Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka durfafi hanyar da zata sada su da dajin da suka fito.
Tafiyar daƙiƙa latalin kacal suka yi suka iso wani gida a dajin. Gidan an gina shi ne da zallar duwatsun wuta, kai tsaye suka kunna kai izuwa gidan.
Daga ciki gidan ya kasance mai kyawun tsari yana ɗauke da ɗakuna guda biyu da makewayi ɗaya sai wani madaidaicin fili da aka kafa turken dabbobi wata saniya guda ɗaya fara sol tana cin ciyawa a cikin wani bawon kaba.
Cikin hanzari matar mafaraucin ta shimfiɗe yarinya Lazimat a bisa wani madaidaicin gado da aka yi shi da zallar itace aka shimfiɗe shi da kilishi mai taushi, bayan ta kwantar da ita sai ta shiga danna ƙirjinta cikin matuƙar tashin hankali.
Shi kuwa mafaraucin sai ya fice daga ɗakin, jim kaɗan sai ga shi ya dawo ɗauke da tafashasshen ruwan zafi gami da tacecciyar madarar shanu, a ɗayan hannunshi kuwa yana ɗauke da wata jakar fata, kawai sai ya shiga ɗauko waɗansu magunguna a cikin jakar ya na haɗa su a cikin wani akushi mai ɗauke da ruwa.
Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya Lazimat bata farfaɗo daga dogon suman da tayi ba.
Sai daga bisani ne ta buɗe idanuwanta tana mai jan gwaron numfashi, nan fa suka cika da matuƙar farin ciki bisa ginin farfaɗowarta, ba tare da wani ɓata lokaci ba matar ta shiga sanya mata magani a raunikan ta.
Bayan ta kammala ne sai ta tashe ta zaune ta shiga bata wannan madarar shanu a baki tana kurɓa, sai da tasha ta ƙoshi sannan ta bata waɗannan magunguna da maigidanta ya haɗa a cikin wannan akushi.
Kana daga bisani mafaraucin ya dubi matarshi fuskarshi cike da annuri gami da tsantsar so da kauna ya ce "ya uwar 'ya'yana ina mai ba Ni farin ciki, kiyi sani cewa ina ji a jikina wannan yarinya da muka tsinta za ta maye mana gurbin da raɗaɗin 'yarmu da muka rasa.
Kuma na ji a jikina cewa za ta zamto silar da zamu ɗauki fansa akan sarki Uhaisu".
Koda jin wannan batu daga bakin mai gidannata sai ta cika da matuƙar farin ciki ta ce "maganar ka haƙƙun ya abin bege na tabbas alamun nasara sun fara bayyana a gare mu";
Mafaraucin ya ce "yanzu zan ɗan shiga izuwa daji, domin na farauto mana abin da zamu yi kalaci sai ki kula da ita har naje na dawo".
Yana gama faɗin hakan sai kawai ya miƙe tsaye ya fice daga ɗakin ya na mai waigen matarshi suna jifan juna da tsantsar so da ƙauna, yana fita ya sake kunna kai izuwa cikin daji .
Jim kaɗan bayan shuɗewar waɗansu daƙiƙu matar mafaraucin na zaune a gaban Lazimat ta ƙura mata idanu sai kawai ta jiyo ƙarar takun sawaye gami da gurnani mai matuƙar ban tsoro, ya cika dajin baki ɗaya.
Koda jin hakan sai kawai ta ɗauko wata takobi a gefen gadonta ta miƙe tsaye zumbur ta ruga izuwa ƙofar gidan, ai kuwa tana fita sai tayi arba da waɗansu irin ayarin gabza-gabzan birrai su kimanin guda ɗari biyu.
Birran sun kasance masu matuƙar tsawo, girma, kwarjini gami da muni, a hannayensu na ɗauke da wani irin sungumi mai waɗansu irin tsinika a jikin shi tamkar zarto,
Wannan shi ne abin da ya faru da mafarauci da matarshi da suka tsinci yarinya Lazimat.
Kallo ne ya wakana tsakanin kilimat matar wannan mafarauci da ayarin gwaggwan birran na ɗan wani lokaci.
Daga can sai birran su kayi wani mahaukacin gurnani mai matuƙar ban tsoro mai ɗimauta duk wata halitta numfashi, bishiyu suka dunga rangaji suna karairayewa suna faɗuwa kasa.
Wani daga cikin birran wanda alama shi ne shugaban su ya daka masu wata tsawa dake nuna cewa su afkawa matar, ai kuwa sai su ka yi ɗauki kanta suna masu daga makamansu suna ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Shi kuwa shugaban birran sai ya samu wani ɗan faffaɗan dutse ya zauna a a kai yana mai harɗe kafafuwanshi yana mai zuba idanu domin ya ga yadda artabun zai wakana.
Koda ganin hakan sai uwar gidan mafaraucin ta ɗaga takobinta sama sannan ta ruga izuwa kan birran tana ihu da kururuwa mai firgitarwa ta far masu da sara da suka, su kuwa suka shiga kai mata duka da bugu da sungumin su cikin wani irin zafin nama, duk sa'adda takobinta ta sari jikkunan birran sai ta ji kamar dutse ta sara domin ko gezau ba su yi
Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin ta kenan, yazamana ta canza salon fadan ta a in da ta dunga saran su gami amfani da hannunta ɗayan tana gabza masu naushi da bugu da dukkan ƙarfin ta.
Gaskiyar masu iya magana da suka ce "Idan kiɗa ya canja dole ne rawa ma ta canja, nan fa ya zamana cewa ta fara samun galaba akan birran, domin duk wanda ta gabza masu naushin sai ka ji ya tsandara ihu ya ya faɗi ƙasa yif!.
Koda ta fahimci cewa ƘARFIN DAMTSE ya fi tasiri akan su sai kawai ta yi jifa da takobinta ta shiga amfani da hannayenta duka biyun gami da kafafu wajen kai farmaki. Duk in da ta sanya a gaba sai dai kaga gawarwakin birran na zube kasa matattu.
Wohoho! Tabbas ƙarfi da jarumtaka ba a siyan su da kuɗi face baiwa daga Allah,
Komai tsakanin hassadar mutum idan ya ga yadda kilimat ke ragargazar birran dole ne ya jinjina mata ya san cewa ta ciri tuta a cikin jerin manyan JARUMAN DUNIYA.
Nan fa kururuwa gami da hargagin su ya cika dajin baki ɗaya, jini ya dunga tsartuwa yana kwaranya a kasa, haƙiƙa waɗannan birrai suna ganin tashin hankalin da basu taɓa ganin irin shi ba.
Domin ta zame mssu alaƙaƙai, kuma ƙadangaren bakin tulu, cikin abin da bai gaza daƙiƙa ɗari biyu ba ta kashe fiye da kaso biyu bisa uku na birran.
Sa'adda shugaban birran ya ga irin muguwar ɓarnar da matar mafaraucin ke yi mashi sai ya cika da matuƙar mamaki kuma ya fusata ainun, domin fiye da shekaru ashirin suna zaune a wannan daji ba su taɓa ganin bil'adama da ya yi masu hasara kamar haka ba.
Nan take zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone, kawai sai ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu da sanya bishiyu suka dunga ƙarye suna faɗuwa ƙasa, duwatsu suna karo da juna su na yin bindiga,
kawai sai sauran birran da ke yaƙin suka zubar da makaman su suka ruga izuwa bayan bishiyu su ka ɓuya
A lokaci guda shugaban ya tsuke bakinshi sannan ya dako wawan tsalle daga inda yake zaune ya durfafi inda take, ya yin da ya isa gare ta nan take ta zamto 'yar mitsitsiya tamkar an ajiye ɓera a gaban giwa, saboda matuƙar tsawo da girman shi.
Kafin ta yi wani yunƙuri shugaban ya shammace ta ya gabza mata wawan naushi a fuska da hannunshi ɗaya.
Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da tayi katantanwa a sama sau uku sannan ta faɗo ƙasa tim! A matuƙar galabai ce,
cikin ƙarfin hali ta yunƙura ta miƙe tsaye da nufin ta mayar da martani amma sai ya damƙe ta da hannunshi ɗaya ya matse ta ya shiga yi mata lugudan naushi a fuska nan take fuskarta ta kumbura, tayi kaca-kaca da jini da majina kuma numfashinta na fita samas-sama.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai ya ji ta ƙwalla ƙara ta suɓuce daga hannunshi sannan ta gabza mashi naushi a idonshi ɗaya.
Take ya fashe wani koren ruwa gami da jini ya dunga kwaranya da ga ciki, nan fa shugaban ya dunga ihu da kururuwar neman taimako, kafin ya sake wani yunƙuri matar mafaraucin ta cire wata 'yar karamar wuƙa ta caka mashi a maƙogaronshi, nan take ya faɗi kasa rikica! Yana shure-shuren mutuwa kafin wani lokaci ya sheƙa barzahu.
A dai-dai wannan lokaci ne mai gidanta ya rugo izuwa wajen, koda ya yi arba da gawarwakin birran sai kawai ya rungume matarshi cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa bisa ganin cewa tana raye bata mutu ba.
Sai daga can ne ya janye jikinshi daga na ta, a lokacinne ya lura cewa ta samu manyan raunika, sai kawai ya ɗauke ta ya shiga da ita izuwa cikin gida cikin matuƙar tashin hankali.
Lokacin da ya isa sai ya shimfiɗe ta a bisa wani gadon na musamman dake cikin turakarshi ya shiga bata taimakon gaggawa,to ta hanyar sanya mata magani a raunikan ta, inda jini ya taru ya gasa mata da ruwan ɗumi.
Har a wannan lokaci yarinya Lazimat ba ta farfaɗo ba tana kwance tana sharar barci sakamakon maganin barci da aka bata.
Ana cikin wannan hali ne sai kawai ya ga uwargidanta shi ta buɗe idanuwanta tana mai yi masa wani murmushin karfin hali, cikin tattausan murya ta buɗi baki ta ce "ya uban 'ya'yana shin mene ne ya sanya zaka saka kan ka a damuwa bayan cewa mun samu abin da zai share mana hawaye, kuma gani a raye ban mutu ba?
Mai gidan nata ya dube ta cikin tsantsar tausayi da so da ƙauna ya ce "zancen ki haƙƙun ya abar kaunata, amma ina so kiyi sani cewa tsananin kaunar da nake yi miki ne ta tayar min da hankali.
Koda jin wannan batu sai su duka biyun suka bushe da yar karamar dariyar murna suna yiwa junan su wani irin kallo mai tattare da tsananin begen juna
Sai aka shafe kwanaki uku mafaraucin yana jinyar matar shi da yarinya lazimat.
A wata rana matar mafaraucin na bawa yarinya lazyimat horan yaƙi, bayan ta kammala bata horan yaƙin sai ta ta ja hannunta izuwa kan wani faffaɗan dutse suka zauna tare a kan shi, sannan ta sanya hannayenta biyu ta ɗora a kan kafaɗunta dube ta cikin nutsuwa ta yi gyaran murya ta ce "ya ke wannan yarinya shin mene ne sunan ki da labarin rayuwar ki?.
Koda jin wannan tambaya daga bakin matar sai hawaye suka kwaranyo daga idanun Lazimat tana mai fashewa da kuka mai tsuma zuciya.
Al'amarin da ya yi matuƙar bata mamaki kenan kuma ya dugunzuma hankalinta dube ta ta ce "shin ina dalilin wannan kuka naki?
Ki sani cewa sanar da ni labarin ki shi ne zai bamu damar taimaka wa rayuwar ki.
Da jin haka sai Lazimat ta share hawayen dake fuskarta ta buɗi baki daƙyar ta ce "da farko ni suna Zalimat bintu Haiman mahaifina ya kasance GWARZON DUNIYA mai tarwatsa maza a filin daga,
Bisa wannan dalili ne ya sanya jama'ar birninmu ke matuƙar kaunar shi domin yana bayar da gagarumar gudummawa wajen kare martabar birninmu daga harin bazato.
Daga wannan ne lazimat ta kwashe labarin farmakin da sarki Uhaisu ya kai birnin su bisa jagorancin shugaba Yesiran,dama abin da ya faru tsakaninta da dakarun jirgin ruwan da ya ɗauko su a saman tekun Baharul-sawara, daaga farko har ƙarshe ta zayyane mata.
Sa'adda da yarinya lazimat tazo nan a labarin ta sai ta sake fashewa da wani matsanancin kuka mai ban tausayi ,
Saboda matuƙar tausayi da matar mafaraucin ta ji bata san lokacin da hawaye ya zubo mata ba ta rungume ta a kirjinta su duka biyun suka fashe da matsanancin kuka, sai da suka ɗauki tsawon lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani ta janye jikinta daga na Lazimat suka fuskanci juna.
Idanu sharkab da hawaye ta dube ta ce "ya ke Lazimat haƙiƙa sarki Uhaisu baƙaramin AZZALUMI ba ne, tun da ya raba ki da iyayen ki dangi da yan uwanki ya mayar dake marainiya.
Ina so ki kwantar da hankalin ki domin ni da mai gidana mun yi miki alƙawarin sai mun ɗauko miki fansa akan sarki Uhaisu, kuma sai mun ceto sauran jama'ar ku ina so ki ɗauke mu tamkar iyayenki";
Koda jin wannan batu sai Lazimat ta cika da matuƙar farin ciki ta dube ta ce "ya ummina ba ki sanar da ni sunanki da na abbana ba da ma labarin ta ku rayuwar?
Da jin wannan tambaya sai matar mafaraucin ta yi murmushi mai taushi a gare ta ta ce "mai gidana ana kiranshi da suna Najwas ibnu Naufal, ni kuwa ana yi min laƙabi da Kilimat bintu kurbas, ya 'yata ki yi sani cewa a halin yanzu ba zan ba ki labarin rayuwar mu ba, kasancewar na ki labarin ya yi min fami a zuciyata, amma na yi miki alƙawarin zan ba ki anan gaba".
Koda Kilimat bintu kurbas ta zo nan a zancen ta sai suka hango mafarauci Najwas ya dawo daga farauta, cikin matuƙar farin ciki suka miƙe tsaye suka je suka tarbe shi,
Kilimat ta riƙe mashi dabbar da ita kuwa yarinya Lazimat sai ta karɓi salkar ruwa da jakar dake rataye a gadon bayanshi suka dunguma izuwa cikin gida.
Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya lazimat bayan ta samu lafiya a hannun mafarauci Najwas da uwar gidanshi.




BABI NA HUƊU

Ƙasaitacciyar turaka ce da aka ƙawatata da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, gaba ɗaya tana shimfiɗe da wani irin kilishi mai matuƙar taushi,wanda idan mutum ya taka shi sai ya ji tamakar kafafuwanshi za su shige ciki, ku san dukkanin abin da ke turakar an sana'anta shi ne da zallar ƙarfen jauhari da yaƙutu, waɗansu irin fitilu masu matuƙar haske sun ƙara fito da kyawun tuarakar.
Kai tsaya wa musalta tsaruwa da kawatuwar turakar ya huce hankali sai dai abin da idanu suka gani kawai.
A wannan lokaci dare ya tsala babu abin da kunne ke ji face kukan gyare gami da haushi karnuka tsilli-tsilli,i' idan mai kallo ya kai duban shi a tsakiyar turakar zai yi arba da wani mutum sanye da riga 'yar shara da wando irin na hamshaƙan sarakai yana kai komo tamkar wanda ya yiwa sarki ƙarya.
Ba wani ba ne face sarki Uhaisu, a wannan lokacin bakomai ne ya hana Uhaisu barci ba face tunanin buƙatar da ɗanshi yarima Zafiyar ya nema a wajen shi, ta ya amince mashi ya zamo mai kula dasu jaruma Nabihat.
An ya kuwa yarima ba saboda zuciyarshi ta kamu da soyayyar Nabihat ba ne yasanya ya ce a ba shi ikon kulawa da su ɗin ba? Yanzu idan har ya yi ganganci soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin su ta ya ya zai iya zartar da hukuncin kisa akan su Nabihat tun da halarar tsafi ta bayyana mashi cewa sune za su kawo ƙarshen MULKIN ZALUNCIn shi daga doran ƙasa.
Sa'adda sarki Uhaisu ya zo nan a tunanin shi sai hankalin shi ya dugunzuma fiye da ko yaushe.
Yana Cikin wannan hali ne wani tunani ya faɗo mashi wanda ya sanya shi farin ciki.
Tunanin kuwa shi ne ai ya umarci sadauki Yesiran akan ya kai su Nabihat izuwa ɓangaren BAUTAR MUTUWA dake kurkukun, tabbas yunwa ce zata zamo ajalin su.
Koda ya zo nan a tunanin sai ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Uhaisu bayan ya baro fada, ya kaɗaita a cikin turakarshi.
Kashe gari tun da duku-dukun safiya kafin hudowar rana aka fito dasu jaruma Nabihat daga cikin ɗakunan da aka kulle su a ɓangaren BAUTAR MUTUWA, dake cikin kurkukun Mautul- shammar, aka rarraba masu aikin farfasa duwatsu, da yake yanayin garin ana cikin wunturu, nan take tsananin sanyi ya addabi ƙananan yara da tsofaffi, saboda ba sa sanye pda tufafi masu nauyi,
Sai da suka wuni cur suna aiki sannan dakaru suka sake mayar da su izuwa cikin ɗakunan su ba tare da an bawa ɗayan su koda loma ɗaya ta abinci ba.
Tun da duku-dukun safiya fadar sarki Uhaisu ta cika ta batse da jama'ar gari gami da fadawa, bayan kowa ya hallara ne sai sarki ya miƙe tsaye daga kan karagar shi ta mulki ya fuskanci jama'a ya buɗi baki cikin tunƙaho da baƙar uzza ya ce "ya ku jama'ar wannan fada mai albarka ku yi sani cewa ba komai ya sanya na tara ku anan ba sai domin sai ku ganewa da idanuwanku yadda zan yanke wa jama'ar birnin DARUL-IMFAL hukunci, domin a cikin su ne za a samu tsageran da zai kawo ƙarshen mulkina, ina so hukuncin ya zamo darasi ga duk wani mai ƙarar kwana irin su";
Koda gama faɗin hakan ya koma kan karagarshi ya zauna, take fadar ta kaure da ce kuce kowa na faɗin albarkacin bakinshi.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka hango shugaba Yesiran ya tuso ƙeyar su jaruma Nabihat sanye cikin sasari na baƙin ƙarfe, dakaru na take masa baya sun Kunno kai cikin fadar, sai da Yesiran da fursunonin ashirin suka iso izuwa wani dogon tudu,sannan ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa ga sarki, kana ya miƙe tsaye ya juya ya yi wani badakare inkiya ta wutsiyar idanu.
Kawai sai badakaren ya tusa ƙeyar jaruma Nabihat izuwa kan wannan gayayyen tudu mai matattakala ta hau ta tsaya kuma ya ɗaure idanuwan ta wani baƙin ƙyalle.
Daga can sai wani badakare ya ratso daga cikin dakarun fadar ya fito waje yana taka tafka-tafkan ƙafafuwanshi. Badakaren ya kasance garjejen kato mai ƙirar samudawan farko, yana da manyan damatsa ya tara kwanji, cikinshi runtumeme ne tamkar an kifa ƙwarya, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa zuciyarshi a ƙeƙashe take da tsantsar zalunci.
Kai tsaye ya durfafi inda jaruma Nabihat take yana mai zare wata sharbebiyar takobi a cikin kubenta, yana wani irin huci tamkar kububuwa ya ɗaga takobin sama domin ya datse mata wuya.
Kafin KAIFIN TAKOBIN ya ratsa wuyan Nabihat
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu kyawawan jarumai biyu mace da namiji da gami da wata yarinya 'yar kimanin shekaru goma sha biyu sun kutso izuwa cikin fadar shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensi rike da miyagun makamai, ba wasu ba ne waɗannan jarumai ba face mafarauci Najwas da uwargidanshi Kilimat tare da yarinya Lazimat.
Har dakarun dake fadar sun yunƙura za su afka masu a kacame da azababban yaƙi sai sarki Uhaisu ya daka mssu tsawa su ka ja da baya, cikin matuƙar fushi ya miƙe tsaye zumbur! Daga kan karagar mulkinshi yana mai zare takobinshi gami da kwarara uban ihu, sannan ya dako wawan tsalle daga inda yake tsaye tamkar an harbo shi daga cikin baka,
Yana saman ya kaiwa mafarauci Najwas wawan sara da nufin tsinke mashi wuya.
Cikin ƙwarewa gami da zafin nama Najwas ya sanya takobinshi ya kare harin,
Uhaisu ya dira bisa turba aka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro.
Koda ganin hakan sai yarinyar Lazimat ta ruga izuwa inda su jaruma Nabihat suke ta sanya takobi ta sare sarƙoƙin da aks ɗaure su.
Nan fa Nabihat da sauran 'yan matan su sha tara suka rungume yarinya Lazimat suna masu fashewa da kukan farin ciki.
Suna cikin wannan hali ne suka hango shugaba Yesiran da dakarun shi sun ya rugo izuwa kan su, koda ganin hakan sai suka yi wuf suka juya suka fuskance su aka yi karon battar ƙarfe aka kacame da azababban yaƙi.
Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin mafarauci Najwas da sarki Uhaisu, su jaruma Nabihat da shugaba Yesiran da dakarun shi.
Sai karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne,
Najwas da kilimat suka wanzu suna kare hare-haren da Sarki Uhaisu gami da mayar da martani.
Wohoho! Haƙiƙa wanda ya iya ya huta, kuma faɗan gwani da gwani daɗin kallo gare shi,in da ace mutum ya na tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan ZARATAN MAYAƘA uku ke kaiwa juna hare hare domin hallaka juna dole ne ya jinjina masu ya kira su da JARUMAN DUNIYA.
Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya da daƙiƙa ɗari da arba'in ana wannan fafatawa amma ɗayan su bai samu nasarar yiwa abokin gwamin shi koda kwarzane ba.
A zahiri ga wanda yake kallon artabun zai lura sarki Uhaisu ya ninka su jarumi Najwas a ƘARFIN DAMTSE, sai dai su nuna mashi ƙwarewar yaƙi.
Al'amarin da ya fusata sarki Uhaisu kenan kuma ya cika da matuƙar mamaki, domin a tarihin jarumtakar shi tai taɓa yin GABA DA GABA da wani jarumi ba face ya kai shi ƙasa, abin tambaya ana shi ne ya aka yi ya kasa samun nasara akan su? Shin wai su waye ma waɗannan jarumai Kuma daga ina su ka fito?
Amsar tambayoyin da ya kasa bawa kanshi kenan, kawai sai ya ja da baya sannan ya yi kururuwa ya sa ke afkawa masu yana mai canza salon faɗan shi.
Ashe Najwas da Kilimat sun lura da abin da sarki Uhaisu ya yi, don haka su ma sai su ka koyi da shi suka canza salon artabun nasu.
Wohoho! Gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya sauya dole ne rawa ta sauya salo.
Nan fa yaz' zamana su sarki Uhaisu sun lalata dukkanin makaman yaƙinsu, sun zubar da su aƙas sun shiga amfani da tsagwaron ƘARFIN DAMTSE suna kaiwa juna naushi da bugu hannu da ƙafa.
Nan fa labari ya sha bamban domin a yanzu Najwas da kilimat basa iya kare naushin Uhaisu. Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne sarki Uhaisu ya shammace su gabza masu wawan naushi a fuska a lokacin da suka dako tsalle sama, take su kayi saman tamkar an janye su da ƙugiya, sannan su ka rikito ƙasa hancinsu na yoyon jini.
A ɓangaren su jaruma Nabihat kuwa ba haka al'amarin yake ba, domin kuwa sun zamewa shugaba Yesiran alaƙaƙai ya rasa yadda zai su da su, duk inda su ka sanya a gaba sai dai kaga MAZAJE na zubewa ƙasa matattu tamakar ana sassabe a gonar auduga.
A ɓangaren yarinya Lazimat kuwa, ta zamo tamkar shaiɗaniya a tsakiyar dakarun, ta wanzu tana aika rayukansu barzahu ta hanyar amfani da KWARI DA BAKAnta,
Ya zamana cewa duk hare-haren da ake kawo mata tana kare wa, tare da mayar da martani cikin zafin nama na ban al'ajabi, ta wanzu wajen ragargazar dakarun, a cikin wannan hali ne sai ta hango shugaba Yesiran ya rugo izuwa inda take hannunshi riƙe wata zabgegiyar adda mai baki biyu,
Koda ganin hakan sai tayi wata katantanwa a tsakiyar dakarun tayi fanka tana mai dukan ƙafafuwansu, a lokaci guda suka zube a ƙasa magashiyan suna aman jini,
sannan ta gyara tsayuwar ta tana mai jiran isowar shi,
Ya yin da rage saura taku goma tsakanin su sai shugaba Yesiran ya ja ya tsaya aka yi kallon-kallo na wani lokaci.
Yesiran ya jijjiga addar dake hannunshi sannan ya duba ɗayan da ya zama dungulmi,
take

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment