan take ta yanke shawarar nema masa auren Saudat, 'yar ma'kwabtansu ce, gidan na kallon gidan Hajiya.

Ta yaba da tarbiyyar yaran gidan sosai, sannan yadda take nuna kulawa ga Muhammad sosai, kusan kullum sai ta shiga gidan Hajiya d'auko shi ko kuma ta tura a d'auko mata shi.

Wannan 'kauna da take nunawa yaron yasa Hajiya ta ji hankalinta ya kwanta da ita, kuma tana hasashen insha Allah ba za'a sami matsala daga gareta ba akan yaran.

Takanas Hajiya ta aika aka kira mata ita don tana so tayi magana da ita, kafin maganar ta je gaban iyayenta, don ba za ta so ta zama sanadin yiwa 'yar mutane auren dole ba.

Wajen 'karfe biyar na yamma ta shigo gidan, cikin shiga ta kamala, sanye da riga da zani na atampa, d'inkin ya zauna jikinta, kasancewarta mace mai 'kiba.

Har 'kasa ta tsugunna ta gaida Hajiya cike da girmamawa, wannan yana d'aya daga cikin d'abi'unta da Hajiya ke so wato girmama na gaba da ita.

Hajiya tace "sai kika ji kira bagatatan ko?"

Cikin sunkuyar da kai tace "eh wallahi, ina ta tunanin Allah yasa ba wani laifin nayi ba."

Gyara zama Hajiya tayi sannan tace "lafiya 'kalau, sai dai akwai maganar da nake so muyi da ke, ina bu'katar ki sanar dani gaskiya akan tambayar da zanyi miki."

Gabanta banda fad'uwa yake sosai don bata san tambayar da zata yi mata ba, a sanyaye tace "insha Allah zan fad'a miki gaskiya."

"Ina son nasan shin akwai wani da kuka yi al'kawarin aure da shi ne, ko magana makamanciyar wannan?"

"A'a, gaskiya babu."

"Saboda me?" Hajiya ta sake tambayarta.

"Wallahi Hajiya duk ban gamsu da halayensu ba."

"Masha Allah." Cewar hajiya.

"To yanzu kuma alfarma zan nema daga gare ki, Allah yasa zan samu."

"Hajiya kin fi 'karfin neman alfarma a gurina, sai dai ki bani umarni na bi, domin kema uwata ce, na

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment