Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga Allah Maɗaukakin Sarki."

Aliyu ya fice da goran ruwa ga hannunsa, ya bar ta nan tsaye tana sallallami. Da ya shiga zaure sai ya iske Banasaren nan zaune. Aliyu ya daka masa tsawa, "Kai wane irin mutum ne mara hankali? Kai da na bari a bakin ƙofa, me ya shigo da kai har cikin gidana?"

Sai Banasare ya ce, "Ya shugabana, ai babu banbanci tsakanin ƙofar gida da zaure. Ina godiya da wannan ɗawainiya da kake da ni." Sai ya karɓi goran ruwa daga hannun Aliyu ya shanye, ya mayar masa da goran. Aliyu ya tsaya yana jira ya ga ya fice daga zauren, ya kama gabansa. Maimakon haka sai ya ga ya gyara zama, ya harɗe ƙafafunsa.

Aliyu ya tambaye shi, "Me kake jira kuma? Tashi ka kama gabanka."

Sai ya ce wa Aliyu, "Ya shugabana, kada ka kasance cikin masu yin alheri da hannun dama, sa'annan su ƙwace da hannun hagu. Yanzu na sha ruwa, ya kamata ka cika alherinka gare ni, ka kawo mini wani ɗan abu da zan ci ko da guntuwar gurasa ce haɗe da albasa."

Aliyu Sharu ya harare shi, "Tashi ka kama tafarkinka, babu komai a gidana wanda za ka ci. Kada ka tsawaita mini da yawan magana."

Yayin da Banasare ya ji haka, sai ya zaro dinari ɗari daga cikin aljihunsa ya miƙa wa Aliyu, "Karɓi wannan ka tafi kasuwa ka sayo mana wani abu wanda za mu ci, ni da kai. Kada ka damu da sayo abinci mai tsada, ko 'yar gurasa ka samu, ka sayo babu laifi."

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, insha Allah.

Bukar Mada
30/11/2022SOYAYYA GAMON JINI 4

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Waziri Aku

Yayin da Banasare ya ji haka, sai ya zaro dinari ɗari daga cikin aljihunsa ya miƙa wa Aliyu, "Karɓi wannan ka tafi kasuwa ka sayo mana wani abu wanda za mu ci, ni da kai. Kada ka damu da sayo abinci mai tsada, ko 'yar gurasa ka samu, ka sayo babu laifi."

Aliyu ya karɓi kuɗi yana tunani a cikin ransa, "Wannan kuɗi sai ka ce za a sayo abincin mutum goma. Lalle wannan Nasara gaula ne, bai san ciwon kuɗi ba. Bari in tafi in sayo abinci na dirhami uku, in ɓoye sauran kuɗin ina yi masa dariya a ciki."

Har zai fita sai Banasare ya ƙara ce masa, "Ba fa sai ka sayo abinci mai tsada ba, 'yar gurasa da albasa kawai sun isa, burina dai in ji cikina ya ɗauka. Ka ji an ce mafi kyawon abinci shi ne wanda aka ci ya kawar da yunwa."

Alisharu ya ce masa, "Bari in rufe gidan in tafi kasuwa in sayo maka abin da ranka ke buƙata." Sai ya sa kwaɗo ya rufe kofar zauren da ta nufi cikin gida, ya sa ɗan mabuɗin a cikin aljihunsa, ya bar Banasare a cikin zauren ya nufi kasuwa. Ya sayo waina da zuma da kuma ayaba, ya kawo.

Yayin da Banasare ya ga abincin da Aliyu ya sayo, sai ya riƙe baki cikin mamaki, "Wannan ai abincin mutum shida ne ka sayo, ina ni ina cinye wannan abinci? Babu makawa ka zauna mu ci tare da kai."

Aliyu ya ce, "Ni kam na ƙoshi, ba zan ci komai ba."

Banasare ya ce, "Ya shugabana, ka manta da maganar nan ne da mutane ke cewa, wanda duk bai ci abinci tare da baƙonsa ba, to, ba ɗan halas ba ne, mai yiwuwa karuwa ce ta haife shi." Da Aliyu ya ji haka, sai ya zauna domin su ci abincin tare. Bayan ya yi loma uku sai ya yi nufin cire hannunsa daga cikin akushi.

Yayin da Banasare ya ga Aliyu na shirin cire hannunsa daga cikin akushin abinci, sai ya faki idonsa ya kaikaita ya ɓare ayaba ɗaya. Ya shafe ta da banju mai karfin gaske, wanda ko da giwa ce ta shaƙe shi sai ta jima tana barci balle kuma ta haɗiye shi. Ya tsoma wannan ayaba a cikin zuma, ya miƙa wa Aliyu Sharu ya ce, "Na rantse da Masihu sai ka cinye wannan 'yar ayabar, idan dai har kana girmama addininka da gaskiya."

Alisharu ya karɓi ayaba ya cinye, saboda rantsuwar da Banasare ya yi. Yana haɗiyewa sai ya ji kasala ta rufe shi, nan take ya faɗi ƙasa cikin bacci mai nauyi. Da Banasare ya ga haka sai ya tashi da hanzari, kamar mayunwacin kyarkecin da ya hangi akuya, ya lalubi aljihun Aliyu, ya ɗauki ɗan mabuɗin nan da ya rufe gida da shi, ya fice daga cikin zauren.

To, ashe wannan Banasare ɗan uwan tsohon nan ne mai matsattsar fuska, mai suna Rashiduddini, wanda ya fara taya Zumurrazi dinari dubu, ta ƙi amincewa da shi. Ashe a fuska kawai yake nuna Musuluncinsa, a ƙarƙashin zuciyarsa kuwa Kirista ne. Lokacin da Zumurrazi ta ƙi amincewa ya saye ta, ga shi kuma zuciyarsa ta ƙawata masa mallakarta, sai ya gaya wa wannan ɗan uwan nasa Banasare, mai suna Barsumu. Shi kuma ya ce masa, ya kwantar da hankalinsa, zai yi dabarar da ya sace ta ya kawo masa ita har gida kyauta.

Wannan Banasare kuwa, watau Barsumu ɗan uwan Rashiduddini, babban boka ne, ya san ilimin bokanci, ya kuma ƙware ga makirci da ƙarya da yaudara da hila fiye da tsohuwa mai shekaru ɗari. Bayan ya ɗauki mabuɗin ƙofa daga cikin aljihun Aliyu, sai ya fice daga cikin zauren, ya nufi gidan ɗan uwansa Rashiduddini ya kwashe labari ya gaya masa, ya kawo mabuɗin nan ya ba shi.

Nan da nan Rashiduddini ya hau alfadararsa, ya tafi tare da wasu bayinsa, ya kuma ɗauki jaka guda ta kuɗi, wadda idan ya haɗu da Sarkin Dogarai zai ba shi rashawa. Suka tafi har suka isa gidan Alisharu, suka tarar da shi yana ta sharar barci a cikin zaure. Rashiduddini ya buɗe ƙofar zauren ya shiga cikin gidan tare da bayinsa. Ya sa suka kama Zumurrazi suka ɗaure, ya ce idan ta yi gardama zai yanka ta. Suka fita da ita, ba su ɗauki ko allura ba a cikin gidan. Suka rufe ƙofa suka mayar da mabuɗin cikin aljihun Aliyu, suka bar shi nan yana barci.

Rashiduddini ya tafi da Zumurrazi gidansa ya saka ta a cikin kuyanginsa ya ce mata, "Ni ne tsohon nan da kika muzanta a cikin mutane lokacin da na so in saye ki dinari dubu. Ga shi yanzu na mallake ki ba tare da biyan ko dirhami ba."

Cikin kuka Zumurrazi ta ce masa, "Allah ya shirye ka, tsohon banza, kafiri! Don me ka raba ni da shugabana, abin ƙaunata?"

Ran Rashiduddini ya ɓaci, ya daka mata tsawa, "Kaiconki 'yar iska mara mutunci! Na rantse da Masihu da Maryamu Uwa, sai na yi miki azaba mai tsanani har sai kin yi biyayya gare ni kin rungumi addinina da gaskiya."

Zumarrazi ta ce, "Na rantse da Allah ko da za ka yanka ni gunduwa-gunduwa ba zan bar addinin Musulunci ba. Ko ba ka ji yadda aka ce ba ne, gwamma raunin jiki da raunin addini. Ga Allah na dogara gare shi nake neman taimako."

Yayin da tsohon nan ya ji haka sai ya ƙara tunzura, kamar an watsa wa wuta mai, ya yi wa bayinsa da kuyangi tsawa, "Ku banƙare mini ita!"

Suka kama ta suka banƙare, ya yi ta bugunta da bulala tana kuka tana neman taimako, amma babu wanda ya saurare ta, daga nan sai ta riƙa cewa, "Ga Allah na dogara, gare shi nake neman taimako. Hasbiyallahu wa ni'imal wakil." Ta ci gaba da faɗin waɗannan kalamai har zafin duka ya sumar da ita.

Bayan ya gaji da bugunta kuma ya ga ta suma, sai ya ce wa bayin nan su ja ta ga ƙasa su jefar da ita kusa ga ɗakin dahuwa, zafin wuta ya buge ta. Ya gargaɗe su kada su kuskura su ba ta ko loma ɗaya ta abinci ko ruwan sha. Suka yi kamar yadda ya umurce su.

Da gari ya waye sai la'anannen tsohon nan ya sa aka ƙara kawo masa Zumurrazi a gabansa, ya sake bugunta har ta suma, ya sa aka ja ta aka mayar. Bayan ta farfaɗo sai ta ce, "Na shaida babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah. Na shaida Annabi Muhammadu Manzon Allah ne. Ba ni da ƙarfi ba ni da dabara face daga Allah Maɗaukakin Sarki, gare shi na dogara gare shi nake neman taimako." Ta yi addu'a tare da yin salati ga Shugabanmu Annabi Muhammadu, ta roƙi Allah ya fitar da ita daga cikin wannan azaba.

Shi kuwa Alisharu ya yi ta sharar barci tun da rana har gari ya waye, sa'annan ya farka bayan banjun ya sake shi. Da ya farka sai ya yi kira da ƙarfi, "Ya ke Zumurrazi!" Amma babu wanda ya amsa masa. Ya laluba aljihunsa ya ɗauki mabuɗi, ya buɗe ƙofar zauren ya shiga cikin gida, ya duba ko'ina bai ga Zumurrazi ba. Daga nan sai ya gane cewa Nasaran nan ne ya yaudare shi, ya sace masa abar bege. Hawaye suka karyo masa, ya yi kuka tare da gunji, ya waƙa waɗannan baitoci:

Tsananin ƙauna ta kama ni,
Zuciyata na cikinsa mari.

Ta faɗa mini na ƙi ɗauka ni,
Yau ga shi ina cikin garari.

Dokar so ce na karya ni,
Wa za ya fitar da ni haɗari?

Wutar bege ta ƙona ni.
Babu wacce nake gani a gari.

Maharbi ne ya yo rawani,
Ya zare kibau a cikinsa kwari.

Ya ja kibiya irin na gwani,
Zai harbi waninsa da ke mazari.

Zare ya katse kamar lagwani,
To yaya zai yi da mai mazari?

A cikin daji na kutsa ni,
Wa za ya gane ni ya kai ni gari?

Ya yi nadama lokacin da nadamar ba ta da amfani, ya zauna ya ci gaba da kuka yana marin fuskarsa yana yayyaga tufafinsa tare da zuba ƙasa bisa kansa. Daga nan sai ya ɗauki duwatsu guda biyu ya fita daga cikin gidansa yana bugun ƙirjinsa da waɗannan duwatsu yana kuka yana kiran sunan Zumurrazi.

Da yara suka gan shi a cikin wannan hali, tufafinsa sun yage, kansa ya yi burtutu da ƙasa, sai suka dafo masa suna tsokana, "Eho, mahaukaci! Mahaukaci!" Mutanen kuma da suka san shi sai suka riƙa cewa, "Allah Sarki, ko me ya sami wannan yaro?" Haka ya yi ta yawo cikin gari tsawon wannan rana. Yayin da dare ya yi sai ya yi kwanciyarsa a gefen hanya, bai kula ba, har gari ya waye.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, insha Allah.

Bukar Mada
03/12/2022SOYAYYA GAMON JINI 5

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Waziri Aku

Da yara suka gan shi a cikin wannan hali, tufafinsa sun yage, kansa ya yi burtutu da ƙasa, sai suka dafo masa suna tsokana, "Eho, mahaukaci! Mahaukaci!" Mutanen kuma da suka san shi sai suka riƙa cewa, "Allah Sarki, ko me ya sami wannan yaro?" Haka ya yi ta yawo cikin gari tsawon wannan rana. Yayin da dare ya yi sai ya yi kwanciyarsa a gefen hanya, bai kula ba, har gari ya waye.

Da gari ya waye ya tashi ya ci gaba da zagaya gari yana bugun ƙirjinsa da duwatsu yana kiran sunan Zumurrazi, haka ya kasance har maraice sa'annan ya koma gidansa.

Cikin maƙwabtansa akwai wata tsohuwa, mutuniyar kirki, yayin da ta gan shi cikin wannan hali sai ta tausaya masa. Ta riƙa cewa, "yaushe wannan yaro ya haukace? Ko menene dalilin haukansa?" Da Alisharu ya ji abin da take cewa, sai ya amsa mata da waɗannan baitocin waƙa:

Suka ce haƙiƙa na zamo mai zautuwa,
Wai don kawai na nuna tsantsar son ta.

Na ce da su ita rayuwa daɗinta ai,
Ta zamo tana nan gab da mai ƙaunar ta.

Na jaddada kuma zan faɗa muku 'yan uwa,
Zan wartsake muku har idan na gane ta.

Daga nan sai ta fahimci cewa yana cikin damuwa ne domin rashin kuyangarsa da yake tsananin so, sai ta riƙa tafa hannu tana sallallami cikin tausayi. Ta ce, "Babu tsimi babu dabara face daga Allah Maɗaukakin Sarki!" Ta ci gaba da cewa, "Ya ɗana, gaya mini abin da ya faru gare ka, wataƙila Allah ya ba ni damar da zan iya taimaka maka."

Alisharu ya kwashe labarin abin da ya faru gare shi duka ya faɗa wa tsohuwa. Yayin da ta ji haka sai hawaye suka zubo mata saboda tausayi, ta ce, "Ya ɗana, haƙiƙa ka afku cikin babban makirci. Amma kada ka damu ina da dabara."

"Wace dabara gare ki, ya mahaifiyata?" Alisharu ya tambayi tsohuwa.

Ta amsa masa, "Ina so ka tafi kasuwa ka sayo mini kwando irin wanda ake tallar jauhari da shi. Ka ciko shi da kayan jauhari irinsu sarƙoƙi, zobba, mundaye, 'yan kunne da sauran kayan kwalliya na mata. Zan ɗauki wannan kwando bisa kaina in shiga gida gida ina talla, ba zan gushe ba har sai na gano gidan da kuyangarka take, da yardar Allah Maɗaukakin Sarki."

Aliyu ya ya yi farin ciki da kalamanta, ya riƙi hannunta ya sumbaci yatsunta don murna. Nan take ya yi wanka ya canja tufafinsa ya kwashi kuɗi ya nufi kasuwa. Ya sayo dukkan abin da tsohuwar ta ce masa ya kawo mata. Ta tashi ta canja tufafin jikinta, ta sanya wata babbar riga da mayafi launin ruwan ɗorawa, ta yi shiga irin ta dillaliya. Ta riƙi sanda ga hannunta tana dogarawa, ta aza kwandon bisa kanta ta shiga cikin gari.

Tsohuwa ta riƙa bi kwararo kwararo tana shiga cikin gidaje tana tallar kayan jauhari, ba ta gushe ba kan haka har Allah ya nufe ta da shiga gidan la'anannen tsohon nan Banasare wanda ya kira kansa da suna Rashiduddini. Tun a cikin zauren gidan ta dinga jiyo gunji da ajiyar zuciya irin na mai baƙin ciki yana fitowa daga cikin gidan. Sai ta ƙwanƙwasa ƙofar shiga gidan, sai ga wata kuyanga ta leƙo ta buɗe mata ƙofa. Bayan sun gaisa da juna, sai tsohuwa ta ce mata, "Na kawo muku tallar jauhari, ko za ku saya?"

"Na'am." Kuyanga ta amsa mata. Sa'annan ta ja ta suka shiga cikin gida. Ta kawo abin zama ta ba ta, ta zauna. Ta kira sauran 'yan uwanta kuyangi suka zagaye tsohuwa, kowa na sayen abin da ransa ke buƙata. Ta yi ta jan su da taɗi, kuma duk abin da suka saye sai ta sayar musu da araha.

Daga nan sai ta riƙa waige-waige cikin gidan domin ganin wacce ta jiyo gunjinta kafin ta shigo cikin gidan. Sai kuwa idanunta suka kai ga Zumurrazi can ƙuryar gidan, ɗaure kusa ga ɗakin dahuwa. Tana ganinta ta shaida ta, ita ce wadda Alisharu ya yi mata kwatance. Da ta gan ta cikin wannan hali sai tausayi ya kama ta, ta ce da kuyangi, "Me ya sami waccan 'yar uwar taku na gan ta cikin wannan hali, laifin me ta yi muku kuka ɗaure ta?"

Suka kwashe labarinta suka gaya wa tsohuwa, suka ƙara da cewa, "Mu ma ba da son ranmu aka ɗaure ta ba, ubangidanmu ne ya yi umurni da ɗaure ta. Amma yanzu ba ya nan ya yi tafiya."

Tsohuwa ta ce, "Ya ku 'ya'yana, ina roƙon ku arziki ku kwance wannan baiwar Allah ta sami sukuni, idan ubangidanku ya kusa dawowa sai ku mayar mata da ɗaurin. Idan kuka aikata haka gare ta haƙiƙa Allah zai yi muku sakayya."

"Mun ji mun yarda." Suka amsa mata. Sai suka kwance wa Zumurrazi ɗauri, suka kai mata abinci da abin sha. Yayin da tsohuwa ta ga haka sai ta yi farin ciki. Da ta ga kuyangi sun baro wurin Zumurrazi sai ta miƙe tsaye ta ce da kuyangi cikin ba'a, "Wai! Sai ka ce wadda aka karya wa ƙafafuwa, tun da na shigo gidan nan naku nake zaune kamar gurguwa, bari dai na ɗan miƙe ƙafafuna."

Ta tashi ta tafi wurin Zumurrazi, ta zauna kusa gare ta ta ce, "Albishirinki. Ki yi murna da farin ciki, Allah ya kawo ƙarshen wahalarki. Za ki koma ga shugabanki abin ƙaunarki."

Daga nan sai ta yi ƙasa-ƙasa da murya ta gaya mata cewa shugabanta Alisharu ne ya turo ta, tana shiga gida gida da sunan talla domin kawai ta ga gidan da aka ɓoye ta. Ta ce, "Yanzu sai ki shirya da dare shugabanki zai zo bayan wannan gida, zai zauna ƙarƙashin tagar wancan ɗaki," ta nuna mata wani ɗaki wanda tagarsa take a wajen gidan, "sai ki shiga cikin ɗakin, idan ya zo zai yi fito da baki, ke ma sai ki mayar masa da fiton. Daga nan sai ki haura ta tagar zai taimaka miki ki sauka ba tare da kin ji ciwo ba, daga nan sai ku gudu zuwa gida."

Zumurrazi ta yi ta yi wa tsohuwa godiya. Ita kuma ta tashi ta tattara 'yan kayan jauharinta cikin kwando ta ɗauka ta nufi gidan Alisharu ta kwashe labari ta faɗa masa. Ta yi masa kwatancen gidan tsinannen Banasaren nan, ta gaya masa dabarar da ta shirya musu, ta yi masa kwatancen tagar da zai je ya zauna ƙarƙashinta da abin da zai yi. Ya yi mata godiya, hawaye na fita daga idonsa har ya waƙe wasu baitoci don murna.

Ya zauna har dare ya yi, daga nan sai ya tashi ya nufi unguwar da gidan Kiristan nan yake. Da zuwa sai ya gane gidan ta amfani da kwatancen da tsohuwa ta yi masa. Ya zagaya bayan gidan ya samu wuri ƙarƙashin tagar nan ya zauna, ya jingina jikin garu. Zamansa ke da wuya sai wata irin kasala ta rufe shi, ga shi ya daɗe bai runtsa ba saboda tsananin bege da tunani. Yana zaunawa kuwa sai barci mai nauyi ya rufe shi sai ka ce wanda ya kwankwanɗe tulun giya. Tsarki ya tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki wannan da gyangyaɗi ba ya riskar sa balle barci.

Aliyu na cikin barci sai ƙaddara ta jeho wani ɓarawo a gidan wannan Kirista. Ɓarawon nan ya riƙa zagaya gidan yana neman wurin da zai haura cikin gidan. Yana cikin zagaya gidan sai ya kawo wurin da Alisharu yake zaune yana sharar barci. Da ɓarawon nan ya ga mutum zaune sai ya yi nufin gudu, amma da ya ji yana minshari har da jan rago sai ya tabbata bacci yake yi, don haka sai ya matsa kusa gare shi domin ganin ko akwai wani ɗan abin kirki da zai ɗauke daga jikinsa.

Da ya je kusa gare shi ya duba bai ga wani abin ɗauka ba, sai rawaninsa da ya faɗi lokacin da yake barci. Barawo ya ɗauki rawanin ya naɗa ga kansa. Lokacin da ya juya zai tafi sai Zumurrazi ta leƙo ta taga, ashe ita kuma ta ji motsin ɓarawon, sai ta ga mutum tsaye cikin duhu. Ta yi masa fito, ta aza shugabanta ne, Alisharu. Sai ta diro daga tagar tana riƙe da wata jaka cike da zinariya da ta kwasa daga taskar Banasare, ta faɗa ga jikin ɓarawo.

Yayin da ɓarawon nan ya ga haka sai ya ce a cikin ransa, "Wannan baƙon al'amari ne, babu shakka akwai wani ɓoyayyen abu tattare da wannan yarinya." Ya sungume ta bisa kafaɗarsa tare da jakar zinariya ya tafi yana sauri kamar walƙiya. Yana cike da farin ciki saboda tsintar dami da ya yi a kala.

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, insha Allah.

Bukar Mada.
07/12/2022
SOYAYYA GAMON JINI 6

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Waziri Aku

Ɓarawo ya sungume ta bisa kafaɗarsa tare da jakar zinariya ya tafi yana sauri kamar walƙiya. Yana cike da farin ciki saboda tsintar dami da ya yi a kala.

Suna cikin tafiya sai Zumurrazi ta ce, "Ya shugabana, tsohuwa ta gaya mini halin da ka shiga na rashin lafiya har take ce mini ƙarfinka ya ƙare saboda tunanina. Amma yanzu na ji ƙarfinka ya dawo sai ka ce doki, menene dalilin haka?"

Ya ci gaba da tafiya bai amsa mata ba. Yayin da Zumurrazi ta ga haka sai wasiwasi ya mamaye ranta. Ta sa hannunta ta lalubi fuskarsa, ta ji fuskar cike da gashi, ga kuma wani gemu duguzum kamar burushin wanka. Da ta lalubi wajen wuyansa sai ta ji wani maƙoƙo a wuyan nasa kamar wanda ɗan goruba ya maƙalewa a wuya. Tsoro ya kama ta, ta ce cikin kaɗuwa, "Wanene kai?"

Ya amsa mata, "Ni ɓarawo ne wanda ake kira Jiwanu ɗan Kurdu. Ina ɗaya daga cikin yaran Ahamadu Danafi. Mu arba'in ne yaransa muka sauka cikin wannan birni naku. Kowa ya bazama ya sami rabonsa cikin wannan dare har zuwa asuba."

Yayin da ta ji jawabinsa sai ta gane cewa ashe ta yi gudun gara ne ta faɗa gidan zago. Hawaye suka zubo mata ta ce a cikin ranta, "Duk lokacin da na kuɓuta daga wani ƙangi sai in faɗa wani. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, gare shi na dogara gare shi nake neman taimako." Ta haƙura ta ga abin da Allah zai ƙaddara gare ta.

Shi kuwa wannan ɓarawo dalilin zuwansa wannan birni a cikin dare shi ne, tun tuni sun shirya zuwa wannan birni su arba'in da shugabansu Ahamadu Danafi. Kafin su zo sai shi ya ce wa shugaban nasu, "Ni na taɓa zuwa wannan birni na san da wani kangon gida a bayan gari wanda mutum arba'in za su iya kwana a cikinsa. Ina so ka yi mini izini in fara zuwa wannan birni, zan tafi da mahaifiyata in ajiye ta a cikin wannan gida, zan zagaya cikin gari in yi sata, duk abin da na samu na sadaukar da shi gare ka, a matsayinka na baƙo a wannan birni. Zan ajiye shi a cikin kangon gidan har sai ka iso.

Ahamadu Danafi ya ce masa ya yi duk yadda yake so. Don haka sai Jiwanu ya yiwo gaba tare da mahaifiyarsa ya baro sauran ɓarayin a baya. Da zuwansa bayan gari kafin ya isa inda kangon gidan nan sai ya tarar da wani mutum matafiyi ya ɗaure dokinsa, ya yi shimfiɗa ƙasa ya kwanta yana barci. Ya yanka mutumin nan, ya kashe shi. Ya kwashe kayansa tare da dokin ya nufi kangon gidan, ya bar su can duka tare da mahaifiyarsa, ya shiga cikin birni yawon sata. Ya yi ta yawo cikin gari yana neman gidan da zai shiga har Allah ya kawo shi gidan Kiristan nan, abin da ya faru ya faru tsakaninsa da Alisharu da kuma Zumurrazi.

Ɓarawo ya ci gaba da tafiya da Zumurrazi bisa kafaɗarsa har ya iso kangon gidan nan na bayan gari. Ya damƙa ta ga hannun mahaifiyarsa, ya ce, "Ki kula da ita kafin in dawo da asuba. Kada ki bar ta ta fita ko'ina." Ya kaɗa kai ya koma cikin gari.

Bayan ya tafi sai Zumurrazi ta yi tunani a cikin ranta, "Yanzu ne lokacin da ya dace in hilaci tsohuwar nan in gudu. Idan na kuskura ɓarayin nan arba'in suka isko ni a wannan gida babu shakka duk sai sun biya buƙatarsu gare ni, su mayar da ni tamkar jirgin da ya cika da ruwa." Sai ta juya wurin tsohuwa, wadda tun da ta iske ta hannuwanta na bisa kai tana ta faman susa, ta yi murmushi ta ce, "Inna, ba kya fita waje ba mu je cikin hasken farin wata, in kashe miki kwarkwatan nan da ta dame ki?"

Tsohuwa ta ce, "Ai kuwa da kin kyauta, 'yar nan. Kan nan nawa duk ƙyaya ce, ba ta ko bari in runtsa."

Suka fita waje, Zumurrazi ta zaunar da tsohuwa a gabanta. Ta kama kanta ta tsefe, ta riƙa kashe mata kwarkwata. Wannan ya sa tsohuwa ta ji sauƙin cizon da kwarkwatar ke yi mata, ta ji daɗi cikin kanta, nan take sai ta fara gyangyaɗi, jim kaɗan sai barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita, ko banza ga gajiyar tafiya da ta yi da ɗanta.

Zumurrazi ta tashi da sauri ta ɗauki kayan matafiyin nan da ɓarawo ya kashe ta sanya. Ta naɗa rawani ta yi amawali ta rufe fuskarta, ta ɗauki takobi ta rataya, duk wanda ya gan ta sai ya rantse da abin da zai kashe shi cewa namiji ne. Ta ɗauki jakar da ta ɗauko daga gidan Banasare ta kwance doki ta ɗare bisa bayansa. Ta ce a cikin ranta, "Ya mai kare bayinsa, na roƙe ka don alfarmar shugabanmu Annabi Muhammadu (SAW) ka kare ni daga dukkan sharri na mutum ko na aljani. Ina jin tsoron in shiga gari 'yan uwan wannan mutum da na sa tufafinsa su gan ni, ban san abin da zan ce musu ba in kare kaina." Sai ta juya wa gari baya, ta sakar wa doki linzami suka nufi cikin sahara.

Ta yi ta tafiya a cikin rairayin hamada, ita da dokinta, suna ci daga 'ya'yan itace, suna sha daga ruwan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment