Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da shi kuma ya k'ara wani marai raice mata sai ta samu kanta da kasa yi masa musu ta koma ta zauna, shima tsulum ya taso daga inda yake ya dawo kusa da ita "lafiya?"

Tace dashi tana kallon yadda yake wani faman shafa cikin sa d'an marairaice mata yayi yace"yunwa nakeji nima"

Abincin da ta zuba zata ci ta tura masa ta d'auki wani flat d'in yay saurin dafe hannunta yana girgiza mata kai ta d'an kafe shi da ido dan neman k'arin bayani "ki bani mana" ya fad'a yana kallonta ta d'an had'e rai shi kuma ya kafa mata naci sai da ta bashi haka kuma shima yabata suka ci suka k'oshi.


Da alama nacin MD ma kawai zai sa yasamu yadda yake so lol🤣🤣🤣🤣🤣






















Maman Islam ce

بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥

2021

NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM




Page 32


Tana fitowa daga d'akin daidai shigowar haj. Sailuba, idanunta k'yar abakin k'ofar Ammey dan sam bata son had'uwa da kowa wannan shine sa ar aikin ta na yau tana ganin Maryam da bata kula daga inda ta fito ba ranta yai masifar b'aci babu makawa wannan la'a nanniyar yarinyar ta b'ata mata shiri.



Tsawa ta buga mata tace "ke dan ubanki daga ina kike bana hanaki mu a'mala da wadannan matsiyatan ba?"
Da kallon mamaki Maryam ta bi mama wadda tun kafin ta kai karshen maganar ta ta gano kuskurenta tayi saurin fuskewa dan kar ta gano ta, amma duk da haka sai da Maryam ta hango tsantsar tashin hankali atareda maman tata.




"Lafiyan ki kalau mama?"
Kallonta mama ta d'an yi cikin alamun rashin gaskiya kafin ta wuce b'angaren ta cikin tsantsar tashin hankali.



Tana shiga bata bi ta maganar sallar magriba da ake ta kwad'awa a masallaci ba ta zari waya jikinta har rawa yake ta dannawa haj. Zakiyya wacce ita shigarta nata gidan kenan kira da mugun mamaki ta d'aga kiran tana cewa.


" Ya akayine k'awata ko zama banyi ba sai ga kiranki?"

" Na mutu zakiyya, shikenan kuma nawa ya K'are na shiga uku zakiyya da wannan la'ananniyar yarinyar na fara karo wacce boka yace har gwanda naga kowa dana fara ganinta?"
Ta fad'a cikin rushewa da wani fitinannen kuka cikin tashin hankali.


Ita kanta wani irin fad'uwar gaba ne ya rufeto mata agigice tace
"Ke kuwa Sailuba wanne gangancinne yasa kika bari kuka had'u?"


"Cikin kuka tace wallahi nima bansan zamu had'u da itaba kawai ina shigowa mukayi kicib'us"


"Allah yasa bakice zakiyi mata fad'a ba dan gudun kar kija mana matsalar kuma"



"Nayi, sai dai kafin na dire na gano kuskurena nayi saurin fuskewa"
Nan dai suka fara tsara yadda zasu sabunta shirin su tunda wannan ya ruguje.





Ganin yadda maman ta d'aga hankalinta har tayi hanyar d'akin sai kuma ta fasa aranta tace ai kina da kud'i zaki sha kan matsalar, ta juya ta shige d'akin ta batare da wani damuwa ba ta shiga wanka a gurguje tayi wanka ta fito ta kabbara salla bayan ta idar ta d'an yi kwalliya sama sama ta fice, duk suna wajen cin abinci kamshinta ne ya sanar dasu zuwanta, duk suka bita da kallo babu MD awajen duk sai taji babu dad'i dan tun d'azu take ta faman juya labarin da Ammey ta bata nasa tana da tausayi duk da kasancewar ba wai yasha wani wuya na azo agani ba amma rashin mahaifiya ba d'an k'aramin gib'i bane ga rayuwar yaro.



Tana shirin zama Baffa ya dakatar da ita yace taje ta dubo yayanta ko lafiya dan tunda ya shigo bai ji motsin saba, jitai gabanta ya wani buga da k'arfi take abinda ya faru agidan m Bash ya dawo mata sai dai bata da damar yiwa Baffa musu hakan yasa ta fasa zaman ta juya kamar kazar da kwai ya fashe wa aciki tayi waje duk suka bita da kallo yayin da Mama ta saki wani arnen tsaki tsanar yarinyar yana k'ara tasiri aranta, duk suka bita da kallo, basu kawo komai aransu ba tunda sunsan yadda ta tsani MD.




Tana tunkaran wajen bugun zuciyar ta yana k'ara yawaita sai da tashafe kusan 5 mint kafin tayi k'arfin halin kama mabud'in k'ofar ta tura a hankali kamar mai jin tsoron wani abu,

Tunda ya dawo salla yake zaune saman doguwar kujera ya jingina bayansa jikin makarin kujeran idanunsa a lumshe bai tantan ce halin dayake ciki ba abinda kawai zai iya ganewa itace ta cika masa zuciya duk inda zai motsa ta tokaresa.


Jin motsin bud'e k'ofar yasa ya maida hankalin sa wajen k'ofar shima bugun zuciyar sa yana kara yawaita bugu ya wani irin kafe k'ofar yay da kallo, a hankali ta shigo bakinta d'auke da siririyar sallama da k'yar ya iya dai daita kansa ya amsa yana dad'a binta da kallo ta d'an kalleshi suka had'a ido bata san sanda ta galla masa harara ba sai ya saki murmushi ya sani sarai takura ta yayi gashi ita kuma babu hak'uri shi yasa.




Bata san tasowar saba sai tsintar sa tayi agabanta ya dafa kafad'anta "babyna me kike sone kika ja kika tsaya anan ki shigo mana?"


Kallo ta bisa dashi mai kama da harara kafin tace "ni ba babyn ka bace, Baffa ke kiranka yace tunda ya shigo baiji motsin ka ba lafiya kuwa?"

"Inafa lafiya an shake min wuya da mugun k'arfi na kasa koda hadiyar yawu" binshi tayi da kallo mai kama da na tausayi dan sam bata gane me yake nufi ba tace "kasha magani me yake damun ka bross?


"Ke ce, ya bata amsa cikin bazata kece damuwa ta, kece tunani na, kece jina, gani na, walwala na, kuma jin dad'i na, Maryam kece komai na" yafad'a cikin muryan daya mugun karyewa ta daga kai tana kallonsa duk yayi wani iri ga damuwa nan kwance acikin idanunshi
" Kazo muje"
"Kije zanzo yanzu"
"Ni dai Baffa yace k'afa na k'afar ka"
"To jira nayi wanka"
Daga haka bai k'ara cewa komai ba ya haye saman sa da gudu.


Cikin 20 mints ya sauka sanye cikin blue jeans da riga ruwan toka kayan sun mugun amsar sa kunsan farin mutum kuma mai kyau duk shigan da yay amsar sa yake.



Tana can yawon kalle kallen ta a falon taji ya rik'o hannunta binshi tai da kallo yadda yayi mata kyau ga wani fitinannen k'amshi dayake yi ma mugun dad'i, har sukaje bakin falon babu wanda yace da d'an uwansa komai sai itace ma da suka zo bakin falon ta warce hannunta daga cikin nasa ta wuce ciki abinta murmushi ya d'an saki kafin ya rufa mata baya


Duk su Baffa suka bisu da kallo yayin da zuciyar haj. Sailuba kamar zaiyi bindiga tsabar fitina da tsanar ganin Maryam daya Kuma mamaye ta Baffa yace "maman malam daga aike kuma sai najiki shiru?"

Rasa me zata cewa Baffa tayi sai ta d'ago ta dubeshi shima ita yake kallo, kafin ta lalubo abin fad'a yay saurin cewa "sanda taje ina wanka"

"To ku gama cin abincin akwai maganar da zamuyi daku duka"

"Nima Baffa akwai abinda nake son fad'a maka tun kafin kaje wajen Inna kuma naso binka sai bansan katafi ba"


Dafa kanta yay yace kar ki damu wannan zuwan ma sai da Inna tai fad'a sosai na rashin ganinki, laifin mamanki ne da tafiya ya tashi sai ta kawo uzurin da dole ake fasa tafiyan dake shiyasa Nassar kawai Inna tafi sani.


Yay maganar yana kallon haj. Sailuba da tayi wani kicin kicin da rai zuciyar ta nayi mata mugun sak'a.


Shima daga haka ya wuce falonsa Ammey ta tashi ta rufa masa baya dake yau ita ce da girki.

Suna barin wajen ta juyo da niyyar zuba abincin dan har ta k'agu taji neman da Baffa yake mata sai karaf idanun ta suka sauka cikin nasa ya wani yi tagumi ya kafe ta da ido, a ranta tace gaskiya wannan mutumin da bansan shi ba babu abinda da zai hana nace maye ne yadda yake da jarababbe kallon nan.

Azahiri Kuma abincin da zata ci ta d'iba a flat ta mik'e zata bar masa wajen, gane hakan da yayi ne yasa yayi saurin dafe hannunta yana binta da wani marai raitaccen kallo "dan Allah kar ki tafi ki barni"



Ya fad'a kamar zai mata kuka, binshi tayi da kallon mamaki, yayin da shi kuma ya k'ara wani marai raice mata sai ta samu kanta da kasa yi masa musu ta koma ta zauna, shima tsulum ya taso daga inda yake ya dawo kusa da ita "lafiya?"

Tace dashi tana kallon yadda yake wani faman shafa cikin sa d'an marairaice mata yayi yace"yunwa nakeji nima"

Abincin da ta zuba zata ci ta tura masa ta d'auki wani flat d'in yay saurin dafe hannunta yana girgiza mata kai ta d'an kafe shi da ido dan neman k'arin bayani "ki bani mana" ya fad'a yana kallonta ta d'an had'e rai shi kuma ya kafa mata naci sai da ta bashi haka kuma shima yabata suka ci suka k'oshi.


Da alama nacin MD ma kawai zai sa yasamu yadda yake so lol🤣🤣🤣🤣🤣






















Maman Islam ce

بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥

2021

NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM



Godiya ta musamman gareku masoyan gaskiya hak'ik'a ina jin dad'in yanda kuke min ina ina sonku domin Allah musamman ma ku d'in nan
MAMAN Jani
Ammeyn Sadik
Antyn muhseen
Ya Rahman
Mare
Jidda
MAMAN Abul
Mom Irchad
Ummey Idris yakub
MAMAN sayyadi
Shamsan
Maman sultan
Umm nawaad
MAMAN Raees
Safiya Sopy
Aisha munir
MAMAN jabir
Xeeyyah
Rashida Muhammad
Afra
Fauzi
Ummukurthum
Aishatu k sani
Zainab autar mm
Jannat Aliyu
Barira Aminu
Hykarianeg 17
Ameenatu
Khadija Muhammad
Hafsat Bala kawu
Maman Arif
Ikilimatu D Baraya
Ummu Abul
Mr maimunatu
Aisha ibarahim ummi
Zainab Muhammad sambo
Juwairiyya Lawal
Maman twins
Mama
Khadija Isa Dari
Duk wanda bai ji sunan sa ba yamin afuwan mutara a text fage ina k'aunar ku nima son so fisabilillahi.



Page 33






Tusio tasa ta goge bakinta kafin ta mik'e " ina zaki?"
Kallon yadda ya wani lafe jikin kujeran dining d'in tayi kafin ta wani tab'a baki tace "ina kaji Baffa yace yana son ganinmu?"

Kai ya d'an dafa alamun ya manta sai kuma ya tashi yace "muje" batareda tace komai ba ta mik'e ta wuce yabi bayanta suka nufi part d'in Baffa.




Tun kafin su shiga suke jiyo b'ab'atun haj. Sailuba sai faman bala i take zubawa Baffa wani mugun tsaki MD ya saki har ga Allah ya mugun tsanar matar nan haka nan, abinda ya dad'a d'aure musu kai shine yadda suka shiga suka tarar tana zuba ruwan tujara shi kuma Baffa yana lallab'a ta yana bata hak'uri, da dai yaga abin yak'i k'arewa ne ya dubi Ammey yace.




"Aminatu dan Allah na rok'eki ke ki hak'ura taje tunda ita ban isa da ita ba baza tayi min alfarma koda sau d'aya na sauke hak'k'in ki ba"



Cikin wani irin yanayin da bazaka tab'a iya fassara shiba Ammey tace "ai dama Baffa ni ba matar gida bace 'yar zaman jiran gida bace da kula da gida ko ba haka ba?
Gaskiya Baffa wannan karon bazan yarda ba nima duk abinda zai faru sai dai ya faru amma nataji wallahi haba dan masifa da bala i shekara da shekaru abu yak'i k'arewa nima wannan karon bazan hak'ura ba Baffa sai dai duk abinda zai faru ya faru.



Nan fa Ammey itama ta bud'e wuta ta rik'a zubar da maganganu masu d'aci kunsan ance mai hak'uri bai iya fushi ba to haka ne yafaru ga haj. Amina yau duk irin yadda Baffa yaso rarrashin ta botsare masa tayi.



Dai dai shigowar su MD da suka gama sauraran komai MD ya kafe Baffa da ido kafin yace "Baffa mai yake faruwa ne nakejin abinda ban tab'a jiba game daku?" ya fad'a yana kallon Ammey cikin yanayin da bai tab'a ganinta aciki ba.



"Kamar yadda aka saba ne Muhammad yauma nayi magana ne akan kujeran hajji danake fitarwa duk shekara, Sailuba bata tab'a bari na bawa Amina tabawa wani nata ba sai sau d'aya kuma ni bansan me take da kujeru har guda goma ba tunda ko ta b'angaren mu nike biyama dangi, to itama mai hak'urin yau ta botsare min tace sam bata amince ba itama na rasa yadda zanyi yanzun"



"Kawai kabawa wanda kake ganin yafi cancanta"

"Baza abawa wanda yafi cancanta d'in ba wallahi ko zata mutu wannan kujeru nawa ne dan haka banga wanda ya isa hanani wannan kujeru ba ehe, idan kuma tak'ama ce naga ubanka ma acan k'auye raba kujerun nan yake kamar babu gobe"




"Ni bana harka da jahilai marasa ilimi dan haka bani da lokacin da k'ik'ancin ki*

"Uwar ka ta kabari itace dak'ik'iya baniba dan is...........kafin ta k'arasa taji wani irin fitinannen zafi ya karad'e fuskar ta ta d'ago a firgice dan ganin wanda yayi mata wannan d'anyen aikin sai da ta wuntsula daga kan kujeran ta ganin Baffa ya kafeta da kallo yana huci, yayin da MD ya mai da kansa k'asa cikin tsantsar b'acin rai da wani irin tsanar haj. Sailuba.



Da wani irin tashin hankali ta bar wajen domin wannan ne karon farko da hakan ya tab'a faruwa iya tarihin rayuwar su dan haka abinda yayi matan yai masifar gigitaya ta sani hakan yana nufin aikin ta yana rawa kenan ai kuwa ya zama dole ta sabunta shiri



Tana barin wajen Baffa ya dubi MD yace "Muhammad na fad'a maka ka fita hanyar Sailuba matar nan jahila ce amma bakaji" da mamaki MD yake duban Baffa to shi mai yace dan kawai yace Baffan yayi abinda yake ganin daidai shine ya shiga sangarta?
Da wani irin fushi MD ya bar wajen yayin da duk suka bishi da kallo sai Maryam ma ta rufa masa baya dan sam bataji dad'in abinda maman nata tayiba.



Ammey ma tashi tayi yayin da Baffa itama ya bita da kallo haka dai duk suka watse kowa zuciya babu dad'i Nassar ne kawai ya zauna ya ci ya koshi abimsa ya kama gabansa ya tafi gidansu boy abokansa.



Sanda Maryam ta isa part d'in MD har ya gark'ame k'ofar da key babu irin bugan da batayi ba yai banza da ita kamar baikita ba.


Haj. Sailuba kuwa tana shiga d'aki a gigice ta nemi wayar ta ta kira haj. Zakiyya kamar wata k'aramar yarinya haka take kuka wurjanjan cikin tsantsar tashin hankali ta kora mata duk abinda yafaru.



Sosai ta rarrasheta tace tunda abin haka ne kawai ta shirya cikin satin nan su wuce India can ne za ayi musu aiki mai kyau sun jima suna tattanawa kafin suyi sallama, sai lokacin ta d'an samu sassauci



Maryam kuwa d'akin ta ta koma cikin damuwa tasani cewa Mama bata kyautaba ko kad'an amma Kuma ita meye laifin ta da zai wani rufe mata k'ofa.


Ganin zaman bazai mata ba kawai ta mik'e ta saka mayafinta da niyyar taje wajen Halima ko zata d'an rage damuwa, daidai bakin get suka had'u da Baffa ya hanata fita dole ta dawo gida cikin k'unci.



MD kuwa tunda da yake babu Wanda ya tab'a zagar masa uwa ido da ido sai yau hakan ya masifar k'ona shi da k'yar yasamu ya rarrashi kanshi ya baro falon shi yasa ya kulle kanshi domin a halin dayake ciki baya buk'atar kusanci ga kowa atare dashi.



Ammey kuwa cikin fushi ta koma d'akin ta ranta a masifar b'ace tasha alwashin bazata k'ara yarda Sailuba ta rik'a juya ta ba tunda babu adalci a lamarin itama ya zama dole ta zage ta kwatar wa kanta yanci.




Haka da ranan mutanen suka kwana kowa zuciya babu dad'i da safe da zasu wuce islamiyya hankalinta yana kan k'ofar sa bata taba alamun ya bud'e k'ofar ba, sai ta tab'e baki a k'ok'arin ta nasan yakice tunanin shi aranta tunda shima fushi yake da kowa na gidan.



Sai dai duk irin yadda taso kore tunaninasa aranta hakan yak'i samu sosai tayi sanyi dan ko k'awayen ta na islamiyya sai da suka gane tana da matsala, sanda suke dawowa daga islamiyya shi kuma ya fito daga d'akin dake lokacin an yi kiran Azhar ne sai da ta d'an razana ganin har ya d'an fad'a daga jiya zuwa yau kacal bata kulashi ba ta d'auke kanta, Nassar ne kawai ya gaida shi, ya bita da kallo har tashiga ciki kafin ya juya ya wuce masallaci.



Koda ya dawo shima cikin gidan ya dawo lokacin har sunyi zaman cin abinci banda haj. Sailuba datake d'akin ta tun juya shima wajen ya tunkaro duk suka bishi da kallo har Baffa wanda yay mamakin ganin shi hakan Ammey tafi kowa shiga damuwar ganinsa a hakan.



K'arasawa yayi ya gaida su kafin shima su Maryam suka gaida shi Ammey ta zubawa kowa nasa abincin amma MD da kanta ta fara bashi dan ta riga tasan halinshi muddun yana cikin damuwa baya iya cin abincin sai dai yayi ta fama da tunani tana cikin bashi ya tsinci muryanta tana fad'in.



"Muhammad yakamata ka gane halin wannan matar ina rok'on ka daga yau komai zai faru kada ka k'ara cewa komai ka barta komai lokaci ne dan haka wata rana sai labari" sosai taci gaba da da tausar shi har ya kammala, itama Maryam ta tubure sai da ta bata itama kafin su bar wajen ta bisu da kallo.



Hannunta da Baffa ya kamo ne yasa ta juyo babu wannan walwalan dayaga tana yima yaranta yanzu, ya d'an murmusa yace "haba maratussaliha dan Allah ki saki ranki tun jiya ake fushi dani na takura da yawa" ya fad'a yana murza hannunta dake cikin nashi.


"Ai Baffa na lura baka Sona ko dan ni ba yar uwarka bace shiyasa kake nuna babanci muraran atsakanin mu"

"Dan Allah ki daina wannan batun Amina ta wallahi nima wani lokacin karkiga yadda abin yake damuna kawai dai tashin hankali ne bana so yasa kikaga ina biye mata"



Amma Baffa shekara ashirin sau d'aya ka tab'a bani kujeran nan ban tab'a cewa dan me ba yanzun ma nagane abin ba na K'are nane dan haka wallahi akan wannan komai zai iya faruwa"


"Dole na baki Amina tunda baki tab'a yi min haka ba sai yau dan haka komai zai faru kece da wannan kujeru na bana" nan dai yaci gaba da tausarta har yasamu ta d'an sakko sukaci abincin tare.



Kai tsaye suna fitowa d'akinta ta dosa dan yau tana buk'atar zuwa gidan su Maryam tana shiga suma suna shigowa yi tayi kamar bata gansuba sai da ya k'araso kusa da ita ya d'an dafa kafad'anta ta juyo ta harareshi.


Murmushi ya d'an saki ya sumbaci goshin ta bai ce komai ya juya ya fice daga d'akin ta raka shi da ido kafin ta juya tacigaba da shirinta.











Taku ce


MAMAN ISLAM

بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥

2021

NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM







Page 34



Cikin atamfa riga da sket kamar ajikinta aka dinka rigar tsabar yadda tayi mata d'as a jikinta, bata wani yi kwalliya mai yawa ba duk kuwa da yadda take da son kwalliyar, mayafin da ya dace da kayan ta dauka ta saka ta saka takalmi mai mugun tsini Allah yayi mata son takalma masu tsini ta fito d'as abinta.




Dukansu juyowa sukayi suka kafeta da ido ba k'aramin kyau tayi ba,kasa daurewa MD yayi sai da ya taso ya d'an matso kusa da ita yace,

"Bakiyi kyau ba" dan hararan sa tayi tace " ai daman badan kai nayi kwalliya na ba bare ka kushe" murmushi yayi tare da mata gwalo domin yasan taji haushi ai kuwa ta k'ufula ta wani had'e rai, ta juya ta wuce d'akin Ammey karab sai a idon mama da ta fito zata fita jitai wani irin fitinannen tashin hankali yakawo mata farmaki da k'arfi tace "ke gidan uwar wa zakije ne" ta fad'a tana kafe Maryam da wani irin kallo.



Ba Maryam ba hatta MD da Nassar sai da suka zabura suka zuba mata ido, ita ko Maryam babu wani shakka ko tsoro tace "haba Mama wallahi har kin bani tsoro irin wannan ihun haka kamar aradu?"


Wani irin tuk'uk'i ne ya tokare haj. Sailuba ta kafe Maryam da wani shegen kallo zuciyar ta yana suya yaushe Maryam ta sami damar fad'a mata magana haka lallai in batayi wasa ba wata rana sai Maryam ta zageta anata haukan tunanin kenan.


Amma azahir cewa tayi "ni nake ihun bab? wai ma tukun me zakiyo ad'akin matar nan bana hanaki mu a'mala dasuba?"



"Hummm mama kenan ai duk randa babu ke dole itace uwata, ko baki tab'a tunanin hakan bane? kuma kadafa ki manta mama ba a raba hanta da jini mun riga mun had'u babu yadda zakiyi tunda ta haifa kin haifa dole ne itama ta sarara agidanna dan Allah mama ki daina irin wannan abun bashi da amfani ko kad'an haba"





Fashewa kawai haj. Sailuba tayi da kuka saboda tsabar tashin hankali da bak'in ciki kasa yi mata magana tayi har ta shige d'akin Ammey tana kallon ta.



MD kuwa wani irin annushuwane ya kamashi sanda Maryam ke fad'awa haj. Sailuba magana wani arnen murmushi kawai yake saki, yana ganin Maryam ta shige d'akin Ammey ya k'arasa kusa da haj. Sailuba yace "hajajju makkatu me kike tunanin zai faru duk ranar da wannan yarinyar tagane cewa ke ba uwarta bace uwar rik'o ce?
Ya zakiji lokacin da tasan cewa mahaifiyar ta kike sawa tanawa cin mutunci da wulak'anci
Me zai faru idan tasan cewa ba dan Allah kike rok'on taba kina rik'on tane saboda wani banzan dalili naki mara amfani?
Hhhhhhhhhhhh kad'an kika gani Sailuba domin Allah baya bacci"




Babu kunya haj. Sailuba ta kuma fashewa da kuka tana kallon MD kafin tace "hummmm Muhammad kenan na maka alk'awarin bazan bar hakan yafaruba sannan kuma ina Mai farin cikin sanar dakai cewa komai ya kusa zuwa k'arshe rayuwar Maryam zaiyi wulakantar da babu wani rayuwa da zata kai tata lalacewa zata bi maza zata yi shaye shaye zata yi sata zata zama abin kwatance da misali na miyagu da munanan halayya"





Sosai gabansa ya fad'i da jin furucin ta domin yasan zata aikata fiye da hakama jiyai hankalinsa yai masifar tashi ya dubeta da tsantsar b'acin rai yace "Allah ya fiki yafi waninki Sailuba kuma duk abinda kike tak'ama dashi insha Allah hakan ki bazai cimma ruwaba"




Wata shegiyar dariya ta saki tace "zaka gani zaka kuma tabbatar muzuba nidakai shege ka fasa" daga haka tayi waje hankali a tashe.


Sosai maganganun ta suka tsaye masa rai sai dai kamar yadda yake tsaye wajen yiwa Maryam Adda a ya zama dole ya k'ara zage damtse.



Maryam kuwa tana shiga d'akin Ammey ta rufeta da fad'a akan maganganun da taji tana sakarwa haj. Sailuba tace mata koba komai matsayin uwa take awajen ta dan haka ta rik'a sanin irin maganan da zata fad'a Mata.


"Nifa Ammey indai akan kune babu abinda zaki fad'a min na fahimta matar da bata da lokacina sai na gantali kullum tana tafe a hanya ita ba kasuwanci ba ba komaiba, ai wallahi duk laifin Baffa ne da yasake mata haka dayawa shiyasa take iskancin ta son Rai"

"Ungo nan Ammey ta yiwa Maryam tace "idan har da gaske kina ganin mutunci na kamar yadda kika fad'a to kada ki sake kinji ko?"



"Naji Ammey, ina Baffa shi nazo nema"
"Lafiya kike neman Baffa?"
Bata b'oyewa Ammeyn komai ba ta fad'a mata tana son bawa baban k'awarta jarine ya fara sana a, sosai hakan yayiwa Ammeyn dad'i arai taji dad'i ya kasance yarta tana da zuciyar tausayi dan haka Ammeyn ce da kanta ta bawa Maryam dubu d'ari tace "gashi idan Kuma bai isaba kimin magana sai na k'ara miki?"

Rungumeta maryam tayi tace "na gode Sosai Ammey na Allah yaja da rai ta sumbaci Ammeyn tayi waje da sauri tana fad'in saina dawo"



Sosai Ammey ke jin dad'in yadda yarinyar ta soma sakewa da ita ta rage wannan d'an banzan yawon dayake sanyata fargaba da damuwa musamman idan haj. Sailuba ta dawo taga bata nan ko zata kwana basata tuhumeta taji inda taje ba.




Tana fita suka gabza wani uban karo da MD ai kuwa taji zafi sosai shima haka duk suka dafe wajen suna kallon juna kafin Maryam ta galla masa harara ta wuce tana sosa goshinta.


Da sauri yasha gabanta ya tsaya yana d'an diddira k'afa irin na shagwab'a yace"ni Allah Allah Allah sai ki bigeni kuma ki wuce babu hak'uri ni sai na rama" yadda yayi maganar dole abin yabata dariya batasan sanda ta saki murmushi ba

Please Login or Register in order to submit comment