Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shahara nida wad'annan larabawa sudais da Assadiq takai takawo ma kullum ina tare dasu a hotel don aikinma dena yi nayi
Daga baya nai tunanin kada wataran su gano cewar dukansu suna mu,amula dani nashiga uku asirina ya tonu kuma Na had'a fad'a saikawai Na xille musu suka dena jina da ganina kwata kwata
To dama natara kudina ina ajiye dasu k'ari kawai nake nema Wanda zanyi guxuri dasu inna dawo
Asatin danake shirye shiryen dawowane muka had'u da wasu kyawawan "yammata a wani shago sunje siyayya su biyu anan muka saba jininmu ya had'u suke fad'a min sunansu d'ayar datafi haske itace *marwa* dayar kuma *safa*
Safa da marwa sun nunan kauna domin sun nuna suna sona da k'awance don 'karshema kacokan nadawo gunsu daxama acikin hotel suke
Sai da nad'an yi sabo dasu Na yan kwanaki Nagano Ashe k'asurgumayen karuwaine masu zaman Kansu kuma karuwanci Mara aji,kaxamin karuwanci domin da kowane Dan iska yin mu,amula suke.
Niko daban saba ba saina ringa mamakinsu ada kafin naxo kasar ana cewa ana wannan harkar k'in yarda nake domin k'asa me tsarki aita girmi haka to Ashe akwai yan iskan amma dai nagarin dole sunfi yawa suma Allah ke ara musu lokacinsu kafin suje gareshi su amsa quiry
Kullum burin su safa da marwa suga ina wannan harka irin tasu bayama kwankwararriyar marwa takancemin" *Ukhty* naga alama bakyason kiji dad'in rayuwa gaki kinada kyau kinada aji gara kawai ki saki jiki kibaiwa maxa dama asha minti abaki kud'i domin kune sune jin dad'in rayuwar duniya
Nakanyi dry ince'indai kudine Wanda nake dashima sun isheni jin dad'i kuwa nabaya danaji ya isa Ni yanzu hankalina ya karkata gida,Nigeria nakeson komawa, safa tacemin"muma yn Nigeria ne amma muna nan ba ranar komawa anan aka haifemu amma babanmu ya rabu da mamanmu ta koma nigeriar yak'i batamu saidai taxo taganmu kawai ga nan da kk ganmu abinda muke shi namu uban yake ahaka kuma yaga uwarmu ya aura
Nakan jinjina abin araina tab lallai wad'annan sunfi karfina
Aiko dai akwai Wanda yace yana sona ta dalilin su shiya ringa ribata ta yadawo dani hanyar da suke dumu dumu
Nasami kud'i kuwa ta hanyar adnan Wanda shiya dawo dani Nigeria sbd Dan can ne ana yakamamin gidan haya ni nikad'ai yana biya yana zuwa muna holewa daga baya kuma nafi k'arfinsa sbd samun Alhazai da yn siyasa harna gujesa domin akarshe duk zuwan da zaiyi gidan baya samuna Na canza layi sbd shi Na nemi gidan haya natashi daga wanna nakama wanda na tararku da yawa aciki
Alokacin Dana tararku Ku biyu kanku ahad'e yake Aunty Ruby da Sis Zuby ganin nima bahaushiya ce musulma kamarsu sai suka sakarmin komai nima nashiga cknsu muka jone muka zama tsintsiya madaurinku d'aya amma fa bama yarsa mubi namiji mukwana dashi wannan umarnin Aunty Ruby ne domin itama batayi tace muxama masu aji shi yafi don kar arenamu
To atakaice dai wannan shine k'arshen tarihin Rayuwata Ni laila.
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*Page 180-185*
Tunda mukai haka da Babana sainaji jikina yai sanyi tunda banga alamar xaibi bayana ba da zancen donko dayace inyasami kawuna da zancen baxan iya tunkarar sa dashiba tunda nasan bazai aminceminba dama dafa Babana ne yaje masa da batun may be ya amince yabarni na k'arasa karatun nawa to dole naja bakina nai gam
Haka abin yaita nuk'urkusata arai har ammaa tagano ina ckn damuwa ta tusani agaba tana tambayata ban b'oye mataba Na gaya mata komai
Ammaa tace"Fiddausi da xaki dauki maganata Dana baki shawarar ki bar zancen karatun nan don baki d'auko wa kanki me bullewa domin kawunki bazai yardaba tunda yafara datse karatun yayarku to nakima dolene a datse kokin fara,kinsan basa nuna bambanci atsakaninnku Dan haka kicire batun wani karatu aranki.
Tunda Ammaa tafadan haka kuma naji raina ya dad'a jagulemin narasa inda xan tsoma raina Dan Inji dad'i nasan innajewa baba mallam da wannan batun shima bayan Kawu xaibi shiyasa kawai nak'i tunkararsa da zancen
Ranar wata laraba nadawo daga islamiyya da yamma lik'is nashigo gidan Knn naji munyi karo da mutum ckn xauren a k'ufule Na d'ago kaina Ashe Fatima ce rasai k'anwar ummie aiko ta makamin harara nikuma Na dankota nakai mata mari tahau xagina Na dad'a zuciya naringa kai mata duka amma bakinta be mutuba ana ckn haka saiga Ummie nan tashigo tana ganin abinda ke faruwa tashigarwa Yr uwarta saijinai ankaimin naushi ta baya aiko nasaki Fati najuyo afusace nakai mata wawura muka kacame da danbe nan suka rufarmin mukaita dambatawa innakaiwa wannan duka da k'afa sai inkaiwa wannan da hannu ana haka sai mukaji shigowar Yaya bashir ya buga mana wata tsawa ba shiri muka bari Ummie sai muxurai take da ido Fatima kuma tahau kuka jikinta narawa Dan tsoronsa take nikuwa nahau harare harare ina kad'a k'afa
Yakalleni yace"ke uwar yn rashin kunya meya hadaku dasu kuke dambe kamar wasu jakuna? Nai masa banxa ina hararar k'asa ya dakan tsawa "ba dake nake ba kkike faman harare harare walh inhar baki ladabtar da wannan kwala kwaln idanun nakiba nixan ladabtar dasu, nakalleshi nace" gasunan kafara tambayar su mana saini Dana tsare maka gaba.
Yace'e kexan fara Tambaya din Dan kece babba amma tunda kin zama babbar banxa Shikenan ke Ummie meya faru?.
Itama Ummien kasa magana tayi Dan batada gaskiya tunda itama batasan ba,asin abinda ya hadamu da fatinba
Dayaga batada niyyar magana saiya tisamu agaba yace muje gurin malam a can zai hukun tamu.....
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*Page 175-180*
Kowacce cknsu tasaki nannauyar ajiyar zcy Ruby tajanye tagumin datai tace"Gaskiya laila labarinki ma akwai ban tausai domin banda ankawo muku tsaiko a soyayyarki da Nasir tabbas da tuni yanzu kina gdn Aure da kun more kedashi arayuwar Auranku to amma dake haka Allah ya kaddaro muku ba yanda zakui Dan haka ba tare da b'ata lokaci ba feedy mundawo gareki domin jin naki labarin rayuwar bissimillah.
Feedy tai ajiyar zcy ta d'anyi murmushi sannan ta muskuta ta fara da fad'in .....
***********************
Dafarko dai kamar yadda kuka sani sunana Na gaskiya fiddausi, sunan feedy da ake gayamin kuma nasameshi agurin masoyina kabiru Sisco
Kabir Sisco yasoni sona hakika nima nai masa soyayya ta tsakani da Allah amma iyayena basa kaunata dashi sbd d'abiunsa ba masu kyau bane nikuma Yr babban gidace kakana babban malamine Wanda kowa ckn unguwar keganin mutuncinsa da girmansa haka kuma kakana shike limanci a masallacin ckn unguwar tamu ta "yan dodo.
Malam balarabe da muke kira da baba malam shine kakan nawa daya haifi ubana,haihuwarsa biyu kacal aduniya dasukai tareda matarsa inna larai
Kawu Adamu shine d'ansa Na fari sai kaninsa wato mahaifina baba Ummaru
Gidanmu babban gidane ginin zamani ne Na bulo da bulo bana k'asaba,saidai b'angaren baba mallam daban haka Na Babana daban Na kawu Adamu daban.
Kamar yadda Babana keda rufin asiri haka kawu Adamu kedashi ba laifi saidai samunsu ya bambanta da Babana shi kawu principal ne a makarantar maxa shikuma Babana be xirfafa a bokoba saiya tsinduma a harkar kasuwanci nan da nan Kuwa Allah yasaka masa nasibi yake samu
Mahaifina duk abinda zaiyi saiyai shawara da d'an uwansa kawu Adamu duk wasu filayensa dayake siya saida amincewar kawu hakama takardun agun kawu yake barinsu ajiya yanada kau dakai a abin hannunsa hakama baida fad'a sanyine dashi mgn ma bata dameshiba duk abinda zasuyi iyayansu suna saka musu Albarka baba mallam yanajin dad'in abinda suke yi Na had'in kai
Mahaifiyata macece me hkr inace mata *Ammaa* sunanta Na gaskiya halima nikadai ta Haifa aduniya amma ta yiyyi wabi, b'ari yayi sau 5 matar kawu Adamu tana nuna mata faccalanci sosae sbd ganin yanda Babana ke mata facaka bata nemi komai ta rasaba gunsa gashi dama iyayanta sunada Arxik'i Yr garin jigawace a dutse
Kawu Adamu mutum ne me xafi yanada fad'a kaf yaransa tsoronsa suke har matarsa Asiya da muke kira da mami, nikaina da nataso da fad'a da saurin fushi da xcy nasan shina gado ko ba,a fad'a ba ba a min lefi inkyale a aji kaf ckn sch dinmu bana tsoron seniors d'ina balle yn made dinmu
"Yayan kawu 5 maxa biyu mata uku babban d'ansa Yaya hamxa yanada kirki yanada ilimin addini hr gemu ya tsayar mutane suna cewa da alama shine zai gaji kakansa mallam Dan Abokansa ma da d'an uztaz suke kiransa
Yaya bashir kebi masa ba halinsu d'aya ba domin shi Yaya bashir akwai tsare gida baya kulamu kannansa balle yajamu da wasa kamar yadda Yaya hamxa ke mana
Gashi da shan k'amshi duk karatu suke a buk shi Yaya hamxa yana matakin k'arshe digri shikuma Yaya bashir matakin farko yake a digirin Aunty Atika ita kebin Yaya bashir tana gidan mijinta a karkasara ta Dade da Aure tana yin candy aka Aurarta Dan kawu yace bazai bar " ya mace ta gand'ame agabansaba da angama krt zai ringa Aurarwa gara in anje gdn miji inxai bari ayi acan karatun namiji zai fad'ad'a
Ummie itace Sa,ata wacce kanmu d'aya da ita sch d'aya muke amma ba aji dayaba tana B, ina A, kanwarmu bata jik'uwa da ita sbd ita Yr jinkaice ga k'arya da d'agawa kuma bata k'aunar ta ganmu da kB shiyasa nima natsaneta da xarar munhad'u a hanya mun xanta saita fad'a agida anci mutuncina sbd anhanshi zuwa gidanmu
Ko tashi akai daga makaranta kowa hanyarsa daban kota rigani zw koni inrigata tun ana mana fad'a hardai aka zuba mana ido a gdn
Fatima itace Autarsu nagirme mata sosai fati tanada tsokana ga giggiwa da reni.
Alokacin Dana kammala karatun secondary dina sai kawu yace nida Ummie mufito da miji Aure zai mana
To nikuma Wanda nakeso din yace shi bazai Aure bashida aikinyiba kb yacemin yafi son naci gaba da karatu kafin nan shima yasami aikin yi yasandai akan hakane yn gidanmu basa sonsa atare dani
Dayake science class nayi sainake da burin Na karanci medicine ba fargaba na samu Babana da zancen amma saiyace inje ingayawa kawu abinda duk yace shi xa,ai...
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*continue page 180-185*
Saida mukaje gaban baba mallam sannan Yaya bashir yace"Fatima koro min jawabin abinda ya hadaku kuke fad'a "
Fati ckn in inarta tace"walh Yaya laifin Fiddausi ne... Ckn k'unar rai da zafin zcy nagalla mata harara nace"laifin uwarki'
Aiko Yaya ya kawon wani mugun duka a bakina,narige gun ina fadin'wayyo Allah walh saina fad'awa Babana wannan ai cin zaline cknsu babu Wanda ka daka saini sbd ka tsaneni,
"Maxa kije ki fad'awa baban kada k'uda ya rigaki banxa Mara kunya saina xubar mk d hakora wataran inhar baki canza haliba.
Na buga tsaki natashi da gudu nai cikin gida sashenmu ina gunguni harya mik'e danya biyoni amma baba mallam ya tsaidashi" Dakata basiru kaima bakada hakurin kuma baka iya sarrafa yara ba,aibata haka zaka Ni da itaba...."amma mallam Fiddausi batada kunya ko kad'an
Mallam yai murmushi yace"hhhhmmm duk wannan halin nata kawunta ta gado saidai ita dayake macece shiyasa akafi ganin tsiwarta sai a hankali zata dena bari ta kara wayo dole xata rage yanzu akwai yarinta a ckn lamuranta kayi hkr..
Yaya yai kwafa yace"haba mallam yrnyr da take kula samari shine xa,ace da ita da yarinya ackn lamarinta bata da wayo ai walh daka barni yau saina koya mata hankali.
Inna larai da batai mgn ba sai yanzu tace"hkr xakai da wad'annan k'annan naka basiru yaran xamani ne sai ahankali inkace zaka ringa biye musu to zasu rainaka ne abanxa,
Yanda yabar gun a zuciye haka su Ummie suka bar gun sum sum
Da suka sami mahaifiyar su da mgnr fad'a tai tayi meyasa Yaya bashir beje har dakinmu ya tattakani ba shikam dayake a k'ule yake baece uffanba.
Anyi haka da kwana 2 baba mallam ya Tara iyayanmu maxan da yayyena maxa yace yanason ya bayyana musu wani k'udiri dake ransa Na son ya had'a Auren bashir da Fiddausi
Aikodai iyayanmu sunyi murna sunyi Na,am da xancen Wanda shi gogan abin bai masa dad'iba domin baetaba jin son fiddausin aransaba gashi jininsu dama bae haduba Dan dai ba yanda xaiyine be isa kuma yai musu turjiyaba sunaiwa iyayansu biyayya sosae
Da zancen yaxo kunnan Ammaa duk saitaji ba dad'i donta san baxan amince inada Wanda nakeso, tasameni da xancen da daddare ina falonta ina kallon ta koromin bayanin yanda baba mallam yatsara Na had'in Auranmu da yya bashir aibansan lokacin Dana mik'e tsayeba ina fad'in"nashiga uku ni Fiddausi arasa dawa ma za,aimin Auran dolen saida babban makiyina Wanda baya k'aunata ko kad'an to walh ba,a isaba.hannu Ammaa tasa ta toshen baki da sauri"haba Fiddausi meyasa zaki fad'i haka a kullum ina gaya miki ki ringa koyawa zuciyarki hakuri akoda yaushe domin kici ribar zaman duniya kinsan dai tunda baba mallam ya tsara kuma iyayenki sunyi Na,am babu me wargaxa wannan had'in sai Allah kuma tunda shi yana namiji ya amince baeja dasuba toke baki isaba Dan haka kiyi hkr Fiddausi kisa dangana aranki xan miki addu,a wataran insha Allahu wataran zakiso shi shima zai soki,
Na rushe da kuka Dan tuno da masoyina kB Sisco tabbas sunyi hakannema Dan suga sun rabamu gabaki d'aya Ammaa ta janyoni jikinta tanata lallashina.
Itako Mamie mahaifiyar Yaya bashir taji dad'in wannan had'in don tasan gaba takaisu tunda Na kasance Ni d'aya kwal gun iyayena zansha gara kuma danta ya huta da wasu abubuwan duk da itanma ba wani qaunata takeba haka tasa Yaya bashir agaba da dabara tana rarrashinsa akan yai hkr ya amshi kyautar da aka masa Na Aurena"kaga inkai haka tamkar kayi jahadine sbd ita tafison wancen d'an iskan yaro da akace ko sallah ba duka biyar d'in yake arananba wasuma suna cewa kiristan ne,gashi kuma zaka gyarata ta daina rashin kunya kada ka damu ko daga baya saika Auro duk yarinyar da kakeso ka Aura baxamu hanaka ba
Washe Garin da akai haka natashi takanas naje nasami kB nake fad'a masa komai akan yanda xa,a rabamu "yakamata kayi wani abun kB walh ina sonka kuma baxan iya Aurar wanin kaba,.
KB ya k'uran ido yana kallona yace" yanzu feedy kina nufin Aure iyayanki ke shirin yi miki? Na gyada kai "kwarai kuwa kuma walh tunda kakana ya tsara hakan ba makawa za,ayin kuma da makiyina Yaya bashir suke shirin yimin Auran,
Kb yai murmushi yace" tun farko naso inbar garin nan da naga alamar hakan tunda aka hanani zw gidanku,to Amma yanzu dole kafin faruwar ganin hakan a idanuwana dole nabar garin nan.
Nace"ina xaka tafi kabarni kB? "Zanshiga duniya feedy kinsan Ni maraya ne dama ba wani gata gareniba shiyasa nake ganin bak'in ck iri iri arayuwa,
Nace" kb duk inda zaka xanbika ina tare dakai kB Abadan daiman har k'arshen rayuwata..yai murmushi yace "Allah zaki iya bina kibar iyayenki?
Nace " kwari kuwa sona hakika nake maka'
Yace"nasani feedy, nasan kina min sona gaskiya ba algus Alla yabarmu tare,"nace,Amin"
Mukai sallama dashi yarakoni har kusan layinmu anan asirina ya tonu Yaya bashir ya ganmu ya kallemu kawai ya d'auke idonsa nikuma Na maka masa harara Dan harga Allah tsanarsa ce ta k'aru araina....
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*page 185-190*
Ina shiga zauren gidanmu nai karo da mutum atsaye ya had'a rai yana kallona ido ckn ido Na d'auke kai zanwuce ta gabansa yasha gabana yana fad'in "Mara kunya kinsan ke nake jira ai dawa naganku a hanya?
Nace" Ni kuma ? Ni bani ka ganiba...kafin nai shiru saijinai yaja kunnena yai ckn gida dani ina ihu ina fad'in nika sakeni walh inkajimin ciwo baxan yardaba
B'angaren baba mallam yanufa dani zaune muka tararsa akan tabarma yana ganinmu ahaka yace"basiru kaida mutuniyar takane, mekuma tayi yau haka xa,a cire mata kunne,
Yaya bashir yasakeni yana fad'in "gatanan mallam walh batajin magana can naganota da wannan d'an iskan yaron can me saka sark'a awuya da yawo da matsatstsen d'an wando iya guiwa Wanda bashida tarbiyya,
Aifa saiya k'ara k'ularni da wannan mugayen kalaman dayake kiran masoyina dasu Na harareshi ina murgud'a masa baki ya kawo hannu zai mareni baba
mallam ya dakatarshi"Barta basiru banda duka ai ba,a dukan mata inhar kasaba dukanta ko anyi Auranku ba dainawa zakaiba a kullum ina fad'a maka gara kayi fad'a ko nasiha shiyafi kuma kadaina aibanta shi haka gara ai masa addu,ar Allah yashiryeshi wai a ina yaron yakene? Ke Fiddausi ba anhanaki kula shiba ko bakisan da maganar Dana tsara atsakanin Ku da basiru ba?
Ckn b'acin rai nace" mallam inma mgnr Auran wannan mugunne walh banayi,Ni ba sonsa nakeba gara abarni in Auri Wanda nakeso shikuma in bashida wacce ke sonsa sai a nemo masa a hadasu...
A kufule da jin kalamaina Yaya bashir yace" da angaya mk Ni d'in sonki nake?walh banda darajar su mallam ke baki isa injera dakebama balle in xaman Aure,matan dake sona kuma sunfiki aji da kyau tunda inba rashin ajiba meye alfanun bin d'an iska kina sonsa shikuma yana yawon zuwa party da bin club club da "yam matan bariki
Baba mallam yace" ya isa haka basiru bekamata kana biye mataba kaifa namijine kadaina b'ata namiji d'an uwanka xato zunubi,inma yana yi to abishi da addu,a
Ke kuma Fiddausi inhar baki rabu da yaronba to zamu kai k'ararsa gun iyayansa suja masa kunne kuma bari kawunki yaxo tunda kunfi shayinsa akan kowa, naga alamar kin fitsare kafarki akansa Ni abinda yasa nahad'a ki da basiru sbd akarfafa zumunci a tsakaninku ina tausayinki sbd bakida dn uwa ko Yr uwa a gaban iyayanki Amma ke bakya tausayin kanki Dan haka zan miki Addu,a akan Allah ya shirya mana ke.
Na buga k'afa ina gunguni nabar gurin baba mallam ya bini da kallo shikuma yaya bashir hararata kawai yake
Anyi haka da kwana 2 kwatsan saiga waya daga jigawa mahaifin Ammaa ya rasu dama babarta ta dad'e da rasuwa aiko anyiwa Ammaa kara agidan motoci uku akai aka tafi ta,aziyya jigawa gidansu
Aranar suka juyo suka baroni da Ammaa acan sai ranar uku suka dawo mana gaisuwar sadakar uku, daganan kuma Babana baedawoba sai ranar sadakar bakwai dayaxo yace mubishi mukoma Ammaa taso yabarta ta k'ara kwana amma bababbaba yace Sam tunda anyi addu,a kowa ai watsewa zaiyi tai hkr nan da kwanaki zai dawo da ita haka muka taho dama Ni aranar inatajin rashin lfy banda kuxari ajikina
To Ashe rabuwa da iyayene yasa domin aranar mukai wani mummunan hatsari ahanya atake Babana ya rasu Ammaa kuwa saida ta kwana a asibiti sannan tace ga garin kunan nikuwa kwana biyu a asibitin bana ckn hayyacina banji ciwo ko kwarxaneba sai buguwa danai a k'irjina da kaina
Nasha kuka kamar raina zai futa rashin iyaye akwai ciwo bayama inna tuno da ranar rabuwarmu munata hira ackn motar Ashe hirar k'arshe mukai dasu Shikenan gatana ya k'are aduniya.
Na dawo abin tausayi ranar sadakar bakwai din Amma tunda Babana ya rigata rasuwa Amma tare aka had'a addu,ar an cika damk'am anata koke koke yn jigawa sunxo sukam abin biyu ya hade musu aranar ina kwance akan cinyar kakata inna larai idanuwana sun xurma dukna rame ba doleba naxama marainiya ta k'arfi da yaji toko wace irin sabuwar rayuwa kuma xan shiga ta rashin iyaye acknta?
*nabilancy Luv*
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*page 190-195*
Aranar sadakar arba,in d'in iyayena kuma muka shiga wani tashin ckn dare ciwon ciki ya turnik'e baba mallam Wanda yaxamo ajalinsa Dan ko awa ba aiba yace ga garin kunan
Fadar irin halin da aka shiga agdn nan b'ata bakine don ba Wanda ya rintsa gida cika yai mak'il wasu nata koke koke shi dama Kawu Adamu fad'uwa yayi aka kwasheshi sai asibiti ba,a sallamo shiba saida akai ukun baba mallam dama tunda Babana ya rasu Kawu ya rasa kuxarinsa kullum baida lfy alhinin bae sakeshiba ga kuma wannan datafi gigitashi
Inna larai takaba ta kamata dama Ni ina dakinta tun rasuwarsu Ammaa bankoma sashen mamieba kamar yadda ta buk'ata niko baxan iyaba Dan nasan babu me k'aunata a cknsu kuma baxan dauki raini ba banda hkr komai sukaimin xan rama babu bata lokaci
Duk wani nauyi nawa Dana inna ya dawo kan Kawu Adamu shike kula da komai namu, dama duk dukiyar Babana tana hannunsa wasu yana juyawa, haka kullum in zai fita xaishigo sashen inna ya gaidata ya dire mata kud'i ya fice daga gun mamie kullum ana aiko mata shayi a flask dinmu da kayan had'i haka da rana in an girka abinci hr dare ana aiko mana.wannan ixinine daga Kawu
Tun bayan rasuwar baba mallam sai limancin masallaci ya dawo kan Yaya hamxa dama yakan d'anyi tun baba mallam Na nan
An sassaka ranar Aure a ckn gidanmu anasaka ranar Aurena da Yaya bashir wai wata biyar sai Ummie itada d'an abokin Kawu sai Yaya hamxa shida wata k'anwar abokinsa duk xa,a had'a ayi tare nanda wata biyar nidai duk jinsu nake don bawani Yy bashir da xan Aura tunda basonsa nk ba kuma baxan tsaya inaji ina gani aimin Auran dole ba
Har a lokacin inada k'udirin bin kB mutuwar da aka yiyyimin ce ta kawo mana tsaiko wani saka rana da akaimin baya gabana Dan kullum innaso zanje inga masoyina agun da muka sake Na had'uwa
Ko kallo Yaya bashir be isheniba babu wata mgnr Arxik'i a tsakaninmu inxai wuce in wuce babu me tankawa dan,uwansa cknmu nicema in yn tsokanar suna kaina nakanyi tsaki Dan yaji ya k'ulu dani to wani zubin shareni yake ya nuna tamkar baejiba Amma wani zubin in yn rashin hkrn Na kusa kufula yake dani ya kawon duka nikuma Na xille aguje.
Akwai ranar da muka keb'e nida kB yake cemin"anya feedy kuwa baki canza kudirinki Na bina ba kuwa? Lokaci nata tfy,kadafa nan gaba Inji ance andaura auranki ina ZAMAN jira, hhhmmm aiko walh inkika yarda kika Auri bashir kika xauna saina kasheshi...
Nai saurin kallon kb ina mamakin furucinsa,ya gyad'a kansa tareda kallona ido ckn ido"ban fad'a donjin dad'in bakinaba nafad'a har ckn raina walh akanki babu abinda baxan iya aikatawaba, ina mk sonda bantab'aiwa Uwata shiba sbd ban sanma son uwarba tunda bantaso tare da itaba bata raye, feedy Ni maraya ne mahaifin nawama baxama yakeba kullum baya gari yana buga bugarsa nmn Na abinci
Ni yanzu ke kad'ai nake tsumayi agarin nan da tuni Na d'aware don haka ki fadamin ranar da zamu tafi kawai,
Nace"akwai abinda yasa kaga nai shiru da xancen lamfo nai musu kB so nake sai biki ya k'arato saimutafi yanxufa yanxufa saura wata guda Dan haka ka jirani ckn satinnan inaso in sama mana kud'ad'e agun angon kaga dole saina sake Na nuna musu kamar inaso,Amma kuma wane gari zamu nufa?
Ya Sosa k'eya yana dariya "garin Kaduna zamuje akwai dangin Uwata a can zan nemi kwatance inmunje.kada ki damu nima zan d'an nemi nawa kudin sbd mui guxuri
Mukai sallama dashi nakoma gida ina tunanin wannan katob'ara da nake shirinyi
Saida biki ya rage saura sati 2 nasamu inna larai a d'akinta tana linkin kayanta Na zauna a gefen tabarmar nace" inna dama wani taimakone nakeso kiymin "
Tace"to Na meyefa?
Nace"Dan Allah kisamu Yy bashir ki karb'amin kudin da zanyi hidimar biki dasu kinsan ba wani hirar kirki muke dashiba.
Inna ta harareni "ke kinga banason guntun iskancinku Na yaran zamani inxaki zage ki karb'i kud'i ki xage ai duk laifinki nake gani kefa macece inshi yana shareki keba saikisan yadda zakiyi ya dainaba ya dawo kasanki macecefa ke,ko baki iya kissa ba?indai baxaki karb'a da kankiba to ba abinda xan iya miki akai.
Tana ckn wannan surutun saiga Kawu yashigo da sallamarsa muka amsa masa ya zauna gavan inna ya gaidata,
nagaidashi ya amsa yana fadin" inna meke faruwa keda k'awar taki?
Inna tace"kaganta nan tasani agaba wai adole Ni take so nakarb'a mata kudin da zasuyi partyn biki gun basiru ita baxata iya tambayaba nikuma nace nima baxan tambayar matan ba saidai kkada ayi partyn,inbanda iyayi mace da mijinta ta ringajin kunya ina dalili yana dn uwanki
Kawu yai murmushi yace"Fiddausi kamar nawane zai ishekin? Nace"Kawu dubu hamsin ba wanima taro sosae zanyiba.
Ya xira hannu a aljihu ya xaro bandir d'in dubu dubu ya mikon yace"ga dubu d'ari asatin nan lefenki zaizo hannunki saiki zabi Na dinki kikai keda Ummi.
Naiwa Kawu godiya natashi da murnata Na fice Na nufi gun kB cancakas Na bashi kudin nan Dan ya ajiye agunsa muka tsaida ranar guduwa sati d'aya lokacin biki ya rage sati Knn.
A ckn satin nahau yn shirye shiryena a b'oye Amma saina dawo sakarwa Yaya fuska inmun had'u nakan gaidashi yakan amsamin shima ckn sakin fuskar nasan zaiyi mamaki Amma banda gaisuwa bana yarda wata mgnr tasake had'a mu....
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*Page 195-200*
Aranar da zamu gudu aka bugo I.V d'in bikinmu wannan baisa Na karayaba,kona canxa kudirina saima Karin k'arfin guiwa Dana dad'a samu daga b'angaren zcy ta, aranar banyi bacciba inata fakon naga hankalin inna baya

Please Login or Register in order to submit comment