Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu ruwan shi."

       A hankali sauran matan gidan suka fara juyawa suna watsewa a wurin.
"Talatu ki kira min Uban shi ya zo ya ciro shi" ciki matsanancin damuwa. Ta ce mata.
"Kiyi hakuri zai dawo Insha Allah, Kinsan baban su ya ce kar na kuma mishi maganar Zayn Malik, ban san ya zan yi ba" ta fada itama cikin damuwa sosai, babu uwar da zata so a ce nata ya lalace, sai dole amma ina ba dan haka ba yaushe Zayn  zai zama haka a cikin unguwa duk da bata san abinda ya faru ba, tana da yakinin yana da gaskiya baya aikata kome sai da hujjar shi.

   Tun karfe biyu ake niman wanda zai amso ZM a hannun yan sanda har dare,

A bisa al'adar gidan idan mazan suka dawo kasuwa, dakin Hajiya Hajiya Umma suke fara shiga kafin su wuce na manta su, Alhaji Uwaisu shi ya fara shigowa gidan, dan haka aka gaya mishi. Be yarda ya shiga wurin Umma ba sai da ya tura Bashir kanin su, kuma babban Uban dakin ZM.

"Assalamu alaikum!!" Aka rangad'a sallama daga bakin kofar Hajiya Umma.
Sai da ta kunkure bakinta sannan ta mike a hankali tana daura zanin ta, ta bude kofar ban dakin ta watsar da ruwan bakin ta. Sannan ta amsa sallamar da kyar.
"Wa'alaikumunsalam" daga haka ta tashi ta koma saman kujeran ta zauna tana taunar goro hannunta dauke da casbil. Sake sallamar aka yi nan ma ta amsa. Sannan ta cigaba da abinda take.
"Umma kiyi hakuri gani nan sai yanzu na samu labarin abinda." Wani lafiyayyen harara ta wurga mishi wanda ya bashi damar hàdiye sauran kalaman ta. Suna cikin haka aka sake sallama,  daure fuska tayi tam.
"Wa'alaikumunsalam"  har da sauran da suke cikin dakin kana ganin su kaga Yaran ta, watsa musu harara tayi iyaka sannan ta juya musu baya tana zumbura baki.
"Umma kiyi hakuri! Insha Allah na tura Bashir ya tawo da shi. Amma maganar gaskiya ki mishi magana ya daina abinda yake domin wallahi"
"Idan ka shirya koran mu a gidan ba sai ka rantse ba, ai na jima da tanada kudin hayan da muke a gidan ku. Kawai Yaro bai da ikon yayi dan wasa jinin shi sai a shiga tsatsagar shi me ye da ake niman kama min kurwan Yaro kawai idan ka gaji da zama damu Abdulmaliku ka kare ni da Baban Umma ka huta ganin mu kawai"

Kallon sauran Yaran tayi da suka sunkuyar da kawunan su, ta zabga musu harara kamar idanun ta zai fadi ta ce musu.
"Kun wani sunkuyar da kai kamar wasu Na Allah, nan kuwa munafukai ne baki dayan ku, sai gyada kai kuke kamar kadangare yasha hantsi. Ku tashi ku bani wuri munafukan banza munafukan wofi, ku da zaku  boye shi kune kuka mika shi ga yan sanda masu rusa-rusan kai kamar tukwanen shuka."
"Allah ya huci zuciyar ki" inji mahaifin Zayn Alhaji Abdulmalik Yanzu haka Bashir yana can! Amma Hajiya a mishi magana abin da yake janyowa yana tab'a martabar siyasata"

"Na kwad'a siyasar na cinye aikin banza, anya AbdulMalik anya kana kaunar Malami kuwa? Yaro karami ka mishi kawon zuga!"
"Hajiya Zayn din ne karami? Shekaru talatin da shida, sau nawa ina nima mishi aure yana ki

Office din Yan sanda.

Kallon shi ispetor na yan sandan yakin yayi, sannan ya kalli wani babban mutum da yake gefen su da wata budurwar yarinya. Murmushi yayi sannan ya mai da Idanun shi kan dan sandan.
"Officer kace me dan ban fahimci abinda kake nufi ba?"

Kallon yarinyar yayi da mutumin gefen ta ya ce mishi.
"Wannan yarinyar me suna Radiyah, tace kai ne ka mata cikin jikin ta"

Dariya yayi sannan ya juya yana kallon yarinyar, kafin ya ce mata.
"Ke!" Da sauri ta d'ago kai tana kallon shi.
"Kika ce abinda yake cikin ki nawa ne?" Yadda yayi maganar yasata girgiza mishi kai.
"Magana nake dake, kuma magana zaki yi"
"Yallabai kaga yana bude mata ido"

Wata ƙatuwar harara ya wulla mata, tare da mikewa.
"Officer ka tambaye ta na tab'a had'a hanya da ita?"  Ya tambaye ispetor yana zare idanun shi.

"Mr Malik calm down! Wannan case din bana nan ne aka shigar da kara amma kasan ba zan  tab'a barin wani abin kunya ya faru da kai ba, balle Alhaji AbdulMalik Zain Malami ba, dan haka ka kwantar da hankalin, kasan case din is About money by..."

Mikewa yayi tsaye ya zuba hannu a kugun shi, ya kalli Yarinyar sannan ya cewa baban ta.
"Zan kebe da Yarka?"
"Yaro bana son abin kunya" juyawa yayi gaban ispetor din ya gyada kai, mikewa dan sanda yayi ya fitar da tsohon waje,  takowa yayi gaban Yarinyar yana kallon ta from toe to head. Cikin wani killer smile ya ce mata.
"Chilling yan mata let me serve you"
Cak ya dauke ta sama, tare da kallon yadda take kokarin magana.
"Don Allah ka rufa min asiri, wallahi biyan mu aka yi dan Majalisar dokokin na garin nan Alhaji Musa Me gari" wurga da ita yayi sannan ya gyara tsayuwar shi.
"Sanata ko?" Girgiza kai yayi sannan ya juya ya fita.

Daga shi sai gajeran wando da rika open chears, yana tafiya kawai zaka fahimci shi din kiran mutanen farko ne, ko ba a gaya maka ba, domin gefen hannun shi tattoo, tsayawa yayi a gaban Uban Yarinyar. Ya ce.
"Kaci Arzikin furfuran ka, da sai nayi ta kwallo da kai wallahi sai na kareraya kashin ka. Akan dan karamin kudi zaka bata shekarun ka!"

"Muje my Boy an gama na yau!"inji wani mutum da yake dauke da takardu da brifcase.
"Uncle bash kafin nan bari na fara zuwa gidan Sanata Musa Me Gari"
"That's my Boy naji kome a wurin ispetor" suna fita kuwa yan jarida suka musu caaaa.
Daga can wata yar jarida ta wurgo musu tambaya.
"Brrst Bashir Zayn Malami shin dama dagaske an jima ana zargin Mr Malik da abin kunya?"

Body guard din Brrst Bashir Zayn Malami ne, suka fara kokarin kare su.
"Zayn Malik Malami dama da gaske kai dan dan daba ne? Dama an jima ana zargin ka da Safaran miyagun kwayoyi da lalata Yan mata shin da gaske ne?" Juyawa yayi sannan ya Zubawa yar jaridar idanu.
Murmushi yayi sannan ya taka har gaban ta, duk da Brrst Bashir yana jan shi bai fasa ba, sai ya ya isa gaban ta sannan ya rike abin nad'an murya ya ce mata.
"Waye ya sani tunda kina cikin su!" Yana fadar haka ya juya abin shi, har dai tafi ya koma dawowa gaban ta ya wani fisgota sai da ya haɗa da kirjin shi.
"I like your dress, you look sexy, amma idan kika sake ba iya gidan jaridar ba hatta wanda ya tsaya miki sai na saka buldoze na binne ku da ranku make my words"

Wani shegen tsoro ne ya kamata, yan jarida basu fasa saukar shi a hoto, hakan ya shiga motar yana me kwantar da kujeran shi.
"ZM"
"Kaci kutmar Ubanka sauka a motar shege" ya fada zafaffe.
"Muje Sam" inji Brrst,
"My Boy!"
"Meye?"

"Ka kwantar da hankalinka"
"Sam ka kai ku resident na Sanata Musa Me Gari!"
Babu musu sam ya bawa motar wuta. Suka nufi gidan sanata Musa Me Gari. Har cikin gidan ya shiga, ya samu sanata yana tattaunawa da wasu yan jam'iyyar shi. Cikin fushi ya bude motar sannan ya nufi inda sanata yake.
Bodyguard din sanata ne suka fara kokarin dakatar dashi, cikin fushi ya mangare daya ya kuma saka kafa ya kwashe dayan.

Yana isa gaban Sanata ya riko kwalar rigar shi.
"Zayn Malik!" brrst Bashir Zayn Malami ya daka mishi tsawa, amma ina jan Sanata yayi ya nufi wurin da aka tara ruwan da agwagi suke wasa ya tsuma kan shi.
"Ban damu ba idan ka tafi gidan Yari dan ka karya wuyar dan iska mara mutunci, ko ciwo dan Allah ya saukar be dan ya kankara zunubi amma da ina da iko ahalina ba zasu yi jinya ba, kai ne zaka kai min ahali matakin bakin ciki, toh wallhi na kuma ganin haka dai na kashe banza irin ka" sannan ya cire kan shi ya cilla gefe guda. Yana tsaki,

*Hi Habibity na fara zayn Malik sabida wasu dalilai, kuma nan da karshen wata zai zama ana azumin arfa so kwanakin Ibadat ne ba na shiririta ba! And ZM na kudi ne 300₦🔞 abu na gaba labarin zai zo yadda ba zaku yi nadamar shi ba thank you fanmily's*

PAID BOOK
[6/25, 9:01 AM] Queen: _....ZAYN MALIK....✿_

*EXQUISITE WRITERS FORUM*
   
              Mai_Dambu

CHAPTER-04
Darkness
"Sannu d'anan! Sannu tako a hankali karka motsa domin Allah kadai yasan iya adadin lokacin da ka dauka kana jele da ciwo ikon sai lillahi, dama haka kake da hakuri da alamu duk matasan gidan nan babu na biyun ka a jarumta, sannu kaji zauna maza zan tsaya ka karya mu tafi asibitin"
Zama yayi tare da wani narke mata yana kara kwantar da kan shi a kafadar ta.
"Hajjos! Good morning?"
"Ayya zafin ciwo yasa ka min Yaren nasara bayan kasan na yashe mishi albarka sannun kaji"
Daga saukowa shi zuwa zaman shi ta mishi sannu ya kai sau bakwai zuwa goma.
"Kallon Yaranta tai da suka zuba musu ido, itama sake baki tayi tana kallon su kan ta a karkace.
"Hala kun tashi daga cutar makanta ne?"
A firgice suka kalle ta, suna fadin.
"A'a " lokaci guda.
"Yoh daure bakin ku aka yi da ba zaku mishi ya jiki ba ko sai na roka?"
"Atta hajiya"
"Uwaka auta!" Ta dankwalawa Uncle bashir hannu bibbiyu.
"Sannu son ya jikin ka?"
"Meye Sannu soooo ya jikin ka Banu tausayi da Imani ne? Wani sooon sai kace dan kasar masu kananun ido wadancan masu magana da hanci!" Wato china,
"Zayn ya jikin ka?" Inji Baban shi.
"Rashin kunya sunan Ubanka kake kira gatsau? Kaii" ta kalli Alhaji Uwaisu da bai yi magana ba dama Uncle Bashir da Abba suka yi magana.

"Sannu ya jikin naka Babana?" Ai kuwa fadada murmushi Hajiya tayi tana cewa.
"Ai Uwaisu yaron nan jiya da kyar yayi barci," kallon juna suka yi, kamar ance ta kalle su, sai kuma ta gimtse fuska.
"Nayi karya ko ? Tabawa, maza wuce sama ki dauko min jakata, da akwai kudi a kasan matashina ki hada ku tawo min dash" Ta tambaye su tana bada umarni, cikin sauri Tabawa ta cika umarninta.
"Wane mutum Hajiya ta, ai bani da ta ukun ki" inji Zayn.
"Ikon Allah Zaynu akwai ta daya na da ta biyu na kenan?"
"Inji waye? Ai hajjos kaf Naija babu wanda ya isa shan gaban ki, ke da nake cewa idan na tashi aure gidan nan zamu bari mu kama haya"
"Yo na sani ko an mana farraku? Tunda muna da masu baki da mudu. Yanzu dai bari Talatu ta kawo abinci sai muje na kaika asibitin"
A zabure ya ce mata.
"What??"
Wani mahaukacin dariya Uncle Bashir ya sake yana cewa.
"So curious and Hilarious"
Abban Zayn shima murmushi yake yana kallon yanayin Zayn yadda mood din shi ya sauya once.
"Ai zan kai ka ne da kaina na musu bayani, lokacin kana yaro idan ja cilla fitsari daga bakin kofa sai ya wuce waje, sannan a lokacin lafiyar na lau" ta fada in comfort, kallon Uncle bashir yayi yana mishi magana da ido.
"Kace mata lafiya ta lau"
"Ayya Hajiya kiyi hanzarin kai shi dubi yadda yake zare idanu alamar ciwon yana cin shi"
"Ai shi yasa zan maza na shirya mu tafi kar mu makara!"
Dafe Goshi yayi yana faɗin.
"Wallahi lafiya ta lau Hajiya Umma"
"Ai kowa haka yake gani lafiyar ka lau shi yasa basu damu da kai ba, zan kai ka domin idan nace Bashir ya kai ka, yanzu zai dauki kundin su na lauyoyi yana rabtabo bayani, idan kuma mace Ubanka ne gashi nan yanzun zai mike yana cewa halo. Idan kuma Uwaisu ne zai ce min ya makara wa kake da shi da ya damu da kai?"

Shigowar Mama da hajiya Umaima kishiyar ta, sai Aunty Rukayyah matar Uncle Bashir, sai Hajiya Maimouna matar Alhaji Uwaisu, dukkan su dauke da kayan abinci, a hankali suka shiga jerawa suna kallon Hajiya da Zayn dinta.
"Son idan ka karya zan baka aika zuwa gidan mu kaji" inji Aunty Rukayyah,
"Bafa inda zai je tam"y inji Hajiya, kallon Uncle bashir tayi taga ya D'aga kafadar shi, Murmushi Hajiya Maimouna tayi tana son ganin draman Hajiya da Zayn dan haka cikin son sanin Meke going tace .
"Hajiya ina kwana ya nauyin jikin"
"Alhamdulillahi nauyin jiki kuma Allah ya sauke min ya daurwa dan ku jiya kamar ba zai rayu ba kin gan shi" ta nuna mata Zayn, da yake ta had'e rai.
"Ayya Baban Umma Meke damun ka?"  Hajiya Maimouna ta tambaye shi.
"Allah sarki Maimunari baiwar Allah, ke daga shigowar ki har kin damu da Zaynu keda mijin ki Allah ta shiga lamarin ku, masu mana mugun alkaba'i ya Allah kasa suna gani zamu kama gidan haya a garin Habuja ko Yarona"
Kunshe dariya suka yi, wannan shine cigaba me tonan rijiya, (😂🤣😂 hajiya zata kashe ni)
"Babana ya jikin ka?" A sakalce ya sauko a kujeran ya zauna a kasa tare da daura kan shi a kafadar ta.
"Maam!"
Tallafe fuskar shi tayi tana jin wani tausayi da kaunar Yaron a yanzun yana yawan fama mata kukan da tayi na tsawon shekaru baya, a ƙalla auren ta da Alhaji AbdulMalik Zain Malami ya kai shekaru arba'in da takwas tunda Fatima babbar Yayar su Zayn ta kai arab'in da wani abu.
"How you feeling?"
"Alhamdulillahi Maam ki ce mata bafa inda zani?"
"Ikon Allah talatu cin amana ta kike da malami karami? Wato kina kintsa mishi yadda zai ce ba zai yarda ba kai shi ganin likita ba?"
Tayi maganar rai a B'ace.
"A'a Hajiya tambayar shi bake ya jikin nashi asha ashe abin ya kai haka ne?"

"Ban sani ba, kawai mun gama shirya yadda zan kai shi ganin likita kizo ki sauya min ra'ayi"
"Allah ya huci zuciyar ki" ta fadawa Hajiya tana zuba mata abun karyawa, abincin ta ta mikawa Zayn din tana faɗin.
"Maza ci sai mu tafi" babu yadda ya iya haka ya tura abincin sai lallashin sa take tana gaya mishi.
"Ai cuta ba mutuwa bane"

Yana gamawa ya mike, wayar shi ce tayi kara.
Duba screen din wayar yayi,  lumshe idanu yayi sannan ya dauka yana haurawa sama.
"Okay I will be there insha Allah"
Sannan ya katse wayar, ajiyar zuciya yayi sannan ya tura sako.
A hankali ya sauko yana kallon Hajiya da ta zuba mishi ido.
"Auta maza kira Jauro ya kai mu"
"Hajiya ga Zayn!" Ya nuna mata Zayn ɗin.
"Eh nasan da shi na ce kai, idan kuma zaka nuna min bani da iko da kai bismillah"
"A'a Hajjos, bari na kira shi."
"Ayya kai da baka da lafiya!"
Kallon su Mama take, Zayn Malik sunan da da ya samu matsuguni a ranta tun daga ranar da ya diro duniya, ba wai dan yana jika ga Alhaji Zayn Malami Malik bane a'a sai dan sunan ya dace da shine, Bata sani ba Allah ya kawo shi cikin su ne dan ya zama abun alfahari a gare su ko kuma ya zo ne a matsayin Jarumin ƙarni, a duk lokacin da zata yi kuka zata iya cewa shi yake share mata hawayen ta.

   "Toh idan kika ji shiru bako yayi halin shi mun tafi ganin likita"
"Allah ya dawo daku lafiya"
"Yawwa Munarih" tana fita suna sauke ajiyar zuciya a tare.
"Wai da gaske bai da lafiya ne?"
"Ina fa tsagwaron rikicin Hajiya mana wallahi lafiyar shi lau."

Shiru suka yi kafin Uncle bashir ya mike yana faɗin.
"Matukar Zayn yana tare da Hajiya ba zai mori kan shi ba, sannan idan ita kanta ba zata tab'a barin ya tafi wani wuri nesa da ita ba." Inji Mama.
"Sai a bar shi yayi ta lalata Yaran mutane a gari ai"inji Hajiya Umaima.
"Bai min kama da me haka ba domin da halin shine da tuni ya bayyana kan shi"

"Ina ga ku ajiye wannan sa'in'san ina da tafiya Sweden, kuma zai yi shekaru daya da rabi ne, ya zata kaya idan na dauke shi?"
"Me zaka je yi can? Ka shirya kome idan akwai abinda kake bukata a gaya min zan bada."
Da haka suka tashi ran Hajiya Umaima a B'ace bata kaunar cigaba Zayn duk da tana da Yara maza Uku da suke manyan aiki a kasar nan bata ki ta ga Zayn a lalace ba, domin lokacin da aka ce an dakatar da shi a aikin soja sai da tayi sati biyu tana sakewa Mama habaici, da gori babu wanda bata yi ba, amma ko a jikin Mama asalima uzuri take mata, shi yasa yanzu take jin zafin tafiya da shi Sweden da Uncle bashir zai yi, bata ki ta hana shi ba.

  Tana shiga dakin ta, wayar ta ta dauka zata yi kira Jud ta shigo, kallon ta tayi sannan ta ce mata.
"Hajiya ya zamu yi da Zayn don Allah ki cewa Mommy tayi wani abu!"
"Yanzu zan yi waya idan na gama zan kirata kin ji jeki zan gaya miki yadda aka yi"
Tana fita ta bita da wutsiyar ido, sannan ta kira wayar ta.
"Hello Hajiya Hanne? Yaron nan fa Sweden zai tai da kanin mijina, mijin Rukayyah"
Ko me aka gaya mata tace mata.
"Ban damu ba, kawai duhun da yake zagaye da shi nake son sani, ina son sani abubuwa akan shi? Yaron duk abinda zan yi mishi baya fushi, kin ga ba zaki gane yana nake ji ba, but am out of my mind bana kaunar Yaron, zan iya tsayawa ya dawwama in darkness, please a dakatar da tafiyar."
Kome aka gaya mata dafe goshin ta tayi, tana jin wani irin bacin rai.
"Ai na gaya Miki Mother in-law na bata son laifin shi. Kinsan malam ya gaya min kashin arziki ne da shi, duk inda ya taka idan so samu ne kome ya zama na Yarana, shi yasa aka mishi aikin da ya zama haka "
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce mata.
"Good abinda nake son sani kenan, ko jiya akan Idanuna Alhaji ya ware mishi shareholders din shi wanda muka zuba a JIKAMSHI GROUPS, dan haka nake son sanin Meye yaron yafi sauran"
Can kuwa ta ce mata.
"Alhamdulillahi abinda nake nufi Kenan dan haka zan nime ki bari na kira Yayar Alhaji muyi magana da ita!"
**
Tsayawa yayi a bakin hanya ya dauki Abul Khair da ya fito cikin shirin zuwa wurin aiki amma da yaji Zayn zasu fita yace mishi.
Ya tsaya ya dauke shi ya fasa zuwa aikin shima dama niman hanyar kin zuwa aikin yake, kawai sai ga kiran Zayn.
"Amma Malami da salula kake shawara da uwar kishiya, uwar me wannan me wuya kamar markin lema fa zai mana?" Kallon wuyar Abul Khair yayi yaga da gaske maganar da Hajiya tai kusan gaskiya ne, murmushi yayi ko banza ba shi daya zai yi fama sa tujarar hajiya ba.
"Umbrella..!" Sai ya fada yana kallon hanya.
"Hajiya kin ga Zayn yana tsokana na ko?" Inji Abul Khair.
"Ikon Allah, kai jariri ne da zai tsokanne ka? Ko sabo dayi gawa da gatsine, dan Albarka yi shiru kayi fama da ciwon ka, Allah ya baka lafiya mata hudu zaka aura rana daya muga shegen da ya isa d'aga maka kai duk fadin Kaduna"
"Ai kuwa Hajiya babu shi." Inji Abul yana kallon Zayn.
"Four for like russss"
"Zan cin Ubanka"
"Wayyo Allah na, kunci kaniyar ku wai hauka kuka fara ne?"
"Toh hajiya baki ji shi ya tsokane Ni ba"
"Ikon Allah, Allah sarki Allah ya baku lafiya" daga haka bata kuma magana ba, domin idan ta cigaba da magana ranta B'ace zai yi haka suka isa asibitin shi dai Abul Khair bin su yake bai san me ya kawo su ba, dan haka ya dauka hajiya ce ta zo ganin likita. Agaban reciption ta tsaya tana kallon matar da take wurin sayan kati ta ce mata.
"Yawwa likita daga ganin ki da katon tabarau nasan kece likita bokan Turai, ao ba banza Allah ya ajiye ki anan ba, toh kin gan shi bai da kuzari ne ki kadan."
"Hajiya wani irin kuzari?" Shi Zayn da Abul Khair suna can suna gaisawa da wani class mate din su, juyawa tayi tana rabtabo bayani.
"Ke ba wancan tsololon ba, ba kuma wancan dan dukushin ba, shi wancan jibgegen yawa shi dai da kika gani kamar jarumin nan shi fa na kawo ganin likita ashe yaron nan ya jima yana jinya bai da kuzari kina mishi maganar aure zai kama rigima, yo ai a tunani na aljanar dare ce ta aure min shi ashe ke dai babu kuzari ina Aljana zata samu biyar bukata, kawai sai dazun Judaal ta je ganin shi yake gaya mata ai shi ba namiji bane, kin ga yadda ya kwana yana matagugun, ai na zata mutuwa zai yi toh kin ga da gari ya waye ya tashi kyam kamar namijin doki, babban tashin hankali na matar da zata aure shi a wannan yanayin ai kin san an cuci yar mutane, iyayen shi basu da d'igon imani,  karshe ka karya tashi suka yi wai lafiyar shi lau, shima da kike ganin shi ai kunya ce da shi dakyar ya biyo ni, yawwa wani magani zaki bashi."

Ajiyar zuciya Matar tayi sannan ta ce mata.
"Hajiya ni ba likita bace, kati nake sayarwa."
Sake baki Hajiya tayi sannan ta ce mata.
"Toh sai ki had'a ni da likitan ko, bayan gama jin sirrin yaron kirki kice zaki wani ce ke ba likita bace, kowa a duniya ya zama munafuki da katon tabarau kamar na waziri aku. Kuma sai na gaya mishi kin ji sirrin shi"
"Allah ya baki hakuri Hajiya anan zaki sayi kati dubu biyu ganin likita dubu da dari Biyar "
Wata uwar harara ta wurga mata.sannan ta d'ago jakarta ta ciro kudin ta mika mata.
"Ina son ganin likita akan lokaci ya samu yi?" Ta dan matsa kaɗan tana mata alama.
"Yadda kika ce haka zamu yi Hajiya na wanke hannu da sabulu zaki bada kawai."
Aikuwa Hajiya ta kirga dubu biyar ta mika mata, kuma kudin fa jiya take gayawa Alhaji Uwaisu zata tura gudunmawar bikin wata jikar su a Zaria, toh karshe dai ga sh nan ana kashe shi a iska, ai kuwa kafin kace me an tura file din su.
Suna gama hira da abokin su, kawai suka tawo wurin ta.
"Yawwa tako a hankali, jeka zauna a can huta kaji ai lalura irin naka sai da kulawa "
Zama yayi yana ya tsina fuska kamar yaga kashi, itama matar kallon Zayn take, musamman yadda yayi dress ya daura wata jack a saman kayan shi kuma abun burgewa yadda jack din me hula,  zuwan abokiyar aikin ta ne, ta fara bata labarin da Hajiya ta bata,  suka shiga kallon shi domin bai musu kama da mara lafiya ba.
"Wallahi he look hot, irin wadannan idan suka rike mace ko? Wow"

"Haba Aunty ai kin girma da wannan aikin sai yara."
Kiran shi aka yi Hajiya ta mike, tare da mishi magana da idanu, mikewa yayi shima suka shiga cikin dakin.
"Yawwa sannun likita, ya aiki ya aka ji da jama'a, yawwa sannun ka gan shi nan na kawo shi bai da lafiya ne ya ce shi ba namiji bane, kai zo ka gaya mishi baka da kuzari, ko kallon mace baka yi, likita jiya kwana yayi yana juyi da ihun ciwon ciki."
"Toh mama ko zaki fita na duba shi,"
"Hmm yaushe na gama mishi tsarki? Toh kaji dai dan albarka idan ya ce ka kwabe wandon karka yi musu ka kwabe zai duba ka ne kaji" dafe Goshi Zayn yayi bakin ciki kamar zai kashe shi...
[6/25, 9:01 AM] Queen: _....ZAYN MALIK....✿_

*EXQUISITE WRITERS FORUM*
   
              Mai_Dambu

CHAPTER-5
Har ta fita ta kuma lekowa,
"Alhaji karka yi taurin kai ba a kunyar ciwo ka nuna dan dai kawai likita ya bukaci na fita ne ai ko da kaina zan danne ka a ga yanayin ai baka fi karfina ba"
Kamar ya nutse kasa, shi da Allah yayi shi ko abokansa baya yarda su yi maganar batsa a gaban shi, sabida kare kan shi daga zina, tana fita likitan ya mishi yaƙe.
"Da me za'a taimaka maka" dauke kai yayi yana latsa wayar shi,
"Ok sir"
Kallon Dr yayi shima ya kalle shi.
"Taya zan taimaka maka?"
"Ka ga nayi maka da me niman taimako ne?"
"A'a kwantar da hankalinka"
Mikewa yayi sannan ya ce.
"Nace maka a tashe yake?"
Ya tambaye shi, fahimtar da yayi Zayn dan zafin kai ne, yasa shi cewa.
"Ok zaka iya tafiya"
Wata uwar harara ya wurga mishi, sannan ya koma ya zauna,
"Kasan me? Ka rubuta min sunan maganin da zan nuna mata"
Daukar takarda da biro me stemp na asibitin ya rubuta mishi su Vitamins b Complex, mentors na mura, da su tom-tom, ya mika mishi yana cewa.
"Allah ya kara sauki a kula da

Please Login or Register in order to submit comment