Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zafi kawai Nanah kefadowa ranta da Farida ga tausayinsu da yanda zasuyi yanda batanan din nan takeji, tai kuka tai kuka harta godema Allah, takai kusan awa biyu awajen kofan kuka take once in a while tana roko abudeta, chan same kamshin turaren nan dataji dazun ne yadaki hancinta hakan yasa tamike tsaye dasauri tana wani kalan bubbuga kofan tana jijjiga kofan tana kuka. “Dan Allah kace su bude ni dan Allah, kayakuri please please please, Nanahhhhhh, Faridaaaa, Ammiiiii……. Dan Allah kayakuri baran karaba” bude kofan dataji anayi yasa tai shiru tashiga kallon kofan da sauri takoma baya, shigowa Maheer yayi dakin yana sanye dawani 3quater navy blue na Fendi sai off white t-shirt mai gajeren hannu dayamai wani kalan mahaukacin kyau dan kunnen diamond dake makale a kunnenshi yana wani kalan shinning yana sheki hannunshi rikeda wayanshi, kafafunshi sanye dawasu fararen crocs designers, yana zuba wani kalan kamshi kaman wanda yafito daga kogin turare, wavy gashin kanshi na kyalli da sajenshi, lips nashi sunyi pink sosai looking so moist and succulent, wannan karan baisaka bakin glasses ba hada idanu sukayi wani kalan faduwa gabanta yayi dasauri ta sauke kanta kasa ganin yanda yakeda dogayen gashin idanu kaman mace, takai bayan hannunta tana share fuskanta, dauke kai yayi yawuce cikin office din shikuma Dan dayake tsaye ata waje yarufo kofan dasauri tai wajen kofan tashiga bugawa tanajan kofan ganin ba’a budeba yasa takife kanta jikin kofan tafashe da kuka sosai kaman wata marainiya da aka kulle adaki tanaso tafita.


Ahankali yazauna kan kujeranshi yaja system yabude ya kunna kafin gently yadago kanshi yadaura manyan idanunshi akanta yanabin tundaga gashin kanta dayake abude da kallo wanda wani shuku dayay tsufa ne akanta but baihana kaga silky black long hair nata ba, gashin ma sun zazzaro waje dan tanada tsantsin gashi gasu kuma so coily, ganin duka gidan nan babu mai imani ko tausayin Nanah karama ma dake kuka balle ita babba yasa tawani juyo da sauri karaf suka hada idanu yahade rai tamau ya tsuke fuska, wani kalan wankamai wani uban harara tayi tareda kai bayan hannunta tashare fuskanta tass tass tawuce wajen dan kwalinta datagani akasa ta dauka takai hancinta ta fyato majina, wani kalan yatsine fuska Maheer yayi shi karan kanshi baimasan yayi ba irin ewww din nan dirty girl, kaman taji ajikinta dago manyan idanunta tayi ganin yanda yayi da fuska yasa takara wankamai wani mugun harara kaman zata kasheshi da idanu dayasa ya zaro idanushi cikeda mamaki irin wat! Sake ballamai hararan tayi ciki ciki tace “mara imani kawai” cikin kakkausan murya yace “mekika ce”? Juyowa tayi takalleshi da sauri suka hada ido cikin tsantsan dakewa dan yanzu jitake dukma abinda zai faru yafaru tace “cewa nayi Allah yasa kada Babana ma yabaka abinda kakeso duk abinda zakayi kayi” tsayawa yayi chak yana kallonta abin looks really strange to him, dan tunda yake babu wacce tama isa tamai wani kalan kallo balle tamai rashin kunya haka wato she’s stubborn kaman babanta, kwallin taba yadauka yabude yazaro daya yakai bakinshi yadauki lighter zai kunna saikuma yakalleta anatse yace “idan Babanki bai bani kayan kwayoyi na ba saina kasheshi har lahira” zaro manyan idanunta dasuke jikeda ruwan hawaye tayi ta kalleshi kana ganinta kaga tsoro da fargaba dakuma shakkan shi aranta jin yanda yake kiran kisan kai kai tsaye, hakanan saiyaji yaji mugun dadin hakan, lighter yasa ya kunna taban sannan ya ijiye ya zuki taban ya fuzar ahankali yace “bashi kadai zan kasheba duk wani tsatso da jininshi daya bari aduniya sainabi na kashesu daya bayan daya” yakara zukan taban ya fuzar, yabita da kallo yanda yaga yan dogayen brown skin yatsunta ke rawa masu kyau dabasu da dark knuckles, gently yadauki wayanshi yabude yay dialing number Dan yasa a speaker yace “bari nafara da kannenki” dawani kalan sauri ta kalleshi dan bata gane takamaimen mene ze fara da kannenta ba, daukan wayan Dan yayi yace “yes sir” dan shiru yayi yakalleta yanda take zaro manya manyan idanunta tana kallonshi cikin wani kalan murya na asalin mugunta da isa yace “shoot those children Dan, ka kwashe gawawwakin su ka bama Kikito yaci don’t cut the call, execute the task ina kan wayan” dasauri Dan yace “Yes Sir” wani kalan mikewa tsaye Yasmeen tayi kanta har juyawa yake jikinta wani kalan bari bari yafara kaman wacce takeda farfadiya tana dumfaro shi tace “dan girman Allah, dan girman Allah malam kada ka kashe kannina, kill me, nika kasheni dan Allah let them be, ka kasheni, kayakuri dan Allah kaya kuri” tana tafiya tana hade hannayenta biyu tana rokonshi tana karasowa wajen dayake ta zagayo ta bayan table din kusada shi tafashe da kuka sosai tahade hannayenta biyu tana kallonshi yanda yakeshan katon lukutin taban abinshi ko kallonta bayayi daidai nan taji karan bude kofa tawayan saiga kukan Nanah kaman zai tsaga wayan, Dan yace “Sir gani nan na iso” zaro manyan idanunta tayi kirjinta na bugawa sosai tarushe da kuka tai kneeling gefenshi takai hannunta saman hannun kujeran dayake zauna tana kallonshi tana kallon wayan tace “dan Allah kada ka kashe kannina dan girman Allah dan ya Rasullullahi, bawan Allah kayakuri kada ka kashe min Farida da Nanah su kadai ne kannina dan Allah” daidai lokacin taji kukan Nanah da ihun Farida tana cewa “wayyo me kake nunani da bindiga” Yasmeen batasan lokacin data mike daga kneeling din datayi ba hannunta har rawa yake tawani kalan daukan wayanshi garin haka hannunta ya gogi nashi wani kalan shocking Maheer yaji dasauri yakalleta, bama tasan tayiba dasauri takai wayan kunnenta kaman ba a speaker wayan yake ba tana ihu sosai tace “dan Allah kada ka kashemin kan……” tuss tuss taji sau biyu wani kalan ware idanunta tayi kafin idanunta suwani kalan juye sama tai baya luuuuu zata zube kasa dawani kalan sauri Maheer yatarota hakan yasa tafado jikinshi a sandare.

✨SPARKLES OF AFFECTION✨



✍🏻M SHAKUR


EPISODE 1️⃣9️⃣

Anty kene ba warwaro, ba dan kunne ba sarka haba dan Allah, Oya Oya shiga group din nan kije ki kwashi sarkoki da dankunnaye akan kudi dan kankani.
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JGCK4a99vpjGLtepWcYwrn


Wani kalan sanyi yaji ajikinshi a asalin cikin bargon kashin jikinshi da tunda yake koda yay zaman Russian ma da Alaska baiji kalan irin sanyin nan acikin jikinshi ba, in his entire life banda Hajiya Maryam this is the second lady dayataba rikewa ko ta taba shiga jikinshi, tundaga kan guntayen hawayen dake gefen idanunta yake kallo harzuwa kan small yar doguwan fuskanta da brown skin nata kewani shinning kaman butter da aka narka, dan karamin bakinta yakara ja kaman wacce zazzabi ke shirin kamawa, goshinta da gashi yacika sun kwanta ga uban zufan daya ketomata agoshi sai sukai lub lub hakan yay mata wani kalan kyau idanunshi ya daura akan katon pimple guda daya daya fito mata a in between giranta guda biyu dayasa tai wani kalan kyau zuwa gudu ukun dasuka fito mata a kumatu dasuka mata bala’in kyau yasake maida idanunshi kan dan karamin pink lips nata dasukai so moist kaman ta shafa vaseline, wani kalan lumshe idanu yayi da bala’in sauri dan abin is somehow ko Hajiya Maryam baijin yataba tsayawa yamata wannan cikakken kallon dayama yarinyar nan ba kuma baimasan mesa yakemata kallan kallon nan ba, abu yaji yanamai yawo aciki kaman tafiyan butterfly dasauri ya runtse idanu saikuma yabude idanunshi da sauri yakai hannunshi kan goran ruwan shi dake kan table din yabude goran dasauri yakai duka ruwan saman fuskanta yana kallon fuskan yadaga goran yashiga juyemata ruwan, wani kalan nishi Yasmeen tayi dan ruwan akwai sanyi sosai hakan yasa ya tsayar da kwarara mata ruwan yamaida goran ya ijiye kan table yana kallon fuskanta still batare daya saki shoulder nata ba, ahankali take bude idanuwanta dasuka mata dishi dishi bamata gani da kyau idanunta na sauka kan wani kalan kyakkywan mutum dakenan kaman bakin balarabe ga lips dinshi jazur yana kallonta shima, cikin yanayi na asalin wacce bata gama farfadowa sosai ba tabude lips nata, saikuma kawai tafashe dawani kalan soft kuka tana karasa bude idanunta tass tana kallonshi still, yanda take kuka kaman irin karaman yarinyar nan dabata dawani hope daya rage mata aduniya hawaye na bulbulowa ta gefen idanunta, wani abu ne yaji yatabamai zuciya ganin yanda take kukan, dawani kalan sauri yadauke kanshi cikin kakkausan murya dake nan a bit calm ba kara sosai yace “tashi daga jikina” makemai kafada Yasmeen tayi batare datayi ko motsi ba, hakan yasa dasauri yajuyo da kanshi ya kalleta kaman yanda take kallonshi shi baitaba ganin karfin hali haka ba, tana kuka sosai mara kara tana kallonshi hade giran sama da kasa yayi yakoma sak Pablo dinshi yace “tashi daga jikina” makemai kafada tayi tana kallonshi cikin idanu kyur batako kyaftawa, kwayar idanunta yakalla yanda yay gray sosai ga idanun sun jike da hawaye sosai sakejin wani abu yayi namai tafiya aciki dasauri ya dauke kai yay baya da kujeran dayake kai zai tashi hakan yasa Yasmeen tai maza cikin kuka ta yunkuro daura kanta tayi akirjinshi in so much agony cikin wani kalan kuka tace “wlh wlh nima saika kasheni, I can’t live anymore mai amfanin rayuwana kannena sun mutu? Wlh wlh saika kasheni baraka tafiba” tacigaba da bubbugamai kanta akirjinshi, baitaba ganin mutumin dabaya tsoronshi ko shakkan shi ba irin yarinyar nan, cikin kakkausan murya yace “dagani to nadauki bindiga na nakashe ki” cikin kuka ahankali ta yunkura zata tashi da jikinta daya mutu sosai karaf ta tsaya sabida yanda gashinta ya makale a boturin jikin riganshi ba karamin zafi abin yamata ba dasauri cikin kuka tace “washhhh” takai hannunta dasauri zata daura akan kirjinshi cikin dan tsawa yace “don’t touch me ke!” Tsayawa tayi cikeda gajiya da komi na duniya tace “to kacire mini” dan kallon kan nata dake saitin kirjinshi yayi da yanda gashin yay tangling akan boturin shi, tsaki yayi kadan tareda yatsine fuska yakai hannunshi ahankali kaman mai tsoron taba gashin nata yace “look at her dirty hair kazamiya” cikin kuka tace “eh naji amma dai inada imani kuma ban taba kashe kow…..” wani kalan kuka ne yaci karfinta mai bala’in kara this time tunawa da yakashe Nana da Farida yanzu, kasa taba gashin nata yayi ahankali yaduko da kanshi kasa yana kallon yanda take kuka ta runtse idanunta gam tana kuka mai taba rai har harshenta yake hangowa jajajir sabida yanda take kukan, wani abu yaji ya tsayamai arai yanda take kukan nan tausayi ne shi baitabajin tausayin wata ba baima cika jin emotions ba to meke damunshi, jitayi kaman ana kallonta hakan yasa tabude rinannun idanunta cikin kuka karaf suka hada idanu saida gabanta yafadi shima haka dasauri yadauke kai tareda kai hannunshi da sauri yana cire gashinta daga jikin riganshi da sauri yakasara cirewa cikin fushi yace “now get up” tashi tayi dasauri tana kuka, shima yamike tsaye yahade rai tareda jawo drawer yaciro bindinga yadago kanshi yakalleta, kallon bindigan tayi yay pointing bindigan saitinta yace “kince na harbeki ko”? Gyadamai kai tayi cikin kuka tace “eh” ahankali yana kallon kwayan idanunta ya matso dab da ita tareda daura bindigan akan goshinta lumshe idanunta tayi da sauri tana wani kalan nishi hawaye na fitowa ta gefen idanunta ta sadakar kawai, pulling trigger yayi bindigan tai wani kalan kara har cikin scull nata taji karan batasan sanda ta kurma wani kalan uban ihu ba. “Wayyoo Ammi na mutu” jikinta ko’ina narawa, wani kalan murmushi ne ya kufce mai daga baki yana kallon yanda ta zare ya girgiza kai kawai yasauke bindigan kasa ahankali yace “ahaka ake mutuwa ko”? Chak ta tsaya tadan zaro idanu saikuma takalli kanta ita wlh tadauka ta mutu, hannunta takai tashafa saman goshinta inda yadaura bindigan ta lakato tadawo dashi gaban idanunta taga ko akwai jini taga bakomi hakan yasa tadago manyan idanunta ta kallai, wani kalan dan iskan kallo yamata sannan yawuce yafara tafiya zaiyi hanyar kofa kaman wanda akace dole yayi magana yace “your sisters are alive” wani kalan zaro idanunta tayi takalleshi dasauri tabi bayanshi tace “da gaske” kojuyowa baiyiba balle yakalleta but hakanan taji kawai ta yarda dashi they’re alive, ganin yakai kofa yasa dasauri tace “dan Allah ka maidani wajensu” chak ya tsaya hakan yasa itama ta tsaya dasauri batare daya juyowa cikeda gadara yace “this is your punishment” cikin wata kalan sanyin murya kaman marainiya tace “dan Allah kayakuri kayafemini” wani kalan juyowa yayi yazuba mata mayun idanunshi dasauri takoma baya tasauke kanta kasa dasauri, anatse yace “I don’t forgive mistakes” juyawa yayi zai bude kofa yafita hakan yasa dasauri Yasmeen tace “ni kuma I forgive you duka abinda kamini da kannina” haryasa kafa yafita ya tsaya chak juyoda fuskanshi yayi yakalli side nashi batare daya juyo yakalleta ba, ahankali yace “why”? Matsowa kusa dashi tayi kadan tace “sabida you are a good person dabai da kow……” wani kalan juyowa Maheer yayi kaman zaki dayasa maganan ya makale abakinta tazaro idanu adan firgice kafin abalain tsorace tace “kayakuri I guess I misspoke” wani kalan juyawa Maheer yayi yabar dakin azuciye tareda rufo kofa.


✨KK✨


✍🏻M SHAKUR


EPISODE 2️⃣0️⃣


ZAKI IYA SHIGA GROUP DIN DANAKE POSTING ✨KYALKYALIN KAUNA✨TA HANYAR DANNA LINK DIN NAN


https://chat.whatsapp.com/HyR79BijM7XFBaNPrFcBYn



***
Daga Baba dake wajen aiki harsu Ammi dake gida babu wanda ya runtsa ranan, dan saida dare yayi Ammi ta birkice sosai dan all this while bata yarda anyi kidnapping yaranta ba saida dare yayi, dare yayi taga yaranta duka basa tareda ita an daukesu kenan yanda take kuka sosai saida Baffa yafita yakira wani likitan anguwansu yazo yama Ammi alluran bacci sannan suka samu tai bacci.


Shima Baba dake station baiyi bacci ba saida ya sumar da direba daya cikin direbobin har saida su Aliyu suka fito dashi daga dakin amman direbobin nan sunki magana ganin yanda ya sumar da dayansu kuma yake fushi yasa suka gane Pablo yadauki wani abu nashi that means sun kusa fita hakan yasa suka kara dake ransu sukaki bada any information dan dasuyi betraying organization din dake basu mahaukacin kudin nan dabasu taba samun irinshi arayuwan su ba gwara su mutu a police station din dasu bada information akan Pablo.


Wuraren 7:15 na safe Baba na zaune kan dogon kujeranshi ya lumshe idanu hannunshi rikeda wayan da babu abinda yake sai fatan Allah yasa Pablo yakirashi Aliyu zaune gefenshi daya damu sosai wayan hannun nashi yayi kara hakan yasa dasauri yabude wayan hannunshi har rawa yake saiga video, Yasmeen ce tafara kokarin karatu saida Farida dasuke bayanta itada Nanah sun kankameta tafito takarba tafara karanta abinda ke paper da yanda tafashe da kuka akarshe, yaran sunyi zuru zuru kaman sunyi shekara dari hannun criminals, kasan sau goma Baba yakalli video sannan yakalli Aliyu yabashi wayan yace “sake kiramin number” dialing number Aliyu yayi kaman tsafi number yayi ringing dauka akayi dasauri Baba ya karbi wayan yace “Hello Pablo” Dan ne yayi magana yace “Oga is unavailable, yariga yamaka kiran dazai maka trust me har abada Oga bazai kara kiranka ba kuma” ijiyan zuciya Baba yasauke ahankali yace “hope my children are fine” dasauri Dan yace “absolutely” ahankali Baba yace “zan saki kayanku yanzun nan bada jimawa ba amman shipment din zan fara saki sainaga yarana zan saki direbobi ku” dan murmushi kawai Dan yayi kadan yace “deal namu is direba da kayanmu, nonetheless Oga always keep promise nashi, za’a kai shipment namu trailer park a ijiye we will take it from there” Dan na maganan ya katse wayan Baba yawani kalan fuzar da ijiyan zuciya abin namai kaman bashiba baitaba sanin wani abu zai iya faruwa dazaisa yayi compromising any case ba sai yau! Bude idanunshi yayi ahankali yakalli Aliyu yace “get the boys ku dauki motocin ku kai inda sukace” dasauri Aliyu yace “direbobin fa” lumshe idanu Baba yayi yace “sainaga yarana tukunna” ijiyan zuciya Aliyu yasauke yawuce kawai yafita wato Baba akwai taurin kai shi bazai iya magana ba Ogan shine he must obey abinda yace amman har cikin ranshi yaso Baba yasaki komi nashi, samin yaranshi yayi dasuka iyajan mota aka kwashi motocin aka tafi dasu har zuwa tipa garage din akai parking tsayawa sukayi suka shige cikin mutane trying to see wanda zaizo yadauka. Baba na zaune a office wayan yayi kara dasauri yadauka cikin kakkausan murya Dan yace “call your boys kace subar wajen nan kafin Oga ya chanza mind dinshi” dip ya katse wayan dasauri Baba yakira Aliyu yace subar wajen dan dole suka tare keke suka shiga sukabar wajen.
***


Fitowanshi daga wanka kenan yana daure da wani short towel a waist nashi da karami a hannunshi yana tsane kanshi, knocking akayi saida yakarasa kan couch dake dakin ya zauna sannan yace “shigo” shigowa Dan yayi cikeda girmamawa yace “Sir munyi securing shipment din komi lafiya lau saidai bai saki direbobin mu ba” dan gejeren murmushi Maheer yasaki sannan yay crossing kafa daya kan daya tareda ijiye karamin towel din a gefenshi sannan yadago kai yakalli Dan yace “kasa Wike to drop the 2 kids, abar babban anan” gyadamai kai Dan yayi yace “yes sir” yajuya yafita daga dakin.

Farida da Nanah nazaune adaki kaman marayu idanunsu sun kumbura kaman babu komi Wike ya shigo da yaranshi dasuka rufe fuskokinsu yana dariya yace “hip hip hurray, time to go home children” fashewa da kuka Nana tayi Wike yamata wani mugun kallo yace “dabakin ta kaman na kifi ke dauketa kafin na bugamata bindiga tasume, mutafi” dasauri Farida dake sanye da hijabin Yasmeen ta dauketa tana leken kofa ganin bataga Yasmeen ba saikuma tai tunani kila tana mota, wani bakin yadi Wike yasamata a fuska yasama Nana sannan aka kama hannunsu aka fita dasu faduwa kawai gaban Farida yake Nanah sai kuka take tanaji aka sasu a mota bata sake sanin ina sukeba sai tafiya suke hankalinta yaki kwanciya, ita batasan iya dadewan dasukai a mota ba but akalla sunkai awa daya sannan taji motan ya tsaya awani waje aka zare hulunan kansu aka bude kofa Wike yamata wani mugun kallo yace “ku sauka”dasauri Farida ta jujjuya takalli motan ganin bataga Yasmeen ba yasa tace “ina Anty Yasmeen”? Wani mahaukacin kallo da Wike yamata yasa tasauka daga motan da gudu tana daukan Nana a hannu yace “idan kinje gida ask your Daddy” sannan sukaja motan dawani kalan bala’in gudu, bin inda suke Farida tayi da kallo sai yanzu tagane ashe agaban school nasu take, goya Nana tayi abaya tashiga tafiya dasauri sauri gudu gudu dan gani take kaman zasu kara zuwa su daukesu kuma tai gida dan basu da nisa sosai da gida, daga Baffa, Baba, da Baba Karami da Aliyu police duk suna tsaye a kofar gida dan yanzun nan Baba yadawo tareda Aliyu baima iya ya shiga cikin gidan ba, kaman daga sama yaji ance. “Babaaaa” dasauri yajuya, hango Farida yayi goye da Nana tana gudu kaman mahaukaciya dawani kalan sauri dagashi harsu Baffa sukayi kanta yana zuwa Farida batai wata wata ba tafada jikinshi sai kuka Baffa kuma ya karbe Nana daga bayanta, dago Faridan yayi daga jikinshi bakinshi har rawa yake yace “i…….ina….ina Yasmeen?”.

✨KYALKYALIN KAUNA✨


✍🏻M SHAKUR



EPISODE 2️⃣1️⃣


KINASON MAGANA DANI M SHAKUR DIRECTLY click on this link

wa.me/+2347012181461


Sake rushewa Farida tayi da kuka jin tambayan da Baba yamata tace “nima bansani ba Baba” ganin yanda ake kallonsu yan layi dake wucewa yasa Baffa yace “muje gida tukunna” gida suka wuce Ammi na zaune a tsakar gida akan tabarma tabuga tagumi ga tuwo agabanta amman takasa tabawa babu abinda yashiga bakinta tun jiya, jin an bude kofa yasa ahankali ta dago kanta, Nanah dake hannun Baffa wani kalan dirkowa tayi kaman wacce tai shekaru bataga Maman ta ba tawani kwasa da gudu tace “Ammi Ammi Ammi na oyoyo” unbelievably Ammi ke kallon Nana batasan lokacin da itama ta taho dasauri ba tana zuwa wani kalan rungume Nana tayi tana kuka, itama Farida ta taho dasauri Ammi tahadasu ajikinta ya rungume kowa ya tsaya yana kallonsu abin gwanin taba rai, sakinsu Ammi tayi tadago kanta tana leka wuraren gate ganin bataga Yasmeen ba yasa tadawo da kanta takalli Farida tace “ina Yasmeen”? Shiru Farida tayi tana kallon fuskan Ammi takasa magana hakan yasa Ammi tadago kanta ahankali ta zubama Baba wasu kalan idanu sai kawai tasake fashewa da kuka ta kankame su Farida da Nanah ajikinta suma suka fashe da kuka, itama Yaya zuwa tayi tazauna gefensu tahau matsar kwalla tace “mudai muna ganin jifa’i kala kala Innalillahi wa innailaihi raji’un, Ya Allah, Ya Allah kabamu ikon cin jarabawan nan, Ya Allah ka tsare Yasmeen aduk inda take aduniyan nan” juyawa Baba yayi yace “zonan Farida” ahankali tasaki Ammi ta tashi tabi Baba da yashiga daki tambaya yamata tabashi tundaga farkon abinda yafaru har karshe tass, anatse Baba yace “kinga fuskan Ogan nasu da kyau?” Girgiza kai tayi tace “a’a ban gani ba mutane uku naga fuskansu, dawani baki mummuna dakuma yan sandan dasuka zo school namu” shiru Baba yayi kafin anatse yace “zaki iya kwatanta su”? Girgixamai kai tayi hakan yasa ya shafa kanta kawai anatse yace “sun muku wani abu”? Girgixamai kai tayi alamun a’a saikuma ahankali tace “Baba maisa basu saki harda Anty Yasmeen ba” shiru Baba yayi baice komi ba sai chan yace “itama zasu saketa, jeki wanka kici abinci kiyi salla” gydama Baba kai tayi Baba ma yabata tausayi duk kamanninshi ya chanza daga gani baiyi wanka ba, yana zaune anan Baffa yayi sallama yashigo wani kallo yama Baba anatse yace “Ibrahim daman duk nuna soyayyan dakake ma yaranka na karyane eh”? Baffa yamai maganan cikeda tsananin fada dayasa Baba ahankali yace “menayi Yaya”? Cikin fushi Baffa yanunashi da yatsa yace “kada ka kara kirana da Yayanka dan baka nuna mini na isa Yaya agareka ba, kabama Pablo abubuwan su kabasu rabi yanzu gashi sun rike Yasmeen so kake su bata rayuwan yarinyar nan? Did you even know the effect of abinda kayi Ibrahim” hannu Baba yasa yakama kanshi tareda sauke kanshi akasa dan kanshi kaman zai fashe ana neman 48hrs kenan baiyi bacci ba koya kulle idanuwanshi, sai yanzu yagane Aliyu ne yagayama Baffa komi, cikeda damuwa batare daya dago kanshi ba yace “Yaya kayakuri” cikin fada sosai Baffa yace “dukanku a family nan are my responsibility, hakki nane ku gabaki dayanku Ibrahim, nace maka kai abu bakayiba kabasu rabin abu, sun baka kaima rabi, Fatima nachan sun rike, what is your problem bari kaji nafada maka” Baffa yay maganan cikeda tsananin baccin rai yace “inhar aikin nan naka zai zama danger akan rayuwan iyalina ina nufin dukanku tatas yan gidan nan wlh wlh zakabar aikin nan I don’t care cewa kayi shekara da shekaru kana dan sanda zakabar aikin ne dukanmu muhadu mukoma kasuwa, and listen listen very well if anything happens to Fatima!” Baffa yanunashi da hannu cikeda mugun baccin rai yace “wlh wlh sainai fushin daban tabayi dakai ba tunda iyayenmu suka kawomu duniya” Baffa yajuya fuuuu yafita daga dakin, Baba yakai kusan minti ashirin zaune awajen yakama kanshi dake sarawa sannan yaciro wayanshi number su Pablo yay dialing amman bata shiga an kara cireta daga kan network ijiye wayan yayi agefenshi yasake kama kanshi daga bisani yamike yatashi yafita daga dakin ko kallon inda su Ammi suke baiyiba yawuce yafita Aliyu ne yama su Baffa sallama sannan yabi bayan Baba da sauri yana zuwa yashiga mota Baba yaja motan zuwa police station.


Yana shiga parking yayi wajen parking sannan yajuyo yakalli Aliyu dake kokarin bude kofa yafita hakan yasa Aliyu ya tsaya batare dayace komiba, anatse Baba yace “jeka sallame su sutafi” gyadamai kai Aliyu yayi dasauri yace “Alhamdulillah” yabude kofan yafita da sauri yamaida kofan yarufe, wani kalan dukan kujera Baba yayi zuciyanshi namai zafi sosai kafin yayi huci anatse yace “you won this time Pablo but trust me next time I will be the one that’s gonna win”.
*****


Taba kofan tayi da sauri tareda bugawa tace “dan Allah kubude ni ku komarda ni wajen Kannaina” bude kofan taji an shigayi hakan yasa takoma baya dasauri ta tsaya kirjinta na dukan uku uku tana kallon kofan, tura kofan akayi aka shigo, wata faran mata ce kaman ma shuwa ce matan tashigo dakin tana sanye dawani lafiyayyen lace purple mai shegen kyau yaji duwatsu da flowers anyi dinkin riga da skirt, batada wani kiba dan

Please Login or Register in order to submit comment