Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

SOYAYYA GAMON JINI 1

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Waziri Aku

Majidu ƙasaitaccen attajiri ne a cikin Birnin Hurassana. Yana da dukiya mai yawa, da bayi da kuyangi, farare da baƙaƙe. Sai da ya shekara sittin sa'annan Allah Mai Girma da Ɗaukaka ya nufe shi da ganin tsatsonsa, matarsa ta haifa masa ɗa namiji, ya sa masa suna Alisharu.

Yaro ya girma cikin kyakkyawar sura da fuska ma'abuciyar haske tamkar wata a daren cikarsa, ya tashi cikin ladabi da biyayya, ya san fannonin ilimi iri iri. Lokacin da ya isa mutum, sai mahaifinsa ya kwanta ciwon ajali. Da Majidu ya ga ciwonsa ba na tashi ba ne, sai ya kira ɗansa ya ce, "Ya ɗana, ina ganin ciwon nan nawa ba na tashi ba ne, ina so in yi maka wasiyya. Ka saurari abin da zan gaya maka da kunnen basira, idan ka yi amfani da shi ko bayan raina ba za ka tozarta ba."

Alisharu ya matso kusa ga mahaifinsa, hawaye na zuba daga idanunsa, ya ce, "Ya mahaifina, mecece wasiyyarka zuwa gare ni?"

Majidu ya ce, "Ya ɗana, ina horon ka da ka yi hankali da mutane, kada ka ba su amana. Ka guji aikata duk wani abu mara kyau. Kada ka yi tarayya da mutanen banza. Domin kuwa zama da mutumin banza, tamkar zama a maƙera ne, ko wutarta ba ta ƙona ka ba, hayaƙinta zai dame ka. Don haka ka zama mai dogaro da kanka, kada ka kuskura ka dogara ga wani. Wannan ita ce wasiyyata zuwa gare ka." Alisharu ya ce, "Na ji na ɗauka, ya mahaifina. Bayan wannan me kuma ya kamata in yi?"

"Ka zama mai kyautatawa ga kowa," mahaifinsa ya amsa masa, "kodayaushe ka kasance mai tausayi da jinƙai ga mutane. Ka yawaita alheri, domin shi alheri danƙo ne ba ya faɗuwa ƙasa banza."

"Na ji na karɓa, zan kuwa yi aiki da dukkan abin nan da ka gaya mini. Akwai sauran wani abu kuma da ya kamata in yi?"

Majidu ya ce, "Ka riƙa tuna Allah a kowane lokaci, shi ma sai ya tuna ka. Ka zama mai tattalin dukiyarka, kada ka yi almubazzaranci. Idan ka banzatar da dukiyarka, to kuwa za ka koma cizon hannu. Domin za ka zama mafi ƙasƙanci daga cikin mutane. Ka sani cewa, dukiya ita ce darajar ɗan Adam a wannan zamani, kamar yadda aka faɗa a cikin wannan waƙa:

Dukiya in ta yi ƙarewa,
Abokaina ka watsewa.

Dukiya in ta yi juyowa,
Abokaina ka dawowa.

Aboki kan zamo maƙiyi,
In babu tudu na dafawa

Maƙiyinka ya zan abokinka,
In ga harka ta damawa.

"Sai kuma me?" Alisharu ya tambayi mahaifinsa.

"Ya ɗana," Majidu ya ce, "kada ka aikata aiki face ka nemi shawara daga waɗanda suka fi ka shekaru. Kada ka biye wa son zuciya wajen aikata kowane irin aiki. Ka zama mai tausayin na ƙasa gare ka, sai na samanka su ji tausayinka. Kada ka ci mutuncin kowa, duk wanda ya ci mutuncinka ka ƙyale shi da Allah. Kada ka sha giya, domin ita ce tushen afkawa cikin masifu duka. Takan kawar da hankalin mai hankali, ya aikata dukkan abin da zuciyarsa ta riya masa. Wannan ita ce wasiyyata zuwa gare ka, ka kiyaye da waɗannan abubuwa da na hore ka da su. Allah ya yi maka albarka." Daga nan sai ya yi wata doguwar shaƙuwa, ya suma.

Yayin da ya farfado sai ya nemi gafara daga Allah, ya yi kalmar shahada, ya ce ga garinku nan. Alisharu ya yi kuka don baƙin cikin mutuwar mahaifinsa, ya roƙar masa gafarar Allah Maɗaukakin Sarki. Mutane suka hallara, manyansu da ƙanana, aka yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, aka rufe shi a cikin kabari. Aka sauke Alƙur'ani mai tsarki a wajen kabarin nan. Aka yi addu'o'i, sa'annan aka rubuta waɗannan baitoci bisa ga kabarin:

Ƙasa ce farkon ɗan Adam,
Daga nan aka yi maka rayuwa.

Ilimin kalmomi ka sani,
Ka furta zance mai yawa.

Yanzu ka mutu ka koma ƙasa,
Ka bar mu da tsantsar damuwa.

Alisharu ya zauna cikin tsananin damuwa da baƙin cikin mutuwar mahaifinsa, ba a daɗe ba kuma sai mahaifiyarsa ta mutu. Ya aikata mata tamkar yadda ya aikata wa mahaifinsa. Bayan an gama zaman makoki, sai ya ci gaba da zuwa kasuwa, ya buɗe rumfar mahaifinsa, yana saye yana sayarwa, bai kula da kowa ba, kamar dai yadda mahaifinsa ya yi masa wasiyya.

Alisharu bai gushe ba bisa ga wasiyyar mahaifinsa tsawon shekara guda. Ana nan sai ya yi abota da wasu samari 'yan iska, waɗanda ba su ganin kan kowa da gashi. Sannu a hankali ya riƙa biye wa shawarwarinsu, suka karkatar da shi daga ɗabi'u na ƙwarai. Da ma an ce, zama da maɗaukin kanwa shi ke sa farin kai. Sai ya soma kwankwaɗar giya dare da rana, ya riƙa cewa a cikin ransa, '"Dubi duk tarin dukiyar nan da mahaifina ya bar mini, shin idan ban more wa rayuwata ba na mutu, wa zan bar wa ita?"

Sai ya shiga cikin dukiya yana ta bundun-bundum, ya riƙa tara samari 'yan birni yana kashe musu gara suna kwasa a fayau. Yau da gobe ba ta bar kome ba, kafin a ce haka dukiya ta kare sarai. Ana tattalinta ma ya aka ƙare balle an banzatar. Alisharu ya shiga mawuyacin hali na talauci, dukkanin abokansa suka guje masa da suka ga abin hannunsa ya ƙare. Ya sayar da rumfarsa, da gonakin da mahaifinsa ya bar masa. Kai, ta kai ma sai da ya sayar da tufafinsa duka, in ban da na jikinsa bai rage kome ba. Daga nan sai ya shiga taitayinsa, wasiyyar mahaifinsa ta faɗo masa. Ya yi nadama, lokacin da nadamar ba ta da amfani.

Wata rana sai ya wayi gari ba ya da ko dirhami, kuma ba ya da abin da zai ci. Ya zauna tun wayewar gari har zuwa rana tsaka bai kai ko loma ɗaya ga bakinsa ba, sai ya ce a cikin ransa, "Bari na tafi wurin abokaina da na yi wa karimci, na san ba za a rasa ɗaya daga cikinsu wanda zai taimake ni da abin da zan ci ba.

Ya tashi ya riƙa bin gidajen abokaninsa ɗaya bayan ɗaya, amma duk wanda ya ƙwanƙwansa wa ƙofa, da ya leƙo ya ga shi ne, sai ya mayar da ƙyaure garam ya rufe, yana cewa, 'hala ni na ƙarar maka da dukiya da za ka dame ni da roƙo?' Haka ya yi ta ragaita tsakanin gidajen abokai har ya gaji, babu ɗaya daga cikinsu da ya ko baɗa masa ƙasa. Daga nan sai ya nufi kasuwa yana tunanin inda zai sami 'yar lomar da zai jefa wa hanjinsa da ke ta faman ƙugi a cikinsa. Da shigarsa kasuwa sai ya hangi mutane sun yi dafifi, sun zagaye wani abu a tsakiyarsu suna kallo. Sai ya ce a cikin ransa, "Shin me waɗannan mutane ke kallo ne, bari in matsa in ɗebe kwarkwatar ido."

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, insha Allah.

Bukar Mada
23/11/2022SOYAYYA GAMON JINI 2

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Waziri Aku

Da shigarsa kasuwa sai ya hangi mutane sun yi dafifi, sun zagaye wani abu a tsakiyarsu suna kallo. Sai ya ce a cikin ransa, "Shin me waɗannan mutane ke kallo ne, bari in matsa in ɗebe kwarkwatar ido.

Ya kutsa cikin mutane har ya kai ga abin da ake kallo. Sai ya ga ashe wata kyakkyawar kuyanga ce ake talla. Tsawon wannan kuyanga zai kai kafa biyar, jikinta madaidaici, ita ba siririya ba kuma ba mai ƙiba ba. Tana da jajayen kumatu kamar furen wardi. Ƙirjinta faffaɗa a cike, ya turo sama kamar zai fasa rigar da ta sanya. Tana da shafaffen ciki da faffaɗan kuturi. Wannan kuyanga ta zarce dukkanin matan zamaninta da kyawo, da haiba da kwarjini. Sunanta Zumurrazi.

Yayin da Alisharu ya ga wannan kuyanga sai ya yi mamaki da irin kyawun da Allah ya hore mata, ya ce, "Na rantse da Allah, ba zan bar wannan wuri ba sai na ji tamanin wannan kuyanga, kuma sai na ga wanda Allah zai ba sa'ar sayenta." Don haka sai ya yi tsaye a cikin attajirai, su kuma da suka ga haka sai suka yi zaton cewa shi ma ya zo ne domin sayen wannan kuyanga, saboda sun san mahaifinsa ya bar masa gadon dukiya mai yawa, ba su san cewa fanko ne ba. Ganin kitse suke yi wa rogo.

Daga nan sai dillalin kuyanga ya tsaya kusa gare ta, ya dubi attajirai ya ce, "Ya ku attajirai, ya ku manyan mutane. Wanene daga cikinku zai fara taya wannan kuyanga mai daraja, sarauniyar watanni, murjanin zamani, kwararrar masaƙiya, farin cikin wanda ya same ta, baƙin cikin wanda ya rasa ta, kuyanga Zumurrazi? Duk wanda zai fara taya ta ya sani, babu komawa baya bisa ga kuɗin da ya ambata."

Daga nan sai wani tajiri ya yi gaba ya ce, "Na saye ta dinari ɗari biyar."

Sai wani ya zaburo ya ce, "Zan biya dinari ɗari biyar da goma."

Yana rufe bakinsa sai wani tsoho mai shuɗin idanu da matsattsar fuska, kamar an matse lemu, mai suna Rashiduddini ya ce, "Ni zan biya dinari ɗari shida."

Sai wani ya cafe, "Zan biya dinari ɗari shida da goma."

Rashiduddini ya ce, "Na saya dinari dubu."

Daga nan sai kowa ya yi tsit daga cikin tajiran nan. Da dillali ya ji babu wanda ya yi ƙari a kan kuɗin Rashiduddini, sai ya juya wurin ubagidan kuyanga domin ya ji ta bakinsa. Ubangidan Zumurrazi ya ce, "Na rigaya na yi rantsuwa ba zan sayar da ita ba sai ga wanda take so. Tambaye ta ka ji, idan ta amince da shi sai a karɓi kuɗinsa."

Dillali ya juya wurin Zumurrazi ya ce, "Ya shugabar kyawawa, wancan attajirin ya nemi ya saye ki," ya nuna mata Rashiduddini, "menene ra'ayinki game da shi?"

Kuyanga ta dubi Rashiduddini, ta gan shi kamar yadda na kwatanta muku shi, sai ta ce, "Ni kam ba zan yarda a sayar da ni ga tsoho mai farin gemu ba, da ganin fuskarsa babu alheri tattare da shi."

Dillali ya ce, "Lalle ke abar yi wa hanzari ce. Darajarki dinari dubu, haka ya saye ki." Dillali ya gaya wa ubangidan yarinya cewa yarinya ba ta yarda da wancan tsoho ba. Ya ce to, sai a nemo wani. Dillali ya faɗa wa tajirai cinikin Rashiduddini bai samu karɓuwa ba, ya kuma gaya musu dalilin haka.

Sai wani mutum ya fito ya ce, "Na saye ta kamar yadda wannan tajiri ya saya, dinari dubu." Kuyanga ta dube shi, ta ga ya shafa wa gemu da sajensa shuni, sai ta ce, "Wane irin abin kunya ne haka? Don me kake ƙoƙarin ɓoye furfura daga fuskarka. Lallai kai ba abin gaskatawa ba ne."

"Na rantse da Allah kin faɗi gaskiya." In ji Dillali, yana dariya.

Tajirai suka tambayi Dillali me ta ce, sai ya gaya musu abin da ta faɗa. Kunya ta kama wannan tajiri, domin kuwa ta faɗi gaskiya. Sai wani mtum kuma ya fito, ya ce shi ma ya mayar da tayi. Zumurrazi ta dube shi, sai ta ga ido ɗaya gare shi, ta ce wa Dillali, "Wannan ai ido ɗaya gare shi, kamar yadda aka danganta shi a cikin wannan waƙa:

"Ka ga wancan mai ido ɗai,
Ya kasance mai hasara.

Zance duka in ya shirya,
Ka taras ƙarya ya tsara.

Da a ce mai kyan hali ne,
Zai zo da biyunsu ƙwara.

Kar ka zamto mai kusantar,
Mai ido ɗaya ko da zarra."

Dillali ya nuna mata wani mutum, ya tambaye ta, "za ki yarda wancan ya saye ki?" Ta dubi mutumin ta gan shi gajere ne kamar a kife da kwando, ga tarin gemu har bisa cibiyarsa. Sai ta ce, "Wannan ai shi ne aka waƙe a cikin waɗannan baitoci:

"Ina da abokina mai gemu,
Ya yi tsawo ga tarin gashi.

Ya yi duhu sai tarin sanyi,
Babu mamora in ka gan shi."

Daga nan sai Dillali ya ce, "Ya shugabata, ki yi duba a cikin taron mutanen nan, ki zaɓi duk wanda kike so ya saye ki, in sayar masa da ke." Sai ta riƙa duban attajiran nan, ɗaya bayan ɗaya har idanunta suka sauka a kan Alisharu.

Tana ganinsa sai ta yi ajiyar zuciya, ƙaunarsa ta caki zuciyarta. Ta ce wa Dillali, "Babu wanda zai saye ni sai wancan saurayi mai kyakkyawar fuska, mai madaidaicin jiki. Babu wanda ya cancanci ya mallake ni face shi. Dubi kumatunsa masu tsantsi, da yawun bakinsa mai zaƙi kamar Salsabil. Kallonsa kawai na warkar da majiyyaci."

Yayin da Dillali ya ji kalamanta sai ya yi mamaki da iya tsara zancenta. Ubangidanta ya ce masa, "Kada ka yi mamaki da azancin mganarta. Ban da wannan kyawo nata mai kunyatar da rana, tana da ɗimbin ilimi na waƙoƙi da na addini. Ta hardace Alkur'ani mai girma, tana iya karanta shi da ƙira'o'i bakwai. Tana kuma iya rubuta shi da kai ba tare da ta duba ba. Ta kuma san fannonin ilimi iri-iri. Tana kuma da wata babbar baiwa, ka ga hannayen nan nata sun fi zinariya da azurfa daraja, domin da su takan saƙa wani irin labulen ƙofa na siliki mai tsananin kyau, akan sayi wannan labule dinari hamsin. Takan saƙa wannan labule cikin kwana takwas kacal."

Dillali ya ce, "Wanda kuwa duk ya saye ta ya yi dace."

Ubangidan kuyanga ya ce, "Je ka, ka sayar da ita ga duk wanda ta zaɓa."

Dillali ya tafi gaban Alisharu ya ce masa, "Ya shugabana, ka biya kuɗin wannan kuyanga domin kai ta zaɓi ka saye ta." Ya gaya masa dukkan halayenta da matsayinta da kuma dukkanin baiwar da Allah ya yi mata. Ya ƙara da cewa, "Ina mai tabbatar maka da cewa idan ka saye ta za ka same ta tamkar kyauta ce aka ba ka domin irin amfanin da za ta yi maka."

Alisharu ya duƙar da kansa ƙasa na ɗan wani lokaci, yana yi wa kansa dariya, yana cewa a cikin ransa, "Wanda har yanzu bai karya ba, ina ya ga kuɗin sayen wata kuyanga can, ana ta kai wa yake ta kaya?" Sai dai kuma yana jin kunyar sauran tajiran da ke wurin su gane ba ya da kuɗi. Sai ya ci gaba da murmushin ƙarfin hali yana sosa ƙeya.

Yayin da kuyanga ta ga Aliyu Sharu ya sunkuyar da kansa ƙasa yana susar kai, sai ta ce wa Dillali, "Riƙi hannuna ka kai ni gabansa. Zan ja ra'ayinsa har ya yarda ya saye ni. Ni kam ba zan amince wa kowa ya saye ni ba sai shi."

Dillali ya riƙi hannunta ya kai ta gaban Aliyu Sharu, ya ce masa, "Me kake tunani ne game da wannan kuyanga da ba za ka saye ta ba?" Aliyu Sharu ya dubi Zumurrazi amma bai ce komai ba.

Zumurrazi ta ce, "Ya shugabana, hasken zuciyata, me ya hana ka mayar da tayi a kaina? Ka saye ni zan zama mai amfani gare ka."

Aliyu ya dube ta ya ce, "Zan saye ki da ƙarfi ne? Ina ce dinari dubu aka taya ki?"

Ta ce, "Za ka biya dinari ɗari tara?"

Ya girgiza kansa, "A'a."

"To, ka biya ɗari takwas." In ji ta. Ya ƙara girgiza kansa. Ba ta gushe ba tana rage kuɗin har suka zama dinari ɗari.

Aliyu ya ce, "Ba ni da dinari ɗari."

Ta yi murmushi, "To, kuɗinka nawa suka kasa ga dinari ɗari?"

"Na rantse da Allah ba ni da ko dirhami ja, balle fari. Don haka ki biɗi wani masayi." in ji Aliyu cikin damuwa da takaicin rashin kuɗin da zai sayi kuyanga.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, insha Allah.

Bukar Mada
26/11/2022

...

Ga alama kun fara gajiya da karatu ba kamar a baya ba, kamar yadda na gani a waɗannan hotuna biyu. LIKES, COMMENTS, da SHARE naku su ke nuna mini kuna da sha'awar wannan labari ko ba ku da sha'awa. Don haka POSTS biyu masu zuwa za su yanke hukunci ko na ci gaba da kawo muku wannan labari ko ni ma in dakata in huta.SOYAYYA GAMON JINI 3

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Waziri Aku

Alisharu ya ce wa kuyanga Zumurrazi, "Na rantse da Allah ba ni da ko dirhami ja, balle fari. Don haka ki biɗi wani masayi."

Yayin da yarinya ta gane cewa Alisharu fanko ne, bai mallaki komai ba, sai ta je kusa ga kunnensa ta raɗa masa wata magana wadda sauran mutanen da ke wurin ba su ji ba. Ta ce, "Riƙi hannuna ka keɓe da ni cikin kwararo, inda babu mai ganin mu, ka yi kamar za ka duba jikina ne a asirce."

Alisharu ya yi kamar yadda ta ce. Da suka keɓe cikin lungu, sai ta fakaici idon mutane, ta sanya hannunta cikin ƙirjinta ta fiddo da wata 'yar ƙaramar jaka mai ƙunshe da dinari dubu, ta cinna masa ita ga hannunsa. Ta ce, "Ka biya dinari ɗari takwas, ka rage mana dinari ɗari biyu waɗanda za mu sayi abinci."

Ya aikata abin da ta ce, ya biya kuɗinta, dinari ɗari takwas, ga Dillali, ya riƙe sauran dinanri ɗari biyu. Ya ja ta zuwa gidansa, da suka shiga sai ta ga babu komai a cikin gidan, hatta shimfiɗu da akussan cin abinci babu a gidan, ta gan shi fayau. Sai ta ce masa, "Je ka kasuwa ka sayo mana shimfiɗu da akussa da kayan abinci na dinari ɗari da hamsin, ka sayo nama na dirhami uku. Ka sayo mini ƙyallen siliki wanda ya kai girman labulen kofa, da zaren zinariya da azurfa, da zaren saƙa na siliki mai launi bakwai."

Ya nufi kasuwa da sauran dinari ɗari biyun nan, ya sayo dukkan abin da ta lissafa. Ta tashi ta share gidan nan kaf, ta shimfiɗa shimfiɗun da ya sayo, ta dafa musu abinci. Suka zauna suka ci suka ƙoshi. Da dare ya yi suka kwana cikin shimfiɗa guda, suka ɗebe ƙishirwar juna. Soyayya da ƙaunar juna ta mamaye zukatansu.

Da gari ya waye, Zumurrazi ta ɗauki ƙyallen nan da aka sayo mata, ta fara saƙa labulen ɗaki da zaruruwa na zinariya da azurfa. Ta zana hotunan tsuntsaye iri-iri da hotunan namun daji bisa ƙyallen nan. Babu wata dabbar daji da ba ta zana hotonta a kan ƙyallen ba. Haka ta ci gaba da ƙawata wannan ƙyalle har tsawon kwana takwas. Ta yayyafa masa ruwa ta ninke, ya kwanta sosai, ta miƙa wa Alisharu ta ce, "Tafi da shi kasuwa ka sayar wa attajiri a kan kuɗi dinari hamsin. Amma ka kula, kada ka kuskura ka sayar da shi ga baƙo, matafiyi, domin wannan zai iya yin sanadin da magauta za su raba tsakaninmu."

Alisharu ya ce, "Na ji, zan kuma kiyaye da wannan." Ya tafi da ƙyalle kasuwa ya sayar da shi ga wani attajiri, kamar yadda ta hore shi. Ya sayo mata wani ƙyallen da zaruruwan saƙa. Ya kuma sayo kayan abinci da abin sha da nama, ya dawo da sauran kuɗi gida. Haka suka zauna tsawon shekara guda, duk bayan kwana takwas takan saƙa irin wannan ƙyalle su sayar da shi dinari hamsin.

Wata rana ya tafi da ƙyalle kasuwa, kamar yadda ya saba, ya ba dillali domin ya sayar masa, sai ga wani Banasare, mabiyi addinin Masihu ɗan Maryama, ya nuna sha'awarsa ga ƙyallen har ya taya shi dinari sittin. Alisharu ya ƙi sayar masa, sai Banasaren nan ya yi ta ƙara masa kuɗi har ya kai dinari ɗari, kuma ya kawo rashawar dinari goma ya ba dillali.

Yayin da dillali ya ga haka sai ya zo wurin Alisharu ya faɗa masa yadda aka sayi ƙyalle ya matsa a kan ya karɓi kuɗin Banasare. Ya ƙara da cewa, "Ya shugabana, kada ka ji tsoron wannan mutum domin ba zai cutar da kai da komai ba." Sauran attajirai ma suka matsa masa a kan ya karɓi kuɗi. Ya sayar wa Banasare da ƙyallen ba tare da zuciyarsa ta so ba. Ya yi sayayyar da zai yi, ya nufi gida da sauran kuɗi.

Yana cikin tafiya sai ya lura da Banasaren nan yana bin sa a baya. Ya tsaya ya ce masa, "Ya kai wannan Nasara, me ya sa kake bi na?" Sai ya amsa masa ya ce, ba shi yake bi ba, yana da wata buƙata ne da zai yi a ƙarshen wannan kwararo.

Alisharu ya ƙyale shi, ya ci gaba da tafiya abinsa har ya iso ƙofar gidansa, ga mamakinsa sai ya ga Banasaren nan na biye da shi. Kafin ya shige cikin gida sai ya cim masa da sauri, ya tari gabansa. Aliyu ya fusata, ya ce masa, "Wace irin shiririta ce wannan, don me kake bi na?"

Sai mutumin ya kada baki ya ce, "Ya shugabana, don Allah ka taimake ni da ɗan ruwan da zan sha mana, ƙishirwa nake ji."

Aliyu ya yi niyyar ya kore shi, sai ya yi wani tunani a cikin ransa, "Haƙiƙa wannan mutum yana ɗaya daga cikin kafuran amana, wanɗanda Halifa ke karɓar haraji gare su. Bai kamata in hana shi ɗan ruwan da zai sha ba." Sai ya shiga gida ya ɗauko goran ruwa zai kawo masa. Yayin da Zumurrazi ta ga Aliyu riƙe da goran ruwa, kuma ya nufi waje da shi, sai ta dakatar da shi ta tambaye shi, "Ya shugabana, ka sayar da ƙyallen?"

Ya amsa mata, "Na'am."

Ta tambaye shi, "Wa ka sayar ma wa, tajiri ko matafiyi? Domin yau dai jikina yana ba ni cewa an fara maƙarƙashiyar raba mu."

Ya ce mata, "Na sayar wa tajiri ne."

Ta dube shi ta ce, "Kai dai faɗa mini gaskiya, ko dai wani matafiyi ka sayar wa?" ta kuma dubi hannunsa, "ina za ka da goran ruwa kuma?"

Alisharu ya amsa mata, "Ai tare da dillalin da ya sayar mini da ƙyallen na zo, shi ne zan kai wa ruwa ƙofar gida."

Yayin da Zumurrazi ta ji haka sai ta buga salati tare da tafa hannu, ta ce, "Babu tsimi babu dabara face

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment