Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba"
"Yau dai zan fada amma bana so ki rike shi a ranki kinji ko"

"Toh Ammina in sha Allahu bazan rike ba" na fada ina zumudin son jin labarin AMMI DA ABBU NAH.....


Kamar yadda kika sani suna HINDU IDRIS AJIDDE, mu cikakkun 'yan asalin kasar Niger ne cikin birnin yamen mu biyar iyayen mu suka haifa kuma dukka mata, akwai Tarmel wacce ita babba sai Haiti sai Hibbani sai ni hindu sai yar autan mu nafi. Gabadayan mu mun taso cikin kulawa da rufin asiri, mahaifin mu babban mutum ne yana da rufin asiri sosai domin bamu san talauci ba, ba kuma musan babu ba, suna kokarin bamu tarbiyya daidai gwargwadon iyawan su, dukkan yan gidan mu sunyi makaranta saboda mahaifin mu yana da ra'ayin boko kuma yana ganin kamar wata cigaba ce aka samu. Ina jss3 yayin mu Tarmel da Haiti sukayi aure inda dukan su suka auri manya manyan 'yan kasuwa don alokacin kansu daya don tare ma aka sanya su a makaranta kuma sai da suka gama sannan akayi masu aure duk da irin maganganun da 'yan uwan mu sukeyi amma haka mahaifin mu ya toshe kunnen sa ya kuma rufe idon sa. Ina ss2 Hibbani ma tayi gidan rufin asiri sai ya rage daga ni sai nafi ita kuma a lokacin tana ss1 kasancewar tsakanin mu babu wani rata....

Duk cikin yan uwana babu wanda na shaku da ita kamar kanwata nafi domin ta zame min tamkar aminiya bana boye mata komi.... Ina ss3 dab da zan gama makaranta muka hadu da mahaifin ki ABUBAKAR JUD, babu wanda bai san familyn JUD ba domin family ne mai girman gaske kaman yadda na fada miki, Abubakar yana da yayyi da kanne sosai domin gidan su mata hudu ne reras, Inna Amra itace ta farko kuma itace mahaifiyar Abubakar sai Inna kulu sai Inna Binta sai kuma amarya Inna Adda wadda itace amarya kuma ita kadai ce mai sona...

ina son ABUBAKAR tamkar raina, son da ban taba yiwa wani namijin ba har yanzu kuma banga tamkar sa ba har yanzu"....

Wasu hawaye ne masu zafi suka silalo daga idanun Ammi ta girgiza kai sannan tace
"Allah ya gafarta maka Abubakar"

Nima hawayen na share nace "Amin ya Allah"

Ammi ta cigaba "da kyar 'yan uwan Abubakar suka yadda mukayi aure don acewar su suna da wacce zasu bashi amma ya tirje yace sai ni ti dan zan juya masa baya akan 'yan uwansa basu sona?

A haka dai mukayi aure inda aka ajiye ni a gidan su duk da ba haka yaso ba, tsana iya tsana an nuna min, tsangwama iya tsangwama sun nuna min, shekarata daya a gidan Abubakar ya samu matsala daga wajen aikin sa shikenan suka danganta abin da cewar wai ya auro mai farar Wa iyazu billah, haka dai nake lallaba auren ina hakuri inda yayyina ma suke bani baki. Shekarar mu biyar da aure amma ko batan wata ban taba yi ba nan ma aka sani a gaba, kullum Abubakar sai tusani a gaba yake yana bani hakuri yana nuna min komai lokacin ne zasu daina wani lokacin har tausayi Yake bani wallahi.....

A haka aka wayi gari ina da juna biyu na wata uku, murna a wajen mu ba'a magana, wata tara cif cif na haife ki, sosai kike kama da dangin mahaifin ki, ke ba fara ba haka ba baka ba... A ranan da na haife ki a ranan mahaifin ki ya fara rashin lafiya mai tsananin da aka rasa gane kansa, 'yan uwan sa suka fara rade radin wai duk nice sanadi sannan kuma haifuwar ki ba alkhairi bane har na fara tsoran kar su kashe min ke.... 'Yan uwana sun zo min da sha tara ta arziki sunyi matukar farinciki da haihuwar ki wadda ciki harda kanwata Nafi da itama tayi aure da yaranta uku

Wata rana da daddare ana gobe suna ina zaune kusa da Abubakar shi kuma yana kwance numfashinsa yana sama da kasa amma duk da haka yana rike dake akan cikin sa, cikin sanyin murya irin ta marasa lafiyaya fara magana

"Hindu na sanyawa 'yata KHADIJA, dan Allah ki rike min amanan ta da kyau, wallahi hindu bayan iyaye na da ke babu wata halitta da nake so kamar diyata amma kaddara zata rabamu" ya fada wasu hawaye masu zafin gaske suka zubo ta gefen fuskarsa ya cigaba

"Kin san me nake so dake hindu? Ki dauki khadija kuyi nesa da garin nan, ina tsoron abinda 'yan uwana zasu aikata akan ki ko diyata"

A lokacin wani abu ne ya daki kahon zuciyata wasu hawaye masu zafin da bana tunanin wani mai rai ya taba yinsa ba, bai bar ni nace komai ba ya miko min ke yace na sannan na bude wata Jakarsa da yake ajiye muhimman abubuwan sa na dauki iya dukiyar da zai isheni rayuwa ni da ke....

Kuka ne ya kufce min na dinga yi babu kakkautwa har da shesheka sannan na kankame ki a jikina kamar zai kwace min ke, cikin gunjin kuka nace

"Abubakar bazan iya tafiya na barka cikin wannan halin ba, kaine wanda na fara so kuma kaine wanda nake so na karashe rayuwana tare dashi, idan ta kama dole to sai dai na tafi gidan mu"

Cikin wahaltacciyar murya yace hindu ni nasan mai naji game da abinda yan ubana suke fada akanki, dakyar ya lallashe ni yace a daren zan gudu kar na zauna su same ni, haka inaji ina kallo na rabu da Abubakar ba dan rai yaso ba, kudi na diba masu yawa na fice daga gidan cikin sirri babu wanda ya ganni cikin ikon Allah....

Ajiyar zuciya Ammi ta sauke sannan ta cigaba

"Na rabu da gida cikin kewan 'yan uwana, abokai na da kuma masoyin da ruhi da gangan jiki baza su taba mancewa da shi ba, babu inda naji ina son komawa da zama kamar Nigeria domin ina jin labarin kasar a bakin Abubakar, a tasha na kwana washegari da asuba muka kama hanya, tunda muka kama hanya nake kuka har na iso Nigeria, da taimakon wata mata da dan saba a mota na sauka garin kano ta taimaka na canjo kudina sannan na kama madaidaicin gida a unguwar da matar take, da ragowan kudin na siya mana kayan sawa, kayan abinci da dai sauran kayan amfanin gida, rayuwa nake amma ruhi na yana kasata ta haihuwa, nasan 'yan uwana sunyi kukan rashina, kullum tunani nake Abubakar ya mutu koda ransa amman zuciyata tafi karkata da ya rigani gidan gaskiya. Sana'a na kama haikan na sai da siyarwa, da shi muke ci muke sha, kuma dashi na sanya ki makaranta cikin rufin asirin Alla, ana haka lokacin kin gams primary zan sanya ki secondary Allah ya hada ni da hajiya zainab wato mami sanadin bigeni da sukayi ita da mijinta a mota shikenan suka nemi mu zauna tare, a ranan da muka dawo gidan nan a ranan kuma Aliyu ya tafi kasar waje karatu shida bamu san shi ba, hakika mami tayi kokari ita take daukan dawainiyyan mu, ta rike tamkar 'yar uwar ta da suka fito ciki daya sannan Allah ya dora mata sanki tun daga lokacin da Ta fara ganin ki, Allah dai yayiwa hajiya zainab albarka"

Share hawayen fuskata nayi nace "Ammi na inaji a jikina Abbu yana raye wallahi"

"Hmmmm Deena kenan, ki cigaba dai da yiwa mahaifin ki samun rahaman Allah......
Bata karashe abinda zata fada ba muka jiyo sallamar Aysha ta karaso tayi tsalle jikina tace

"Shine tun dazu kika taho kika ki komawa ko? Yanzu tashi muje mami na kiran ki"

Murmushi nayi nace kaina ke ciwo shisa amma yanzu da sauki"

"Ayya sannu my dear ban sani ba ai, kodai shisa naga idon ki kamar kinyi kuka" ta juya ta kalli Ammi tace

"Ammi ciwon kan ne yasa take kuka?

Dariya Ammi tayi tace "kin san mutuniyar ki da ragwanta"

Dariya Aysha tayi tace "an dai ji kunya wallahi, tashi muje to tunda yanzu da sauki"

Haka ba yadda na iya na bita saboda nasan baza ta taba bari naba, haka na bita Ammi nayi mana dariya.....

Tun a hanya take ta bani labarin yaya Aliyu ni dai sai murmushi nake ina binta da "eh" ko "uhm" a raina kuwa nace wannan wani irin so suke yiwa wannan Aliyun nasu, wata zuciyan ta kwabe ni da ina ruwana su da dan uwan su"

Aysha ce a gaba ina biye da ita a baya muka shiga palon, kowa ya hallaru a palon, babu inda idanuna suka sauka sai cikin nasa, wani shock naji tun daga babbar yatsar kafata har kwakwalwata, da wannan daman yayi amfani ya sarke idanunmu waje daya wanda da banyi dagaske ba ban isa na janye idanun nawa ba, dakyar na janyo kafafuna na shigo palon na zauna a kasa gefen kujeran da mami take zaune shi kuwa gogan wani balance ya kara yi saboda inda na zauna din ina fuskantan sa....

Nana autar mami ce ta taso ta zauna gefe na tace "Adda Deena ina kika shiga yau duk nayi missing dinki kuma su Adda mufida sai cin zalina sukeyi san bakya nan" ta karashe maganan cikin sigar wanda yake fushi.
Allah ya dora min son Nana saboda yarinya ce mai shiga rai cikin kankanin lokaci

Shafo kanta nayi nace "gashi yanzu na dawo naga mai taba ki, kawo kunnen ki ma kiji" magana nayi mata a kunne ai kuwa ta tuntsire da dariya nima nayi dariya wanda ya kara bayyana tsantsan kyawuna har sai sa beauty point dina suka lotsa

"Damn it, tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya tsara wannan kyakkywan halittan" Aliyu ya fada cikin zuciyan sa yana mai kara nishandantuwa da kallo

Duk motsin da zanyi idanun sa nake ji suna yawo a jikina hakan yasa naji sam sam bazan iya dogan zama

Gaisawa mukayi da mami inda take tambaya ta ya jikin nawa nace mata na warke sannan muka cigaba da hira da su Islam da Aysha, mufida kuwa ita da Nana suke hiran Mami kuwa da Aliyu.

Ina zaune ne amma bana jin dadin zaman kasancewar tsare ni da yayi da idanunsa...

Mami ce tace
"Deena jeki kitchen mana ki yanka min fruits amma banda lemo"

"Toh" nace tare da mikewa na nufi kitchen

Mami tafi so ta sanya ni aiki fiye da kowa a cewarta nafi su nutsuwa nayi mai kyau sannan ina tsaftace komi yadda ya kamata....

Bayan kaman minti biyu Aliyu ya mike yace
"Ahmm bari naje na hada coffee" ya nufi hanyar kitchen din shima

Babu wanda ya kawo komai cikin ransa sai Aysha da tasan komai, dariya tayi ta dan daga murya tace "yaya Aliyu ka hado dani dan Allah "

Juyowa yayi ya galla mata harara sannan yayi kitchen din.....



*08038231353 for comment and please share to other groups*
[18/04 17:55] W Hajara MB: KWARYA TA GARI






*HOME OF QUALITY*
*WRITE'S ASSOCATION*
_[The Home Of Quality Which Are Educated The Humanities]_

*⚖(H.Q.W.A)⚖*

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=101128334840967&id=101127231507744&sfnsn=mo


*INGANTACEN ALKALAMI BAYA RUBUTA SHIRME🖊*


WRITTEN AND STORY
BY
HAJARAT M BASH




💦31-35💦

Ina shiga palon na tadda Aysha da yaya Aliyu suna hira kasa kasa kamar masu gulma, ni kam burge ni sukeyi, babu kowa a palon kasancewar dare ya fara yi domin takwas ya wuce domin al'adan gidan ne bacci da wuri.

Karasawa nayi wajen da suke cikin wannan sanyin muryan da ake cewa na shagwaba ne kawai nace

'Aysha dan Allah ga wannan idan mami ta fito ki bata'

"Waye ya baki? Ta fada tana kallon ledan amma bata karba

"Mami ce tace na karbo wajen Uncle J"

Harara ta Aysha tayi cikin sigar wasa Tace "lallai ma an aike ni kuma kisa ni, wallahi yi zaman jiran fitowanta ni kinga ma tafiyata"

Sororo nayi ina kallonta har ta kurewa gani na, ba yadda na iya haka na samu daya daga sofan palon na zauna wadda kujera daya ne tsakanin na da yaya Aliyu nayi kasa da kaina Ina wasa da zarazaran yatsun hannu na da yasha jan lalle wanda bana rabuwa da yinsa yana gogewa zanyi wani.....

"Nice henna" abinda naji kenan an fadi kusa dani da sauri na dago ina kallon sa, ko yaushe ya taso daga inda yake ya zauna a kujeran da yake kusa dani?

Wannan killer smile din yayi min mai narkarda zuciyan 'yan mata, mayar da kaina nayi kasa

"Idan an yabi abinka godiya akeyi amma ke kinyi wani shiru"

Murmushi nayi still bance komai ba

"hmmm wai ke baki magana ne koni ne ba'a so ayi min?

Girgiza kaina nayi alaman a'a

"Ikon Allah yace sannan ya gyara zama ya fuskance ni da kyau sannan yace

'Kalli kiga wani abu"
Cikin rashin sani na dago kuws muka hada ido, ido daya ya kashe min yana murmushi, ni sai ya bani kunya ma da dariya

"Kin san me nake so dake? Feel free with me, nima yayanki ne ko?

A hankali na furta "eh" kamar mai ciwon baki

Hannu yasa ya dan doki gashinsa yace
"Oh Ya Allah, ki bude bakin ki da kyau, wai baki kalli yadda muke da su Aysha bane? They are just like my friends so i want you to be like them kinji?

Eh din da na kuma cewa kaina a kasa, hannusa ya dago ya kai saitin hanci kamar zai kama yace
"Idan bazaki bude baki ba sai na ja wannan dogon hancin kamar nawa"

Baya nayi da kaina don a tunanina kamawan zaiyi, sai ji nayi yayi dariya yace "matsoraciya kawai"

Dariyan nima nayi ba tare da nace komai ba, hannun sa ya sa ya tallafo gefan fuskarsa yana kallona, shi kawai burge shi nake yi musamman idan ina dariya har kumatuna ya lotsa sai duk ya rasa inda zai sanya ransa dan dadi.

"You are cute DEENA, very beautiful," ya fada cikin sanyin murya tamkar mai rada, tunawa nayi da yace Idan an yabi mutum godiya yake don ni kwata kwata ban san inda ya dosa ba don nima ban taba soyyan ba...

Murmushi nayi nace
"Thank You"

"Yauwa 'yar gari haka ake cewa ba wai ayi shiru ba sai kace a kauye" ya fada cikin sigar zolaya

Agogon hannunsa ya duba yaga har tara ya wuce ya mike tsaye yace
"Ajiye sakon mamin anan dan naga bata da niyyan fitowa gashi dare yayi, ni zan jira sai na bata'

Kaman yasan daman na gaji da zaman ai kuwa na mike tare da ajiye ledan a inda na tashi na fara tafiya

"Tsaya mana na miki rakiya ko bakya so?
Dakatawa nayi ina jiran ya karaso don dama tsoron bin hanyan nake ni daya duk da akwai wadataccen hasken fitilu tar tamkar rana shjyasa ma bana yin dare idan kuwa nayi dare sai dai na kwana wajen su Aysha.

Tafiya muke muna taku a hankali sai hira yake min ina bin sa da dariya ko murmushi har muka zo kofan shiga cikin gidan sannan yayi mun sallama tare da cemin gobe zai shigo ya gaida Ammina, godiya nayi masa sannan ya wuce ni kuma na shige ciki inda na tadda Ammina har tayi bacci, sai da nayi sallan Isha'i sannan na haye gadon da Ammi take na kwanta a bayan ta tare da yin addu'a amma sai me, bacci ya gagara daukana abin mamaki Uncle J nake kallo lokacin da yake tambaya ta full name dina da lokacin da ya tabe baki ya miko min ledan yace
"Jeki" dakyar da karfin addu'a na samu ya sace ni......

Yana isa gida, a kofar gate yayi parking kasanewar sallan da akeyi na isha'i a masallacin gidan sa, alwala yayi sannan ya shiga yabi jam'i, bayan ya idar ne maigadi ya bude masa gate ya shiga da motar

tun daga main palo yake jiyo kukan gudan jininsa, daga kafa yayi da sarsarfa yake tafiya kamar zai kifa har ji yake tamkar an kara ratan wajen, sallama yayi tare da tura kofan palon yasa kai ya shige

Binta mai renon su ya gani ta goya Arif sai Arifa da take faman jijjigawa a hannunta su kuma sai tsala kuka suke kamar wadda ake yankan naman jikin su,

"Me ya same su"

Cikin tsoro da gigicewa Binta ta juyo dan har ga Allah bata san ya shigo ba saboda kukan da suke tsalawa baka jin komi

Russunawa tayi tace "Yallabai ban san meke damun su ba kawai suke ta kuka tun dazu"

"Sun ci abinci?

"eh na basu madaran sun sha"

Bai kara magana ba illa mika hannu da yayi ya karbi Arifa ya zauna kan kujeran palon, ganin haka yasa Binta ta kwanto Arif ta mika masa su sannan ta juya zata tafi, bai ko kalle ta ba yace "kawo min ruwa na basu"

"Toh" tace jiki na rawa ta tafi daukowa

"Shhhhhh sorry ya isa haka kukan daddy's angels sorry"

Abin mamaki suna jin muryan baban suka bude idon wanda da sun rufe sai ihu suke ba ji ba gani, dariya sukayi a tare suka fara kamo fuskansa wanda shima abin ya basa mamaki, kissing dinsu yayi duka a kumatu sannan yace

"Kukan rigima ko? Why uhmm? You daddy loves you so much amma ku dinga daga min hankali..... Shi kadai dai ya dinga surutun sa suna masa dariya

Binta da ta kawo ruwa itama mamaki abin ya bata wato yara sun san baban su, russunawa tayi ta bashi ruwan ya karba ya fara basu har ta juya zata tafi yace
"Ina mamansu?

"Eh tace na fada maka za a sauke kaya a shagonta wai ta tafi"

Rintse ido yayi sannan ya bade ya cigaba da basu ruwan bai sake magana ba ganim haka yasa Binta mikewa ta bar wajen.

Dakin sa ya kaisu yayi musu wanka ya canja musu kaya tare da sanya musu diapers suka haye gado yana ta musu wasa daga baya sukayi bacci sannan ya gyara musu kwanciya tare da tofa musu addu'a yana ta kallon su tsawon mintina sannan yayi musu peck a kumatu shima ya kwanta.

A rigingine ya kwanta yana tunanin makomar yaransa ace yaro ya tashi babu kulawan uwa babban hatsari ne bugu da kari UWA ita ginshikin tarbiyya tunda uba ba mazauni bane.
"Ya Ilahi" ya furta a fili
"Gaskiya ya zama dole na nemo mafita UMMU RUMANA doesn't deserve children kawai dai Allah ya fimu sanin dalilin da ya bata baiwan haifan 'yan biyu"

Wani guntun tsaki ya ja jin an taba kofan dakin yasan babu tantama Rumana ce, shi sam sam bashi ma bukatan ganinta.....


08038231353 for comment and pls share to other groups
[18/04 17:55] W Hajara MB: 💦KWARYA TA GARI💦





*HOME OF QUALITY*
*WRITE'S ASSOCATION*
_[The Home Of Quality Which Are Educated The Humanities]_

*⚖(H.Q.W.A)⚖*

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=101128334840967&id=101127231507744&sfnsn=mo


*INGANTACEN ALKALAMI BAYA RUBUTA SHIRME🖊*



💦36-40💦



IN DEDICATION TO MY MENTOR JAMILA UMAR TANKO (MOMY JUT) ALLAH YA KARA LAFIYA DA NISAN KWANA, THIS PAGE IS FOR YOU....


Babu sallama haka ta turo kofan dakin ta shigo kanta tsaye dan dama ita kanta addinin ma ba damunta yayi ba, yana kallonta ta cikin dim light din dake dakin tana sanye da wani shegen sleeping dress kamshi na tashi irin mai daga hankalin nan amman gogan ko ajikinsa hasalima ji yake kamar ya korata dan ko ganinta baya bukatan yi.

A hankali cikin tafiyan jan hankali ta karasa gadon da yake kwance dan tana da yakinin yana kallonta saboda Junaid miskili na karshe, hawa gadon tayi ta kwanta ta gefensa tare da daura kanta akan faffadan kirjin sa cikin muryan yaudara tace
"Daddyn twins, i missed you today through out ban ganka ba"

"Uhmm" ya fada don bai son aja maganan domin ransa ya fara baci

"Daddyn twins ina so muyi magana dan Allah i know idonka biyu"

"Anzo wajen ya fada a ransa, daman yasan tana bukatan wani abu ne shisa ta lallabo da salon yaudara, shiru yayi bai tanka ba, cikin muryan shagwaba tace

"Daddyn twins"

"Rumana ya fada a takaice
"Magana nake so muyi kuma ka share ni kana jina?

"Inaji"
Jin haka yasa ta kara gyara kwanciya tare da marairaice murya ta fara magana

"Daman maganan twins ne lokaci yayi da zan yaye su tunda sun girma kuma jikin su mai kyau ne wallahi ina shan wahala wajen shayar dasu kum.... "

Bata karasa ba ya daka mata tsawan da sai da Arif ya farka itama kuwa ba shiri ta matsa daga jikinsa don zata iya cewa a iya shekaru biyar da sukayi da aure wannan ne rana ta biyu da ya taba mata tsawa haka, kuka Arif ya fara ya lallabasa ya koma bacci sannan ya mike ya kunna hasken dakin ya dawo bakin gado ya zauna cikin muryan dake nuna bacin rai yace
"Rumana tashi ki zauna"
Ba shiri ta mike ta zauna

Kallonta yayi sama da kasa sannan yace

"Maganan yaye kike ko meye? Lallai Rumana ban taba tunanin rashin hankalin ki ya kai har haka ba, yarana zaki yaye min suna da nine months a duniya? Ke haka aka miki? Idan haka aka miki ni ba haka akayi min ba saboda muna daraja al'adan malam bahaushe da kike gani kamar rashin wayewace sannan muna sanya addinin mu gaba da komai, yanzu ke baki ji kunyan ki kalli tsaban idon JUNAID ki fada wannan maganan ba Rumana? Take a good look at this poor babies, basu san kauna ta uwa ba, basu san kulawa ta uwa ba, basu san shakuwa ta uwa ba, idan suna kuka babu mai sanya su ajiki ya rarrashe su, babu mai yi musu wasa irin ta uwa, anya Rumana kina da zuciyan uwa a kirjin ki kuwa?
Iska ya shaka ya fesar sannan ya cigaba
A bar maganan yara ma tukanna dan wannan magana taki ba maiyuwa bane sam, ni yanzu baki dauke ni a bakin komai ba har zaki fita kiyi dare hankalin ki kwance ba tare da kin fada min ba Rumana? Rumana kin san meye aure kuwa, kin san meye miji kuwa? Kai Rumana kin san meye musulunci ma? Gaskiya baki sani ba, bazan ce miki komai ba Rumana amma ki sani bazan iya daukan iskancin ki yanzu ba dan nagaji wallahi in fact Rumana nayi danasanin auren ki"

Da sauri ta dago kanta ta kalle shi cikin ido yayin da idanun ta suka ciko da kwallah ta dafe kirjinta da hannunta, ita dai tasan tana son Junaid kuma baza ta iya rabuwa dashi ba kawai dai banbancin ra'ayi ne wanda ta dauki nata a matsayin shine wayewa sannan gaskiya bazata iya sauke nata ra'ayin tabi gidadancin Junaid ba.... Cikin sarkewar murya tace
"Junaid ni kayi danasanin aure?

"Yes Rumana wallahil Azim i regret marrying you, tell me me kika taba tsinana min na jin dadi a gidan nan tun bayan two weeks na farkon auren mu? Uhmm fada min, Rumana na soki duk da hada mu akayi but i did my best naga na sanya ki farinciki, i gave all that i had just to make you happy Rumana, kama daga kan muhalli, sutura, abinci, abin sha, kulawa, soyayya wanne na rage ki dashi? Nayi shi kuma ina kan yin shi saboda nasan meye aure kuma wacece matar sunnah amma kika saka min dashi? Kinci sa'a Allah ya shirye ni bana neman matan bariki da kin shiga uku, ki tuna yadda kika dinga zubar da yara a kwararo wai ke baki son ki haihu ki tsufa gaki 'yar fashion, wadannan bayin Allahn ma Alla yasa zasu zo

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment