Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu aiki, wayoyinsa ya diba a hannu ya nufi side din matarsa kawai so yake yaga twins dinsa yayi missing dinsu, rabonsa dasu tun jiya da ya dawo daga gidan yayarsa Anty Zainab

A hankali yake tafiya cikin takunsa na kasaita da gadara hannunsa daya cikin aljuhun wandonsa, wata corridor yabi inda zai sada sa da palon RUMANA.

Sallama yayi tare da murda handle din kofan sannan ya tura kofan ya shiga babu kowa palon, idanunsa basu sauka kan komai ba sai farincikin sa, gudan jininsa, kuma rayuwarsa suna ta wasa su kadai, bai san lokacin da ya saki wani lafiyayyen ajiyan zuciya ba tare da murmushi mai nuni da tsantsan farinciki.

A hankali ya furta
"My angels"
Ai kuwa jin muryan mahaifinsu da sukayi suka waigo da sauri suna ganin shi din ne kuwa suka fara bangala masa dariya suna mimmika hannayen su alaman ya dauke su....

Da sarsarfa ya karasa cikin palon inda suke, a tare ya daga su sama ya rungume su tsam ajikinsa suma kuwa suka rike shi gam sai dariya suke, yaran dama sunfi sabawa dashi saboda shike jansu a jiki yana musu wasa shisa kullum idan yana gida bashi da time sai na yaransa kasancewar basu samu kulawa ta wajen uwa ba shi gani ma yake ma kamar RUMANA bata son yaran nan shi kadai ke son su shisa yake jin zai iya yin komai akan gudan jinin sa ARIF DA ARIFA...

A hankali ya sauke su kasa shima ya zauna kan carpet din sannan ya dora su dukkan su kan cinyar sa yana shafa kansu yana mai jin wani irin tausayin su wai ace yaran dako rarrafe mai kyau basuyi amma basu san kulawan uwa ba?
"Kai Ya Ilahi" ya furta afili wannan wacce irin rayuwa ce Allah gani gareka"

Gwalagwalatan su suke masa shi kuwa sai biye masu yake yi, ya taba kumatun wannan, ya lakuce hancin wannan su kuma sai dariya suke suna kama hancin sa da bakinsa...

Arif ne ya dan fara kananan kuka yayi ya tsaya sai itama Arifa ta kama ganin haka baban ya gane yunwa suke ji rarrashinsu ya fara yi sannan ya daga murya ya kira mai renon su.

Da azama Binta mai renon su ta shigo jikin ta na rawa ganin yau maigidan ne da kansa yake kiranta addu'a takeyi a zuciyanta Allahu yasa ba laifi tayi ba

Durkusawa tayi daga gefen kujera tace "yallabai sannu da hutawa gani"

Murmushi yayi ya kalle ta yace
"Binta yaran nan ne suke jin yunwa"

Mikewa tayi da sauri tace "bari na hado musu madaran su yallabai"

Daga kanshi yayi ita kuma tayi hanyar kitchen da sauri

Mikewa yayi da yaran yana jijjiga su su kuma suka kwanta a jikinsa sannan ya zauna dasu akan kujera yana jiran zuwan binta sannan kuma yana tunanin hali irin na RUMANA a daidai lokacin yaji karan takalmanta tana saukowa daga stairs din bedroom dinta, kafin ta karaso turarenta ya karaso inda yake, ko dagowa baiyi ba balle yasan mutum na tahowa gunsu, cigaba yayi da rarrashin yaransa

Sanye take cikin wani tsadaddan less maroon color anyi masa ado da stones milk color sannan ta yafa mayafi milk color haka takalmi da jakanta milk color, haduwa iya haduwa kam tayi lallai kana ganin ta kasan wannan ta dace da zama uwargida ga JUNAID B ARAB...

Zaunawa tayi kusa dashi har kadadun su na gogar juna, cikin yar karamar murya tace

"Daddyn twins ina kwana?

"Lfy" ya fada a takaice ba tare da ya kalleta ba

Wannan yana daga cikin halayensa dake kara tunzura RUMANA wanda ta dauke shi a matsayin walaqanci

"Daddyn twins" ta kara fada tana kallon sa

"RUMANA" ya fada shima

Bata ko damu ba sabida inda sabo ta saba da hakan, murmushi tayi tace

"Zan wuce bikin gidan su Balkisu da na gaya maka, kaga mune manya ya kamata muje da wuri mu shirya yadda abubuwa zasu kasance, bata jira ansan sa ba don tasan ba maganan zaiyi ba sannan ta mike ta fice tana taku dai dai har ta fice...

Wani iska mai zafin gaske ya furzar har sai da yaran suka razana suna kallon sa, murmushin karfin hali yayi sannan ya rungume su a jikin sa yana mai jin wani zazzafan son su na kara shigan su.....

Binta ce tayi sallma dauke da kofuna guda biyu akan karamin tray

"Yallabai miko su a basu"

"Kar ki damu Binta nima zan iya basu"

Mika mata Arif yayi yace yi hakuri binta ki rike min Arif kafin na gama bawa Arifa

Karban Arif din tayi tana mamakin hali irin na ubangidan nasu sam sam bashi da girman kai irin na masu kudi ga tausayi da kyautatawa na kasa dashi wanda suka sha banban da uwardakin nasu da bata dauki talaka ba a bakin komai ba..

A hankali ya dinga bawa Arifa tana sha har ta koshi duk ta bata masa jiki amma bai ko damu ba

Karban Arif yayi shima ya bashi sannan yace Binta taje tayi musu wanka shima ya nufi nasa dakin dan sauya kaya, tafiya yake amma zuciyar sa na suya da danasanin auran RUMANA, bata ko damu da yaci abinci ko bai ci ba ita dai tayi abinda zuciyarta ke so...






08038231353 for comment and please share to other groups...


*KWARYA TA GARI*



*HOME OF QUALITY*
*WRITE'S ASSOCATION*
_[The Home Of Quality Which Are Educated The Humanities]_

*⚖(H.Q.W.A)⚖*

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=101128334840967&id=101127231507744&sfnsn=mo


*INGANTACEN ALKALAMI BAYA RUBUTA SHIRME🖊*


*WRITTEN AND STORY*
*By*
*HAJARAT M BASH*




*Pg16-20*



Tsaye yake gaban tangamenen dressing mirror dake cikin kayataccen bedroom din sa yana feshe jikin sa da wani tsadadden body spray mai kamshin gaske wanda kamshin sa kawai zai tabbatar maka da tsadan sa....

JUNAID B ARAB ya kasance mutum mai son kamshi da tsafta sai dai kash baiyi dacen samun mata ma'abociyar tsafta ba, idan kaga RUMANA na kyalkyale jiki to fita zatayi ko kuma ana son wani abu gurin miji, ita dai RUMANA masu aiki ne ke yi mata komai, mace ce mai halin i don't care miji baya gabanta baya ga neman kudi babu abinda ta sanya a gaba balle kuma ta kula da yaranta da suke tsananin bukatan kulawar uwa, idan akace yau harka ce ta neman kudi to kuwa sam sam bata wasa dashi anan za tafi maida hankali.

JUNAID kuwa ma'abocin son rayuwa ne yana son yaga yana gudanar da rayuwan aure kamar wasu LAILA DA MAJNUN amma kaddara ta riga fata wadda ta hada shi da UMMU RUMANA.....

A hankali ya gama feshe jikin sa da spray din yana karewa kiran halittan da Allah yayi masa, wani guntun tsaki ya ja gami da ajiye spray din ya nufi wardrobe din sa ya ciro wani three quarter wando da armless riga duka farare kasancewar lahadi ne babu aiki, wayoyinsa ya diba a hannu ya nufi side din matarsa kawai so yake yaga twins dinsa yayi missing dinsu, rabonsa dasu tun jiya da ya dawo daga gidan yayarsa Anty Zainab

A hankali yake tafiya cikin takunsa na kasaita da gadara hannunsa daya cikin aljuhun wandonsa, wata corridor yabi inda zai sada sa da palon RUMANA.

Sallama yayi tare da murda handle din kofan sannan ya tura kofan ya shiga babu kowa palon, idanunsa basu sauka kan komai ba sai farincikin sa, gudan jininsa, kuma rayuwarsa suna ta wasa su kadai, bai san lokacin da ya saki wani lafiyayyen ajiyan zuciya ba tare da murmushi mai nuni da tsantsan farinciki.

A hankali ya furta
"My angels"
Ai kuwa jin muryan mahaifinsu da sukayi suka waigo da sauri suna ganin shi din ne kuwa suka fara bangala masa dariya suna mimmika hannayen su alaman ya dauke su....

Da sarsarfa ya karasa cikin palon inda suke, a tare ya daga su sama ya rungume su tsam ajikinsa suma kuwa suka rike shi gam sai dariya suke, yaran dama sunfi sabawa dashi saboda shike jansu a jiki yana musu wasa shisa kullum idan yana gida bashi da time sai na yaransa kasancewar basu samu kulawa ta wajen uwa ba shi gani ma yake ma kamar RUMANA bata son yaran nan shi kadai ke son su shisa yake jin zai iya yin komai akan gudan jinin sa ARIF DA ARIFA...

A hankali ya sauke su kasa shima ya zauna kan carpet din sannan ya dora su dukkan su kan cinyar sa yana shafa kansu yana mai jin wani irin tausayin su wai ace yaran dako rarrafe mai kyau basuyi amma basu san kulawan uwa ba?
"Kai Ya Ilahi" ya furta afili wannan wacce irin rayuwa ce Allah gani gareka"

Gwalagwalatan su suke masa shi kuwa sai biye masu yake yi, ya taba kumatun wannan, ya lakuce hancin wannan su kuma sai dariya suke suna kama hancin sa da bakinsa...

Arif ne ya dan fara kananan kuka yayi ya tsaya sai itama Arifa ta kama ganin haka baban ya gane yunwa suke ji rarrashinsu ya fara yi sannan ya daga murya ya kira mai renon su.

Da azama Binta mai renon su ta shigo jikin ta na rawa ganin yau maigidan ne da kansa yake kiranta addu'a takeyi a zuciyanta Allahu yasa ba laifi tayi ba

Durkusawa tayi daga gefen kujera tace "yallabai sannu da hutawa gani"

Murmushi yayi ya kalle ta yace
"Binta yaran nan ne suke jin yunwa"

Mikewa tayi da sauri tace "bari na hado musu madaran su yallabai"

Daga kanshi yayi ita kuma tayi hanyar kitchen da sauri

Mikewa yayi da yaran yana jijjiga su su kuma suka kwanta a jikinsa sannan ya zauna dasu akan kujera yana jiran zuwan binta sannan kuma yana tunanin hali irin na RUMANA a daidai lokacin yaji karan takalmanta tana saukowa daga stairs din bedroom dinta, kafin ta karaso turarenta ya karaso inda yake, ko dagowa baiyi ba balle yasan mutum na tahowa gunsu, cigaba yayi da rarrashin yaransa

Sanye take cikin wani tsadaddan less maroon color anyi masa ado da stones milk color sannan ta yafa mayafi milk color haka takalmi da jakanta milk color, haduwa iya haduwa kam tayi lallai kana ganin ta kasan wannan ta dace da zama uwargida ga JUNAID B ARAB...

Zaunawa tayi kusa dashi har kadadun su na gogar juna, cikin yar karamar murya tace

"Daddyn twins ina kwana?

"Lfy" ya fada a takaice ba tare da ya kalleta ba

Wannan yana daga cikin halayensa dake kara tunzura RUMANA wanda ta dauke shi a matsayin walaqanci

"Daddyn twins" ta kara fada tana kallon sa

"RUMANA" ya fada shima

Bata ko damu ba sabida inda sabo ta saba da hakan, murmushi tayi tace

"Zan wuce bikin gidan su Balkisu da na gaya maka, kaga mune manya ya kamata muje da wuri mu shirya yadda abubuwa zasu kasance, bata jira ansan sa ba don tasan ba maganan zaiyi ba sannan ta mike ta fice tana taku dai dai har ta fice...

Wani iska mai zafin gaske ya furzar har sai da yaran suka razana suna kallon sa, murmushin karfin hali yayi sannan ya rungume su a jikin sa yana mai jin wani zazzafan son su na kara shigan su.....

Binta ce tayi sallma dauke da kofuna guda biyu akan karamin tray

"Yallabai miko su a basu"

"Kar ki damu Binta nima zan iya basu"

Mika mata Arif yayi yace yi hakuri binta ki rike min Arif kafin na gama bawa Arifa

Karban Arif din tayi tana mamakin hali irin na ubangidan nasu sam sam bashi da girman kai irin na masu kudi ga tausayi da kyautatawa na kasa dashi wanda suka sha banban da uwardakin nasu da bata dauki talaka ba a bakin komai ba..

A hankali ya dinga bawa Arifa tana sha har ta koshi duk ta bata masa jiki amma bai ko damu ba

Karban Arif yayi shima ya bashi sannan yace Binta taje tayi musu wanka shima ya nufi nasa dakin dan sauya kaya, tafiya yake amma zuciyar sa na suya da danasanin auran RUMANA, bata ko damu da yaci abinci ko bai ci ba ita dai tayi abinda zuciyarta ke so...






*08038231353 for comment and please share to other groups...*

[19/04 00:58] W Hajara MB: 💦KWARYA TA GARI💦




*HOME OF QUALITY*
*WRITE'S ASSOCATION*
_[The Home Of Quality Which Are Educated The Humanities]_

*⚖(H.Q.W.A)⚖*

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=101128334840967&id=101127231507744&sfnsn=mo


*INGANTACEN ALKALAMI BAYA RUBUTA SHIRME🖊*




WRITTEN AND STORY
BY
HAJARAT M BASH





💦26-30💦




Hankali kwance nake yanka fruits din da mami ta sanya ni yankawa nake sannan kuma ina muraja'an karatun islamiyya na inda nake karanta suratul Naml cikin sassanyan murya ta

Jiki na ne ya bani ana kallo na ai kuwa take zuciyana ta sinke ya hau dukan tara tara, a hankali na waigo da iya fuskata ta gefen ido na gane waye ne, nan kuwa gabana ya kara faduwa

Ban san lokacin da na furta A'uzu billahi ba sannan na maida kaina kasa amma ban cigaba da yankawan ba

Wata husky voice naji ta fara magana badan naga waye ba to da ba shakka kuwa har rantsuwa zanyi nace Uncle J ne

" nifa da salama nazo har ake min a'uziyya" ya fada yana karasowa inda nake tsaye

Tasayawan da yayi kusa dani tamkar kara min gudun zuciya akayi

Hannayen sa duka ya zira a aljihun wandansa sannan ya karkatar da kansa yana kallona

"Ina yini" na fada cikin hargitsatsiyar murya, na rasa meke damuna a duk lokacin da na ganni kusa da wannan bawan Allahn sai naji akalar rayuwata ta canja baki daya, ko mesa?

Bai amsa min sai sai wata ajiyar zuciya da sake a hankali

"Please ki cigaba kinji" ya fada cikin murya kamar mai rada

Cikin rashin fahimta na daga kaina ina mai neman karin bayani, abinda yake nema kenan mu hada ido, da sauri na janye nawa idon cikin kasalalliyar murya nace

"Me zan cigaba"

Lumshe ido yayi ya bude yace
"Karatun mana, muryan ki dadi kamar ki kwana kina rera min ni kuma ina saurara"

Dariya maganan tashi ta bani amman ban dara ba murmushi kawai nayi wanda har fararen hakorana suka bayyana sannan dimple dina suka lotsa

"Masha Allah" ya fada a fili sannan ya zaro hannunsa daya daga aljihu yayi nuni ga kumatuna daidai saitin dimple dina kamar zai taba yace

"I like this " sannan ya maida hannun tare da kura min ido

Cikin rashin fahimta na shafo gurin amma banji komai ba na kalle shi ina neman karin bayani

Wani killer smile yayi har na kusa shagala wajen kallon sa sannan nayi saurin kawar da kaina
"He looks more handsome when he smiles" na fada a zuciyana

"Kawo na taya ki kar mami tace kin dade ko kuma ta biyo sawu"

Sai a sannan na tuna ashe fa aiki aka sani

"Barshi zan karasar na kusa ma"

Bai kula ni ba yasa hannu kan wukar zai karba nayi saurin cika masa, cikin kwarewa ya fara yankawa har mamaki yake bani ganin yanda yake yankawa kamar mace very perfect, baya na ja na jingina da jikin lokan kitchen din ina kallon sa, in few minutes ya gama sannan ya zuba a wani bowl mai kyau na glass yace

"Finish, ya kika gani?

Murmushi nayi nace
"Kayi kokari" na karasa zan dauki bowl din yayi saurin daukewa yace

"Tabbb shikenan abida zaki ce ma?

"Me kake so nace toh" ina turo baki

"Ok tunda baki san me zaki ce ba bari na.....

Bai kai ga karasawa ba muka jiyo muryan Aysha

"Su yaya ashe anan aka makale ko? To kaje Abba ya dawo yana neman ka"

"Aysha kin fa raina ni, zo kiji wata magana"

Ganin haka yasa na na karbe bowl din da sauri na fice daga kitchen din, bai damu ba sai bina da kallo yayi zuciyar sa na kara hura masa wutan sona"

Aysha ce tayi masa tafi daidai fuskan sa, da sauri ya juyo yana kallon ta, bai san lokacin da yayi murmushi ba tare da shafo suman kansa ya kalleta yace
"What"

Riko hannunsa na dama tayi cikin nata cikin sanyin murya mai cike da nuna tausayi tace
"Yaya you have gone deep, ka tuna fa idan zaka so abu kaso shi dai dai kar ka zurfafa haka idan kuma idan zaka ki shima kar ka zurfafa, hadisi ne kuma ka sani"

Iska ya fitar a hankali ya kare damke hannun 'yar uwar tasa yace
"I don't know what to do Aysha, she is my first love, ban taba son wata mace da sunan soyayya ba sai ita, ban taba kallon macen da nake ji i can't live without her ba sai DEENA! from the very first day i set my eyes on her naji she is the one, tun daga ranan na fara rokan Allah da ya rabamu da kaddaran da zata shiga tsakanin mu, Aysha wallahi ina sonta with all my life "

Wasu hawaye ne suka silalo daga idanun Aysha wadda da za'a sanya wuka a wuyanta bata san meye dalilin kukan ba

"Yaya Allah yasa taso ka itama kamar yadda kake sonta, Allah ya barku tare dan zanfi kowa farinciki"

"Meye haka Aysha? Ya fada yana share mata hawayen fuskan ta
"Common stop this sai kace tace bata son nawa? Kalle ni fa i'm sure babu maccen da zan taya taki amsan tayina ko?

Murmushi tayi tace "wannan haka yake yaya".......

Ina isa palon na tadda babu kowa sai Abba da ya dawo, karasawa nayi kusa da mami na ajiye mata fruits din daga gefe sannan na gaida Abba, ya amsa min yana tambaya ta ya gida, Alh Yusuf Jajere kenan mutum mai son jama'a da kyauta halin sa daya da matars da yaransa...

Mikewa Abban yayi yacewa mama ta hada masa ruwan wanka sannan ya haye sama, itama mamin mikewa tayi tace DEENA kibi Uncle din ku zai baki sako na a mota ki karbo min"

"Toh nace ba tare da na gane wani uncle din take nufi ba, waige waige na fara ko zanga waye take nufi ba don har ga Allah ban san da mutum a palon ba, ganinsa nayi zaune cikin sofa kansa a kan wayan sa yana dannawa, sanye yake cikin wata farar yadi kal har kana hango farin vest din sa, kansa babu hula sai suman kansa irin na ainihin fulanin ne yake sheki yasha gyara, haiba, manyata da cikar zati kawai zai nunawa Aliyu amma duk inda cikakken namiji burin ko wacce mace to Uncle Junaid ya kai.

"A hankali na dan matsa kadan kusa da kujeran da yake nace

"Ina yini Uncle J" cikin sanyin murya

"Lfy" ya fada a takaice ba tare da ya dago ya kalle ni ba nima kuwa na samu waje na zauna ina jiran ya tashi na bishi na karbo sakon mamin...

Mintina kusan goma kamar bazai tashi ba sannan ya mike tare da daukan car key dinsa dake ajiye kan stool sannan ya fara tafiya cikin takun birgewa ni sai binsa nake a baya a hankali dan ji nakeyi tamkar idan nayi kwakwaran motsi zai juya ya kikkifa min mari.

Har bakin mota na bishi na tsaya daidai bakin marufin motan inda shi kuma ya shige motan ya rufo sannan ya sauke glass din sannan ya mika hannunsa bayan motan ya dauko wata 'yar karamar farar leda, takaici ya kamani dama wannan 'yar ledan ne sai an biyo sa an karba shi bazai iya daukowa ba? Na fada a zuciya na cike da haushin sa

Har ya miko min ledan sai kuma ya mayar ya kalle ni cikin ido tamkar mai son gano wani abu akan fuskata ni kuwa na saukadda da kaina kasa zuciyana na harbawa da karfin tsiya kai kace tsere nayi, kusan mintina uku zuwa hudu naji wannan murya tashi mai nuni da shi din cikakken jarumi ne, zan iya cewa wannan shine farkon kallo na da yayi mai tsayi duk da da irin zamana a gidan... yace

"Ke wai meye cikakken sunanki ake kiran ki da wani suna mara ma'ana"

Da mamaki na kalle shi ina tunanin yau shi kuwa meye hadin sa da sunana, still ni din da yake kallo

A hankali na maida kaina kasa nace
"KHADIJA ABUBAKAR JUD"
"Khadeejahhh" ya maimata sunan cikin wani salo da zan iya rantsewa ban taba jin wani mahaluki ya taba kiran Khadeejah yayi dadi haka ba"

Tabe baki yayi yana mamakin ina ruwansa da tambaya ta sunana

Miko min ledan yayi yace "jeki"

Karba nayi tare da russunawa na juya cikin gida, tafiya nake kafafuna suna harhardewa saboda a jikina nake jin irin kallon da yake min.
Shi kuwa sai da yaga na shige ya daina kallona sannan ya dawo hayyacin sa, da dan karfi ya daki sitiyarin motan sannan cusa hannayen cikin suman kasan yace
"What's wrong with me ya Allah?

Tada motan yayi ya fice daga gidan, tafiya yake a hankali yana tukin cikin nishadi, haka kawai yake jin wani dadi a ransa da nishadi wanda bai san dalili ba, wata bangaren zuciyarsa ce ta hasko masa fuskanta lokacin da take gaida Abba dazu a palo tana wani murmushi mai birgewa, kuma babu abinda yafi daukan hankalinsa kamar dimple dinta, can kuma ya kara hasko fuskanta lokacin da ya tambayeta sunanta....

"Murmushi ya sake wanda da akwai wanda suka san shi zasuyi mamakin ganin wannan fara'a tasa, a haka har ya karasa gida.....




08038231353 for comment and please share to other groups
[19/04 00:58] W Hajara MB: *KWARYA TA GARI*


*HOME OF QUALITY*
*WRITE'S ASSOCATION*
_[The Home Of Quality Which Are Educated The Humanities]_

*⚖(H.Q.W.A)⚖*

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=101128334840967&id=101127231507744&sfnsn=mo


*INGANTACEN ALKALAMI BAYA RUBUTA SHIRME🖊*


*WRITTEN AND STORY*
*By*
*HAJARAT M BASH*




*Pg21-25*




Bayan sallan magariba kwance nake akan cinyar Ammina tana kama min kalba muna hiran Ammi tana bani labarin yan uwana da suke kasan nijer da labarin Abbu na wato mahaifina wanda ban taba ganin shi ba sai sai dai a photo.

Gyara kaina nayi akan cinyar Ammi sannan nace

"Ammi wa yaushei zamu je muga yan uwan mu ne muma mu shiga cikin su kamar kowa"

Murmushi Ammi tayi tace
"Zamu je Deena watarana zamu je amma ba kwana kusa ba"

Mikewa nayi zaune na fuskanci Ammi na da kyau nace
"Ba yanzu ba kuma Ammi? shikenan haka zamu ta zama muna rayuwa mu kadai ace kaf fadin garin nan babu mutum daya da zamu nuna muce wannan dan uwan mu ne na jini Ammi, bamu da kowa a duniyan na sai su mami, rayuwa zata cigaba ne haka" na karashe maganan wasu siraran hawaye na zubo min

Hannuna Ammi ta kama ta matso dani kusa da ita sannan
"Daina kuka Deena ta share hawayen ki kinji? Ko bayan raina nasan ke kadai ma zaki iya zuwa, a babban birnin yamen idan kikace a kai ki gidan MAMMAN JUD ko karamin yaro zai kaiki nan ne gidansu mahaifinki domin zuriya ce mai dumbin yawa wanda suka hada da manyan 'yan kasuwa, manyan 'yan siyasa, ga sarauta ga kuma dukiya,

Gidan mu kuwa duk inda kike kice a kaiki gidan IDRISS AJIDDE kowa ya sani domin muma babban zuriya ce masu ji da kudi, kyau da mulki....."

Da sauri na katse maganan nace in sha Allahu sa ranki da lafiyarki zamuje Ammina da yardan Allah"

Murmushi Ammina tayi tace "Allah yasa"

Kara gyara zamana nayi nace Ammi baki fada min dalilin da yasa kika baro gida

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment