Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duniya if not da suma sun bi ruwa kuma kin san babu abinda nake so kamar yara Rumana. What have i done da zaki saka min da wannan iskancin? Nasan maganinki amma, dan Allah fitan min a daki wallahi bani son ganinki" ya fada yana hayewa gadonsa tare da janyo bargo ya rufe su da yaransa

"Junaid kayi hakuri i can explain please "

Yaye bargon yayi ya kalle ta sannan yace

"Get out and one more word Rumana sai gane kuren ki a daren yau kuma ki kashe mana wutan dakin" ya juya ya barta zaune yasan ko hauka take baza ta sake magana ba dan iya zaman su bai taba bata time yana mata magana haka ba.

Jiki a sanyaye kamar jefi kaza da da gishiri ta mike ta kashe masa wutan kamar yadda ya bukata sannan ta fice

A daki juyi take kan gado kwarai tasan Junaid gaskiya ya fada, shekara biyar da auren su ba zaman jin dadi yake da ita ba irin mata da miji, to amma ni gaskiya bazan iya rayuwa yadda yake so ba" ta fada a fili sannan ta cigaba "na sanya hijab idan zan fita, na dinga shiga kitchen ina girki wanda ko gidan uwata da ubana bana yi sannan na dinga zaman gida kamar wata illiterate? Ina bazai taba yiwuwa ba wallahi sai dai kawai ka cigaba da hakuri dani Junaid amma bazan iya bin wannan so called ra'ayinka ba. Wani tsaki ta ja ta share batun ta cigaba lissafin kayayyakin da aka kawo mata dazun da irin riban da zata samu......




08038231353 for comment and please share to other groups
[18/04 17:56] W Hajara MB: 💦KWARYA TA GARI💦




âš–
*HOME OF QUALITY*
*WRITE'S ASSOCATION*
_[The Home Of Quality Which Are Educated The Humanities]_

*âš–(H.Q.W.A)âš–*

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=101128334840967&id=101127231507744&sfnsn=mo


*INGANTACEN ALKALAMI BAYA RUBUTA SHIRME🖊*



WRITTEN AND STORY
BY
HAJARAT M BASH


💦41-45💦




Yau ya kasance monday ina kwance kan kujeran palon mu muna hira da Ammina duk dai hiran akan garin su ne da kuma Abbuna nacewa Ammina zanje na gaishe da Mami don duk safiya kamar karfe goma na safe na kan ja side din mamin mu gaisa sannan mu danyi hira sai na dawo saboda Allah ya dorawa Mamin sona tana jina har cikin ranta tamkar su Aysha....

Mami ce tayi min a dawo na kuma gaishe ta itama zata shigo anjima

"Toh" nace sannan na janyo mayafin dogon rigan dake jikina na yafa kasancewar ni mace mai mai ra'ayin son dogon riga shisa mami take yawan siya min sannan ko Atamfa zata dinka mana ko less to dinkin dogon riga take bayarwa ayi min daga baya kuma da ta gane nafi son irin arabian gown shi take sayo min....

Tafiya nake a hankali cikin nutsuwa kaina a kasa tamkar bani son taka kasa dai dai zan sanya kaina cikin palon shima ya sanya kan shi zai fito sai ji kake kummm mun gwara goshin mu, wani duhu duhu na fara har kaman wasu taurari ne naga kaman suna yawo tsabar naji azaba, da sauri na dafe wajen n furta "wash Allah na"
"ya Ilahi ya fada cikin kidimewa

"Sannu dan Allah Deenah, i really don't know you are behind please sorry "

Idanuna da suka dan kada sukayi ja na kalle shi sai duk ya wani rikice
Murmushi nayi na sauke hannuna kasa nace
"Ina kwana"

"Baki ji ciwo ba? Shine tambayan da ya jeho min
"Eh" na fada sannan na maida kaina kasa ganin irin kallon da yake min

"Hey feel free i'm your friend, brother and also a doctor, so fada min akwai zafi?
Yadda yayi maganan sai duk naji wani abu ya taho zirrr daga tsakiyan kaina har babban yatsana.

"Babu zafi yaya dagaske"

"Ok kalle ni kice babu zafi idan kuma kikayi min karya zan gani a idona"

"Ikon Allah" na fada a raina sai kawar da zancen nace
"Mami ta tashi ne yaya?

"Hmmm baki son tambayan da nayi miki ko? Well mamina ta tashi muje na raka ki nima dama bamu gaisa ba"

Bance kala ba nayi gaba yana bina a baya, wallahi a jikina naji ya kure ni da ido yana kallo na, tafiya ta fara so ta gagareni, ganin haka yace
"Wait Deena" cak kuwa dakata da tafiyar kamar dama jira nake ayi min magana na tsaya, a hankali ya tako ya jera dani ya dan sunkuya ya leka fuskata yace
"Irin wannan sauri haka kaman zaki tashi sama?

"Uhmmm nace kurum na fara tafiya shima ya biyo ni muka jera har dakin Mami.

Zaune take bakin gado tana ninke wasu kayan ta, gaishe ta nayi nace ta bari na karasa, murmushi tayi tace "yauwa na kuwa gode, bari naje wajen Abban ku kafin ya fita"

Har ta kai bakin kofa taji yaya Aliyu yana magana
"Mami halan kin manta ma dani a dakin sai gaishe ki amma hankalinki yana wani wajen"

Murmushi mamin tayi sannan tace
"Ta yaya zan manta da jarumin jarumai, Aliyu haidar gadanga kusar yaki, my handsome good obedient child" ta kaeashe tana dariya sannan ta fice

Wani nishadi yake ji duk lokacin da mami take yi masa irin wannan kirari, lumshe ido yayo sannan ya bude yana murmushi, ni kuwa wani birge ni sukeyi saboda wannan kadai ya nuna Aliyu daban ne a cikin ran mami, cigaba nayi da ninke kayan ina kallon shi ta gefen ido sai kallona yake tamkar ya samu talabijin.

"Bani labarin saurayin ki"
Tambayan da naji ya jefo min da sai da naji kirjina ya hau lugude da karfi wanda har sai da kayan da nake ninkewa sai da ya fadi

"Uhm ina sauraranki" ya kara jahon min tambayan

Dukkan karfin maganata na tattaro na furta
"Bani dashi"

Dariya yayi ya mike daga kishingiden da yake ya zauna mai kyau yana kallona da kyau yace

"No bazan taba yadda ba, su Aysha da suke ss2 ma suna da saurayi balle keda kika gama? You know it's unbelievable, common tell me i'm your friend "

"Murmushi nayi nace
"Dagaske fa nake yaya Aliyu"

"Ok toh naji, kina so nayi miki daya?

Da sauri na kalle shi ina zaro ido amma bance komai ba, shi kuwa girar sa daya ya daga yace

"Yes, ko baki so ne? Kinga ni yayan ki ne bazan baki abinda zai cutar dake ba ko?

Mayar da kaina nayi kasa zuciyata na tambayata toh mesa Yaya Aliyu ya damu dani har haka..... Ban gama tunanin ba naji ya cigaba

"Duk mutuncin diya mace gidan ta Deenah, kin gama makaranta me zaki jira? Ko kema kina da ra'ayin cigaba da karatu ne? Idan ma kina dashi gwara ki canja...... " bai kai karshen maganan ba wayarsa ta fara ringing, dakatawa yayi tare da ciro wayar daga aljihun wandan sa, screen din kurum ya kalla yayi wani murmushi sannan ya daga yasa a kunne

"Assalamu Alaikum Uncle J, ina kwana? Shiru yayi alaman yana sauraran me ake fada sannan yace
"Ok toh bari na fito ina dakin Mami ne"

Sannan ya kashe wayan tare mikewa yayi hanyar kofar fita nabi shi da kallo, har ya kai bakin kofan ya juyo ya kamani ina kallon sa wani kunya ne ya kamani nayi saurin dauke kai shi kuwa wannan killer smile din yayi yace
"Idan kin gama kar ki tafi ki jira ni sai mun karasar da maganan mu" sannan ya fita ya barni cikin zullumi da tunani....

A falo ya tadda Uncle J ya hakince a kan kujera ya tsare gida fuskan nan tamkar bai taba murmushi ba yana ta faman danna waya, yana sanyi da wani farin yadi kal kasancewar sa mutum ne mai son fararen kaya, yayi kyau mutuka ainun, karasawa Yaya Aliyu yayi suka gaisa yana tambayan twins sai a sannan ya daga kai yace they are doing good" sannan yace

"Ina Anty ta shiga nayi ta kiranta bata yi pickin ba har na kama hanyan office sai na fasa sabida ina so muyi magana da ita ne"

Tana side din Abba ne bari nayi mata magana" Aliyu ya fada tare da mikewa yayi hanyan side din Abba shi kuwa uban miskilin bai ce komai ba illa mayar da kansa kasa da yayi yana danna wayar sa.

Kusan minti goma sai ga Mami da Aliyu sun taho Aliyu kuwa ganin magana zasuyi ya koma daki wajen Deena...

Mayar da wayan yayi cikin aljihu ya juya da kyau ya kalli mami.

"Anty ina kwana "

Bata amsa ba illa matsowa da tayi ta zauna a kujeran dake kusa da nashi ta sanya hannunta ta daga habarsa tace

"Junaid why please? For how long zaka dinga boye min damuwan ka bayan baku da kowa da ya wuce ni duk duniyan nan? Ehh, ko ba fada min ba nasan kana cikin damuwa Junaida, koba baka fada min ba i can feel ita Junaid, ko kamanta abu daya ne ya samar mu? Ko ka manta nice nafi kowa sonka da sanin damuwan ka tun kafin ka fada min, ko kuma mantawa kayi mudin aminan juna ne? Dan Allah Junaid ka fada min kaji?

Riko hannunta yayi cikin nasa yace "anty ina sauri zanje office we will talk later and nazo neman alfarma ne"

Zare hannunta tayi daga nashi ta dungure masa kai tace " see you ni zaka tambaya alfarma bayan kasan zan iya baku duk wani abu da na mallaka kai da Omar"

Murmushi yayi wanda bai baiyana hakoransa ba a hankali ya furta
"Thank You "

"Uhmmm ina jinka, ya akayi?

"Kansa ta dan sosa da key din motar sa yace
"Dama so nake ki bani aron yaranki ko Aysha ko Islam suje gida na for I ne week haka saboda twins saboda nanin su ta tafi kauye wai 'yarta ta haihu'

Tabe baki Mami tayi tace
"Uwarsu kuma baza ta iya kula da yara na sati daya ba kawai, kai halin Rumana sai ita wallahi, ai da sun isa yaye da dauku su zanyi ai suma su huta da galeji" ta karashe tana mai jin haushin Rumana a ranta sosai sabida yadda ta kasa samawa 'dan uwanta kwanciyar hankali da farinciki bayan shi din bai rasa komai ba na jin dadin rayuwa...

"Su Aysha suna makaranta sai dai Deenah taje tunda ita ta gama nata makarantan ba ta kuma jona wani ba sai idan sun dawo suje"

"Ok toh sai Aliyu ya kaita yanzu Anty sabida nasan suna can su kadai" ya fada yana mikewa

"Eh bari Aliyu zai kaita"

Godiya yayi sannan ya tafi ya bar mamin cikin tsananin tausayin 'dan uwanata'......




08038231353 for comment and pls share to other group...
[18/04 17:56] W Hajara MB: 💦KWARYA TA GARI💦





âš–
*HOME OF QUALITY*
*WRITE'S ASSOCATION*
_[The Home Of Quality Which Are Educated The Humanities]_

*âš–(H.Q.W.A)âš–*

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=101128334840967&id=101127231507744&sfnsn=mo


*INGANTACEN ALKALAMI BAYA RUBUTA SHIRME🖊*



WRITTEN AND STORY
BY
HAJARAT M BASH




💦46- 50💦


INA MAI NEMAN AFUWA BISA JINA DA KUKAYI SHIRU KWANA BIYU KASANCEWAR MAKARANTA CE TA RIKE NI GA PROJECT DAN ALLAH AYI HAKURI.

MASU KIRA NA DA MESSAGES NA GANI KUMA NAGODE DUK DAMA WASU BAN SAMU DAMAN YI MUSU REPLY BA AYI MIN AFUWA, ALLAH YA BAR ZUMUNCI MASOYANA DA MASOYAN LITTAFI NA NAGODE....


THE WHOLE OF THIS PAGE IS DEDICATED TO THE GREAT HAUSA NOVEL WRITTER SUMAYYA ABDUKADIR (TAKORI)



Zaune muke a dakin mami na gama gyara mata kayan amma ban fita ba saboda Yaya Aliyu ya hana ni ya kasa ya tsare wai sai na bashi labarin samari na don shi bai yadda bani da saurayi ba, duk na takura na kasa kwakwaran motsi saboda yanda ya zuba min ido ko kiftawa babu shi a dole yana jiran Yaji na bashi labarin samari na, hakuri na bashi har da rantsuwa amma yayi kunnen shegu yayi kaman baya wajen... Shigowan mami ne ya ceceni.
Da murmushi ta kalle ni tace
"Sannu Deenah, Allah ya kawo miji nagari"

Ban iya na amsa ba sai murmushi da nayi na mayar da kaina kasa ina wasa da zarazaran yatsun hannuna.

Shi kuwa yaya Aliyu a zuciyan sa yace "Allah ma ya bata mamai"

Mikewa nayi nace zan koma wajen Ammi na, mami tace
"Yauwa Deenatu ki shirya ko Aliyu ma Ya kaiki gidan Uncle dinku Junaid zaki dan zauna da yaranki ne wai nanin su tayi tafiya kuma kin san halin matar uncle din naku ba iya kula zatayi dasu ba sai ki gayawa Ammin ki ko?

Wani farin ciki ne ya kamani zanje na zauna da twins saboda Allah ya dora min son yara barin ma Arif da Arifa, na manta da wani yaya Aliyu a wajen nayi wani tsalle na fita da gudu nayi side din mu.

Dariya mami tayi tace
"Kai Deena akwai son yara....

Aliyu ya gyara zamansa ya kalli mami sannan yace

"Wai ita matar yaya Aliyu har yanzu bata canja ba?

"Hmmmm kai dai bari Aliyu ahm ai jira nake su kai yaye na dauko su gabadaya sai suyi ta zaman su kadai tunda haka take so"

Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke kadan yace
"Allah ya rufa asiri ya kuma shirya ta"

"Amin ya Allah, yanzu ka tashi ka shirya ka kai min Deenah gidan"

"Ah mami sai kace wata mace wai na shirya? Ni a shirye nake bari na jira ta a main palo kawai, ya karashe maganan tare da mikewa ya nufi kofa"

"Toh ai shikenan sarkin tsari, idan ta shirya kamin Magana kafin ku wuce"

"Toh" kawai ya fada ya fice

Gudu gudu sauri sauri na fada side dinmu kana kallona kasan ina cikin farin ciki mara misaltuwa.

Ammi tana zaune a palo tana kallon sunnah TV na shigo ina ta zuba murmushi kamar wanda akayiwa albishir da gidan aljanna.

Ammi ce ta dube ni da mamaki a fuskan ta
"Lafiyan ki kuwa Deenah?

Gefenta na zauna na rugumeta ta gefe nace
"Mami ce tace na gaya miki na shirya naje gidan Uncle J na zauna da twins nanin su tayi tafiya" na karashe magana da wata amo mai nuna jin dadi...

"Ah lallai toh shikenan ai sarkin son yara shirya kije, waye zai kaiki?

"Yaya Aliyu ne mami tace ya kaini" na fada tare da mikewa na shige dakina

Murmushi Ammina tayi tare da girgiza kai a ranta tace "Khadija akwai son yara tamkar Abubakar"

Ina shiga daki na fada toilet nayi wanka cikin sauri duk dama ina da sanyi amma yau na danyi abu da hanzari saboda ina dokin ganin twins, ina fitowa a wanka mai kurum na shafa har na dauko wata doguwar arabian gown baki mai adon stones ja sai naji ina sha'awan yau dai na danyi kwalliya kadan, bakin dressing mirror na koma na dauko powder na murza, na dauko jan janbaki na shafa, na dauko brush na gyara girata sannan na shafa kwalli, da na kalli kaina a madubi nima nasan nayi kyau sosai murmushi nayi na dauko kayana nasa nayi rolling din mayafin kayan na feshe jikina da turarirrika masu kamshi da tsada, sannan na janyo trolley na karami na jera kayana kala biyar sannan na saka abubuwan amfanina kamar su sleeping dress, hijab din sallah, sosan wanka da sabulu da brush sannan na dauko hand bag karami na sanya powder da turarika na rataya jakan na dauko wani flat shoe baki na sanya a kafata, na janyo trolley na nufi palo inda samu Ammi inda na barta sai dai wannan karan ta dan kwanta kan kujeran, ajiye akwatin nayi a gefe naje kusa da ita cikin zumudi nace
"Ammina na shirya zan tafi"

Hannuna ta rike tare da mikewa ta zauna tana kallona sannan tace
"Khadija" sai da na daga kai na kalleta jin ta kira
ni da sunan da sai ta shekara bata kira ba, sai naji jikina yayi sanyi
"Na'am Ammina'

Shafa kaina tayi tace
"Ki kula da kanki kinji? Kiyi abinda ya kaiki ki dawo babu ruwanki da shiga abinda bai shafe ki ba duk dama nasan halinki Khadija, komai Rumana zatayi miki karki tanka mata tunda kowa ya san halinta, ki kuma kula da ibadanki Khadija, tashi kije Allah ya kiyaye a gaishw min da jikokina

"Jiki a sanyaye na mike tsaye nace " toh Ammina zan kula In sha Allahu, sai na dawo, sannan na nufi hanyar fita

"Allah yayi Albarka sai kin dawo"

"Ameen nace sannan na fice na nufi side din mami.
A main palo na tadda Yaya Aliyu yana zaune sai faman danna waya yake cikin kwarewa, ban gama shigowa ba sai ga mami ta sauko daga dakinta ta karaso tace
"Sai yanxu ma ashe kika karaso ni ai na dauka ma kun tafi"
Sai a sannan ya dago kai ya kalleni......




08038231353 for comment
[18/04 17:56] W Hajara MB: 💦KWARYA TA GARI💦






âš–
*HOME OF QUALITY*
*WRITE'S ASSOCATION*
_[The Home Of Quality Which Are Educated The Humanities]_

*âš–(H.Q.W.A)âš–*

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=101128334840967&id=101127231507744&sfnsn=mo


*INGANTACEN ALKALAMI BAYA RUBUTA SHIRME🖊*



WRITTEN AND STORY
BY
HAJARAT M BASH



💦51- 55💦



WANNAN PAGE DIN NAKI NE KAWATA BESTY NA HALIMA ADAMU (COOL BABY) UMMU KULTSUM......



........ Kaina a kasa sai murmushi nake yi, shi kuwa yaya Aliyu sai kallona yake babu ko kiftawa yana kara godiya ga Allah da ya hada shi da wannan kyakyawar halittan,

Mami ce ta miko min wani leda tace "ga wannan kiyi amfani dashi dan nasan Rumana ba baki zatayi ke kuma shegen zurfin ciki balle kuma uban gayyan Junaid da baya shiga sabgar mutane"

Hannu nasa na rusna na karba tare da yin godiya wanda hakan da nayi na kara samun wani babban matsayi da muhalli mai girman gaske a zuciya yaya Aliyu.

"Aliyu tunanin me kakeyi ne ka tashi ku tafi mana rana yana kara yi"

Sosa kansa yayi da makullin motansa ya mike yana murmushi ba tare da yace komai ba ya fice nima nabi bayansa mami itama ta biyo mu dan yi mana rakiya, har ga Allah Mami bata so tafiyana ba dan dai babu yadda zatayi ne don tana son zama dani kasancewar ni mutum ce mai saurin shiga rai sai idan bamu zauna ba duk dama bani da magana.

Har bakin mota mami ta raka ni tana ta kwantar min da hankali kan Rumana, gidan gaba na zauna inda yaya Aliyu da kansa ya sanya min kayana a buth din motan sannan ya dawo mazaunin driver ya zauna tare da tada motan, murmushi yayiwa mami yace "sai na dawo Mamina"

Itama murmushin tayi sannan tace "Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya"

Tada motan Aliyu yayi ya juya kan motan yana dagawa mami hannu nima na daga mata maigadi ya bude mana gate muka fice.

Tafiya muke shiru cikin motan baka jin karan komai sai sanyin ac dake ratsa jiki da jijiyoyi, ni dai sai wasa nake da yatsan hannuna da yasha jan lalle da bana rabuwa dashi, shi kuwa tuki yake cikin nutsuwa da jin dadi ga wani nishadi da yake dawainiya dashi....

Hannun sa daya yana kan sitiyari dayan hannun kuma ya daura a gefen seat din sa, kallona yayi na wasu sakanni sannan ya maida duban sa zuwa titi, a hankali kamar mai rada yace

"Kwana nawa zakiyi naga kin dauko wani katon akwati?

Da mamaki na kalle shi wai na dauko katon akwati sai nayi murmushi nace
"Yaya Aliyu wannan ne katon akwati?

"Eh mana gashi kuwa na gani" wata nawa zakiyi toh?

"Sai nanin su ta dawo zan dawo" na fada ina mai maida kaina ta window

"Ba rana kenan? Tamkar ba shi bane Yaya Aliyu mai wasa da dariya ba ya wani sha mur....

"Ikon Allah" na fada a raina, ban ce komai ba na cigaba da kallon window, shima bai kara magana ba har na tsawon mintina goma sannan yace

"Deenah kin kina da kyau?

Wani banbarakwai naji wai namiji da suna Hajara tare da wani faduwar zuciya "hmmm nace kawai, ban gama tunani na ba naji alaman an tsayar da motan kallon sa kawai nake cike da mamaki da kuma tsoro har ya gama packing gefen titi kusa da wani babban plaza,

"Ban ansa na" ya fada yana kure ni da wani irin kallo da ban taba gani wani da namiji yayi min ba, kallon da yake so ya sauya min tunani na lokaci daya, kallon da nake jin shi tun daga tsakar kaina har babban yatsan kafata....

Gyara zamana na kara na takure gefen kofan motan, dariya yayi yace
"Matsoraciya kawai ni babu abinda zan miki and kuma na fada miki idan an yaba ki thank you ake cewa ba wai ayi shiru ba, 'yar kauye kawai" ya karashe yana fita daga motan ya barni cikin tunanin al'amuran shi....

Kusan mintina ashirin sai gashi yazo dauke da wata katuwar farar leda ya bude seat din baya ya ajiye sannan ya zagayo ya shiga muka tafi, muna tafiya yana ta jana da hira daga karshe ya jaddada min sati daya ya bani nayi a matsayin sa na yayana ni kuwa ba dinga bainsa da toh kawai dan nima kaina ban san adadin kwanakin da zanyi ba.....

Unguwa ce wacce kana gani kasan ta manya ce dan gidaje ne na gani na fada, kullum idan munzi unguwan Uncle J bana gajiya da kallon unguwan da yake muna zuwa amma ba sosai ba kasancewar rashin sake fuska na Rumana, horn mukayi mai gadi ya leko ta wani buli na gate din sannan ya wangame mana wawakeken gate din muka shiga, yaya Aliyu ne ya dauka min kayana duka nayi nayi dashi ya bani ko daya amma yaki, da sallama muka shiga main palon amma ba kowa sai da muka kara shiga ainihin palon nan ba kowa sai twins su kadai a tsakar palon suna ta wasa ga kayan wasa kala kala masu tsadan gaske irin na 'ya'yan gata a watse a tsakar palon, suna jin sallaman mu suka juyo a tare, ganin Yaya Aliyu sai suka fara daddaga masa hannu badan komai ba sai dan tsantsan kaman da yake yi da daddyn su, shima baiyi kasa a gwiwa ba yaje wajan su yana daga su daya bayan daya yana kissing kumatun su sannan ya zauna shima kan carpet din yana musu wasa.

Ni kuwa sai binsu nake da kallo cikin kauna, soyayya da tausayin yaran, gefen su nima na zauna tare da daukan Arifa na dora ta kan cinya na ina mata wasa abin mamaki kuwa sai dariya take min.....

Dakatawa yaya Aliyu yayi daga wasan da yake yiwa Arif yana kallon mu a lokaci daya kuma kamar ana kara hura masa wutar kaunata har yana jin dakyar ya iya rayuwa babu ni, a hankali kamar mai rada yace
"She looks more cute when she is laughing"

Ni kuwa dakatawa nayi da wasan da nake mata ba tare da kuma na kalle shi ba ina mai mamakin kalaman sa.......

Shigowan Rumana ne ya katse min sauran tunani na, tana sanye da wani dogon riga rubber babu dankwali a kanta sai taunar chewing gum take kamar wata sabuwar kilaki, daya daga cikin kujeran ta samu ta zauna tana wani yamutsa fuska tamkar taga wasu kashi...

Shi kuwa Yaya Aliyu ko daga kai baiyi ya kalle ta ba dan dama shima ba shiri suke ba sabida

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment