Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

FATAUCIN BAYI





















MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071










Haƙƙin mallaka
Mansur Usman Sufi
Shekarar bugu
2023


GARGAƊI


Ban yarda wani ya sarrafa min littafi ba ta hanyar yaɗa shi a soshiyal midiya, karantawa a rediyo ko manhajar YouTube, website da sauran su ba tare da izina na ba, yin hakan zai kai mu zuwa ga hukuma a kiyaye.
Ko kuwa zuwa babban mai sakamako Allah (SWT).


Sako daga
Sarkin Marubutan Yaƙi






GODIYA


Ta tabbata ga Allah SWT bisa iko da ya ba ni na rubuta wannan littafi mai taken FATAUCIN BAYI.
Tsira da amincin Allah ya ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama da iyalanshi tsarkaka.




SADAUKARWA


Na sadaukar da wannan littafi ga dukkanin masoyan Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama a ko ina suke a faɗin duniya.




Bugawa da yaɗawa SUFI PUBLISHING COMPANY
R/lemo Kano state Nigeria
08137237071










BABI NA ƊAYA




Ƙasaitaccen jirgin ruwa ne da aka cika shi maƙil da fursunoni maza da mata, manya da yara, gaba ɗaya an ɗaure hannayen da waɗansu irin murtuka-murtukan sarƙoƙi kuma an haɗa da katakon jirgin an ɗaure tamau, ta yadda babu mai iya tserewa daga cikin su.
Duba ɗaya za ka yiwa fursunonin ka fahimci cewa sun kasance jama'ar ƙabila ɗaya, abin da zai tabbatar maka da hakan shi ne yanayin ƙirar jikkunansu da kamanni gami da tufafin su iri ɗaya ne sak!
A wannan lokaci jirgin ruwan na tafiya ne a saman wani makeken teku, a kowace kusurwa a jirgin an zuba dakaru masu tarin yawa, suna shirye suke cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensu ɗauke da miyagun makamai, suna ta kai komo domin tabbatar da cikekken tsaro.
Sai da jirgin ya shafe tsawon sa'a biyu da daƙiƙa ɗari biyu yana tafiya a saman tekun ba tare da watsala ba, shi dai tekun ana yi mashi laƙabi da Baharul-sawara.
Ana cikin wannan tafiya ne wani garjejen ƙato daga cikin dakarun ya dubi wani badakare wanda da alama shine shugaban su ya risina a gare shi sannan ya buɗi baki ya ce "ya shugaba na ina ganin ya kamata a kwance waɗannan fursunonin a basu abinci domin sun galabaitu ainun, haƙiƙa a koda yaushe za su iya rasa rayuwar su, kuma sanin kan ka ne cewa mutuwar ɗaya daga cikin fursunonin tamkar rasa rayukanmu ne baki ɗaya''.
koda jin wannan batu daga bakin badakare Sharkar sai shugaba Yasiran ya dube shi cikin alamun matuƙar damuwa cikin wata irin kakkausar murya mai tattare da jarumtaka ya ce "ya kai Sharkar tabbas ka zo da shawara mai kyau, amma fa wani hanzari ba gudu ba, shin ba ka tsoron kwance fursunonin zai bada matsala a tare damu?
Koda jin wannan tambaya sai Sharkar ya bushe da dariya ya ce ''haba ya shugabana ka duba fa ka ga irin tsananin yawan mu, ta ya ya kake tsammanin cewa akwai wanda ya isa ya tsere mana.
Yanzu mafita ɗaya ce ta rage mana, ko dai mu bawa waɗannan fursunonin abinci domin su rayu, ko kuma mu ƙyale su yunwa da ƙishirwa su zamo ajalin su".
Sa'adda shugaba Yasiran ya ji wannan batu daga bakin Sharkar sai ya ce "tabbas zancen ka dutse ya kai Sharkar ya zama wajibi mu yi amfani da wannan shawara da ka kawo".
Yana gama faɗin hakan ya umarci waɗansu dakaru mutum arba'in suka kwance fursunonin mutum ɗari biyu, sannan suka rarraba masu wata bushasshiyar gurasa gami da wani ruwa mai yauƙi a matsayin abin kalacin su.
Dakarun na cikin aiwatar da hakanne wani badakare ya miƙawa wata yarinya gurasar.
Kafin hannunshi ya kai inda take, sai kawai ta shammace shi ta ciri wata siriyar wuƙa a damtsen shi ta soka mashi a marainanshi, sannan ta sanya ƙafafuwanta biyu ta daki a ƙirji, take ya hantsila izuwa cikin tekun yana mai tsandara ihu
Al'amarin da ya janyo hankulan sauran dakarun kenan, suka zubar da abincin suka zare makamansu suka ruga izuwa inda yarinyar take.
koda ganin hakan sai yarinyar ta ɗauko wata doguwar igiya cikin wani irin zafin nama ta yiwa igiyar wasu ƙulluna barkatai ta jefawa dakarun, sannan ta daka wawan tsalle ta faɗa izuwa cikin tekun tana riƙe da sauran igiyar a hannun ta, take igiyar ta zarge kafafuwan dakarun ta ja su izuwa cikin tekun.
Koda ganin hakan sai Sharkar ya dakawa sauran dakarun tsawa da su sake ɗaure fursunonin, kuma aka umarci masu tuƙin jirgin su tsayar da tafiya, sannan ya yiwa dakaru hamsin inkiya da hannu da su biyo bayan shi suka ruga izuwa bakin jirgin.
Ai kuwa koda tsayuwar su sai suka yi arba da gawarwakin 'yan uwansu dakarun da suka faɗa sun taso izuwa saman ruwa, gaba ɗayan su an yi masu yankan rago,
Al'amarin da ya yi matuƙar ba su mamaki kenan kuma ya harzuƙa su.
Abin da ya ba su mamaki shine ya za ayi a ce yarinya ƙarama ta samu ƙarfin damtsen da za ta yiwa zaratan dakaru sha biyar yankan rago.
Cikin matuƙar fushi Sharkar ya umarci dakaru goma waɗanda suka ƙware wajen iya ninƙaya a ruwa, suka faɗa izuwa cikin tekun domin laluben inda yarinyar ta shiga.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, domin da a ce waɗannan dabaru sun san abin da zai biyo baya da ba su gangancin faɗawa tekun ba, domin abin da ba su sani ba shi ne lokacin da suka faɗa tekun wani ƙaton kifi ya wangame bakinshi, yana hamma ai kuwa bisa sa'a sai suka faɗa ciki, kawai sai ya lamushe su ya yi loma ɗaya da su sannan ya yi nutso izuwa cikin tekun.
Nan fa ya zamana cewa Sharkar ya tura gaba ɗaya dakaru hamsin dake biye da shi izuwa cikin tekun, amma ɗayan su bai taso a raye ba.
Kwatsam Sai aka ga gawarwakin dakarun birjik sun taso daga ƙarƙashin tekun.
Al'amarin da ya ƙara firgita shugaba Yasiran da Sharkar kenan.
Kawai sai shugaba Yasiran ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu, sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da WASIƙAR MUTUWA, sannan ya buɗe bakinshi yana mai karanta waɗansu dalasiman tsafi, gami da yin nuni da ɗan yatsanshi izuwa saitin inda fursunar yarinyar ta faɗa.Take ruwan wajen ya daskare ya zama ƙanƙara, kawai sai ya zare waɗansu zabga-zabgan takubba a godon bayanshi, sannan ya dako wawan tsalle ya faɗa tekun yana mai yin nitso izuwa ƙarƙashin ta,
A dai-dai wannan lokaci ne rana ta take kuma ta yi zafi ainun, nan fa gaba ɗaya fursunonin suka shiga cikin mawuyacin hali, musamman ƙananan yara, suka fara faɗuwa ƙasa sumammu, wasu ma na sheƙawa barzahu, nanfa iyaye matan da 'ya'yansu suka mutu suka shiga rusa kukan baƙin ciki.
Inda a ce mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da wannan al'amari ke faruwa, dole ne tausayi ya kama shi ya zubar da hawaye.
Al'amarin shugaba Yasiran kuwa lokacin da ya yi nutso izuwa ƙarƙashin tekun Baharul-sawara, domin ya lalubo yarinyar fursunar da ta faɗa cikin tekun, sai ya shafe tsawon rabin sa'a yana dube-dube da kalle-kalle, amma bai ga inda ta shiga ba.
Al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan kuma ya fusata shi, ya cigaba da yin nutson.
Lokacin da ya zamana ya shafe sa'a biyu cur! Yana wannan bincike, kwatsam bazato babu tsammani sai ya ji an kirɓa mashi wawan naushi a wuya.
Saboda ƙarfin naushin sai da ya yi katantanwa sau uku, ya saki takubban dake hannunshi yana mai kurma wawan ihu.
Cikin baƙin zafin nama ya juya domin ya ga wanda ya naushe shi ɗin. Ai kuwa sai ya yi turus bakomai ya gani ba face yarinyar 'yar shekaru sha biyar, hannayen ta ɗauke zaratan takubban da suka suɓuce daga hannun shi.
Abu na farko da ya bashi mamaki shine ya aka yi wannan yarinya ta samu ƙarfin damtsen da ta hallaka dakarun tamkar takasance basadaukiya mace mai kamar maza.
Koda ya zo nan a tunanin shi sai jikinshi ya kama tsuma yana ƙyarma, idanunshi suka kaɗa suka yi jajur, gashin jikinshi ya mimmiƙe.
Kawai sai ya zare waɗansu takubban na daban a damtsen shi, yana mai yin iyo ya durfafi inda take yana shaƙar numfashi ta hanyar amfani ƙarfin sihiri.
Koda ganin hakan sai yarinyar ta gyara riƙon wani mazirari a bakinta da take amfani da shi wajen shaƙar iska. Lokacin da suka haɗu sai suka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban al'ajabi.
Shugaba Yasiran da fursunar suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JUTIYA DA BAJINTA ta ban mamaki.
Babu abin da zai burge mutum ga jaruman biyu irin yadda suka kaiwa juna hare-hare cikin zafin nama tamkar na'ura ce ke sarrafa su.
A wasu lokutan sai kaga sun taso izuwa saman tekun.
A cikin jirgin ruwa kuwa
koda sadauki Sharkar ya ga an shafe tsawon sa'a biyu bai ji ɗuriyar shugaba Yasiran, kuma ya ga yadda fursunonin na sheƙawa barzahu sai hankalinshi ya dugunzuma ainun, ya rasa abin da yake yi mashi daɗi, domin hakan za su iya rasa rayuwar su baki ɗaya idan har su ka isa ga sarki.
Nan take ya faɗa izuwa kogin tunani domin samun mafita, abu na farko da ya faɗo masshi shine, shin yanzu zai sake ƙwance fursunonin ne ya ba su abinci da ruwan sha domin su rayu? Ko zai ƙyale su, sannan ma yanzu za su cigaba da tafiya ne ko kuwa za su jira fitowar shugaba Yasiran daga cikin tekun.
Sa'adda Sharkar ya zo nan a tunanin shi, sai kwakwalwarshi ta saƙe dagulewa, da ƙyar da siɗin goshi ya samu mafita.
Koda samun mafitar sa kawai ya juya ya nufi wani ɓangaren a jirgin, ya umarci waɗansu dakaru mutum ashirin ya ce su buɗe wani katon murfi, take dakarun su ka cika aikin su suka murfin, sai ga wata matattakala guda goma ta bayyana wacce ta zata shigar da mutum zuwa ƙasan jirgin, sannan Sharkar ya yiwa dakarun wata inkiya ta wutsiyar idanu.
Kawai sai suka kwance fursunonin suka shigar da su izuwa ƙarƙashin cjirgin, sannan ya yi umarni da a basu abinci da abin sha.
Sannan ya juya yana hangen inda shugaba Yasiran ya yi nutso izuwa cikin tekun Baharul-sawara.
A ɓangaren shugaba Yasiran da wannan fursuna kuwa, sun wanzu suna bawa hamata iska suna kaiwa juna hare-hare, gaskiyar masu iya magana da suka ce, duk wanda ya riga ka kwana dole ne ya riga ka tashi.
Nan fa yazamana idan shugaba Yasiran ya kaiwa yarinyar hari idan ta kare harin da takubbanta sai ka ga ta durkushe ta nutson izuwa ƙasa, amma ta sake taso sama, nan fa ya zamana ta fara galabaita ainun, ya zamana bata iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kanta, domin daƙyar take iya shaƙar iska.
Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne Yasiran ya shamma ce ta ya yanke ta da takobinshi a gadon bayanta. Nan take inda ya yanke ta ya haddasa wani lafcecen rauni, jini ya kwaranya, saboda tsananin zafi da zugi sai da ta tsandara ihu.
Sannan ta saki takubban dake hannunta, jikinta ya sandare tamkar babu rai tare da ita.
Al'amarin waɗannan dakaru kuwa suna cikin rabawa fursunonin abincin ne sai waɗansu zaratan yan mata guda ashirin waɗanda suka ƙware ainun a fagen sarrafa takobi da sanin dubarun yaƙi, su ka shammaci dakarun suka afka masu da yaƙi, cikin ƙanƙanin lokaci suka hallaka dakarun ta hanyar murɗe masu wuya.
Koda samun wannan nasara sai wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa mai annurin fuska da kwarjini daga cikin 'yan matan, ta dubi wasu 'yan matan daban a cikin fursunonin ta ce da su "ina so ku cigaba da baiwa jama'ar mu wannan sauran abinci, kuma ko me zai faru dar ku kuskura ku fito daga cikin wannan ɗaki, ko ku kira sunayenmu, kawai ku kira sunayen ababan bautarmu.
Ina so ku yi sani cewa ɗayan mu ba zai dawo nan ba face mun tserar da sauran rayukan jama'ar birnin mu kuma mun ɗauki fansa akan sarki Husnalu".
Koda kyakkyawar budurwar ta zo nan azancenta sai jama'ar suka cika da matuƙar farin ciki mara musaltuwa.
Sannan budurwar ta zira hannunta a aljihun riga ta ɗauko hodar banju ta miƙa wa sauran 'yan matan ta ce da su "wannan hodar zamu yi amfani da ita ne kafin mu kai ga ɗaukar makaman yaƙi ina fatan kun fahimce ni, tana gama faɗin hanak sai ta juya ta shige ba sauran suka mara mata baya.
Su na fita sai suka shiga yin sanɗa da laɓe-laɓe, suka nufi madafa.
Lokacin da kyakkyawar budurwa da ake kira Nabihat suka iso izuwa bakin madafar, sai Nabihat ta ɗauko hodar banju a cikin aljihun rigarta ta busa ta izuwa ciki, jim! Kaɗan sai suka kunna kai ciki suna shiga suka tarar dakaru masu dafa abinci sun kama barci mai nauyi.
kawai sai suka cire tufafin su suka maye da na dakarun, sannan suka rufe fusakunsu da hulunan ƙarfe.
Kawai sai suka matsa izuwa inda dakarun suka ɗora sanwa akan wuta suka buɗe murafun tukunyoyin suka zazzaga wannan hodar banju a cikin, sannan suka mayar suka rufe ruf.
Bayan shuɗewar daƙiƙa goma sai suka zuzzuba abincin a cikin waɗansu ƙananan akushi, suka ɗora akan farantai na azurfa, sannan juya suka fice daga tantunan suka shiga rarrabawa dakarun dake cikin jirgin ruwan abincin mai dauke da hodar banjun har suka iso izuwa inda wani sadauki yake.
Nabihat ta ɗauki akushi ɗaya ta miƙa mashi ya karɓa ya bude ya sanya hannunshi ya yi loma ɗaya, kawai sai ya dubi Nabihat ya ce "ya kai Himairu ya aka yi abincin nan ya yi ɗan karen daɗi haka?
Koda jin wannan tambaya sai Nabihat ta yi murmushi gami da gyaɗa kai, kawai sai ta huce gaba ba tare da bawa sadaukin amsar tambayar shi ba.
Haka dai suka cigaba da rabawa dakarun abincin, har suka iso inda suka bar saduki Hushaibu. Nabihat ta ɗauki akushin ta miƙa mashi ya karɓa.
Har Hushaibu ya buɗe da nufin cin abincin kwai ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi, kawai sai ya yi jifa da akushin ya durfafi madafa cikin hanzari.
A dai-dai lokacinne su jaruma Nabihat suka kammala raba abincin suka samu wata maɓuya a cikin jirgin suka laɓe.
A fusace Hushaibu ya kunna kai izuwa cikin tantin, ai kuwa sai ya yi arba da masu dafa abincin kwance suna sharar barci babu tufafi a tare da su.
Cikin matuƙar fushi gami da tashin hankali ya zare takobinshi ya ruga izuwa waje yana mai ƙwallawa sauran dakarun kira.
Al'amarin da ya janyo hankalin sadauki Sharkar kenan ya zare takobinshi da nufin dakawa dakarun tsawa.
A dai-dai wannan lokaci ne hodar banjun da su Nabihat suka zuba a cikin abincin ta fara bugar da dakarun suna ɓingirewa kasa suna sharar barci.
Kafin Sharkar da Hushaibu su farga fiye da rabin dakarun dake cikin jirgin ruwan sun kamu da barci mai nauyin gaske, cikin matuƙar kaɗuwa gami da tashin hankali sadauki Sharkar ya cigaba da falfala azababban gudu, yana mai kurma wawan ihu
Nan fa sauran dakarun da ba su kai ga cin abincin ba suka firgice suka ɗauko makaman yaƙin suka dinga fitowa daga kowace kusurwa a jirgin.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga su jaruma Nabihat da sauran 'yan matan fursunonin sun yo fitar burgu daga maɓuyar su suna, suka yi ɗauki izuwa kan dakarun suna ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Koda ganin hakan sai dakarun suka yi ɗauki kansu suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA a filin daga.
Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan zaratan 'yan mata su ashirin kacal! Suka tunkari ɗaruruwan dakarun dole ne ya cika da mamaki kuma ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA, mata masu kamar maza.
Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro daban al'ajabi.
Nan fa gaba ɗaya jirgin ruwan ya yamutse da ƙarar haɗuwar makaman yaƙi, gami da ihu da kururuwar mazaje.
Nanfa Nabihat da 'yan matan fursunonin suka wanzu suna kaiwa dakarun sara da suka cikin matuƙar zafin nama tamkar jikkunan ba su kasance na jini da tsoka ba.
Cikin abin da bai gaza daƙiƙa arba'in ya zamana cewa sun samu nasarar hallaka fiye da mutum hamsin na dakarun sun rauna ta fiye da ɗari biyu.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin dakarun kenan kuma ya fusata su ainun, bisa ganin cewa a matsayin su na GWARAZAN MAYAƘA, amma a ce 'yan mata sun zame masu alaƙaƙai kuma GOBARAR ANNOBA.
Nan fa dakarun suka ZAGE DAMTSE wajen kaiwa su Nabihat miyagun hare-hare.
Ana cikin wannan artabu ne wani garjejen sadauki, ya kaiwa wata daga cikin 'yan matan wani wawan sara, da nufin tsinke mata wuya amma budurwa ta sunkuiya cikin zafin nama, takobin sadauki ta sari iska. Kafin ya sake mayar da martani, budurwar ta cire wata siriyar wuƙa a damtsenta s caka mashi a maƙogaranshi, sannan ta sanya ƙafarta ɗaya ta daki ƙirjin shi da dukkan ƙarfin ta.
Saboda da matuƙar ƙarfin dukan sai da ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya ya faɗa cikin tekun yana mai tsandara ihu.
Kawai sai budurwar ta sake afkawa cikin dakarun ta ci-gaba da saran su.
Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne SADAUKi Sharkar ya samu nasarar make Nabihat ta faɗi ƙasa, magashiyan nunfashin ta na fita daƙyar, kawai sai ya sanya hannunshi ya damƙo wuyanta ya tattare dukkanin karfinshi da nufin karya wuyan Nabihat.


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment