Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kai mu"ta amsa kafin ta nufi ɗan madaidaicin ɗakinta wanda sam bai yi kama da na mai aiki ba.
Kamar kullum ta na ɗaga pilow ta ga kuɗi sabbi ras a jere,ta ja dogon numfashi duk da ta san ba ta hanyar ƙwarai ta same su ba amman hakan bai hana ta jin daɗi ba.

Ko sallama ba ta yi ba ta buɗe ɗakin ta shiga,Daddy ya waigo ya na kallonta sosai ta yi masa kyau a ido sai dai kash sam bai ra'ayin yin sunnah ya fi son yin luwaɗi amman ko giyar wake ya sha ya san ba zai bari Mamy ta san shi ɗan luwadi ne ba balle ma har su yi.
"Daddyn Sheera ko ban yi kyau ba ne shine ka wani share ni ?" cewar Mamy ta na mai shigewa jikinsa,yayi saurin ja da baya kafin yace"mu tafi ina son kallon tv" ta ɗan haɗe rai tace "Daddyn Sheera wai miye ba ka son ina shigowa ɗakin ka ko da matsala ne?kullum a falo na gaji da rayuwar nan"kicin-kicin yayi da fuska hakan yasa ta nufi ƙofar fita ta waigo kenan za ta sake yin magana idonta ya sauka da gadon da suka tumurshe shi da Jumma ,ta fita ba tace komai ba.





###

Ƙofar gidajen biyu tanƙ ya ke da al'umma wanda dawowar su kenan daga ɗaurin aure,tuni an fara fitowa da tururuwan abinci ana ɗorawa gaban jama'a.
Basheer ango sai wasar baki ake ana tattare malum-malum kai kace mijin abara haka ya ke tafiya abokansa na take masa baya.Waya ce laƙe da kunnensa ya na sauraren kukan Badiya tun ɗazu ƙawarta ta kirasa ta na zolayar sa,cikin nishaɗi yace "Malika ki rarrasheta mana kin barta ta na ta kuka ba ki san hawayenta masu tsada ba ne?"daga can Malika tayi dariya tace "ai ruwan hawayen da ta zubar sun fi Litter biyar hhh! To wai ina abokan ka har yanzu ba su kawo mana lemun da za mu raba ma ƙawayen mu ba" Basheer yace "bari ina zuwa ana min magana ne"
Ya kashe kiran ya na mai zuwa gun Ƙanwar Inna da ke tambayar makulen gidan da Kawu Laminu ya kama masu haya,sai da ya shiga tsohon ɗakinsa wanda tuni ya kwashe kayan jikinsa sannan ya ɗauko mata key.
Shigarsa cikin gidan ya saka dangi fara basa gudummawa,sosai hakan yayi masa daɗi dan dama ya na buƙatar kuɗin.Abokin ango Lawan shi ke tarban baƙi tare da basu jus,kowa ya yaba bakin gwargwado sun fita kunya.




Bayan magrib
Badiya an yi wanka ana zaune mai kwalliya na yi mata,sai wani irin fat-fat zuciyarta ke yi mata saboda yadda yau ƙawayenta suka ta zuzuta daren farko da irin azabar da ake sha.
Tsaf ta fito cikin doguwar riga ta farar shadda wacce aka yi ma kwalliyar jan zare,masu salula sai ɗaukarta hoto suke.Bayan an kaita ta nemi gafarar iyayenta an yi mata nasiha aka jata zuwa waje inda motar kan amarya ke jiran su.



Babu wasu motoci duk babura ne ƙawayen amarya suka hau da ma wasu sauran mutane.

Bayan école Soura aka kaita gidan kewaye uku ne na ƙarshe ne ɗakin Badiya,ciki guda ne babu ƙurwa.Gado ne daidai kwancin mutum biyu sai drower ƙire uku,babu laifi kayan sun yi kyau sai ƙamshin sabunta ya ke,daidai tsakiya ango da amarya suka zauna yayin da Ustaz ke kwararo karatun Yaseen gami da wasu addu'o'i kafin kowa ya watse.



Sai wuraren ƙarfe tara na dare Lawan ya yi masa rakiya ɗakin amarya.Duk nacin Lawan Badiya ƙin buɗe fusktarta ta yi sai bayan ya fita ne, BASHEER ya ce " ki yi alwala zan je na yi sallama da abokina na dawo" ba ta ce komai ba,shi kuma ya fita ƙofar gida don yi sallama da Lawan.
"Abokina don Allah kar ka yi garaje,ita ɗin matar ka ce kar ka nuna son kai ka bi ta a sannu " cewar Lawan ya na riƙe da hannun BASHEER .
"In sha Allah abokina ,na gode sosai Allah bar zaman tare ya ƙara danƙon zumunci"
Lawan ya amsa da "Amen!" Kafin su rabu.

Ko da BASHEER ya dawo ya tarar Badiya ta yi alwala,shi ma ya je yayi bisanin ya dawo.

Shi ke gaba Badiya na bayansa, raka'a biyu suka yi suka salamce.Tambayoyi yayi mata game da addini ta kuwa amsa ras dan tayi karatu sosai,abin da ya shigo masu da shi suka ci kafin su yi barci😂😂(Kun yarda Basheer zai yi kwanan banza😆)




"Ki aje hankalin ki sosai babyta kar ki wani damu balle tsoro kin ji?" Badiya ta gyaɗa kai,ya ci gaba da cewa "duk wacce kika ji ta na cewa daren farko na da zafi to laifin ta ne ba ta tsaya ba balle ta bai wa mijin haɗin kai wanda zai taimaka masu yin komai a sauƙaƙe kin gane ko?" Nan ma kai ta gyaɗa masa.

Wutar ɗakin ya kashe ya kunna ta ƴar ƙaramar wayarsa hakan ya basu damar hango fuskokin juna,da dubara ya rabata da kayan jikinta.A hankali ya fara sarrafa Badiya ,ta yadda zai kawo masu sauƙi.
BASHEER ji ya ke tamkar a mafarki ne wai yau ne ke tare da mace a ɗaki guda .
Sai da ya tabbatar ya gama game mata jiki kafin ya fara ya ida jawota jikinsa sosai.Da sauri Badiya ta fara kiciniyar ƙwatar kanta tuni zuciyarta ta fara bugun tamanin-tamanin.
Murya na ɗan rawa tace "Ya Basheer dan Allah ka bari har gobe ka ga gobe ana damu kuma ƙawayena za su zo"

Basheer wanda idonsa suka ƙanƙance ya dubeta yace "ina ruwan ki da ƴan damu?Ki bari mu dama furar mu tun yau" ta yunƙura za ta tashi ya riƙe mata hannu ya matse daidai jijiyar magudanar jininta doli ta kwanta ta na hawaye.Basheer ya karanto addu'a ta neman tsari daga shaidan da duk wasu maƙarabansa......
[07/10 à 09:37] MRS SADAUKI 💫: *BASHEER...*🌼


MRS SADAUKI💫✍🏻


Page 13-14

Tashin hankali wanda ba a saka masa rana,duk yadda Badiya ta yi tunani ashe lamarin ya wuce haka.Sai yanzu ta fahimci muhimmancin kawo budurci gidan miji,da kuma tattalinsa da iyaye suke nuna wa ƴaƴansu.

"Innalillahi !Ya Basheer wane mugun abu kake min ? Wayyo Allah Iya mai wake zo cetar ni,anty Murja Basheeri zai kashe ni "Badiya ta fara faɗa lokacin da taji azaba na f ratsata,ashe wasa farin girgi,numfashinta ya ɗauke ɗif na wuccin gadi .
Duk ya haɗa gumi burinsa kawai ya gama komai a yau, duk da kuwa Lawan yayi masa nasiha amma ga banza wai harare cikin duhu.
Idon Badiya har wani irin dishi-dishi ta ke gani tsabar yadda Basheer ke gana mata azaba.





"Ni ka tada ni marar imani kawai,sai wani liƙe min kake kamar cingam"cewar Badiya ta na mai ture ƙirjin Basheer wanda sam bai da niyyar janyewa daga gare ta.
Ya ware idonsa a kanta sai dai bai ganinta da kyau saboda ƙaranci haske,a hankali ya janye jikinsa daga gare ta kafin ya zauna bakin gado.
Masturber kansa ya fara ya na biya ma kansa buƙata kamar yadda ya saba,sai da ya samu nutsuwa.
Can gefen gado ya kwanta ya na jan numfashi,gefen kansa na ɗan sara masa a haka barci ya ɗauke sa.



Washegari
Shi ya fara tashi yayi wanka ya tafi masjid,har ya dawo Badiya na barci ya tasheta dakyar ta iya tsayuwa a kan ƙafafunta.
Bayan ta yo wanka ta shigo ɗaki ta na buɗar ƙafa ,Basheer ya gumtse dariyar sa ita kuwa ta turo baki ta na jin wani haushinsa.Dakyar tayi sallah a tsaye kafin ta kwanta kan sallayar tayi ta barci, Basheer shi ya wanke zanen gadon kafin ya shimfiɗa wani.Zama yayi bakin gado ya na mai rero karatun Alkur'ani,a can gefensa kuwa wani irin haske ke fitowa daga cikin madubi wanda sam bai yi lura ba.



Yayi nisa sosai a karatu muryar sa ta fara rawa alamun kuka,saboda ya zo daidai Ayar أَفَحَسِبْتُمْ أَنَّمَا خَلَقْنَاكُمْ عَبَثًا وَأَنَّكُمْ إِلَيْنَا لا تُرْجَعُونَ

```Shin ku na tunanin mun halicce ku ne haka nan ragaga babu horo babu hani?ko ku na tunanin ba za ku dawo gare mu ba?``` (Suratul Al'Mu'umin)


Jin shashekar kuka na fitowa ne ya saka Basheer waigawa ,Badiya barci take hakan yasa ya ɗaga ido inda har yanzu kukan na fitowa bai ga komai ba sai wannan hasken na cikin mirror kafin bisani kuma ya ɓace.Ko kaɗan Basheer bai wani ji tsoro ba sai yayi tunanin ƙila kunnuwansa ne suka jiyo masa ba daidai ba,tashi yayi ya canza kaya dan tuni gari ya fara haske.


Direct gidan su ya nufa wanda har yanzu akwai sauran ƴan biki uwanda ba su koma garin su ba.
Duk gaishe su yayi kafin ya wuce gun Inna wacce ke zaune kan sallaya ta na jan casbi,gefenta ya zauna kafin ya gaisheta ta juyo ta kalle sa sannan ta amsa "lafiya lau ya gidan naku?" Ya amsa da "alhamdullah"ya na mai sunne kai,gaban Inna ya faɗi tace "fatan dai Badiyar na lafiya ba abin da ya same ta?" Ya kalli mahaifiyarsa da kyau sai kuma ya turo baki yace "shikenan Inna har kin fara raba soyayyata gida biyu ni mi yasa ba ki tambaye ni in ina nan ba abin da ya same ni ?"



Inna ta girgiza kai tace "to in ba abun ka ba Auta kai da ga ka a gabana ba?" ya kuma turo baki kafin ya ji wani sanyi na ratsa jikinsa ya na shiga can cikin ɓargonsa,a take yanayinsa ya sauya Inna da ke ankare tuni ƙirjinta ya fara bugawa dan kuwa yanayin ya tuno mata da shekaru goma sha da suka wuce.


"Basiru lafiyar ka kuwa?"bai ce komai ba sai idonsa da ya kafe a bakin ƙofa ,Inna ta dubi hanyar shigowa ba ta ga komai ba sai innuwar mace na tafiyarta.



Ya lumshe ido kafin ya kwanta kan tabarma,Inna ta ɗauki kansa ta ɗora kan cinyarta ta na mai tofe shi da addu'o'i.


Wani nauyayyen barci ya ɗaukesa wanda ya kai sa wata duniyar daban,cikin wata ƙatuwar Masarauta wacce aka gina da zinare gami da ƴaƴan lu'ulu'u.

"Sarauniya Abrar wannan kukan na ki ya isa haka,mi kuma ya sami Sheebar ɗin?" Wani farin Dattijo ya faɗa ya na mai dafa kafaɗar Sarauniya Abrar wacce ta ke fara sol sai baƙin dogon gashin kanta,manyan idonta ta zuba kan Sarkin wanda ya kasance mahaifi gare ta kafin tace " Sheebar ne yayi kuka a gaban idona Abih,ya karanta Ayar da tafi taɓa min zuciya.Lokacin da ya karanta ta sai na ke hango kaina a filin alƙiyama Allah na bincikata tare da tuhumar mi yasa zan so wani bare wanda ba jinsina ba?" Cikin kwantar da murya Sarki Nurein yace "haba Sarauniya kar fah ki manta ke ba da niyyar cutar sa kike sonsa ba,sannan ba ki taɓa kishinsa ba kawai soyayya ce ta tsakanin Musulmi da Musulmi "


Ta goge hawayenta tace "amman Abih ina tsoro mahaifiyarsa ta ga innuwata tabbas kuma na san za ta ɗauki mataki" sarki Nurein yace "ba na ce ba! Ita kanta a yanzu ta san ba za ki taɓa cutar da ɗanta ba"ba tace komai ba sai kofin ruwa ta jawo da aka kawo mata tun ɗazu.
Yatsarta manuniya ta saka a ruwan,fuskar Basheer ta bayyana ta saki murmushi tace "bawan Allah!" Sarki Nurein yace "ya kamata ki rage shishige masa haka saboda auren ki ya gabato ban so mijin ki ya kawo ƙorafi" ta busa ruwan wanda har sai da Basheer ya zabura kafin tace "Abih ina son Jameel sosai fa saboda shi ma Masoyi ne wanda ya cece ni ne" Sarki Nurein yayi murmushi yace "ina ma ace duk zuciyoyin jinsin Jinnu haka suke irin ta ki da ba'a samu yawan mugunta ba" ta rungume Abbanta tace "Abih kamar yadda jinsin Jinnu ake samun mugaye haka suma Jinsin bil'adama suke kawai dai fatan Allah ƙara tsare mana imanin mu" ya amsa da amen kafin ya zubar da ruwan kofin ta ɓata rai shi kuwa ya laƙace mata hanci yace "kar ki tsoratar da Sheebar ɗin kin saka masa barci tare da yin mafarkin ki"





Basheer kuwa a daidai lokacin da sarki Nurein ya zubar da ruwan a lokacin ya tashi bakinsa ɗauke da addu'a, duka-duka barcin bai wuce minti goma ba.
Inna ta sauke ajiyar zuciya ganin ya tashi daram cikin ƙoshin lafiya,amman duk da haka tayi alƙawarin sai ta tafi ƙauyen Luka.


"Inna wai ashe barci na yi"cewar Basheer,ina ta murmusa tace "mafarkin mi kayi?"shiru yayi ya na tunani can kuma ya ɗage kafaɗa yace "na manta bari na tashi na fita yanzu su Lawan za su zo mu je yiwa iyayen amarya godiya" jin haka Inna tace "shine tun ɗazu ba ka faɗa ba?Tsaya na baka goron"ta tashi ta nufi ɗakinta.




A al'adar Maradi abokan ango sukan je yi wa iyayen amarya godiya in amarya ta kai budurcinta,sai a haɗa da goron godiya.Basheer ma haka suka je shi da abokansa ,bayan sun fito daga gidan su Badiya ne ya kira wani abokin aikin sa na lebaranci.
"Amman ka cika banza a kai ma amarya jiya amman shine za ka tafi aikin kwaɓa siminti?"Lawan ya tambaya ya na duban BASHEER wanda yanzu ya gama waya zai tafi aiki,ya ɗan harare shi yace "au!so kake na zauna a gida to mi za mu ci?" Lawan yace "amman ai sai ka bari ka yi hutun sati guda" Basheer yace "na ƙi ɗin,mu je mu ci abinci ka aje ni chantier"haka kuwa aka yi bayan sun ci abincin karin da Inna ta girka ya kai Basheer wajen aikin sa,abokansa sai tsokanar sa suke bai kula su ba ya cire shaddar jikinsa ya saka kayan aiki.




Badiya kuwa ko da ta farka ,ba ta ga BASHEER ba.Sauran kazar jiya ta ci ta hauda da madara,kafin wani lokaci ƙawayen ta su zo su fara hirar banza ta na basu labarin daren farko.
Bayan sallah asar tuni ƴan damu sun zo,dakyar Badiya ke tafiya duk in ta motsa idon mutane kanta.Ƴan uwanta biyu suka sakata tsakiya kafin su kaita gun dangi Inna "ga amanar Badiya nan mun kawo maku, Allah baku ikon riƙewa in tayi laifi a tsawatar mata daga yau ta zama taku ...."nan dai tayi ta rabbata jawabi kafin dangin Inna su karɓa,can anty Murja ta miƙe tace "Heee!" Duk hankulan mutane suka dawo kanta bayan ta rangaɗa buɗa tace "an baiwa ango jika hamsin 50k,uwar ango turmin atamfa biyu da buhun shikafa da Littre biyar na mai,shi kuma ango ga nashi kayan abincin" nan aka shiga sauke kayan abincin daga cikin ƙatuwar baro sosai dangin Inna suka yi ta murna ana godiya gabanin duk kowa ya watse.




_____ ADS

Ƙarar takun takalminta ya saka iyayen nata suka maida hankalinsu kanta,sanye take da riga da wando na jeans ta baza gashin kanta ya zuba har a kafaɗa.
A shagwaɓe ta gaishe su kafin Jumma ta ƙaraso ta haɗa mata tea,a baki ta rinƙa bata har ta shanye kafin ta ɗauki garin chocolat ta fara sha can ta ɗago ta dubi Daddy wanda ya kafeta da ido.
"Ya dai Daddy ?"ta tambaye sa ya sauke ajiyar zuciya yace "zan yi tafiya ne zuwa Dubai na san zan yi kewar ki sosai"cokalin ta ajiye ba tare da ta shirya ba kafin kace wani abu har hawaye sun fara yi mata zuba ta farararen idonta wanda ba ta taɓa shafa masu kwalli ba.
"Sheera zan dawo fah ba jimawa zan yi ba akwai wani meeting da za mu yi kuma zan rinƙa kiran ki a waya"cewar Daddy ya na mai tasowa daga kujerar da ya ke ya dawo gabanta,Sheera ta miƙe tsaye tare da rugawa ta fara taka step da ƙarfi kamar za ta faɗi.




Daddy ya dafe kai yace "oh my god!" Mamy ta kawar da kai yayin da Jumma ta tsuresa da ido,hararta yayi kafin ya bi bayan Sheera.Kan bed ya tarar da ita ta na kuka kamar ranta zai fita,hips ɗinta ya kalla yadda ɗamamen jeans ɗinta ya fito da shap ɗin da kyau.Ya haɗiye yawu kafin ya ƙarasa gun ta,gashin da ya rufe mata fuska ya ɗan janye gefe,kafin ya saka bakinsa gefen idonta ya na shanye hawayenta.Ido ta rumtse ta na turo baki,ya tada ta zaune ya jawota jikinsa rarrashinta ya fara kafin yace "mine ne Babyna ko ki na so mu tafi tare?"da sauri ta gyaɗa kai yace "makarantar fah?"tayi ƙyaf-ƙyaf da ido ta na kallonsa a can ƙasan zuciyarta kuwa wata irin wuta ce ke gasata ta na jin in Daddy yayi mata nisa kamar mutuwa za ta yi.


Fuskarta ya fara shafa ya na hura mata iskan bakin shi,ta lumshe ido ta na sauke ajiyar zuciya,ya na ƙoƙarin kai bakinsa akan nata ak turo ƙofa........
[07/10 à 09:37] MRS SADAUKI 💫: *BASHEER...*🌼

MRS SADAUKI💫✍🏻


Page 15-16


Mamy ta ƙaraso cikin ɗakin fuskarta a murtuƙe kafin ta zauna gefen Sheera,kumatunta ta goge ta na mai kallon ƴarta ta cikin ido.
Ta kwaɓe baki tace "Mamy Daddy zai tafi ya bar ni kuma ni ban so" Mamy ta sauke ajiyar zuciya tace "kar ki damu zan zauna tare da ke har lokacin da zai dawowa,maza tashi ki wanke fuskar ki kar ki makkara" Sheera ta nufi toilet Mamy ta dubi Daddy tace "daga yau in za kayi balaguro Please ka bar gaya mata,na lura in kai ka sanar da ita ne ta ke shiga wani hali saɓanin ni" bai ce da ita komai ba ya tashi ya fita.



Mamy ta ja hannun Sheera suka fito falo,a tsaye suka tarar da Daddy.Cikin bada umarni yace "daga yau ke za ki rinƙa kaita makaranta, Sheera ki aje motar ki Mamyn ki za ta rinƙa kai ki ta na maido ki" kai ta jinjina ta na langaɓe wa a jikin Mamy.
Murmushi na kwantar mata da hankali ya sakar mata kafin yayi mata kiss a goshi,Mamy tayi draving Sheera zuwa makaranta.
Tun daga nesa ta tsinkayi abokanta ko kuma matanta Farida da Maryam,rungume juna suka yi su na ihu.
"Dan Allah Sheera ki rinƙa barci a nan cikin makaranta Allah sosai mu kayi kewar ki jiya da dadare"Farida ke faɗa ta na mai sake shiga jikinta,Sheera ta ɗan tureta tace "ke mutane fah na kallon mu" Maryam tayi dariya tace "mi ya ke ?ai kusan kowa wayayye ne kuma suma su na less ɗin" Farida ta ƙara da "wasu kuma su na sex ba,mu je dan Allah ki ɗan rage min zafi kafin mu shiga aji"
Sheera ta taɓe baki tace "ke da ma ba ki bari na saka na yi yadda nake so saboda wata banzar virginity" Farida tace "Sheera ke ma fa tattalin taki kike saboda ki bai wa mijin ki daren farko"tayi shiru kafin tace "Ni fah ban son aure balle in ji sha'awar namiji" "ki na nufin ba ki taɓa soyayya ba?"Maryam ta tambaya ,Sheera ta gyaɗa kai tace "babu ma wanda ya taɓa cewa ya na sona sai wancan banzar"ta nuna Ameer wanda ya ke ɗan kallon su daga nesa.



"Dan Allah mu je ciki saura minti goma fah a shiga aji"cewar Farida a shagwaɓe,Sheera ta tamke fuska tace "sai in kin yarda na yi komai da komai" Farida ta kwaɓe fuska tace "kawai yawun ki na ke son sha" Sheera tayi mata wani kallo kafin tace "kamar ƙarama na sha yawun ki wai ki na tunanin zan iya haɗa baki da baki Allah kiyaye ƙazanta"ta na gama faɗa tayi wucewarta.




"Duk wannan wulaƙanci da take yi mana dan ta ga ta nada kuɗi ne,amman na lashi takobi ko ta halin yaya ne sai nima na zama star zan yi kuɗi ko da ta hanyar cutar maza ne" Farida ta ke magana rai a ɓace,Maryam tace "tun farko fah ke ce kika samu wannan hanyar amman ni ban jin daɗin komai na fi son tarraya da namiji"
"Wai ina alhajin da ya taɓa ce maki ya na sona?"Farida ta tambaya,Maryam ta bata amsa da "ya na nan ko yanzu in kin shirya sai na gaya masa" Farida ta ɗan yamutsa fuska tace "Ni fah ban son sex" Maryam tace "shi fa dagaske ya ke son ki ba wai harakar banza ba kuma tun farko na gaya miki"
Farida ta ɗan dara tace "haba matsalar muni yayi masa yawa" "ina ruwan ki ke da ba auren sa za kiyi ba"
"Kuma haka ne,to ki haɗa ni da shi" "ba ki da matsala yau in na tafi club zan gaya mashi tunda ya na zuwa kallon rawa"nan suka ta tsara sabuwar rayuwar da za su yi.




A ɓangaren Sheera kuwa ajin su ta wuce,a table ɗin gaba ta zauna kafin ta fiddo wayarta ta na daddannawa.Facebook ta shiga ta fara kallon blague du jour haɗi da publication ɗin mutane kafin ta hau WhatsApp, compte ɗin Daddy ta shiga ganin ya turo mata hoto.Ta buɗe hoton zaune ya ke cikin jirgi alamu yau ne ya ɗauki hoton,duk da idonta sun cika da ƙwalla hakan bai hana murmushi suɓuce mata ba saboda ba ƙaramin so ta ke yi ma Daddy ba.



Voice ta fara yi masa cikin shashekar kuka gami da shagwaɓa,Mr Salis da ya shigo tun ɗazu ya kafeta da ido.Wani irin bugu zuciyarsa ta shiga yi ya na jin tamkar ita ɗaya ce kawai macen duniyar da ya taɓa gani,jin kamar sawun mutane na daɗa yawa ya saka Sheera ɗagowa sai ta ga ashe students ne ke shigowa kowa na samun waje ya na zaunawa.
Mr Salis ya daidaita nutsuwarsa ya gabatar da kansa kafin yace kowa ya tashi ya faɗi sunan shi,Sheera ita ce a table ɗin farko hakan yasa Mr Salis ya dubeta amman sam hankalinta bai kan shi.



Jin kamar ana kallonta ne ya saka ta ɗago manyan idonta ta zuba su kan kyakkyawar fuskarsa wacce ke ɗauke da ɗan siririn gemu.Ta turo baki ta na wani tamne leɓe,damshin yawunta ya ƙara ma jan leɓenta kyau Mr Salis yayi ta maza yace "tashi ki faɗi sunan ki"sanin shi ne malamin na su ya saka Sheera ɗan ɗagawa tace "Sheera" "cikakken suna za ki faɗa " ta kuma turo baki tace "Busheera AlGabid" nan kowa ya fara gayin nasa kafin ya fara yi masu cours.




Tsabar yadda ya ke satar kallonta ya sa ta matsu ya gama cours ɗin ya fita,sai dai ashe shine mushen da zai koya masu science da kuma pédagogie médical.
Wata ƴar kwalba ya fiddo daga cikin bag ɗinsa,daga ciki ka na hangen ƙaton kwaɗo wanda yayi ƙiriƙiri da ido tuni jikin Sheera ya ɗau rawa sai ta tashi ta koma table ɗin baya.
Mr Salis bai so haka ba,nan ya ci gaba da cours ya na sokar kwaɗon nan da allura ya na kwatanta masu komai a haka har lokacinsa ya ida ya fita.
Sheera ta nufi su Farida sai dai sam ba ta ga fuska ba,kawai sai tayi ficewar ta.





Ƙarfe tara na dare Farida da Maryam suka shirya suka nufi hotel horizon,yadda tsarin wajen ya ke ma kawai ya isa ya tabbatar maka hotel ɗin VIP ce.
"Tun da na ke ban taɓa zowa nan ba amman albarkacin ki Alhaji yace mu zo" Maryam ke faɗa ƙasa-ƙasa, Farida wacce ta ci kwalliya cikin riga bleu bic duk ta ɗame jikinta tace "ai kuwa dai ni ma yanzu na ɗan kashe ƙyar idona,amman Maryam ki na ganin zai bani kuɗin kuwa?"
"Mi zai hana ai na riga da na gaya masa mun ci bashi gun mai kanti saboda mu yi shiga mai kyau..." Ganin alhajin ya fito ne ya saka Maryam yin shiru sai murmushi take ta na yaƙar haƙora kamar gonar auduga .


"Haba Mary ta ya za ki bar gimbiyata a nan iska na bugunta ai sai ku wuce réception da kun tambaya za'a kai ku har ɗakin da na ke"Alhajin ya faɗa ya na yiwa Farida wani kallon ƙasa-ƙasa.
"A'a Alhaji gwara da na kira ka ai hakan ya fi"cewar Maryam ,yayi murmushi tare da yin gaba su na bin sa a baya har ɗakin da ya kama.





_______SURA BILDI


Basheer ne da Badiya zaune a gidan Inna sun kawo mata abinci,hira suke ɗan taɓawa kafin Innar tace "ya kamata ku tafi gida fah kafin hadari ya taso" basheer ya ɗaga kai ya kalli hadarin da sai sake yin baƙi ya ke.
"Tashi mu lalaɓa kafin ruwan su fara sauka"gaban Badiya ya faɗi ras saboda ta san yau duk wanda yayi mata tsaye sai Basheer ya ida karɓe budurcinta tunda period ɗin ta ɗauke.
Ba dan ta so ba suka yi ma Inna sallama suka nufi na su gidan,a bisa hanya tace "Allah duk na gaji ƙafafuwana sun yi ciwo wai Ya Basheer mi yasa ka ƙi sayen babur?"ya dubeta yace "in ba abun ki ba ina na ga kuɗin babur"ta taɓe baki tace "ai tarawa za kayi da sannu-sannu har ka

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment