Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

isa garin su tatafi asibiti.
Umma ta kalli Abdul azeez tace, "Sadauki nasan zakayi kewana, saidai inason aduk lokacin da katuna ni kayimin addu'a, kakulamin da kan ka kaji, kazama jarumi ga mahaifin ka, karka cutar da wani, kakula da abinda zan haifa."
Tunda tafara magana sadauki sauraran ta kawai yakeyi, sai yana ganin kamar idan Umman tashi tatafi bazasu sake haɗuwa ba.
Umma dakanta tace, "kutashi kutafi, nima yanzu zantafi, kar Yadado taji ku shiru."
Abdul azeez yace, "Umma nidai zanbiki, dan Allah karki tafi kibarni kinji? Kidawo muyi zaman mu."
"Kaje kazauna da iyayenka, Allah yana tare dakai Abdul, hawaye yaci gaba da gan gara mata a fuska Abdul azeez yatashi ya rungumeta yana bata haƙuri kafin ta tsagaita da kukan.
"Baffa yace zamu tafi kar Yadado ta fahimci wani abu, Allah yasauke ki lafiya."
Tana gani suka fita jiki ba ƙwari, ta girgiza kai kawai tana addu,ar neman mafita.

Yadado ganin Baffa ya daɗe a masallaci tayi zargin anya kuwa bai bi bayar matar shi ba.
Tana cikin tunanin zuci taji sallaman su, tace, "yo ai nazaci kabi mayyar matar takace."
Tsugunawa yayi har ƙasa ya gaishe da yadado, ta amsa cike da isa, shima Abdul azeez ya gaishe ta, tana gutsirar goro ta amsa, "lafiya, tashi kaje ka ɗebo min ruwa arafi, ruwan rijiyar nan ta ƙafe."
Sadauki yace, "Yadado makaranta zan tafi."
"Kaji min sha-shanci, na aikeka kana cewa makaranta zakaje, ungo naka, maza kitashi kije ki kawomin ruwa, yo wani makaranta zaki, alhalin ba abinda ake koya a makarantar kaɗo sai rashin tarbiya."
Tashi yayi ya ɗauki tulu ya fita, dan yatabba yasake magana zata iya sawa yadaina zuwa makaranta.
Baffa yatashi yace, "Yadado bari nashiga garke naduba negge (shanu)."
Yatashi zaitafi tace, "madarar yau idan ka tatso ka kawo min, akwai wata Aminiya aminiyata zata zo ta ɗauka."
Inna wuro tana kicin tace, "Inna kin manta yau nishe da karɓar nono? Gobe nishe da talla, gashi gobe kasuwa."
"Yo yarinyar nan ai namanta, manu, yimaza kaje ka tatso tun kafin afita kiwo, ka tatso da yawa."
"To Yadado." Ya amsa yafice.
Koda ya isa garke zama yayi yakasa aikata komi, tunaninshi ɗaya wazaije yagaya ma kukan shi yazo ya lallaɓa Yadado akan yadawo da matar shi, duk cikin dangin su yarasa wazai tunkara, danhaka yatashi yasoma tatsar nono yana tunani, ahaka saida ya tatsi manyan bokatin fenta biyu, dan wannan karon shanayen sun hayayyafa da yawa.
Abdul azeez yana isa rafi ya ɗebo ruwa, anan yayi wanka.
Yana dawowa yaga alamar kamar Yadado tafita, dan haka yashiga ya ɗauki jakar buhun shi na zuwa makaranta ya fito zai tafi, Bala yace, "kaɗo harzakaje makarantar taku? Kamata yayi kishigo kigaida mauɗe ko."
Bai kulashi ba yafice abishi dan yau yayi latti.
Yana isa makaranta, yasamu ansoma tare latti, abinda bai taɓa yi ba kenan, gashi yau sanadiyar rashin uwar shi yayi latti.
Malam Iro yana ganin shi yace, "Abdul azeez ya akayi kayi latti yau?"
"Malam kayi haƙuri matsala aka samu yau, amma in Allah ya yadda bazan sake latti ba."
"Abdul azeez baka latti, sabida haka yau yaran nan sunci albarkacin ka kutashi kushiga class."
Yaran suka fara godiya yau ba'a duke suba.

***
Umma tana isa ƙauyen su tasanar da iyayen ta abinda yafaru, iyayen nata basu da matsala, dan kosu abin yayi musu daɗi,ace mutum yana da ciki yawuce watannin aihuwa ace baza aje asibiti aduba lafiyar taba, dan haka baban ta yace da innar ta su shirya anjima sutafi asibiti acikin garin Bauchi.
Aiko haka akayi, batare da ɓata lokaci ba, suka nemi mashin yafidda su hanya inda ake shiga motar Bauchi.
Suna isa asibiti, suka tambayi inda ake sayar da card, aka nuna musu, wani likita yana ganin su yaji tausayin su ya tambaye su mesuke buƙata?
Inna tayi mishi bayani, yace kuzo muje, suna tafiya yana tambayar su shin ta taɓa yin awu?
Inna tace, "a'a yaune zuwan ta na farko, likita dan Allah kuyi koma miyene zamu biyaku."
"Anyway, kubiyo ni muje.
Office nashi yakaisu, dakanshi ya iba jinin ta yaba ɗan aiken shi yakai lab (ɗakin gwaji).
"Tashi muje wajen scanning."
Sudai duk abinda yace yi sukeyi, suna isa inda ake scanning yaga mutane sunyi yawa, sa'an da yayi shine abokin shine yake duty, dan haka yashiga yamishi bayanin yanason yayi ma wannan petient ɗin scanning yanzu.
Batare da ɓata lokaci ba akayi ma umma scanning, shi kansa nauyin scanning ganin condition nata saida ya tsorata.
Tambayar ta yayi cikin ta wata nawane?
"Wata shaɗay, yanzu ma yashiga wata goma sha biyu."
Likitan yana ganin komi, dan agabanshi akeyi mata, kuma ya tabbatar da cewa operation za ayi mata a cire babyn, danhaka ana gama scan yace, "mukoma office.
Bayani yasoma yi musu cikin hankali da nutsuwa irin na likitocin da suka san makamar aiki, danhaka bayanin shi ya gamsar dasu, suka amince ayi aikin.
Batare da ɓata lokaci ba akashiga da ita operation room, cikin minti talatin likita ya kammala komi, inda yaciro baby gril fara kyakykyawar gaske, sai dai yarinyar bata da ƙoshin lafiya.
Ana fitowa da ita aka kaita ɗakin hutu.
Likita ne yayi ma Inna bayani, jaririyar bata da lafiya, itama tana buƙatar asai mata magani.
Inna tace, "likita kayi duk abinda yadashe, akwai kuɗi, zamu biyaka."



*Ummy Khaleel*

*Taku ce*
[1/7, 7:27 PM] FIRST CLASS: بسم الله لله الر حمن الر حيم

*ABDUL AZEEZ* (Sadauki)

*2020*

By ummy khaleel

*7&8*

_*SADAUKARWA GAREKI MY SWEET MUMMY JIDDA (BAIWAR ALLAH) INA ALFAHARI DA KAUNAR KI GARENI ALLAH YABAR ZUMUNCI*_

*GODIYA MUKE OGA YUSUF DA IRIN KULAWAR DA KAKE BAMU, MUNGODE ALLAH YASAKA MAKA DA ALKHAIRI*

______________________________________

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION*

FCWA

*home of qualities and trusted writers of the nation*

________________________________________

.........Duk wani kulawa da yadace yabasu yana iya bakin ƙoƙarin shi, Inna akoda yaushe addu,a takeyi ma Umma Allah yabata lafiya, ga yarinya ba cikakkiyar lafiya take dashi ba.
Shigowar doctor ne yakatse mata tunanin zucin da takeyi, file ɗin su ya ɗauka yagani, Umma tace, "likita kaduba min wannan yarinyar mana tun ɗazu taƙi buɗe ido."
Hanu ya ɗaura akan gashin ta yaji sanyi, ga kuma bugun ƙirjinta very slow, kallon Inna yayi yace, "wai ina mijin matar nan yake, baizoba?"
"Yana shan garin su amma zatazo likita lafiya?" Inna ta tambaya.
"Lafiya kalau akwai saƙon da tabani tace inbashi kafin ayi mata operation kuma a yanzu haka munason ganinshi."
Inna tace "yo likita komi zakiyi, kiyi kawai dan Allah nidai yaron nan yasamu lafiya shine burina."
Kallo ɗaya yasake yi ma Umma, duk da cewa yasan ranta ba a hanun shi yakeba, amma duk wani sign and symptoms na mutuwa sun bayyana atare da ita.
Allura yake ƙoƙarin yimata tayi saurin buɗe idanu tare da girgiza mishi kai alamar kar yayi mata.
"Dan Allah kayi ƙoƙarin bada saƙon nan ma mijina, Inna kiyafeni nidai nasan bazan tashiba."
Inna tace, "yo 'yan nan ai cuta ba mutuwa bace, in Sha Allah zaki tashi, zaki samu lafiya kinji Habi."
Likita fita yayi yabarsu yaje duba wasu petients (marasa lafiya).
Kwanan su uku a asibiti ba aba babu nono ba gashi uwar ma jiya iyau.
Baban Umma ne yazo dubasu, Inna tayi-tayi aje asanar ma Manu amma baban Umma yaƙi.
Akwana na huɗu ne Allah yakarɓi ran Umma, Inna tayi kuka sosai tare da yi mata addu,a, anan Bauchi akayi jana,izar ta, gashi ba asanar da Baffa Manu rasuwar ba.
Wata guda kenan da rasuwar ana tafaman jinyar jaririyar, Baffa yaje bingire wato garin su Umma yasamu basa nan maƙotan su ma basa an,' dan haka yadawo.
Abdul azeez yasha tambayar shi yaushe zaikai shi wajen Umman shi, Baffa cewa kawai yake zasuje insha Allah.
Ahaka dai har Allah yaba jaririyar lafiya wacce taci sunan mahaifiyar nata wato Habibah.
Madara baban yarinƙa saya ana bata, koda zasu koma bingire Baba yasai madarar kusan gongonin goma yace kafin ya ƙare adawo asaya wani.
Koda suka dawo gida maƙota da ƴan uwa suka rinƙa zuwa ganin baby, duk wanda yaga Habibah yaga mahaifiyar ta, saidai kawai haske da yarinyar take dashi amma kamannin kam babu maraba.
Yau Baffa yatashi da niyyar shiga bingire shi da Abdul azeez, tun asuba suka ɗauki hanya gashi babu abin hawa.
Koda suka iso bingire, Abdul azeez yace, "Baffa ƙirjina bugawa yakeyi kamar dai bani da lafiya nakejin kaina."
Baffa yace, "kana murna ne kawai zakaje kaga Umma ka."
"A a Baffa..." shiru yayi kawai saidai yarasa wani irin baƙon yanayi da yakeji.
Koda suka iso ƙofar gidan Sallama sukayi, Abdul azeez baijira amsawar su ba yashiige cikin gidan yana kiran "umma na, kina ina ne."
Kakar tasa ta kalleshi tace, "yo Abdul azeez daga zuwanka babu wanda zaka dara tambaya sai Umman ka."
Murmushi yayi yace, "Umma na nayi missing inason ganinta."
Inna tace, " oh hande enboni minene kuma missing?"
"Kewa" yafaɗa yana rarraba idanu yana son ganin ta inda Umman tashi zata fito.
Abdul azeez yaƙara tambayar ta "Inna Wai Ina Umma nane Please kifaɗa min inda take."
"Accu Mana Abdu kayimin hausa ko fillanci kawai nasan abinda kake faɗa meye kuma fulus."
Sallamar Baba da Baffa ne sukaji, Abdul azeez ya amsa da.
Inna tana ganin Baffa tayi saurin tashi tashige cikin ɗaki wai kunya irin na suruki, Baffa yasaba da irin ɗabi,ar Inna Dan haka yanemi guri ya zauna agefe.
Bayan sun gaisa da Baba, Abdul azeez yace "baban
wai ina Umma na takene?"



Next page


*Ummy khaleel*

*Taku ce*
[1/8, 7:16 PM] FIRST CLASS: بسم الله الرحمن الرحيم

*ABDUL AZEEZ* (SADAUKI)

*2020*

By ummy khaleel

*9&10*

*Wannan page naku ne ƙungiyar *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION INA MATUƘAR ALFAHARI DAKU ALLAH YABAR MU TARE*

_______________________________________

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION*

FCWA

*home of qualities and trusted writers of the nation*


______________________________________

......tashi yayi yashige ɗaki ya tarar da Inna tana kuka, "hande Innajo bazaki bar wannan kukan ba iye addu,a yakamata kiyi mata, ba kuka ba."
Ɗaukar yarinya yayi yafito da ita, yasan cewa Innajo bazata taɓa yadda tafito su haɗa ido da Manu ba sabida kunyar su ta fulanin asali.
Yana fitowa ya nufi Manu da yarinyar ya miƙa mishi ita yakoma ya zauna akusa da Abdul azeez.
Yakalli Baffa yace, "dukkan mai rai mamaci ne, inason kayi haƙuri da abin da zanfaɗa maka, Allah yayima ma Biba rasuwa, kwana arba'in kenan da suka wuce bayan jinyar da tayi."
Duk da dauriya irin na ɗa namiji bai hana Baffa zubda hawaye ba, Abdul azeez yace, "Baba umma na ta daɗe da rasuwa shine ba asanar mana ba?"
"Kayi haƙuri Audu laifi nane, kuma fushin surukar tashe yasa nashe basai anfaɗa maku ba amma kuyi haƙuri nayi laifi."
Baffa ya matse ƙwallar idanunshi yace Biba Allah yaji ƙanki da rahama, Allah yasa aljannace kakomar ki, nikam bakiyimin komi ba."
Abdul azeez yace Allah sarki Umma na kin mutu kinbarmu ni da ƙanwa ta Allah yayi miki rahma."
Hawayen dake zuba a idanun Baffa Abdul azeez yatashi yaje yasa hannu yana goge mishi yace, "Baffa a islamiyya ance babu kyau yima wanda ya mutu kuka, addu,a akeson arinƙa yimusu."
Baba yace, "haƙƙun maganar ka gaskiya ce addu,a yakamaci Biba."
Baba yace, "mun maida ma ɓingel (yarinya) sunan Umman ta."
"Allah ya raya ta da imani." Baffa yafaɗa.
Duk wannan dauriyar da Abdul Azeez yakeyi yanayi ne kawai dan baison ganin damuwar mahaifin shi, shikanshi yasan cewa yayi babban rashi a rayuwar shi, saidai yana tuna abinda aka faɗa musu a islamiyya cewa, mamaci addu,a yakeso ba kuka ba sai yaɗanji sanyi a zuciyar shi sannan yayi ta ma Umman shi addu,ar neman rahamar Allah da dukkan musulmai gaba ɗaya.
Da zasu dawo, Innajo tace akwai wasiƙa da Biba tabayar abaku, Abdul azeez yashiga ya karɓo wasiƙar yamiƙa ma Baffa.
Baffa yace, "aini ban iya karatun boko ba, amma nasan cewa kai ka iya ka buɗe ka karanta muji."
Ahankali ya buɗe takaddar yasoma karantawa kamar haka;

_"Assalamu alaikum ya Usman mijina, ina mai roƙon gafara agareka azaman da mukayi dakai na shekaru goma sha uku a matsayin mata da miji, ina roƙonka ka nemamin yafiya awajen surukata, tayafemin abinda nayi mata. Ga yarinya ta nan dan Allah duk wuya duk runtsi karku bari a ɗaura mata talla, nasan cewa Yadado zata tursasa maka karɓar ta, sabida haka gatanan amana._
_bdul azeez (sadauki) tabbas kai sadauki ne jajir tacce inason kazama mai biyayya ga Allah da manzon sa, ka riƙe gaskiya aduk inda kake hakan zaisa kaci ribar rayuwarka duniya da lahira, ga ƙanwar ka nan, nasan ragamar tarbiyyar ta zai rataya awuyan kane, sabida haka kayi iya ƙoƙarinka dan ganin ka bata tarbiyya mai kyau hmm *Abdul azeez* *(sadauki)* Allah ya jagoranci lamurran ka."_ kafin ya kammala karanta wasiƙar ji yake kamar ya rushe da kuka, yana gama karantawa yayi wani ajiyar numfashi, "yace namiki alƙawarin kula da ƙanwata in Sha Allah Umma na."

Koda zasu tafi Abdul azeez ya roƙi Baffa akan yabarshi yayi koda kwana biyu ne agurin Innajo, Baffa ya amince.
Koda Baffa yakoma gida ya sanar ma yadado rasuwar Biba.
Yadado tace, "Allah yaji ƙanta kwana ya ƙare idan angama anshayar da yarinyar sai aje a ɗakko ta, ina shi Audu?"
"Nabarshi acan gurin Innajo yayi kwana biyu."
"Maza katabbata gobe kaje ka ɗakko min jika yo in banda abinka ina Ni ina barin jika wajen kaɗo."
"In Sha Allah zanyi yadda kikace Inna."
Larai da Inna wuro ne suka doka uban sallama suna shewa yau kowacce tasayar da nono.
Inna tana ganinsu tace, "yaran albarka kindawo?"
"Mundawo Inna yau kasuwa tayi kyau."
Inna tace "haka akeso, kunji Biba ya mutu ko."
"Lah ha ilan ha illallahu yaushe hakan tafaru, ta aifune?" Larai ta tambaya.
Yadado ta sanar musu duk abinda yake tafiya.
Atare sukace "Allah yaji ƙanta tafuta." Kowacce ta nufi ɗakin ta.
Girgiza kai Manu yayi, dan ganin ko rashin kulawar su gare shi.
Maƙota sai zuwa gaishe da yadado akeyi ana mata ta aziyya dan su basu san abinda yafaru ba.
Bayan kwana biyu Yadado ta azalzala ma Manu akan yaje yadawo da Abdul azeez, ba yadda ya iya dole yayi abinda takeso.
Bello da Jafaru suna wajen kiwo sukaji rasuwar Umman sadauki, Bello yace, "Jafaru wannan kaɗon ya mutu ya huta kaga kenan yaronshi Audu yazama namu sai yadda mukayi dashi."
"Yo kai Bello tun yaushe nakeson namaida yaron nan jaki na amma namanta ta hana, yanzu ai tazama namu." Cewan jafaru.
Ahanyar su ta dawo wa daga bingire sun kusan isowa garin daɓe anan suka tsinci wata yarinya kwance agala baice tana numfashi sama-sama.
Baffa yace "ikon Allah wannan yaro daga ina kuma?"
Sadauki yace, "Baffa kawai kuɗauke ta taimako take nema."
Ɗaukar ta Baffa yayi akafaɗa har suka iso gida, inda suka tarar da jama,a a kusa da ƙofar gidan su suna tafaman ce ce kuce. Matar da take tafaman kuka tana faɗin "wayyo zuwaira na shike nan narasaki daga zuwa rafi ibo ruwa tun safe baki dawo...... Ganin Baffa da yarinya akafaɗa ta nufi wajen da gudu tana kiran, "zuwaira ! Zuwaira!" Tana zuwa tasa hanu ta karɓe ta tana tambayar Baffan Audu a ina kaganta?"
Baffa yace "ahanyar shi ta dawowa daga bingire anan muka ganta kwance."
Cikin gida ta wuce da ita inda baban yarinyar yayi Godiya shima yabi bayansu.
Kwantar da ita tayi akan gado tana kuka tana tambayar ta meyasa meta a Ina ta tsaya.
Zuwaira cikin wani irin wahalalliyar murya tace "yafendo mai gari ne yamin irin abinda ake cewa yanayi." yafendo tasa uban ihu tace shike nan yakashe ni, baban zuwaira kam yakasa cewa komi tabbas mai gari ya cuceshi yarinyar tashi kenan guda ɗaya tilo gashi ya ɓata mata rayuwa, gashi babu yadda ya iya, yasan cewa yanzu idan yayi magana za akore shi agarin.
Abdul azeez suna isa gida saida yafara gaishe da yadado kafin yatashi yashiga ɗakin Umman shi, jiyayi ƙirjin shi ya buga ras atunanin shi kamar zaiganta yakeji, wani hoton da sukayi tare yanufa yaciro yanemi guri ya zauna ya ƙura ma hoton ido, hawayen shi ya ɗiga akan hoton yace "Umma na Allah yaji ƙanki, Allah yakai haske kabarin ki."
Mauɗe da sule ne suka shigo cikin gidan da gudu suna haki, sule yace, "Yadado kinji wani abin mamaki kuwa?"
"Sai kafaɗa ango na metake faruwa ne?"
Bala yace, "mai unguwa ne tayi ma zuwaira lalata yarinyar da aka sanya mata aure watan ni shahuɗu da zasu zo yanzu ma naji ance zuwairan tamutu."
Yadado tana salallami tace, "oh ni Mairo, abinda mai gari yakeyi agarin nan yasoma yawa kai Allah yayi maganin abin."
Tashi tayi ta zari wani baƙin hibinta da ya koɗe harya soma canza kala tasaka tace "bari naje gidan naji abinda ke tafiya."
Abdul azeez yana ciki yana jin duk abinda yake faruwa, azuciyar shi yace "Allah ka kawo mana maganin wannan fitinar."
Fitowa yayi cikin gidan yasamesu suna cin tuwon dawa miyar kuka, ga uban warin daddawa dake tashi.
Kallon shi sukayi sule yace "kai ɗan kaɗo ashe Umman ka ta mutu?"
Baikula shiba yafice abinshi, inda yanufi garken shanun Baffa ahanya suka haɗu baffa yace, "yawwa Sadauki muje gidan su yarinyar da muka gani ahanya Allah yayi mata cikawa."
Abdul azeez yace "nima abinda nazo faɗa maka kenan." Juyawa sukayi suka nufi gidan su zuwaira, Abdul azeez suna isa yaga baban zuwaira ya tsuguna agaban makaran yana kuka yana cewa "Allah zai saka miki zuwaira in Sha Allah bazai gama da duniya lafiya ba."
Sadauki ne yadafa bayanshi cike da tausayi yace, "Baffa ba ayima mamaci kuka addu,a zakayi mata."
Ɗaukar gawan zuwaira akayi zuwa gidan ta nagaskiya.
Mahaifiyar zuwaira tayi kuka sosai tayi ma maigari Allah ya isa yafi a ƙirga.

Next page

*Ummy khaleel*

*Taku ce*
[1/11, 8:42 AM] FIRST CLASS: بسم الله الرحمن الرحيم

*ABDUL AZEEZ*(SADAUKI)

BY UMMY KHALEEL

*2020*

*11& 12*

KARKI KARANTA INHAR BAKI BIYABA

________________________________________

☀ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION* ☀

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the y*

_______________________________________

*Wannan page sadaukarwa ne gare ki Ummu xar een ina matuƙar alfahari dake ubangiji Allah yabar kauna*

*KUSKUREN DA MATA SUKE AFKAWA YAYIN 'DAUKEWAR JININ HAILA*
______________________

Mafi yawan mata idan jinin al'ada ya 'Dauke musu suna jinkirta wanka da niyar ko jinin zai Qara dawowa.

Wasu sukan Qara kwana 'Daya zuwa biyu bayan haila ya 'Dauke.

Wasu kuma idan suka ga alama guda 'Daya na 'Daukewar jinin, sai suce zasu jinkirta wanka domin su jira zuwan sauran alamomin. Misali: Mace taaga bushewar gaba amma bata ga Farin ruwa ba, wanda ake kiransa da larabci (قصة البيضاء), daga nan sai tace bari ta bari sai farin ruwa yazo sannan tayi wanka ta cigaba da sallah da azumi.

Duka Wannan kuskure ne babba ❌❌

Abinda yake wajibi shine: Da zarar taga jini ya tsaya ko taga alamomin Daukewar Jinin haila, toh wajibi ne tayi wanka nan take ta cigaba da ibadar ta. Qin yin wanka har lokacin sallah ya wuce babban zunubi ne.

Allaah ya tanadi Azaba mai tsanani ga masu wasa da sallah.

Allaah yace:-

" ﻓَﻮَﻳْﻞٌ ﻟِﻠْﻤُﺼَﻠِّﻴﻦَ ‏(4 ‏) ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻫُﻢْ ﻋَﻦْ ﺻَﻠَﺎﺗِﻬِﻢْ ﺳَﺎﻫُﻮﻥَ "
{ﺍﻟﻤﺎﻋﻮﻥ : 5-4 }

Allaah ya qara da cewa:-

" ﻓَﺨَﻠَﻒَ ﻣِﻦْ ﺑَﻌْﺪِﻫِﻢْ ﺧَﻠْﻒٌ ﺃَﺿَﺎﻋُﻮﺍ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍ ﺍﻟﺸَّﻬَﻮَﺍﺕِ ﻓَﺴَﻮْﻑَ ﻳَﻠْﻘَﻮْﻥَ ﻏَﻴًّﺎ "
{ﻣﺮﻳﻢ : 59 }

...... Da ayoyi masu yawa cikin al-Qur'ani.

daga lokacin da jini ya 'Dauke, ibada ya wajaba ga mace.

idan mace ta jinkirta sallah toh sai ta rama su bayan tayi wanka, sannan tayi istigfarin jinkirin sallah

*_Idan kin karanta kiyi Qoqarin turawa yar uwarki musulma zaki samu lada in shaa Allaah._*

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_______________________________________

............Acikin wata guda bayan rasuwar Zuwaira mai gari yayi ma yara mata shida fyaɗe, kuma duk cikinsu babu wacce ta haura shekaru goma sha biyu, wasu su rayu wasu su mutu, duk wannan abin da akeyi Abdul azeez yana mamakin shin wai mene fyaɗe shi baima sani ba, sabida ƙarancin shekaru irin nashi, sai yasan tabbas koma menene abun bashi da kyau.
Sanye yake da rigar su irin ta fulani mara hanu ya tokare da sanda ya harɗe ƙafa, yana kallon shanayen su da suke ta kiwo gwanin sha'awa.
Jiyayi an dafa bayan sa yajuyo sukayi ido huɗu da Baffa.
"Tunanin me kakeyi ne Sadauki?"
"Hmmm! Baffa ina tunanin wani abu ne wanda yake ɗaure min kai."
"Mekenan yake ɗaure maka kai Sadauki?"
Kamar daga sama ya hurgo mishi tambayar "menene fyaɗe Baffa?"
Baffa ya amsa mishi da faɗin "fyaɗe wani abu ne wanda ake aikatawa akan yara mata, ko ince harma da maza a wannan zamani namu a nayi musu fyaɗe, Sadauki duk yadda zanyi maka bayani a yanzu bazaka fahimta ba."
"Zan fahimce ka Baffa kayi min bayani kawai dan Allah."
Baffa yace shikenan yaci gaba da yi mishi bayani a takaice yadda zai fahimta, kuma alhamdulillah Sadauki ya fahimta, dan haka ya ƙuduri niyyar kawo ƙarshen matsalar idan ya girma, haka yaji yana son yakaranci community leadership kodan saboda ƙauyen su.
Yayi alƙawarin insha Allah zai ɗauki mataki akan wannan mai garin nasu mai lalata rayuwar ƙananan yara.

*TAKAITACCEN TARIHI*

Garin daɓe ƙauye ne dake cikin ƙaramar hukumar Bauchi, ƙauye ne na na fulani, duk da cewa ba wani yawa mutanen cikin ta suke dashi ba, sai dai Allah ya albarkaci fulanin ƙauyen da kiwon dabbobi ire-iren su shanu, akuyoyi da tumakai.
Acikin manyan makiwata ƙauyen malam Usman wato (Baffa) yana daga cikin manyan masu garken shanu, hakan yasa har wasu mutanen daga cikin gari suke ba malam Usman kiwon shanu, sabida yariƙi gaskiya a lamuran shi.
Malam Usman su uku ne awajen mahaifiyar su gaba dayan su maza, saidai shi malam Usman mahaifin shi yarasu, tun yana yaro, bayan gama takabar mahaifiyar shi Yadado ta sake yin wani aure inda Allah ya albarkace ta da aihuwar ɗa namiji wato Bello, bayan shekara uku da aihuwar Bello ta haifi ƙanin shi Jafaru, tun daga kan Lawal bata sake samun aihuwa ba.
Usman wanda ake kira da Manu tun bayan rasuwar kakar shi yadawo wajen mahaifiyar shi Yadado da zama.
Usman tun yana ƙarami yaro ne mai ƙwazo da hazaƙa gashi da zafin nema, bugu da ƙari abun hanun shi bai rufe mishi ido ba, ko fita aiki

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment