Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

ta tana jin wani irin farin ciki da k'aunar 'yar k'anwar tata.

Tana rike da hannun maryam suka shiga k'aton falon momman wanda ke d'auke da wasu had'ad'd'un kukeru masu kyau da numfashi.

Shigar su yayi dai dai da ahigowar yaran mamma 'yan mata guda biyu saiga k'aramar sun nanma ta shigo tana kukan wai sun barota amota babu wanda yabi ta kanta suka shige da gudu suka rungume maryam dan sun santa sosai a hoto duk da cewa tun tana yarinya ne irin wanda Ammey take fakar idon haj. Sailuba tayi mata, amma Kuma ai ga kama nan domin babu ta inda Maryam tabar Ammey.

Ita kanta Maryam tayi matuk'ar farin cikin had'uwar ta da su yayinda wani irin so da k'aunar su yayi ma zuciyar ta kamun farat d'aya.

Nanfa falon ya gauraye da hayaniyan su dan maryam dama can bata da bak'unta dan haka ta sake a cikin su suna kwasar shafta sannan Kuma duk wanda yay mata ta mangare shi kunsan babyn ba hak'uri๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚

Hakan ba k'aramin nishad'i yasaka momma ba hatta abinci ita ta rik'a bata a abakin ta da k'yar su mardiyya sukayi nasaran janye maryam zuwa dakinsu.

Haj. Shamsiyya yayar Ammey ce inajin nayi muku wannan bayanin tun farko itama mijinta babban d'an kasuwa ne yana da rufin asiri mai yawa dan shima Allah yayi masa farcen susa

Yaran ta biyar na farkonta 'yan biyu ne duk maza Abdul Malik, da Abdul jabbar, dukan su sanyi aure da yaransu, sai Fadeela itama yanzun haka yaranta biyu dan tun kafin auren Ammey aka haifesu da wayon suma akayi bikin Ammey da Baffa.

Daga bayan sun fidda rai da sake samun haihuwar ne kuma Allah ya sake bata wasu 'yan biyun duka mata Mardiyya da Fauziyya sai autar su Hanifa wacce itama ak'alla su mardiyya sun bata kusan shekara goma dan duka yanzune suke shirin zana jarrabawan su na shiga jami'a.

Suna barin gidan Ammey ta dubi haj. Shamsiyya sai hawaye shar shar haj. Shamsiyya ta dubeta tace "a yada haka Kuma?
Memakon ki farin ciki ki godewa Allah 'yarki ta dawo gareki" rungumeta Ammey tayi tace anty sai kuma ta kuma fashewa da kuka.

Sai da taci kuka sosai kafin ta d'ago daga jikin'yar uwar tata kafin tace "anty dan Allah idan na mutu kada kibar Nassar a hannunta zata gur b'ata masa rayuwa" K'are zancen cikin zubowar wasu sababbin hawayen.

Had'e rai haj. Shamsiyya tayi tace me kuma ya kawo zancen mutuwa ana zaune kalau kadama ki sake wannan maganar insha Allah tare zaku girma da yaronki har kiga auren shi"

"Karki ga yadda ta tsaneni tana yarinya karkiga halin dana shiga akan ta naci wuya anty yau zan fad'a miki abinda baki sani ba, INA DA CIWON ZUCIYA, duk a sanadin halin danake ganin'yata a ciki kuma bani da ikon magana yarinyar tayi wata irin rayuwa ne mara dad'i mara ma'ana.

Sosai haj. Shamsiyya ta kafe Ammey da ido jikinta yana rawa sosai tace "CIWON ZUCIYA Amina wannan wane irin mugun hali Allah yayi miki na barin abu arai bazaki fitar dashi kiji sanyi ba haba Amina" ta karasa maganar cikin fashewa da kuka sosai, taci gaba da cewa "ashe duk fad'an da nake miki na ki janye 'yarki bakiyi hakan ba kikayi tasa abu aranki har ya zamar miki ciwo arai, kar kimin haka Amina dan Allah" momma take maganar cikin gurshek'en kuka dan tasan tunda har Ammey ta furta tana da ciwo to abinne ya girmama.

"Ki yafemin dan Allah anty bana son sakaku adamuwa ne banda ke babu wanda yasan ina da ciwon dan Allah kar ki bari su Baffa suji hankalin su zai tashi"

Rungumeta momma tayi cikin tsantsar tashin hankalin da tausayin 'yar uwar tata yayin da Ammey kuma taci gaba da bawa yayar tata labarin irin rayuwar da maryam tayi tare da irin halin da ta rik'a kasancewa a ciki a duk lokacin da Baffa ya juya mata baya, akarshe kuma dad'a jadaddawa antyn tata take ta kular mata da yaranta idan ta mutu, nan kuma ta kuma bata labarin irin mugun mafarkan da takeyi mara dad'i wanda tasawa ranta akwai abinda wannan makirar matar take shiryawa.

Sosai hankalin haj. Shamsiyya ya tashi amma sai ta danne nata damuwar ta rik'a tausar 'yar uwar tata har sai da taga ta samu nutsuwa, anan take sanar mata Baffa ya tsaida lokacin auren Maryam d'in da Muhammad, ai kuwa ba k'aramin dad'i hakan yayi mata ba dan ta jima tanayi wa Maryam d'in shi'awar auren MD saboda nutsuwar yaron.

Acan d'akin da su Maryam suka bajakolin hirar su kuwa Fauziyya ce ta dubi Maryam tace "dan Allah sis ki rik'a biyo Ammey kuna zuwa wallahi munji dad'in zuwanki ke d'in fa JININ muce" murmushi Maryam ta sakar mata tace "shikenan sis zan rik'a zuwa dan nima naji dad'in kasancewar mu tare Allah ya bar k'auna.

Acan gida kuwa MD ji yai hankalinsa yayi wajen Maryam kamar ya bita sai dai yana binta Ammey zata gane saboda Maryam ne hakan kawai yasa ya yanke shawaran yakai ma m Bash ziyara.

Kar ku manta Baffa bai sanar da MD maganar aurensa da Maryam ba hakanan haj. Sailuba bata sani ba, bawai kuma saboda wani abu yak'i sanar da ita ba sai dan b'ata masa ran da tayi na barin Ammey ta tafi da maryam d'in alhalin yana son zuwa da ita wajen Inna wanda dama zai jene dan sanar da ita maganar auren Maryam da MD d'in ne.

Ku muje dai masoyana
Ina alfahari daku duk inda kuke a fad'in duniya

MAMAN ISLAM taku ce mai matuk'ar k'aunar ku
ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑ ุญูŠู…
*__________________________________*

โ˜€ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* โ˜€

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
๐Ÿ”ฅ BA JININA BACE๐Ÿ”ฅ
2021

NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 42

Bayan ya gama shirin sa ya fito cikin k'ananan kayan da suka matuk'ar amsar sa,ya fito yana baza k'amshin sa mai kwantar da zuciya.

Yana sako kai haj. Sailuba na fitowa daga lambum kusa da Pat dinsa cikin wani irin sauri tana wage wage gudun kar wani ya ganta da ganinta ba abin arzik'i ta shuka a wajen ba, wani mugun kallo ya bita dashi cikin tsana sannan ya yaja wani uban tsaki ya shiga lambun dan haka nan yaji yana son ganin meta aikata awajen.

Da kallo ya rika karewa wajen kallo har idanunsa suka sauka kan wajen da aka hak'e da alama wani abun aka bunne awajen, gabansa ne yai mugun fad'uwa ya taka a hankali cikin nutsuwar sa ya karasa yana nazartar wajen kafin yayi Bismillah ya durk'usa dan tsabar saurin da take hatta abin hakar bata d'auke ba ta manta da shi a wajen.

Sai da yai addu a sosai kafin ya fara hak'a ramin da tayi, yayi mamakin yadda ta iya hak'a rami mai uban zurfi haka, yajima yana hak'a dan har ya fara tunanin babu abin da ta binne kafin yaji hannunsa ya caki wani abu mai mugun tsini da sauri ya janye hannun saiga jini yana bin hannun nasa wanda jini ya fara bi ga wani mugun radadi da ya zuyarci har kwakwalwar sa, mamakin hakan yasa kashi saurin lek'a ramin haba da sauri ya janye kansa yana sauke wani irin wahalallen numfashi sabo da wani fitinannen wari daya daki hancin sa, sai dai abinda ya gani yasa shi saurin komawa tare da dauke numfashi dan tabbas wannan masifar zai iya masa illah.

Mikewa yayi ya koma d'akin sa hankali a tashe ya d'auko hanglob jikinsa har wani rawa rawa yake sosai yazo ya hau fito da abin bakinsa d'auke da addu'a, yanzu kam rawa jikinsa ya kama sosai saboda tsabar mamaki.

Kan mujiya ne jikinsa duk wasu irin manyan allurai sai kuma wata 'yar k'aramar benu da aka sa wata katuwar allura aka caki daidai zuciyar ta sai numfashi take fitar wa da k'yar ga wasu irin curin layu masu yawa suma a saman wata tsuntsu da baisan ko ta mecece ba itama daga gani ajikace take tama kusa mutuwa.

Idanunsa da sukayi wani fitinannen ja ya runtse da mugun k'arfi ya zauna dab'as a wajen cikin ciyayin gun ya dafe kansa da yake mugun sara masa da k'arfi yace "innalillahi wainnailahi raji'un Maryam ko Ammey zata kashe?"

Dan shi abinda ransa ya bashi kenan na ganin wannan masifar alluran dake jikin tsuntsayen da suke da rai ya fara zarewa kafin ya cire na jikin mujiyar gaban sa na wani irin mugun fad'uwa hankalin sa a masifar tashe bai ma yarda da kona kayan kai tsaye ba sai da yayi musu fitsari kafin yasa fetur ya Kone.

Tunda taga Ammey ta fara shiri tace itafa sai gobe zata dawo dan gajiyan hanya bai gama sakinta ba sosai Abdul jabbar da yake ta binta da kallo yasaki murmushi yace "kawai ki k'yale ta Ammey ma kawota nida Abdul Malik"

"Rufamin asiri Abdul jabbar Baffanku baisan nazo da itaba, kabari tunda bikin ta za ayi tazo tayi muku kwana biyu" sai da gabansa ya fad'i da yaji wai bikin ta za ayi dan har ga Allah tayi masa sosai.

"To 'yata sai kinzo gyaran jikin ni da kaina zanwa 'yata gyara na musamman, dake sana 'ar tane gyaran amare da haka sukayi sallama.

Tana zaune cikin jin dad'in cikar burinta haj. Zakiyya ta kira tana d'agowa tace "ba nutsuwa ba kwanciyar hankali ita ba mahaukaciya ba kuma ba mai hankali ba sannan ita ba rayayya ba sannan kuma ba matacciya ba" hhhhhhhhh suka saki wata muguwar dariya haj. Zakiyya tace an aikata ke nan?"

Me zan jira k'awata kinajifa boka yace uban yatsaida aurenta da wannan tsinannen yaron dana fi tsana fiye da komai a rayuwata wallahi bazan bar wannan banzan auren ya faru ba na rantse kuma" ta k'arasa maganar tana huci

Har lokacin MD yana d'akin sa cikin tsantsar damuwa da nazarin son gane shin cikin Ammey ko Maryam wa akayi wannan bak'in asirin dayai masifar d'aga masa hankali?
Ya sandai wannan tarkacen bala in ba abin arzik'i aka shuka a cikinsu ba.

Kamar wanda aka tsikara ya mik'e zumbur domin kaiwa haj. Sailuba fatanyar ta da ta manta.

Yana fitowa ana budewa motar su Ammey gidan, dan haka ya dakata har driver ya shigo ya faka motar duk suka fito da gudu Nassar ya k'araso ya rungume MD wanda yai kasak'e yana kallon su, yana mai murnan ganin yayan nasa.

Da wani irin kallon mamaki Ammey tabi kayan hannun MD yayin da Maryam ta wuce ciki tana mai dok'in ganin mamanta.

"MUHAMMAD wannanfa me kayi dasu naganka futu futu haka?'

" Ammey" sai kuma yai shiriu zuciyar sa na wani irin zafi yay saurin dafe kansa kafin yace "wa take son kashewa Ammey ke ko ZUCIYA TA?

Muje dai

DAGA MAMAN ISLAM

๐Ÿ”ฅ BA JININA BACE๐Ÿ”ฅ

2021
NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 43

Kallon Ammey yake dafe da kirjin sa wanda zuciyar sa take barazanar fitowa, itama kallonsa take da son k'arin bayani.

Dak'yar ya bud'a baki yace "Ammey wani aikin nayi mai wahalarwa Ammey me waccen matar take nufin yi ne akan ni da matata Ammey na rantse da Allah wani abu yasamu matata ni da kaina zan d'auke kanta da wu'ka da wadannan hannayen nawa.

Ya fad'a yana d'aga hannun nasa wanda suke wata irin rawa sama.

Da wani irin rawa Ammey ta danki hannun MD jikinta na kakkarwa tace "wayyo Muhammad rik'e ni zan fad'i" tayi luuuuuu da wani azababban zafin nama MD ya rik'o ta cikin wani irin rikitaccen yanayi yace "Ammey lafiya kuwa"?

"Kaini d'akina Muhammad banida lafiya" da sauri ya d'auke ta akafad'unsa yayin da jikinsa yake wani irin rawa jikinsa kuwa ta ko ina gumine yay masa wanka.

Da sauri ta janye wayar daga kunnenta tana fad'in "zan sake kiranki anjima k'awata" nakamakon juyowa da tayi sukayi ido biyu da Maryam da tajima abakin k'ofar tanajin irin mugun abun da maman tata take k'ullawa tambayar da Maryam take wa kanta shine
"Shin waye za'a haukata?
Waza a tozarta ya wulak'anta?
Waye zai zama abin k'yamar al'umma?
Me yaye mata take son ya zamo kamar mujiya?
Akan me take so yayi warin jab'a?
Shin dama mama tana yawon bin malamai ko yanzun ta fara?
Ta yarda da daukar wannan babban zunubin ko kuwa?
Dawa take wannan Killin?"

Inda haka ne mama baki da imani baki da tausayi baki damutunci matsayin ki na musulma ki rink'a had'a mugun k'ulli haka?

Duk tayiwa zuciyar ta wadannan tambayoyin, yayin da zuciyar ta yake wani irin bugawa sai taji hankalin ta yai masifar tashi wani irin tsoron maman tata ya mugun kamata da gudu ta juya ta fice daga d'akin cikin tashin hankali gaba d'aya idanunta ya rufe.

Tazo shiga d'akin suka gwabza karo da MD wanda yazo neman ta ta tsaya da Ammey wacce ya gama duba zai nemo mata magani, take tayi baya zata fad'i da sauri MD ya taro ta ya rik'e ta yana kallon yadda jikinta yake rawa

Suna had'a ido da shi ta fashe da wani irin kuka har da shashshek'a, ina ma ace Ammey ce maman ta ba wannan matar mai bak'ar zuciya ba, inama ace hannun agogo zai dawo baya data rok'i ubangiji ta fito a tsatson Ammey, sai dai Kash d'an Adam bashi da damar zab'a ma kansa rayuwa sai yadda ubangiji yayi da bawan sa,

"Allah kaza gatana Allah kazama gatana Allah kazama gatana" take ta maimaitawa cikin tashin hankali da wani irin fitinannen kuka, baisan lokacin da yajata jikinsa ya rungumeta da mugun k'arfi hannunsa na wata irin rawa ya d'ora abayan ta yana shafawa a hankali.

Jabbar Mama ta koma saman gado ta zauna tare da d'ora hannunta saman kanta tace "shi kenan na shiga uku taji komai wayyo Allah yau dubana ya cika innalillahi asiri na zai tonu"

Jiki na rawa ta ja waya ta kira haj. Zakiyya tun kafin ta d'aga tace "shi kenan k'awata yau taji komai dakanta ta kamani muna waya dake shikenan zata had'a ni da Baffa na shiga uku na lalace"

"Ke taya akayi kika san tajiki ba kince sun fita da Amina ba?"

"Wllh taji karkiga mugun kallon da take bina dashi dana ganta ma zan wayance bata saurare ni ba juyawa tayi da gudu ta fice"
Kinsan ya za ayi?"
"A'a"

"Zuwa zakiyi kiji idan kin tabbatar da taji abinda muka tattauna sai kibi duk hanyar da zakini nuna mata cewar kunnenta bai juyo mata daidai ba" daga haka suka yi sallama ta mik'e tayi d'akin Maryam.

Tana d'aga labulan tayi wani irin baya cikin girgizar zuciya batasan sanda ta kurma wani mugun ihu tace" jama'a kukawo min d'auki kwarto zai lalata min 'ya"

A firgice duka suka juyo suka kafeta da ido yanayin sa ba karamin firgita ta yayi ba tayi saurin k'asa da kanta jikinta yana wani irin masifaffen rawa,bata san sanda ya k'arasa kusa da itaba yace adaidai kunnen ta yace "ajiyar ki tananan acikin lambun na bar miki"

A firgice ta d'ago tana kallonsa kafin tayi wani luuuuuu ta zube awajen tsabar tashin hankalin jin abinda yace mata

Plss manage

MAMAN ISLAM CE
*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

*โ˜€๏ธ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION โ˜€๏ธ*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*

https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?type=3&source=45&refid=17

______________________________________
๐Ÿ”ฅ *BA JININA BACE* ๐Ÿ”ฅ
*2021*

NA

*HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI*

*MAMAN ISLAM*

PAGE 44

Da sauri Maryam ta nufeta, yay saurin tareta yana kallon cikin idonta da kallon kar ki soma.

"Mama nace fa" ta fada a raunane "maman naki ban lamunta ba kibar ta zata tashi ga Ammeyn ki cen ciwon zuciyar ta ya tashi" da sauri ta kafe shi da ido gabanta yana wani irin dokawa tace "ba yanzun muka dawo daga unguwa ba?"
"Eh kinsan al'amarin ubangiji babu yadda baya juyawa bawa kuna shigowa bayan shigewar ki ciki ta yanke jiki ta fad'i, yanzun ma magani zan amso mata na gama dubata.

A hankali ta juya ta kafe mama da wani irin kallon tuhuma da tsoro tace "kece ko?"
Mama da tun da ta fad'i take wani irin kukan zuci mai azabar radadi tayi saurin girgiza kai, alamun babu ruwanta.

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tare da kwafa ganin yaja hannunta sun fice,.
"Sai naga bayanka wallahi Muhammad tunda kayi sanadin rusamin shirina saikayi nadamar yin hakan dan haka nice ajalinka wallahi saikayi nadamar shiga rayuwana da kayi" ta mik'e tashige d'aki tana sakin kukan bak'in ciki.

Yanayin da taga Ammey yasa ta k'arasa da sauri ta rungumeta tareda fashewa da kuka tace "Ammeyna me ya sameki daga dawowar mu?
Kodai akanki ne naji mama na waya?"

Kafeta da ido Ammey tayi batare da tace mata komai ba yayin da zuciyar ta yake mata wani irin fitinannen suka, batasan lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba mai mugun cin rai.

Ita ma maryam fashewa tayi da kuka tare da k'ara k'ank'ame Ammey tana fad'in "sannu Ammey yana miki zafi ko zai daina kinji dan Allah ki bar kukan nan haka yana Kona min rai.

Wani mugun kukanne ya kuma taho mata tayi saurin toshe bakinta da hannun ta tana jin wani mugun tausayin Maryam yana kamata, ta sani rayuwar Maryam yana cikin gagarumin matsala, tasan Sailuba tasan wacece ita muguwa ce azzalumar matar da batasan Allah ba babu d'igon tsoron Allah a tareda ita makira ce ta ajin k'arshe bata da imani ko k'ank'ani.

"Maryam kiyi hak'uri da rayuwa ki gyara d'abi'unki duk da kasancewar naga sauyi mai yawan gaske atare da ke, amma ina so kisani rayuwa bashi da tabbas, idan yau mune gobe ba mu bane, dan Allah zan rok'eki duk halin da kika tsinci kanki, ki kasance mai yawan godewa Allah, ki kare Martaba da kimar ki na d'iya mace k""""'''''''''ya isa dan Allah ya isa Ammey ki daina min irin wannan zantukan masu kama da wasiyya, daga kinyi d'an zazzab'i sai ki kama wasiyya kamar mai shirin barin duniya yanzu yanzu, insha Allah sai kinga jikoki na" ta fad'a cikin matsanan cin rawan jiki ga kukan da take ya kasa tsayawa tsabar tashin hankalin da kalaman Ammey suka saka ta a ciki.

Wani irin murmushi tayi mai ciwo sannan hawayen ta basu bar zuba ba, sannan bata fasa yiwa Maryam nasiha ba akan rayuwa da zaman takwar mutane tare da fad'a mata yau da gobe kai ranan dai babu wani jin dad'i a wannan gida.

Acan k'auye kuwa bayan Baffa ya isa ba k'aramin farin ciki Inna tayi da ganin tilon d'an nata ba, sai dai shi kad'an sa ta ganshi babu maryam kamar yadda yadda ta buk'ata, hakan bai wani bata mamaki ba tunda tafi kowa sanin halin Sailuba "kai wannan yarinya Allah dai ya shirya, Allah kanaji kuma kana gani na fita hakkinta na bata tarbiyya gwargwadon iyawa ta Allah karka kamani da laifin gurbacewar halinta dan alfarmar fiyayyen haltta (S A W).

Nan falon ta tayi masa shimfida ya zauna takawo masa ruwan randa mai sanyi da fura wacce taji lafiyayyan nonon shanu zuryan, kasan cewar tasan da zuwan sa.

Sai da suka gama gaisawa sannan ya soma furar kasancewar yana sonta sosai yana sha suna d'an tab'a hirar duniya da Inna wanda duk rabin sa nasiha ne da shawarwari cikin hikima.

Bayan ya kammala ne ta dubeshi tace "kaje kasamu kawun Muhammadu dan a tsaida daidai lokacin da za a d'aura auren Maryama da shi Muhammadun dan insha Allahu jibinnan za'ayi babu jinkir tawa"

Da sauri Baffa ya dubeta yace "jibi kuma Inna?"
K
"Ko ban isa zartar da hukunci akan jika ta bane?"
"A haba Inna kin isa har kinyi yawa"
"To katashi kaje ka dawo kazo ka amshi naka iv da zaka rabawa 'yan uwa da abokan arzik'i, saboda nasan shiriri tarka shiyasa nasa aka buga har kai, sannan magana tagaba Baffa koda wasa Sailuba kar tasan jibi daurin auren Maryama domin na fahimci ita d'in fitina ce arayuwar Maryama, kai wannan yarinya Allah dai ya ganar da ita"

Daga Baffa ya fita zuwa gurin yan uwan marigayi aminin shi Hassan

"To katashi kaje ka dawo kazo ka amshi naka iv da zaka rabawa 'yan uwa da abokan arzik'i, saboda nasan shiriri tarka shiyasa nasa aka buga har kai, sannan magana tagaba Baffa koda

Please Login or Register in order to submit comment