Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ashe duk wahalar da yakesha da kudin da yake kashewa ita ta qullah komai itace ta lalata masa gabansa saboda kawai ta hanasa farin ciki da iyalinsa shikam me yayi mata haka me Habeey tayi mata da suke burin nakasta ta?.




Bashi da amsar tambayoyinsa saboda haka suna shiga ya zube a parlourn yana wuci jikinsa da bakinsa na wani turirin zafi saboda ran maza ya baci, itakam lura da yanayinsa yasata haurawa sama ta shiga tayi wanka ta canja kayanta zuwa wasu marasa nauyi cikinta ya fito sosai da yake bana fari bane ta sauko qasan ta zauna a kusa dashi ta shafo kansa tace “kayi hqr don Allah koma menene kaji" kwantowa yayi a jikinta ya fashe da kuka yace “ashe Mom tasan komai itace ummul aba'isin faruwar komai da yake faruwa damu sune suka dora miki wannan faduwar gaban data qararmin dake ta hanamu kwanciyar hankali, ashe sune suka kwantarmin da gabana ya daina aiki Habeey ashe ciwon da aka cemin Saudat tana fama dashi tsayin watanni ke akaso a dorawa shi Allah ya dawo musu da mugun nufinsu ashe a nufinta na ta sake dora miki ciwon da kika tashi dashine taje sukayi hatsari Munafukar yayar tasu Ummah ta mutu Mom ta samu wannan matsalar ita Kuma aunty Zahrah ta karairaye"



Sake shigar da ita yayi jikinsa yace wlh Mom ta cucemu hatta zargin da nakeyi miki ashe duk sa sa hannunta nayi danasanin sanin Mom dama ba ita ta haifem..."
Rufe masa baki tayi tace “aa kar ka fadi haka don Allah komai yayi farko fa yanada qarshe yamazo qarshen insha Allahu abinda akayi a baya bazaayishi gababa"
Lumshe idonsa yayi ya shafa cikinta yace “zan samu sauqi insha Allahu zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi amma dai yanzu zaki barni na fadawa su Abba matsalarmu ko?" Rufe idonta tayi tace “nidai kunya nakeji gsky..." Bakinsa ya dora saman nata tace “nikam banajin kunyar neman lfy so nake da kin haihu na qara dura miki wani babyn" harararsa tayi shima ya harareta sukayi dariya ya miqe yace “kina wanka Addah ta aiko mana da abinci muci ki huta sai jibi zakije ku gaisa da su"
Abincin ya dauko ya ajiye musu a gabansu tuwon shinkafa ne miyar agusi ta dago ta kalleshi tayi murmushi tace “Allah sarki Addah na ashe tana riqe da abinda nace mata inaso" qasa yayi da idonsa yanajin dama mahaifiyarsa ce haka.



Sunci abincin sosai sunata zuba santi sauran yace ta ajiye ta dumama masa ya fice saboda ya matsu yaga Abba su zauna ya zayyane masa matsalarsa sannan ga shauqin son ganin Safnansa.
Yana shiga gdan ita ya gani tanata wasanta a saman lilo a harabar gdan ya qarasa inda take ta dago ta kallesa ita a zatonta Mahfuz ne ta rungumeshi tana dariya shima dariyar yayi yanata juyawa da ita yana cillata yana cafewa.
A haka Abba ya fito ya tarar dasu ya tsaya yanata kallonsa yanda ya ke wasa da yar tasa soyayyarsa da yarinyar dabance dama ashe gaskene irin wadannan yaran shiga raine garesu, duba da yanda shima yakejin yarinyar a cikin ransa.




Matsawa yayi suka gaisa yace “ta riqeka ko sarkin surutu ba baki sai gwaranci" murmushi yayi yace “ai bakin ya kusa idan tayi qani zata ware ne" shiga sukayi ciki sun jima suna tattaunawa sosai yasha fada yake cewa “akanme zakuyi Shiru da matsala banda shirmenku"
Qasa yayi da kansa yace “wlh Abba My life ce ta hanani fada wai kunya takeji" haushi ya cika Abba yace “shine kuma kai dake juyin mace ne ka biye mata ko?" Wayarsa ya dauka yace dare yayi yanzu amma gobe ka fito da wuri sai muje Billire gurin Mal Zaa dace insha Allahu" da wannan suka fita ko Addah basu gaisaba tana sama tanata girki.
Da yarsa ya tafi Habeey ta gama aikinta ta haye sama ta kwanta ta rinqa jiyo hayaniyarsa a parlour bata fito ba har ya gama abinda zaiyi ya hauro saman ya taddata a kwance ta miqe da sauri tana murmushi tace “Safnah ta" karbarta tayi da sauri ta rungumeta tace “inata kewarki ke bakiyi tamu ba ko?" Daga Kai yarinyar tayi suka kalli juna sukayi dariya yace “dama ai abinda akaso kenan kada ki shaqu damu to kinzo kenan yarinya"




Sosai suka shagala da yiwa yarsu wasa sai dare yayi mata wanka suka kwanta bacci.
Washegari da asuba ya tashi yayi wanka ya fice itama tayi sallah suka koma suka kwanta goma ta gama komai sukayi wanka suka karya tanason zuwa ta gano jikin Mom amma data kirashi wayarsa busy dole ta hqr ta zauna da yarta wajen qarfe tara na dare ya shigo baije inda take ba Saida ya shiga dakinsa yayi wanka ya canza kaya yayi duk abinda Mal Kakan Habeey ya bashi tun a Billire ya farajin sauyi a jikinsa ya shiga dakin Habeey suna kwance itada Safnah ya janye Safnan a hankali ya kwantar da ita a gefe ya shige jikin matarsa yanajin wani yanayi daya dade baiji a jikinsa ba,
Yanda taji yana shafeta dinne yasata saurin bude idonta ta saukeshi akansa ya daga mata gira tana binsa da kallo shi Kuma yana lasheta tuni ya mantar da ita komai suka lula duniyar da suka dade basu shigaba ranar sun gurzu sun qwaquli juna kamar ba gobe ta dandana Habeey saboda ta dade bataji mazan ba.
Qarfe biyu daidai wayarsa ta buga ya dauka ya kashe batare daya duba me kiranba, sake shigowar kiran ne yasashi dagata ya dauki wayar tare da janye jikinsa daga na Habeey ya kara a kunnensa Kubrah ce cikin kuka tace “ta mutu Yaya Mom ta mutu tana kiran sunan matarka kaqi barinta tazo su gana"
# *UMMUH HAIRAN*
[8/14, 7:22 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *27* Miqewa yayi a sanyaye yace “da gaske ta mutu? Innanillahi wa Innah ilaihirraji'un" itama tashi tayi tace “waye ya rasu Life?" Kamota yayi ya rungumeta ya fashe da kuka yace “mom Habeey Mom dinace ta rasu"
Kuka ta fashe dashi jikinta na rawa tace “ya Allah Allah ya jiqan Mom wayyoh Allah Taheer shikenan Mom ta tafi ta barmu" hakanan suka qarasa kwanan nan da asussuba suka dunguma suka tafi gidan government suna shiga suka tarar da gdan a cike da yan'uwa Kubrah ce ta kama hannunta suka shiga dakin da Mom take kwance.




Suna shiga ta matsa da sauri ta bude fuskar Mom ta fada jikinta ta fashe da kuka abubuwa da dama suka rinqa dawo mata tace “Allah ya jiqanki Mom Allah ya gafarta miki" shigowar su Dad ne yasa Taheer ya janyeta daga jikin Mom din suka dauketa suka sanyata a makara aka fito da ita suka fice da ita zuwa harabar gdan akayi mata sallah aka fice da ita gabadaya,
Haka suka yini a gidan suna karbar gaisuwa itadai sulalewa tayi ta tafi bangaren Saudat yau sai taga jikin da sauqi tana zaune ita da me kula da ita sai Abba da Addah sunata yimata sannu Adda na shafa mata magani.
Sannu tayi mata ta zauna sukaci gaba da kula da ita har bayan magrib da Taheer yasa aka kirata yace tazo su tafi, kallonsa tayi a mamakance tace “na dauka anan zamu kwana?"




Girgiza mata kai yayi yace “ba haka na tsara ba kizo kawai mu tafi" bazata iya yi masa musu ba amma qwarai bataji dadi ba Addah ce tace “to dama zaman me zakiyi kema da ba cikakkiyar lfy ba shi mamaci ai addu'a kawai yake buqata" da wadannan kalaman suka tafi har sukaje gda bata kulashi ba, suna isa ta bude motar ta fita shima ya shigo.
A sama ya tarar da ita ta cire kayanta zata shiga wanka zama yayi a gefen gadon yana kallonta har ta wucceshi taje tayi wanka ta fito ta fara shafa mai ya miqe ya zagaya ta bayanta tare da tallafo qugunta ya kwantar da kansa a kafadarta hawaye nabin kuncinsa,
A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta shafo kansa ya qara shigewa jikinta yace “kiyi hqr don Allah ki yafewa Mom ko ta samu salama cikin kabarinta Habeey duk wani hali da rayuwarki ta shiga Mom tanada hanu a ciki ta roqi Bushirah ta roqeki ki yafe mata ita Kuma tace kunyarki takeji...."




Hannunta ta dora saman bakinsa tana hawaye tana girgiza masa kai tace “ka...kadaina roqona don Allah wlh ni na yafe mata tun kafin wannan lkcn Mom uwatace kamar Addah bazan taba barinta da nauyin haqqina akanta ba Taheer ba itaba kowa ma daya cutar da rayuwata ta baya na yafe masa banda mutum daya..."
Dago kanta yayi da sauri yace “waye?" Jan zuciya tayi tace “pappa Taheer shine mutumin da bazan taba yafe masa ba ya cutar dani fiye da kowa ya rabani da gatana ya zama silar lalacewar rayuwata ya cutar da mahaifiyata ya nakasta mata farin cikinta, ta Yaya zan yafe masa?"




Numfashi ya sauke yajata suka zauna yace “watanmu biyu a U.S.A Abba yace ya makashi qara kotu akan abubuwan da suka faru lkcn da aka kai masa sammacin kotu sai ya gudu yaje wani guri ya kama haya dama ya rabu da matarsa sabida babu kudi kece me turo masa da kudi ke kuma kin dawo shiyasa Deborah ta gudu ta yasheshi tsaf, ranar da sukaji lbrn inda yake akaje domin a kamashi sai ya haura katanga domin ya gudu bai sani ba ashe bayan gdan tsohuwar rijiyar kankare ce kawai saiya zunduma ciki aikuwa filla fillah aka fito dashi daga rijiyar rai yayi halinsa"
Numfashi ta sauke tace “to Ina su Ibrahim da akace ya debe ya gudu dasu?" Murmushi yayi yace “Ibrahim yana A.B.U Zaria Idris Kuma yace Solder yakeson zama yanacan makaranta sojoji Fatima kuwa ta dawo harma ansa bikinta da Dr Shattima, ita kuwa Aisha tayi aure a Saudia"



Daga hannu tayi tace “Alhmdllh naji dadin wannan lbr my life saura Hajiyan data kaini Saudia " dariya yayi Mata yace “wato fansa kikeso akan kowa to hukumar yaqi da safarar mutane ta kamata ita kuwa qawarki Aysher Jabir ne ya aureta suna Dubai amma gobe zasuzo magajiyarku kuwa tananan qanjamau ta nakasata tana faman bara tsakanin wannan rumfa da wannan, saiwa Kuma?"
Murmushi tayi tace “saura kai daka rabani da Abu mafi daraja a gurin kowacce ya mac...." Rungumota yayi yana shafa cikinta yace “nima na haifi ya daya babu aure wacce kullum tunanin makomar rayuwarta yake damun zuciyata" daga haka bai qara bata damar mgn ba yaci gaba da romance dinta saida suka samu nutsuwa sannan sukayi wanka sukayi Isha suka kwanta.




Washe gari da wuri suka tafi gdan karbar gaisuwar hakadai Taheer ya sanya Habeey yawo a hanya kowa kowa yakeyi har akayi bakwai amma shi jarabarsa ta hana yabarta ta huta ga girman ciki daqyar take takawa,
Shima Mahfuz ya dawo da amaryarsa yar izza da dagawar tsiya kowa kallon banza takeyi masa a gdan harshi bai tsira daga rashin mutuncinta ba, cikin lkcn nan Saudat sauqi yanata samuwa abinka da aikin sihiri ana dacewa da magani shikenan qurajen suka rinqa salubewa asalin fatarta tana fitowa abin mamaki cikin sati dayan nan kwata² babu alamar qurajen sai saba da fatarta taketayi ko tabo babu, nanfah hankalin Mahfuz ya koma kanta babu kunya yaje yana bata hqr waishi wlh bayin kansa bane baisan sanda ya auri Raliya ba baisan sanda ya tsallake yabar Saudat ba.




Ana bincikawa akaga ashe kuwa asirin da akayine idan Habeey ta kamu da ciwon Taheer ya gudu ya barta yayi aure ya fada kan Mahfuz, sannan itama Raliya da asirin ta aureshi aikuwa ranar bakwai din da daddare bayan kowa ya watse zatayi masa hauka ya nada Mata dukan da yaja mata barin cikinta dan watanni uku sannan ya rattaba mata saki uku.
Sosai su Dad sukayi masa fada shikuwa yace aikin gama ya gama saboda haka taje da abinda ta satar masa.
Satinsu biyar da dawowa Saudat ta murmure sosai tace “itafa bazata koma gdan Mahfuz ba qarshe ma ta gudo gdan Habeey ta buya shikuwa Taheer da taya bera bari shine me qara boyeta wai bazata koma gurin butulu irin Mahfuz ba.
Shikuwa kullum yana hanyar gdan nasu har kuka yasha yiwa Habeey yana Mata magiyar ta bawa qanwarta hqr ta dawo rayuwarsa wlh baisan yana sonta ba saida ya auri Raliya, sosai Habeey ta rinqa yi mata fada itakuma sai tasa Mata kuka tace “Aunty a tarihin soyayya bantaba ganin halaccin qauna irin taking da Yaya Taheer ba a halin Suma ma da bazaki masa amfanin komai ba ya zauna dake ya yarda zai rayu dake amma mutumin nan irin cin mutuncin da yayimin akan abinda bani na dorawa kaina ba idan kikaji sai kin zubar da hawaye Kuma yanzu saboda lfyta yakeso ya wani dawo yace na koma gdansa, hmmm wlh aunty ko su Abba basu raba aurena dashi ba saina kaishi qara ya sakeni"




Ana haka Bushirah ta haihu a wannan jigilar haihuwar ne Allah yabawa Mahfuz saa ya sace Saudat ya gudu da ita ya boyeta a gdansa neman duniya yace shima bai sani ba sai daga baya yace shine ya dauke matarsa.
Bayan haihuwar Bushirah da sati hudu Habeey suna kwance a daki da dare ciwon baya ya tasheta aikuwa ta tashi Taheer da sauri yana ganin halin da take ciki ya dauketa sai asibiti.
Wasa farin girki tun yana boyewa har ya fito ya fadawa su Addah aikuwa tun daren saigasu, Habeey dai bata haihu ba sai safiya ta haifo yaranta uku kyawawa maza biyu mace daya.
Wayyoh murna gurin Taheer kamar anyi masa busharar aljannah har kusan susucewa yayi da anzo barka zai tareka yace “uku...uku Habbatullah ta haifamin"
Aikuwa yan uwa da abokan wasa suka samu abin tsokana da sun ganshi zasuce “uku Habbatullah ta haifamin" saidai yayi dariya kawai.
Ranar suna yara sukaci sunan kakanninsu Aliyu da Salahuddeen macen taci sunan Granny wato Khadijatul Kubrah, akasha shagalin suna hatta gdajen TV da jaridu ranar zancen da akeyi kenan Matar dan governor Aliyu Waziri sannan matar shugaban rukunin kamfanonin T.H Fabrics and Counseling Kuma ya a gurin shugaban likitocin qasar 9ja ta haifi yara uku.
Yaran da iyayensu sunsha addu'a sosai, itama Aunty Zahrah taga rayuwa tayi ladab saboda babu jigogin nata Mom da Hajiya Ummah ga Kuma shagidewa da tayi saboda karairayewar da tayi.



Haka rayuwa taci gaba da tafiya duk jarabar Taheer saida ya qyale Habeey ta koma gda na kwanaki arba'in aikuwa Abba yanashan zarya don a rana sai yaje gurin yaransa da matarsa sau uku sau hudu hakadai daqyar aka rurruma tayi arba'in din, a nufin Addah sai yaran sun qara qwari wata biyu ta mayar da Habeey.
Ai yanajin haka ya saka musu daru dan iskanci harda cewa shi tsoron gdan yakeji shi kadai, babu arziki suka bashi matarsa da yayansa tare da Mai rainonsu suka tafi Safnah ce kawai ta zauna a gdan saboda tafi sabawa da kakanninta.
Wannan dare an kashe arna iyakar arna duk wata tsumammiyar sha'awarsa ta kwanaki arba'in dinnan saida ya sauketa saboda Tasha qyara baga iyayen ba baga kakarsu ba baga qannen mijin nata ba hattada Yadikko Laure Amaryar Dad Kuma Yaya a gurin Addah uwa daya uba daya da mijinta ya rasu kasancewar bata taba haihuwaba Dad ya aurota itama gyara matar dan nata take Kuma yarta, aikuwa watan yan uku hudu saiga wani cikin itadai Habeey bataso ba amma Taheer murna kamar baa tabayi masa haihuwa ba wata tara ta haifi danta namiji ranar sunan Muhammad ranar Saudat itakuma ta haihu yarta mace kwana uku tsakani Kubrah ta haifi Namiji habawa aikuwa anyi shagali sosai a wannan Fam din zumunci ya qullu zaman lfy ya dore kamar baa taba samun sabani ba,
Alh Taheer da manyan Mata Habeey an zama manyan mutane rayuwa sai yanda sukaso sukeyinta Habeey anata karatu haihuwa ta tsaya ko nace sun tsayar yau gata harda Masters a bangaren Business administration lkcn data gama ta fantsama kasuwanci da manyan nairori aikuwa ana ganin albarka.




_Tammat bi hamdullah_



_Nan wannan lbr yazo qarshe me taken *DUBAI* kuskuren dake ciki Allah ya yafe mana baki daya, sai mun sake haduwa a sabon lbrnmu me taken *NAJMAH* Wanda zai fara zuwar muku *20/8/2020*_
# *UMMUH HAIRAN*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment