Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

momy,,,, da sauri ta fito dan kada momy tace ta ɓata mata lokaci,,,

Farlo ta samu momy,,,, tana mata sannu da zuwa,,, bayan sun gaisa ne, momy tace miya sameki wai?"",,,, raihana tace ba komai,,, momy cikin sakin fuska tace aina na ɗauka an samu ƙaruwa ne,,, cikin jin kunya raihana ta duƙar da kanta ƙasa tare da cewa gajiya ce kawai,,,, momy haba nidai koda nace,,,,, raihana tayi shiru,,, ita kuma momy jakarta ta buɗe ta ɗauka maganin tsarin iyali tace ma raihana anshi wannan,,,,,

Raihana ta ɗago kanta, tare da miƙa duka hannayenta biyu cikin girmamawa, momy ta bata sannan tace kinsan ko miye ne?"",,, raihana tace A, a, kuma bata san komiye ba,,,,, momy tace to maganin gajiya ne kiyi ta mafani dashi zaki samu sauƙi kinji raihana tace to,,,,

Momy taci gaba da cewa kuma kada ki bari umar ya gani dan wayau zaiyi maki ya shanye kinji ko?"",, raihana tace to, momy tace duk dare zakisha ɗaya kinji, ta nuna mata yanda zatayi amfani dashi, sannan tace idan ya ƙare zata kawo mata wani, raihana tayi godiya momy tace jeki ɓoye abunki,,, da sauri raihana taje ta boye sannan ta dawo,,, bayan ta dawo ne, momy tayi mata sai anjima ta tafi,,,,,

Momy kuwa tana fita ta kece da dariya, tace sakara,,, da gani dai wannan daɗo ce, kifin rijiya,,, bazata kawo ma ranta maganin hana ɗaukar ciki bane,,, ba,asan komai ba, sai wahalar rayuwa,,, ai babu ke ba aihuwa a gidan ɗana,, niko nace ai kinxo a makare,,,

raihana kuma kicin ta koma bayan ta gama abincinta ta zuba taxo taci,,,, tana gamawa taje tayi sallahr la"asar,,, wayarta ta ɗauka dan kiran ummanta, ta kirata suka gaisa,, raihana tace umma yaushe zakixo gidan ɗiyarki ne wai?"",,,, umma tace haba keko?",,, nidai bazan zo ba, amma su gwaggo zasu zo ita da bushira dasu fiddausi wato "ya"yan gwaggo, raihana tace ke kuma fa?"",,,, umma tace zanzo amma ba yanxun ba,,, haka dai sukayi firarsu daga baya sukai sallama,,,,

Har bayan isha"i, faruk bai dawo ba, raihana kuma bata kirashi ba,,, wai ita fushi take ya tafi baiyi mata ban kwana ba,,, dan ta saba idan zai fita ko tana bacci zai tasheta yace mata zaije wuri kaza,,,, tayi mashi fatan dawowa lafiya, niko nace keko raihana baki san yau da gobe ba?"",,,,

ta gaji da zaman jiran dawowar shi, ta tashi ta nufi ɗaki,,,, harta kwanta ta tuna batasha maganin da momy ta kawo mata ba,,, saukowa tayi daga saman gado ta shiga toilet, ta daɗe sosai sannan ta fito, tana fitowa farlo ta nufa komi tayi oho, bayan ta dawo ne, ta zauna a gefen gado,,,,,

zuwa wani lokaci ta tashi taje ta ɗauko maganin inda ta ajiye,, sannan ta ɗauki ruwa , ta fasa ruwan tasha a bakinta bata haɗiya ba ta riƙesu,,, tana ɓallar maganin faruk ya shigo,,, da sauri ta miƙe tsaye, ta ɓoye maganin a hannunta, niko nace waya ga marowaci,,,,

yanda tayi abunne yasa faruk yace miye?"",,,,, har yanxun bata haɗiye ruwanba, da su take magana irin mummmm,,, alamar dai akwai wani abu a bakin mutum,,, dariya yayi sannan yace mi kike ci ne?""" aciciya, a daidai lokacin daya matsa kusa da ita ya latsa mata cikinta, tayi dariya, har yanxun ruwan yana cikin bakinta,,,,,

shima dariya ya sakeyi sannan yace wai mi kike ci ke?"",,,, raihana ta girgiza kanta tare daja da baya,, dan samun inda zata yada maganin,,,, shi kuma ganin tana ja baya yasa shima ya fara binta, tana matsawa shima yana matsawa, harta isa wurin kusurwar bango ta maida hannunta ta baya ta ɓoye,,,,,,, kuma har yanxun baƙi ta haɗiye ruwan ta mashi magana,,,,,

faruk murmushi yayi yana cewa da Allah wai miye kike ɓoyewa,?"",,, kai ta girgiza alamar ba komai,,, yace to muga hannunki, miƙo mashi hannu ɗaya tayi ya riƙe sannan ya sinsina shi, murmushi tayi, shima murmushin sannan ya riƙe hannun yace muga ɗayan shima,,,, da sauri ta matse maganin a cikin cinyoyinta,,,, ta miƙa mashi ɗayan hannu, shima yanda yayi ma wancan haka yayi ma wannan , jawota yayi daga inda take rakuɓe,,, tana matsawo maganin ya faɗo,,, faruk yace muga abinda kike ɓoyewa, sai yanxun ta haɗe ruwan bakinta tana cewa Allah kada kasha man abu,,,,,

Duƙawa yayi ya ɗauki maganin,,,, gaban faruk ya faɗi, lokaci guda kuma yanayinshi ya canja,,,, kallon raihana yayi lokaci guda kuma launin idonshi ya canja,,,, wani matattacen murmushi wanda lokaci guda idonshi ya kawo hawaye, sannan yace innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, ke kuma da wannan salon kika zo?"",,,,,, a daidai lokacin da hawayen suka gangaro daga idonshi,,,,

Ganin faruk yana kuka yasa raihana matsawa kusa dashi tana cewa miye?"",,,, wani irin kallo yayi mata wanda yasa ta sakin fitsarin tsaye,,,,, dan tunda take bata taɓa ganin faruk a irin wannan yanayin ba,,,, lokaci guda kuma jikinta ya fara kyarma,,,,, tsaki faruk yayi sannan yabar ɗakin,,, yana fita da gudu raihana taje ta rufe ƙofar ɗakin sannan ta dawo ta shige toilet ta cire kayan jikinta,

dawowa tayi ta gyara wurin taje tayi wanka ta wanke kayan data cire,,, bayan ta fito ta shirya, kasa fita tayi dan gaba ɗaya tsoron faruk ya kamata,,, zama tayi a gefen gado komi ta tuna Oho,,,,,, sai kawai ta kama kuka,,,,

shi kuma faruk yana fita ɗakinshi ya tafi,,,, yana zuwa ajiye maganin yayi,,,, ya shiga wanka, bayan ya fito, zama yayi a gefen gado,,, murmushi yayi sannan yace a bayyane gaskiya yarinya baki more ma faruk ba,,,,,, nine na more maki,,,,,

Raihana saida tasha kukanta ta gaji,,,,, sannan ta ɗauko wayarta ta fara kiran faruk, lokacin daya ga,,,,, kiran ta,,,,,, tsaki yayi sannan yace ai na gama dake , na goge babinki a zuciyata,,,,,,,

wani kiran ne,,,, ya sake shigowa,,,,,, bai ɗauka ba, haka tayi ta kiranshi amma yaƙi ɗauka,,,, ganin bai ɗauki wayar ba,,,, yasa ta tashi cikin dakiya ta nufi ɗakinshi,,,,,

sallama tayi ta shiga,,,,, amsa sallama itace ta zama wajibi, dan haka daga ita bai sake magana ba,,, raihana tace zaka sha lipton?"",,,, kallonta yayi amma baiyi magana ba,,,,,, yanda yake kallonta yasa taji gabanta na faɗuwa,,,,,,,, cikin tsoro ta dake tayi wurinshi,,, ta kusa hawa saman gadon yasa ƙafarshi ya halbata ta faɗi ƙasa,,,,,, cikin fushi raihana tace wannan wane irin wasa ne?"",,,,, yace baki san na isa mugun wasa ba saina fasa maki da bindiga, a daidai lokacin daya ɗauko bindiga daya ajiye a gefenshi,,,,,

da sauri raihana ta duƙe ta riƙe kanta da hannuwanta, ta rufe idonta ,tana jiran ta ina zataji saukar harsashi?"",,,,, jin bai harbeta yasa ta buɗe idonta tana kallonshi,,,,, faruk yace tashi ki fita,,, raihana tace wai mi nayi maka ne?"",,,,, tsawa ya daka mata tare da maimata abinda ya faɗa,,,,, kuka raihana ta fara, faruk yace shi kike so kiyi ne?"",,,, raihana tayi shiru,,,, yace tashi ki fita nace,,, bansan ganin ki kwata kwata,,,, ki fita tun kafin inbi ta kanki in wuce,,,,, cikin kuka raihana tace zan fita,,, amma saika faɗa man abinda nayi maka,,

rainin hankali wato bata ma san abinda tayi ba,,, faruk ya faɗa a ranshi,,,, miƙewa yaje inda take tsaye ya yayimeta saida ya fitar da ita farlo sannan ya koma ya rufe ɗakinshi,,,, miƙewa tayi ta koma ɗaki,,,,

haka ta kwanta cikin ɓacin rai, dan ita a haƙiƙanin gaskiya bata san komi yasa faruk yake fushi ba,,,, saida tayi kukanta ta gaji sannan ta kwanta bacci......

***

*A*bu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba,,, dan kwata kwata yanxun faruk ya daina yadda yama haɗu da raihana,,,, kuma ko abinci yanda ta kawoshi haka zatazo ta ɗauka,,,, kuma idan zaiyi tafiya yama daina faɗa mata,,, zaiyi tafiyarshi,,, yayi iyakar kwanakinshi ya dawo,,, kuma idan ya dawo harya gama zaman shi raihana bata ganin shi,,,,,,,, waya ma idan ta kira baya ɗauka,,,, kuma idan ta tura mashi saƙo dashi da bbu haka ya ɗauka, dan baida lokacin karantawa ma,,,,

Dan haka ta gaji da zaman gidan duk yayi mata babu daɗi,, saboda tana ta ganin abinda bata saba gani ba,,,,,, magani kuwa idan momy ta kawo saida ta ajiye,,, tunda taga maganin ne ya haɗasu faɗa da faruk,,, duk raihana ta rame ga wahalar ciki,, ga kulawar da take samu yanxun babu ita,,, abinci kuwa kamar jaka haka takeci,,,,, amma babu kama bbu alama,,,,,

wayarta dake ringing yasa ta miƙewa,,,,,taje inda ta ajiyeta ta ɗauka,,,, ganin farida ne yasa tayi murmushi,,,,, bayan ta ɗauka suka gaisa,,, farida tace mata gani nan zuwa gidanki , raihana tace to Allah yasa kuxo lafiya,,,,, farida tace amin,,,,,,,

Raihana har tayi bacci ta farka bataji zuwan farida ba, don haka ta kirata, farida tace yi haƙuri gani nan insha Allah,,,, raihana tace to,,,,,

suna gama wayarne,,,,, ta tashi ta fito farlo,,,,, bata daɗe da zama ba, farida tayi mata waya, taxo, tashi tayi ta fita dan tarota, tana zuwa ta rungume farida,,,,, tana dariya,,,,, haka suka rantafo suka nufo ciki dukansu sai dariya suke su biyu,,,,

bayan sun shigo a farlo suka yada zango, suna gaisawa, dan raihana kwata kwata batasan faruk yana gidan ba,,,, shi kuma tun lokacin da raihana ta taro farida saman idonshi , yana kallonsu, da suka shigo farlo kuma duk maganar da suke kamar a gabanshi yana jinsu,,,,

raihana tace farida dama ina san kixo wallahi,,,, farida tace miye?"",,,,,, raihana tace muje ɗaki, farida tace ki muyi zamanmu anan mana, raihana ta matsa kusa da farida ta fashe da kuka,,,, faruk dake saurarensu gabanshi ya faɗi,, yace kardai yarinyar nan wani zata faɗa ma halin da muke ciki?"",,,,,

Bai gama tunanin ba yaji raihana tana cewa nidai banda lafiya,,,,, farida tace miya sameki?"",,,,, raihana cikin kuka tace "yan hanjina suke tsintsinkewa cikin tashin hankali farida tace wane irin "yan hanji kuma?"",,,, faruk dake sauraransu yayi tsaki sannan yace kaji wani shirme kuma?"",,,,,

Farida tace ya kike ji ne?"",,,, cikin kuka raihana tace cikina yake man yawo,,, farida tayi dariya sannan tace banza amosanin ciki ne,,,,, dan itama farida batasan ciki ba,,,, tunda bata haihu ba, ta taɓa ɓari so ɗaya, kuma har yanxun bata sake samun ciki ba,,,,, faruk saki ya sakeyi sannan kace kaji wata yarinta kuma,,,,,, banda sakarcin raihan farida likita ce?"",,,,,,

farida tace nidai lokacin da nayi irin wannan ciwon cikin likita cewa yayi in daina aiki sosai , wai ke ya kike jin abun ne?"",,, ita raihana bata san ciki ne ba,,,, ita kuma farida bata fahimce abun ba, dan haka gaba ɗaya sai shirme suke,,,, tsaki faruk ya sake yi sannan yace kaji wani hauka kuma,,,, wai ta faɗa mata yanda take ji,,,, tsaki ya sakeyi,,,,,,,

Maganar raihana yaji cikin kuka tana cewa,,,,, nidai ina yawan bacci, wani lokaci kuma inacin abinci sosai,,,, sai cikina,,, wana man wani wuntsil wuntsil,,, shidai baiji ƙarshen firarsu ba, saboda wayarshi tayi ringing ya ɗauka,,,,,

farida tace ke wannan ciwo naki saidai kije kiga likita, daga nan suka canja fira,,, wani faruk yajisu wani bayaji,, wani yayi dariya wani yayi tsaki,,, haka dai sukasha firarsu,,,, sosai, sannan farida ta tashi tafiya,,,,, raihana ta shiga, ta haɗo mata talatin da tara ta arziƙi,,,,,, tayi mata rakiya har wurin motarta,, saida ta tafi sannan ta dawo .....

tana dawowa, ɗaki ta wuce,,,,, tana shiga saman gado tahau ta kwanta, sannan ta ɗauki wayarta, ta fara kiran ƙawarta zulaihat, bata ɗauka ba,,,,,,

Dawowa tayi farlo ta zauna tayi jigum dan gaba ɗaya gidan ya daina mata daɗi,,,,,, wayarta ta duba dan ganin mai kiranta, zulaihat ce,,,,,, ɗauka tayi suka gaisa tace kwana biyu, zulaihat tace ai dama nasan saina aihu zaki zo,,, raihana tace insha Allah gobe zanzo,,,, niko nace kaji ƙarfin hali,,, ashe bani ba, har faruk yaji, to sai nazo insha Allah ta kashe wayarta,,,,,,

faruk tashi yayi sannan ya fito,,,, raihana dake zaune da sauri ta tashi zata ruga ya riƙota,,, rufe idanuwanta tayi da sauri tana ihu,,,,,, daɗe mafa baki yayi sannan yace ina zaki?"",,,,, buɗe idon tayi a hankali sannan tayi ajiyar zuciya, dan ita bata ɗauka yana nan ba,,,,,

Ƙara ajiya ajiyar zuciya tayi sannan ta gyara tsayuwarta, cikin shasheka tace ai dama nasan kaine,,,,, tana sake nishi kuma ƙarya take tsorata tayi,,,, ɗaure fuska faruk yayi sannan yace miya sameki ne?"",,,, har harxun nishi takeyi sannan tace ba komai,,, mika gani ne?"",,,,,,,, kallonta yayi sosai sannan yayi tsaki,,,, yace jeki shirya inkaiki asibiti,,,,,, raihana tace ka daina fushin ne?,,,, baiyi nagana ba,,,,, ya koma ɗaki,,,,,,,,,,,

Yana komawa ɗaki,,,, yace kila maganin da kike ɗirkawa kanki ne yasa maki matsala,,,,,,

Ita kuma tana zuwa ba ɓata lokaci ta shirya,,,, ta fito, ɗakinshi ta shiga, tace ta shirya, kallonta yayi sannan yace *KHADIJA* wato ainahin sunanta ya kira,,,, raihana tace na"am,,,, yace zo ,,, matsawa tayi kusa dashi,,, hannunta ya riƙo ya zaunar da ita kusa dashi, sannan ya dafa ƙirjinta yana halɓawa da alama tana cikin tsoro,,,, kallonta yayi ta ɗauke kanta,,,,, da hannunshi ya maido fuskarta tana fuskantar tashi yaci gaba da kallonta,,,,,,

raihana tace don Allah ka daina man haka wani iri yake man,,,,, faruk yace in tambayeki?"",,,,, raihana tace Eh, yace kada ki boye man komai,, tsakanin ki da Allah waye ya baki wannan maganin ?"",,,, raihana tace wannan magani maganin miye don Allah, wani kallo faruk yayi mata,,, sannan yace ni ban tambayeki ba,,, kina tambayana?"",,,, raihana tace idan har ka yadda dani maganin rashin lafiya ne,,,, faruk yace miya sameki ne?"",,,, raihana tace kawai ina yawan bacci ne,,,, yace to wane likita ya baki shi?"",,, raihana tace likita na ne,,,,, faruk yace waye shi?"",, raihana tayi shiru,,,

Juyawa bayanshi ya ɗauko "yar ƙaramar bindiga ya ɗora a saman kanta,,,,, zufa ta keto mata,,,, hawaye suka cika mata ido,,,, ta haɗiye miyan bakinta kamar ta haɗiye kunama,,,,,,,,,, tana kallon faruk jikinta sai karma yake,,,, faruk yace ko ki faɗa man wanda ya baki ko in fasa maki kai,,,, hannun raihana yana karma takai hannunta zata taɓa faruk yaja baya yana zaro mata ido yace ki faɗa man idan ba haka ba,,,,, anan zan fasa kanki inje inba karnuka su cinyeki kowa ya huta,,,,,,

kuka raihana ta fara sosai,,,, faruk yace kuka na tambayeki ne?"",,,, cikin kuka raihana tace don Allah faɗa man maganin miye,,,,sai in faɗa maka,,,, yace idan kika sake cewa maganin miye saina zaro maƙoshi na faɗa maki,,,,, raihana sai kuka takeyi ta kasa magana,,, dan bata san ko maganin miye ba,,, idan tace mamanshi ta kawo bata san yanda zai ɗauki maganar ba,,,,, dan taga ya ɗauki zafi akan maganin sosai,,,,,

Faruk yace inajinki,,,,,, sallamar da sukaji a farlo ne, yasa raihana ta yage baki tayi wani irin ihu tana cewa a kawo mata ɗauki,,,,...............

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment