Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙoramu tsawon kwanaki goma. A kwana na goma sha ɗaya sai ta fara hango wani kykkyawan birni a gabanta. Lokacin kuwa ya kasance lokacin ɗari ne, ta ga birnin cike da itatuwa ganyayensu tsanwa shar gwanin ban sha'awa, sun yi furanni launi daban daban. Ga tsuntsaye iri iri bisa gare su, kowane yana rera waƙa da irin kukansa. Ga kuma wata babar korama ta ratsa ta cikin garin, ruwanta garai garai yana bugun gefe da gefe na gaɓar ƙoramar yana fitar da wani sauti mai daɗi yayin da yake gudu.

Da ta yi kusa da wannan birni sai ta ga mutane masu yawa sun fito ƙofar garin sun yi tsaye cirko-cirko, kamar waɗanda suka fito tariyar wani babban mutum. Wasu a kan dawaki, wasu a kan alfadarai, wasu kuma a ƙasa, kowanensu ya caba ado. Yayin da ta gan su sai ta yi mamaki, gayar mamaki, ta ce a cikin ranta, "Waɗannan mutane wa suke jira haka? Babu shakka dai ruwa ba ya tsami banza." Sai ta nufi inda suke, gabanta na faɗuwa.

Yayin da mutanen nan suka hango ta sai suka yiwo ca zuwa gare ta. Suka tare ta da girmamawa, suka sauka daga kan dabbobinsu. Suka faɗi ƙasa gaba ɗaya suna yi mata gaisuwa, suna cewa, "Allah ya ja zamaninka ya Sarkinmu, Shugaban Muminai."

Ta ga wasu masu tiƙa-tiƙan rawunnan sun ware gefe guda, dogarai suka yi nasu sahu, sauran talakawa su ma suka ware gefe guda suna ta faɗin, "Allah ya kare ka, Allah ya yi maka jagora ya Sarkin Musulmi." Zumurrazi dai ta kasa kannewa ta tambaye su, "Me ke faruwa ne jama'a? Wanene kuma Sarkin Musulmi?"

Masu manyan rawunnan nan, waɗanda ta fahimci fadawa ne, suka amsa mata, "Haƙiƙa wannan wanda ba ya zaɓe a wurin kyautata wa bayinsa, ya yi maka babbar baiwa ta zama Sarkinmu, kuma Sarkin Musulmin wannan ƙasa tamu baki ɗaya. Ka sani cewa al'adar wannan ƙasa ce idan Sarki ya mutu bai bar ɗa wanda zai gaje shi ba, jama'ar birni sukan fito su tsaya a nan bayan gari tsawon kwana uku. Duk mutumin da Allah ya jeho ta wannan hanyar da ka biyo, to, shi za mu naɗa a matsayin sabon Sarkinmu. Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya turo mana kai. Muna fatar ka zama Sarki mai adalci mai tausayi." Da Zumurrazi ta ji haka, sai ta ɗaga hannuwanta sama ta yi wa Allah godiya da ya kuɓutar da ita daga wahala kuma ya yi mata wannan babbar baiwa.

Daga nan sai dogarai da fadawa da sauran jama'ar gari suka raka ta zuwa fada. Da zuwansu sai wasu dogarawa suka riƙa mata, ta sauka daga kan dokinta suka shiga fada da ita, suka aza ta bisa karagar mulki, ita kuwa ta harɗe abinta. Duk wannan bidiri da ake yi mutane ba su gane cewa mace ce ba, saboda sunƙe fuskarta da ta yi da amawalin rawani.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, insha Allah.

Bukar Mada
10/12/2022SOYAYYA GAMON JINI 7

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Waziri Aku

Daga nan sai dogarai da fadawa da sauran jama'ar gari suka raka ta zuwa fada. Da zuwansu sai wasu dogarawa suka riƙa mata, ta sauka daga kan dokinta suka shiga fada da ita, suka aza ta bisa karagar mulki, ita kuwa ta harɗe abinta. Duk wannan bidiri da ake yi mutane ba su gane cewa mace ce ba, saboda sunƙe fuskarta da ta yi da amawalin rawani.

Bayan sun zaunar da ita bisa karaga, sai duk suka faɗi ƙasa suka yi gaisuwa a gabanta, suka yi mata mubayi'a. Ta kira ma'aji ta ce ya buɗe taska ya kwaso mata dukiya. Da ya kwaso mata ta karɓa ta yi ta raba wa mutane. Jama'a suka yi ta yi mata addu'a suna mata fatar ɗorewa bisa karagar mulki, dukansu suka yi murna da zamanta sabon Sarki.

Haka ta ci gaba da zama a cikin wannan gari tana shimfiɗa mulkinta bisa ga adalci. Ta rage wa talawa kuɗin haraji, ta sallami 'yan sarkan garin masu ƙananan laifuka. Ta kasance mai yawan kyauta ga askarawa da fadawanta. Jama'ar gari duk suka so ta, suna yi mata addu'ar fatar alheri. Amma abu ɗaya yake damunta a rai, wannan abu kuwa shi ne rabuwa da shugabanta Alisharu. Duk lokacin da ta tuna wannan abu sai hawaye ya yi ta zuba daga idanunta, ta yi ta rera waƙoƙin bege, tana addu'ar Allah ya sake haɗa su da gaggawa. Ta tashi manzanni ta aika su garin da ta bari domin a nemo mata masoyinta.

A cikin gidanta kuwa sai ta ware wa dukkan kuyangi da bayinta shiyyarsu daban. Ita kuma ta keɓe wani ɗaki nata, ta zaɓi wasu ƙananan kuyangi guda biyu waɗanda za su riƙa shiga wurinta. Ta faɗa wa sauran kuyangi da bayi cewa ba ta buƙatar kowa ya riƙa shiga wurinta sai waɗannan kuyangi biyu, domin tana so ta sadaukar da kanta wurin ibada. Ta duƙufa ga azumi da sallar dare kullum, har bayi da kuyangi suka riƙa gulma a tsakaninsu suna cewa, "Lalle wannan Sarki mai yawan ibada ne." Sai ya kasance babu mai shiga inda take sai waɗannan kuyangi biyu da ta keɓe.

Zumurrazi ta ci gaba da mulki har shekara guda amma ba ta sami labarin Alisharu ba. Manzannin da ta tura ma tuni suka dawo babu labarinsa. Hakan ya sa ta shiga cikin tsananin damuwa da tunani. Wata rana sai ta kira wazirai da fadawanta, ta umurce su da cewa su samo mata ƙwararrin masu gini. Ta ce musu tana so a gina mata wani babban ɗakin taro a nan ƙofar fadarta. Nan take kuwa suka cika umurninta, suka nemo magina suka dukufa ga aikin gina babban ɗaki har suka gama shi kamar yadda take so. Ta sa aka yi wani ɗan dakali daga gaban ɗakin taro, aka haƙa mata karagarta saman dakalin, aka kuma shirya karagun wazirai da na fadawa kusa ga tata karagar, duk a saman dakalin. Cikin ɗakin kuma duk aka shirya abubuwan zama waɗanda za su iya ɗaukar dukkan mutanen garin.

Ta sa aka shirya abinci da nama da 'ya'yan itace da abin sha iri iri. Ta zauna tare da dogarawa da wazirai da fadawanta suka ci suka sha suka yi hani'an. Daga nan ta ce musu ina so a yi shela cikin gari, a gaya wa mutane cewa, kowace rana ta farkon wata su hallara cikin wannan ɗakin taro, su ci su sha kyauta daga alherina. Ba na so kowa ya buɗe rumfarsa a wannan rana, ina so a haɗu nan gaba ɗaya, ko da mutum ba ya da sha'awar ci daga abincin Sarki, wanda kuma ya ƙi zuwa wannan ɗaki to zan sa a rataye shi a gaban gidansa.

Fadawa suka yi yadda ta umurce su. Da ranar farko ta wata ta zo, Zumurrazi ta shiga cikin ɗakin taro tare da wazirai da fadawanta, kowa ya harɗe bisa karagarsa. Mai shela kuwa ya shiga gari yana cewa, "Ya ku mutanen wannan birni, manya da yara, ku yi gaggawa zuwa ga ɗakin taro ku ci abincin da Sarki ya shirya domin ku. Wanda duk ya kuskura ya buɗe rumfarsa a cikin wannan rana, za a rataye shi a gaban ƙofar gidansa." Mutane duka suka nufi ɗakin taro cike da farin ciki, suna mamakin alherin wannan Sarki.

Aka shirya abinci da abin sha iri iri a kan abubuwan zama, kowane mutum ya zauna da akushin abinci a gabansa. Ita kuma Zumurrazi da fadawanta suna zaune bisa karagun mulkinsu da aka haƙa bisa dandamali, suna kallon kowane mutum da yake cikin ɗakin. Mutane suka fara cin abinci, duk lokacin da wani ya ɗago kansa sai ya ga kamar shi kaɗai Sarki ke kallo, sai ya duƙufa ga cin abinci. Fadawa suka riƙa ce wa mutane, "Ku ci abin da ranku yake so, kada ku ji kunya, domin ku Sarki ya shirya wannan abinci."

Mutane suka ci suka ƙoshi, suka fita suna godiya ga Sarki suna ce wa junansu, "Wallahi ba mu taɓa ganin Sarki mai ƙaunar talakawansa kamar wannan ba." Suka yi ta yi mata addu'a da fatar alheri. Bayan mutane sun watse sai Zumurrazi ta shige gidanta cike da farin ciki, tana cewa a ranta, "Idan Allah Maɗaukakin Sarki ya yi murna da wannan alheri na ciyarwa da nake aikatawa ga talakawa, babu shakka wata rana zan sami labarin shugabana Alisharu."

gumurzu


Yayin da sabon wata ya kama, a rana ta farko mutane suka ƙara haɗuwa a cikin ɗakin taro. Aka gabatar musu da abinci da abin sha, kamar yadda aka yi a watan farko. Zumurrazi na zaune bisa karagarta tana kallon mutane suna cin abinci sai idanunta suka faɗa kan Banasaren nan, Barsumu, wanda ya sayi labule daga hannun Alisharu ya sa masa banju a cikin ayaba. Tana ganinsa ta shaida shi, ta ce a cikin ranta, "Wannan shi ne mutum na farko da zan fara ɗaukar fansa a kansa."

Barsumu na zaune da akushin abinci a gabansa, sai ya ƙyalla ido ya hango akushin farar shinkafa wadda aka yayyafa wa ruwan sukari, nesa da inda yake zaune. Sai kuwa yawunsa ya kawo, ya ture akushin da ke gabansa, ya tashi ya nufi wurin wannan shinkafa. Ya zauna ya jawo akushin shinkafa zai fara ci, sai wani mutum dake zaune kusa gare shi ya ce, "Me ya sa ka baro akushinka ka dawo nan? Ba ka jin kunya ka bar akushinka, ka keto mutane kana taka su saboda akushin shinkafa?"

Barsumu ya ce, "Babu ruwanka, abin da nake so shi zan ci."

Mutumin ya ce, "Ci, amma dai babu amfani ga wannan abu da ka aikata."

Daga nan sai wani saurayi, mashayin ganye, ya tsoma musu baki ya dubi mutumin ya ce, "Kai ina ruwanka da abin da mutum zai ci? Bari in taso mu ci shinkafar tare da shi, ni ma ita nake sha'awa."

Sai mutumin nan ya dubi saurayin nan a yatsine yace, "To, ai ba ganye ba ne a cikin akushin, balle ka yi kumfar baki don an hana ka ci."

Barsumu dai bai kula da su ba sai ya fara cin shinkafa. Ya yi loma ɗaya, ya ɗebi ta biyu zai kai ga baki Zumurrazi ta yi wa dogarawa tsawa, "Ku kawo mini mutumin can mai ci daga akushin shinkafa, kada ku bar shi ya kai lomar da ke hannunsa baka."

Dogarawa huɗu suka zabura suka nufi wurin Barsumu, suka kwaɓe lomar da ke hannunsa, suka cakume shi suka kai gaban Zumurrazi. Mutane duka suka dakata da cin abinci, sai wannan ya dubi wannan, wannan ya dubi wannan, suna cewa da juna, "Wallahi ya aikata laifi, me ya sa ya ki tsayawa ga abincin da aka tanadar masa? Ƙarshen mai ruwan ido ke nan."

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, insha Allah.

Bukar Mada
14/12/2022SOYAYYA GAMON JINI 8

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Waziri Aku

Dogarawa huɗu suka zabura suka nufi wurin Barsumu, suka kwaɓe lomar da ke hannunsa, suka cakume shi suka kai gaban Zumurrazi. Mutane duka suka dakata da cin abinci, sai wannan ya dubi wannan, wannan ya dubi wannan, suna cewa da juna, "Wallahi ya aikata laifi, me ya sa ya ki tsayawa ga abincin da aka tanadar masa? Ƙarshen mai ruwan ido ke nan."

Wani kuma ya ce, "Abincin da aka ajiye gabana ya ishe ni, ba ni da kwaɗayin wani."

Shi kuwa saurayin nan mashayi, da ya ga an cafke Barsumu a kan cin shinkafa, sai ya ce, "Wai! Yau Allah ya so ni, da kwaɗayina ya ja mini halaka."

Sai mutane suka riƙa cewa da juna, "Bari mu ga abin da zai faru gare shi."

Dogarawa suka durƙusar da Barsumu a gaban Zumurrazi. Ta dube shi ta daka masa tsawa, "Menene sunanka? Kuma daga ina ka fito?"

Sai tsinannen mutumin nan, da yake ya naɗa rawani fari a kansa, ya canja suna ya ce, "Allah ya ba ka nasara ya Sarki. Sunana Aliyu, ni masaƙi ne na zo wannan birni domin yin kasuwanci."

Zumurrazi ta dubi wani dogari ta ce, "Kawo mini yashi a cikin faifai da alƙalamin tagulla." Nan take ya tafi ya kawo mata abin da ta nema. Ta share yashin da tafin hannunta, ta ɗauki alƙalami ta yi wani zane mai kama da siffar biri bisa yashin. Ta daɗe tana nazarin abin da ta zana, can sai ta ɗaga kanta ta dubi Barsumu ta yi masa tsawa, "Ya kai kare! Don me kake yi wa Sarakuna ƙarya? Ba kai ba ne Banasare mai suna Barsumu? Kuma ka zo wannan birni domin neman wani abu, ba kasuwanci ne ya kawo ka ba. Gaya mini gaskiya ko in sa a fille kanka yanzu!"

Yayin da Barsumu ya ji haka, sai ya kiɗime, jikinsa ya ɗauki ɓari. Da mutane suka ga haka sai suka riƙe baki cikin mamaki suna cewa, "Lalle Allah ya hore wa Sarkin nan namu ilimi mai yawa. Har da ilimin taurari ya sani."

Zumurrazi ta sake daka wa Barsumu tsawa, "Gaya mini gaskiya ko kuwa yanzu ka ɗanɗani gidauniyar mutuwa."

Barsumu ya duƙar da kansa ƙasa yana cewa, "Allah ya ba ka nasara, haƙiƙa alƙalaminka ya nuna maka gaskiya. Wannan bawa naka ba kowa ba ne face Banasare Kirista. Ina neman afuwa gare ka." Duka mutanen da ke wurin suka cika da mamakin yadda Sarki ya san ilimin taurari haka.

Zumurrazi ta ba da umurni a tafi da Barsumu a feɗe fatarsa a cika ta da ciyawa, ayi mutum-mutumi da ita a sagale shi daga wajen ƙofar shigowa ɗakin taron. Naman da ƙasusuwan kuma a tafi da su bayan gari a gina rami a ƙona su, a kwashi tokar a watsar, iska ta tafi da ita. Dogarawa suka ce mun ji mun karba. Suka tafi suka aikata abin da Zumarrazi ta umurce su. Aka sagale mutum-mutumin Barsumu a bakin ƙofar ɗakin taro. Mutane kuwa kowa sai faɗin albarkacin bakinsa yake yi. Wani ya ce, "Har abada kuwa ba na cin farar shinkafa a gaban Sarki." Wani kuma ya ce, "Ai gwamma in saki matata saki uku da in ci farar shinkafa a gaban Sarki." Saurayin nan mashayi kuwa sai cewa yake yi, "Yau Allah ya so ni, da yanzu an kashe ni tare da wannan mutum." Mutane duka suka watse suna tunanin abin da ya faru.

Da ranar farko ta wata na uku ta zagayo, aka shirya abinci a cikin ɗakin taro. Zumurrazi ta zo tare da fadawa da dogarawa suna take mata baya, suka taka dandamali suka zauna bisa karagunsu. Daga nan sai mutanen gari suka shigo kamar yadda suka saba. Kowa ya sami wurin zama ya zauna amma babu wanda ya zauna ga akushin shinkafa. Sai wani mutum ya dubi ɗan uwansa ya ce, "Ya kai Alhaji Halifa." Sai ɗayan ya amsa, "Na'am Alhaji Halidu." Wanda aka kira da Alhaji Halidu ya ce, "Kada ka ci daga akushin shinkafa, idan kuwa ka ci za a rataye ka." Suka zauna ga akussan nama suna ci.

Mutane na cikin cin abinci sai Zumurrazi ta ga wani mutum ya shigo ɗakin taron cikin hanzari. Da ta dube shi da kyau sai ta gane Jiwanu ɗan Kurdu ne ɓarawon nan da ya sace ta. Dalilin zuwansa wannan birni shi ne, lokacin da ya bar Zumurrazi da mahaifiyarsa a cikin kangon gida sai ya nufi wurin sauran ɓarayi ya ce musu, "Wannan tafiya tawa ta yi sa'a. Na kashe wani mutum na ɗauke dokinsa da tufafinsa masu tsada. Bayan haka kuma ina cikin yawon neman gidan da zan fasa, sai na ga an jeho mini wata jaka cike da zinariya daga wata taga. Sai kuma wata kyakkyawar budurwa ta diro daga kan tagar, ni kuwa na cafe ta na tafi da ita kangon gidan nan na bar ta wurin mahaifiyata. Yanzu haka da ita da jakar zinariyar da kuma dokin mutumin da na kashe duk suna nan ajiye."

Yayin da ɓarayi suka ji haka sai suka yi murna, da dare ya yi tsaka suka tashi gaba ɗaya suka nufi kangon gidan. Amma da suka isa sai ba su tarar da kome ba sai tsohuwar nan tana barci. Jiwanu ya tayar da ita ya tambaye ta ina yarinyar da ya bari tare da ita? Ta gaya masa abin da ya faru tsakaninta da Zumurrazi, ta ce ita tun da barci ya kwashe ta ba ta ƙara sanin abin da ya faru ba. Da ya ji haka sai ya riƙa tafa hannu cikin takaici ya ce cikin fushi, "Na rantse da Allah sai na nemo wannan karuwa duk inda ta shiga, ko a cikin kwasfar gyaɗa ta ɓoye sai na gano ta domin in kashe ƙishirwar sha'awata gare ta." Daga nan sai ya fita neman ta, ya yi ta tafiya daga wannan wuri zuwa wancan har Allah ya jeho shi cikin wannan gari da Zumurrazi ke mulki.

Lokacin da ya shigo garin sai ya ga kamar an share mutanen garin, babu kowa a waje. Ga kuma rumfuna a rufe. Ya tambayi wasu mata da ya ga suna leƙe ta taga, suka gaya masa ai mutane duka suna babban ɗakin taro wajen cin liyafar da Sarki ke shiryawa duk ranar farko ta wata. Suka yi masa kwatancen wurin, ya tafi yana sauri yana lasar baki, dama yana cike da shegiyar. Da ya shiga ɗakin taron sai ya ga kowa ya sami wurin zama ya zauna yana cin abin da aka ajiye a gabansa. Ya duba ko'ina bai ga wurin zama ba sai inda aka ajiye akushin shinkafa. Don haka sai ya je ya zauna gaban akushin shinkafa, ya janye hannun rigarsa ya saka hannunsa cikin akushi.

Wani mutum ya dube shi cikin kaɗuwa ya ce, "Kai ɗan uwa, me za ka yi?"

Jiwanu ya ce, "Zan ci daga wannan akushi na shinkafa."

"Idan kuwa ka ci shinkafar nan babu makawa kashe ka Sarki zai sa a yi, domin ba ya so ana cin shinkafa a gabansa." In ji mutumin.

Jiwanu ya ce, "Ƙyale ni, ko me zai same ni ya same ni amma sai na ci wannan shinkafar. Da Sarki bai so a ci shinkafa a gabansa da ba a kawo ta nan ba." Saurayin nan mashayi na kusa yana sauraren su, lokacin kuwa ya yi sha kansa ya juya, sai ya baro wurin zamansa ya zo kusa ga Jiwanu ya zauna ya ce, "Ni ma ina da sha'awar cin shinkafar nan."

Jiwanu ya sa hannunsa mai kama da ƙafar jimina a cikin akushi, ya kwaso rabin shinkafar da ke cikin akushin, har kasan akushin ya bayyana. Ya rumƙe shinkafar a cikin tafin hannunsa, ya riƙa mulmula ta har ta dunƙule wuri guda ta zama tamkar wani ƙaton lemu. Ya jefa ta gaba ɗaya a cikin ƙaton bakinsa, ya yi mata haɗiya guda. Ta bi ta cikin maƙogwaronsa ta faɗa cikin tumbinsa da wata irin ƙara mai kama da saukar aradu.

Wani mutum da ke kusa gare shi ya tsorata, ya dakata da cin abinci, ya ƙwaƙƙwale idanu yana kallon ikon Allah. Ya dubi akushin shinkafa ya ga Jiwanu har ya ci rabinsa a cikin loma guda.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, insha Allah.

Bukar Mada
17/12/2022
SOYAYYA GAMON JINI 9

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Jiwanu ya sa hannunsa mai kama da ƙafar jimina a cikin akushi, ya kwaso rabin shinkafar da ke cikin akushin, har kasan akushin ya bayyana. Ya rumƙe shinkafar a cikin tafin hannunsa, ya riƙa mulmula ta har ta dunƙule wuri guda ta zama tamkar wani ƙaton lemu. Ya jefa ta gaba ɗaya a cikin ƙaton bakinsa, ya yi mata haɗiya guda. Ta bi ta cikin maƙogwaronsa ta faɗa cikin tumbinsa da wata irin ƙara mai kama da saukar aradu.

Wani mutum da ke kusa gare shi ya tsorata, ya dakata da cin abinci, ya ƙwaƙƙwale idanu yana kallon ikon Allah. Ya dubi akushin shinkafa ya ga Jiwanu har ya ci rabinsa a cikin loma guda. Ya dube shi ya ce, "Na gode wa Allah da bai yi ni shinkafa ba! Dubi yadda ka kusa cinye akushin shinkafa cikin loma guda."

Jiwanu bai kula ba, ya kara sa hannunsa cikin akushin shinkafa, ya damke sauran da ta rage a cikin hannunsa. Ya fara dunkula ta ke nan a cikin hannunsa, sai Zumarrazi ta yi wa dogarai tsawa, "Ku kawo mini wancan mutum mai ci daga akushin shinkafa! Kada ku bari ya kai lomar hannunsa cikin baki." Suka zabura da sauri suka kama Jiwanu, suka ride shi sama, duk karfinsa, suka saba ga kafada suka kai shi gaban Zumarrazi.

Mutane suka rika cewa, "Ai sai da muka gargade shi kada ya zauna ga akushin shinkafa, amma bai ji gargadinmu ba. Wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho." Zumarrazi ta dubi Jiwanu ta tambaye shi sunansa da dalilin zuwansa birninta. Sai kuwa ya karkace kai ya ce, "Allah ya taimake ka, sunana Usmanu, sana'ata lambu. Na zo wannan birni neman wani dan uwa nawa da ya bace."'

"Ku kawo mini faifai da yashi da alkalamin tagulla." In ji Zumarrazi.

Aka kawo mata abin da ta bukata. Ta sa hannu ta share rairayin, ta yi zane da alkalamin tagulla bisa ga rairayin. Ta yi jim tana nazarin abin da ta zana, zuwa wani dan lokaci ta dago da kanta ta dubi Jiwanu, "Makaryacin banza! Don me ka gaya mini karya? Wannan zanen ya nuna mini cewa sunanka Jiwanu dan Kurdu, daya daga cikin yaran kasurgumin dan fashin nan Ahamadu Danafi. Ba ka da wata sana'a sai ka tare falke ka kashe shi ka kwashe dukiyarsa. Allah kadai ya san adadin rayukan bayin Allah da ka kashe." Ta daka masa tsawa, "Gaya mini gaskiya ko in sa a fille kanka yanzu!"

Da ya ji haka sai tsoro ya kama shi, launin fuskarsa ya canja, bakinsa ya rika rawa hakoransa na haduwa kaf kaf kaf, kamar wanda ruwan kankara ya yi wa duka. Ganin cewa Sarki ya gane shi, sai ya yanke shawarar ya fadi gaskiya, watakila ya sami sassauci daga Sarki. Sai ya sunkuyar da kansa kasa cikin ladabi ya ce, "Allah ya ba ka nasara, duk abin da ka fadi game da ni gaskiya ne. Amma yanzu na tuba a nan gabanka, na yi alkawari ba zan kara sata ba har abada. Zan ci gaba da neman gafara ga Allah Madaukakin Sarki."

Zumarrazi ta ce, "Ban yarda da wannan tubar muzuru taka ba, ba zan bar annoba a cikin al'ummata ba." Ta juya wurin dogarawa ta ce, "Ku tafi da shi ku fede fatarsa, ku aikata masa kamar yadda kuka yi wa Banasaren nan a watan da ya wuce." Nan take masu fushi da fushin wani suka tafi da shi, suka aikata kamar yadda Sarki ya umurce su. Aka rataye mutum-mutuminsa a bakin kofar dakin taro.

Yayin da mashayin nan ya ga abin da ya faru ga Jiwanu, sai ya dafe kirjinsa cikin kaduwa, ya juya wa akushin shinkafa baya yana cewa, "Babban zunubi ne a gare ni in dube ka. Har abada ba zan ci shinkafa ba." Bayan an gama cin abinci, mutane suka watse kowa na tofa albarkacin bakinsa bisa ga abin da ya faru, dukansu suka camfa akushin shinkafa, suna cewa akushin mutuwa ne, kowa ya ci shi babu makawa sai an kashe shi.

Yayin da ranar farko ta wata na hudu ta zagayo, aka shirya abinci a cikin dakin taro kamar yadda aka saba. Mutane kowa ya zauna a gaban akushi suna jiran izini fara ci daga Sarki. Zumarrazi ta shigo tare da fadawanta ta zauna bisa karagarta, sauran fadawa duka suka zauna. Ta dubi mutane sai ta ga babu wanda ya zauna ga akushin shinkafa, ta yi dariya a ciki. Ta ba da izini a ci gaba da cin abinci. An fara cin abinci kenan, sai ta ga wani tsoho ya shigo dakin da sauri. Tana lura da tsohon nan ta ga ya duba ko'ina bai ga wurin zama ba, sai ya nufi wurin akushin shinkafa ya zauna. Ko da ta sake duban tsohon nan da kyau sai ta gane ashe la'anannen tsohon nan ne Banasare, wanda ya kira kansa da suna Rashidu. Sai ta ce a cikin ranta, "Hakika wannan dabara ta ciyarwa ta yi mini amfani, ga shi makiyana suna fadawa cikin tarko ba tare da sun sani ba." Shi kuma dalilin zuwansa wannan birni shi ne, lokacin da ya dawo daga tafiya sai kuyangi suka shaida masa cewa Zumarrazi ta gudu tare da jaka cike da zinariya. Da ya ji haka sai ya yayyaga tufafinsa don hushi, ya rika marin fuskarsa yana tsige gemanyarsa. Ya kira dan uwansa Barsumu ya gaya masa abin da ya faru, ya umurce shi da ya nemo masa ita duk inda ta

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment