Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin yi mata rakiya.






Tayi zaton shi zai jasu, sai kawai taga ya bud'e wajen mai zaman banza ya k'ame abinsa, tura baki tayi tana d'an hararansa ta gefen ido, sarai ya ganta sai ya mai da kansa gefe yana d'an murmushi hakanan yanzu komai tayi burge shi take.






Sai da ta zauna ta sakarwa mai gadi k'aton hon wannan ba sabon abu ba ne awajenea sam indai zatayi tuk'i batayin na nutsuwa tun lokacin data ke a matsayin Maryam ba yanzun da ta zama mero ba lol🤣🤣🤣







Shi kanshi Muhammad sai da yai mamakin ganin yadda ta wani figi motar da masifar gudu bai san sanda ya juyo yana kallonta ba "ke baki da hankali ne?"
Ya fad'a lokacin dayaga ta kusa fad'awa wani d'an rami dake tsakiyar titin data hau tayi wani irin kaucewa ramin
"Princess tsaya" ya da sauri yana dafe kan sa da duka hannayensa.



Babu musu ta nemi waje ta faka dama da biyu ta keyi dan ya amsa banda son banza tana tare dashi d'in zata zauna ta jashi🤣🤣🤣




Canjin wajen zama sukayi ya amshi tuk'in yana fad'in"naga alamun ke kin shirya mutuwa ni kam gaskiya bana so na mutu banyi aure ba"
Ya fad'a cikin barkwanci.




Murmushi kawai tayi bata tanka masa ba, sai ma wayar ta data d'auko ta bud'e data tana chat da friend d'inta tana duba no d boy babu shi kwata kwata a jerin contact d'in ta da gaske yake ya goge.




D'an kallonsa tayi sai akayi sa a shiama ya wago yana kallonta ta gira ya dage mata alamun ya dai?
D'auke kai tayi tana tuna hargagin sa na d'azu akan mama wani lokacin bata cika ganin lafim su ba domin halin mama sai mai hak'uri.






Kusan sau uku tana kamashi yana kallonta kuma duk sanda zasu had'a ido sai yamata alaman yadai?
Sai kawai ta hak'ura bata k'ara kallonsa ba har suka isa sper market d'in da yawanci anan suke siyayya duka 'yan gidansu.






Bayan ya samu waje ya faka ya bud'e ya fito sannan ya zagayo ya bud'e mata bayan tagama gyara mayafinta ta fito a hankali ya Mai da motar ya rufe ya kama hannunta suka fara jerawa cikin wajen.





Duk inda suka gifta sai idanu sun bisu saboda masifar kyawunsu da kuma yadda sukayi macin d'in da mutane sukayi da juna.





Sunzo shiga shi Kuma d boy sun zo fita shi da abokansa ya gansu sai da gabansa ya fad'i ganin ta tare da wannan gwaskan yayan nata ya wani kafesu da ido har suka k'araso inda suke, sai lokacin ma Maryam ta kula da d boy ta d'an saci kallon MD wanda gaba d'aya hankalin sa yake kan wayar sa.





Sai da tagawa d boy hannu ne shi kuma kamar wanda akace ya d'ago sai kawai yabi hannunta da kallo lokacin shima d boy ya d'ago mata tare da wani irin mumushin farin cikin ganin da yayi, kafesu yayi da wani fitinannen kallo zuciyar sa ya hau wani fat fat fat ko ko kad'an bai damuwa da labarin mutane amma ko cikin miliyan sai ya fidda d'an jakin mutumin can, kuma ko da ace shi bai son Maryam wallahi datayi mu 'amala da wancen gwamm ace masa ta mutu ne shi zai fi masa sauk'i.








Sam bata kulla da kallon da yakafe d boy da shi ba amma shi d boy yana ankarewa take jikin sa ya hau rawa ta ina zai manta da wannan basumuden mutumin wanda babu abinda ya ajiye sai mugunta tsantsar ta, kafin Maryam tayi wani motsi d boy ya b'acewa ganinta, ta d'ago kai da zummar yiwa MD magana yadda taga yayi kicin kicin da rai sai da gabanta ya fad'i ta d'auke kai aranta tana tunanin anya wannan bashi da aljanu?







Duk abubuwan data siya shine ya biya k'udin, suka fito daga wajen har lokacin babu annuri atare da shi dan haka taja bakin ta ta tsuke bata k'ara kallon inda yake ba.



Mai makon ya wuce gida kai tsaye taga ya d'auki wani hanya daban amma dake haushin sa take ji bata dube shi ba bare tayi masa tambayar inda zai kaita, har suka isa wani d'an madaidaicin gida mai kyau ya faka motar a k'ofar gidan ya fita ya kwankwasa aka bud'e masa wanda m Bash ya ganine yasashi hangame baki


"Amma dai b'atan hanya kayi ko MD" m Bash ya fad'a yana d'an rik'e baki, harara MD ya zafga masa yace "aini gwanda ni na kawo maka ziyaran kai yaushe rabonka da inda nake? Kuma yanzun ma ba wajenka nazo ba wajen madam nazo tana dai ciki ko?"


" Hum tana ciki mana ina zata bayan gani yawo ai sai ku manyan gwaraye"


Harara ya galla masa batare da yace masa koma mota, har lokacin bata saki ranta ba hannunta kawai ya kama batare da yace mata komai ba ya nufo gidan.





Ido ta d'an waro lokacin da suka tunkaro gidan, yayin da shi kuma ya sakar mata murmushi,itama murmushin tayi masa ta d'an rusuna ta gaida shi kafin ' yace ta wuce ciki,




Kallo MD ya bita dashi har ta shige kafin ya maida hankalin sa kan m Bash da yafe shi da ido'
" Muje man munafiki ka wani zubamin ido kamar zaka cinye ni" murmushi m Bash yayi kafin yace "SON TA KAKE KO?"
"Na fad'a maka"
"Sai ka fad'amin gashi nan ina ganin sa acikin idanunka"



" Hum abokina ban san sanda yarinyar nan tayi tsalle ta daki zuciya naba lokaci guda sonta yamin wani irin kamu wanda har ya fara tab'a wasu daga cikin al'amurana na yau da gone"
"Ka fad'a Mata?"
"Ban fad'a mataba"
"Me yasa?"
" Inajin tsoron kar tace bata sona duk da nasan cewa idan nace ina sonta ko bata so sai an bani ita"




"To kajarraba Mana"
Ta yaya bazan iya ba ina matuk'ar jin tsoron kada tace a a" ya fad'a cikin tsananin damuwa sosai


Sosai m Bash yaji yana jin tausayin abokin nasa dafa kafad'ar sa yayi yace "abokina kada ka bari ya huce" daga haka yaja hannunsa zuwa cikin gidan.


Har Hajara matar m Bash ta tarb'eta duk da cewa bata santa ba amma ta cika mata gabanta da kayan makulashe suna d'an tab'a hira sama sama dake Maryam bata da bak'unta sam.





Kusa da ita MD ya zauna yana kallonta tare da tunanin ta yadda zai fara taranta da maganar musamman idan ya tuna irin kallon da take masa.





Ji ta ta takura da kallon daya takura masa dashi d'agowa tayi ta d'an kalleshi kafin ta kauda kanta tana hararan gefe






Taku ce MAMAN Islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥

2021

NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM







Page 31

Kayan da Hajara ta aje mata ya kalla yaga babu abinda ta tab'a, sai ya d'an dubeta yaga yadda take ta faman hararan gefe ta wani turo baki gaba baisan sanda ya saki murmushi ba, yasa hannu ya d'ago hab'an ya kafeta da wani shegen kallo.


Ganin haka yasa m Bash ya janye matarsa suka bar musu falon, kasa daurewa kallon nasa tayi sai kawai tayi saurin rufe idanunta.


"Waye shi?"
Ta tsinci muryarsa yana mata tambayar da bata san inda ya dosa ba kallonsa take da alaman tambaya a fuskar ta itama?.


"Wanda ya d'auke miki hankali a sper maket?"
Yanzu kam kallon shi take da madaukakin mamaki, yadda yai bala in d'auke mata kai har kawo zuwansu nan batayi tunanin zai kula da hakan ba.


"D boy ne yaron daya dakeni a schl"
"Meye hadinki dashi?"
Sai data d'an K'are Masa kallo, irin kallon dayake binta dashi sai kace wani tsohon maye yasa tayi saurin d'auke kanta.
"Mutunci ne tsakanina dashi?"
Ta amsa tana jan tsaki aranta ganin yadda ya fitineta da kallo.


Juyo da fuskar ta yayi saitin tasa ya k'ura mata ido yana mamakin furucin ta lallai ta sauya ba dan kad'an ba tunda har ta kula d boy wanda yagama wulak'anta ta a bainar jama'a.


"Amma baki da zuciya princess, mutumin da ya gama gurza miki rashin mutuncin a tsakiyar makarantar ku ke yamzun har akwai wani mutunci da zai had'a ki da shi?"

Shiru tayi saboda kallon da yake mata ya masifar ta kurata dan har jikinta ya d'an soma rawa rawa.

"Ni kadaina min wannan kallon" ya tsinci muryanta da yayi can k'asa sosai tana fad'a, kallon ya cigaba da binta dashi yayin da ya dad'a kusanto da fuskarta daf da tashi wanda har suke iya jin saukar numfashin juna.


Take jikinta ya kama rawa ta soma k'ok'arin kwace fuskar ta daga hannunsa, sai dai bai bata damar hakan ba dan ya rik'e ta gam

"Babu abinda yafi min dad'i kamar kallon ki kuma hakan yana saukar min da nutsuwa sosai, dan Allah Kar ki haramtamin kallon fuskar ki yin hakan zai cutar dani sosai.



Yanzu kam gaba d'aya ta ware idanunta akanshi Al 'amarin bross d'in nasu ya fara bata tsoro anya bai samu wani ciwon ba kuwa?
Yadda yake mata d'innan gaskiya ya kamata a bincike shi


"Zaki iya min wani alfarma?"
Ya tambaya yana cigaba da kallon ta kuma har lokacin bai saki fuskar ta ba,
"To kasakar min fuskana sai muyi maganar"
Kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa ya sake tan kamar yadda ta buk'ata, ya kwantar da kansa jikin kujeran da suke kai yana maida numfashi.
Kafe shi tayi da ido aranta tana mamakin yadda yake da zallar kyau da mugun kwarjini.


Tana tsaka da kare masa kallon ne ya ware idonsa akanta yadda take binsa da kallo ya bashi mamaki
"Yadai yarinya? Irin wannan kallo haka ai sai kisa naji kunya" ya fad'a yana d'an gyara zamansa.


Ai kuwa wani irin fitinanniyar kunya ne ya kamata yadda ya kamata dumu dumu tana K'are masa kallo da k'arfi ta runtse idonta gam gam, yasaki wani murmushi ya d'an matsa daf da ita batayi aune ba sai ji tayi ya sakar mata wani kasalallen kiss a idanunta ai da sauri ta yunk'ura zata gudu bisa ga tsausayi sai taci karo da kayan da Hajara ta ajiye mata tun d'azu, saura kad'an ta kife wajen yayi wani irin fisgota ta fad'o jikinsa, wani irin ajiyar zuciya suka sauke atare.


K'ank'ame ta ya kumayi acikin jikinsa yana sauke wani irin numfashi wani irin abu na mai yawo acikin jikinsa ji yai wasu irin hawaye suna k'ok'arin zubo masa wanda bai san dalilin faruwar su ba.


"Zaki aure ni?"
Ta tsinci muryarsa da yayi wani irin mugun sanyi, a wani irin firgice ta d'ago kai tana kallonsa, har lokacin idanunsa a rufe suke gashi ya wani irin cukwaikwauye ta, shikenan hasashen ta ya tabbata yayanta yana da matsala banda haka ina aka tab'a auren JINI D'AYA?



K'ok'arin kwatar kanta ta soma amma ko gezau saima k'ara rik'e ta da yayi
"Ki bari mu fahimci juna dan Allah princess ina son na aureki zaki aure ni?"
Ya kuma k'arasa zancen da tambayarta, jitai hankalin ta yai masifar tashi take maganganu Maryam wanda su yi dad'ewa ya soma dawo mata inda take ce mata
"Da kyar inba sonki wannan bross d'in naku yake ba yadda yai mugun saka miki idonnan da alama dai bazai bawa wani daga waje damar d'auke masa wannan tsaleliyar budurwar ba"

Sanda maryam tai maganar hararan ta tayi tace "da alama kin sami b'acewar tunani name sake banda haka babanmu fa d'aya da kike wannan zancean aman babu tashin zuciya" ta k'arasa tana wani irin kallon Maryam d'in da kuma yin kamar da gaske aman zatayi.

A lokacin murmushi Maryam ta sakar mata tace "ai lokaci zai nuna kuma kinsan lokaci baya k'arya"

"Hmm amma wallahi name sake ban tab'a tunanin kina da tab'in hankali ba sai yau"

"Zaki ce na fad'a miki wallahi kallon SO bross yake miki bana sister ba kuma zaki tabbatar da magana na wata rana"



Ji tai wani irin fad'uwar gaba ya rikito mata lokaci guda ta ware idanunta akanshi tayi wani mugun tureshi da k'arfi ta mik'e daga jikinsa, ta doshi hanyar fita hankali tashe.
Shima ji yai hankalinsa yayi mugun tashi ya bita yana kuranta bata ko juyo ba bare yasa ran zata amsa sai ma wani maganar na Maryam da yake dad'a dawowa kanta a yanzun.

"Ki duba da kyau Ammey batayi shekarun da zata haifi mutum kamar bross ba sai dai ko k'aninta kuma idan kinje gida ki tambayi Mama"
Tsayawa tayi a jikin motar MD ya k'araso yana kallon ta hankali tashe' yayin da Hajara da m Bash ma suka fito domin yadda MD yake kwala kiran Maryam princess princess ba na lafiya bane sai dai duk nacin m Bash wajen son jin abinda ya had'a su babu wanda ya tanka musu

Da k'yar Maryam ta iya d'ago idanunta da sukayi mugun ja tsabar damuwar daya kawo mata farmaki lokaci guda ta kalli Hajara ta daga mata hannu har da murmushin k'arfin hali tayi mata.

Shi ko MD bai iya yace komaiba ya figi motar da mugun k'arfi,duk da yadda hakan ya kad'ata yadda taga yana musu ganganci da rayuwa, amma bata d'ago ba saima mai da kanta datayi k'asa batare data shiryawa hakan ba wani fitinannen kuka ya kwace mata, wani irin wawan burki ya taka wajen wasu bushiyoyo ya faka ya kafeta da ido kafin a hankali ya d'ago da kanta yana kallon yadda take rusgar kuka sai kace wacce aka ce mata Baffa da Ammey ne suka mutu


"Ki rufamin asiri dan Allah ki tausayawa zuciya ta ki daina kukan nan haka"
Kallonsa ta kumayi yayin da kukan ya dad'a kwace mata wanda shi kukan nata yafi komai d'aga masa hankali
"Pls" ya fad'a a hankali amma ina bata saurare shi ba "dan Allah" ya kuma fad'a a hankali yana d'an janta kusa dashi ya soma share mata hawayen da k'yar yasamu tayi shiru amma bata ce masa kanzul ba.




Har sukaje gida bata k'ara yarda ta tanka masa ba duk irin yadda yake rarrashin ta kuwa,
Yana fakawa ta balle murfin motar tayi cikin gida da sauri ko kayan da suka siyo bata tsaya d'auka ba, binta yayi da kallo har ta shige kafin yasaki wani irin ajiyar zuciya mai k'arfin gaske.

Har lokacin Mama bata dawo ba dan k'ofar ta yana nan a yadda ta barshi da zata fita wani irin mugun tsaki tasaki wanda yasa Ammey dake fitowa daga d'akin ta zata shiga kicin, da kallon mamaki Ammey ta bita ganin yadda tayi mugun fita a hayyacin ta.


"Ke lafiyar ki 'kalau ina yayan naki?"
Ammey ta k'arasa tana tambayarta ta fad'awa tayi jikinta tare da fashewa da kukan da yake ta cinta, rik'o ta Ammey ta yi hankali a tashe tajata zuwa d'akin ta zaunar da ita tayi abakin gado ta d'ago kanta tana share mata hawayen kafin tace
"Me yafaru, ko wani abunne ya samu yayan naki?"
Girgiza mata kai Maryam ta yi " to me ya faru?" ta k'ara tambayar ta hankali tashe " Ammey kece kika haifi Muhammad?"
Maryam ta tambaya tana kafe Ammeyn da idanunta da suka kad'a sukayi jajur,

"Me ya faru da har ya daga hankalin ki haka kike min wannan tambayar? ji dan Allah yadda ki koma ji yadda idanunki yadda suka kubura tsabar kuka, bana san haka karki karamin irin haka ji yadda kika tashi hankalin ki nima kika tayar min da nawa?"


Duk abinda yafaru ta kwashe ta fad'a wa Ammey, wani irin sanyi ne ya kwaranya mata arai ta rungumeta tana fad'in "yanzu ke dan wannan abun kike tayar da hankalin ki ai wannan ba abun tada hankali bane Kinga shikenan zai samu mai kula dashi ko"?

Ammey ta d'igawa dogon sharhin ta aya "kamar ya zai samu mai kula dashi ban gane ba Ammey?"
Eh kinsan Abban ku Hassan?"
Na garin su Inna?"

Itama ta tambaye ta
"Yauwa d'iyar albarka shifa ina d'an sa da matarsa ta haifa ta mutu ta barshi?"
"Ba ance yana k'asar waje karatu ba?"
"An fad'i hakane kawai saboda wasu dalilai amma ba kowa bane face Muhammad"
Idanu Maryam ta zaro duka waje tana kallon Ammeyn da madaukakin mamaki
" Hum shine" Ammey ta fad'a tana daga mata kai ganin irin kallon da Maryam take mata.

Nan ta bata labarin MD kamar yadda Baffa ya bata tundaga haihuwar sa da mutuwar mamansa wanda ko abinda ta haifa bata sani ba da yadda Inna ta raune shi har ya girma da yadda matan banansa suka soma azabtar da shi duk da cewa ba gida day'a suke ba har dai MD ya fara wayo ya daina zuwa gidan har zuwa d'auke shi da Baffa yayi har yanzun da yazama wani abun sosai Maryam taji tausayin sa yayi wani irin kamata Allah sarki bawan Allah shi baima tab'a ganin mahaifiyar sa ba ta ayyana aranta "Allah ya jikanta da rahama" ta fad'a tana share guntun hawayen da ya zubo mata
"Amen" Ammey ta fad'a tana shafar kanta kafin tace "maza jekiyi wanka kiyi salla kinga lokacin ta ya shiga Kuma yanzun hajiya zata iya shigowa tunda magriba yayi kar ta ganki anan"

Batace komaiba ta fice a d'akin.






Taku ce

MAMAN ISLAM

بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥

2021

NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM




Page 32


Tana fitowa daga d'akin daidai shigowar haj. Sailuba, idanunta k'yar abakin k'ofar Ammey dan sam bata son had'uwa da kowa wannan shine sa ar aikin ta na yau tana ganin Maryam da bata kula daga inda ta fito ba ranta yai masifar b'aci babu makawa wannan la'a nanniyar yarinyar ta b'ata mata shiri.



Tsawa ta buga mata tace "ke dan ubanki daga ina kike bana hanaki mu a'mala da wadannan matsiyatan ba?"
Da kallon mamaki Maryam ta bi mama wadda tun kafin ta kai karshen maganar ta ta gano kuskurenta tayi saurin fuskewa dan kar ta gano ta, amma duk da haka sai da Maryam ta hango tsantsar tashin hankali atareda maman tata.




"Lafiyan ki kalau mama?"
Kallonta mama ta d'an yi cikin alamun rashin gaskiya kafin ta wuce b'angaren ta cikin tsantsar tashin hankali.



Tana shiga bata bi ta maganar sallar magriba da ake ta kwad'awa a masallaci ba ta zari waya jikinta har rawa yake ta dannawa haj. Zakiyya wacce ita shigarta nata gidan kenan kira da mugun mamaki ta d'aga kiran tana cewa.


" Ya akayine k'awata ko zama banyi ba sai ga kiranki?"

" Na mutu zakiyya, shikenan kuma nawa ya K'are na shiga uku zakiyya da wannan la'ananniyar yarinyar na fara karo wacce boka yace har gwanda naga kowa dana fara ganinta?"
Ta fad'a cikin rushewa da wani fitinannen kuka cikin tashin hankali.


Ita kanta wani irin fad'uwar gaba ne ya rufeto mata agigice tace
"Ke kuwa Sailuba wanne gangancinne yasa kika bari kuka had'u?"


"Cikin kuka tace wallahi nima bansan zamu had'u da itaba kawai ina shigowa mukayi kicib'us"


"Allah yasa bakice zakiyi mata fad'a ba dan gudun kar kija mana matsalar kuma"



"Nayi, sai dai kafin na dire na gano kuskurena nayi saurin fuskewa"
Nan dai suka fara tsara yadda zasu sabunta shirin su tunda wannan ya ruguje.





Ganin yadda maman ta d'aga hankalinta har tayi hanyar d'akin sai kuma ta fasa aranta tace ai kina da kud'i zaki sha kan matsalar, ta juya ta shige d'akin ta batare da wani damuwa ba ta shiga wanka a gurguje tayi wanka ta fito ta kabbara salla bayan ta idar ta d'an yi kwalliya sama sama ta fice, duk suna wajen cin abinci kamshinta ne ya sanar dasu zuwanta, duk suka bita da kallo babu MD awajen duk sai taji babu dad'i dan tun d'azu take ta faman juya labarin da Ammey ta bata nasa tana da tausayi duk da kasancewar ba wai yasha wani wuya na azo agani ba amma rashin mahaifiya ba d'an k'aramin gib'i bane ga rayuwar yaro.



Tana shirin zama Baffa ya dakatar da ita yace taje ta dubo yayanta ko lafiya dan tunda ya shigo bai ji motsin saba, jitai gabanta ya wani buga da k'arfi take abinda ya faru agidan m Bash ya dawo mata sai dai bata da damar yiwa Baffa musu hakan yasa ta fasa zaman ta juya kamar kazar da kwai ya fashe wa aciki tayi waje duk suka bita da kallo yayin da Mama ta saki wani arnen tsaki tsanar yarinyar yana k'ara tasiri aranta, duk suka bita da kallo, basu kawo komai aransu ba tunda sunsan yadda ta tsani MD.




Tana tunkaran wajen bugun zuciyar ta yana k'ara yawaita sai da tashafe kusan 5 mint kafin tayi k'arfin halin kama mabud'in k'ofar ta tura a hankali kamar mai jin tsoron wani abu,

Tunda ya dawo salla yake zaune saman doguwar kujera ya jingina bayansa jikin makarin kujeran idanunsa a lumshe bai tantan ce halin dayake ciki ba abinda kawai zai iya ganewa itace ta cika masa zuciya duk inda zai motsa ta tokaresa.


Jin motsin bud'e k'ofar yasa ya maida hankalin sa wajen k'ofar shima bugun zuciyar sa yana kara yawaita bugu ya wani irin kafe k'ofar yay da kallo, a hankali ta shigo bakinta d'auke da siririyar sallama da k'yar ya iya dai daita kansa ya amsa yana dad'a binta da kallo ta d'an kalleshi suka had'a ido bata san sanda ta galla masa harara ba sai ya saki murmushi ya sani sarai takura ta yayi gashi ita kuma babu hak'uri shi yasa.




Bata san tasowar saba sai tsintar sa tayi agabanta ya dafa kafad'anta "babyna me kike sone kika ja kika tsaya anan ki shigo mana?"


Kallo ta bisa dashi mai kama da harara kafin tace "ni ba babyn ka bace, Baffa ke kiranka yace tunda ya shigo baiji motsin ka ba lafiya kuwa?"

"Inafa lafiya an shake min wuya da mugun k'arfi na kasa koda hadiyar yawu" binshi tayi da kallo mai kama da na tausayi dan sam bata gane me yake nufi ba tace "kasha magani me yake damun ka bross?


"Ke ce, ya bata amsa cikin bazata kece damuwa ta, kece tunani na, kece jina, gani na, walwala na, kuma jin dad'i na, Maryam kece komai na" yafad'a cikin muryan daya mugun karyewa ta daga kai tana kallonsa duk yayi wani iri ga damuwa nan kwance acikin idanunshi
" Kazo muje"
"Kije zanzo yanzu"
"Ni dai Baffa yace k'afa na k'afar ka"
"To jira nayi wanka"
Daga haka bai k'ara cewa komai ba ya haye saman sa da gudu.


Cikin 20 mints ya sauka sanye cikin blue jeans da riga ruwan toka kayan sun mugun amsar sa kunsan farin mutum kuma mai kyau duk shigan da yay amsar sa yake.



Tana can yawon kalle kallen ta a falon taji ya rik'o hannunta binshi tai da kallo yadda yayi mata kyau ga wani fitinannen k'amshi dayake yi ma mugun dad'i, har sukaje bakin falon babu wanda yace da d'an uwansa komai sai itace ma da suka zo bakin falon ta warce hannunta daga cikin nasa ta wuce ciki abinta murmushi ya d'an saki kafin ya rufa mata baya


Duk su Baffa suka bisu da kallo yayin da zuciyar haj. Sailuba kamar zaiyi bindiga tsabar fitina da tsanar ganin Maryam daya Kuma mamaye ta Baffa yace "maman malam daga aike kuma sai najiki shiru?"

Rasa me zata cewa Baffa tayi sai ta d'ago ta dubeshi shima ita yake kallo, kafin ta lalubo abin fad'a yay saurin cewa "sanda taje ina wanka"

"To ku gama cin abincin akwai maganar da zamuyi daku duka"

"Nima Baffa akwai abinda nake son fad'a maka tun kafin kaje wajen Inna kuma naso binka sai bansan katafi ba"


Dafa kanta yay yace kar ki damu wannan zuwan ma sai da Inna tai fad'a sosai na rashin ganinki, laifin mamanki ne da tafiya ya tashi sai ta kawo uzurin da dole ake fasa tafiyan dake shiyasa Nassar kawai Inna tafi sani.


Yay maganar yana kallon haj. Sailuba da tayi wani kicin kicin da rai zuciyar ta nayi mata mugun sak'a.


Shima daga haka ya wuce falonsa Ammey ta tashi ta rufa masa baya dake yau ita ce da girki.

Suna barin wajen ta juyo da niyyar zuba abincin dan har ta k'agu taji neman da Baffa yake mata sai karaf idanun ta suka sauka cikin nasa ya wani yi tagumi ya kafe ta da ido, a ranta tace gaskiya wannan mutumin da bansan shi ba babu abinda da zai hana nace maye ne yadda yake da jarababbe kallon nan.

Azahiri Kuma abincin da zata ci ta d'iba a flat ta mik'e zata bar masa wajen, gane hakan da yayi ne yasa yayi saurin dafe hannunta yana binta da wani marai raitaccen kallo "dan Allah kar ki tafi ki barni"



Ya fad'a kamar zai mata kuka, binshi tayi da kallon mamaki, yayin

Please Login or Register in order to submit comment