Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi mutum ne wanda baya son raini ko kadan shisa take shakkar sa dan shi bai taba ganin ta ba sai a photo kasancewar baya nan akayi auren yana kasar waje karatu...

Kamar an sanya ta dole ta fara magana kodan dolen ce ma don sai da Uncle Junaid yayi mata kyakyawan warning game da zuwana....

"Su likita ne a gidan namu yau?

"Ina yini" kawai yace da ita ba tare da kalleta ba yana wasa da Arif

Nima nace "ina yini"

"Lfy" kawai tace a takaice

Palon ya dauki shiru sai dariyan su twins dake tashi, kusan mintina goma ta mike tace
"Na bar baki su kadai" sannan ta juyo tana kallona tace "ke kuma idan kin shirya kiyi min magana a nuna miki dakin ki" tana fadan haka ta juya ta hau sama, wani kallon takaici yaya Aliyu ya bita dashi zuciyar sa na tafarfasa, shi abinda tayi min ne ma yafi bata masa rai.... Ajiye Arif yayi sannan ya dauke Arifa dake kan cinyata ya ajiyeta gefen dan uwanta sannan ya mike tsaye tare da sanya hannayensa cikin aljihun wandan sa ya dube ni fuskansa babu alaman wasa yace, "tashi mu tafi gida"

A razane na dube sa naxe
"Yaya gida kuma?

"Eh ko baki ji mai kyau ne? Idan baza ta zauna ta kula da yaranta ba sai ta bar su ai ita ta haife su tafi mu jin zafin su ko kuma shi mijin nata yasan yadda zaiyi da yaran sa, su da haifan yara wasu da yi musu wahala? No way bazaki zauna a gidan nan ba wata kazama ta dinga bata miki rai ba alhalin kuma taimaka mata kikeyi" ya rufe ido sai masifa yake ban san haka yake da fada ba sai yau, duk nabi na tsorata wallahi.

Ganin haka yaran suma suka fara kuka, nima sai naji zuciyana ba dadi dan tausayin su kuma inajin bazan iya tafiya na bar su haka ba kuma zan iya jure komai kan yaran nan ko ba komai su din basu san komai ba kulawan mai kulawa kawai suke bukata...

Wasu hawaye ne suka zubo min kuma ban damu da na goge su ba

"Ya salamm" yaya Aliyu ya fada tare da shafa suman kansa "to meye na kukan kuma?

Cikin muryan kuka nace
Yaya Aliyu kaji tausayin yaran nan, su basu san komai ba sannan ita Anty Rumana taci darajan Uncle J dan Allah ka barni na zauna dasu wallahi ina son su sosai" na karashe maganan cikin muryan tausayi

"It's OK, ya isa haka, zan barki ki zauna amma da sharadi"

Ko jin sharadin banyi ba na goge hawayen fuskata ina murmushi na rungumo yaran a jikina

Shi mamaki abin ma ya basa ganin lokaci daya har na canja sai ya fasa fadan sharadin yace

"Baki da waya ko?
Daga masa kai kawai nayi

"Ok toh ina zuwa" sannan ya fice daga palon ni kuwa na cigaba da wasa da yaran har suka daina kukan, mintina kusan goma sha biyar sai gashi ya dawo dauke da karaman farar leda ya zauna kusa dani ya bude ledan ya ciro kwalin waya sannan ya bude kwalin ya ciro wata azababbiyar mai waya kyawun gaske kirar Samsung S9, nima kaina wayan ta tafi da imani na, ajiyewa yayi akan cinyata sannan yace

"Manage this phone kafin mu sayi mai kyau, idan kin nutsu ki sanya a charge sannan kuma a cikin kwalin akwai sim card kisa zan kira ki anjima kinji? Kuma ki kula da kanki" yana gama fada ya mike tsaye yace zai tafi, godiya na fara masa ya dakatar dani yace baya so, har ya kai kofa yace "wancan ledan naki ne idan akwai abinda bai yi ba idan na kira ki anjima sai ki fada min ko? Ya fada tare da ficewa daga palon, ni kuwa binsa nayi da kallon mamaki sannan nayi murmushi na dawo da kallona kan yara.....




08038231353 for comments
[18/04 17:56] W Hajara MB: πŸŒŠβ„πŸŒŠβ„πŸŒŠβ„
KWARYA TA GARI
β„πŸŒŠβ„πŸŒŠβ„πŸŒŠ

_____________


*STORY AND WRITING*
*BY*
HAJARAT M BASH
_________________________________________
https://www.facebook.com/100220014964656/posts/100220668297924/?sfnsn=mo

πŸ“•πŸ“•πŸ“•
*HOME OF QUALITY WRITER'S ASSOCIA*
πŸŽ‘πŸŽ‘πŸŽ‘ _{The Home Of Quality Which Are Educated The Humanties}_
______________________


56-60


THE WHOLE OF THIS PAGE IS DEDICATED TO MY SISTER AND ALSO A FRIEND SALAMATU USMAN SAMBO, ALLAH YA BAR KAUNA DA ZUMUNCI🀝




Bayan tafiyan yaya Aliyu ina zaune da twins sai wasa nake musu su kuma sai dariya suke ta bangala min yayin da nake jina cikin wani farin ciki mara misaltuwa.

Arif ne fara dan kananan kuka sai Arifa ma ta kama kana gani ka san kukan yunwa ce daya fara damun su, mayafin kayana na warware na goya Arifa dashi sannan na dauki Arif a hannu ina jijjiga shi ko zasuyi shiru amma kamar kara ziga su nake yi, a tunanina kukan nasu zai sanya Anty Rumana ma ta fito amma ko leke ni inaga irin uwa taji yaro yana kuka a jikin tan nan ma Rumana bata ji....

"Ya Allah " na fada a fili ina cigaba da jijjiga su, ni kuwa bazan iya zuwa wajen ta ba ta disga ni gaban bakin ta ba dan kadan daga aikin ta kenan, wata dabara ce ta fado min da sauri nayi part din masu aiki na tambaye su inda madaran yaran suke, da hanzari nayi kitchen na hada musu anan kitchen din na basu suka sha sai gashi sun fara wasa da junan su.
"Allah sarki" na fada a raina.

Daukan su nayi muka dawo palo na ajiye su kusa da kayan wasan su ni kuma na hau sama naji inane masaukin nawa domin na fara gajiya kuma ina bukatan nayi wanka.

Sallama nayi bakin kofan bedroom dinta har sau wajen biyar amma bata ansa tsaban walaqanci kuma gashi ina jiyo hiran su ita da kawayen nata kuma nasan sarai taji kawai salon ta walaqantani ne.

Murda marikan kofan nayi nasa kaina ciki ba tare da jin wani dar ba, suna zaune sunyi baje baje a palon tsakiyan su warmers ne na gani na fada har guda uka sai plates din da suka ci abinci da kofunan da suka sha lemo. Rumana akwai son harkar girma duk wani abu da zai janyo mata girma tana so, zata iya yin komi don ace ita din wata ce....

A hankali na tako har kusa da inda take cikin sanyin murya ta nace
"Ina yinin ku" daya ce ta amsa sauran biyun ko kallon inda nake ma basu yi ba balle uwar gayyan,
Abinda nafi tsana kenan a rayuwata walaqanci bana iya jure shi ko na sisi wallahi taci albarkacin twins da bata isa tayi min haka ba"

Daure zuciya ta nayi tare da hadiye wani abu mai daci nace
"Anty Rumana wani daki ne zan zauna?

Kamar bazata yi magana ba tsawon mintina biyar sannan ta juyo ta kalle ni cikin isa da gadara da nuna ita din wata ce ta fara magana dan rumana akwai ji da kai, nuna isa, gadara da nuna kai din ba komai bane a wajen ta amma sai dai kash duk wannan kasaita nata da gadara ko dan karamin yatsan JUNAID B ARAB bata kai ba dan itama ta wannan fagen sara masa takeyi....

"Kije main palo akwai bedrooms guda uku sai ki zauna a daya and sannan nasan kinsan dalilin zuwanki gidan nan ba sai na kara fada miki ba amma zan iya sanar dake sharadodina wanda kin san wasu baki san wasu ba koda kwana daya zakiyi balle kuma zaki fi sati ma, na farko bana son shine bana son shishigi a al'amari na da sanya ido akan abinda bai shafe ki ba, na biyu kuma shine yadda kike a main palon nan bana so ki kara debo wannan siraran kafafun naki ki shigo min side kiyi zaman a can har ki koma gidan ku, na uku ki kulan min da yara yadda ya kamata ba sai na fada ba dan mutumin kauye ya iya reno sai dai kar abar su da kazanta dan babansu ysna yawan daukan su suyi wasa, sai na karshe shine tsakanin ki da mijina shine ki kai masa yaransa ko ki dauko su, bana bukatan ya dinga ganin wannan mummunan fuskar taki da babu komai sai idanu, kiyi matukar kiyaye shiga affairs din maigidana idan ba haka ba wallahi sai kinyi danasanin zuwanki duniya, zaki iya tafiya ta juya wajen kawayen ta da sukayi sororo suna kallonta.

Da sauri na juya na bar dakin domin wani irin kuka ne yazo min na walaqancin da Anty Rumana tayi min a gaban mutane... Ina bude kofan naji nayi karo da mutum kaina ya bugi kirjin sa ga wani daddadan turaren dake tashi a jikinsa mai sanya kasala, idanuna da suke zubar da hawaye na daga na kalle shi kana ganin sa kasan yana cikin bacin rai da alama yaji komai, tsaban bacin ran da nake ji ya kore tsoron Uncle J dan ban sake kallon sa ba na raba ta gefen sa na bar wajen ina mai kukan takaici.

Shi kuwa tun shiga na yake bakin kofan sannan yaji duk abinda rumana ta fada, da yayi niyyan ya sameta a gaban kawayen nata amma sai ya fasa tare da kudirin ba yanzu zaiyi mata magana ba, juyawa yayi ya nufi nasa side din yana jiyo shewan su alaman duniya tayi musu dadi.

Na isa palon da niyyan daukan kayana na bar gidan baki daya amma sai me? Arifa na hango kwance tana bacci hannun ta daya a baki alaman tayi kukan yunwa har ta gaji tayi bacci, Arif kuma sai kuka yake a hankali yana jajjan kayan Arifa alaman yana so ta tashi, wani tausayin yaran naji ya mamaye zuciya na, Allah sarki yara 'yan gata da uwarsu da ubansu a raye amma sun koma tamkar wasu marayu? Gaskiya na yadda uwace jigon yaranta, uwace bango abin jinginan yaranta, wanda ya rasa uwa yayi kuka ya daura hannu aka yayi ihu.......

Da sarsarfa na karasa na dauke Arif na rungume shi tsantsan a jikina kamar zan maida shi jikina, wani kuka naji ya kara taso min har da shesheka, mayafina na dauka na goya Arif sannan na dauki Arifa a kafadana sannan na dauki hand bag dina na nufi main palo can dakin da aka bani, duk wannan abinda nake yi ashe shi gogan yana baya na yana kallona dan fitowan sa daga side din Rumana kenan, ajiyar zuciya mai sanyi ya sauke sannan ya nufi nashi bangaren...

Kafin ma na karasa dakin har Arif yayi bacci, dakin a share tas ko ina a gyare sai kamshi yake, a hankali na kwantar da Arifa dake hannuna sannan na kwance Arif shima na kwantar da shi na koma palo na dauko jakan kayana da ledodin da Yaya Aliyu da Mami suka bani da kuma ledan sabuwar wayata, ajiye akwatin nayi a gefe sannan na janyo ledan da Mami ta bani na bude wasu turare ne masu tsada da kamshi mai dadi sai man wanke baki da brush, sai sabulun wanka, murmushi nayi tare da girgiza kai a fili nace "Allah ya saka miki mamina"

Ledan da yaya Aliyu ya bani na bude shima wasu dogayen Arabian gowns ne masu kyawun gaske guda uku sai turare designers guda biyu da flat shoe biyu sai man shafawa kala daban daban, mamaki nayi sosai ganin irin kayan da yaya Aliyu ya jido min sannan ga waya 'yar ubansu, addu'a nayi musu sannan na tattare kayan na ajiye waje daya sannan na jona wayar a chargi na shiga wanka domin an fara kiraye kirayen sallan azahar.....





08038231353 for WhatsApp
[18/04 17:56] W Hajara MB: *πŸ’¦KWARYA TA GARI* πŸ’¦




*πŸ’¦BY:HAJARAT M BASH* πŸ’¦




πŸ’¦ *61-75* πŸ’¦



*



*ASSALAM ALAIKUM MASOYAN LITTAFIN KWARYA TA GARI DA KUMA MASOYANA, INA MAI BAKU HAKURI A BISA JINA DA KUKAYI SHIRU KWANA BIYU, HAKAN TA FARU NE SANADIN WATA MATSALA AMMA ALHAMDULILLAH YANZU KOMAI YA WUCE SANNAN DA YADDAN ALLAH ZAN KAMMALA KAFIN AZUMI NAGODE....*

*MASU KIRANA DA KUMA MESSAGE NAGODE SOSAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI.....*





Bayan na fito daga toilet tare da dauro alwala na dauki daya daga cikin gowns din da yaya Aliyu ya bani na zira tare da feshe jikina da turare masu kamshi sannan na dauki hijab a cikin kayana na sanya nayi sallahn azahar sannan na haye gado kusa da twins na kwanta tare da rumgumo su a kirjina tsam ina jin wani sanyin dadi na ratsa zuciya da gangan jiki, Ina mai ji a cikin raina dama wadannan kyawawan halittan su zama mallaki ko Kuma dama mallakina ne a haka har bacci mai dadi ya kwashe ni cike da mafarkai kala kala masu dadi......

Kamar a mafarki naji a jikina ana kallona irin kallon nan wanda dole kaji a jikin ka, juyi nayi da kaina kadan sannan na kara rungume su Afrif a kirjina kai kace kwace min su za'a yi..

Karo na farko kenan da yaji yarinyan ta basa dariya amma bai yi ba sai murmushi da yayi mai bayyana kyawun sa na usuli ya cigaba da kallon su cikin nishadi tare da kara jingina rabin jikin sa a kofar dakin.

Kiran sallan la'asar naji kamar a mafarki, cikin nutsuwa nayi mika tare da addu'an tashi a bacci sannan na janye twins daga jikina na mike zaune, caraf idanuna suka sauka cikin nasa , gabana ya fadi tare da bugawa da karfi, da sauri na dafe dai dai saitin zuciya na Ina karanto dukkan addu'an da yazo bakina sannan na samu na saita kaina, na janyo dankwalin kayana na rufa a kaina sannan na sunkuyar da kaina kasa cikin sanyin murya nace

"Ina yini Daddyn Arif"

Wani sanyi yaji ya ratsa dukkan ilahirin jikin sa saboda rabon da yaji an ambace shi da Daddyn Arif ko Abban Arifa tun lokacin da Rumana ta haife su, abokan sa B Arab suke kiran sa, 'yan uwan sa Kuma Junaid sai yaran Anty da suke kiran sa da Uncle J, a hankali ya sauke ajiyar zuciya mai sanyi sannan ya gyara tsayuwan sa , kasancewar shi mutum ne wanda da wuya ka gane alkibilan sa walau farinciki ko akasin hakan....

"Idan kinyi sallah ki kawo min yaran side dina" yana gama fada ya fice tare da janyo kofan.

Da ido na bi kofan sannan na dawo da kallona kan yaran da suke bacci hankali kwance, tabe baki nayi, a raina nace "masu yara manya" sannan na mike na shiga toilet na dauro alwala na fito nayi sallah , Ina idar da sallahn naji sun tashi sun shirin Fara kananan kuka da sauri na isa garesu na dauke su ina murmushi

"Angels Kun tashi ne? Duk da nasan ba ansa zasu bani ba amma sai naga suna min dariya, biye masu nayi mukayi ta Wasa sannan nayi musu wanka na sanya masu kaya daga cikin kayan da aka ajiye a dakin kafin zuwa na, a hada masu madaran su suka Sha suka koshi, sai a lokacin na tuna babansu na son ganin su, da sauri na goya Arif da towel din su sannan na dauki Arif a hannuna muka nufi bangaren babansu ina mai yiwa Arifa wasa tana kyalkyala dariya har muka iso bakin kofan dakin, sallama nayi sau uku naji shiru, har kamar zan koma Kuma sai nace kilan ko yana can uwar daki shisa bai jina ba, a hankali na murda marikan kofan dakin tare da tura kofan sannan na sanya kaina ciki a hankali tamkar wata mara gaskiya, wani kamshi ne mai dadin gaske ya ratsa hancina tare da sanya min kasala har Ina lumshe ido, kara rungume Arifa nayi sannan na kara kwararo sallama, amsawa naji anyi daga gefena ashe ma yana kusa.

A hankali na karasa kujeran da yake kwance na tsugunna daga gefe na sunkuyar da kaina kasa, cikin siririyar muryana nace

"Ina yini?

"Lfy" yace a takaice tare da mikewa daga kwancen da yake gami da miko min hannu wato na bashi Arifa, mika masa ita nayi sannan na kwance Arif shima na mika masa, dukkan su ya Dora akan cinyan shi cikin nuna jin dadi da bayyana tsan tsan kauna tsakanin diyoyi da uba ya furta "my angels" fuskansa mai dauke da wani kayataccen murmushi Wanda idan ba da yaransa ba to da wuya kaga yana murmushi haka....

Murmushin nima nayi tare da mikewa zan fita, ban kai ga karasa mikewan ba naji yace
"Ina zuwa?
Ban san me zan ce masa kawai na dawo na zauna kaina a kasa ina Wasa da yatsun hannaye na wanda yake dauke da jan lallen da bana rabuwa dashi.....

Wasa yake tayi musu suna dariya yana biye musu can ya daga kai ya kalle ni yaga ko kwakwaran morsi bana yi sai wasa nake da yatsun hannaye na, idonsa ya zubawa yatsun nawa domin a rayuwan shi yana so yaga mace da jan lalle especially matarsa amma Rumana ta dauke shi kauyance ita a ganin ta kauyawa ne keyi....

Kamar saukar aradu naji muryan sa har tsakar kaina wanda ya ratsa dukkan sassan jikina inda yace

" Mesa baki yiwa Arifa jan lallen ba itama?

Murmushi nayi mai cike da mamaki nace
"Babu"

"Babu ai ba ansa bane, kodan kinga ita 'yan mata bane?

Wani mamakin ne ya kara kamani, dama Uncle J yana magana haka? Ban gama tunanin ba naji kara da cewa

" Yayi kyau"

Cikin jin kunya nace

"Nagode"

Bai kara cewa komai ba ya cigaba da wasa da yaransa suna ta faman dariya, ni dai ban kara magana ba

"Tell me more about yourself Khadija" na kara jin tambayan har kwanyata, wannnan wani irin mutum ne ni Deena? Na tambayi kaina, duk na rasa ta inda ma zan fara, ban gama tantance abinda zance ba ya kara cewa "in brief ba wai a takaice ba"

"Ya Ilahi" na furta a kasan makoshi na gami da hadiye wani yawu mai daci sannan bude bakina cikin wannan muryan tawa mai sanyi na fara cewa

"Sunana Khadija Abubakar Jud.......... Na kwashe labarin da Ammina ta bani gabadaya na fada masa inda na karasa sauran labarin da kuka mai nuna ina kewan mahaifi na da 'yan uwana"

Bai ce komai ba illa jingina kansa da yayi jikin kujeran da yake kai yana mai jin wani abu yana taba ransa har zuciyan shi na bugawa da karfi....

Ni kuwa kukan nake ba kakkautawa domin an fama min inda yafi min ciwo ne, an tabo min inda bazai taba warkewa ba har na koma ga mahalicci na ba....

"It's okay Khadija, kukan ya isa haka please, dauki yaranki ku koma daki lokacin sallah ya kusa, har cikin ransa yake jin kukan, yayi danasanin tambayana da yasan zanyi kuka.

A hankali na mike na dauki Arif na goya sa sannan na sunkuyo zan dauki Arifa inda shima ya dago zai miko min ita goshin mu ya hadu sai ji kake _kummm_ ,da sauri na dafe wajen nace "wash Allah na"

Tashin hankali bayyane a fuskansa yace
"Subhanallah sannu please yi hakuri ban san kin sunkuyo ba"

Murmushin karfin hali nayi nace "ba komai" sannan na dauki Arifa dai dai lokacin Rumana ta shigo tana zuba kamshi, ganina da tayi ne ya sauya fuskanta ta hau huci tamkar maciji tana hura hanci, ni tsoro ne ya kamani baki daya nayi saurin jan kafafuna na raba ta gefenta na wuce, har na kai bakin kofa naji ya Kira sunana

"Khadija idan kinyi sallah zamu je chemist sai a duba ki, take care"

Wani rugugi naji zuciya na tayi ai kam da sarsarfa ma fice daga palon, shi kuwa da gayya yayi, yana gama maganan sa yayi hanyar bedroom dinsa ai kuwa itama Rumana tabi bayansa tana hayagaga da babatu, kuskure daya ne Rumana bata yiwa Junaid shine zagin sa ko cin zarafin sa tana matukar kiyayewa, a tsakiyar bedroom din ya dakata ya juyo sannan ya tako inda take ai kuwa daga nan Tasha jinin jikinta ta dauka ma dukanta zaiyi.


"One more word Rumana wallahi fushina zai sauka akanki yanzu kuma wallahi ko alif kika furtawa KHADIJA sai kinyi danasani mara amfani" yana gama fada yayi toilet inda ya barta a tsaye cikin mamaki da ciwon rai.......


Ina fita daga palon ina sauri na isa daki na hango Yaya Aliyu a main palo sai safa da marwa yake yi, yana sanye da wata farar yadi kal, ansa babu hula sai suman sa da yasha gyara sai sheki yake, hannayen sa duka biyu zube cikin aljihu kansa a kasa , da ka gansa kasan yana cikin matsanancin damuwa....

A hankali na karasa sannan na tsaya ta bayansa na furta
"Yaya Aliyu"

Ai kam da wani hanzari ya waigo, yana tozali da ni kuwa ya wani sauke zazzafan ajiyan zuciya tare da ciro dayan hannun sa ya dora kan kirjin sa saitin zuciyan sa yace

"Deenatuh"






08038231353 for comments

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment