Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abubuwan da suka faru tsakanin shi da yarinya Lazimat a ƙarƙashin tekun Baharul-sawara, ya dunga dawo masa a cikin kwanyarshi.
Daga can sai hawayen baƙin ciki su ka kwaranyo daga idanuwan shi, kawai sai ya taƙarƙare ya kwarara ihu ya afkawa Lazimat da dukkanin ƙarfin shi suka garƙame da masifaffan yaƙi.
Lokacin da su mafarauci Najwas suka fahimci cewa wankin hula zai kai su dare, idan aka cigaba da wannan yaƙi a haka za'a iya yin ragas ko ayi kare jini biri jini.
Sai su ka zurfafa izuwa cikin kogin tunani domin samun mafita. Koda samun mafitar sai suka ja da baya sannan suka rugo da gudu suka haɗa ƙarfin su waje guda suka gabzawa sarki Uhaisu wawan naushi a fuska da hannayensu biyu,
saboda ƙarfin naushin sai da sarki Uhaisu ya tuntsira baya har sau uku ya kife a ƙasa yana aman jini, sannan suka shiga da naushi.
Nan fa Uhaisu ya dunga kwarara wawan ihu sakamakon naushin dake ratsa sassan ƙasusuwan jikinshi, fuskarshi duk ta daddauje jini na zuba.
A ɓangaren Lazimat da shugaba Yesiran kuwa sun cigaba da kaiwa juna miyagun hare-hare da niyar hallaka juna,
Idan Yesiran ya kaiwa Lazimat sara da addarshi, idan ta kare harin sai ta durkushe ƙasa saboda bambancin ƙarfin a bayyane yake,
Ana cikin wannan yaƙi ne Yesiran ya shammaci Lazimat ya yanke ta da addarshi a kwiɓin cinyarta ta dama jini ya yi tsartuwa. Lazimat ta ƙwalla ƙara sakamakon zafi da raɗaɗin da ta ji. Sannan ta mayar da martani cikin gwanin ta, nan take ta yanki Yesiran a damtsen cinyarshi ta hagu jini ya kwaranya.
Haka su ka cigaba da wannan ɗauki ba daɗi ya zamana cewa sun yiwa junan su rauni fiye da biyar dukkanin su jiri na ɗibar su suka kife a ƙasa magashiyan, ma'ana dai an yi RAGAS tsakanin su
A dai-dai wannan lokaci ne Nabihat suka samu nasarar hallaka gaba ɗaya dakarun dake fadar,
ya yin da Nabihat ta hango halin da Lazimat ke ciki sai ta ruga izuwa inda take kwance ta ɗauke ta ta goyata a gadon bayanta, sannan ta kama ingarmar doki ta haye 'yan matan fursunonin suka yi koyi da ita, suka sakar masu linzami suka sukwane su a guje suna masu ficewa daga fadar.
A dai-dai wannan lokaci ne mafarauci Najwas da matarshi kilimat suka dako wawan tsalle daga kan ruwan cikin sarki Uhaisu suka dira a can gefe, cikin wani irin baƙin zafin nama suka kama dawakai suka haye suka rufawa su Nabihat baya suka fice daga fadar.
Lokacin da mafarauci Najwas suka samu nasarar tserar da rayuwar su jaruma Nabihat daga fadar sarki Uhaisu, sai suka wanzu suna ratsa layuka da unguwannin birnin har suka samu nasarar ficewa daga birnin baki ɗaya, suka nausa izuwa cikin daji suna tsala azababban gudu a bisa dawakansu.
Tafiyar daƙiƙa arba'in kacal suka yi suka iso wata mararrabar hanya guda biyu a dajin, hanyar ta farko ta gangara ne izuwa wani waje mai ɗauke da kwazazzabai, ta biyun kuwa ta durfafi wata sahara.
Ya yin da aka ga waɗannan hanyoyi biyu sai aka ja linzamin dawakai aka tsaya cak! da tafiya, mafarauci Najwas ya buɗi baki ya yi gyaran murya ya dubi jaruma Nabihat cikin alamun matuƙar damuwa ya ce "ya ku wadannan jarumai yanzu ga shi mun iso mararrabar hanya shin yanzu wacce ya kamata mu bi?
Koda jin wannan tambaya sai kowa ya yi shiru aka rasa wanda zai ce kala,
sai daga bisani ne jaruma Nabihat ta buɗi baki cikin damuwa ta ce "waccan hanya mai ɗauke da sahara babu alkairi a cikinta, domin ba za mu damu ruwan sha, da 'ya'yan itace da zamu yi kalaci ba.
Ita kuwa mai ɗauke da kwazazzabai dole ne a samu halittu masu cutar wa a cikin ta ba, amma dole ita za mu bi''.
Koda jin wannan batu daga bakin Nabihat sai kowa ya na'am da hakan, aka sakarwa dawakai linzami aka cigaba da tafiya, ana cikin wannan tafiya ne aka iso wani waje mai tattare da duhuwa a dajin, kwatsam! Sai aka ga ganyayyakin bishiyun motsawa,
alamun dake nuni da wani abu mai rai na shirin bayyana.
kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu irin mutane bila-adadin suna fitowa daga duhuwar bishiyun suna masu yiwa su Najwas ƙawanya.
Sa'adda su mafarauci Najwas su ka yi arba da mutanen sai suka raza ainun, domin a iya tsawon rayuwar su ba su taɓa ganin dakaru masu kwarjini tamkar su ba.
Su dai mutane sun kasance girɗa-girɗa masu ƙirar samudawan farko, suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro,
fusakunsu a murtuke suke tamkar ba su taɓa dariya ba, hannayensu rike da makamai dangin gatari, majaujawa, al'amudi da takobi.
Haƙiƙa waɗannan dakaru sun cika ababan tsoro.
Domin ƙaramin jarumi ba zai iya haɗa idanu da su ba face JARUMIN ƘWARAI mai dakakkiyar zuciya, a hankali mayaƙan su ka cigaba da matsowa kusa da su Najwas sai da ya rage saura kamar taku goma sannan su ka ja suka tsaya cak!
Sannan suka dare gida biyu suka buɗe wata 'yar siririyar hanya a tsakiyar su,
Jim kaɗan sai ga wani garjejen ƙato ya da nunka sauran dakarun girma da kwarjini gami da cika idanu.
Idununshi ɗaya a makance yake ya jirkice ya zama fari gaba ɗaya. Ya fito gaban dakarun yana mai tako lafka-lafkan kafafuwanshi.
Sannan ya ja ya tsaya cak yana mai ƙarewa su Najwas kallo, kawai sai ya bushe da dariyar mugunta sannan daga bisani kuma ya murtuke fuska tamkar an ai ko mashi da WASIƘAR MUTUWA ya shaƙi iska da manyan ƙofofin hancinshi masu kamar da mazirari ya busar, sannan ya buɗe tafkeken bakinshi mai kama ƙofar gari cikin wata irin kakkausar murya ya ce " shin wane rashin sani ne yasa ku shigowa wannan daji, shin ba ku da labarin cewa nan ce fadar sarkin ɓarayi na wannan nahiya baki ɗaya.
Kuma alamu sun nuna cewa ku ba fatake ba ne bakwa ɗauke da wani abu da ya danganci dukiya ko da za a amfana da shi, hakan ya tabbatar min da cewa kenan ɗayan ku ba zai tsira da rayuwarshi ba''.
Koda jin wannan batu daga bakin shugaban dakarun sai mafarauci Najwas ya tari numfashinshi yana mai daka mashi tsawa cikin ƙarfin hali ya dube shi ya ce ''shin wane ne kai a jerin JARUMAN DUNIYA da har za ka kira kanka da shugaban 'yan fashin wannan nahiya, ka sani cewa kawar da mu ba abu ne mai sauƙi ba''.
Da jin wannan batu daga bakin Najwas sai badakaren ya fusata ainun ya dakawa mashi tsawa wacce ta firgita dukkan wata halitta dake wajen, sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA ya dubi Najwas ya ce "tabɗijan! Wai yanzu a duniyar nan har an samu jarumin da zai tsaya a gaba na yana faɗa min baƙaƙen maganganu, ya kai wannan jarumi tabbas ka sayi ajalinka da kuɗinka, Amma kafin hakan zan sanar da kai ko ni wane ne kamar yadda ka buƙata.
Suna na Mazabir ibn Sharr shugaban 'yan fashin wannan nahiya baki ɗaya.
Koda gama faɗin hakan sai sadauki Mazabir ya shammaci mafarauci Najwas ya gabza masa wawan naushi a fuska,
take Najwas ya sulalo ƙasa daga kan dokinshi yana mai aman jini.
Al'amarin da ya harzuƙa zuciyar kilimat da su jaruma Nabihat kenan suka zare makaman su domin su afkawa sadauki Mazabir.
Amma sai suka ga Najwas ya daga masu hannu yana mai nuna cewa su dakata.
Sannan ya yunƙura ya miƙe tsaye yana gyara tsayuwarshi da riƙon takobin dake hannunshi, sannan ya furzar da gudan jini daga bakinshi ya dubi Mazabir ya ce "ya kai Mazabir ka yi sani cewa ni kaɗai zan iya kashe yaranka baki ɗaya ba tare da ka samu nasarar taɓa lafiyar ɗaya daga cikin 'yan uwana ba''.
Koda jin wannan batu daga bakin Najwas sai Mazabir ya bushe da dariyar mugunta ya dubi Najwas a karo na biyu ya ce "dakyau SARKIN SADAUKAI haƙiƙa ka tabbatar min da cewa kai GWARZON NAMIJI ne, to ai ga fili ga mai doki, kuma sai an gwada akan san na ƙwarai''.
Koda gama faɗin hakan sai shugaban 'yan fashi Mazabir ya yi wa yaran shi inkiya ta wutsiyar idanu dake nuna cewa kada su kuskura su yaƙi su jaruma Nabihat.
Take dakarun suka ja da baya suka buɗe masu wani fili, kamar haɗin baki Najwas da Mazabir suka ruga izuwa kan juna suna ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Lokacin da ya zamana cewa saura taku goma a tsakanin su nan take Najwas ya zamo ɗan wada a gaban Mazabir, saboda yadda Mazabir ya nunka shi a girma da tsawo. Mazabir ya zare wani al'amudi a jikinshi.
Ana haɗuwa aka rincaɓe da masifaffan artabu, suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JUTIYA DA BAJINTA ta ban mamaki, sai da aka shafe sa'a ɗaya cur ana wannan fafatawa amma babu nasara ga ZARATAN MAYAKAn biyu.
Al'amarin da yayi matuƙar ɗaurewa shugaban 'yan fashi Mazabir kai kenan kuma ya ba shi mamaki, domin fiye da shekaru ashirin suna gudanar da wannan sana'a ta su ta fashi da makami, amma bai taɓa haɗuwa da jarumi mai zafin nama da juriya tamkar Najwas ba.
Haƙiƙa yau ya gamu da gamon shi.
Sa'adda Mazabir ya zo nan a tunanin shi sai zuciyar shi ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone ta faso ƙirjinshi ta fito waje, sai kawai ya sake zare wani makami a jikinshi mai kama da lauje mai matuƙar tsawo gami da kaifin tsiya ya cigaba da kaiwa Najwas sara da suka ta ko ina.
Sa'adda kilimat, Nabihat da sauran fursunonin su ka ga yadda shugaban 'yan fashi Mazabir ke kaiwa Najwas miyagun hare-hare sai hankulan su su ka dugunzuma ainun.
An cikin wannan hali ne Mazabir ya shammaci mafarauci Najwas ya danƙara mashi wani sara da wannan makami na shi a cinyarshi ta dama, jini yayi tsartuwa Najwas na ƙwalla ƙara sakamakon zafi zugi da raɗaɗin da ya ji a cinyarshi.
Kafin Najwas ya sake wani yunƙuri Mazabir ya sake kafta mashi wani saran a karo na biyu a hannunshi jini ya zuba.
Ya yin da Najwas ya ga halin da yake ciki sai ya faɗa izuwa Kogin tunani domin samun mafita.
Koda samun mafitar sai kawai aka ga ya daka tsalle sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan ya ya sanya ƙotar takobin shi ya daki kan Mazabir da dukkan ƙarfin shi,
saboda ƙarfin dukan sai da Mazabir ya kurma ihu sannan ya runtuma da ƙasa, amma saboda juriya da nacin tsiya sai ya zumbur ya miƙe tsaye. Cikin gwanin ta Najwas ya kama reshen wata bishiya a lokacin da ya yi ƙasa zai faɗi, sannan ya yi sufa yana riƙe da reshen ya durfafo inda Mazabir ya ke ya shammace shi ya sake maka mashi ƙotar takobin a ƙeyarshi
Mazabir ya kurma wawan ihu ya faɗi ƙasa da rubda ciki.
A dai-dai lokacin da Najwas ya dira a gadon bayanshi ya riƙe hannayenshi ya banƙara su ta baya.
Nan fa Mazabir ya shiga ƙoƙarin ƙwacewa daga hannun Najwas amma sai abu ya gagara ya ci-gaba da kurma wawan ihu domin ji yake tamkar najwas zai ɓalla masjid hannaye.
Tabbas in da a ce mutum ya na tsaye a wannan waje ya ga irin bajintar da Najwas ya yi dole ne ya jinjina mashi, bisa ganin yadda ya danne garjejen basamuden ƙato ya hana shi rawar gaban hantsi,
Ya yin da Mazabir ya ga cewa Najwas yana yunƙurin yanka mashi wuya ta baya da wata 'yar siririyar wuƙa, sai ya buɗi baki cikin matuƙar galabaita ya ce "ina roƙon ka ya kai wannan jarumi da kar ka kashe ni na yarda cewa kai shugaba na ne kuma duk abin da kake so shi za'a yi nayi maka rantsuwa da rayuwa ta.
Koda jin wannan batu daga bakin Mazabir sai Najwas ya ce "bazan yarda da abin da ka faɗa ba har sai ka umarci yaranka da su zubar da makamansu.
Da jin hakan sai Mazabir ya ɗaga kanshi kaɗan yana daga kwancen a lokacin da idanuwanshi suka kaɗa suka yi jajur tamkar garwashin wuta, cikin kakkausar murya ya dubi yaranshi ya ce "na umarce ku da ku zubar da makamanku''.
Koda jin wannan batu daga bakin shugaba Mazabir sai gaba ɗaya 'yan fashin suka ajiye makaman su suka durƙusa a ƙasa bisa gwiwoyin su suna masu yin MUBAYA'A.
Ya yin da Najwas ya ga cewa dukkanin 'yan fashin sun miƙa wuya sai ya tashi daga kan gadon bayan Mazabir ya na mai duban kilimat da su Nabihat yana mai yi masu murmushin samun nasara.
Da ya ke a wannan lokaci duhun magariba ya fara kawo kai sai Mazabir ya umarci yaranshi suka sanyawa Najwas magani a raunukan sa, da yarinya Lazimat dake cikin mawuyacin hali sakamakon artabun da ta fafata da shugaba Yesiran a can fadar sarki Uhaisu.
Duk wani abu da su Najwas suke buƙata 'yan fashin ke kawo masu hatta abin kalaci da taceccen ruwan sha.
Shi kuma shugaban 'yan fashi Mazabir sai ya shiga aikin nemo manyan itace aka haɗa su Najwas tafkeken ɗaki domin su shiga ciki su huta, sannan ya rarraba 'yaran a kowacce kusurwa a dajin domin tabbatar da cikakken tsaro, shi kuma sai ya tsaya a ƙofar ɗakin da su Najwas ke ciki ya shiga yin rangadi, hannunshi riƙe da wata sharbebiyar Adda, ɗayan kuwa riƙe da wutar ice domin haskawa. Yana cikin wannan hali ne sai ya hango mafarauci Najwas ya tawo gare shi.
Koda ya iso daf da shi sai Mazabir ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa.
Najwas ya dube shi a nutse sannan ya yi gyaran murya ya ce "shin wane azzzalumin sarki ne ake kiran shi da suna Uhaisu?
Koda jin wannan tambaya daga bakin Najwas sai fuskar Mazabir ta murtuke tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA, ya dubi Najwas ya ce "ya shugabana ai wannan sarki da ka ambata babban abokin gabar mu ne, babu aminci ko yarda tsakanin mu da shi face yaƙi''.
Da jin wannan batu sai Najwas ya kwashe labarin da yarinya Lazimat ta ba su, da kuma abin da ya faru da su a fadar sarki Uhaisu lokacin da suka ceto su jaruma Nabihat tun daga farko har ƙarshe ya zayyanewa Mazabir.
Sa'adda Mazabir ya ji wannan batu daga bakin Najwas sai ya cika da matuƙar mamaki ya yi ajiyar zuciya ya ce "ya shugabana haƙiƙa ka zo mani da labarin da muka daɗe muna jira, wato hanyar da zamu bi wajen ɗaukar fansa akan sarki Uhaisu.
Ya shugabana tun da dai yanzu babban burin ku shine kawar da sarki Uhaisu, tabbas zama bai same mu yanzu zan haɗa dakarun yaƙi domin kai FARMAKIN BAZATO izuwa kurkukun Uhaisu domin mu ceto sauran fursunoni 'yan uwan su Nabihat.
Za mu bar yarinya Lazimat da 'yan uwanta biyu su kula da lafiyar ta, sauran dakarun mu za su yi gadin su, ka sani cewa babu abin da zai same ta a wannan daji.
Koda kuwa dakarun sarki Uhaisu ne domin akwai iyaka tsakanin mu dasu, haƙiƙa na san duk wata hanya da za mubi wajen shiga kurkukun ba tare da mun sha wata wahala ba, da zarar sun ceto fursunonin, sai kuma mu fara shirin yaƙi domin kuwa dole ne sarki Uhaisu ya kawo mana FARMAKIN BAZATO''.
Sa'adda Najwas ya ji wannan batu daga bakin Mazabir sai Najwas ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba Najwas ya juya ya shige izuwa cikin wannan ɗaki na su, shi kuwa Mazabir sai ya ƙwallawa wani badakare kira mai suna Hidairu.
Hidairu ya bayyana a gare shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa, Mazabir ya dube shi ya ce "ya kai Hidairu ayi maza a shirya mana dakarun yaƙi mutum dubu biyar domin zamu kai wata mamayar bazato";
Koda jin wannan umarni sai barde Hidairu ya ce "an gama ya shugabana". Yana gama faɗin hakan ya miƙe tsaye zumbur ya ruga izuwa wani ɓangare a dajin, jim kaɗan sai ga shi ya dawo tare da waɗansu ZARATAN MAYAƘA shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensu riƙe da miyagun makamai suna zaune a bisa dawakai fusakunsu rufe ruf da hulunan ƙarfe.
A dai-dai wannan lokaci ne mafarauci Najwas tare da matarshi Kilimat, jaruma Nabihat da mutum uku daga cikin waɗannan 'yan matan fursunonin shirye cikin shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro suka durfafo wajen.
Koda ganin hakan sai wani barde dake tsaye a can gefe guda hannunshi riƙe da takobi,
ya janyo wani ingarmar doki ya kawowa su Najwas da Mazabir suka kama suka haye.
Cikin hanzari Najwas da Mazabir suka sakarwa dawakansu linzami suka shige gaba, Kilimat, jaruma Nabihat da 'yan mata uku suka mara masu baya dakaru a ƙarshe, aka fara tsala azababban gudu na keta sa'a ana ratsa duhuwar bishiyu gami da ƙoramu da kwazazzabai.
Da yake a wannan lokaci dare ya tsala akwai matuƙar duhu, sai wa su daga cikin dakarun suka kunna fitilar ice suka riƙe a hannayensu.
Lokacin da aka iso wani waje mai tattare da waɗansu duwatsu 'yan madaidaita sai Mazabir ya ja linzamin dokinshi ya tsaya ya kama ya sakko ƙasa, take kowa ya yi koyi da shi aka tsayar da tafiya.
Mazabir ya tsugunna ƙasa ya sanya hannayenshi ya ɗauke waɗansu duwatsu dake wajen ya shiga kwashe ƙasar wajen,
jim kaɗan da fara aiwatar da hakan sai ga wata makeken murfi ya bayyana a wajen da aka yi shi da zallar baƙin ƙarfe.
Cikin baƙin zafin nama Mazabir ya sanya hannayenshi biyu ya buɗe murfin, sai ga wata matattakala da zata shiga izuwa ƙarƙashin ƙasa, nan fa su Najwas suka cika da matuƙar mamaki maral-musaltuwa.
Mazabir ya juya ya dubi Najwas da mutum dubu uku daga cikin yaranshi ya ce "duka za ku ajiye dawakan ku anan mu shiga izuwa wannan ƙofa, sannan ya dubi sauran yaran ya ce "Ku kuma ku tsaya anan ku jira har mu fito daga wannan ƙofa ina jan kunnenku da ku kiyayi saɓawa umarni na.
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Mazabir ya shiga cikin wannan kofa yana mai taka matattakalar. Najwas, kilimat, 'yan matan uku da dakaru suka mara mashi baya, suna masu kunna kai cikin Kofar, tafiyar daƙiƙa latalin kacal aka yi aka iso ƙarshen matattakalar. Nan take aka yi arba da wata ƙatuwar ƙofa Mazabir ya matsa daf da ita ya ƙwanƙwasa sau biyu.
Daga can sai wata 'yar siririyar taga ta buɗe a saman ƙofar wani badakare mai turɓunanniyar fuska ya leƙo da kanshi ya buɗi baki da nufin ya ce wani abu sai Mazabir ya cire hular ƙarfen dake kanshi,
Koda badakaren ya yi arba da fuskar Mazabir sai ya sakar mashi wani ƙeƙashasshen murmushi da ya ƙara wa fuskarshi muni cikin wata irin kakkausar murya ya ce mai kama da haushi kare ya ce "barka da zuwa ya shugabana".
Badakaren ya mayar da kanshi ciki, jim kaɗan sai aka ji ƙarar zare sakatun kofar, zuwa can sai ta buɗe.
Mazabir, Najwas, kilimat, yan mata uku wato Shamirat, Luwaisat, Zulfirat da dakaru dubu uku suka kunna kai izuwa ciki aka cigaba da tafiya, duk inda suka huce sai kaga dakaru na zube kasa suna kwasar gaisuwa ga Mazabir.
Nan fa su Najwas suka cika da matuƙar mamaki da al'ajabi, bisa ganin yadda Mazabir ya tsara wannan hanya ta cikin ƙarƙashin ƙasa domin kawai yana shirya hanyar da zai bi wajen ɗaukar fansa akan sarki Uhaisu.
Haka dai aka cigaba da wannan tafiya har ya zamana an kawo ƙarshen wannan hanya an tarar da wata ƙofa.
Cikin hanzari waɗansu ZARATAN MAYAƘA suka buɗe ƙofar aka fita izuwa waje.
Ya yin da aka fito nan take aka tsinci kai a cikin birnin Darul-kashmal, kuma a kayi arba da kurkukun Mautul-shammar.
Mazabir ya yi gyaran murya umh! Sannan ya dubi Najwas ya ce "yanzu ga shi mun iso kurkukun Mautul-shammar, ya zama wajibi mu zage damtse wajen yaƙar dakarun kurkukun, mu ceci rayuwar al'ummar su Nabihat, mu koma izuwa sansanin mu domin mu sake sabon shirin yaƙi a gobe.
Koda jin wannan batu daga bakin Mazabir sai Najwas ya gyaɗa kai, sannan ya zare wata sharbebiyar takobi daga cikin kuben ta ya durfafi ƙofar kurkukun. Mafarauci Najwas, Kilimat, Nabihat, Shamirat, Luwaisat, Zulfirat da dakaru dubu uku suka yi koyi da shi suka zare makamansu suka rufa mashi baya.
Lokacin da ya zamana saura kamar taku goma tsakanin su da kurkukun, su Najwas suka yi arba da dakarun dake tsaron kurkukun sai suka firgice ainun, su dai waɗannan dakarun sun kasance zabga-zabga tamkar samudawan farko, suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, hannayensu ɗauke da waɗansu miyagun makamai, suna ta kai komo tamkar za su ci babu.
Mazabir ya ɗaga takobinshi sama yana mai yiwa dakarunshi wata inkiya, kawai sai dakarun suka zaro kibiya suka saka a cikin bakansu suka ja suka ɗame sannan suka harba su izuwa dakarun dake saman ganuwar ƙofar kurkukun.
Nan take suka hallaka fiye da rabin dakarun, kuma fitilun dake wajen suka ɗauke, wajen ya yi duhu dunɗum!
Ta yadda mutum ba zai iya hango wanda ke nesa da shi ba, a dai-dai wannan lokaci ne su Najwas suka ƙarasa ƙofar kurkukun suka hallaka dakarun ta hanyar yi masu kisan sunƙuru, suka murɗe masu wuya ba tare da dakarun dake cikin kurkukun sun ji ihun su ko wani sautin ƙara ba.
Kafin cikar rabin sa'a sun hallaka dakarun sun ɓalle ƙofar kurkukun ta ƙarfin tsiya suka kunna kai ciki.
Ya yin da dakarun kurkukun suka yi arba da su Najwas sai suka zare makaman su suna ihu da kururuwa mai firgitarwa suka rugo izuwa kan su. Ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro.
Ɓangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JUTIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance.
Ana fara wannan arbu ne dakarun suka fahimci cewa tabbas

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment