Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuya gaban k'irjin rigar anmata shatin k'ok'on brexiyya dama gani Dana shanun suka mik'e sukai cako-cako
Gyalen rigar d'an mitsitsine nayanashi akaina nai _simple make up_
Karansy tashigo tatarar ni ina fesa turarena Na *Firstly* tak'are min kallo sama da k'asa ta girgixa kai tace" sai ina haka wannan kwalliya kamar zakije gasar kyau?, nai dry nace" walh jippatu nake son naje zan siyo turare naji ance sunkawo designers gara inje kada ayi bamu mukaso kud'inmu mukwaso,
Tai d'an guntun murmishi tace"haka dai kekam bakya gajiya da siyan turare anya aljanunki basuda nasaba da k'amshinki kuwa? Nace" _may be_inxakije dai kawai taho kiyi rakiya a siya miki ko d'an karami ne kema ladan rkyr
Ta tab'e baki tace"A,a ina naga ta rakiya zanyi bak'o yau"
Nace mata "bak'o kuma daga ina? Tace" _new catch_ ne walh a _network_muka had'u shine yau zai fara kawon ziyara
Nace"lallai Toni saina dawo kawai,nai mata sallama ta fito ta koma d'akinta Na rufo d'akina nai waje....
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*page 140-145*
Naji ddin had'uwa da Aunty Ruby a wannan sabon gidan haya Dana kama domin munyi zaman mutunci da ita ta rik'eni amana sainake mata kallon Auntyna Zeenah data rasu kusan halayyarsu d'aya ta son mutane da faran faran itama abin hannunta berufe mata idoba ko zatai tafiya key d'in d'akinta a hannuna yake wuni koda Na awani ne munhad'e kanmu da ita tamkar Yaya da k'anwa ita taxamar min abokiyar shawarata duk da cknmu bawanda yasan labarin juna a lokacin
Su uku natarar a gidan biyun yarensu d'aya sun had'e Kansu ko fita zasui yawo tare suke tafy saidai in da saurayi za,a fita shine suke rabuwa
Alokacin da Al,amin ya nunan halin nasu Na maxa naikuka kamar raina zai futa sbd Na amince masa yaci amanata ya amanta alk'awuran dayaimin Na zai Aureni bazai tab'a gudunaba sai gashi yayi domin yaxomin da xancen iyayensa sun tursashi saiya Auri Yr uwarsa Dan haka inyi hkr zaiyi biyayya bazai iya bujirewaba kawai insami wani agaba
Aunty Ruby ta tayani jin takaici ita taringa tausata tana nuna min aidama ba,a amincewa maxa har a xcy a bariki
Da Allah yasama banyi sake ciki ya gifta atsakaninmu ba domin planning yaita sawa nakeyi kokuma mui amfani da condom
Aunty Ruby jajirtacciyar mace tanada kaifin basira ita ta dage wajen binciken gaskiyar lamarin Al,amin don cewa tayi bata yadda da abinda yaceba
Ya xa,ayi yana Namiji kuma da girmansa da uwar kudin Sa ayi masa dole aiko mata awannan xamanin andena yi musu Auren dole
Ashe kuwa Al,amin k'arya ya sub'urbud'a mana domin saida ta gano Ashe "yar ubangidansa agun Aikinsu zai Aura kuma suna son juna
Nan taita bani shawarwari akan halin maxa konan gaba kada Na sk aminta domin kuwa itama anshata ta warke sannan xaman duniya iyawane
Da shawarwari Aunty Ruby nai amfani wajen iya taku da duk wani namiji dayaxo min da xummar zai Aureni bana yarda har araina sbd bakowane namiji ke Aurar macen dake barikiba
Nayiyyi samari kala kala amma ba bijari-bijariba manyan masu kud'i " yan siyasa da "yan kasuwa haka naringa samun kud'i ina Tarawa a banki Aunty Ruby tabani shawara damu fara Business tunda muna samun kudi.
Alh Sammani shiya fara siyamin motar hawa " yar karama kafin daga baya nacanxa wacce tafita tsada.
Aunty Ruby ta iya takunta itama,domin barikinta metsafta takeyi itama tai motar kanta kafin had'uwarmu musai wannan gidan
Tokunji Tarihin Rayuwata da abinda yai sanadin shigowata bariki....
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:47] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*page 145-150*
Kowacce cknsu ta zabga uban tagumi suna sauraron Zubaida
Ruby tace"tabbas Zuby labarin ki yafi nawa rikitarwa da tausayawa domin kinga ke a budurwarki aka kwareki aka keta miki "yancinki Na budurci nikuwa saida Na tab'a yin Aure sannan mahaifinki akwai asiri a ckn lamarinki dashi anshiga tsakaninku dolene yanzu musamo mafita baxamu zauna hakaba dole mui wani abin aciki addu,a zamu saka ayi domin Allah ya karya lagon Hjy Rakiya matarsa yakuma bayyana miki Ummanki
Ukhty tace" gaskiya ne Aunty, Ni walh mata masu asiri suna bani mamaki kwata2 suna manta akwai Allah agabansu kuma k'arshen tuka tiki dai tik!
Feedy ta muskuta ranta a b'ace tace"walh sister Zuby da xaku barni da saina shigar da k'arar abinda *b.kamal* yai miki sannan a dank'o Hjy atuhumeta akan b'atan junior da suka sace tun yana tsumma dakuma abinda taiwa ummanki...
Rubayya tai murmushi kana tace"Duk baxata kaimu ga hakaba domin abinda hkr bebakaba to rashinsa ma bazai tab'a bakashiba
Addu,ar dai danace zamu saka manyan malamai ayi akai shi xamui baxamu biye ta takiba sarkin "yan kato b'ara,feedy bakida hkr ga saurin fushi kekam walh zamuso muji naki labarin.
Aisha simoli tace'wai Aunty Ruby waya kamata ya fara a ckn sune nifa nak'ara aci gaba domin dare yanayi duk da namu labarin bazai kai naku tsayiba,
Ruby tace" aikomin dare sai kowa ya ida zamu tashi mubar gun nan ba Wanda nasa labarin zai zama kwantai koda zamu kai ukun dare anan duk saurin baccinki yau saidai kiyi hkr,Dan haka *ukhty* ke zaki fara,dagake sai feedy Auta ce a k'arshe.
Ukhty ta gyara zama tafara dacewa....
***********************
Kamar yadda kuka sani sunana Na Ainahi *laila* sunan ukhty nasame shine a k'asar saudiyya ta dalilin wasu k'awayena
Nataso agaban kakata gwaggo Attu mahaifiyar Babana
Mahaifiyata ta rasu tun daga haihuwata ba dad'ewa asakamakon jinya datasha haka mahaifina ma ya rasu ta dalilin ciwon sugar da k'oda
Gwaggo Attu masifaffiyar gaske ce Wanda intana fad'a bakinta harfidda kumfa yake, hartakai a ckn k'auyen namu Na marke ana shayin tab'ota sbd jarabarta
Mijinta baba Musa bayada aikinyi kullum yana gida ko danya tsufa inkaga baya gida to yana gun "yan tsoffin abokansa a majalisarsu gwaggo Attu itace keyin komai n gidan tun tana takura baba da masifar daya futa ya nemo hardai tazuba ms ido kyaleshi tunda taga ba iyawa zaiyi ba
Da safe tana saida koko da k'asai a ckn gida Nike tayata suyar da bayarwa in anxo siya dayake ba,a sani a makarantaba
Da rana tana min wake da shinkafa natafi talla da yamma kuma ina mata sana,ar awara a k'ofar gida nake soyawa kafin ishha,i nasiyar natashi dayake Allah yana samin nasibi bana kwantai a sana,ata
Nikenan banida lokacin kaina sai dare dayake kuma ina mugun tsoronta bana kawo mata ciniki gib'i kokuma nai mata ragi nasan halinta batamin ta dad'i inna shiga hannunta
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*page 150-155*
Kamar yadda nasaba fitowa sana,ar awarata k'arfe shida nayi nafito nafara ko kaskon farko ban kwasheba sai gashi yaxo a motarsa ya faka a kofar gida ya k'araso guna da fara,arsa
Yaimin sallama Na amsa tareda gaidashi ya amsa yana fad'in"toke bakya d'an ajiye d'an benci ko kujera ta xaman costomer?
Nai murmushi nace"bana ajiyewa saidai in kanaso ka zauna ne sai in d'auko maka kujerar tsugunno ackn gida.
Yace"barta kawai ba zama xanyiba sauri nake zanje gun abokina yana jirana zamuje zance
Ai bansan lokacin Dana ware ido ina kallonsaba araina ina maimaita Kalmar zance? To gunwa kuma?
Yakatsen tunanin da fad'in "duka awarar taki takai ta nawane? Nace" ta d'ari takwas da hamsin ce, ya bud'e walet d'insa ya xaro sabuwar dubu d'aya kar tana shek'i ya mik'omin yana fad'in"gashi kisoyata duka kirabawa almajirai da mabuk'ata sadaka
Nasa hannu nakarb'a nace"to bari akarb'o maka canjinka a ckn gida' yace"a,a nabar maki indai canjine,
Nai murmushi nace"nagode,amma dai katsaya inkwashe wannan kaskon katafar mata.
Ya zaro ido yace"wa xan tafarwa, nace"ita mana,banaji kace zance zakaba,
Yai wata dry sannan yace "lallai yarinyarnan bakida mantuwa da alama kuma zakiyi kishi daga cewa zamu zance,har abin ya tsaye mk to sorry abokina hannafi zanje Na raka nasan baxaki gaxa saninsaba,
Nace" hannafi d'an bokon nan Yayan hansai?
Yace"kwarai shifa yanada k'anwa hansai ashema kinsanshi toki cire aranki ba gun budurwa xanjeba rakiya xanyi, ina da budurwa xanbartane naxo nayi wata ai sai akirani da d'an yaudara tunda nasameki kuma ai nagama budurwa kokuwa?
Nai dry kawai Dan tunda yafara koron bayani naji raina yai fari amma da harga Allah naji kishin araina
Mukai sallama yatafi wannan ranar dai ban dad'e awajenba kamar yadda yace haka Na rabarta naji dad'i nima da ban dad'e awajenba ita kanta gwaggo taji dad'in ganin haka
Haka zuwansa Na biyu guna ya dad'a bani dubu yace insoye duka in rabarta yana gun nasoye naringa rabawa almajirai shima yana tayani kafin yatafi kuwa saida mukasha hirarmu saina samu kaina da sakewa dashi haryake tambayata cewar ina zuwa makaranta
Nafad'a masa gaskiya cwr bana xw ba,a sakaniba beji dad'iba har a fuskarsa nagani
Yacemin"kina son kiyi karatu ? Nace"sosaima inaso walh" yace " to kwantar da hankalinki zansakaki inhar za,a bari a gidanku,
Nahau murna ina masa godiya,sai a ranar yake fad'amin sunanshi *Nasir* nima nafad'a masa nawa sunan
soyayya me k'arfi ce ta k'ullu tsakanina da Nasir Wanda kullum yana k'ofar gidanmu baefasa siye awarar yana rabawa sdk ba domin shi fitowa suyarne bayaso haka har gwaggo ta daina saidai taga dubu ita adad'inta ma tsuntsu daga sama gashashshe kunsan kunsan yn kauye da ganin yawan dubu basai Nasir yaxama d'an gidaba hatta baba yasan dashi
Daga bayama saiya kansile min tallar danake da rana Na shinkafa da wake yace zairinga baiwa gwaggo dubu uku kullum haka ko akai domin har kayan abinci yake siya mata duk wata gashi yasakani a makarantar boko a primary akasani wai nai girma a one kuma sungwadani sunga zanyi basira
Dayake Nasir ya kashe bakin tsanya ai gwaggo bata hana sakani a makarantar ba
Nasir ya sami karb'uwa gun gwaggo sosai, (Nasir malamine a makarantar danake zuwa yana koyarda b'angaren "yan sakandare )
A yanzu nasami Hutu ko ince nasami yncin kaina saboda wahalhalun da nake acikin gidan ya ragu saidai inna tashi sallar asuba bana komawa zanhau sharar tsakar gida zan gyarawa gwaggo waken k'osai inkai mata nik'a sannan ind'ora mata ruwan koko takwas tanayi nagama shiri nakarya sai makaranta tana bani kud'in break naira goma kullum....
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *continue*.... *ZAMAN MARINA*.... *145-150*
Nassir shine saurayin danai munsha soyayya dashi had'uwata dashi ne Rayuwata ta haskaka
Baxan tab'a mantawa da ranar had'uwar mu da Nassir ba Wanda nadawo daga tallana ina hanyar komawa gida yabiyoni abaya amotarsa bak'a yanata min hon alamar intsaya zai magana dani nai funfurus naki saurararsa bekyaleniba harsaida yaita bina abaya hrnaje gida yaga shigata ya juya
Bayan sallar magriba yadawo yasameni a k'ofar Gida nagama suyar awara nasiyar ina harhad'a kaya xan shiga gida akusa dani ya faka motarsa
Da sallamarsa ya iso gareni Na amsa ina kallonsa Dan baganeshi naiba,"yace" Ranki ya dad'e me ake siyarwane Naga kamar har an gama anci kasuwa ank'are bani,?'
Nai murmushi nace"walh awarace nake siyarwa kuma ta k'are don kfn magriba nake fara suya ba,a ishsha take k'arewa yauma dai natashi da wuri wanine ya siyewa Almajirai kusan rabinta.
Yace"yayi kyau gobe insha Allahu nadawo nima insiya d'in amma ina Neman alfarmar abani ko minti 5 ne naxo da d'an batu gunki xamu tattauna
Nace"ba komi ai fad'i komiye ina sauraranka.
Ya gyara tsayuwa yace"nagode, nasan baki gane niba to nine Na d'axu da rana da naita binki abaya nai nai ki tsaya kk k'i tunda naganki alokacin Allah ya jarabceni da sonki,nikuma banida kwauron baki naga dana cutu gara naxo nakawo k'ok'on barata ko Allah xaisa nasami karb'uwa gunki
Nai murmushi wata kunyarsa ta rufeni naji kamar k'asa tsage nashige don ba tab'a yin saurayi nayi bansan kuma amsar da ake bayarwa ba idan saurayi yace yana son budurwa
Na rufe fuskata da hannayena biyu ya dad'e atsaye yana jiran amsata yaga nakasa bashi sai nuk'u nuk'u nake dayaga dai banida niyyar in had'a ido dashima a wannan lokacin saikawai yaimin sallama yatafi kan cewa zai dawo gobe da wuri.
Aiko dai awannan rana bacci ya dad'e bed'aukeni sbd tunanin wannan saurayi dayace yana sona nima harga Allah nakamu domin da gari ya waye Allah Allah naringayi dare yayi koya dawo Na sake ganinsa....
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*page 155-160*
Asalin Nasir d'an cikin unguwar Fagge ne dake ckn garin kano mahaifinsa Alhaji Nuhu meshadda d'an kasuwane dake harkar saida shaddoji da lasa lasai atamfofi,a kasuwar kwari shagunansa sunyi goma mahaifiyar Nasir hajiya Rabi bakatsiniya ce suna kiranta da Mamie Nasir ne d'anta Na fari sai k'annansa mata biyu Na gidan miji sai Autarsu dake karatun NCE a Sa,adatu Rimi
Nasir d'an bokone don digirinsa Na biyu yakammala bautar k'asa aka turashi a mkrntr k'auyen mu shine daya gama suka rik'eshi a sch d'in saidai yakoma Fagge duk juma,a yai weekend d'insa a can yadawo Monday
Dafarko k'in amincewa yyi saida Allahbya had'ashi dani sannan ya amince da k'udirin inhar naxama mallakinsa zai d'aukeni mukoma ckn birni
Nasir mutumne shi me rik'o da ibada Dan har tabon salla ne a goshinsa,wankan tarwad'a neshi yanada doguwar fuska gashin bakinsa ya mugun yi masa kyau shi ma,abocin saka glass ne mahaifinsa yanaji dashi domin shine magajinsa ko bayan ransa tunda bayada namiji saishi kadai don hakane ma yake sakar masa kud'i duk wata yake tura masa kud'ad'e a Account d'insa tun farko fara krtunsa har kawo lokacin daya gama be dainaba.
Ajinmu d'aya da hansai k'anwar hannafi abokin Nasir Kawata ce haka hannafi tunda yasan muna soyayya da Nasir Shikenan muke mutunci ko Nasir bayanan ya tafi gida a weekend yakanxo guna musha hira
Nasir yatsaya tsayin daka Dan ganin nasami ilimin zamani Dana addini, donshiya sakani a islamiyya ma
Shekara uku muna zuba zazzak'ar soyayya nidashi alokacin nagama primary d'ina dama dg aji uku akasaka ni
Na d'ada zama budurwa sai baba yasami Nasir yace masa yaturo magabatansa don ayi mgnr Aure inhar da gaske yk
Asatin daxai tafi gida ranar wata Alhamis muna k'ofar gida muna hira yace dani" *lainas* kitayani da addu,a akan tunkarar iyayena da xanyi nabatun Auranki domin akwai yarinyar da take sona "yayar Mamie nace dake katsina amma yarinyar a gidanmu take da zama tana diplomarta a FCE
harga Allah Umaima tana sona amma nikam tun kafin nagamu dake babu soyayyarta araina abinda yasa ma tun farko ban gaya mikiba don karki tashi hankalinki ne akanta don Nagano kinada kishi banaso kuma kiyi zargin inna tafi gida soyayya nk da ita, idan ina tare dake walh mantawa nake da ita kuma tun farko da akaimin zancenta banyi amannaba
Amma yanzu nasan zata iya yiwuwa su taso da xancen ta nikuma inhar sundage Na Aureta to saidai su yarjemin Na had'a dake kixo ata farko sai ita taxo ata biyu kinga ai nayi adalci ko?
Kaina yana k'asa amma zuciyata kamar ta fashe Dan Allah yasani inada tsannin kishi
Amma Dan ink'arfafa masa guiwa saina kanne nai murmushin yak'e nace"Ba komai *lainas* abinda Allah ya tsara akanmu dole mui hkr dashi mubi Allah dai ya shige mana gaba Allah kuma yasa Umaima ta hkr da *lainas* d'ina (sunan da muke fad'awa junanmu kenan shiya tsara hakan farkon sunansa da nawa)
Bak'aramin dad'in lafuxana yajiba yayi murmushi yace" Amin'
Saida ya shak'amin kud'i dubu goma wai inyi amfani dasu kfn ya dawo don zai kwana 2 tunda anbada hutun makaranta gashi nikuma munyi command entrance zamui shirin shiga secondary inta fito....
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*page 165-170*
Inaji suna kirana amma nai banxa dasu kuka nake sosai xcy ta Na tafarfasa nashiga gida gwaggo tana tsakar gida tana k'arasa Tatar Dana bari Na wuceta nai d'akina aituni ta dire a tsorace taxo tana Tambaya ta meya faru nake kuka?.
Saida nai kukana nagode Allah bata dakatar niba harna gama sannan daga bisani nake gaya mata duk abinda Nasir yazomin da shi
Itama ta kokonta abin acikin ranta bataji dad'iba ranta ya b'aci gashi taga samu taga rashi
Anan taita rarrashi Na tana bani baki da baba yaxo ta gaya masa komai,shima abin ya tsaye masa arai amma saiyace mana ba komai kada mu damu wannan jarabattace Allah ya d'oro mana mui hkr domin musamu cinye jarabawar Allah ya musanya min da mafi Alkairinsa yasa haka shiyafi min Alkairi arayuwa
Bamu dad'e da Rabuwar mu da Nasir ba baba ya kwanta ciwon kafa jinya sosae Ashe sugar ne harda cwn k'oda baba yaji jiki gashi danginsa basa kusa dashi haka haka gwaggo tai tayi masa hidimar jinya harya Amsa kiran mahaliccin Sa sarki Allah
Baba ya tafi ya barmu da kewarsa mutum ne Wanda ba ruwansa da tashin hankali ma,abocin rahane da farkwanci gashi yanada rik'o da addini
Bayan sadakar arba,in d'insa naceda gwaggo inaso inje gun dangin innata a yankatsari tunda ba makarantar nakeba gara inje can kawai
Aiko inna ta hana ta fututtuke idonta tace suda basa nemana kuma mesika tab'a tsinana min tun girmana sai yanzu zanje garesu su rik'eni kenan gudunta zanyi
Danaga aranar tanata masifa tun rana har dare akan zancen saina bata hkr nace nafasa zan zauna atare da ita
Anyi haka ba dad'ewa tazomin da zancen wai tasa gdn nan akasuwa xata had'a da filinta Rabin filoti ta biya mana kud'in zuwa makka mutafi can munemi kud'i don anan d'in bame taimakon ta a yn uwa ita kuma ba "yayaba.
Nace" haba gwaggo yaushe kudin gidan nan Dana filinki zai mana wani kudin kujerar maka harmu biyu alhali naji ance kudine tsububu yayi miliyoyi mu biyun
Tace"waya fad'a miki ta jirgin sama zamu tashi? To ta jirgin ruwane inmunje Sudan ta boyayyen hanya. Na xabura nace"gwaggo bantab'a jiba walh kinga kadafa muje a cinye miki kudin ki abanxa kizo kiyi b'atan b'akatantan
"Insha Allahu ma baxa ai hakaba da yardar Allah zamu samu hayewa lfy.
Hakan data tsara kuwa akayi munsami zuwa Sudan inda naga mata dayawa kowacce nason ta tsallake saudiyya, agent d'in gwaggo yace mata sainan da sati biyu zamu samu tfy,aina tsorata ganinmu a dokar daji ckn bukkoki gashi har ana kira mana sati biyu naxaci xaice kwana biyu
Aikodai saida mukai wata Allah yataimakemu mukai Sa,ar tfy muka baro wadanda sukai kusan wata biyu agun agent dinsu yanai musu hanya hanya
Munyi kwanaki ahanya kana muka sami isa k'asa me tsarki agigace guxurinmu bame yawa bane Dan haka ba bata lokaci gwaggo ta nemi gidan aiki tafara kfn nima nasamu sainake binta nake tayata wanke wanke ne agidan larabawan sai gyarae gyaren gida,sai renon yaransu
Hardai nima matar data samawa gwaggo tasamomin aikin agidan wata balarabiya datake futa aiki mijinta yana gida ba lfy mutuwar barin jiki Ni nake masa kusan komai kanta dawo wanka kawai take masa kafin ta futa nikuma nice kula da cin abincinsa sakawa da canza pampers d'insa ta manya inyai kashi ingoge masa da tissue Dan baxan iya masa tsarkiba๐Ÿ™„๐Ÿ˜‰
Dan ma basuda yara har kayansa Nike wankewa amma tana biyana albashi me tsoka har Allah ya karb'i ransa asakamakon jinyar da yakeyi ta tashi don k'arshe asibiti ta maidashi a can ya rasu.
Saikuma nadawo zaman gida tunda dama agidan haya muke kafin wani aikin yasamu ammafa duk abinda zamui a d'arare muke Dan kar akamomu amaidamu k'asarmu tunda bamuda igama....
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
_wannan page d'in nasadaukar dashine ga duk wata Zainab da Fatima dake fad'in duniyar nan_ *jinjina gareku "yayana* *ZAINAB*( _Sayyada_) *FATIMA*( _Shahida_) *Allah ya rayamin ku* _Amin_
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*page 160-165*
Inata xuba ido Inji dawowar Najir amma bulum buk'ui wai shaho yaci shirwa
Shine har aka koma hutun makaranta da sati uku banji duriyar Saba har jarabawarmu ta common ta fito naci makarantar kwana,amma saisu gwaggo da baba sukace ba inda xani kota jeka ka dawoce baxaniba harsai sunga dawowar Nasir sunji inda zance ya kwana
Bikin Kawata hansai da yayanta hannafi yanata gabatowa kullum naje nasami hannafi nagaya masa halin danake ciki Na rashin dawowar Nasir kwana kusa, toshikansa hannafin Ashe kullum ckn buga wayarsa yake sbd shine babban abokinsa tun a B u k
Hakama dasuke koyarwa tare baida kamarsa a ckn mkrntr da ckn unguwar hannafi yacemin" walh laila da ace nasan gidansu Nasir tabbas danabi baya sbd baxanji dad'i ayi bikina bashiba
Amma kiyi hkr ki dena damuwa insha Allahu zai dawo da yardar Allah lfy ce ta b'oye shi
Wata biyu da tfyrsa duk Na rame sbd damuwa ko bikin hansai da akai ckn rashin kuxari Na aiwatar da komai
Ranar asabar aka k'are biki don tun laraba aka fara gabatarwa washe garin d'aurin Auran su hansai da yamma ina ckn gida inaiwa gwaggo Tatar k'ullin gasarar koko saijinai yaro yai sallama yace ana sallama da laila awaje inji Nasir
Aibansan lokacin Dana dakataba nace yace ganinan Na gyara jikina Na fice gwaggo tana band'aki
Har tuntub'e nai axaure Dan sauri daga nesa nak'ura masa ido yayi mugun kyau yasha boyel ske blue da yasha tsadadden Aiki a agaban rigar ya kafa hula zanna light blue da sassarfa Na isa garesu shida hannafi ne suka amsamin Na tsaya ina k'are masa kallon tsaf!
Ya rame sosai yai duhu daganinsa ackn damuwa yake idonsa ya canza kala ya rine zuwa ja
Ashe nikuma nawa idon hawaye yake shatatarwa bansaniba munacan muna kallon kallo
Saida hannafi yacemin"laila bekamata kiringa zubda hawayeba tunda gashi agabanki ya dawo duk da wannan dawowar tana d'auke da wasu damuwowi wanda ke kad'aice zaki fitar dashi ack
Sannan kuma inaso kixama me tawakkali da bashi kwarin guiwa domin kusamu gaci anan gaba don komai Na dny sai kayi hkr zaka sameshi..."hannafi me kakeso ka gayamin?kanaso kafahimtar dani cewar iyayan Nasir basu yadda da Aurenaba Knn?
Hannafi ya girgixa kansa fuskarsa da kalar tausayi yace'ki kwantar da hankalinki zakiji komai a gunsa
Idon Nasir a k'asa yakasa ci gaba da kallona yace'ki gafarceni laila nasan kin shiga wani hali Na rashin dawowata da wuri gareko walh ba ason rainaba,iyayena ne suka sakani agaba suka tirsasani akan dole saina Auri Yr Uwata Umaima
Koda naje musu da xancenki kwata2 basu saurareni da zancen ba suka k'i yarda futuk ssuka rufe idonsu akan baxan Auro musu Yr kauyeba kuma sukace ga gida bata koshiba nadawa bazai samuba
Damuwar Dana shiga Allah ne sheda domin dasuka saka ranar Aure wata d'aya da Auren yaxo ina kwance gadon asibiti akai Auren
Walh koda Na fito Amarya ta tare bana kulata cikakkiyar kulawa
Laila nid'in da kika ganni me biyayyane agun iyaye,bana yarda naga nasab'a musu balle Na tirje akan mgnrsu jini Na saida ya hau
Amma mahaifina duk son da yake min ya to she kunnansa kuma ya haneni da sake dawowa wannan k'auyen duk Dan karmu had'u tunda sunsan ina sonki
Mahaifina shago ya bud'e min nawa nakaina a sbn gari market yasamin jarin kaina yahana aikinma don haka ma Ni yanzu nayanke shawarar komawa karatu zanyi masters d'ina amma ba a kasar nan ba
Laila ki....Na d'aga masa hannu idona Na xubar hawaye nace"kana nifin kacemin ayanxu umaima matarkace?kai kuma Mijin tane?
Yace" hakane laila amma...kafin yasake cewa komai nayi baya nai ckn gida aguje ina kuka...
*nabilancy Luv*๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
[4/7, 13:48] Nabilancy Luv: *ZAMAN MARINA*๏‘ฉโ€๏‘ฉโ€๏‘งโ€๐Ÿ‘ง
*4rm*~NabilancyLuv~ยฎ
*page 170-175*
Ban rufa wata biyar a xaune ba aikiba nasamu a gidan wasu "yan biyu maxajensu ya da k'ani babban gidane amma kowa da part d'insa Mijin hassanar shine babba Sudais Mijin hussainar kuma Assadiq,
Inajin dad'in aiki atare dasu bawani aikin wahala nakeba domin goge gogen tayel d'in kasan gidan ne da kuma jikin bango sai wanke wanke da share share arana sau d'aya ina gamawa nake tafiya gd kowacce inai mata aiki maxajensu ke biyana matan kullum basa zama agida suna makaranta sukan barni ackn gidan suna riga maxajensu fita kullum
Hakan ne yasa shed'an yafara baiwa babban dama yafara nemana munkai ruwa rana dashi ata dole k'arfi da yaji sudais ya sanni a " ya mace, yana shak'a min kud'i sosai duk randa ya kwanta dani yana bani kud'in dayafi albashina todayake matan suna gida week end basa fita suna Hutu bana zuwa aranar
Muna ckn haka da sudais saiga assadiq da tashi sha,awar akaina ashe ya dad'e da auno kwad'ayinsa akaina shiru kawai yayi
Hhhhmmm banyi ja da tayinsa akainaba domin d'an uwansa ya gama b'atani haka shima ya ringa mu,amula dani tamkar matarsa ackn gidan kowanne idan Na gama yin aikina a part d'insa nake kasancewa
Dashi amma fa babu Wanda yagano cewar ina tare da d'an uwansa
Takai takawo asatin da bana zuwama ina tare da sudais domin yafi assadiq nuna jarabarsa akaina sannan yafi bani kud'i
Duk uban kudin danake baiwa gwaggo bata tab'a tuhumata ba akan tai yawa wayake bani su haka akai akai?
Rashin lfyr gwaggo shiya kawomin tsaiko axuwana gidan wad'annan yn iskan larabawa nina ringa jinyar gwaggo Ashe cutar bata tashi bace donko sati biyu bataiba ta rasu tabarni Ni d'aya kwal a k'asa me tsarki
Matar sudais Nabeela da matar Assadiq Ni,imah matane da suke da kirki baruwansu da fitina irinta matan zamani insunga mijinsu Nada kud'i suita wulakanci ko shan k'amshi kodon suma nasu iyayan akwai abin hannu ba laifi
Bayan inna tai sati uku da rasuwa nakoma gidan aikina sbd xama bekama niba don burina danasa agaba shine inga nasami kudin komawa gida Nigeria
Aiko dai ganin banda mafad'i balle me kwabata ko harara sai abin nawa

Please Login or Register in order to submit comment