Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qarfi yayi abinda zaiyi bayan ya gama yayita yimata dariya yana cewa ai tama fisa jin dadi kawai don dai shi aka dorawa jarabar ne.
Cikin wannan kwanaki na farkon zuwansu abubuwa da dama sun faru abun da takasa mantawa shine kyautar wata siririyar sarqa da barimarta da Chan's din hannu dana qafa sai zobe da yayi mata na white gold and diamond da kudinsu a qimance suka haura lissafin da qwanyata zata iya yace mata.




Tun washegarin ranar da tayi masa kyautar budurcin ta ya bayar da aikin qera masa su da qudurin duk ranar da suka kwana suka tashi cikin yanci matsayin ma'aurata zai batasu a matsayin tukuicin qauna,
Ranar tayi kuka sosai itakam batasan irin qaunar da dan'uwanta Kuma mijin nata yakeyi Mata ba,
Abu na biyu shine mugayen mafarkan da takeyi da Mom da Aunty Zahrah kullum sunayi mata gargadi akan kada ta kuskura ta dauki Taheer a matsayin abokin zama na dindindin saboda talala sukayi mata me kamar sake.
Wannan abu yana damunta musamman lkcn da ta fara mugayen mafarkan wai Taheer ya kamata ya nada mata duka ya saketa saki uku ko kuma tayi mafarkin ya biyota da bindiga ko wuqa zai kasheta.
A kowanne lkc takan tashi tayi alwala tayi sallah tare da tubarwa Allah da neman daukinsa wajen galaba akan maqiyanta.




Duk sanda sukayi waya da yar'uwarta Saudat takance mata Aunty Habbatullah ki rinqa kusanta kanki da ubangiji akwai maqiya gabanki da bayanki don Allah kada kiyi wasa da addininki nasan Allah zai iya miki Ina tsoron lamarin Hajiya Ummah Mom da Aunty Zahrah bansan me kika tsare musu ba da suka sakoki a gaba basa iya boye qiyayyarki sai a gurin mazajensu.
Takance “karki damu qanwata wata qiyayyar batada dalili hakanan Allah yake kimsawa bawa ita a cikin zuciyarsa kedai ki tayani da addu'a kawai"
A haka har sukayi watanni uku a U.S.A, a wannan lkcn ne Kuma abubuwa suka fara canzawa tsakaninta da mijinta babu kyara babu habaici saidai kawai idan taganshi taji gabanta yana faduwa takan danni zuciyarta da addu'o'i sannan ta tareshi suci gaba da rayuwarsu, to shima a bangarensa mugayen mafarkai ne suka aureshi ga wani mugun zargin Habeey da yakeyi a zuciyarsa hakan da ya fita sai zuciya ta rinqa raya masa gatacan tare da wani namijin a gdansa.




Babu shiri zai dawo ya gama dube dubensa bazaiga kowa ba lamarin da yake sanyashi shiga tashin hankali shidai yasan ko lkcn da suke zaman dadiro baya zarginta to meye yasa a yan kwanakin nan zuciyarsa takeqin nutsuwa da itane?
Tambayar da yakeyiwa kansa kenan amma bayada me amsa masa saboda haka ya barwa zuciyarsa yaci gaba da addu'a kawai,
A wannan taqinne kuma ta rinqa rashin lfy ciwon bazai tashi ba sai dare ta kwana tana sheqa amai da safe Kuma saita warware suna zuwa asibiti ana aunata akace shigar ciki gareta.
Wayyoh zo kuga murna gurin Taheer kamar ya hadiyeta haka yakeji itama tayi murna saboda kadaici yana damunta ga qulafucin yarta Safnah data sanya a ranta to shima gogan hakane don ko qofar gdansu ya fita saiya shigo da tsaraba yace ta Safnah ce.




A ranar da suka dawo gda zazzabinta ya tsananta ga faduwar gaba data aureta cikin kwanakin nan ko qofa aka taba sai gabanta ya fadi, dakewa kawai takeyi saboda kada abin yayi masa yawa.
Da dare tanajinsa wayarsa tayi ring tana rungume a jikinsa ya daga suka gaisa da Dad yake cewa dashi “eh wlh dazu mukayi waya da Abba nake fada masa mun samu qaruwa My life cikine da ita amma tanashan wahala yanzu haka kaganta a jikina zazzabi ya hana mata sakat"
Murmushi Dad yayi yace “zataji sauqi dama qaramin ciki sai a hankali ai" hakanan sukayi sallama ya aje wayar baiyi minti goma da ajiye wayar ba ya fara lalubarta a cewarsa idan ya jijjigata zataji sauqi,
Wayar ta qarayin ring ya janyo ganin number Mom yayi kamar bazai dagaba Habeey tace “Allah My life ring dinnan fadarmin da gaba yakeyi ka daga"




Karawa yayi a kunnensa kawai sai jinta yayi tana huci tace “wato harma dama ka samu kayiwa wannan shegiyar yarinyar ciki ko aikuwa baka isaba ni nama gaji da zamanta a qasar nan tana qara nisantani dakai kayi gaggawar hadota da kayanta ta dawo gda tayi rainon cikin anan"
Ajiyar zuciya yayi yace “bansan meye yasa kikasa mana ido ba Mom kodai kina daya daga cikin matan da suke kishi da matan yayansu ne haba don Allah Habeey fa zabina ce kuma yar'uwata ce kodon zumunci yakamata ki sassauta mana mu samu salama a rayuwarmu"
Yana farin haka ya kashe wayar yaci gaba da abinda yakeyi itama tana tayashi saida suka gamsar da junansu sannan sukayi wanka suka kwanta.
Me zai faru? Cikin dare yaji Habeey tana buge buge tana kiran sunansa ya zabura ya miqe ya dagota jikinsa yana Kiran sunanta amma Shiru sai surutai da takeyi daya kasa gane me take cewa jikinta yana qara daukar zafi tana rirriqe cikinta,
Hankalinsa yayi masifar tashi ya sake matseta a jikinsa yanata yi mata addu'a, kusan awa guda sannan ya samu bacci ya dauketa yayi ajiyar zuciya ya miqe ya dauro alwala ya tada sallar asabu da lkcn ya riga ya shiga itakam sai safiya ta tashi yanata yimata sannu yana binta da kallo tare da tambayarta inane yake mata ciwo,



Kallonsa takeyi da alamun rashin fahimta tace “meye ya hana ka tasheni nayi sallah akan lkc?" Murmushi yayi yace “bakida lfy ne shiyasa"
Dirowa tayi daga gadon tace “tunda ka riga ka hadani da aiki lfy kam ai sai Allah ya rabamu tukunna nidai kada ka qara barina nayita bacci har lkcn sallah ya wucce don Allah" mamaki ne ya hanashi cewa komai saboda ya lura batamasan meye ya faru da ita jiyan ba so shima bai bawa abin muhimmanci ba ya shiga kitchen ya hado musu abin karyawa ita Kuma tayi wanka tayi sallah ta shirya cikin wani yadi mara nauyi dinkin riga da siket ta fito parlourn yana zaune a dinning yana jiranta kamar yanda suka saba ya miqe suka rungume juna tare da tsotsar bakin junansu yace “kin wahalar min da baby jiya da dare fatan kinji sauqi dai Kuma bazaa Kuma ba?" Murguda masa dan qaramin bakinta tayi tace “idan kabani hutun sex ba" dariya yayi yace “tabdi aikuwa kina ruwa"



Zama sukayi suka fara breakfast cike da nishadi idan ya kalleta wani dadi yakeji inda ita kuma gabanta yaketa faduwa,
Matsowa yayi jikinta yace “bansan me kika sanya a ranki haka ba cikin wata daya zuwa biyu sai ramewa kikeyi My life don Allah ki cire ko menene muyita addu'a kinji"
Dago kanta tayi idonta ya ciko da ruwa tace “ciwon faduwar gaba ya sarqeni sama da wata guda shi kadai lalata farin cikin mutum yakeyi balleni da dama ba lfy na cika ba Kai shaidaine akan hakan sannan kuma kullum cikin tararrabi da tunanin yaushe mafarkaina zasu fara tabbata nake duk da ina addu'a amma inajin kamar zasuyi nasarar rabani dakai Taheer..."
A razane yace “su waye!" Yanda yayi mgnr da qaraji yasata firgita tace “A baya fuskar mutum uku nake gani amma yanzu basu nake gani ba fuskar Pappa nake gani kullum yana firgitani tare da cemin saiya cusa maka tsanata saika tsaneni fiye da yanda ka tsani mutuwarka Taheer idan hakan ta qara faruwa dani ya zanyi a baya ni kadai ka tsana amma yanzu bansan mu nawa zaka tsana b...."
Rufe mata baki yayi yace “to Kuma wanne Pappan bayan Pappa ya mutu anya Habeey bakida aljanu kuwa?"
Kuka ta sake rushewa dashi tace “kaima abinda Addah tace shi ka maimaita Taheer ni kadai nasan abinda nakeji a jikina wani lkcn ji zanyi kamar tsutsa tanayimin yawo a cikin jikina na rasa meye matsalata anya Taheer ba mutuwa zanyi ba...."
# *UMMUH HAIRAN*
[8/11, 10:41 AM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *_HABEEYTAH_*
*_DUBAI PART 2_*



_Littafina na kudine ki biya kafin ki karanta bazance Allah ya isa ba amma nasan zai isarmin tunda shi isasshene just 200 VIP 600 ta account number 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko kati MTN ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment dinki  ta wannan number dake sama Idan VTU ne ta wannan layin Zaki tura dari biyunki ko dari 600 ki/ka 09013307566 idan fah kika tura a wancan layin na sama to ki qaddara sadaka kika bani shi evidence of payment kawai zaa tura._


_A mafi yawan lokuta gaɓɓai kan yi aiki tamkar wasu makamai, sai dai basu da ƙumajin faɗa da alƙalamin ƙaddara. Ba duka sauyi ne yake zama me daɗi ba , sai dai kuma yakan iya zama maƙasudin samar da wani giɓi da cikuwar ramukansa ke da matuƙar wahala wajen jinyatuwa, idan sauyin ya kasance matsayin gyara to ku daukeshi alkhairin da yake tunkarar rayuwar abinda kuka rajaa akansa_


*24* Kamota yayi ya mannata da qirjinsa yana shafa kanta saida yaji ta nutsu sosai sannan yayi kissing nata yace “zanje na dawo ki kulamin da kanki da babyna idan na dawo zamuje asibiti wanna ramar taki tana damuna.
Jinjina masa kai tayi ya fice ita Kuma ta miqe a gajiye ta gyara musu dakin ta koma ta kwanta baccin da batayi ba jiya shi tayi bata farka ba saida ya dawo taji yana shafa fuskarta, bude idonta tayi cikin kasala tace “My life Ina baccina me dadi ka tasheni"
Zama yayi kusa da ita ya dafa cikinta yace “kina jin abinda nakeji kuwa Life?" Kallonsa tayi da sauri tare da miqewa tace “me kakeji?" Lumshe idonsa yayi ya kamota ya kwantar da ita a jikinta ya dora habarsa a bayanta kawai saijin saukar hawayensa tayi a tsakiyar bayanta.
Dagowa tayi da sauri tasa hannunta ta tallafo fuskarsa ta sanya harshenta tana lashe hawayen nasa tace “kada matsalata ta dameka My life komai yayi farko yana da qarshe nafi buqatar farin cikinka fiye da nawa"




Rungumeta yayi ya fashe da kuka yana cewa “banida zargi a baya Habeeytah amma yanzu zuciyata tana neman jefani a hallaka wlh idan na fita daga gda hankalina baya kwanciya kawai sai na zuciyata take saqamin gakican kina mu'amala da wani....
A gigice ta rufe masa bakinsa tare da fadin “ a'uzubillahi minasshaidanur rajim! Please kada ka qara don Allah wlh bantaba jin haka araina ba bantaba zarginka ba mijina na yarda dakai fiye da yanda na yarda da kaina nasan bazaka taba cutar dani ba"
Sake shigar da ita jikinsa yayi yace “naji hakan a jikina nima qasan zuciyata yana fadamin hakan nasan bazaki taba cin amanata ba Amma na rasa meye yasa da zarar nasa qafa na fita nakejin hakan wlh Ina fita daga corner din line dinnan abin yake saukomin"
Murmushi tayi domin ta kwantar masa da hankali taci gaba da shafa qirjinsa tace “da zarar kaji hakan ka rinqa a'uziyyah shaidan ne yakeson wasa da imaninka akaina My life Habibatullah takace har abada"




Da wannan kalaman ta samu ta rinqa rarrashinsa har ya saki ransa sukaci gaba da harkokinsu tare sukayi girki suka gyara gidan ya dauketa sukaje asibiti aka dauki hoton qirjinta babu wata matsala aka bata magunguna suka fito.
Ba gida sukayi ba wani wajen shaqatawa sukaje suka zauna suna kallon yanda turawan suketa kaiwa da komowa sunata wasanninsu na soyayya, Basu sukabar gurin ba sai dare suka tafi gdansu suna zuwa yace Mata.
“Nifa yau marata ciwo takeyi tun safe" sannu tayi masa ta wucce daki tayi wanka tana shiryawa ya biyota ya tsaya a bayanta yana wasa da gashinta yace “shine kikayi wankan kika qyale mijinki ko?" Girgiza masa kai tayi tace “ka wahalar dani yau babynka yanason hutu shiyasa"



Bathroom din ya nufa yace “ok amma ai yasan babansa jarumi ne" itadai batace masa komai ba taci gaba da shirinta, bayan ta gama ta fito parlourn ta zauna shima daya gama yazo yayi matashin kai da cinyarta yana wasa da boobs dinta dake cikin riga har yakai ga fito dasu ya rinqa wasa da nipples dinta tasan idan ta hanashi ma tsokanowa kanta zatayi shiyasa ta shareshi.
Wasa yake sosai da ita tun tana jurewa har ta fara gajiya ta soma tayashi nan suka shagala wajen wasanninsu sunfi awa daya sunayi abinda ya bawa Habeey dashi kansa Taheer din mamaki shine yanda taketa wasa da dick dinsa amma bata tashi ba mamakin ne yasasu kowa ya tashi zaune.
Kallonta yakeyi itama tana kallonsa ta sake kamawa ganin yanda take a kwance hankalinta kwance tace “My life meye hakan?" Gumin daya karyo masa ya share yace “nima abinda nake tambayar kaina kenan meye hakan?"





Iska Habeey ta furzar ta kwantar da kanta a saman qirjinsa gabanta yanaci gaba da faduwa tsoronta na qaruwa tana fadin “Ya Allah" lumshe idonta tayi tana tuno mafarkinta watanni uku da suka wucce a irin wannan yanayin da suke yanzu.
A hankali tace “Allah kasa bacci nakeyi irin mafarkin dana sabayi ne..." Dagota yayi yace “wanne mafarki?" Batasan a fili tayi mgnr ba ganin yanda idonsa ya kada yayi jawur yasata tsorata tasan komai zai iya faruwa indai ya shiga irin wannan yanayin.
Miqewa tayi da sauri ta juya ta shige dakinsu ta fada gado ta rushe da kuka tana toshe bakinta to shima cikin tashin hankali yake saboda haka ya kasa miqewa yabi bayanta yaja pillow din Soorper din kawai ya kishingide zuciyarsa nakai kawo so yake ya tuna wani Abu da yayi Wanda zai iya sashi cikin wannan matsalar amma ya kasa.





Wannan rana cikinsu babu Wanda ya rintsa itadai kalaman Abbanta lkcn da zai miqata hannun mijinta ne suka sanyata miqewa ta dauro alwala tayi salla raka'a hudu tana kuka tana fadawa Allah ya kawo musu qarshen wannan lamari da suka kasa gane ta Ina yake tunkarosu,
A mafarkinta na shekaran jiya taga an shafi al'aurar mijinta to amma waye? Ko giyar wake tasha bazata taba kawowa uwa zata nakasa dantaba saboda mace girgiza kanta tayi tare da fadin "astagfurullah" saboda batason ta dora rayuwarta akan zato kasancewarsa shima zunubi ne me girma maganar Abbanta tana mata yawo a kwanyarta “kada ki dorawa kowa laifin gindayowar wata kawalwainiyar qaddara cikin rayuwar aurenku babu wanda ya Isa ya cutar da wani bawa saida sahalewar ubangiji kuma koda zakiji ance wane yayiwa wane abu kaza yayi tasiri tofa bashine yayi ba shidai sanadi ne Amma asalin abun daga Allah ne"




Rungume qur'anin dake hannunta tayi tana kuka me ban tausayi tana furta “Mijina ya Allah mijina! Hmmm Uhmmm!! Allah kabarni da mijina Allah kada kabawa wani bawanka abin halitta ikon cutarmin dashi Allah kasa kowacce jarabawa ta tsaya iyakar ni inada tabbacin tunda baiqini a baya ba babu tsananin da zaisa yaqini a gaba...."
Ji tayi ya dagota cak ya hade bakinsa da nata cikin wani irin yanayi na tsananin qaunarta da tausayinta ya janye bakinsa daga nata yace “ki daina kuka Habeeytah komai yayi farko zaiyi qarshe insha Allahu zamu samu mafita gobe zanje asibiti ina tunanin ciwon marar dana yini dashi shine yaja mana wannan matsalar"
Dago idonta tayi dayake cike da hawaye tace “badon ni ba saidon don ita lfyr kowacce gaba alfahari ce wa dan adam Ya Taheer koda ace haka zamuci gaba da zama na yarda Kuma na amince zan rayu dakai rayuwa me tsafta rayuwar farin ciki rayuwar da tafi wacce mukayi a baya ingancin"
# *UMMUH HAIRAN*
[8/12, 9:52 AM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *_HABEEYTAH_*
*_DUBAI PART 2_*



_Littafina na kudine ki biya kafin ki karanta bazance Allah ya isa ba amma nasan zai isarmin tunda shi isasshene just 200 VIP 600 ta account number 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko kati MTN ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment dinki  ta wannan number dake sama Idan VTU ne ta wannan layin Zaki tura dari biyunki ko dari 600 ki/ka 09013307566 idan fah kika tura a wancan layin na sama to ki qaddara sadaka kika bani shi evidence of payment kawai zaa tura_



*25* Sake matseta yayi a jikinsa yana sunsunar wuyanta ya dorata a gado ya zauna a gefenta yana shafa cikinta tare da kwantowa jikinta da haka har bacci ya dauketa shima ya kwanta.
Washegari da safe ko karyawa bai tsaya yayi ba ya nufi asibiti iyakar binkicensu sunce qalau yake babu wata matsala a tare dashi, hakanan ya dawo gda a kasalance wanna rana sunga ikon Allah shi naci dole sai yayi sex abu Kuma yace baisan zance ba.
Days gaji saiya kwanta kawai zuciyarsa nayi masa zafi tunda yake bai taba shiga tashin hankali irin na yau ba ita kuma sai rarrashinsa takeyi tana fada masa yayi hqr zai samu sauqi.




Wasa wasa abu sai qara gaba yakeyi itadai Habeey bata wani daga hankalinta ba tanayi masa addu'a kullum sannan taqi barinsa ya fadawa kowa tace suyi addu'a kawai, suna addu'a yana zagaya duk wani asibiti amma babu wani sauqi sai kamar qara gabama da abin yakeyi.
Lkc sai qara turawa yakeyi lamura suna qara tsamari tsakanin ma'auratan musamman Taheer da yabi ya tsangwami kansa ya hana kansa sukuni kullum cikin damuwa yake.
Mafi yawan lokuta zuwa zatayi ta tarar dashi a dakinsa ya hade kai da gwiwa yana kuka hakanan zata zauna tayita rarrashinsa idan yaqi yin shiru itama saita sanya masa kuka dole ganin tanayi shidin ya haqura yayi shiru.





Watanninsu takwas lkcn cikinta yanada watanni biyar, a ranar da ya gama abinda yakeyi yace ta fara package na kayanta jibi zasu tafi cikin murna tace “wlh dama duk na gaji My life" kallonta kawai yayi ya girgiza kai ya fice.
Jikinta ne yayi sanyi ta dafe qirji a ranta tace “yanzu fah sai yayi tunanin da wata manufa nayi maganar nan ko?" Ilai kuwa yana dawowa taga idanunsa ya kada yayi jajir ya kalleta yace “kin gaji da zama dani saboda bani da amfani a gurinki ko Habeeytah?"
Idonta ne ya kawo ruwa ta matsa gabansa ta ruqo hannunsa yayi saurin janyewa tare da komawa jikin bango ya dora kansa a bangon yace “nasan ba kowacce mace takeda qarfin imanin zama da namijin da yake da matsala irin tawa ba"




Juyowa yayi suna fuskantar juna tana girgiza masa kai ya matso gabanta yace “hakanma kinyi qoqari Habeeytah ko iya haka kika barni kinyimin halacci ki fadi duk abinda kikeso kafin muje zanyi miki shi Koda kuwa Zaki zabi rabuwa danine...."
Dagowa tayi da sauri ta fada qirjinsa ta rushe da kuka tace “meye yasane Taheer me yasa kullum kake dangantani da abinda bantaba dangantaka dashi ba meye yasa kakemin kallon butulu Taheer meye yasa ka kasa gane matsayinka a gurina? Kullum nayi magana saika fassarata da wani abu daban, ta yaya Taheer tayaya zan zabi nesanta kaina dakai, aa ka dainamin haka don Allah kana saremin qwarin gwiwata ne please kada ka kuma inasonka a duk inda kake zan rayu dakai ko bakada wani abin amfanawa rayuwata...."





Ajiyar zuciya ya sauke me qarfi ya dora bakinsa saman kuncinta yana lasar hawayenta nasa suna zubowa yace “inaji kamar Ina cutar dake Habeey inajin kamar Ina zalumtarki ne kunyata da soyayyarki gareni tasa kin kasa gane hakan wlh Habeey banajin ruhina zaici gaba da zaga gangar jikina matsawar baki tare dani"
Sake narkewa tayi a jikinsa tace “ni takace har abada My life" da wannan suka mantar da junansu damuwarsu suka shiga bathroom sukayi wanka sukazo suka shirya suka fita wani shopping mall sukaje duk wata siyayyarsu ta Safnah ce da babyn dake cikin Habeey itakam kallonsa kawai takeyi.
Koda suka gama suka juya gida sunata shagalinsu a parlourn yanata qissima mata irin dadin da zaiji idan yaga Safnansa, wayarsa ce tayi ring ya dauka yana murmushi ya kara a kunnensa yace “hello Dad..." Zabura yayi ya miqe yace “what innanillahi wa innah ilaihirraji'un yaushe?" Jifa yayi da wayar ya zube a gurin jikinsa na rawa.




Nufoshi tayi da sauri ta zauna a gabansa da rawar murya tace “waye ya mut..." Dago kananun idanunsa yayi da suka canza launi yace “Mom ce tayi accident ta hadu da matsalar spinal cord"
Dafe kanta tayi tana fadin “innanillahi wa innah ilaihirraji'un garin yaya" share hawayensa yayi yace “bansani ba nima" Shiru ce ta ratsa babu abinda kakeji sai shassheqar kukan Habeey kawai akeji dagota yayi yace “meye kikeyiwa kuka?" Cikin kuka tace “ina tuna halin da mutum yake kasancewa idan ya rasa gabar da zatayi motsi a jikinsa"
Kwantar da ita yayi yana murmushi yace “karki damu kowanne bawa baya wucce qaddararsa gobe zamu tafi Dad yace akwai jirgin da zai tashi da kayansa gobe sai mu bisa" jinjina kai tayi suka tashi suka shiga daki suka kwanta kowa da abinda yake saqawa a ransa har bacci ya daukesu.




Tashin asuba jirginsu yayi suka lula 9ja abbanta ne yazo ya taresu tsoro ya kamashi ganin yanda yar tasa ta rame sosai shima Taheer din duk ya zabge sai dogon hanci.
Bai iya tambayarsu ba har sukaje gdan gwomnatin yana riqe da hannunta suka fara ratsa parlourn gabanta sai faduwa yakeyi da Bushirah sukayi kicibis da tsohon cikinta tana ganinta ta saki wani ihu ta rungume Habeey tana cewa.
“Allah dai ya biya yayana sunqi Allah yaso kace mun kusa cika Fam da yara" kunya ce tasa Habeey yin qasa shikuma yayi yaqe yace “ya jikin Mom din?" Tabe baki tayi tace “au Wai dama saboda matarnan ka dauko baiwar Allah ka wahalar mana da baby? Hmmmm tana ciki tana girbar abinda ta shuka"
Kallonta sukayi da rashin fahimta ta nuna masa dakin tace ka shiga ka ganta tana ciki ke kuma zona rakaki bangaren yar'uwarki kiga mugun abinda son zuciyar uwarta yaja Mata Habeey ki godewa Allah dakansa yake baki kariya"
# *UMMUH HAIRAN*
[8/12, 5:22 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *26* Bin bayan Bushirah tayi gabanta na faduwa suka shiga bangaren Saudat din tana kwance saman kujera lullube da wani mayafi suka qarasa, a razane Habeey take kallonta tace “Subhanallahi meye haka" tsugunnawa tayi wani wari da qarni ya daki hancinta zuciyarta ta hautsina ta toshe hancinta da sauri tana duban jikin Saudat da da yake cike da wasu munanan manyan quraje sai zubar da mugunya sukeyi ta zabura ta miqe tace “Innanillahi wa innah ilaihirraji'un meye haka Bushirah meye ya sameta haka me yasa baa kaita asibiti ba?"
Numfashi Bushirah ta sauke cikin kuka tace “Anyi maganin har an gaji watanni takwas kenan take fama da wannan ciwon satinku daya da tafiya su Mom da Aunty Zahrah da Hajja Ummah suka tafi wani qauye a Zuru kwanansu uku sannan suka dawo cikin dare Aunty Zahrah ta tashi ta dora ruwa a saman gas ta dauki barjajjiyar maiwa ta zuba a ciki ta kawo wani ruwan asiri ta zuba taje ta bawa shanu suka shanye ta koma ta kwanta, tsakiyar talatainin dare gefin asuba Saudat ta tashi ta rinqa ihu jikinta yana qaiqayi ana haskawa akaga wasu manyan quraje ne suka feso a jikinta"




Rungume Habeey Bushirah tayi tace “da gari ya waye lbr yajewa Aunty Zahrah ta rinqa ihu tana kururuwa wai ta manta ashe cewa akayi ta kiraki ta tabbatar da darene a U.S.A sannan tayi ita Kuma ta manta tayi amfani da darenmu na 9ja Habeey ke akaso a dorawa wannan mugun ciwon bakiji ba baki gani ba kawai saboda jahilci da zalumci bansan me kika tarewa bayin Allan nan ba"
Hawaye ne ya rinqa sintiri a fuskarta ta sunkuya ta riqe hannun Saudat ta bude idonta a hankali tana kallonta itama wasu hawaye na zuba a idonta ta buda bakinta da yake cike da quraje tace “kin...kinga yanda Allah yayi dani ko Aunty Habbatullah Aunty ta jamin saboda Allah ba azzalumin sarki bane gashi Mahfuz yace bazai iya zama dani Ina wari ba harma ya qara aure sun tsallake sun barni shida matarsa sun tafi yawon cin amarci...."




Kuka sosai Habeey takeyi na tausayin yar uwartata da bataji ba bata ganiba laifin uwarta ya shafeta, Saudat ta qara bude bakinta da yake buga wani uban wari tace “ashe dama Mom da Aunty sune suka mantar da ruhin Abba dake da tunaninki tsayin shekaru saboda kawai basason ki bayyana a matsayin yar Abbanmu ya kwanta ya mutu kici gadon"
Miqewa Habeey tayi tace “Allah ya baki lfy Saudat bari naje naga jikin Mom" fita sukayi zuciyar Habeey a karye sukaci karo da Taheer ya finciki hannunta a fusace yace “muje kawai basai kinje ba"
Taso tambayarsa ba'asi amma yanda taji yana huci yasata jan bakinta tayi shiru suka fita ya kira drive yazo yajasu zuwa gdansu da Addah tasa aka gyara musu suna tafe tana kwance a jikinsa yana share hawaye zuciyarsa na quna ya gama tsinkewa da lamarin Mom dinsa Mom tayi nisa

Please Login or Register in order to submit comment