Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasa Sailuba kar tasan jibi daurin auren Maryama domin na fahimci ita d'in fitina ce arayuwar Maryama, kai wannan yarinya Allah dai ya ganar da ita"


Daga Baffa ya fita zuwa gurin yan uwan marigayi aminin shi Hassan






MAMAN ISLAM CE
*بسم الله الرحمن الرحيم*

*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*



https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?type=3&source=45&refid=17

______________________________________
🔥 *BA JININA BACE* 🔥
*2021*


NA


*HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI*

*MAMAN ISLAM*

Masha Allah kungiyata kungiyar albarka ce kungiyar da babu irin ta d'aya tamkar da dubu ina matuk'ar alfahari da first class tare da dukkan 'yan uwa masoya na cikin ta Allah ya k'ara had'e kanmu


Allah sarki islamiyya ta Allah ya k'ara shiryamin ke ya sanya miki nutsuwa da jin tsoron sa Allah ya tsarkake min zuciyar ki tareda kullum yayan musulmi baki d'aya



D'an auta na Al'mustapha d'an rikici na yanzun an girma ya kamata a daina rigimar banza da wofi.



PAGE 45


Bai wani jima ba ya dawo haka ma Inna yana dawowa tace ya koma gida yaci gaba da shiryen sa ita tagama nata haka nan gobe zata iso da tawagar ta, sannan ta kawo wani rubutu ta bashi tace yana shiga get d'in gidan sa kafin yakai ciki yayi Bismillah ya sha daga tsaye, ta jaddada masa hakan sau ba adadi har ya daga yana mamakin wannan wane irin rubutu ne me muhimmanci haka.



Sanda ya isa sai da yafara zuwa gidan malam lokacin yana tare da bak'i ganin Baffa yasa ya sallami bakin yace "k'araso mana Baffa kamar wani bak'o zaka tsaya daga nesa".


K'arasa wa yay yana d'an murmushi yace "barka da yamma malam"
Yauwa Baffa, ya kuma na ganka fasa zuwa wajen Innan kayi?"
"Naje malam sai dai bata barni na kwana ba saboda tace auren Maryam jibi ne, gama iv ta bayar wai araba tun yau tunda abin ya kure".



Cikin madaukakin farin ciki malam yace " a a to Abu yayi kyau gaskiya naji dad'in hakan sosai Allah ya tabbatar mana da alkhairi" amen amen sun dan jima da malam suna tattaunawa kafin ya sallame shi ya taho gida.





Kafin ya shiga gid saida ya kira Halima dake yar abokansa ce Kuma makocin sa na amana yabata iv na daurin auren masu dan dama yace ta kaiwa Abban ta sannan ya bata na 'yan mata yace dan Allah yau ta fara rabawa k'awayen saboda Maryam bata nan su sosai tayi mamakin auren na Maryam yadda yazo musu babu shiri yadda sukaci burin wannan ranar, take ta kira Maryam k'awar Maryam ta jami'a suka sha mamakin su kafin su sannan suka fara rabo tunda lokaci ya riga da ya k'ure.



Wannan tsaye tsaye da Baffa yayi shi yasa ya manta da rubutun da Inna tace lallai lallai yasha kafin ya shiga gida



Dake yau Ammey ce da girki kuma yasan yadda suka rabu akan sai anbata 'yarta dan haka d'akin ta ya fara nufa sai dai yadda ya tadda ita ba k'aramin d'aga masa hankali yayi ba ya k'arasa kusa da ita yana tambayar Maryam abinda ya faru shida ya fita basa nan.



Cikin kuka tace itama bata sani ba bayan sun dawo MD ya kirata yace tazo ta kula da ita kafin ya kawo magani, daga haka ta fice ganin yadda Ammey take kalloan Baffa tasan akwai abinda take son fad'a masa.



Tana fita sukayi kicibus da MD wanda da k'yar ya samu maganin da Ammey take sha yace "ya kika fito?"
"Baffa ya dawo yana ciki"
Da mamaki yake kallon ta yace "bai kwana ba?"
"Inaga ya fasa ne"
Ta bashi amsa tana wucewa ciki saboda jin ana kiran sallar isaha, dan haka shima ya nufi part d'insa dan yayi tasa alwalar dan kar ya rasa jam i.





A b'angaren Mama kuwa tunda ta shiga d'aki ta kasa nutsuwa sai zarya take daga k'arshe ma kai tsaye bokanta ta kira ba aminiyar tata ba ta sanar masa duk halin da ake ciki,
Yace "kin lalata komai Sailuba dole ne abinda kike gudu zai faru, sannan bazaki samu komai da kike buk'ata ba, idan kina son cikar burinki dole ne kizo nan mu kadaice dake na kwana biyu dole nayi kwana biyu ina saduwa dake da wannan maniyin da zai fita a jikin ki zan miki aikin da zai baki mamaki bayan haka banida wata hanya ta samun nasarar ki".



Idanunta ya rufe,
Zuciyar ta ya toshe
Tunanin ta ya b'ace
Imanin ta ya barta
Bata da wani buri ko fata illah tarwatsa rayuwar yarinyar da babu abinda tayi mata wanda ya wuce yi mata biyayya da gwada mata k'auna irin na uwa mahaifiya da 'ya mai mutukar biyayya agareta.
Hakkan ne yasa Baffa yana shigowa ta fice dan boka yace kar ta bari su had'u dama dakon dawowar sa take wannan kenan.



Bayan Maryam ta idar da sallar tana shirin komawa b'angaren Ammey kiran name sake d'in ta ya shigo wayar ta ta d'aga tana fad'in 'yar halak wallahi jikin Ammey ne ya hanani kiranki"

"Eh kyace haka mana saboda rainin hankalin da kika saba, yanzu sahiba ace jibi jubi daurin auren ki amma sai yau muke sani kin kyauta ai"

Dakatar da ita Maryam tayi ta hanyar cewa " dake yar tsana ce ni shiyasa aurena zai kasance jibi har na kasa sani, ko shirin film ko kuma a littafi wanda suke shirya abu nan take"
"Idan kina musu ki bud'e data ki duba status dina mana ko muna da wata MARYAM BAFFA ABUBAKAR ne bayan ke?"
Ai bata tsaya jin k'arshen labarin ba ta katse kiran tana katsewa kiran Halima yana shigowa ta daga asanyaye saboda bazata iya katse kiran Halima ba amma bataso Kiran ba sai ta fara duba sak'on Maryam.




"Ba zaiyiyu mu zaga duka k'awayen mu yau ba dan haka waso duk ta whatsoapp muka tura musu katin gayyatar, idan Kuma kina da wani wanda zaki bawa idan kun dawo daga unguwar saina kawo miki sauran"

Da mamaki Maryam tace "ke nifa bangane inda wannan dogon sharhin naki ya nufa ba katin gayyatar me?"
Yadda tayi maganar ya tabbatar wa da Halima cewa Maryam bata san da maganar aurenta jibi ba dan haka tace mata "kun dawo ne?"
"Eh "kawai tace mata tana dafe kanta da ya soma k'ullewa da maganganun Halima da maryam

"Bari nazo yanzu" ta fad'a tare da katse kiran.
Ba a rufa cikakken minti uku ba Halima ta shigo d'akin ta karasa kusa da Maryam ta dafata tunda tayi sallama bata jitaba ta fad'a duniyar tunani.

Ba tare da ta ce mata komaiba ta mik'a mata iv mai d'auke da sunanta baro baro da sunan MD tareda tabbatar da d'aurin auren su ranan 2/3/2021
Sosai mamakin ganin katin ya kamata yaushe nema har tace tana son MD da za ayanke mata d'anyen hukunci haka?


Dafatan da Halima tayi ne ya maidota hankalin ta a hakanli tace "nayi matuk'ar farin cikin kasancewar wannan abun kuma nasan cewa kema baki san da maganar ba Maryam nasan wannan shirin Baffa ne dan Allah karki bujere"
"To" shine kawai abinda Maryam ta iya fad'a tana tunanin yadda MD zai d'auki abin yadda yake nacin soyayyar ta d'in nan bai samu gamshashshen amsa ba gashi yanzun ya sameta a arha, arha mana tunda tasan cewa wannan ba shirin Baffa bane na Inna ne dan Baffa duk abinda zaiyi sai yai shawara da ita da MD daga haka sukayi sallama da Halima bayan tayi mata nasiha ta bata ahawarwari sannan tace yanzun maman Niger zatazo tunda abin yazo a kurace ta d'an yi mata gyara sama sama Umma ne tasa a kirata.




Tana fita MD yana shigowa d'akin cikin wani irin sauri ya k'araso kusa da ita ya tsaya yace "my happiness kinga abinda nagani kuwa?"
"Eh na gani" ta fad'a a sanyaye haka nan maganar take sa mata wani irin fitinannen bugun zuciya "me kika ce akai to?"
A dan sanyaye ta kalleshi kafin lumshe idanunta ta bud'e akanshi zuciyar ta na wani irin fitinannen bugu har tana dafewa tace "me kake so nace to?
So kake naje nacewa Baffana ban amince da zab'in saba?"

Sam bai kula da yanayin ta ba ya duka ya d'an tsotsi tattausan lab'b'an duk kuwa da irin yadda take nuna masa bata son hakan ya dafa kanta yace "miki alk'awarin insha Allahu bazaki tab'a nadamar kasancewa na mijinki ba ya kuma manna mata wani kiss d'in a goshinta kafin ya fita da d'an gudun sa dan kar tayi masa magana, gane hakanne yasa ta saki murmushin da bata shiryawa zuwansa ba.




Bayan Baffa ya dawo daga massalaci ya shigo d'akin Ammey yaji dad'in ganinta akan sallaya itama tayi sallar tana jingine a jikin gado tana jan carbi.


K'arasawa yayi kusa da ita ya zauna dab'as yana dubanta kafin yakai hannun saman fuskar ta ya d'an shafo "ya jikin babyta?"
Ya fad'a da salon tsokana wanda rabon da hakan ya kasance an d'an jima sai abin ya bata dariya sosai, sai ta d'an murmusa tace "da sauk'i kafin takai hannunta saman nashi tace "Baffa"
"Na am" ya amsa mata cikin sanyin jiki

D'an Allah kada ka bari abinda yake faruwa da rayuwar Maryam yaci gaba da faruwa dan girman Allah, saboda kaga rayuwa ba tabbas idan yau mune gobe fa jibi fa haka wata rana bama nan an gina rayuwar 'yata cikin wani irin gurbataccen yanayi wanda sam bai min dad'i ba Baffa, kasancewar Sailuba na 'yar uwar ka bai kamata ace tayiwa 'yarka irin wannan tarbiyyan ba, kasan mai yafi d'aga min hankali?"

"a a" ya fad'a yana kafe ta da wani irin kallo gabansa na mugun fad'uwa ya saboda yadda yaga ta koma kamar babu jini a jikinta, yayin da taci gaba da cewa "ce matafa tayi taje tayi duk abinda zatayi itadai karta sake ta d'auko mata ciki"
"Ita Sailuban?" Baffa ya tambaye ta a fusace nan ta kwashe duk irin abunuwan da maryam take fad'a mata idan sun keb'e ta fad'a masa tas.



Ran Baffa ba k'aramin b'aci yayi ba ya nufi part d'in Sailuba a fusace, sai dai abin ta kaicin yana shiga ya tarar bata nan a gogon hannun sa duba tara da rabi na dare, yaushe har nayi saken da Sailuba takeyin yadda taga dama a cikin gidannan?
Ni kuwa nace an maka dabaibayi ne malam Baffa shi yasa take yadda taga dama hhhhhhhh.


Tun yana saka ran dawowar ta har k'arfe daya ta buga wanda ya tabbatar masa cewa Sailuba bazata dawo daga yawon gantalin ta yau ba, ai kuwa ransa ya kai k'ololuwar b'aci yasha alwashin sai ya sab'ar mata fiye da kima.




Acan wajen boka kuwa irin yadda ya rika durza Sailuba ko Baffa bai tab'a yi mata irin wannan durzar ba iya bak'ar azaba awannan daren Sailuba tasha a hannun katon kafirin da babu Allah ko kad'an a zuciyar sa haka ya kwana abu d'aya da ita ga abin nasa mai mugun tsayin da ya wuce tunanin ta gashi mugun fitinanne ka masifar warin da yasa ta rik'a yunk'urin amai amma ta kasa yi bashi ya k'yale ta ba sai da garin Allah ya waye tangaram Kuma ya hanata yin sallar yace ita da salla sai in ta koma gida tayi, dake idanunta ya riga da ya rufe cikar burinta kawai take buk'ata ba wani ja ta amince hakanan ya wuni sa suk'ar ta kamar ya samu abinci.


Ganin k'arfe uku ya buga yasa Baffa komawa d'akin Ammey cikin tsantsar b'acin rai ga mamakinta saman dadduma ya tadda ta tana lazumi duk da kasancewar k'arfin hali kawai take hakan ba k'aramin dad'i yayi masa ba.




K'arasawa yayi kusa da ita ya zauna ya kamo hannunta yace "ki kwantar da hankalin ki Amina ta addu'ar ki ya amsu jibi daurin auren Maryam da MUHAMMADU inji Inna"



Wani irin kafe shi tayi da ido kafin ta fad'a jikinshi ta k'ank'ame tace "na gode na gode ba ka gama min komai naji duk wani fargabana ya kau Baffa Allah ya sakawa Inna da mafificiyar Aluannah.


Ta fad'a cikin fashewa da kuka yace "to meye kuma na kukan 'yan mata na kunya ne ta kamata dan haka ta b'oye fuskar ta a k'irjinshi, ranan dai haka suka karasa wannan daren cikin farin ciki da nishad'i wata irin hira sukayi mai dad'i da tsayawa a rai Sosai Baffa ya samu sauk'in b'acin ran da Sailuba ta dasa masa.





Abangaren MD kuwa tunda ya fita daga d'akin ya koma part d'insa ya zauna cikin wani irin farin ciki duk shafukan sa na sada zumunci babu inda bai d'ora sanarwar auren su da Maryam ba yayin da itama maryam kwana tayi saman abin salla saboda halin da ta kasance ya k'azanta ba ita ta samu ta hutaba sai bayan anyi assalatu.





Rana baya k'arya sai dai uwar diya taji kunya yaune d'aurin auren Maryam da MD wanda yau tun safe ake shirye shirye wanda yasa duk damuwar da take ji tsayin kwanakin ta nemeshi ta rasa.



Ta bangaran Ammey 'yan uwanta sunzo sosai sai hidima ake, haka b'angaren ango cike tab da abokansa ana ta zuba masa shakiyan ci, haka dai aka shiryawa auren abokin nasu wanda har lokacin ya karato, idan ka kalli MD kuwa wani irin annurin farin ciki ne kwance a saman fuskar shi yayi kwalliya cikin bluen shadda wacce akayiwa riga da wanda da babba riga kayan sun yi mugun amsar jikin sa yayin da ya dinkawa Maryam nata ita kuma ruwan hoda tayi wani irin fitinannen kyau itama ba k'arya.



Hum zo kaga Baffa uban amarya shima yasha wanka iya wanka duk da kasancewar yana cikin halin damuwa na rashin sanin inda Baffa ya tafi hakan bai hanashi sakin fuskar ta shi ba da farko yaso a d'aga auren a tunanin sa Sailuba b'ata tayi amma Inna wacce ta k'araso da tawagar ta mota kusan biyar tace babu abinda zasu fasa haka aka cigaba da shagalin batare da sanin uwar amarya ba🤪🤪🤪🤪





Haka haj. Sailuba tayi kwanan wahala kwanan tashin hankalin kwanan masifa, a yadda takejin k'asan ta da k'yar idan mutumin nan bai farkata ba, amma idan ta tuna cewa muradin ta ya kusa cika sai taga hakan ba komai bane, kafin ta baro wajen boka sai da ya shaida mata yau za adaura auren Maryam da MD dan haka ta yi k'ok'arin ganin ta isa gida kafin agama shafa fatiha domin idan an d'aura bazai kuntu ba, haka ta baro wajen sa hankali a tashe tana fatan ta tadda ba a d'aura ba.





Tana shigowa dakin wani butu butu da ita suka fara ido hudu da Baffa wanda shigowar sa kenan daga wajen daurin auren a fusace yayo kanta cikin bala' i amma suna had'a ido ya nemi fushin nasa ya rasa sai ma washe baki da yayi yace "a a Sailuba, Sailuba, hajajjuna daga ina haka?"
Yai mata tambayar cikin sanyin jiki yayin dayake jin wani irin d'aci can k'asan ranshi.




Ganin yadda aikin yayi saurin tasiri yasa tace "ban sani ba daga inda ka aike ni"
"A a Allah ya baki hak'uri nifa badan na b'ata miki na tambaya ba ganin yadda hankali na ya tashi ne yasa na ke tam""''""' kai dan Allah karka cika min kunne da surutun ka na banza" sai kuma ta bi 'yan falon da wani kallo kafin ta maida hankalin ta kanshi tace



" Me ake yine naga an wani cika mana gida da wannan kazaman k'auyawan?"
Washe baki Baffa ya sake yi da dariya yak'e yace "d'aurin auren yarki ake " 'yata kuma wacece hakan?"
Ta tambaya tana tamke fuska a hankali yace "Maryam nake nufi Mana"

Sai tayi wani shu' umin murmushi tace auho " cemin zaka kayi shegiyar da akayo cikin ta a waje aka halarta maka"
Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara Baffa ya kafe Sailuba da ido yayin da duka 'yan taron bikin suka kewaye su da hayaniya da son jin kwakwaf wasu kuwa fad'i suke ji tsinanniya saboda bak'in cikin ke baki haihu ba shine zaka sheganta masa 'ya shi kuwa Baffa ji yai kansa yayi wani masifaffen sara masa take jikinsa ya kama rawa, yay saurin dafe kannan nasa da yake wani jin kamar ana buga masa gudu da sauri yayi saurin durkushe wa a wajen, yayin da itama Sailuba tayi saurin durkushe wa a gabansa ta bud'e dukan muryar ta da mugun k'arfi tace "EH BAFFA ABUBAKAR BA K'ARYA NAKE BA CEWA MARYAM BA YARKA BACE BA JININ KA BACE AN KAWOTA NE KAWAI DAN A GURBATA MAKA ZURI A KATAMBAYI UWAR TA WANENE UBANTA?


Da k'arfin gaske Baffa ya dafe kansa dayake bara zanar rabuwa da gangar jikinsa, yayin da kalaman ta sukayi wa Maryam da Ammey wani irin duka wanda atare suka shigo babban fakon Maryam tare da k'awayen ta dan amsa kiran Inna yayin da Ammey kuma tazo kawowa su Inna abincin su.

Tab Cha kwakiyar fa kenan
To masu karatu shin an d'aura auren Maryam da MD?
Baffa yana yadda da da maganar Sailuba?
Wane hali MD yake shiga idan yaji wannan mummunan al'amarin?
Da gaske ne Maryam BA JININ Baffa bane ko makirci ne?
Sannan wane hali Ammey take shiga sakamakon jin wannan mummunan al'amarin?


Duka wannan amsoshin dama wanda baku nema ba suna cikin littafin BA JININA BACE kashi na biyu wanda zai zo muku nan bada jima wa ba insha Allah ga mai buk'atar cigaban sai ta nemeni a lamba ta kamar haka 09030311095


Daga taku insha Allah
MAMAN ISLAM CE maiyi muku fatan alkhairi a koda yaushe

Thank you so much Allah yabar zumuch

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment