Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalla ba kanta akasa tana wasa da dogayen yatsunta ahankali kaman yar yarinya tace “ance…….ance kashigo” tunda tafito yake kallonta hartazo wajen, hannayen ta datake wasa dasu ya kalla kafin yasaki dan murmushi softly yace “wayace in shigo”? Dan dagokai kaman barauniya tayi danta kallai karaf suka hada ido dasauri tasauke kanta kasa, murya chan kasa kaman mai shirin fashewa da kuka tace “Maman Intee” tana maganan tajuya da sauri tawuce ciki yabita da kallo wani irin sweet smile yasaki ganin dukya kara firgitata ganinshi datayi yazo nan kuma yakira number ta, ga mamakin Dan saukowa yayi daga motan tareda gyara zaman suit nashi ya da bakin glass na idanunshi yafara tafiya ahankali yawuce cikin shagon tana tsaye chan wajen kanta, kujerun dake wajen tanunamai da yatsa ahankali tace “kazauna” murya chan kasa yace “okay Wifey” dasauri takalleshi shima ita yake kalla tareda zare glasses na idanunshi daidai Maman Intee tafito tace “laaaa shine tabarka bata baka ruwa ba kaga shirmen Yasmeen ko” tajuya takalli Yasmeen dake rakube awajen kanta tace “wuce kije ki dauko ruwa sai kizo ki tambayeshi mai zaici yafito daga aiki keda kikasan harka da dalibai da wuya imaza” juyawa tayi tashige ciki itakuma Maman Intee takaraso wajen kan Maheer akasa kaman bashi ba yace “Ina yini Hajiya” washe baki Maman Intee tayi tace “ina Hajiya ai kirani da Maman Intee na ai yanzu an dawo daya, to ina gaji? Ya aiki? Yakuma fama da dalibai? Tacemini kai lecturer sune, Allah ubangiji ya taimaka” dan murmushi yayi kadan batare dayay magana ba ganin yanada kunya yasa tajuya takalli kofan ta kwala kara tace “ina ruwan zama kikai aciki” tajuyo takalli Maheer tace “Yasmeen fa akwai shirme abinka da yar fari, kuma yarinya ce she’s just 20yrs, FCE ma banjin tacika 2months da farawa ba dan Allah asamata ido dan gaskiya na yaba da natsuwa ka kaine saurayinta na farko wlh wlh aduniya, yaya sunanka”? Ahankali Maheer yace “Maheer” murmushi Maman Intee tayi daidai Yasmeen nakawo ruwan gora mai sanyi a tray ba zobo bakomi Maman Intee tasaki baki saikuma tace “bari naje ciki ni, Yasmeen yafada miki kome zaici idan ma babu saikizo ki dafamai kinji” Gyadamata kai tayi batai magana ba Maman Intee tawuce ciki itakuma Yasmeen ta ijiye ruwan akan table tajuya dasauri zata wuce karaf taji yarike kasan hijabinta amman irin rikewan dabazaka taba gane shine yarike ba dasauri tajuyo kaman zatai kuka ta tsaya tareda dauke kai, lumshe idanu yayi yabude su asanyaye, murya chan kasa yace “baraki tambayeni mezanci ba” batare data kalleshi ba makemai kafada tayi tahaderai tace “ka saken” dan juya mata idanu yayi yace “naki” dasauri takalleshi, wani cute smile yasakin mata dasauri tasauke kanta kirjinta na bugawa murmushi namai mugun mugun kyau, murya chan ciki kaman baiso wani yajisu yace “I want tuwo da miyan kuka da zobo” dan turo baki tayi batare data kalleshi ba tace “toni ka sakeni” ahankali yana kallonta yace “toni ki kalleni” juyowa tayi dasauri suka hada ido jin yanda yay magana kaman ita, faduwa gabanta yayi ganin yanda kwayan idanunshi kewani irin kallonta kaman zai hadiyeta dasauri ta fizge hijabinta da karfi tawuce tai ciki yabita da kallo.
✨Kk✨


EPISODE 4️⃣6️⃣




Bata wani jima da shiga ciki ba Maman Intee taleko tana murmushi tace “tace tuwo kake so ko wlh bamu cikayin tuwo akasa ba amman yanzun nan zata maka dan Yasmeen makes the best tuwo da miyan kuka a shagon nan” adan kunyace ya gyadamata kai ciki Maman Intee takoma ganin Yasmeen kikam atsaye bata fara komiba yasa Maman Intee tashiga salati tareda kama baki tace “yau ina ganin bakin hali, yanzu baraki daura miya awuta ba nina tayaki yin tuwon ba kin tsaya kikam kaman gunki anan, ke bakiji dadi Allah yabaki mutumin arziki haka ba yaro gashi matashi ga kyau ga aikin yi abinshi, ga uwa uba kunya ke kinsan yanda mijin aure ke wuya kuwa, je daura miya kafin na makeki” wucewa tayi tana turo baki tahau daura miyan kukan itakuma Maman Intee ta tayata daura ruwa, Maman Intee tajuyo ganin tahada sawa yasa tace “to hadamai juice na pineapples da banana da kwakwa tunda bamu da zobo yau” batai musu ba tawuce tashiga hadawa tanayi tana gamawa tasa a fridge dan yay sanyi.


Cikin 15min sun hada tuwo da miya Maman Intee tasa tahada komi a tray ga man shanu abin yayi kyau daukowa tayi tafito daga kitchen din, dago kanshi Maheer yayi yana kallonta kaman yazo ya karbe tray a hannunta but baiso yataso tsoro yasa ta kabar hakan yasa bai tasoba har wajen tazo ahankali ta ijiye tray zata juya dasauri yarike hijabinta karaf hakan yasa takasa motsi tajuyo takalleshi murya chan kasa Maheer yace “sit down” duk yanda taso tamai musu kasawa tayi ahankali sabida yanda ya tsareta da idanu tazauna tasauke kanta kasa, tuwon yakalla dake tiriri da zafinshi saikuma yakalleta murya chan kasan makoshi yace “thanks” kin kallonshi tayi still, spoon yadauka yana kallonta yanda maroon hijabin yamata kyau, gashin giranta sun kwanta sosai, yakai spoon din cikin tuwo ya gutsuro ya dangwala amiya shi wlh yamanta tuwon da zafi yakai bakinshi wani kalan konamai lips da harshe tuwon yayi baisan lokacin dayasaki spoon din kasa ba yace “auuuchhhhh!” da sauri Yasmeen takalleshi jin faduwan spoon akasa, hannunshi yakai wajen bakinshi yabude mouth dinshi yana fifita da hannunshi yana hura bakinshi daya kasa hadiye tuwon dake tafarfasamai harshe, he looks super cute and innocent and so sweet yanda yakeyi mantawa tayi dakomi dasauri tasa hannunta tadauki glass cup da cold pineapple juice datamai keciki tabashi batare datai magana ba tsabagen yanda yakejin zafi cup din yakarba hannunshi ya gogi nata dasauri yakai bakinshi yahausha da sauri da sauri wani kalan mugun dariya abin yabata, murmushi tayi tareda daukekai zuwa one side cikin kukkuni chan kasa tace “rago kawai” “me kikace?” Taji muryanshi ahankali yay maganan dasauri takalleshi suka hada ido har lips nashi sun kara pink sabida yanda tuwon ya konasu, dan hararanshi kadan tayi cikeda tsiwa tace “ni badakai nake ba” dan murmushi kadan yayi yasauke cup din kasa yakalleta yace “ni kika cema rago”? Sake dauke kanta tayi cikin kunkuni tace “kunne kaman na maciji” “nine maciji”? Juyowa tayi tadan kalleshi tana zaro idanu takasa magana idanunta yabi da kallo dasukaji kwallin Ammi batare daya dauke idanunshi daga kanta ba yace “you have the most beautiful eyes I’ve ever seen in my entire life Fateema” dasauri Yasmeen tasauke kanta gabanta nafaduwa yatsunta tashiga wasa dashi bata kara dago kanta ba, tass yacinye abincin ya shanye juice din tareda lumshe idanu wlh yakoshi kaman cikinshi zai fashe, wannan tuwon yamafi na rannan daya sayo dadi, she is such a talented cook, duk yawace yawacen dayayi aduniya bai tabacin abinci Mai dadin abincinta ba.
Zaro kudi yayi daga aljihunshi 20k ya ijiye a gefen tray din kafin yamike tsaye ahankali yana kallonta, yace “kicema Anty natafi” dagokai tayi anoke ta kalleshi, glasses na idanunshi yamaida kan idanunshi anatse yace “by 4 kibar nan and go back home banson ki kai 5” dan juyamai idanu tayi azuciyanta tace “sannu ubana” anatse yawuce yafita daga shagon adan sace tabishi da kallo kaman tace yadawo batamasan mesa ba, sai alokacin taga kudin daya ajiye dasauri tadauka duka duka abincin dayaci 7k ne wannan plenty money fa, daidai nan Maman Intee tafito ganin kudi yasa da sauri takarba tace “badai kudin abincin yabiya ba akan mene yana surukina to be” turo baki Yasmeen tayi ta kwashi tray tawuce ciki abinta.
Karasa taya Maman Intee ayyukanta tayi jin ana kiran la’asar haka nan maganan shi yafado mata arai, dudda tana gayama kanta bazatabi umarnin shi ba samin kanta tayi da saka hijabi tama Maman Intee sallama kan zata tafi tatafi, tana fita Keke tagani already pake agaban shagon, Mai keke yace “Hajiya kece Yasmeen ko wani bawan Allah yabiyani na ijiyeki agida yabani ledan nan kuma nabaki” Keken yajuya yadauko wani cute leda mai kyau daga bayan keken yamikama Yasmeen dake tsaye tana kallonshi, ledan ta kalla takasa amsa mai keken yace “amshi mana Hajiya” ahankali tasa hannu ta amsa, Mai keke yace “yauwa to shigo mutafi” kalle kalle tashigayi awajen saikuma ahankali tai bismillah tashiga tariga ta sadakar ita wannan mutumin tasan ko kasheta yay niyyan yi yanzu zai iya gwara tabishi ahankali kawai surabu lpy Baba ya tsokano shi.
Saida taga hanyar da akebi aje anguwansu akabi hankalinta yadan kwanta, ahankali tabude ledan dake hannunta chocholates ne ciki dayawa irin expensive cute chocolates din nan dasauri ta maida ledan tarufe tacigaba da kallon hanya, nunamai har anguwansu tayi har kofar gidansu mai keken yakaita sai alokacin tasauke ijiyan zuciya tasauka mai keken yatada kekenshi yatafi abinshi itakuma tabude jakanta ta wurga ledan chocholate din sannan ta rataya jakanta tai sallama tashiga gidansu daidai Ammi na fitowa da kitchen rikeda kula tace “ba biyar zaki dawo ba incedai lafiya”? Murmushi ta kakalo tace “Ammi lecturer 4-5 wai bazata zo ba” Gyadamata kai Ammi tayi tace “to jeki rage kayan jikinki kizo kici abinci” murmushi tayi tawuce dakinsu su Farida ne kadai aciki jefar da jakanta tayi kasa tana kokarin cire hijabi chocholate din suka watso daga jakan dawani kalan sauri da Farida da Sa’a suka kwasa tareda daukan jakan, Farida tahau bude chocholate zatakai baki tace “waya baki hadaddun chocholates din nan Anty Yasmeen”? Dasauri Yasmeen dabama tasan Chocolate din sun watse ba kokarin cire kaya take takallesu dawani kalan sauri ta yarda rigan nata tazo wajensu ta fizge jakanta da chocholate dake hannun Farida tazuba ajakan back tarike jakan gam tace “wayace ki budemin jaka”? Dasauri Farida tace “laaaa Ya Sa’a dan Allah ba ita ta jefar da jaka ba suka zubo”? Dan dariya Sa’a tayi dan ita harta karanta wata yar karaman takardan ciki tace “wlh saurayi ne yabata ai harna karanta takardan saisa dukta tsure” dasauri Yasmeen takalli Sa’a ahankali tace “wace takarda?” Dariya Sa’a tayi tace “duba jakan ki” dasauri Yasmeen tabude jakan wata yar karaman takarda ne da note jiki da akayi da byro handwriting din so fine.
Take Care
MM❤️

Aka rubuta dawani kalan sauri taboye takardan abayanta daga Sa’a har Farida suka kwace da dariya ganin yanda tayi tana zaro ido, Sa’a tace “dalla chill bazamu fadama Baba ba mudai kibamu chocholate muci” hararan Sa’a tayi tace “baram bayarba” zata juya Sa’a ta fizge jakan tabude ta kwashi chocolate son ranta taraba biyu ta watsama Farida rabi tace “Allah sanya alheri first boyfriend din Yasmeen, her first love, nasan yanzu duk afirgice kike sabida Baba kika natsu kya bamu labarin shi ko Farida” kasa magana Faridan tayi tana danne dariyanta bakinta cikeda chocholate yarda jakan kawai Yasmeen tayi tajuya tafita daga dakin dan zuwa dakin Ammi cus she’s loosing her mind.

EPISODE 4️⃣7️⃣



Kusan atare dagashi har Hamad sukakai gida, Hamad yafara isowa sai shi daga baya, wucewa ciki yayi Dan biyeda shi, afalo yasami Baba da Hamad zaune suna magana, kafin ma yayi magana Baba yace “Maheer” anatse Maheer yace “Na’am Baba” “taho nan” dan juyowa Maheer yayi yakalli Dan da idanu yamai alamu yatafi sama yahuta wucewa wurin Baba yayi waje yasamu yazauna kusada Hamad yasauke kanshi kasa dan yasan maganan shi Hamad yama Baba, shiru dukansu sukayi chan Baba yace “kalleni Maheer” dago kanshi ahankali Maheer yayi yakalli Baba dake da bakin glass kaman Baba yanagani yace “Maheer zan maka tambayoyi biyu kagayamin tsakaninka da Allah dan Hamad yafada mini komi daga farko zuwa karshe, baka tabamini karyaba Maheer tunda kake yaro kawowa yau dan haka ka amsani tsakaninka ga Allah” Baba yadanyi shiru sai chan yace “kanaso ka auri yarinyar nan dan kaci mata mutunci ne ka wulakantata kodan ka kara tozarta mahaifinta sabida yataba kayanka??? Kaa gayamin gaskiya Maheer” shiru Maheer yayi kafin chan yace “a’a Baba” shiru Baba yayi tun yana karami Allah yabashi baiwan gane idan mutum yana karya ajikinshi kodan sabida shi makaho ne Allah yabashi baiwan oho, cikin kwantacciyan murya Baba yace “sai tambaya tabiyu kanason yarinyar ne Maheer”? Hakanan Maheer jiyayi gabanshi yafadi, wannan karan yakusan kai 5min yakasa amsa maganan kafin chan cikin murya mai taushin gaske tsakanin shi ga Allah dakuma zuciya daya yace “nima bansani ba Baba” dan shiru Baba yayi yana kallonshi sunnar da kanshi kasa Maheer yayi kusan 10min suka bata ahaka kafin Baba yasauke ijiyan zuciya yace “tashi katafi zan kira Malam Sani yau zaije yama Baban ta magana yaneman mana izini idan ya yarda cikin satin nan zamuje sai ayi magana kutashi kutafi” cute smile Maheer yasaki yatashi ahankali yawuce sama shikuma Hamad ya tsaya batare daya tashi dagakan wajen ba yana kallon Baba cikeda mamaki dan baiyi tunani Baba will accept maganan nan dawuri haka ba, dan murmushi Baba yasaki dan yasan Hamad na zaune awajen har yanzu, anatse yace “hanyar shiriya Maheer ya dauko Hamad I have to support him dudda nasan kalubale na gabanshi, akasin hakan zai iya jefashi yaje yayi wani babban kuskuren dayafi komi muni, tashi kaje soon u will understand abinda nayi dakuma abinda hukunci na ke nufi” harya tashi Baba yadauki wayanshi yamikamai yace “gashi kiramini Malam Sani, idan kaje sama ka karbi address na gidan su yarinyar saika turama Malam Sani ta wayanka” ijiyan zuciya Hamad yasauke yayi ma Baba dialing number sannan yawuce yatafi sama yana tunanin kiran telanshi dan dinkama Maheer manyan kaya dan bazasu neman aure yana sanye da kananun kaya ba.


As usual wuraren 6 na yamma Baba yadawo gidan saida yafara duba yaran dan yau babu islamiyya sannan yawuce daki, wanka yayi agurguje ya chanza kaya zuwa shadda yasa hula yafito dan tafiya masallaci atare suka fita da Baffa da Baba Karami dan suma sun dawo daga kasuwa.

Ana idar da salla andanyi jawabi suka fito suna gangarowa Baffa namusu magana kan kayan gonna da aka samu a gonan Baban su, wani magidancin mutum suka gani akofar gidansu tsaye jikin wata yar mota corolla tsaf tsaf dashi yaci manyan kaya harda Malum malum suna karasowa cikeda girmamawa yabasu hannu yace “Assalamu Alaykum barkanmu dai” dasauri Baffa dan yafisu raha yace “barkanmu bismillah naga kaman mu kake nema ko”? Atsanake yace “kwarai kuwa nazo naganku ne gaskiya kam ni ina matsayin kaman dan aike ne, wajen Malam Ibrahim nazo”

Yay magana yana kallon Baffa, Baba dashi kadaine babu wata fara’a akan fuskanshi bawai kuma ko wulakanci bane no he’s just a serious person, sanin halin Baba yasa dasauri Baffa yace “incedai bawata matsala bane, ga kanina nan shine Ibrahim Meya faru”? Dan dariyan dattawa mutumin yayi yace “to dafarko dai sunana Malam Sani nine babban aminin Malam Maheer Makaho wanda a gaskiya shiya aikoni nan na nemi izini wajenku” anatse Baba da sai alokacin yah magana yace “izinin mene”? Ahankali yace “Kunsan dayake makaho ne baya iya fita sosai ya aikoni ne nazo na nemi izini awajenku yanaso yazo axauna ya nemawa danshi Maheer izinin neman auren diyarku Fateema” wani kalan gyara tsayuwa Baba yayi dan maganan ta saukanmai kaman aradu, baki yabude zaiyi magana Baffa sanin halinshi yadagamai hannu yace “waye dan nashi a ina yasan Fateema? Sannan ita tasan shi”? Anatse Malam Sani yace “ehh to kusan zan iya cewa Fateema tasanshi amman bawai irin sannin dakuke tunani ba dan banjin wata magana ma yataba hadasu ba danshi Maheer lecturer ne a makarantan su yana koyar da English ma duka department dake makarantan, yasami Baban shi yau kan yanaso afara sanarda iyayenta idan sun bashi izini sai afara neman aurenta gaskiya banjin suntaba magana bama” kusan Baba zai iya cewa ya yarda dan wayanta akai akia yake bincika wa kuma da aka dauketa wayan all through na hannunshi ba’a taba kiranta daidai da 1 miss call ba” anatse Baba yace “ba yanzu zan aurar d……” tareshi Baffa yayi da sauri ta hanyar sakin ma Malam Sani murmushi yace “gobe juma’a zaku iya zuwa bayan juma’a dan bayan salla bama komawa kasuwa agida muke yini” murmushi Malam Sani yayi yace “Masha Allah to too Allah ya zabamana abinda yafi alkhairi, bari na barku ku shiga gida to saida safenku” yasake babbasu hannu suka gaisa, motanshi ya shiga yaja yabar wajen Baffa yakalli Baba da bacin rai dan dama baiwani huce sosai ba dudda Baba yabashi hakuri yace “kana kokarin gayamusu baka shirya aurar da Yasmeen ba kasan alamomin gidan mutunci kuwa”? Baffa yanuna motan mutumin daya wuce yace “gidan mutunci ne da yaron kwarai awannan zamanin zasuzo sufara tambayan izinin iyaye kafin dansu yama yima diyarka magana, kadaisan bazan taba bayarda Yasmeen banyi bincike ba kabar ganin kanka kaine dan sanda kaine ka iya bincike kasan abubuwa nafika sanin rayuwa Ibrahim, kabari gobe suzo muga yaron idan natsuwanshi yayi zamu bashi izini ya nemi Yasmeen inyaso saina hada bikinta dana Sa’a dan iyayen yaron sunzo kasuwa sun samen, kuam iyayen yaron sun damen sunaso asa rana nan da wata daya kanajina” badan yasoba Baba yace “eh” Baffa yakalli Baba karami yace “koba hakaba” anatse yace “hakan yayi Yaya, Yasmeen ta isa aure ai” jinjina kai Baffa yayi jin ana kiran isha’i yace “mutafi muyi isha’i kawai gabadaya” duk suka juya suka wuce mosque, koda suka dawo sama sama Baba yaci abincin yawuce dakinsu Yasmeen dukansu na zaune adakin harda Nana suna hira suna dariya ganin Baba yasa sukai tsit, binsu yayi da kallo one bye one sannan yasaki labulen yawuce yashiga dakinsu, direct kan kujera yayi yazauna Ammi dake zaune ganinshi haka yasa tace “lafiya Baban Nanah kanka ciwo yake ne”? Girgixa mata kai yayi baice komi ba yawuce yatafi uwarka da kawai.

Har wajajen dayan dare Baba yakasa bacci juye juye yake hakan yasa cikeda damuwa Ammi ta kunna wutan dakin takalleshi shima kallonta yayi saikuma yatashi yazauna tareda folding hannu akirji cikeda damuwa Ammi tace “wai menene Baban Nanah am getting worried? Meke troubling naka haka ka kasa bacci sai juye juye kake” shiru yayi yana kallon Ammi kasa dannewa yayi yace “wani mutumi dazu yazo tambayan neman Auren Yasmeen shine Baffa yace suzo gobe” wani kalan murmushi Ammi tayi da abin harsaida yasa Baba sakin baki dasauri tace “waye shi”? Cikeda dan bacin rai Baba yace “nima bansani ba sai gobe idan sunzo amman ance yaron lecturer ne a school nasu” wani kalan murmushi Ammi tayi kaman anmata albishir da kujeran makka hannu ta daga sama tace “Ya Allah ka tabbatar da Alkhairi kabawa Yasmeen miji mai sonta sama da yanda Baban ta ke sona” dan tsaki Baba yayi kawai yakoma ya kwanta tareda juyamata baya dariya Ammi tayi da shewa tace “wlh Baffa Yamin daidai aka biyemaka bazaka taba aurar da yaran nan ba” kashe wutan tayi tadawo rungume Baba tayi tace “zonan wlh saikai farin ciki” daganan salon labarin ya chanza.

✨KK✨


✍🏻M SHAKUR


EPISODE 4️⃣8️⃣



EPISODE 48



To Jama’a anan nakawo karshen FREE EPISODES na wannan littafin nawa Mai suna KYALKYALIN KAUNA wato SPARKLES OF AFFECTION✨


Wannan aure zai yu kuwa??
Yaya Baba zaiyi idan yagano Maheer shine Pablo Escobar??
Kuna ganin kafin aure ko bayan aure ne Baba zai gano gaskiya???
Hajiya zata taba barin Maheer da Yasmeen suyi zaman aure???
Hmmmm!!! Kubiyoni.

Idan kinason cigaba da karanta littafin nan all you have to do is pay ko 1k or 500 into 3107021073 Aisha Muhammad first bank.

Zakimin magana a WhatsApp wa.me/+7012181461 sainai adding naki a paid group.

Group na 1k is 2updates daily banda alhamis da juma’a.

Group na 500 is 1update daily banda alhamis da juma’a.

And inada EXCLUSIVE shi a Email nake musu update yanzu haka sun wuce ku is 5k.
4episode daily❤️


Please patronize my little work, and appreciate my talent, show me support ta hanyar subscribing ki shiga paid group.


Thank you I love you all❤️

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment