Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tanasha hakan yasa yakalli Matar tashi yace “Yasmeen da Farida fa suna islamiyya”? Dan kallonshi tayi itadai tunda yake bata taba ganin uba da baya wasa da lamarin yaranshi irin mijinta ba, anatse tace “Farida dasu Sa’a duka suna islamiyya” dasauri yace “Yasmeen fa”? Ahankali tace “har yanzu bata dawo daga wajen Maman Intee ba, kuma ina kiranta bata dauka, maybe basu gama aiki dawuri bane” take yanayin fuskanshi ya chanza, duk wani walwala da annuri na kan fuskanshi bacewa yayi bat, hannunshi yatura cikin aljihu dasauri yaciro wayanshi kiran Infinix zero number dayay saving da Yasmeen yay dialing saidai harta katse ba’a dagaba, dasauri yamaida wayan aljihu yajuya hakan yasa Ammi tabishi dasauri tace “ina zaka kuma Baban Nanah ko kayan aiki baka cire ba fa”? Batare daya juyo yakalleta ba yace “zanje gidan Maman Intee, nagayamata anything 3:30 tasallami Yasmeen sabida kafin hudu tadawo gida ta shirya tawuce islamiyya” hannu yasa zai bude gate karaf Ammi tarike hannunshi hakan yasa yajuyo yakalli fuskanta, anatse tace “dan Allah calm down, nasan ko’ina Yasmeen take yanzu haka tana hanyan dawowa gida ko kaje zakusha bambam ne, you are being over protective dayawa over this girls Baban Nanah, Yasmeen is a big girl remember?” Tai maganan tana kallon kwayan idanunshi Anatse trying to calm him down tace “Yasmeen is 20 yanzu, she’s not more yarinyar 12yrs old da zaka kasa ka tsare akanta haka please kadawo gida ka chanza kaya nakawo maka tuwo kaci Yasmeen zata dawo yanzun na. Besides yaune rana na farko data makara tunda tafara zuwa koyan su cake din nan awajen Maman Intee da kaine da kanka kasata please kazo kai wanka kahuta” tunda take maganan kallonta yake kaman mai nazarin wani abu kaman kuma baraiyi magana ba sai chan cikeda ihu dakuma fada ya nuna kanshi yace “are you telling me nazo na zauna na natsu y’ata daya kamata tadawo gida since bata dawo ba har zuwa yanzu kusan 5:15 yanzu? Kin zaci yanda baki sonsu baki damu da su ba haka nima nake? Diyarki daya kamata 3:50 ko 3:45 tana gida baki ganta ba baraki saka hijabi kibi hanya ba kin zauna agida ko ajikinki yanzu zanbi sahun ta kuma kinaso ki hanani what is your problem Hajara?” Yay maganan da tsawa cikin fushi da saida Yaya ta leko daga kitchen ta tabe baki takoma ciki abinta ita daman tasan za’ayi haka, cikin fushi yace “kina banzan tar mini da yara kina wulakanta mini su, nashigo gida na tarar da y’ata my sick little girl da duka duka yaushe taji sauki daga kyanda tana kuka she wants yoghurt baraki iya siyamata ba idan ma baki da kudin ne baraki ara ba in yaso nadawo saina biya amman no kin barmin ita tana kuka ita kadai a tsakar gida ke kina kitchen ko ajikinki, tun yanzu da raina da lafiyata kina neman maidamini da yara marayu” baki Ammi tasaki tana kallonshi takasa cewa komi kawai ganin ta inda yake shiga batanan yake fitaba balbaleta kawai yake da masifa, hannunshi ya fizge yace “when it comes to yarana don’t ever, I mean it don’t ever try to tell me wat to do or wat not to do” yawuce azuciya yabude gate yafita, sanin duk inda take yanzu tana hanya kuma bayaso yasha bambam da ita yasa yashiga tafiya da kafa bai dauki motanshi ba zuwa bakin junction na anguwan su yana kallon titi.


Wata yar yarinya ce yar doguwa kadan dan bawani tsayin kirki ne da ita ba at the same time kuma ba gajera bace kana ganinta kasan bazata wuce shekaru 20 aduniya ba, wani kalan coffee skin ne da ita irin wayanda ake cema glass skin dinan, kana ganinta kaga mahaifiyarta Ammi saidai Ammi tafita duhu ita batakai Ammi duhu ba, tana sanye da hijabi dark blue mai hula daya kaimata har kasa anma hijabin hannu data fito da hannun data rike wata yar simple jaka da shi baki, wani flat takalmi ne akafanta baki irin na yan 1500 din nan masu hanci daya kara haska kananun kafanta da babu safa, dudda hijabinta mai hulane kana ganin tulin gashin kanta da some suka kwanta agoshi ta sabida dan zufan datayi na tafiyan datakeyi akasa, tanada wasu kalan manyan idanu da kwayan idanunta are complete gray kaman idanuwan yar tsuntsuwa, ga cikan bakin gashin gira dana idanu sai dan karamin dogon hancinta da lips dinta yan dis so pink dasu kaman na jiririyan da aka haifa yau, tana tsaye akan titin tana juye juyen da kalle kalle da kai trying ta tsallaka titi dan titin is so busy gashi two sided titi ne kasancewan yamma kowa na kokarin komawa gida.


“Yasmeen!” Kaman daga sama taji muryan Babanta na kiranta dasauri takalli saitin inda taji muryan gabanta nadan faduwa tana zaro idanunta fiki fiki kaman wata zabiya looking so calm and scared atare, hannu Baba yadaga mata alamun ta tsaya inda take hakan yasa anatse ta gyadamai kai tana hadiye miyan dataji ya katse abakinta kirjinta na bugawa still ganin Baba, tsallaka titin Baba yayi ahankali yakarasa daidai inda take yana kallonta ahankali dakuma sauri tana dari dari tace “Baba ina wuni” batare daya amsaba yakai hannunshi yakama hannunta kaman wata yar karaman yarinyan 5yrs yashiga dadduba titin sannan ya tsallako da ita yana tafiya da ita suka shiga layinsu ko kunyan jama’an anguwan su baijiba gam yarike hannunta yanda kasan yasaki hannun zaa dauketa ne suka shiga tafiya tana binshi ahankali kanta akasa har zuwa gida. Bude gate yayi tashiga sannan yashigo shima tareda sakin hannunta yamaida kofan yarufe sannan yace.


Yace “ya akayi kikayi latti baki dawo ba” wani kalan ijiyan zuciya tasauke kana ganinta kasan itama duk atsorace take yanda kirjinta ke bugawa har a idanunta kake gani lips nata har rawa rawa suke tace “Baba bansamu keke bane kwata kwata shine nadawo akafa” cikin fushi kaman zai rufeta da duka yace “maisa baki kirani kingayamin baki samu keke ba?” Dan hawayen datake rikewa ne ya sauko mata dukta rude tashiga tura hannunta cikin jakan hannunta taciro wata yar techno phone rakani toilet tanunamai tace “Baba wayana yafada cikin zobon damuka yi ne, shine Maman Intee tace nabude naje nasa a shinkafa, saida zan tafi nadauko nahada na kunna ta kunnu amman anata kirana bana iya dauka har Mama ma takirani ban iya na dauka ba Baba kayakuri dan Allah” takarashe maganan tana sauke kanta kasa hawaye na saukowa daga idanunta yana sauka akasa gabanta faduwa kawai yake sabida tsoro, dan ijiyan zuciya Baba yasauke yana kallonta still yace “bani wayan” dasauri ta mikamai, karba yayi yace “wuce kije kicire kaya kiyi wanka kici abinci” gyadamai kai tayi tajuya ahankali tawuce, dakinsu tashiga Nana tabiyota dan aduniya Nanah nason Yasmeen sama da kowa na gidan, dan Yasmeen nakawo mata kayan dadi dasauri tace “Anty Yasmeen sorry Baba yasa kinyi kuka, nace kidawo ni kidaina kuka idan ana miki fada” wani kalan murmushi Yasmeen tayi takai bayan hannunta tagoge fuskanta da sauri tace “nadaina” sannan tazauna kan katifar su dasauri itama Nanah tazo tazauna kusada ita tace “Anty Yasmeen Baba yasayamini yoghurt kuma narage miki nawa bari nakawo miki” ganin zata tashi yasa Yasmeen dasauri tarike mata hannu tace “tsaya tukunna” tace “yajiki kin warke nakawo miki cake da zobo” dasauri Nana tasauka dagakan gadon tana tsalle sosai Yasmeen tabude jakan data dawo dashi taciro cupcake guda daya tabata da zobo na gora daidai nan Ammi tashigo dakin ganinsu yasa Ammi tace “sai yashigo yaga baki wankan dayace kije kiyi ba kika zauna kika biyewa Nanah” dasauri ta tashi hakan yasa Ammi takalli Nana data shiga bude ledan cake din tace “kidaici ahankali dan kika fara zawo da ubanki zan barki nasan bazaiji kyashin wanke kashin yaranshi ba” dariya Nana tahauyi tana kallon Ammi cikeda yarinta tace “Ammi ai Baba na wankemin kashi idan nayi a po yakuma je bayi ya zubar tuntuni” tsaki Ammi tayi tawuce tafita daga dakin itakuma Yasmeen tadaura zani tasa hula akai tafito waje bucket tadauka na ruwa takai bayi sannan tadawo dakin Yaya tashiga tasameta zaune a tsakar falo tana cin tuwo tace “Yaya ina yini” kallonta Yaya tayi tareda washe baki tace “sannu yar nan jibi duk kinbi kin zuru zuru sabida fitinar ubanki Allah dai ya kyauta, Allah yakawo miki karshen fitinan mahaifin nan naki kisami miji ki aure ki barmai gida sai muga zai dinga bikin gidan mijinki ne yana bibiyan lamarinkj, jeki wankan ki kafin yafito yamiki wani sabon fadan” murmushi tayi tamike tsaye tafice Yaya tabita da kallo yarinya har yarinya amman fitinan ubanta yasa har yau ko mashinshini batadashi saisa ita tayi alkawari duk iskancin Baba yayi amman wlh barata bari yahana Sa’anta sakat ba, idan saurayinta yazo zance turata zatayi Sa’adatu ce kadai diyarka mace dan haka barata bari ya cuci rayuwanta ba shidai nashi yaran Yasmeen da Farida da Nanah karama yacigaba da musu haka sukai kwantai yakada su a nono yasha atoh, tana cikin tunanin taji sallaman yaran gidan an dawo daga islamiyya hakan yasa ta leko, yaran Hajjo ne agaba dan sune kananun yaran gidan dama su hudu manyan biyu maza sai mata yan shekaru 7-7 yanbiyu Hasana da Husaina, sai yaranta biyu maza Aliyu da Bashir dasuke nan sa’onnin Farida 15 yrs, sai Sa’adatu data girme Yasmeen da shekara daya ita she is 21, dukansu anatse suke ganin motan Baba awaje ansan yana gida, gabaki dayansu dakin Ammi sukayi dan zuwa gaida Baba.



Yana zaune a falo bayan yayi wanka dan shi adakinshi akwai bayi yana sanye da farar jallabiya suka shigo atare dukansu sukace “Baba sannu da zuwa ya aiki” binsu yayi da kallo one by one kaman mai nazarin abu kafin yayi murmushi yace “Alhamdulillah” kafin ahankali yace “kuje Ammi taraba muku yoghurt dinku sai ayi shirin salla” atare dukansu suka tattashi karaf idanunshi yasauka kan jelan gashin Sa’a daya fito dan kitson gaba ne akanta babu wasa akan muryanshi yace “Sa’adatu” adan daburce tajuyo tace “Na’am Baba” wani kalan mugun kallo yamata yace “me gashin nan ke nufi daya fito” dasauri takai hannunta tana maida gashin dukta rude tace “wlh Baba bansan yafito bane bazan karaba” mugun kallo yamata yace “next time kisaka hula kafin ki daura hijabi akai, gashi suturce shi ake kinajina” dasauri tace “eh naji Baba” “tafi” yafadi ahankali.

✨ SPARKLES OF AFFECTION ✨


✍🏻 M SHAKUR


AMMNUR APHRODISIAC is home of lafiyayyun kayan mata na ban mamaki, kayan matsi, kayan gyaran nono, kayan gyaran amarye dana maijego da abubuwan mallaka kome kikeso zaki samu awajensu.
Chat them up by clicking on this link;
wa.me/+2349080070762


EPISODE 3️⃣



Fitowa daga wanka tayi tana tafiya ahankali sabida yanda tagaji dan yau ta taku, Farida tagani adakinsu tana kokarin cire Hijabin islamiyya itakuma Sa’a bata dakin tana dakin Maman su (Yaya) Farida dake kallon Yasmeen din dataga gajiya karara akan fuskanta tace “Anty Miemie mekika kawo mana yau daga bakery dinku Chef”? Wata doguwan riga Yasmeen taciro daga drawer dakin tasaka sannan tajaye igiyan wankan daga jikinta ta shanya akan kofan dakinsu ahankali tace “anjima zan baki gashinan a leda yanzu muyi salla kafin Baba yazo” dasauri Farida tace “ni banayi” Gyadamata kai Yasmeen tayi tadauki hijabi tasaka ta kabbarta salla, saida Baba yafito yasa dukansu matan suje suyi salla sannan yawuce yatafi masallaci shida yara mazan gidan.

Babban gida ne wanda iyayensu suka rasu suka banmusu bayan sun haifesu su uku suka, Baffa wanda shine Babba mijin Yaya kuma, kowa na gidan Yaya ake cema matarshi, dan kasuwa ne Baffa yana saida kayan hatsi akasuwa, Yaya ce kadai matarshi ta haifamai yara biyar guda 4 maza wanda uku sunyi aure suna aiki agaruruwa daban daban Abba kawai yaragemai da Sa’adatu da basuyi aure ba, dukansu na university Sa’a na 200 level shikuma Abba na 300level, sai Baba shi dan sanda ne yaranshi uku duka mata, Yasmeen ce Babba, sai Farida dakuma Nanah, sai kanninshi da ake cema Baba Karami mijin Hajjo yaransu kananu hudu maza biyu sai yan biyu Hassana da Husaina.


Bayan sallan magrib gabaki dayansu mazan suka shigo gida duka yaran zuwa sukayi gaidasu banda Yasmeen da tana sallan magrib ta bingile da bacci danta bala’in gaji, anatse Baba yakalli Farida dake zaune kusada Ammi akan tabarma yace “ina Yasmeen”? Dan ita kadaine bata tsakar gidan, ahankali Farida tace “tayi bacci Baba” bai damu da abincin da aka kawomusu da zasu fara ci ba tashi yayi ahankali yakalli Yayanshi yace “ina zuwa Baffa ku faracin abincin” idan da sabo kowa na gidan yasaba da yanda Baba yake da yaran gidan ma gabaki daya bawai nashi kadaiba gyadamai kai kawai Baffa yayi, direct dakin yaran yawuce wanda shine atsakiya dakinsu wanda yakenan ciki da falo da bayin wanka da dakin Baffa shima ciki da falo da bayin wanka sai akama yara matan dakinsu awajen babban daki guda daya, da sallama chan kasa yadaga labule yashiga dakin, kwance yaga Yasmeen din akasa tai shane shane tana bacci ga hijabin datai salla dashi agefe babu hula akanta sai kitson kanta dakenan all back dayay tsufa amman gashin baki sidik sai uban tsawo tana shakan bacci, ahankali ya tsugunna akanta hannunshi yakai yadaura asaman kan goshinta jin jikinta ba zafi yasa ahankali yakai hannunshi yabugi kafadarta yace “Yasmeen Yasmeen” cikin bacci murya chan ciki tace “uhn Baba” dan shiru yayi yana kallonta saikuma ahankali yatashi gadonsu katon gaske dan su uku ke kwana adakin, wani zubin kuma Nana nazuwa tace ita wajen Anty Yasmeen zata kwana ba wajen Ammi ba sai su zama su hudu, hijabinta dake wajen Baba yadauka ya kakkabe gadon sannan yadawo yaduka yadagata ahankali yace “tashi kihau gado” cikin bacci yadagata tamike tsaye kana ganin yanda take kasan ta bala’in gaji dan har layi layi take kaman zata fadi da taimakonshi yasata akan gadon tana lumshe idanu cike da bacci sannan yakashe wutan dakin dayake kunne yawuce yafito tsakar gida daga Yaya har Hajjo kowa yabishi da kallo anamai harara ciki ciki itadai Ammi ko kallonshi batayiba dan sosai yau yabata mata rai, zama yayi wajen yayinshi yasa hannu suka cigaba da cin tuwon duk wanda zai shigo gidan saisun bashi sha’awa sabida yanda family suke three brothers da iyalansu suna zaune agidan da iyayensu suka bar musu da iyalansu zaman lafiya kuma kansu ahade.
Saida suka cinye tuwon sannan yakalli Yayan nashi anatse yace “Yaya gobe za’amini karin girma awajen aiki zan koma Commissioner of Police CP” duka gidan hatta Ammi saida takalleshi cikeda farin ciki yaran sukahau cewa “Baba Allah ya sanya alheri” murmushi yamusu yace “Ameen” su Yaya da Hajjo ma sukace “Allah sanya Alheri Allah tayaka riko” anatse yace “Ameen nagode” murmushi Baffa yayi yace “Alhamdulillah Alhamdulillah shi daman duk wanda yarike Allah haka Allah ke daukaka shi, mutane na yawan cewa ai duk Dan sandan da baya karban cin hanci baya kaiwa ko’ina, ko akasuwa idan ana hiran nan nakan cemusu uhm’uh kada suce haka, inada kani da tunda yashiga aikin yan sanda yau kimanin shekaru kusan sha takwas kenan daidai da cin hancin naira biyar baitaba karba ba kuma ahankali ahankali anata karamai girma gashi yau za’a nadaka CP maiyafi haka? Nan gaba saidai muji an maidaka IG gabaki dayama” Baffa yadanyi shiru tareda daukan ruwa ya kurba sannan anatse yace “a kullum ina fadamaka kowani matsayi kasamu arayuwan nan kayi amfani dashi wajen magance matsalolin al’umma gabaki daya, wajen yaki da rashin gaskiya da kafa gaskiya, wajen taiwakama addinin musulunci, wajen tsare hakkin dan adam da saman da zaman lafiya adoron kasa, ta hanyar kawo karshe sata, kidnapping, shaye shaye, fyade, kisan kai da sauransu, Allah ubangiji yabaka sa’a yakuma tayaka ruko sannan kasani wannan position din amana ce, karkaci amanan sabon seat din nan kaji Ibrahim” anatse Baba yace “naji Baffa nagode sosai” dafashi kanninshi mai binshi yayi Baba Karami wanda shine mijin Hajjo yace “Allah yatayaka riko Yaya” murmushi yayi yace “Ameen” tashi Baffa yayi yace “to kumu tashi mutafi masallaci, kukuma matan sai kuyi naku sallan” dan juyawa Baba yayi yakalli Ammi dake kallonshi cikeda farin ciki dauke kai tayi dasauri ganin sun hada ido dan haushin shi takeji wani kalan murmushi yayi yabi su Baffa suka wuce mosque batare dayace mata komiba.

As usual daman gidan ana sallan isha’i kowa ke shigewa daki dan yara anje school angaji, weekends ne dama yaran gidan basu cika bacci da wuri ba dan ranan baaje boko ba, Ammi na idar da salla tadauki Nanah datai bacci asaman gadonta tafito waje tashigo dakin su Yasmeen tagansu duka sun kwanta dudda ba bacci Sa’a da Farida keyi ba amman Yasmeen tadade da bacci, kwantar da Nana tayi tareda su tana kallon Yasmeen tace “kin gaji ba dole kiyi bacci ba cikin dare kya tashi kiyi ishan kukuma baraku kashe wutan bane” dasauri Sa’a dakejan lullubi tace “Ammi dan Allah kikasha mana” dan hararansu tayi sannan takashe musu tajawo musu kofan tafito tashiga nata dakin, maida kofan falon tayi tarufe sanan tashiga uwar dakinsu, dan matsakaicin bayinsu da wanda kadai ake aciki ta shiga ta watsa ruwa sannan tafito ta shirya cikin kayan bacci ta fesa yan turarukanta ta kwanta.


Wuraren 10 su Baba suka shigo gidan, direct dakin yara yawuce, shikuma Baffa yana kulle gate, ahankali yatura kofansu yashiga wayan hannunshi ya kunna saida ya dudduba su ganin duk sunyi nisa abacci sannan yasake Tofa musu addu’a yafito tareda maida kofan nasu ya kulle sannan yama Baffa sallama duk kowa yashige dakinshi maida kofan dakinsu yayi yarufe sannan yawuce uwardaka, jallabiyan shi yashiga cirewa yana kallon Ammi dako sallaman shi bata amsaba kuma yasan ba bacci take ba, bayi yashiga bakinshi ya wanko tareda dauro alwala wanda wannan haka yake kullum sannan yafito ya kashe wuta taredayin bismillah yahau gadon, ahankali ya matsa kusada Ammi yakai hannunshi yana kokarin juyoda ita cikin wata kalan murya yace “juyo kimin Allah sanya alheri dan ke kadai ce kika rage baki samini albarka ba” kabarda hannunshi tayi cikin fushi da rashin son yin magana dashi tace “stop touching me” dan shiru yayi saikuma chan yace “kiyakuri to” kaman jira take wani kalan juyowa tayi saikuma ta tashi zaune cikeda masifa amman bamai karfi sosai ba gudun kar ajinsu tace “nagaji da hakurin dakeke bani kullum saikagama cimini mutunci agaban uban kowa sabida yara saika biyoni da daddare kana cemin nayakuri yau bazanyi ba kaji Ibrahim bazan yi ba” shiru Baba yayi jin takira sunanshi yau kai tsaye yasan ranta yabaci, cikin wani yanayi na nuna kunci tace “Ibrahim ka manta cewa nine mahaifiyar yaran nan, nine nadaukesu wata tara acikina, nine nai laulayinsu, haka kuma nine nan nikadai nashiga labour room nasha nakudan yaran nan nahaifosu maisa kake treating dina kaman banson yarana kaine kadai ke sonsu why? Inda ba nine na haifesu ba sai ace eh dama banice mahaifiyar su ba but this girls are mine, nine mahaifiyar su, mesa kakemin abinda kakemin akansu eh Baban Nanah”? Shiru Baba yayi baice komiba baki Ammi tabude zatai magana sai kawai kuka ya kufce mata kawai tafashe da kuka sosai dan abinda yake mata na kona matarai ainun, wani kalan sanyi jikin Baba yayi ahankali yajawota zuwa jikinshi batai musu ba tashige bayanta yashiga shafawa cikeda lallashi yace “kiyakuri bazan karaba, I know you love our girls beside yaranmu ne nidake muka haifesu sometimes ina miki fadane sabida sakaci, Maryam yara mata muka haifa guda uku, hakki ne su akanmu nida ke we have to protect them, support them, musa idanu akan lamarin su, mu tarbiyantan dasu da kyau kinsan idan ka tarbiyantan da yara mata da kyau ka aurar dasu Allah zai bamu aljanna ranan gobe kiyama? Hadisai daban daban daga Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata agareshi inda yake nuna falalan da iyaye suke samu ranan gobe kiyama dasuka tarbiyantan da yara mata da kyau, Please understand me kidaina fushi dani, inaso kiyi tsayin daka kaman ni akansu that’s all stop crying matata, I am simply doing the right thing” yay maganan yana bubbuga bayanta, da kyar tai shiru ta dago daga jikinshi sannan takalleshi dudda cikin duhu ne tace “I understand abinda kake kokarin yi kan yaran nan perfectly well but is too much! You are overreacting, Yara mata garemu kana tareda yaran nan 247, kana yawo dasu kana rike musu hannu a anguwa, anguwan nan kap babu wanda baisan how protective you are towards this kids ba, wazai taba zuwa ya aure su kowa tsoron tinkaranka yake, Yasmeen dinmu is 20yrs kasan mates nata guda nawa sukai aure yanzu alayin nan kadai? Ita ko saurayi batadashi sabida kai, kowa yasan babanta dan sanda ne kuma bai bari akula yarshi” Haderai Baba yayi dasauri kaman bashi ba yace “nina gayamiki aurar da ita zanyi yanzu?” Dasauri itama Ammi dan yau kome zai faru yafaru daidai take dashi tace “to karatu kakeson tayi da kana gani dai she is not going anywhere akaratun”? Shiru Baba yayi yajuya kawai zai kwanta dasauri Ammi tarikemai hannun tace “Ibrahim listen to me ba lallai saikabi abinda nake fadi ba amman inaso kai nazari kan maganata, nagaji damaka shiru ne so I have to tell you abinda ke raina yau, Baban Nanah” Ammi tai maganan asanyaye tace “Yasmeeen tun tana yarinya bansan ko dan ita yar fari bace amman dai me and you munsan tun tana yarinya batada kokari, adaddafe a repeating da chanje chanjen makarantu daban daban sabida kai kanka kagaji da repeating da ake mata aka samu tagama sakandare at the age of 18, tai waec na farko duka f9, waec din daka biyamata tana 19yrs Allah ya taimaka taci shima Allah kadai yasan tayaya tai passing dan am sure kai karan kanka har yau u are still in shock ya yanda tai passing exam din, har yau har gobe bakomi Yasmeen ke iya gani takaranta tsaf ba wani zubin Farida nan kanwarta that is just 15yrs SS3 student ke taimakonta dasu Sa’a, dudda babu kalan lesson teachers da lessons dabaka sata ba, Yasmeen is just like that haka Allah yayo brain nata, I am sorry to say this banson nakira yarda na haifa dakikiya amman me and you munsan cewa kusan hakanne, ka kaita school of nursing tafara anayin weeding exam nasu aka koreta batai passing ba shima F tasamu, dudda lokaci yakuri ni nasan dayaya dayaya kasamu da kyar kasamo mata admission na FCE part term shima yanzu tafara an bata Islamic studies amman she’s not going anywhere with it, infact ni aganina ma FCE yafi bata wahala kan school of nursing, subject daya kusan malamai ashirin akai Baban Nanah kuma kowa da nashi abubuwan karatun ina kakeson yarinyar nan tasa kanta?” Ammi tai shiru tana kallon Baba ganin yaki magana yasa ahankali tace “nasan ka hadata dawata lecturer daka biya tana zuwa office nata ana kara maimaita mata komi sannan da kanka kadauketa ka kaita school na Maman Intee nakoyan su abinci, drinks da cakes which shine abu na farko danaga Yasmeen tasoma iyawa sharp sharp tunda na haifo yarinyan nan” Ammi tai shiru sai alokacin Baba yajuyo yakalleta yace “all lissafe lissafen nan what are you trying to say? Nagayamiki nagaji da kashe kudina akanta ne? Koko kintabaji nai korafi kan rashin gane karatun ta dawuri ne? Ai ni ke biya bakeba ko to ki barni da maganan nan please bansonji” girgiza kai Ammi tayi trying to make him understand her tace “Baban Nanah, abinda nake kokarin cewa shine you might thing abinda kakema Yasmeen shine the best thing any father zaima diyarshi but you are wrong yarinyar nan is going through a lot nine mahaifiyarta kwayan idanunta kadai nake gani nasani, karatun nan yamata yawa, sannan yanda ka tsaya tsayin dakan nan akan yaran nan baka basu breathing space karage, let this children be ko masamu wani yayi approaching Yasmeen da maganan aure, Yasmeeen tayi girma, she’s a very fine beautiful girl, give her space wannan kaita FCE dakake duk Saturday da sunday sannan ka koma ka daukota kabari, let her go on her own and mingle da dalibai irinta, allow Yasmeen kullum tadinga zuwa shagon Maman Intee da kanta, stop holding hannun Yasmeen a anguwa kowa nagani yes ansai kai babanta ne but stop treating

Please Login or Register in order to submit comment