Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi yasami kuɗi kai tsaye zai kai ma Yadado, saidai kuma abin haushin shine, duk wani abin burgewa da zaiyi mata bata taɓa gode mishi bare yabawa, ƙarshe ma kuɗin a kan yaranta Bello da Jafaru yake ƙarewa.
Ahaka shekaru sukayi ta tafiya, har cutar ajali ya kama mahaifin Bello, saidai babu mai kulawa da shi da ya wuce Manu, kullum idan Baffajo suna tare da Manu nasiha yakeyi mishi akan yayi haƙuri da ban-bancin da Yadado take nuna musu in Sha Allah wata rana sai labari, haka dai zaiyi ta mishi wasiyya.
Satin Baffajo ɗaya da cutar Allah yaɗauki ranshi, saidai Bello da Jafaru ko ajikin su inda kasan ba mahaifin su yarasu ba.
Bayan kwana arba'in, da rasuwar mahaifin nasu, Jafaru ya matsa saidai araba gado, dashike Abdul azeez (Baffajo) mahaifin su yabar musu gadon shanaye, dan haka dole aka taba gado, ko kyautar dabba ɗaya basu ba Manu ba, shima dai manu bai damu ba, dan yasan bashi da gadon Baffajo.
Ahaka rayuwa take tatafiya har manu yakai aure, Saidai bashi da sana,ar yi.
Ana cikin haka wata ranar laraba yashiga kasuwa kamar yadda yasaba, ya tarar da wani mutum yana taya wani shanu, zai saya Manu yazo wucewa mutumin yace "ɗan fillo zo mana, daganin ka nasan zakasan dabba mai kyau dan Allah dabbar nan tana da kyau?"
Manu yayi murmushi ya ƙara so inda mutumin yake, yakalli shanun da kyau ya girgiza mishi kai yace "gaskiya wannan ba shanu mai lafiya bane, duba da yanayin fuskar shanun da idanun shi."
Aikuwa mai shanu yace "baƙin ciki kakeyi dan za asaya dabba na shine kake kishi, gashi har yau ka'isa aure baka da sana,ar yi."
Manu yayi murmushi yace "aure nufi ne na Allah, Alhaji muje na duba maka dabban da zaka saya mai kyau da lafiya, idan kiwo zakayi?"
Binshi kawai Alhaji yayi suka nufi gurin wani mai shanu Manu yace "wannan dabbar tana da kyau na sayar wane?"
"Eh nawa zaku saya?" Inji mai shanun.
"Kai dai kafaɗa nawa zaka sayar, Alhaji kiwo zakayi?" Manu ya tambaya.
"Eh kiwo ne."
Anan dai suka taya shanu aka sayar musu, Alhaji ya biya kuɗi Manu ya tambaye shi "ina za akai shanun?"
Biyoni kawai yace
Manu yariƙe mishi shanu yabishi har wajen mota,ashe ma ba shanu ɗaya yasaya ba sunkai biyar da na hanun shi shida kenan.
Alhaji "tace Nagode fa da kulawa menene sunan ka?"
"Sunana Usman (Manu)."
"Menene sana,ar ka Usman?"
Murmushi yayi yace "ni bana sana,ar komi."
Alhaji yace "duk da baka tambayi sunana ba, sunana Alhaji Adam ina zaune agarin Bauchi, gaskiya bazan ɓoye maka ba ka kwanta min arai sosai, shin ko zaka iya min kiwo?"
Manu ya dafa kirji yace, "gaskiya Alhaji idan nace zanyi maka kiwo nayi ƙarya, dan bansan inda zan ajiye maka dabba ba, kaganni ko filin da zangina idan zanayi aure bani dashi."
"Karka damu da wannan idan ka amince nizan sai maka filin da zaka ajiyemin dabbobi harma da na wasu."
"Eh to wani hanzari ba gudu ba, ko da zan amince da hakan nafison kaje kasami mahaifiyata kayi mata bayani idan ta amince falillahil hamdu."
"Shikenan muje."
Suna isowa ƙofar gidan Manu yace "bari nasanar mata zuwanka."
Yadado yasama suna ta hira da Jafaru, shima zama yayi ya gaishe ta sannan yayi mata bayanin abinda ke tafe dashi.
"Shigo dashi naganshi, dan banason abin magana daga haɗuwa da mutum shikenan yace yana sonki, kilamma ɗan yankan kai ne."
Acikin moto ya sameshi yayi mishi izinin shiga cikin gida, Yadado tana ganin shi tasan mutumin akwai Naira, dan haka tasaki ranta sosai dashi, Jafaru kam kishi da tsanar Manu ya dirar mishi, gaisuwar da mutumin yayi ma Yadado yakatse mishi tunanin shi.
Yadado cike da fara,a ta amsa harda tambaya "ya iyali."
Murmushi Alhaji Adam yayi yace "bani da iyali amma nan gaba kaɗan zanyi aure in sha Allah."
Da mamaki tace "hande baka da iyali kace kaima tuzuru ne."
Murmushi kawai yayi, nan ya sanar ma Yadado da buƙatar shi, Yadado ta amince dan haka Alhaji Adam yace ayi mishi cigiyar fili zai saya dan ajiye dabbobin shi.
Ko sati ba ayi da maganar ba aka samu wani babban fili dake kusa da gidan su Alhaji Adam yasaya haryasa aka gina mishi store na abincin dabbobi.
Nan da nan kiwo yafara, Jafaru da Bello sai kuma suka ƙullaci Manu acikin zuciyar su.
Tsakani da Allah Manu yake kulawa da dabbobin Alhaji Adam, idan ka gansu tubarkallah masha Allah.
Bayan wata biyu da haɗuwar su Alhaji Adams ya kawo ma Manu invitation card na Auren shi.
Aikuwa baiyi ƙasa agiwaba yaje ɗaurin auren, wannan shine karo na farko da Manu yafara shiga birnin Yakubu.
Anyi biki har sabbin ɗinki Alhaji Adam yayi ma Manu, idan kaga Manu bazaka taɓa tsammani shi ɗan ƙauye bane.
Dashike yana da ƙirar wayayyun mutane.
Bayan gama biki mamu ya shirya dawowa inda Alhaji Adam ya haɗa mishi shatara na arziƙi, Manu yayi Godiya sosai.
Bayan wata biyu manu yahaɗu da wata budurwa awajen kiwon shanu itama kiwon shanun takeyi sanye take da rigar saƙi irin na fulani da sandar ta taraya a kafaɗa.
Anan dai suka ƙulla soyayya duk da cewa awannan lokacin Habibah, tagama primary dangin Mahaifin ta suka matsa lallai sai a aurar da ita.
Dan haka batare da ɓata lokaci ba akayi bikin Habibah da Usman.
Habibah su biyu iyayen su suka haifa yayan ta Habu namiji wanda aƙalla zasuyi sa,a da Manu.
Tunda akayi auren Yadado ta rinƙa gallaza ma Habibah masifar yau daban na gobe daban, Allah yasa Habibah tana da haƙuri sosai, gashi duk wani abun da yadace tayi ma Yadado amatsayin ta na uwar miji, bugu da ƙari Bello da Jafaru sun raina ta ko abinci tayi haka zasu cinye harma da na mijin ta, idan tayi magana Yadado ta hauro mata da masifa tazageta uwa ta uba.
Ahaka har aka shafe wata uku Habibah batasan daɗin gidan aureba ko ince daɗin uwar miji.

Watan su shida da aure Alhaji Adam yakawo musu ziyara tare da duba dabbobin shi.
Manu Yana cikin ba dabba ruwa yahango motar shi, da fara,ar shi yanufi inda yake suka gaisa tare da shiga cikin garke, Alhaji Adam yayi matuƙar mamakin canzawar shanayen cikin ƙaramin lokaci.
Manu yace "yakaga dabbobi, sunyi kyau."
"Dabbobi alhamdulillah gaskiya na yaba sosai Allah yasaka maka da alheri."
"Ameen."
Anan dai manu yake sanar mishi cewa yayi aure.
Alhaji Adam yace "yaushe kayi aure ban sani ba gaskiya nayi fushi tunda ba agayyace niba."
"Kayi haƙuri abubuwan ne sunyi yawa."
"Nayi maka uzuri muje nagaida amarya."
A kicin suka sameta tana tafaman uban hura wuta gaba ɗaya idanunta sun canza sunyi jazur, tausayin ta yakama shi, jin sallamar su yasa tatashi tafito tana share hawayen tsaban hayaƙi.
Alhaji Adam yace, "malam Usman dama kana da ƙanuwa mace?"
Murmushi Manu yayi yace, "itace mai ɗakin nawa."
"Oh yi haƙuri, Madam barka dai."
Cike da kunya tashige ɗaki da gudu, Manu yace "haka Habibah take."
Kuɗi yaciro ya miƙa mishi yace to ga wannan aba amarya idan zandawo zantaho da mai ɗakina kugaisa."
"A,a Alhaji ɗawainiyar tayi yawa, dan Allah kabari kawai."
"Amarya zakaba tunda anƙi gayyatar mu."
Karɓa yayi tare da yimishi godiya.
Bayan tafiyar shi yaba ma Biba kuɗin da aka bata taki karɓa, yace shikenan zai saya mata saniya yayi mata kiwo.
Ita dai batace komi ba Kitchen tashiga ta ƙara sa aikin ta.
Alhaji Adam ya girmi Manu da shekaru shida, dan haka Alhaji Adam yaɗauki Manu amatsayin ƙani.

Bayan shekara uku da auren su ko ɓatan wata bata taɓa yiba balle ɓari.
Shirye shiryen ɗaurin auren Bello da Jafaru akeyi inda suka samu yaya da ƙanwa a maƙota suka nuna sunaso aka kuma amince musu.
Duk da kiwon da Jafaru da Bello sukeyi, Yadado ta matsa lallai saidai Mamu shi zai biya sadakin su duka biyun.
Dole Manu ya nemo sadaki ya biya, gashi Yadado kullum a cikin goranta ma Biba takeyi wai aci ayi kashi ankasa aihuwa.
Duk wani aikin gidan hatta da wankin Yadado Biba ita keyi.
Yadado tasa dole Manu ya gina ma Bello da Jafaru ɗakuna ciki da falo da za asa amare, duk kuɗin hanunshi haka ya bayar akayi aikin ginin, sisin biyar ɗin su basu kashe ba a wannan biki, duk wani hidima Manu shi yayi hatta da abincin da za aci abikin Manu shi yasaya.
Bayan auren akayi rashin sa,a laure da Inna wuro suka haɗe ma Biba kai basa kulata sai habaici da halbin iska.
Shekarar su ɗaya da aure kowacce ta aihu da ratan kwanaki, kuma dukansu maza.
Yaron Laure yaci sunan Amadu mahaifin Laure, inda yaron Inna wuro yaci sunan Bala.
Bayan shekara ɗaya da aihuwar su suka sake samun ciki, a lokacin Biba itama tana ɗauke da ƙaramin cikin ta bata saniba.
Wata rana Biba tana jan ruwa arijya taji jiri yana neman ɗaukar ta tayi saurin sake gugar tabar wajen.
Yadado yana ganin haka tace "su oo kuma ansmu ne ci ba ƙiba asarar gari, bana anyi abun kai."
Laure tafito tace "Yadado kardai shiki itama take dasho."
"Yo ga alamu sun nuna."
Aiko Inna wuro tana dawo wa daga tallar nono Laure tasanar mata Biba tana da ciki
Inna wuro tace hande ao mun haifo magada mace zata haifa meye abin damuwa.
Cikin wuya da tsangwama Biba tayi rainon cikin ta, ko abin marmari takeso sai dai Manu ya kawo mata a ɓoye.
A haka har cikin yashiga watan aihuwa, Laure tunda takula da yanayin Biba tace, "yau zakiji yadda mukaji alƙur an gashi ba Yadado."
Inna wuro tace "hmmm! Allah yasa kimutu awajen aihuwa."
Duk tana jinsu bata kulasu ba dama bata kulasu idan sunayi mata irin wannan maganar.
Ciwo yaci ƙarfin ta gashi sunƙi kulata ga Yadado bata nan Manu kuma yana garke batasan yadda zatayi ba.
Daurewa tayi tace "Inna wuro dan Allah ki taimakeni cikina zan mutu."
"Gara ki mutu kawai dan natsane ki banza." ta sheƙe da dariyar mugunta.
Sallamar Yadado sukaji ta dawo daga nemo itace, Laure tace "yaufa akwai aiki agidan nan."
"Me yake faruwa?" Inji Yadado.
"Naƙuda takeyi zata aihu shine take tafaman raki."
"Mtsss dama ai raguwa ce kana ganin abu kamar a hure ta faɗi ina za ayi abin arziƙi ni kubani guri yunwa nake ji, ina jikoki na?"
"Suna gidan mu." Inji Laure.
Haka Biba tayi ta wahala babu wanda ya kulata gashi Manu bazai dawo ba sai dare.
Haka dai tai tafama har Allah ya taimake ta tawahala ta aihu, nan ma Yadado ko takula ta bare yanke cibi.
Daure wa tayi ta tsuguna ta ɗan matse cikinta mahaifa yafito ta ɗauki wuƙar da ta rataye amatsayin Gaye ta yanke cibi ta ɗauki jaririn ta namiji ta naɗe shi acikin zani tunda basu sayi komi ba.
Acikin jinin nan ta kwanta bacci ya ɗauke ta ga sanyi dake damunta. Babu wanda ya kulata duk cikin su.

Next page

*UMMY KHALEEL*

*TAKUCE*
[1/13, 4:32 PM] FIRST CLASS: .سم الله الر حمن الر حيم
*______________________________*
*ABDUL AZEEZ*(SADAUKI)

*2020*

by ummy khaleel

*13&14*

Karki karanta idan baki biya ba Naira ɗari ne kacal 💯

_____________________________________


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The notion}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*Wannan page sadaukarwa ne gareki my sis subai at Ina alfahari da comments naki ubangiji Allah yabar kayan*
*______________________________________*

..............Jariri yashe agefe shima cikin jini, yayi ihu haryagaji babu wanda ya kula shi.
Yadado ce tafito daga ɗakin ta tashiga tasameta kwance cikin jini ga mahaifa awajen da jariri.
Sallaman Manu taji ta amsa tare da cewa "yawwa gara da Allah yakawo ka dama yanzu nake tunanin yadda zanyi da wannan kayan ƙazantar."
Manu cike da farin ciki yashiga ɗakin, ganin Habibah ayashe agurin hankalin shi yatashi yanufi inda take yana kiran sunan ta "Habibah kitashi."
Yadado tana kallon shi batace uffan ba ta ajiye yaron awajen tafice tana jan dogon tsaki.
Kallo yabi ta dashi yana mamakin wanne irin tsana Yadado yakeyi mishi ne da har zata kasa kula shi da abin da matar shi tahaifa.
Bayan ta yabi yasameta aɗaki tana taunar goro, ko kallon shi batayi ba yace "Yadado dan Allah badan niba kitaimaki rayuwar Habibah da abin da tahaifa."
Wani kallo tamishi wanda yasa shi saurin sadda kai ƙasa.
"Bari kaji infaɗa maka Manu, nice na haife ka amma bana jin ƙaunar ka acikin raina sabida haka kafice kabani waje ba abinda zan iya yi maka a yanzu, kaje kasan yadda zakayi da matar ka da ɗan ka." Taci gaba da gutsirar goron ta.
Maganar ta yayi matuƙar bashi mamaki, shin meyasa tatsane shi? Tambayar da yayi makanshi kenan yakuma rasa amsar, dan shi yasan yana matuƙar yimata biyayya yadda ya kamata, juyawa yayi yafice a ɗakin ta banka mishi wani uban harara tare da jan dogon tsaki.
Yana komawa ɗakin ya sameta tana ɗan buɗe ido ahankli, ƙara sawa yayi wajenta da sauri ya tsuguna yana faɗin "kibuɗe idon ki dan Allah Habibah karki mutu kibarni, yanzu zanje na kira miki Innajo kinji."
Tana jin abinda yake faɗa girgiza mishi kai kawai tayi, ya ɗauki yaron ya ɗaura shi akan gado yace "bari naje nakira Innajo."
Yana fitowa yasami Laure da Inna wuro suna ta hiran su, ko kulasu baiyiba ya wuce abin shi.
Yana fita kai tsaye yaje inda masu mashina suke, ko ciniki bai Yiba yahau ɗaya yace yakaishi bingire sannan yace ɗaya yabiyo bayansu.
Koda suka isa bingire Innajo tana ganin shi tayi saurin tashi tashige cikin ɗaki, inda sabo ya saba da haka, baiyi ƙasa agwiwa ba ya sanar mata abinda ke faruwa, tace mishi yaje gidan ƙanwar ta yaɗauke ta sutafi tare, hakan kuwa akayi gidan Laminde suka nufa, sunyi sa,ar tana nan bata fita ba, bayan sungaisa yasanar mata da abinda yakawo shi.
Hijabin ta yaɗauka tare da kayan da zatayi amfani dasu.
Koda suka iso kai tsaye Laminde ta shiga ɗakin tasameta a yashe ga jariri akan gado yanata mutsu-mutsu, ɗaukar shi tayi ta kalleshi da kyau tace "oye Baffajo sak." wato yayi kama da baban Habibah.
Kicin ta nufa dan ɗaura ruwan wanka, Allah yasa ya tanaji itace sosai dan ma Laure da Inna wuro suna kwashe wa suna sayarwa.
Tukubya ta ɗauka ta nufi inda rijiya yake tazura guga taja ruwa taɗauka ta kai kicin.
Laure ce tafito daga ɗakin ta tace "Yasin babu wacce zata ɗaukar min tukunya tayi amfani dashi, tunda bana uwale bace."
Ko kallo bata ishe Laminde ba dan haka taci gaba da abin da takeyi.
Yadado tafito tace "hande hayaniyar me nakeji ne haka?"
Laminde tafito tagaishe da Yadado, sama-sama ta amsa gaisuwar.
Laure tace "Yadado kinga kiyi musu kashedi kar ataɓamin kayana dan al ƙur an bazai yuwu ba."
Yadado ta kalli Laminde sheƙeƙe tace, "yo ke yarinya karki taɓa mata kayan aiki mana."
"Ba kayanta na ɗauka ba na Biba ne." Inji Laminde.
"Yo ai shikenan badamuwa kinji ba naki ta ɗauka ba."
Komawa tayi ɗaki Laminde itama tashiga ɗaki tana ƙoƙarin tashin Habibah wacce take ta baccin wahala.
Gyara wajen tayi tsaf ta nemo kanufari ta ɗebo garwashi tasaka kanunfarin acikin ɗakin, tuni ɗakin ya kaure da ƙamshin kanumfari.
Bayan tagama gyara ɗakin tsaf ruwa yayi zafi tajuye takai bayan gida, taje takira Biba tayi mata wanka.
Duk da zafin ruwan da takeji haka ta daure, aka gama mata.
Bayan tagama wanka suka fito, Laure da Inna wuro suka sheƙe da dariya.
Harara Laminde tayi musu suka sake sheƙewa da dariya.
Ƙyalesu sukayi suka barsu a wajen.
Jariri tayi ma wanka babu kayan da za asa mishi haka dai aka ƙara naɗe shi acikin zanin.
Bayan sallan magriba Manu ya dawo da kayan jarirai masu kyau da yasayo awani ƙaramin shagon da ke ƙauyen.
Laminde tana ganin shi ta karɓi kayan hanun shi yace, "kayan jariri ne ayi amfani dashi."
Fita yayi yasami Yadado a ɗakin ta, ba ta idar da Sallah, zama yayi agefe yagaishe ta, ta amsa ko kallon shi batayi ba.
"Dama inason kifaɗi sunan da kikeso asama yaro."
Harara ta banka mishi tace, "duk sunan da kaga dama kasa mishi kawai fita kabani waje."
Tashi yayi yafita yakoma ɗakin shi.
Bayan sallan isha,i Bello da Jafaru suka dawo daga wajen kiwo, Bello ne yafara magana "wai nikam ƙamshin me nake ji ne agidan nan?"
Inna wuro tafito da sauri har tana tun tuɓe tace "aifuwa akayi mana."
Taɓe baki yayi yace "okkaran yinrri e diyam." (Bani tuwo da ruwa)
Tabarma Laure ta shimfiɗa musu a tsakar gida kamar yadda suka saba idan suka dawo daga kiwo, basa wanka bare suyi tunanin yin Sallah haka zasu zauna suci abinci su kwanta, ko tsabtar jikin su bai damesu ba.
Manu ne yafito daga ɗakin yana musu sannu da dawowa amma ko su kula.
Wucewa yayi yaje sayo ma Biba nama.
Ɗauri biyu yasa akayi mishi, dan gujewa shiga hakkin mahaifiya, harma na Yadado yafi na matar shi yawa.
Koda yadawo yakaima Yadado nata, Yadado tace sam saidai yakawo na matar shi tagani wanne yafi yawa.
Baiyi ƙasa a gwiwaba Allah yasa bai fara wucewa ɗakin shiba ya miƙa mata.
Karɓa tayi tarage wai yayi mata yawa, dan haka dole tarage.
Yana kallon ta tarage tabashi takira Laure tazo ta ɗaukar musu nasu.
Koda yashiga ɗakin yabata naman ta karɓa tayi godiya tace, "ina na Yadado?"
"Nakai mata nata kici wannan kiyi haƙuri gobe zansa ayanka miki akuya kinji."
Murmushi tayi tace, "karka damu karka wahalar da kanka."
Kwana uku da aihuwar daga Bello har Jafaru wabu wanda yayi musu Barka, Laminde ta fahimci irin zaman da Biba takeyi da matan ƙannen mijinta.
Ana gobe suna Manu yasanar mata da sunan yaro wato *Abdul azeez* tace to Allah yaraya mana *Abdullahi azeez Sadauki*

Aranar suna aka yanka babban rago wanda hakan ya matuƙar ɓata ma Yadado rai, wai ya za ayi irin wannan katon rago akan anyi aihuwa.
Washe garin suna Laminde da sauran 'yan uwa suna suyan nama, Yadado tazo ta samesu tace idan angama suyar a kawo ɗakin ta ita zata raba.
Laminde tace to.
Aikuwa ana gama suya aka kai ɗakin ta tace sai gobe zata raba nama, tayi haka ne dan kar ƴan uwan Laminde su ci naman.
Washe gari da Yadado ta raba nama karkuso kuga na mai jego ko cikin ƙaramin kwanon miya bai kaiba, na Manu tace idan zaici ya tambaye ta tabashi, dan tasan idan tabashi tare zasu cinye da matar shi.
Haka taba Laure da Inna wuro nama kamar su ne suka aihu, alhalin lokacin da suka aihu ki yankan nama ɗaya basu bata ba, haka kuma Yadado batayi magana ba.
Bayan suna da kwana arba'in, Laminde zata koma Biba tayi kuka sosai dama ita ke ɗebe mata kewa gashi yanzu zata tafi ta barta.
Da zata tafi saida Manu yakaita har inda zata hau mashin yayi mata godiya sosai tare da bata kuɗi, amma taƙi karɓa, da ƙyar ya roƙeta ta karɓa.
A haka rayuwa tayi ta tafiya da daɗi ba daɗi haka Biba ta rinƙa rainon yaronta, gashi yaran Inna wuro sun hana Abdul azeez sakewa, mauɗe da Bala.
Ga ƙannen su da aka haifo abaya, suma basu da kirki.

*Bayan shekara shida*

Laure matar Bello tana da yara uku maza biyu Amadu (Mauɗe), Saleh, sai jaririyar da ake shayarwa Bintu.
Haka itama Inna wuro tana da yara biyu maza Bala da Umamaru sai cikin da ke jikin ta.
Ita kuwa Biba bata sake ɓatan wata ba bare ɓari.
Wata rana Inna wuro tana girki naƙuda ya kamata, aikuwa Biba ita tayi ƙoƙarin ganin ta taimake ta, har ta haifo ɗan ta namiji.
Bayan ta aihu rashin mutunci yaci gaba, wai tarabu da ita karta cinye mata mahaifa.
Aranar suna yaro yaci sunan Khalifa.

*****

Rayuwa na tafiya kwanaki na ƙarewa, Abdul azeez yataso cikin kulawar iyayen shi, duk da ƙarancin shekarun sa ya fahimci cewa mahaifiyar shi bata jin daɗin zama agidan su.
Watara Biba tanason zuwa duba iyayenta, koda ta tambayi Manu yabata izini, da zata tafi Yadado ta hana artafi da Abdul azeez dolen ta tahaƙura ta tafi ita kaɗai.
Acikin 'yan kwanakin nan da Biba tayi a garin su gaba ɗaya Abdul azeez ya canza saboda ' rashin kulawa, to dama basu kula da tsaftar nasu yaran ba balle na wata.
Aranar da Biba zata dawo mahaifiyar ta ta haɗa mata goma na arziƙi harda jari tabata tare da yi mata nasiha. Hakama yayan ta habu ya ƙara mata jari ya ɗauke ta a mashin ɗin shi yakaita har garin su daɓe.
Abdul azeez tun yana ɗan shekara bakwai yafara talla har Allah yayi yashiga makaranta, kasancewar ranar Laraba ake cin kasuwar garin, aranar baya zuwa makaranta talle kawai yake zuwa. Har Allah ya rayashi , ayanzu haka Abdul azeez yana primary 6 kuma a shekarar nan zasu gama.

*Cigaban labari*

Abdul azeez ne kwance acikin garke kan wani ɗan ƙaramin gado sai faman tunanin mahaifiyar shi yakeyi, yatuna irin rayuwar da sukayi abaya, girgiza kai kawai yayi yana jin jina mutuwa mai raba ɗa da mahaifi.
Tashi yayi ya nufi inda wata saniyar su take naƙuda da sauri ya nufi gida yasanar ma Baffan shi suka dawo tare suka samu saniyar ta aihu.
Abdul azeez yayi murmushi yace "Baffa ashe ma aihuwar ba wuya."
Baffa yace "haka kake gani amma idan wata saniyar ta sake aihuwa agaban idonka zaka tausaya mata, bari na kira Alhaji Adam na sanar mishi dabbar shi ta aihu."
Waya ƙirar Nokia ya ciro a aljihu ya danna number alhaji Adam, bugu ɗaya yayi aka ɗauka.
"Hello, wake magana?"
"Usman ne ina baban ka?"
"Yanzu zai fito bari na kai mishi."
Cikin nutsuwa ya sami Daddyn nashi yana karanta news paper, ya miƙa mishi waya.
Ganin Number da aka kira yayi murmushi yakashe ya sake kira.
Manu cikin ladabi ya gaishe da Alhaji Adam, shima cikin mutunci ya amsa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment