Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga Nabihat ta dunƙule hannayen ta biyu ta girɓawa sharkar naushi a fuska.
Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da ya yi katantanwa a sama sau uku, sannan ya kife a ƙasa, yana mai tsandara ihu sakamakon zafi da zugin da ya ji, haƙorinshi guda ɗaya ya yi fitar burgu daga cikin bakinshi jini ya yi tsartuwa.
Amma saboda karfin zuciya gami da juriya irin ta manyan GWARAZAN JIYA sai ya miƙe tsaye zumbur yana mai goge jinin dake bakinshi yana mai gyara tsayuwa.
A dai-dai lokacin da Nabihat ta miƙe tsaye zumbur, aka sake sabon kallon kallo, sannan suka sake afkawa junan da yaƙi, ana fara wannan arbu ne Nabihat ta shammaci Sharkar ta gabza mashi naushi a kirjinshi da kafafuwanta biyu, saboda ƙarfin naushin sai da ya yi sama ta tamkar an janye shi da ƙungiya sannan ya faɗa izuwa tekun Baharul-sawara.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai jaruma Nabihat ta ruga izuwa inda 'yan uwanta suke ta kai masu ɗauki su ka cigaba da ragargazar dakarun.Cikin kankanin lokaci suka hallaka su baki ɗaya.
Kawa sai Nabihat ta umarci 'yan mata uku da su tuƙa jirgin ruwan a cigaba da tafiya
Cikin matuƙar kaɗuwa ɗaya daga cikin fursunonin ta dubi Nabihat cikin tashin hankali ta ce '' ya ke Nabihat ta ya ya zamu cigaba da tafiya bayan cewa yarinya Lazimat na cikin wannan teku, kuma bamu da tabbacin a wane hali take ciki tana raye ne ko ta mutu.
Koda jin wannan batu daga bakin Sharimat sai idanun Nabihat su ka ciko da ƙwalla, ta dube ta ta ce "ya ke Shamirat tabbas a yanzu ba ni da tabbacin yarinya Lazimat na raye, shin yanzu zamu tsaya neman ta ne? Ko kuwa zamu cigaba da tuƙa wannan jirgin ruwa domin ceto daruruwan jama'armu da suka haɗar da yara ƙanana da mata gami da tsofaffi,'? Ina so ki kwantar da hankalinki idan har yarinya Lazimat na raye zamu sake saduwa da ita".
Koda jin wannan batu daga bakin Nabihat sai Shamirat ta gyaɗa kai cikin alamun matuƙar damuwa ta matsa kusa da 'yan uwanta, suka shiga tuƙa jirgin ruwan domin koma izuwa birnin su.
A dai-dai wannan lokaci ne shugaba Yasiran ya taso daga ƙarƙashin tekun fuskarshi a murtuke babu annuri, tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta, gundulmin hannunshi da Lazimat ta sare mashi na zubar da jini.
Sa'adda jaruma Nabihat ta cigaba da jagorantar sauran 'yan uwanta fursunoni, a bisa jirgin ruwan dake tafiya akan tekun Baharul-sawara, domin gudun TSIRA DAGA HAKA.
Sai suka shafe tsawon sa'a biyu suna tafiya babu sassauci.
Lokacin da ya zamana an shafe sa'a ɗaya ana tafiyar sai jaruma Nabihat ta yi umarni aka shiga ɗakin sirri dake ƙarƙashin jirgin ruwan, aka ɗauka gurasar gami taceccen ruwan inabi, aka shiga rarrabawa jama'arsu domin kowa ya kimtsa cikinshi.
Ana cikin wannan hali ne
kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka hango waɗansu tawagar jiragen ruwa kimanin guda ashirin, sun bayyana a saman tekun a kowa ce kusurwa, wato gabas, yamma, kudu da Arewa,
Cikin matukar kaɗuwa gami da tashin hankali Nabihat ta yi umarni aka tsayar da tafiya, kawai sai 'yan matan suka ruga izuwa wani ɓangare a jirgin suka ɗebo makaman yaƙi, sannan suka ruga izuwa tsakiyar birnin suna masu gyara tsayuwar su zukatansu cike da matuƙar firgici.
Ya yin da ya zamana cewa jiragen ruwan sun matso daf juna, sai Nabihat ta sake ɗimauce wa, su dai jiragen ruwan suna ɗauke ne da waɗansu irin zaratan dakaru masu ƙirar samudawan farko, suna sanye cikin sulken yaƙi na baƙin ƙarfe, ɗauke da miyagun MAKAMAN ƘARE DANGI.
Kaico! Haƙiƙa waɗannan dakaru sun kasance masu ban tsoro, domin babu halitta da za ta yi arba da su face ta yi nadamar wanzuwar ta a doran ƙasa.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su Nabihat da tawagar dakarun.
Tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali, a lokacin ne su Nabihat suka hango shugaba Yasiran a ɗaya daga cikin jiragen ruwan, shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannunshi ɗaya ɗauke da wata sharbebiyar takobi, ɗayan kuwa da ya yi dungulmi ya naɗe shi da wani farin ƙyalle, fuskarshi a murtuke babu annuri har gyatsune take saboda matuƙar fushi.
Al'marin da ya yi matuƙar ba su mamaki kenan, suka tambayi kansu a cikin ransu suna masu cewa, ya aka yi Yasiran ya rayu shin ina yarinya Lazimat take tana raye ne ko kuwa ta mutu?
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kawunansu kenan.
Kawai sai Nabihat su ka hango dakaru masu tarin yawa suna dako tsalle daga inda suke suna sauka akan jirgin da suke suna shawagi a sama tamkar tsuntsaye, suna ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Koda ganin hakan sai Nabihat ta ɗaga takobinta sama cikin ƙarfin hali gami da ƙarfafawa sauran 'yan matan gwiwa ta falfala da gudu izuwa kan dakarun.
Ya yin da 'yan matan suka ga haka sai suka yi koyi da ita, suna masu mara mata baya.
Tabbas shi ƙarfi a zuciya yake ba wai a girman jiki ba, domin idan ba haka ba taya ya mutum ashirin za su za su tunkari ɗaruruwa.
Amma dai masu iya magana na cewa shi bala'i kafin ya zo ne ake neman mafita, amma idan yazo babu abin da ya rage face a karɓe shi hannu biyu.
In da a ce mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan dubban dakarun suka yunƙura kan su jaruma Nabihat, sai ya yi zaton DANDAZON zakuna ne suka farwa barewa guda ɗaya jal, saboda matuƙar kwarjinin su.
Ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi mai matuƙar firgici da ban tsoro.
Ƙarar haɗuwar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne.
Ana fara wannan artabu ne su jaruma Nabihat suka fara gane cewa sun haɗu da gamon su.
Domin kuwa koda ba'a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza, kuma ruwa ba sa'an kwando ba ne. Domin a zahiri dakarun sun ninka su a ƘARFIN DAMTSE gami da zafin nama nesa ba kusa ba.
Sai da aka shafe sa'a ɗaya da daƙiƙa ɗari biyu ana wannan baƙin artabu, kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI sai ya zamana
dakarun sun yi masu miyagun raunuka suna zubar da jini, bisa hakan ya sanya suka faɗi ƙasa a sune.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai dakarun suka sake ɗaure fursunonin da waɗansu irin murtuka-murtukan sarƙoƙi.
Koda aiwatar da hakan sai waɗansu dakaru na musamman suka shiga tuƙa jirgin ruwan aka cigaba da tafiya, sauran jiragen tawagar guda ashirin suka mara masu baya.
Tafiyar sa'a uku kacal suka yi aka iso izuwa gaɓar tekun, take dakarun suka fito da su Nabihat daga jirgin ruwan, nesa kaɗan da inda aka sauka wani ƙasaitaccen birni mai dogayen gine gine, masu tsari da kyawu.
Kallo ɗaya za ka yiwa birnin ka fahimci cewa an kashe dukiya mai tarin yawa wajen ƙawata shi.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka tusa ƙeyar fursunonin izuwa birnin su su Nabihat kuwa sai aka ɗora su
a bisa kan keken doki.
Nan fa tsananin wahala ya sanya sauran jama'ar su Nabihat suka dunga yanke jiki suna faɗuwa ƙasa, sakamakon matuƙar zafin rana amma a haka dakarun suka cigaba da jan su a ƙasa.
Komai rashin tausayin mutum idan ya yi arba da halin da ƙananan yara da mata ke ciki dole ne ya zubar da hawayen tausayi.
Domin wasu lokutan idan mutum ya faɗi ƙasa sai dakarun su zabga mashi wata murtukekiyar bulala, take inda ya daka ɗin zai fashe jini ya yi tsartuwa.
Tun kafin a iso kofar birnin waɗansu girɗa-girɗan dakaru suka wangame makekiyar kofar birnin, suna zuwa suka kunna kai izuwa ciki.
Daga ciki birnin ya kasance tafkeke na gaban kwatance, gaba ɗaya gine-ginen shi an yi su ne bisa tsari mai ban sha'awa, duk inda mutum ya kalla jama'a ne rututu na kai komo suna gudanar da ayyukan su na yau da kullum, haka dai su shugaba Yasiran suka ci-gaba da tafiya a cikin birnin, duk inda jama'a suka hango su sai ka ga sun dare sun buɗa masu hanya.
Kai tsaye aka shiga izuwa fadar birnin wacce ta kasance ƙasaitacciya da aka ƙawata da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, kai tsayawa musalta tsaruwa da ƙawatuwar fadar zai iya zama ƙauyanci sai dai abin da idanu suka gani kawai.
A wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a maza, mata yara da manya tare da yan majalisa.
Zaune a bisa wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'anta ta da ƙarfen jauhari aka yi mata feshin da ruwan zinare.
Wani garjejen mutum ne mai kimanin shekaru talatin da ɗoriya, yana sanye cikin tufafin alfarma irin na hamshaƙan sarakai, kanshi sanye da KAMBUN SARAUTA.
Kallo ɗaya zaka yiwa mutumin ka ji baka marmarin sake haɗa idanu dashi, saboda matuƙar munin fuskarshi tamkar murmushi bai taɓa wanzu akan ta ba.
Ba wani bane wannan mutum ba face sarki Uhaisu ibn Falluz.
A gefen hannunshi na dama bisa wata ƙasaitacciyar kujera wani kyakkyawan saurayi ne ma'abocin kwarjini da haiba, ya caɓa ado irin hamshaƙin BASARAKE, babban abin da ya ƙara tona asirin kyawun shi shine saje da gemunshi da suka kasance baƙaƙe siɗik.
Ba wani ba ne kyakkyawan saurayin ba face yarima Zafiyar ibnu Uhaisu, wanda ya kasance ɗa guda ɗaya tilo ga sarki Uhaisu.
Sarki Uhaisu ibn Falluz ya kasance GWARZON DUNIYA a fagen jarumtaka gami da sanin ilimin tsafi, daɗin daɗawa kuma ya kasance AZZALUMI na gaban kwatance.
Tun yana da shekara goma sha biyar ya hau bisa karagar mulki, duk da yana da ƙarancin shekaru amma sai jama'a suka ga yana gudanar da sha'anin mulki cikin tsari fiye da na mahaifinshi marigayi sarki Falluz.
Lokacin da sarki Uhaisu ya cika shekaru ashirin a bisa kan gadon sarauta, sai ya zamana cewa ya fara kai mamayar bazato izuwa ƙauyuka da biranen dake maƙwabtaka da shi, ana farauto mashi bayi gami dukiya mai tarin yawa.
Cikin ƙanƙanin lokaci Uhaisu ya zama mashahurin attajiri da babu tamkar shi a nahiyar.
Da wannan dukiya da ya tara yake siyo manyan sadaukai daga sassan duniya domin su taimaka mashi wajen FATAUCIN BAYI.
Shin mene ne dalilin da ya sanya su jaruma Nabihat suka baro birninsu har aka farauto su a cikin wannan jirgin ruwan?
Amsar hakan kuwa shi ne kamar haka:-




BABI NA BIYU


Wata rana daga cikin ranakun da sarki Uhaisu ke kai FARMAKIN BAZATO izuwa birane da ƙauyuka domin FATAUCIN BAYI.
Yana zaune a cikin lambun shaƙatawar shi sanye da riga 'yar shara irin ta hamshaƙan sarakai, waɗansu irin tsala-tsalan kyawawan kuyangi na shayar da shi taceccen ruwan inibi da barasa a bisa waɗansu kofuna na zinare, a gefe guda kuwa waɗansu kuyangi ne sanye da tufafi mai bayyana tsiraicinsu.
Babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da su face hankalinshi ya tashi.
Su na yiwa sarki Uhaisu tausa tamkar wani jariri, shi kuwa yana kallon korayen tsirrai gami da waɗansu irin tsuntsaye dake shawagi a wajen, su suna fitar da wani irin sautin kuka mai daɗin saurare.
Zuciyarshi cike da matuƙar farin ciki, yana cikin wannan hali ne kawai sai ya ɗauko madubin tsafinshi ya shafe shi da hannunshi na hagu ya fara gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi.
Kamar yadda a duk sa'adda zai kai farmakin yana gudanar da bincike ne domin ya gano birnin da zai kai aiwatar da hakan,
Tsawon daƙiƙa hamsin yana gudanar da binciken sannan ya gano wani baƙon birni dake iyaka da tekun Baharul-sawara wato birnin DARUL-IMFAL,
Abin da ya firgita shi a binciken shi ne, tabbas a wannan birni ne za a samu mahalukin da zai kawo ƙarshen mulkin zaluncin shi a doran ƙasa.
Kooda ganin hakan sai sarki Uhaisu ya miƙe tsaye zumbur yana mai kurma wawan ihu, ihun na shi ya firgita kuyangin dake yi mashi hidima, gami da tsuntsayen dake lambun suka tashi sama furrrr!. Al'amarin da ya janyo hankulann dakarun dake gidan sarautar kenan suka rugo izuwa lambun ɗauke da makamai.
Amma koda suka yi arba da sarki Uhaisu a tsaye tsam! fuskarshi a murtuke babu annuri tamkar an watsa mashi garwashin wuta a kan ta, kuma idanuwanshi sun kaɗa sunyi jajur.
Sai suka yi turus! Kowa ya kasa isa izuwa inda yake,
cikin matuƙar fushi sarki Uhaisu ya ƙwallawa wani badakare kira mai suna Hushaibu.
Kafin ya gama rufe bakinshi Hushaibu ya bayyana a gare shi ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa jikinshi na ƙyarma saboda tsananin tsoro.
Cikin matuƙar fushi sarki Uhaisu ya dakawa kuyangin dake yi mashi hidima tsawa da su fice daga cikin lambu, sannan ya mayar da uban shi ga Hushaibu cikin kakkausar murya ya sune shi ya ce "ya kai Hushaibu ka yi sani cewa bakomai ne ya sanya na kira ka nan ba sai domin ina son ka hanzarta kira min sadauki Yasiran''.
Muryar Hushaibu na rawa ya ce "An gama ya shugabana, yana gama faɗin hakan sai ya miƙe tsaye ya fice daga cikin lambun da sauri.
Jim kaɗan sai ga Yesiran ya bayyana gareshi, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance SADAUKIN SADAUKAI, mai tarwatsa maza a filin daga.
Sarki ya dubi Yesiran ya ce "ya kai Yasiran ka yi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka tafi izuwa wani birni dake iyaka da tekun Baharul-sawara, ana kiran birnin da suna DARUL-IMFAL
ina so gaba daya mazajen birnin su zamo matattu, sannan ka kawo min matayensu da dukiyoyin su cikin ƙoshin lafiya,
sai dai ina son kayi sani cewa kuɓucewar ɗaya daga fursunonin dai-dai yake da rasa rayuwar ka baki ɗaya''.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Uhaisu sai Yesiran ya ce "ya shugabana ai wannan aiki abu mai sauƙi a gare ni tamkar kurɓar ruwa, na rantse da ƙarfi mulkin ka sai na kawo maka matayen birnin DARUL-IMFAL cikin ƙoshin lafiya'';
Koda jin wannan batu daga bakin Yesiran sai Uhaisu ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Kafin sarki Uhaisu ya sake furta wani abu Yesiran ya miƙe tsaye zumbur ya fice daga lambun.
Kamar yadda sadauki Yesiran ya yiwa sarki Sarki Uhaisu alƙawari haka al'amarin ya kasance, a in da yana fita ya ɗebi dakarun yaƙi guda dubu hamsin, suka durfafi hanyar da za ta sada su da birnin DARUL-IMFAL bisa wani makeken jiragen ruwa.
Da la'asar sakaliya, sadauki Yesiran da rundunar mayaƙanshi, suka iso gaɓar tekun Baharul-sawara sakamakon hango kofar birnin DARUL-IMFAL da su kayi.
A wannan lokaci jama'ar birnin DARUL-IMFAL na gudanar da ayyukan su na yau da kullum cikin walwala da jin daɗi, hakan ya faru ne sakamakon saukar ruwan sama a daren jiya.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ji ihu da kururuwar dakaru masu tsaron ƙofar gari, kafin ka ce me, gari ya hargitse da guje-gujen jama'a gami da ifice-ifice, yara da manya mata da maza,
Nan take dakarun sadauki Yesiran suka afkawa jama'ar birnin da masifaffan yaƙi, nan fa mazaje suka dunga yin MUTUWAR JARUMTA, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, ƙarar karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje gami da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne.
Kaico! Haƙiƙa yaƙi abin tausayi ne in da a ce mutum zai ga yadda dakarun Yesiran ke hallaka mazajen birnin ba ji ba gani, dole ne ya zubar da hawayen tausayi domin hatta ƙananan yara maza kashewa suke yi, koda kuwa jariri ne sabuwar haihuwa ba su ƙyale ba.
Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN KARFI sai ya zamana dakarun Yesiran sun kashe gaba ɗaya mazajen birni ɗayan su bai tsira da rayuwar shi ba. Nan fa ƙananan yara da mata suka dunga rusa kuka mai matuƙar ban tausayi da narkar da zuciya, wasu na kuka ne bisa rasa mazajensu, wasu 'ya'yensu, wasu 'yan uwansu.
Bayan sadauki Yasiran ya kashe sarkin dake mulkin birnin wani dattijo mai suna Sha'aran sai ya yi umarni aka kwashe baki ɗaya dukiyar dake birnin, aka sanya matayen birnin da suka rage a raye sasari na baƙin karfe, bayan an fice daga birnin sai waɗansu dakaru suka bankawa gidadanjiin birnin wuta, take aka nufi gaɓar teku aka sanya ɗora dukkanin jama'ar a bisa wannan makeken jirgin ruwa.
Lokacin da aka ɗora su jama'ar a bisa jirgin ruwan suka hango yadda birninsu ke ci da wuta, kuma an mayar da da yawa daga cikin su zaurawan yara kuwa sun zamo marayu.
Sai suka fashe da matsanancin kukan takaici da baƙin ciki.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba sadauki Yesiran ya yi umarni aka tuƙa jirgin ruwan a aka cigaba da tafiya zuciyarshi cike da matuƙar farin ciki da samun wannan nasara.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya sarki Uhaisu ya farauto su jaruma Nabihat daga birnin DARUL-IMFAL dake iyaka da tekun Baharul-sawara.




BABI NA UKU




Al'amarin shugaba Yesiran kuwa, lokacin da ya gabatar da su Nabihat da sauran jama'ar birninsu gami da dukiyar ganima a gaban sarki Uhaisu sai sarki ya dube shi a lokacin da yake durƙushe a gaban shi ya buɗi baki cikin alfahari da BAƘAR IZZA ya ce
''ya kai Yesiran haƙiƙa kayi aiki mai kyau yadda na buƙata saboda ina mai tabbatar maka da cewa zaka samu gwaggwaɓan kaso daga cikin ganimar dukiyar da aka farauto. Yanzu abin da nake ya kamata ayi shine a tafi da dukkanin fursunonin izuwa kurkuku a ajiye su a ɓangaren BAUTAR MUTUWA".
Koda yarima Zafiyar da ya kafa idanuwanshi akan jarumai jaruma Nabihat dake cikin halin suma, ya ji wannan batu daga bakin mahaifinshi sai ya yi caraf ya tari numfashin shi ya ce "ya abbana ina neman alfarma a gare ka da abar fursunonin a hannuna har izuwa lokacin da za'a yanke hukunci akan su."
Da jin wannan batu daga bakin yarima sai sarki ya juya ya dube shi yana mai fahimtar wani abu akan fuskarshi, sannan ya yi tattaunawar murmushi a gare shi ya ce "ya abin alfaharina kuma muradin zuciyata kayi sani cewa babu wani abu da zaka nema a gare ni face na baka shi koda kuwa raina ne, amma akwai buƙatar ka ba ni lokaci na yi nazari, domin bisa binciken da na gudanar ya tabbatar min da cewa a cikin jama'ar za a samu wanda zai kawo ƙarshen mulki na".
Sa'adda yarima ya ji wannan batu daga bakin sarki sai ya gyaɗa kai cikin alamun matuƙar damuwa, domin wannanne karo na farko a rayuwarshi da ya ji ya kamu da matuƙar tausayin bayin da mahaifinshi ke farautowa.
Koda gama wannan tattaunawa sai shugaba Yesiran ya huce kai tsaye izuwa hanyar da za ta sada su da kurkukun birnin, koda isowar su sai masu gadin suka wangame makekiyar ƙofar shiga, suna masu risinawa ga shugaba a gare shi.
Daga ciki kurkukun ya kasance tafkeke tamkar gari guda, katangun shi sun kasance masu matuƙar tsawo da aka yi su da zallar duwatsun wuta masu ƙwarin gaske.
Duk inda mutum ya kai duban shi a ciki bayi ne maza da mata, yara da manya na ta gudanar da ayyukan bauta nau'i daban-daban, waɗansu na aikin farfasa duwatsun wuta da manyan gudumun ƙarfe, wasu na ɗinka kayan adon dawakai da tufafin sarauta.
Koda shigowar shugaba Yesiran cikin kurkukun sai gaba ɗaya bayin su ka dunga a jiye aiyukan su suna zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa a gare shi, cikin hanzari shugaban dake kula da kurkukun ya karɓi su jaruma Nabihat ya yi umarni aka rarraba jama'ar su a cikin waɗansu ɗakunan na musamman.
Koda jama'ar dake wajen suka ga cewa an shigar da su jaruma Nabihat izuwa ɓangaren da ake yiwa laƙabi da BAUTAR MUTUWA, sai suka cika da matuƙar tausayin su. Domin kuwa duk wanda aka shiga da shi izuwa ɗakin BAUTAR MUTUWA baya fitowa a raye sai daigawar shi.
Sa'adda jama'ar su Nabihat suka tsinci kansu a cikin ɗakunan sai suka fashe da kukan baƙin ciki mai matuƙar tsuma zuciya.
Wannan shine abin da ya faru da su Jaruma Nabihat ya yin da aka isa da su izuwa kurkuku.


Al'amarin wannan yarinya fursuna da ta fafata yaƙi da shugaba Yesiran a ƙarƙashin tekun Baharul-sawara kuwa, bayan ta samu nasarar datse nashi hannunshi ɗaya, shi kuma ya samu nasarar yi mata miyagun raunuka, ɗaya a gadon bayanta na biyu a cinya na ukun kuwa a damtsen ta na hagu.
Saboda yawan jinin dake zuba a jikinta take numfashinshi ya ɗauke, kuma ta taso izuwa saman tekun igiyar ruwa ta cigaba da tafiya da ita, har ta kawo ta izuwa gaɓar tekun ta ɓangaren yamma maso kudu.
A dai-dai wannan lokaci ne wani mafarauci da matarshi suka nufo gaɓar tekun ɗauke da bahon ɗibar ruwa.
Sa'adda suka yi arba da ita kwance babu alamun rai a tare da ita ga manyan raunika a jikinta sai suka yi turus! cikin kaɗuwa suka matsa inda take.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba suka ajiye bahon ruwan dake hannunsu, mafaraucin ya ɗauki yarinyar ya saɓa ta a kafaɗarshi.
Cikin hanzari suka juya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment