Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta na ɓari zataje sadauki yayi mata magana da turanci kartaje.
Rugowa tayi da gudu tafaɗa jikin sadauki, mauɗe yace "aradun Allah tunda kaga tafasa zuwa gurinka wannan hegen ne yahana."
Sadauki yana gama shanya musu kayan suka fice sukabar gidan.
A garke suka sami Baffa yana kwance bacci ma yakeyi.
Biba tasa hanu tana buga bayan shi yatashi.
Buɗe idanu yayi yaga Biba ce yayi mata murmushi, lemu ta miƙa mishi tana murmushi tace *"jaɓɓo."* (Karɓa)
Hanu yasa yakarɓa yace nagode Biba ta, sadauki yace Baffa kagaji ko yanzu na gama wanki shine nafito.
Tashi yayi ya zauna Biba taga wani hoto a ƙasan bonon Baffa ta ɗauka tana kallo, ta kalli Sadauki tace "waye wannan?"
Ganin hoton yasa Sadauki saurin kawar da kai, domin kuwa idan yaga hoton Umman shi yakan tuno mishi rayuwar da sukayi abaya.
Sake tambayar shi tayi "who is this?"
Sadauki yace Umman mu ce amma tarasu kirinƙa yi mata addu,a idan kintunata, da kuma idan kinyi sallah."
"To." Kawai tace ta rungume hoton a ƙirjinta tace "nima zaka saya min irin kayan jikinta Baffa?"
Sadauki yace akwai nata zanbaki amma sai kin ƙara girma."
Da murna tace "to yayana nagode."
Shriye-shiryen zana jarabawar ss3 sukeyi, saidai ba anan cikin ƙauyen zasuyi ba a cikin birnin Bauchi zasuyi, damuwar sadauki shine a ina zaibar ƙanwar shi, harga Allah bayason yatafi yabar ƙanwar tashi ko kaɗan, dan baisan irin halin da zata shigaba idan yatafi yabarta.
Baffan shine a ɗaki yana kwance ya kunna gidan radio yana sauraro ita kuwa Biba sai faman baccinta takeyi.
Yanayin da Baffa yaga Sadauki yasa yatashi yazauna yana kallonshi yace "Sadauki ya nagan ka wani iri?"
Sadauki yace "Baffa tunanin tafiya ta birni nakeyi, banason natafi nabar mummy na, idan natafi nabarta bansan irin halin da zata shiga ba, Baffa dan Allah kabarni natafi da ita."
"A'a sadauki birni fa ba irin ƙauyen mu bane birni faɗi gare shi, kayi haƙuri kaje kayi jarabawar ka kadawo insha Allah zaka dawo kasame ta lafiya, wuya bata kisa, karka manta cewa na sanar da Yadado zaka tafi kiwone a daji har na wata ɗaya, kasan muddin tasan abinda zakaje yi a birni bazata amince ba."
"Hakane Baffa saidai hankali na bazai kwanta ba ne a can amma insha Allah zanci gaba da yi mata addu,a."
"Yawwa abinda nakeson naji daga bakin ka kenan."
Aranar da sadauki zai tafi Biba tayi kukan rabuwar su sosai, gashi bata saba da mutanen gidan ba kwata-kwata, Sadauki yana gani yatafi yabar tilon ƙanwar sa.
Bayan kwana biyu da tafiyar sa Biba har saida tayi zazzaɓi, dan ma tasamu Baffa yana tafiya da ita garke su zauna.
Wayar Baffa ne tafara ringing, Biba ta ɗauka ta amsa cikin siririyar Muryar ta da "Assalamu alaikum."
"Wa alaikissalam Biba kina lafiya, ina Baffan ki?"
"Lafiya ƙalau, Baffa na gashi can yana ba shanu magani, bari nakai mishi." Yana jin ta cikin waya tana kiran Baffa ankiraka awaya.
Tana miƙa mishi wayar ya kara akunne tare da yin sallama.
Alhaji Adam ya amsa sallamar cike da fara,a kamar agaban shi, bayan sun gaisa Alhaji Adam yake tambayar shi ina Abdul azeez?
"Abdul azeez yana Bauchi yana jarabawar karshe a secondary."
Kashe wayar Alhaji Adam yayi, inda Manu yasake kiran wayar yayi ta ringing bai ɗagaba, sai a karo na uku ya ɗaga.
Alhaji Adam yace "haba Usman meyasa zaka rinƙa yimin haka, ace Abdul azeez yana garin Bauchi yau kusan kwana biyar kenan duk da bansani ba ai Waheed yana jarabawar ace bazaka sanar daniba, haba ashe ma baka ɗaukeni a yadda na ɗauke kaba, abu ɗaya yanzu zakamin ka fidda kanka a wani makaranta yake zana jarabawar?"
Baffa yace "kayi min haƙuri ɗawainiyar ne yayi yawa shiyasa ban faɗa maka ba amma kayi haƙuri."
"Idan kaga na haƙura ka faɗa min sunan makarantar, bazanbari yaro na yazauna a school compound ba."
Baffa ya faɗa mishi sunan makarantar *SA'ADU ZUNGUR*
Alhaji Adam yace "ai kusa muke bamu da nisa sosai zanleƙa anjima na ɗakko shi na dawo dashi gida na."
"To Alhaji mungode Allah yasaka da alheri, mungode da kulawa."
Alhaji Adam yace "babu godiya atsakanin mu." Sukayi sallama da juna.
Alhaji Adam baiyi ƙasa a gwiwa ba yatada motarsa da kanshi ya nufi SA'ADU ZUNGUR, kai tsaye office ɗin principal ya nufa, bayan sun gaisa da principal, yafaɗa mishi abinda yakawo shi.
Principal yace tabbas akwai yaran da aka kawo daga daɓe maza goma mata uku "meye sunan yaron?" Principal ya tambaya
"Abdul azeez Usman."
Principal da kanshi yace "muje muduba ajin ko za ayi sa,a."
Aikuwa suna zuwa suka tambayi mai sunan akace ai suna da ɗan yawa dan sunkai su biyar.
Akace duk mai suna Abdul azeez Usman yatashi, aikuwa Alhaji Adam yana ganin shi yayi murmushi yace "gashi can a last bench."
Alhaji Adam yace idan yagama yana son ganin shi.
Bayan sun fito daga jarabawar Abdul azeez ya nufi office ɗin principal.
Sallama yayi, principal ya amsa mishi tare da cewa come in
Cikin ladabi yashiga office ya tsuguna a ƙasa, Alhaji Adam yace "come close to me."
Tashi yayi ya'isa wajen shi, anan Alhaji Adam yayi ma principal bayanin yanason yatafi da Abdul azeez gidan shi.
Principal yace to shi bazai hanaba amma akira shaidu, alhaji Adam yace ya amince da hakan. Shaidu aka kira da wanda zasubi shi suga gidan, Alhaji Adam ya ɓoye musu inkiyar sunan shi ne kawai dan kar su fahimta, dan duk wanda yaji sunan Alhaji Adam Abubakar mai kuɗi yasan shi, ko ba a zahiri ba yasanshi agidan Radio, tv, da news paper.
Koda suka iso gidan, tundaga gate ɗin shiga gidan suka tabbatar da cewa lallai wannan babban mutum ne, saidai shigarshi da irin motar da yake hawa zaka ɗauka irin gidan masu kuɗi wanda ba alissafa su acikin jerin masu Naira.
Koda suka shiga cikin ƙayataccen falon ido biyu suka fara yi da wani babban family elargement asaman hoton anrubuta Alhaji Adam Abubakar mai kuɗi family, malamai biyun suka juyo suka kalleshi, sai yanzu suka gane ashe mai kuɗi ne.
Aikuwa mamaki yakama su, Abdul azeez kam kallon aljannar duniya yakeyi.
Malam Yusuf ne yace "Alhaji dama dakai muke tare, ai da munsani da ba mubiyo ka ba."
Alhaji Adam yace "nifa kun birgeni, hakan yana nuna cewa kuna sane da abinda ya dace kuzauna ga waje."
Yan aiki ne suka fara shigowa da abinci kala-kala lemuka daban-daban, wannan dama al adar house helpers na gidan kenan.
Hajiya ce tafito cikin shiga ta alfarma, sanye take da doguwar riga lemon green sai farin gyale mai kauri da ta sanya akan kafaɗa ya rufe mata jiki.
Cikin girmamawa ta gaishe da baƙin.
Sunan Abdul azeez takira, ya ɗago kai ya kalleta ya gaisheta cike da ladabi. Murmushi tayi mishi ta amsa mishi cike da fara,a.
Bayan sun kammala cin abinci, sun ɗan taɓa hira suka tashi zasu tafi, Alhaji Adam yabasu open check yace kowa yaciri abinda yakeso.
Aikuwa murna sukeyi sosai yau kakarsu ta yanke saƙa.
Da zasu tafi sukayi ma Abdul azeez sallama, dan sunsan cewa albarkacin yaron sukaci, Alhaji Adam ya rakasu har tsakar gida yasa wani driver nashi ya kaisu har gida.
Bayan yadawo daga rakiyar su yasami Abdul azeez da Hajiya a falo.
Zama yayi yace "Abdul azeez kasaki ranka nan ma gidan kune kaji."
Gyaɗa kai kawai Abdul azeez yayi.
Jiniyar moto Abdul azeez yaji, ganin Hajiya tayi murmushi tace "andawo kenan, bari muji da me aka dawo yau."
Alhaji Adam yace "kema kinsan idan akwai babban yaya rigimar tana da sauƙi, sareena da waheeda suka shigo da sallama, Waheed shima ya biyo bayan su tare da yin sallaman.
Waheeda ce tafaɗa jikin mummyn nasu tace "mummy am hungry."
Waheed yace "yanzu kika gama cin abinci a moto amma yanzu wai kina jin yunwa."
Sareena ce tafara kula da Abdul azeez, tayi saurin durƙusawa ta gaishe shi, waheeda ma gaisar dashi tayi.
Waheed kallon sheƙe-ƙeƙe yayi mishi ya ɗaga mishi hanu alamun barka, ya wuce ɗakin shi, waheeda ce tabi bayanshi da gudu tana kiran yaya baka bani chocolate dina ba.
Oh Waheeda namanta anjima kizo ki karɓa.
Abdul azeez kam baidamu da abin da Waheed yayi mishi ba dan yariga yasaba da hakan tundaga gida bare nan da yaso a baƙo.
Mummy da kanta tatashi tace muje na kaika ɗakin ka ko Abdul.
Wani ɗaki ta buɗe mishi kusa da ɗakin da Waheed yashiga.
"Nan ne ɗakin ka duk abinda baka ganeba ka sanar dani ko kasami Waheed yayi maka bayani.
Fita tayi tabuɗe ɗakin Waheed tasami Alhaji Adam shima a ɗakin yana zaune akujera yana jiran Waheed yafito daga wanka.
Itama zaman tayi tasan abu ɗaya ne yakawo su.
Yana fitowa daga toilet yaga iyayen nashi, kallo ɗaya yayi musu yasan akwai magana.
Zama yayi akan gado yana kallon iyayen nashi, Alhaji Adam ne yakalleshi da kyau yace, "waheed me ka ɗauki kanka ne?" Wannan abinda kayi ma Abdul azeez bai dace ba, karka manta shimafa mutum ne mekake gadara dashi Waheed?"
Mummy ce ta karɓe zancen da cewa yana nufin shi yana da arziƙi Abdul azeez kuma talaka, to kasani cewa da mai kuɗi da talaka Allah ne ya halicce su, babu wanda yafi wani awajen Allah sai wanda yafi shi bauta masa, karka manta cewa wannan dukiyar da Allah ya mallaka mana jarabawa ce babba akan mu, haka shima talauci jarabtace na ubangiji, sai wanda Allah yaso yake cinye wannan jarabawar sabida haka ka kula ka nutsu kasan me kakeyi."
Waheed tunda mummy tafara mishi magana sauraran ta kawai yakeyi amma badan yashige shiba, saidai bayason baƙanta ma iyayen shi rai, dan haka yabasu haƙuri yace bazai sake ba.


Next page


*UMMY KHALEEL*

*Taku CE*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment