Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"yanzu fah ka ga ma yi min faɗa ban kai ma ruwan wanka ba"yace "shikenan ke kuma ba ki da wannan fasahar ta Mata ta karantar abin da miji ke buƙata sai shirme"ta ɓata fuska tace "to ni na san mi kake so kuma"ya bata amsa da "ke na ke so!Yau kusan sati guda dan baƙin ciki kin ƙi tafiya a cire miki zaren balle ki bani haƙina,yanzu dai duk ba wannan ba zo kwanta min a nan ina son jin ƙamshin jikinki"ya nuna mata bed,Badiya tayi tsaye ƙiƙam sai da ya zo ya ɗorata da kan shi.Sosai BASHEER ya bata kulawa ta musamman,shi ɗin mai yawan buƙata ne dole sai da ƴan dabaru amma kasancewarta sokuwa sam ba ta maida hankali....
[07/10 à 10:09] MRS SADAUKI 💫: *BASHEER...*🌼

MRS SADAUKI💫✍🏻

Page 21-22

Dayawan mata sakaci da rashin sanin ya za su tafiyar da rayuwar aurensu ke sa a kawo masu kishiya.To kusan hakan ne ga Badiya,bayan kasancewarta matsoraciya sam ba ta iya wata kissa ba ballantana zance ya zan yi na burge miji.
Cikin jin haushin wannan ƙauyancin nata BASHEER ya yi biris da ita ya sauka daga bed ya zauna ƙasa tare da jawo abincin da tarar Badiyar na ci.Sai da ya canye shi tass kafin ya ce "je ki kai min ruwan wanka" ta yi jimmm kafin tace "ka jira har a jima mana"
"Yanzu nake son yi"
"Don Allah Ya BASHEER ..." Ya yi saurin katse ta da "Badiya ki kai min ruwa na ce,ina wasa da ke ne?"

"Allah kunya nake ji su Sa'adiyya na nan gindin icce,ɗazu sun ga na kai ma ruwan wanka fa,yanzu kuma a ƙara ganina na kai wasu?"
Basheer yace "to sai aka yi yaya kuma?"ta sunne kai kafin tace "ai za su gane mun yi wani abu" Basheer ya ƙanƙance ido yace "au !Yin sunnar Manzon kike ji ma kunya?Daga cikin su akwai uban da ya cika min kuɗi da zan auren ki?"
Badiya tace "don Allah ka yi cikin ɗaki ka ji"wani banzar kallo yayi mata wanda yasa ta fita ba ta shirya ba,ta cika bokitin ta kai masa banɗaki a kunyace ta bi ta gaban su Sa'adiyya uwanda suke ƙus-ƙus.


Sa'diyya ta kece da dariya tace "kin ga bari na tashi na shiga kewayena"ta na gama faɗa ta bar Mariya nan zaune wacce ita kuma ta sha alwashin babu inda za taje sai ta ga fitowar Basheer.
Ta na nan zaune ya shiga yayi wanka ya fito,tun daga nesa ta ke ƙare masa kallo ,sam ta kasa gane don shi take ko kuwa kawai dai ya na burge ta ne? Basheer kuwa ko gaisu haka ya wuce part ɗinsa,kuka ya tarar Badiya na yi bai tambaye ta ba yayi shirinsa ya fice.




Ya na zuwa gun aikin lebarancinsa amma abun mamaki sai ya tarar da ogansu ya zuba sabbin ma'aikata.Ya ƙarasa ya gaishesa Oga ya juye kai gefe kafin ya fara magana "na sauya ma'aikata tunda ku daɗi yayi muku yawa a kullum in na baku kuɗi sai kun yi ƙorafi,in kuma na gusa ku yi ta gulmata ku na cacakar namana wannan ya saka na ɗauko hayar ma'aikata daga Nigeria uwanda suka san daɗin dala kuma ka ga na gani ma har aiki sun fi ku iyawa.Dama can ba ku iya komai ba sai ɗan banza surutu da cin abinci shikenan sai kewaya wa yin kashi"


Tsabar zuciya Basheer bai san lokacin da ya bangaji Oga ba yace "dallah can banza wanda yayi ƙaton ciki da kuɗin haramun,shine mi in ka hana mu aiki?To ka hana mu numfashi in ka isa" Oga yace "eh naji dai a tafi ma'aikata ne dai na kuma canza"




Zuciya na masa ciwoya fara zagayen gari ya na jin kamar ya hau sama ya faɗo tsabar baƙin ciki.
Ya gangara kenan ya ga wani tsoho kayansa duk sun yi datti yayin da wasu samari suka kewaye shi su na zagin sh, Basheer ya ƙarasa da sauri ya na tambayar ba'asi.Wanda ya fi kowa surutun ne ya fara koro bayani "ka na ji ɗan uwa wannan tsohon da kake gani tsohon banza ne,kullum nan ya ke zama wani sa'in har abinci mu ke basa shine ya nemi yayi lalata da yarinyar mutane" Basheer ya ƙare ma tsohon kallo ko banza ya bai wa shekara ɗari baya,tsabar tsufa fatar jikinsa har tayi tamoji yayin da idonsa suka shige suka yi zurfi.
Basheer ya riƙo hannunsa yace "Baba faɗa min yadda aka yi don sam ba ka yi kama da tsohon banza ba,sannan a wannan shekarun naka mace ko zigidir za tayi ban ce za ta baka shawa ba balle har ka buƙace ta" tsohon ya jimƙe hannun Basheer yace "Jikana magani ta zo na bata ashe sharri ne ta ke son ƙulla min ba ta son ganina ne,ina tsaka da yi mata bayani shine ta fasa ihu su kuma samarin nan ƴan majalisa suka yo kaina" ɗaya daga cikin samarin yace "ƙarya kake a gaban idonmu ka riƙe mata hannu" idon tsohon tuni sun kawo ruwa yayin da samarin ke ƙoƙarin bugun shi ita kuwa yarinyar da ta laƙa masa sharrin sai ƙara sautin kuka take saboda ita dai a rayuwar ta zaman tsohon a unguwar su sam bai mata ba.



Basheer ya ja hannun tsohon da niyyar tafiya ya ji saukar ƙaton icce a bayansa ya saki ƙara kafin ya juyo su shiga yin dambe da saurayin wanda ya kasance Yayan yarinyar.
Dakyar aka raba faɗan wanda tuni jikin Basheer yayi birdi saboda kusan tarewa suka yi masa,bayan sun yi nisa shi da tsohon yace "Baba daga wane gari kake zowa tallar maganin?" Yayi shiru kafin yace "Jikana ko na faɗa ma ba za ka gane ba,amma maganin ya na yi sosai bari na baka kyauta ka sha" Basheer yayi murmushi yace "ai ni lafiya ta lau,yanzu dai bari na tarar maka abun hawa sai a kai ka gida"tsohon yace "mu je ga innuwa can mu zauna na yi maka bayanin wani lamari dangane da rayuwar ka"


Su na isa suka zauna abin da ya bai wa Basheer mamaki shine yadda aka yi tsohon ya san sunan sa, "Basheer buɗe bakin ka" tsohon ya sake faɗa a karo na biyu ,ba tare da yayi muso ba ya buɗe tsohon ya zuba masa wani garin magani mai bauri haka ya shanye ba don daɗi ba.
Sautin murmushi Basheer ya ji daga can saman iccen da suke ƙarƙashin innuwarsa,ya ɗaga kai sama bai ga kowa ba sai wata innuwar mace ga gashin kai nan ya zubo.
Jin shigar zobe a yatsansa ya maido hankalinsa ga Baba tsoho wanda fuskar shi ta cika da annuri,cikin murya ta tsoffi yace "Jikana alƙamin ƙaddarar ka ya nuna za ka auri mataye dayawa saboda yanayinka,hakan yasa ba za su juri zama da kai ba amman ka ga wannan zoben shi zai taimaka ma wajen gane daidai kai wato macen ka ta har abada tabbas za ta zo gare ka amma ban san yaushe ba"

Jikin Basheer tuni ya ɗauki rawa karon farko a rayuwarsa da ya ji tsoro,murya na ɗan rawa yace "to amma Baba ta yaya zan gane ta?" "ta wannan zoben domin ita ɗaya kawai za ta ga kyawunsa sauran mata kuwa tamkar kwano mai lamba za su gansa" kafin Basheer ya kuma cewa wani abu Tsoho mai magani ya miƙe tsaye yace "yaro zan tafi ka ƙara riƙo da addini sannan banzar aƙidarka ka yi ƙoƙarin cire ta daga rayuwar ka"
Tsohon yayi ɗan nisa kaɗan ya ɓace ɓat daga idanun Basheer wanda ya ke zaune a ƙasa kamar an dasa dutse,dakyar ya yunƙura ya kama hanyar gida tunani fal ransa.



____ADS


Da mugun gudu Sheera tayi tsalle ta ƙanƙame DADDY,sanye yake cikin costume blue gashin kan nan nasa sai ƙyalli ya ke kamar wani sabon saurayi.Ya tallabota da kyau kafin ya dire bakinsa kan laɓanta ya bata kiss mai sautin muaaah sai kuma ya sauketa ƙasa.Har zai wuce Mai Gadi ya ƙaraso alamun magana bakinsa sai kuma yayi shiru hakan yasa Daddy ya miƙa ma Sheera bac ɗin sa mai ɗauke da system ta shiga ciki da ita.
Mai Gadi yayi ƙasa da murya yace "Alhaji jiya wani ya zo wajen Hajiya ƙarama da sunan zance,sunan shi Mr Salis Na so hana shi ganinta sai kuma ita hajiyar ta zo"ran Daddy ya ƙara daɗa baƙi kafin yace "ok na gode aikin ka na kyau,ko ka ji mi yace mata?"nan ya kwashe komai ya faɗa ma Daddy shi kuwa da takaicin haka ya ƙarasa falon.



Direct ɗakinsa ya wuce ko gaisuwar Mamy bai tsaya amsawa ba,ya na shiga ya hango Sheera zaune ta na jiransa fuskarta fal farin ciki.
"DADDY albishirin ka?"ta faɗa ta na mai yin wani murmushi tare da nufo shi ta kama hannunsa,ya ɗan saki fuska kafin yace "goro fari tass amma bai kai Sheerana ba"ta yi dariya ta faɗa jikinsa kafin tace "na faɗa soyayya !" Sautin bugun zuciyarsa ya saka Sheera saurin janye kanta daga ƙirjinsa Daddy kuwa murya na ɗan rawa yace "kika ce mi?kin faɗa soyay...."kawai sai tari ya ƙwace masa.Hankali tashe Sheera tace "Daddy don Allah kar kace ba ka sonta wlh ina son Farida tamkar raina" Daddy ya waro ido cike da murna ya ɗaga Sheera sama ya na juyata,sosai ya ji daɗi shi a zatonsa Mr Salis ne ta ke so..........




🤧🤧🤧🤧 Littafin nan akwai Cakwakiya 😂 to wai nan ma ba mu shiga cikin gundurun labarin ba, Hajiya kar ki bari a baki labari ki shigo daga ciki 400 ne kacal +22795045822 mai buƙata ta min magana ta WhatsApp
[09/10 à 06:18] MRS SADAUKI 💫: *BASHEER....*🌼


MRS SADAUKI💫✍🏻


Last free page 23-24

Domin shiga paid group za ki biya 400 kacal,katin MTN in kuma transfer za ki yi sai ki min magana ta WhatsApp na baki account number +22795045822


Da farko hankalin Daddy ya tashi da SHEERA ta sanar da shi ta fara soyayya,duk a tunaninsa da namiji ne don ba ƙaramin kishinta yake ba amma jin mace ce take so sai cewa yayi "Ki bani lambarta sannan ki faɗa mata ina son ganin ta dan lalle ya zama doli na yi mata kyauta ta musamman"Daddy ya faɗa ya na kallon Sheera wacce ke cike da farin ciki.
Lambar Farida ta basa kafin ta barsa ya ɗan huta,bayan Sheera ta fita Daddy ya kira wata lamba ban ji mi ya ce ba amman yanayinsa ya nuna ba abu mai daɗi ya ke faɗa ba.
Ya ajiye wayar ya furzar da huci, Mamy ta shigo ta tsaya ta na kallonsa.Ya sakar mata murmushi tare da yi mata alama ta zo,jiki ba ƙwari ta faɗa jikinsa,bayanta ya shiga shafawa ya na mata magana ƙasa-ƙasa wacce iya ita ɗaya ta ke jin abin da ya ke cewa.
"Mu je na yi ma wanka"cewar Mamy ta na mai ɗan ɗaga kai ta dubesa saboda yin wanka mata da miji sunnah ce mai kyau,Daddy ya murmusa duk da a zahiri bai son haka amma haka suka wuce zuwa toilet.


Bayan sun fito ta taya shi ya kimtsa,ta feshe shi da turare sannan suka fito.
A falo suka tarar da Jumma ta na kallon tv,kallo ɗaya ta yi masu kafin ta kawar da kanta saboda zuwa yanzu ji ta ke kamar ta fara kishin Mamy.Daddy ya zaunar da Mamy kan cinyarsa ya na mai cewa "Jumma a haɗa mana abincin da za mu ci ni da wifer" Mamy ta ƙara shigewa jikinsa ta na murmushi mai sauti wanda ya ke bayyana tsantsar farin cikin ta,gefe guda kuma kallon ƙasa-ƙasa ta ke yiwa Jumma ta na an kare da ita.
Rai haɗe Jumma ta haɗa masu komai kafin ta ja gefe ta tsaya,su na tsaka da cin abinci Sheera ta fito daga ɗakinta sanye da wata riga rose iya cinya sai wasu manyan takalmi irin na ƴan ƙwallo,gashin kanta kuwa ta tubkesa a tsakiya.



Wani irin kallon ƙurilla Daddy ke yi mata kafin ya sakar mata murmushi yace "Babyn Daddynta sai ina kuma?"ta kewayo ta bayansa ta sarkaye hannuwanta ga bayan kafin tace "Daddy kar dai ace har ka manta?Shine kuma kake cin abinci alhalin za mu restaurant mu da baƙuwar mu ta musamman"jin furcinta ya saka Daddy aje cokalin hannunsa yace "au !Har kin shirya mana zaman?"Sheera na dariya tace "Yes Daddy"


Ran Mamy yayi kicin-kicin,da ace ta na da ikon hana wannan tafiyar to da ta yi.Sam ba ta son wannan shishigewar da Daddy yake yi wa SHEERA ,amma ya za ka yi da Uwar miji tunda ita ta haifi abin ta? Dole ta ja baki ta yi gum! Jumma kuwa kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha.


Wata haɗaɗiyar restaurant suka je babu jimawa sai ga Farida kamar yadda Sheera ta tsara,tsukaken kwankwasonta ya tsure da ido zuwa ƙugunta wanda ya ɗan buɗe ya fitar da shap mai kyau.
Sheera ta rungume ta cike da murna kafin ta nuna Daddy tace "Daddyna ne wannan Daddy ga Farida"cike da wayewa yace "Barka da zuwa matar mu"da murmushi a fuskarsa ya miƙa ma Farida hannu,ta miƙa nata ta saka cikin nasa Daddy ya ɗan jimƙe sa sosai ya na jijigawa wani abu mai sanyi-sanyi zafi-zafi ya ratsa tafin hannun Farida wanda launin fuskarta ya canza, Daddy ya sake mata hannu kafin ya nuna mata kujera duk suka zauna.
Jikin Farida duk yayi sanyi kafin wani lokaci ta dawo normal sai ta ji ta daram,hira suke sosai da Daddy in da a ƙarshe yayi mata alƙawarin waya iphone 12 da ita da Sheera suka yi shewa haɗi da godiya.

Da kwatance Daddy ya sauke Farida sabon gidan su kafin su koma gida, Daddy na gama parking wayar shi tayi ringing "kun kamo shi ok gani nan zuwa"shine abin da ya faɗa ya kalli Sheera yace "Baby shiga ciki na samu kiran ujila"ta zumɓure baki kafin ta fita ta na jin haka kawai zuciyarta na bugawa.





Cikin fitar hayyaci ya ɗago kansa bakinsa da hancinsa suna zubar da jini,duk ya galabaita.Murɗa-murɗan ƙattin duk ko wane fuskar sa tamau babu alamar imani balle sassauci,ɗakin da suke bai da wani yalwatacen haske.
"Shugaba tun ɗazu mu ke jiran ka ga yaron nan mun ɗan lalausa sa kaɗan"wani ɗaya daga cikin ƴan daban ya faɗa, Daddy bai ce komi ba har suka ƙaraso ɗakin da aka aje Mr Salis.
Hasken ɗakin ya kunna ya na mai tsura masa ido kafin ya taka zuwa gabansa,wani mahaukacin mari Daddy ya ɗaukesa da shi kafin yace "Abbas bani wuƙa"wanda aka kira da Abbas ya zaro wata dalleliyar wuƙa ya miƙa ma Daddy.


"Kai ga ɗan iska duk yadda na killace Ƴata sai da ka samu zarrar furta mata kalmar soyayya,to yau zan cire zuciyar taka na baiwa Karena" Daddy na gama wannan jawabin ya sa aka taushe masa Mr Salis ya sa wuƙa ya ɓarka ƙirjinsa ya ciro zuciyar sa.
Hannuwansa duk jini haka ya saka zuciyar cikin wani ƙyalle ,murya a kausashe yace "ku ɗauke shi ku jefar da shi a ƙofar gidan su" Abbas yace "Oga ba mu san gidan su ba yanzu ma bisa hanyar makaranta mu ka cabke sa" Daddy na goge hannuwansa da suka ɓace da jini yace "to ku jefar da shi can"


Daddy bai dawo gida ba sai bayan isha'i saboda meeting da haɗa ma yaransa na ƙungiyar ASOMA ,ƙungiya ce wacce ta yi ƙaurin suna ga dukan ƙasashen duniya saboda suna da reshe kusan ko wacce ƙasa.
Fuskar ko wanensu a murtuƙe yayin da suke kallon shugaban nasu wanda ke ta yi masu bayani game da sabbin dokoki da kuma technique ta janyo hankalin al'umma cikin su.
Kusan a gajiye ya ke,Mamy na zaune falo ta na jiransa .Bai kula ta ba ya wuce ɗakinsa ya ƙargama key,jajayen kaya ya saka ya ɗauki wani farin gari ya shafa a goshi sannan ya buɗe wata drower ta ƙarfe hoton wani ƙaton kare na gumki ya bayyana.Suratai ya fara kafin karen ya dawo na ƙwarai ya fara habshi,zuciyar Mr Salis ya basa ya canye sannan ya rufe drower.
Ya na jin yadda karen ke wani irin gurnani ya na cin zuciyar.
Aka shiga bubuga ƙofa, Daddy yace "waye?" A ƙyale,a ka cigaba da bubugawa da zarar Daddy ya tambaya sai a ƙyale shiru yayi zuwa can ya miƙe tare da buɗe ƙofar wayam ba kowa,har zai rufe ya ga hoton innuwar mutum zankaɗeɗe duk da ya na cikin secte hakan bai hanasa ɗan jin tsoro ba amman ya daure ya rufe ɗakin.





Tun cikin daren mutuwar Mr Salis ta garwaye duniyar media,wasu har hoton sa suke turawa tare da bayanin an kashe sa bayan an cire masa zuciya.Sheera da ke kwance ta na shating a facebook sai da ta kusan suma ganin saƙon,ta tashi a firgice ta fito daga ɗakinta sai dai tun kafin ta fara saukowa daga step ta ke jin muryoyin mutane a can ƙasan falo.
Gabanta na ɗan faɗuwa ta ɓuya a jikin bango kafin ta leƙa ta wata ƴar hanya,Daddy ta hango zaune bisa salon kofin wani abu ja a hannunsa ya na sha yayin da lokaci zuwa lokaci yake yin magana.Ba taji abin da yake cewa ba amman ta na jin dariyar mutane uwanda sam ita ba ta ganin su,duk Yaren da suke ba ta ji sai yanzu da wani mai babbar murya ya ɗauki parol "meeting na gaba a maƙabarta Dubai za'a yi shi kamar yadda Demon ya tsara amman ina sa ran zai ƙara mana girma musamman kai AlGabid" Daddy yayi murmushi tare da jinjina kai yace "ƙa'idodin da aka gindiya ma Karena tuni sun cika,yanzu saura ya fara farauta hhhh har na ganni na zama multimaloniya hhhh"duk ɗakin ya ɗauki dariya sai kuma suka yi tsit jin ƙarar buɗe ƙofa.


Mamy ce idonta cike da barci ta nufi table a mangé,ruwa ta cika da kofi ta shanye ta ƙara cikawa ta shanye kafin ta sauke ajiyar zuciya.
Inda Daddy ke zaune ta kalla tace "Daddyn Sheera mi kake a falo kai ɗaya?ko ka na da wata damuwa ne?"kamar walƙiya haka Sheera ta ga kofin hannun Daddy ya ɓace saboda zuwan Mamy.
"Yanzu zan tashi kar ki damu"ya bata amsa amman ta ƙi gusawa tace "to tashi mu tafi na raka ka wlh ni tsoro nake ji wani mummunan mafarki nayi akan Sheera"jin ta ambaci Sheera yasa shi maido duk hankalin sa gare ta yace "mi ya samu Sheerar?" Mamy ta goge ƙwalla tace "cikin duhu na ganta ta na neman taimako ga wani ƙaton kare baƙi ƙirin na biye da ita,ya na shirin cizonta sai ka zo ka tare sa" Daddy ya sauke ajiyar zuciya yace "na gode Allah da Ram bai cijeta ba"
"Ram ?kuma waye kuma shi?"Mamy ta tambaya Daddy yayi saurin cewa "ah ina nufin Karen" ta murmusa tace "to zan shiga na dubo Sheerana hankalina duk a tashe" jin haka ya sa Sheera saurin tashi ta koma ɗakinta idonta tuni sun yi ja tsabar kuka.



Mamy ta shigo ta tarar da ita ta na kuka,jikin mahaifiyata ta shige ta na jin wani irin ciwo,ta rasa mi ke mata daɗi.
Mutuwar wulaƙancin da Mr Salis yayi ko kuwa ganowa da tayi Daddy na cikin ƙungiyar asiri?
"Sheera mi kike ma kuka?mi ke damun ki?"Mamy ta tambaye ta,wayarta ta ɗauka ta gwada ma Mamy hoton Mr Salis tsit Mamyn ta yi ta na kallo Sheera cikin kuka ta ke cewa "Mr ɗin mu ne kuma har cewa yayi ya na sona kwanaki da ya zo nan gidan mai gadi ya hana sa shigowa,Mamy ban son shi amman na ji zafin yadda aka wulaƙanta shi"



Zuciyar Mamy ta shiga dakan uku-uku bakinta ya kasa furta komyi,sai Sheera da ta jawo a jikinta ta na bubuga bayanta gami da fara tofa mata addu'o'i a haka barci ya ɗauketa.



Washegari
Sheera da zazzaɓi ta tashi hakan yasa ba ta sauko ƙasa ba,Jumma ta kawo mata abinci kamar kullum.Ruwan shayi kawai ta sha ta kwanta,cike da tausayi Jumma ke kallonta kafin ta fice ta na jin zuciyarta na suya tare da tunanin kawo ƙarshen lamarin.
Daddy ya ci karo da Jumma ƴar kallon-kallon suka yi kafin yace "kar ki ma soma ki aje wannan banzar tunanin na ki in ba haka ba billahil azim ke da ganin Ahmad sai a lahira" Jumma ta haɗiye wasu yawu muƙut dan kuwa duk yadda ta ke son Sheera ai bai kamo ƙafar na Ahmad Ɗa ɗaya tilo gare ta ba.
Sheera na jin muryar Daddy jikinta ya ɗau rawa yayin da ta shiga barcin ƙarya,kumatun ta ya shafa yace "Babyna jikin ne ya motsa koko sakalci ne? Kin ga tashi ki yi wanka da ruwan ɗumi za ki ji ki garas"shiru ta ƙi tankasa hanka yasa ya ajiye kwalin waya guda biyu yace "to ga alƙawarin da na yi nan na cika ki baiwa FARIDA ɗaya ke ma ki ɗau ɗayar"ya na gama faɗa ya fice.
Sheera ta tashi zaune ta fara duba wayoyin kafin ta kira farida.






__________SURA BILDI


Dakyar Basheer ya ƙarasa gida jikinsa duk ya mace ji yake tamkar su biyu ne a cikin gangar jikin.Ya na shiga da Mariya ya fara cin karo,kauce mata yayi amman ga mamakinsa sai ta ƙara nufo sa.Yayi tsaye ya na kallon ikon Allah,ta sosa ƙeya tace "dama tun ɗazu nake jiran ka akwai maganar da za mu yi"
Basheer ya haɗe rai yace "sai kuma aka ce miki ina buƙatar ji da har za ki zo ki tare ni ?"ta girgiza kafin tace "dan Allah ka saurare ni mana dan ƙaunar da kake ma Inna "Basheer ya ture ta ya wuce ya tsinkayo muryarta ta na cewa "daman a kan Badiya tace ba za ta iya jurar yadda kake mata ba wai na bata maganin wanda zai sa ta dinga...." cak ya tsaya kafin ya juyo ya na kallonta,da ɗan gudu Mariya ta ƙaraso tace "dan Allah ka aure ni tunda Ni daidai da kai nake zan iya ɗaukar larurar ka ,tun tuni na gama takaba"


Tsabar ɓacin rai ya saka idon Basheer ƙanƙancewa gami da yin ja,da sauri ya ƙarasa shiga kewayensu.Shara ya tarar Badiya na yi ta saka abun sauraren sauti a kunnenta,da yayi kutufo da ita har sai da ta wuntsila ƙasa.Jibgarta ya fara yi kamar wanda Allah ya aiko ita kuma ta na ihu da neman taimako,Mariya ita ɗaya ce a gidan don Sa'adiyya ta fita hakan yasa ta koma gefe ta na ta dariya wai ana dukan kishiyarta.



Sai da ya yi mata lilis kafin ya ja ta zuwa ɗaki,wuyanta ya tuƙe yace "kenan sirrina da na kwanciyarmu gami da komai ma kike tafiya ki na barbaɗa ma duniya salon a dinga yamiɗiɗi da ni?" Badiya ta shiga jujuya kai,ta na kakarin wahala.....


Kash! Free page ya ida mai son ci gaba da karanta wa 400 ne ta min magana ta WhatsApp +22795045822

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment