Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaisuwar inda yake tambayar shi ya Abdul azeez, Manu yace "Abdul azeez lafiya albishir nakeson nayi maka saniyar da kasaya waccan shekarar ta aihu."
"Alhamdulillah, ne ta haifa?"
"Namiji."
"Dama yanzu muke magana da mai ɗaki na zamuzo mu duba dabbobi sati mai zuwa."
"Allah yakaimu, na manta ban faɗa maka iyalina Allah yayi mata rasuwa."
"Innalillahi wa Inna ilaihi Raji,un yaushe?"
Manu yafaɗa mishi lokacin da akayi rasuwar, Alhaji Adam yamishi ta aziyya yace in Sha Allah gobe zasu shigo da matar shi harma da mahaifiyar shi suyi ta aziyya."


Next page


*Ummy khaleel*

*Taku ce*
[1/13, 8:10 PM] FIRST CLASS: .سم الله الر حمن الر حيم
*______________________________*
*ABDUL AZEEZ*(SADAUKI)

*2020*

by ummy khaleel

*15&16*

Karki karanta idan baki biya ba Naira ɗari ne kacal 💯

_____________________________________


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The notion}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*Wannan page sadaukarwa ne gareki my sis NAIMA Ina alfahari da comments naki ubangiji Allah yabar kauna*
*________________________________*

"Daddyn kids waya kake yi ne da Malam Usman."
"Wallahi kuwa, Allah yayi wa matar da rasuwa da jimawa sai yau ya sanar dani kusan wata uku kenan."
"Hmmm ni narasa zurfin ciki irin na malam Usman, ayi rasuwa baza ka sanar da mu ba aida tuni munje mungaishe su." Inji mummyn Waheed.
"Kushirya dake da yaran gobe zamu je, idan nafita masallaci anjima zanbiya na sanar ma Hajiya sai mutafi tare da ita."
"To Allah yakaimu Daddyn Kids."
"Bayan sallan isha,i Alhaji Adam yasami mahaifiyar tasa, bayan sun gaisa yake sanar mata dace idan tana da lokaci gobe idan Allah yakaimu zasuje ta aziyar matar malam Usman.
Hajiya Balaraba tace "to fa yaushe akayi rasuwar?"
"Kusan wata uku kenan amma sai yau yake sanar min."
"Usman akwai zurfin ciki, to Allah yakaimu goben sai muje."
Washe gari tun da asuba suka shirya, bayan idar da Sallah suka nufi ƙauyen tare da tarin tsaraba ire-iren su shinkafa, indomie, taliya, manja, mangyaɗa da dai sauransu.
Ƙarfe tara agarin yayi musu.
Abdul azeez ne sanye da rigar su irin ta fulani da hula sai wando irin na kayan kana ganin shi kaga fulanin asali, acikin garke yake, yana ba shanaye abinci da ruwa ya hango motar su.
Kafin yagama basu abincin sun ƙaraso wajen.
Alhaji Adam shi yafara buɗe motar yafito ya zaga yabuɗe ma mahaifiyar tasa tafito, Abdul azeez saida ya jin jina kai ganin yadda Alhaji Adam yake ba mahaifiyar sa kulawa.
Wani yaro ne ɗan gaye shima yafito wanda a ƙalla zasuyi sa,anni da Abdul azeez, yafito daga motar riƙe da yarinyar da bazata wuce shekara huɗu ba."
Sai mummyn Waheed wanda tafito a karshe da ƙaramar yarinyar da bata wuce watanni takwas zuwa tara ba.
Cike da ladabi Abdul azeez ya gaishe su, suka amsa mishi da fara,a saɓanin Waheed Wanda yake ji da kanshi kamar wani sarki.
Ganin yanayin yaron yasa Abdul azeez share tashan shi.
Alhaji Adam ne ya tambaye shi ina Abba shi?
Bai jima da tafiya gida ba yaje kawo maganin da zaiba saniyar da ta aihu.
"Waheed bakaga Abdul azeez bane?"
"Na gan shi ya ɗaga mishi hanu alamar sannu."
Abdul azeez yayi murmushi ya amsa da sannu da zuwa.
Sareena yarinyar da take hanun Waheed tana mishi murmushi shima murmushin yayi mata.
Suna isa gida dai-dai lokacin Baffa yana fitowa zaije garke.
Yana ganin su ya saki murmushi yace, "Alhaji har kin iso ku shiga ciki."
Yadado suka samu atsakar gida tana wanke waken alale, tana ganinsu ta hau washe baki tana faɗin, "baƙi mukayi ne kai sannunku da zuwa."
Tsugunawa har ƙasa Alhaji Adam da matar sa sukayi suka gaishe ta, ta amsa cike da fara,a suka gaisa da Hajiya Balaraba, tare da yi mata ta,aziyya.
Ɗakin Umma yakai su suka zauna yafito ya aika Abdul azeez da Naira ɗari yasayo musu ruwa.
Abdul azeez yana dawowa daga sayo ruwa Yadado tashiga ta kai musu damammen fura, Bello da Jafaru ne suka shigo gidan a hargitse suna tambayar ina baƙin?
Ɗakin Manu suka shige da gudu kamar mahaukata har saida Sareena da waheeda suka tsorata.
Inda kasan jakuna haka sukashiga, Sareena tace "Daddy are they mad?"
Daddy ya ce "no" yashare zancen dan yasan sareena da surutu da tambaya.
Waheed cike da takaici yace "they are mad, can't see the kind of hab......bai ƙarasa maganar sa ba yaji Abdul azeez yace "don't try to abuse my family in my present."
Cike da mamaki Waheed ya kalli Sadauki, dama ashe yana jin turanci yafaɗa acikin zuciyar shi, shi a tsammanin shi Abdul azeez baijin turanci.
Ko shi kanshi Alhaji Adam yayi mamakin Abdul azeez.
"Abdul azeez ajinka nawa a makaranta?"
" Ina aji shida ne wannan shekarar zan fita nashiga secondary."
"Allah Sarki Allah ya taimaka, me kakeson ka karanta idan ka gama makaranta?"
"Village development."
"Amma meye dalilinka na karantar *village development*?"
"Ina da wani buri araina akan wannan ƙauyen tamu da ta mahaifiya ta."
Sun ɗan taɓa hira sosai, dazasu tafi Alhaji Adam ya roƙi Usman da ya bashi Abdul azeez.
Manu yace "bani da iko da sadauki, ki da Ni zan amince maka mahaifiyata baza amince min ba.
"Idan har zaka amince na tabbata mahaifiyar ka zata amince idan kabani izini zangwada tambayar ta."
"Shikenan ka gwada." inji Manu.
Koda alhaji Adam yasami Yadado da zance, da farko ta amince, Jafaru yace "Yadado so kike aje a kafirta Audu ko nan gaba idan yazama maye ke zaifara kashewa kinga kenan munrasa ki."
Yadado ta yadda da maganar Jafaru dan haka tace gaskiya baza atafi mata da jika ba aje akoya mishi halin yan iska.
Dole ya haƙura, Hajiya Balaraba tace "shikenan, mutanen ƙauye kunayi ma mutanen Maraya mummunar zato amma bakomi, koni naso yaron nan dan yanada niyya mai kyau acikin zuciyar shi."
Tsarabar da suka kawo musu Jafaru da Bello suka fara kwashe wa, suna cikin kwashe wa Laure da Inna wuro suka dawo daga tallar nono.
" Iyyyi yau baƙin burni mukayi kenan sannunku, wani ƙara sukaji ana hele aradun Allah yau agidan mu za a yanke namun dajin nan, su mauɗe da Bala ne suka nufo wajen.
Mauɗe yana ganin niƙi-niƙin kaya yace "aradun Allah yau akwai cin daɗi a gidan nan mutan birni sunzo."
Ihu sukayi irin na mafarauta, suka ƙarasa wajen suna buga sanda.
Waheed tsabar haushi ya shige moto yayi zaman shi.
Godiya Manu yayi musu tare sosai hakama Yadado.

*BAYAN SHEKARA BIYU*

"Manu, Manu, Manu Wai ko baka nan ne ina takiran ka baka amsaba."
"Kiyi haƙuri Yadado ina kama ruwane gani."
"So nake gobe kaje ka ɗakko yarinyar nan me ma sunan ta, Habibah ko, to maza gobe kashirya kaje ka ɗakko ta."
Ji yayi kamar an sara mishi adda akayi dan jin abinda Yadado ta faɗa.
"Bakaji nane kayi shiru kamar kurma?"
"Allah yakaimu goben."
Haya-hayan da sukaji ne yasa Manu yace,b"bari na duba naga meke faruwa."
Wata yarinya ce batafi shekara biyar ba an tsinto ta adaji anyi mata fyaɗe, mahaifiyar ta sai kuka takeyi tana Allah ya'isa duk wanda yayi mata irin wannan aikin.
Abdul azeez sanye da uniform yadawo daga makaranta yana kallon yadda mahaifiyar yarinyar take kuka sosai harda share majina, ya tausaya mata sosai yawuce.
Tambayar yarinyar akeyi wayayi mata irin wannan aika-aika? Yarinyar ko magana bata iyayi, numfashi sama-sama takeyi.
Haka dai aka haƙura aka barta.
Washe gari da safe Manu ya shirya tsaf zuwa ɗakko Habibah.
Koda ya isa ƙauyen bingire Baffa yafara samu a wajen shanye yana kula dasu.
Bayan sun gaisa yayi mishi bayanin abinda yakawo shi.
Baffa yasan za arina dan haka yace karya damu suje ahaɗa kayan Habiba su tafi.
Koda suka iso gida Baffa yasanar da Innajo za atafi da Habiba, Innajo duk da kunya irin nata tace, "naso kubarmin Biba tarinƙa ɗebemin kewa amma nasan hakan bazai yuwuba." Tana hawaye ta haɗa kayan Habibah acikin leda mai ƙayau-ƙayau.
Tana kallo aka tafi da Habiba ba Yadda ta iya, shima Manu yaso barin mata yarinyar saidai yana tsoron halin Yadado to sai muce Allah ya kiyaye hanya Habibah


Next page


*UMMY KHALEEL*

*TAKU CE*
[1/15, 9:51 AM] FIRST CLASS: .سم الله الر حمن الر حيم
*______________________________*
*ABDUL AZEEZ*(SADAUKI)

*2020*

by ummy khaleel

*17&18*

Karki karanta idan baki biya ba Naira ɗari ne kacal 💯

_____________________________________


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The notion}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp


*________________________________*
AMFANIN KABEJI GUDA GOMA (10) GA LAFIYAR JIKIN DAN ADAM:

1- Yana karawa kwakwalwa kaifi.
2- Yana taimaka wajen rage kiba.
3- Yana karawa fatan jiki kyeu.
4- Yana wanke dattin ciki.
5- Yana karawa garkuwan jiki karfi.
6- Yana yaki da cutar cancer ko wacce iri.
7- Yana saukaka ciwon kai.
8- Yana Daidaita suga.
9- Yana taimakawa masu gyembon ciki.
10- Yana Kare mutum daga kamuwa da cutar zuciya.

Allah yayi mana jagora


*17&18*

Koda suka iso gida Manu atunanin shi Yadado zatayi farin ciki da dawowar Habiba, sai yaga akasin hakan.
Ɗakinta yanufa yasameta tana sana,ar nata wato cin goro.
Ko kallon yarinyar batayi ba tace, "aiki yasame ka idan zaka kula da yarinyar sai ka kula da ita kasan dai Ni natsufa bazan iya kula da yara ba."
Jafaru yace, "Yadado kigama shin kashin mu sannan kuma kiyi na jika ai ƙarya kenan."
" Yo banda abinka me zaikaini rainon ɗan kaɗo, aishi zai kula da abinshi."
Tashi yayi da Biba suka fita kasu yanufa yasai mata shinkafa da wake yabata taci.
Bayan sun dawo ya haɗa murhu ya dafa ruwan zafi yayi mata wanka ya shafa mata mai ya canza mata kayan jikin ta.
Abdul azeez ne yadawo daga makaranta yana ganin Biba ya rungume ta yace "ummy na kindawo?"
Murmushi Habiba tayi tana kallonshi tajuya ta kalli Baffan nasu ta kafe shi da ido.
Sadauki yace "nine yayan ki sadauki, daga yau kirinƙa kirana yaya sadauki kinji ummy na."
Murmushi tayi ta sauka daga jikin Baffa ta je wajen shi, cikin maganar ta irin na yara da fulatanci tafe "ne indema?" (Me sunanka)
Sadauki yace "bakiji abinda nace miki ba kenan, Sadauki."
Baffa kallon su yakeyi cike da so da ƙaunar yaran tashi yayi yace zai wuce garke yaje yabasu abinci.
"Baffa kabari kawai bari na cire uniform sai naje nabasu kai ma kahuta."
Murmushi Baffa yayi yace "Allah yayi maka albarka Sadauki, kaci abincin sai mutafi tare."
Yana gama cin abinci yayi alwala yayi sallah yaɗauki ƙanwar shi suka nufi garke.
Haka rayuwa tayi ta tafiya da daɗi ba daɗi a gidan Manu, Inna wuro da Laure ko kula sha'anin Sadauki da ƙanwar sa basayi, ko yaransu ma basa samun kulawa balle wasu, neman kuɗin su kawai suka sa a gaba, hakama Yadado neman kuɗin ta takeyi, hatta yaransu farauta tazame musu jiki, basa taimakon iyayen su ga shegiyar ƙazanta dake damunsu, su Bello kam idan suka nisa kiwo sai sufi wata biyu basu wai-wayo gida ba sabida sunsan akwai mai ciyar musu da iyali.
Bintalo ce ta shigo gidan da gudu tayi tsokana, Yadado tana ganinta tace, "yau nan aka nufo kenan wakika tsokana?"
Bintalo ta turo baki tace tace "wasu yara ne suka biyo ni wai zasu duke ni banyi musu komiba."
"Anya Bintalo bake kika nemi tsokana ba kuwa nafasan halinki sarai?"
"Shi yasa banson zuwa gidan nan wallahi kincika masifa Yadado."
"Ai dole kice nacika masifa tunda bakyason gaskiya, kishiga ɗaki akwai sauran ƙosai ki ɗauka, iyayen naki sun fita kasuwa."
Ɗakin Yadado tashiga ta ɗauki ƙosai tafito cikin gidan tasoma ci, Sadauki riƙe da hanun ƙanwar suka shigo gidan, gaishe da Yadado yayi Habiba itama ta kwaikwayi yadda yayi.
Yadado tace "kini babbiya."
"Yadado waye wannan?" Bintalo ta tambaya.
"Ƙanwar Audu ce, aka dawo da ita."
Taɓe baki tayi taci gaba da cin ƙosan ta tana ɗan waƙe-waƙen ta.
Ɗaki suka shiga ya ɗakko kunun da Baffa ya sayo musu da alale yaba Biba, Biba tace ita sam da ƙosai takeso inba haka ba baza taciba.
Yana da naira ashirin dan haka yafita yaje yasiyo mata ƙosai takawo yabata, bata wani ci ƙosan ba tace ta ƙoshi, suna gama karya wa ya share ɗakin yaja ya kulle ya ɗauke ta suka fice.

***
Alhaji Adam ne zaune a cikin ƙayataccen office ɗin shi wanda za a iya kira da aljannar duniya, office ne irin na manyan mutane, masu ji da naira.
Wani takadda ke gabanshi wanda yajima yana nazari akai, wayar shi ce tasoma ringing, ganin Mai kiran yasa shi saurin ɗaga wayar tare da amsawa. Kara wayar yayi a kunne tare da faɗin "assalamu alaikum kum, malam Usman dafatan kana lafiya?."
"Lafiya kalau Alhaji, kwana biyu dafatan dai lafiya, naji ka shiru shine nace bari dai na kira naji ko lafiya?"
"Alhamdulillah lafiya kalau, ayyuka ne sukayi min yawa akai shi yasa kaji shiru, abubuwa sunkusa zama daidai in Sha Allah zan leƙo mugaisa, badai wani abu ko?"
"A babu komi gaisuwa ne kawai, dabbobi kuma alhamdulillah, jiyama wata tinkiyar ka ta haifo 'yan biyu maza."
"Masha Allah, Allah yaraya su Nagode sosai da kulawar ka akaina malam Usman, kazame min tamkar ɗan uwa, gashi dama nikaɗai ne awajen mahaifiya ta gashi yanzu alhamdulillah nasameka kazame min ƙani wanda nake alfahari dashi."
Murmushi Manu yayi yace "to Allah yataimake mu, yaushe zaka leƙo duba dabbobi?"
Alhaji Adam yace "Ni ba dabbobi zanzo na duba ba ku zanzo naduba, wai ina yarona Sadauki ne?"
"Sadauki yatafi makaranta sai ƙanwar sa, kasan naje na ɗakko ta."
"Allah Sarki kagaishe min dasu sai nazo."
"Nima agaida min da mutanen gida."
Abdul azeez ne sanye cikin uniform nashi yashirya zai tafi makaranta, ga Biba ta naniƙe mishi kuma yasan dole tare zasu tafi tunda yasan babu wacce zata kula mishi da Biba.
Jakar buhun shi na zuwa makaranta ya ɗauka, ya goya Biba har sunfita ƙofar gida ya manta da biron shi a kan kujera ya ajiye Biba yace "ina zuwa jirani na ɗakko biro na."
Yana fitowa daga ɗaki yaji ihun Biba a guje ya fito yasamu Bintalo ce take zabga mata bulala, aikuwa wani wawan fincikar ta yayana faɗin *"WALA HORE KO* (baki da hankali)"
Ɗaukar Biba yayi suka tafi, tun kafin Yadado tafito tasamo masifa.
Bintalo da kuka tashiga gidan wai Abdul azeez ya bigeta batayi mishi komiba, Laure tafito da sauri tana faɗin "ina shi kaɗon?"
Bintalo tace "yatafi mana wai sai yakashe ni tunda na bigar mishi ƙanwa."
Inna wuro ce ta fito da tsohon cikin ta tace, "rabu dashi zai zo ya sameni daga shi har mayyar ƙanwar tasa, *War mu dilli yami marori* (zo muje muci shinkafa) aiko Bintalo da murnar ta tace "yawwa dama nagaji da gidan su yafendo kullum tuwo sai gwate." Wato gidan su kakar ta kenan.
Abdul azeez yana isa makaranta yara sai kallon shi sukeyi wasu na mamaki wasu na gulma wai namiji da goyo.
Wani malamin su ne ya hango shi ya sa yara suka kirashi.
Cikin ladabi da biyayya ya sauke ƙanwar tashi abaya ya gaishe da malamin cikin harshen turanci, wannan ɗabi'a na Abdul azeez yana burge malaman makarantar, bayarda za'ayi kaji Abdul azeez idan yashigo school compound kaji yana speaking hausa.
"Abdul azeez wannn yarinyar kuma daga ina?"
"Ƙanwa tace mahaifiyar mu Allah yayi mata rasuwa shekara biyu kenan."
Malam Ali yace, "Allah yaji ƙanta da rahama, babu mai kulawa da ita ne dahar ka ɗakko ta zuwa makaranta?"
Cikin sanyin jiki Abdul azeez yace "dole yasa nazo da ita sabida wasu dalili masu ƙarfi."
"Wani dalili kenan Abdul azeez?" Malam Ali ya tambaya.
Abdul azeez yace "bazan iya faɗa maka ba malam, amma dan Allah karku koreni akan wannan abu, zai iya yuwuwa har na kammala makaranta ina zuwa da ita."
"Kafaɗa min matsalar ka Abdul azeez, mai yuwa ina da hanyar da zan magance maka ita, na ɗauke ka tamkar ɗan da nahaifa a ciki na, kafaɗan min komi karka ɓoye min."
Ganin yadda malam Ali ya damu da damuwar shi ya sanar mishi dukkan abin da ke faruwa.
Malam Ali yayi matuƙar tausaya mishi dan haka yace in Sha Allah zai taya shi kula da yarinyar har Allah yasa itama takai shiga makaranta.
Abdul azeez yayi mishi godiya sosai tare da yi mishi fatan alheri a rayuwar shi.
Bayan an tashi daga makaranta Abdul azeez bai nufi gida ba garken shanun su yanufa shida ƙanwar tasa dake goye abayan shi.
Anan suka samu Baffa yana kishingiɗe a inuwar bishiyar mangoro.
Baffa tana ganinsu yatashi ya zauna, suna ƙarasowa wajen Abdul azeez ya gaishe shi, itama Biba ta kwaikwayi yadda yayan nata yayi cikin halshen fullanci, Abdul azeez cikin halshen turanci yace mata kinyi ƙoƙari.
Bata fahimci abinda ya faɗa ba murmushi tayi kawai.
Baffa yace "kundawo, Abdul azeez Allah yayi maka albarka, tabbas ina jin daɗin yadda kake kulawa da marainiyar ƙanwar ka Allah ya tsare min rayuwar ku, ina fatan tafiya da ita makaranta da kakeyi bazai shafi karatun kaba?"
"Ana Baffa malam Ali yace kar na damu shima zai sa akulamin da ita, kuma yace zai sanar da matarshi idan zantafi makaranta narinƙa kaita wajen matar shi, idan muntashi sai naje na ɗakko ta."
"Allah Sarki mungode idan Allah yakaimu goben sai muje nima nayi mishi godiya." Inji baffa.
Bayan sun dawo gida Laure ta rinƙa masifa, tana zaginsu ta uwa ta uba harda tsine musu wai Abdul azeez ya bigi Bintalo.
Abdul azeez baice komiba abincin su kawai suke ci da ƙanwar shi, suna gamawa yace "karki fita bari naje nayi wanka ko." cikin halshen turanci yayi mata magana.
Bayan gidan yanufa da bokiti a hanu, ashe Laure tana ankare dashi, koda taga yaɗan jima tacire sucket ɗin Radio ta nufi ɗakin takama Biba cike da rashin imani ta rinƙa zabga mata sucket bida sai faman ihu takeyi.
Jin ihun ta Abdul azeez yayi saurin watsa ruwa ajikin shi yasa gajeren wandon shi yafito yanufi ɗakin aguje, ganin yadda Laure take zuba ma Biba wayar wuta yayi wani kukan kura ya fizge igiyar yajefar yaɗauki Biba yana lallashin ta, nan take jikin Biba ya kumbura.
Laure tasa ihu tana kuka, mauɗe da Bala suka fito daga ɗakin su aguje suna tambaya cikin halshen fullanci lafiya?
Ƙarya da gaskiya ta faɗa musu wai Abdul azeez ya bigeta, aiko sukayo kan Abdul azeez su biyun da gudun su na masifa, matsa musu yayi suka faɗin rub a ƙasa, ko wannen su ya tashi yana huci kamar kubu-buwa.


Next page


*Ummu Khaleel*


*Taku ce*
[1/15, 4:39 PM] FIRST CLASS: بسم الله الرحمن الرحيم

*ABDUL AZEEZ*(SADAUKI)


*2020*

BY UMMY KHALEEL

*19&20*

KARKI KARANTA IDAN KINSAN BAKI BIYA BA Naira 💯 kacal

________________________________________

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION*

FCWA

*home of qualities and trusted writers of the nation*

*Wannan page din sadaukarwa ne gareki A'isha Ibrahim (mum) Ina alfahari da comments naki ubangiji Allah yabar kauna*

_______________________________________
*19&20*

.............Mauɗe ne ya ƙara nufarsa da gudu, Abdul azeez yasake darewa saura ƙiris ya faɗi Allah ya tsare shi, Laure tace "wallahi yau sai naci ubanka Audu wato nizaka zaga kana ƙoƙarin duka na, mauɗe yace ai wallahi yau saina feɗe banza a gidan nan."
Bala kam kallon su kawai take dama shi ba ƙarfi yake dashi ba.
Wani kallon banza Abdul azeez yayi mishi yace, "kai kufita a ɗakin nan bani da lokacin ku."
Laure tace "gidan ubanka ko gidan ubansu, ai Manu bashi da gado a gidan nan arziƙi kawai yake ci."
Rigar shi ya ɗauka yasa yaɗauki Biba suka fita suka barsu a ɗakin.
A koda yaushe yadawo daga makaranta bashi da gurin zuwa da yawuce garken shanun mahaifin shi yabasu abinci ya kula dasu shine kawai aikin shi, a duk ranar Laraba kuma yafita tallen shi da ƙanwar shi, tun bata saba ba har tasoma sabawa.
A duk ranar asabar kuma yakan kai dabbobi kiwo kusa da gida, haka zai ta yawo da Biba.
A haka har Allah yasa Habibah tafara wayo, duk maganar da yaya Sadauki zaiyi mata da turanci yakeyi mata ko kuma fullanci, kuma tana ganewa.
Inna wuro ce ta haifo ɗiyar ta mace mai kama da ita sak, aranar suna akasa mata sunan Yadado wato Hafsatu.
Yadado tayi murnar wannan takwara da akayi mata, dole tasa manu ya nemo ƙaton rago a cikin ragunan shi ya bayar aka yanka aranar suna.
A yanzu Habibah tana da shekara shida Sadauki yasata a makaranta, Yadado tatuma tace sam saidai acire Habiba a makaranta, kuma daga yanzu ta daina bin sadauki makaranta itama tafara zaman gida.
Da farko sadauki yaso yaƙi yadda da maganar Yadado, sai kuma mahaifin shi ya take mishi birki.
Sadauki yaji ciwon hana ƙanwar shi karatu da akayi saidai a cikin ranshi yayi alƙawarin zai koyar da ita karatun boko dana addini, wanda zai taimake ta anan gaba.
Da haka Sadauki yasayo mata littafai idan dare yayi zasu kwanta ya rinƙa koya mata karatu da rubutu. Haka kuma bai daina yi mata magana da turanci ba, dan ko acikin gidan ne idan suna maganar su da turanci sukeyi,saidai Biba tana matuƙar tsoron Laure da Inna wuro da Yadado.
Haka Hafsatu saita bigeta ba abinda zasuce.
Bintalo kuwa anfara zama 'yan mata dan har anfara tsayawa da samari, abin haushin kuma bata da kamun kai iyayen sun saketa tana abinda taga dama.
Yau asabar Abdul azeez baije kiwoba yana wanke musu kayan sawan su.
Biba ce ke zaune kusa dashi tana karanta mishi ا ب ت har zuwa inda suka tsaya, shikuwa yana cemata جميل hakan yana matuƙar ba yaran gidan haushi, musamman mauɗe da Bala da Bintalo, sauran yaran kam antura su yawon almajiran ci, ba asan cin suba ba'asan shan suba.
Cikin halshen turanci Abdul azeez yace "mummy na je ɗaki cikin aljihun wando na ki ɗakko kuɗi muje nasaya miki lemo da ayaba ko."
Mauɗe dake shan sigari yace "aradun Allah ina ma ina jin abin da akeshewa inshi uban mutum."
Da gudun ta tafito tana cewa "gashi yaya itama da turancin take magana."
Bala yadaka mata tsawa yace tazo.
Jikin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment