Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga cikin duniya. Bayan Barsumu ya yi wata guda da tafiya bai ji labarinsa ba, sai shi ma ya shirya ya biyo bayansa. Kwanci tashi har Allah ya kawo shi wannan birni, ya kuwa iso a ranar farko ta sabon wata. Da ya shigo cikin gari bai ga kowa ba sai mata da ke leke ta taga. Ya tambaye su abin da ke faruwa, suka gaya masa. Suka kuma yi masa kwatance da dakin taron.

Da isarsa dakin taron ya duba ko'ina bai sami wurin zama ba, sai ya zauna ga akushin shinkafa. Ya jefa hannunsa cikin akushi ya debo shinkafa zai kai ga bakinsa ke nan sai Zumarrazi ta yi wa dogarawa tsawa, "Ku kawo mini mutumin can da ya zauna ga akushin shinkafa!" Dogarawa suka sabe shi ga kafada suka kai gaban Zumarrazi suka yar.

Ta dube shi ta ce, "Kai! Menene sunanka? Me kuma ya kawo ka birninmu?"

"Ya Sarkin zamani," Rashidu ya amsa, "sunana Rustamu, ni talaka ne ba ni da wata sana'a sai bara. Allah ya ba ka nasara."

Zumarrazi ta ce a kawo mata rairayi cikin faifai da alkalamin farin karfe. Da aka kawo mata sai ta share rairayi ta dauki alkalami ta yi wasu zane-zane bisa rairayin. Bayan ta gama nazarin zane-zanen sai ta dago da kanta cikin fushi ta dubi Rashidu ta yi masa tsawa, "Karya kake yi, tsohon banza! Don me ka gaya mini karya? Sunanka Rashidu Banasare, a fuska kana nuna kai Musulmi ne bayan kuwa a karkashin zuciyarka kai Kirista ne. Sana'arka cinikin kuyangi, idan ka sayi Musulmi sai ka mayar da su Kirista, ko ba haka ba ne? Fadi gaskiya ko in sa a tsire ka."

Ya yi shiru bai ce kome ba ya sunkuyar da kansa kasa. Wani dogari ya matso ya kwashe shi da tafi har sai da ya fadi, ya ce masa, "Sarki ke magana ka yi masa damo kamar wani mummuni!"

Rashidu ya amsa a gigice, bakinsa na rawa, "Iye, na'am. Hakika abin da ka ce gaskiya ne, ya Sarkin zamani."

Ta sa aka cire masa takalmi, aka samo mata tsumagiya mai karfi. Ta tashi da kanta ta yi masa bulala dari dari, a bisa kowane tafin kafarsa. Sa'annan ta ce a yi masa wasu bulolin dubu a jikinsa. Da aka gama bugunsa ta ce a tafi da shi a fede fatarsa, a cika ta da harawa a yi mutum-mutumi da ita. Naman da kasusuwan kuma a gina rami a bayan gari a kone su. A zuba shara da kwata bisa ga tokar. Aka aikata kamar yadda ta umurta.

Bayan mutanen gari sun ci sun koshi sai suka fita daga dakin taro, kowa yana tofa albarkacin bakinsa game da akushin shinkafa. Zumarrazi kuwa ta koma gidanta cike da farin ciki tana mai godiya ga Allah da ya ba ta damar daukar fansa ga mutanen da suka cutar da rayuwarta. Ta wake wadannan baitoci tana cewa:

"A'aha, dube su lokacin da suke da karfi da iko, suna ganin kansu tamkar wasu duwatsu don girman kai. Da a ce sun yi adalci, da an yi musu adalci. Amma sai suka yi zalunci, aka aikata musu daidai da irinsa. Aka share su daga doron kasa, tamkar ba a taba yin su ba. Kada ku zargi zamani da yi muku zalunci, zaluncinku ne ya koma muku"

Bayan ta gama wannan waka sai shugabanta Aliyu Sharu ya fado mata ga rai. Nan take annurin fuskarta ya gushe, kwalla ta cika mata ido, ta ce a cikin ranta, "Babu shakka Allah da ya sanya makiyana suka fada cikin hannuna wata rana zai kawo mini abin kaunata har nan. Domin shi ne mai aikata yadda ya so, mai tausayi ga bayinsa." Ta roki Allah Mai girma da daukaka da ya kaddara saduwarta da abin begenta Aliyu Sharu.

Za mu ci gaba in sha Allah.

Bukar Mada
21/12/2022

...

Rubutun yau fa sai haƙuri, ayyuka sun sha kaina 'yan kwanakin nan. Yau ma don mutane da yawa sun yi ta kirana kan ba su ga cigaban labarin ba, na so na bari sai ranar asabar idan na gama shirya shi yadda ya kamata. To, amma ga shi dai haka nan na ɗebo muku daga tsohon rubutun da na yi, ban gyara shi yadda ya kamata ba. Haruffa babu lanƙwasa, waƙa babu baituka balle ƙafiya. Ban kuma samu lokacin binciko hoton da ya dace a ɗora ba.

A karanta da haƙuri.SOYAYYA GAMON JINI 10

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Waziri Aku

Zumarrazi ta roƙi Allah Mai girma da ɗaukaka da ya ƙaddara saduwarta da abin begenta Aliyu Sharu. Ta yi ta rera waƙoƙi saboda bege.

Ta ci gaba da mulki, tana umurni tana hani, tana shari'a tsakanin mutane da adalci. Idan dare ya yi kuma sai ta duƙufa ga roƙon Ubangiji domin ya sada ta da shugabanta Aliyu Sharu. Haka ta kasance har wannnan wata ya ƙare, sabon wata ya kama.

A ranar farko ta wata na biyar, ta sa aka shirya abinci a cikin ɗakin taro kamar dai yadda akan yi duk wata, ta zauna tare da fadawanta. Mutane kowa ya sami wuri ya zauna, ana jiran umurnin fara cin abinci daga Sarki, aka bar akushin shinkafa mawofanci.

Zumarrazi ta ƙura wa ƙofa ido, tana kallon mutane masu shigowa, ta riƙa addu'a a cikin zuciyarta, "Ya wanda ya sadar da Yusufa ga mahaifinsa Yaƙuba bayan rabuwa. Ya wanda ya yaye cutar Ayuba, don alfarmar Shugabanmu Annabi Muhammadu (SAW) ka sada ni da shugabana Aliyu Sharu. Ya mai jin roƙon wanda ya roƙe shi. Ya mai amsa addu'ar bayinsa. Ka karɓi addu'ata, ka sada ni da shugabana Aliyu Sharu."

Allah ma ji roƙo! Tana rufe bakinta sai ta ga wani kyakkyawan saurayi ya shigo ɗakin cin abincin. Wannan saurayi yana da jiki madaidaici kamar iccen turare, shi ba siriri ba kuma ba mai ƙiba ba. Yana da kyakkyawar fuska, sai dai fuskar tasa ta ɗan kumbura saboda yawan kuka. Da ya shigo cikin ɗakin ya duba bai ga wurin zama ba, sai ya nufi inda aka ajiye akushin shinkafa.

Tun lokacin da Zumarrazi ta ga wannan saurayi ta shaida shi a matsayin shugabanta Aliyu Sharu. Zuciyarta ta riƙa bugawa da sauri, ta ji kamar ta tashi ta je ta rungume shi don farin ciki, ta yi ƙarfin hali ta kanne farin cikinta domin kada fadawanta da sauran jama'a su gane halin da take ciki.

Yadda aka yi Aliyu Sharu ya zo wannan gari kuwa shi ne, bayan ya farka daga barcin da ya kwashe shi a ƙarƙashin tagar gidan Banasare, ya laluba kansa bai ji rawaninsa ba, ya duba ƙasa ko ya faɗi lokacin da yake barci, bai gan shi ba. Sai ya tabbatar da cewa wani mutum ya zo wurin nan, kuma babu makawa ya ɗauke Zumarrazi ya tafi da ita, sai ya furta kalmar nan wadda mai faɗin ta ba ya tozarta watau, "Daga Allah muke, kuma gare shi muke komawa, (innalillahi wa inna ilaihirraji'un)."

Ya tashi ya nufi gida cike da baƙin ciki, ya gaya wa tsohuwa abin da ya faru. Daga nan ya fashe da kuka har sai da ya shiɗe. Bayan ya farfaɗo tsohuwa ta zarge shi da yin sakaci ta ce, 'Wannan ai laifinka ne, kome ya same ka ba ka da kaico!" Ta ci gaba da aza masa laifi har saboda baƙin ciki jini ya riƙa fita daga cikin hancinsa, ya ƙara faɗuwa ƙasa sumamme.

Yayin da ya farfaɗo sai ya ga tsohuwan nan bisa kansa tana kuka. Ya yi ƙarfin hali ya tashi zaune, idanunsa cike da hawaye. Tsohuwa ta tausaya masa, ta ce, "Ka zauna nan har in shiga cikin gari in samo maka labarin abin da ya faru ga kuyangarka." Ya ce mata, to.

Ta tashi ta shirya ta shiga cikin gari, ba ta dawo ba sai da rana ta take. Bayan ta dawo sai ta ce masa, "Ya ɗana, ina jin tsoro wataƙila rayuwarka za ta salwanta saboda baƙin ciki. Haƙiƙa yana da wahala ka sake ganin kuyangarka har abada, wataƙila sai a Darussalam. Domin kuwa na tafi gidan Kiristan nan, kuyangi sun shaida mini cewa Zumarrazi ta gudu har ma da jakar kuɗin Kiristan tare da ita, kuma sun tarar da tagar da ta fita a cikinta buɗe. Babu tsimi babu dabara face daga Allah Maɗaukakin Sarki."

Yayin da Aliyu Sharu ya ji wannan mummunan labari sai hasken da ke fuskarsa ya gushe, hawaye ya yi ta tarara daga idanunsa kamar ruwa. Nan take zazzaɓi mai tsanani ya rufe shi. Ya kwanta a gidansa cikin halin ciwo tsawon shekara guda. Tsohuwa ta yi ta ɗawainiya da shi, ta kira masa bokaye da 'yan ɗibbu da masu bugun taurari suna yi masa magani, amma duk a banza. Daga nan sai ta koma shirya masa abinci mai kyau da abin sha. Yana ci yana sha a hankali har ƙarfin jikinsa ya soma dawowa.

Da tsohuwa ta ga jikinsa ya fara ƙarfi ga shi kuma har shekara ta biyu ta shigo yana kwance, sai ta ce masa, "Ya ɗana, wannan kwanci naka da damuwar da kake ciki ba za su maido maka da kuyangarka ba. Ka yi ƙarfin hali ka tashi ka shiga duniya wurin nemanta, wataƙila Allah ya yi maka gamo da katar ku sadu da juna." Ta yi ta ƙarfafa masa gwiwa har ya yarda. Ta tafi da shi ɗakin wanka, ya yi wanka. Ta kawo masa naman kaji da zuma ya ci ya ƙoshi. Haka ta riƙa yi masa kullum tsawon wata guda, ya fara murmurewa, ya maida jikinsa, ƙarfinsa ya komo. Ya shirya fita zuwa neman abar begensa Zumarrazi.

Ya fita daga gida bai san inda zai nufa ba, ya dai yi addu'a ga Allah Ubangijin talikai domin neman dacewa ga abin da ya fita nema. Ya yi ta tafiya ya shiga wannan gari ya fita, yana cigiyar abar begensa har Allah ya kawo shi garin da take mulki. Ya kuwa shigo garin a ranar farko ta sabon wata, da aka faɗa masa ɗabi'ar Sarkin garin ta ciyar da mutane a babban ɗakin taro duk ranar farko ta sabon wata, sai ya nufi ɗakin taron. Da shigarsa sai ya tasar wa akushin shinkafa saboda babu kowa a wurin.

Da mutane suka ga ya zauna ga akushin shinkafa, suka gan shi saurayi kyakkyawa sai suka gargaɗe shi, "Ɗan samari, kada ka ci daga wannan akushi domin kuwa duk wanda ya ci wannan shinkafa ƙaddara takan faɗa masa har ya rasa rayuwarsa."

Aliyu ya ce musu, "Wa yake da kwaɗayin rayuwa a cikin wannan hali da nake ciki? Ina maraba da duk wani abu da zai yi sanadin mutuwata ko na huta da wannan damuwa da nake ciki." Ya sa hannunsa cikin akushi ya ɗebo shinkafa ya kai bakinsa.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, in sha Allah.

Bukar Mada
24/12/2022SOYAYYA GAMON JINI 11

HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI

Waziri Aku

Aliyu ya ce musu, "Wa yake da kwaɗayin rayuwa a cikin wannan hali da nake ciki? Ina maraba da duk wani abu da zai yi sanadin mutuwata ko na huta da wannan damuwa da nake ciki."

Ya sa hannunsa cikin akushi ya ɗebo shinkafa ya kai bakinsa. Zumarrazi ta yi nufin ba da umurni domin a zo mata da shi gabanta, sai ta canja shawara ta ce a cikin ranta, "Wataƙila yunwa yake ji, bari ya ci ya ƙoshi tukuna sai ina sa a kawo shi wurina."

Aliyu Sharu ya ci gaba da cin shinkafa, mutane na kallonsa suna mamaki me ya sa Sarki bai sa a kama shi ba? Suka ci gaba da cin abincinsu suna jiran su ga abin da zai faru ga wannan saurayi. Da Zumarrazi ta lura cewa Aliyu ya ci ya ƙoshi, sai ta kira wasu kuyangi ta ce musu, "Ku tafi wurin saurayin can da ya ci daga akushin shinkafa, ku zo mini da shi cikin girmamawa. Ku ce masa, Sarki na so ya yi masa wasu 'yan tambayoyi in ya yarda. Idan bai yarda ba kuma ku ƙyale shi, kada ku tilasta shi."

Kuyangi suka rusuna cikin girmamawa, "To, Allah ya ba ka nasara."

Suka tafi wurin Aliyu Sharu suka ce, "Ya shugabanmu, Sarki na so ya yi maka wasu 'yan tambayoyi in ka yarda."

Aliyu Sharu ya ce, "Na ji na ɗauka."

Ya tafi tare da kuyangi, mutane na magana da junansu suna faɗin “babu tsimi babu dabara face daga Allah mai girma maɗaukakin sarki, babu shakka sarki kashe shi zai yi.”

Wasu kuma suna cewa, “alheri zai aikata masa, domin da yana da nufin cutar da shi da ba zai bari ya ci har ya ƙoshi ba.”

Daga nan aka tsayar da shi gaba ga Zumarrazi ya yi mata sallama sanna ya sumbaci ƙasa gabanta. Ta amsa masa sallamar ta karɓe shi da girmamawa. Ta tambaye shi, “menene sunanka, menene aikinka, menene sababin zuwanka wannan birnin namu?”

Ya amsa ya ce, “ya sarki, sunana Ali Sharu, ni ɗa ne a fataken Hurassana, kuma dalilin zuwana wanan gari shi ne domin neman kuyangata da ta ɓace min, ta kasance abar ƙauna gare ni fiye da jina da ganina da numfashina. Na rasa waɗannan duka tun lokacin da na rasa ta. Wannan shi ne labarina.”

Da ya kawo nan sai ya fashe da kuka mai yawa har sai da ya suma. Ta yi umarnin a zuba masa ruwa. Suka aikata haka sannan ya farfaɗo ya nutsu.

Zumurrazi ta ce musu, “ku kawo min faranti da rairayi da alƙalamin farin ƙarfe.”

Suka kawo mata abin da ta nema sannan ta duƙufa ta buga ƙasa da alƙaluma ta yi nazarinsu zuwa wani lokaci sannan ta ɗago kanta ta ce wa fadawanta, "karo na farko ke nan da na samu wanda ya faɗa mini gaskiya." Ta dubi Aliyu ta ce, "haƙiƙa ka yi gaskiya cikin zancenka. Ina roƙon Allah ya sadar da kai da abar begen ka a kusa. Kada ka damu.”

Ta sa aka kai shi wani ɗaki aka ba shi tufafi riga mai kyawo irin ta sarakuna. Sanan aka ba shi wani lafiyayyen doki keɓaɓɓe domin sarakuna. Sannan ta ce a kai shi fada idan yamma ta yi.

Wani babban bawa ya amsa da girmamawa ya ɗauke shi ya tafi da shi. Mutanen da ke wajen suka riƙa cewa, “me ya sa sarki ya yi masa irin wannan karamcin?” Wani ya ce, “ba na faɗa muku ba cewar ba zai cutar da shi ba?” Ai tunda na ga sarki ya sa an ba shi abinci ya ci ya ƙoshi na haƙiƙance ba zai masa komai ba.” Haka dai kowa na ta faɗin albarkacin bakinsa har suka gaji suka watse.

Game da Zumarrazi kuwa, ta zauna cikin matsuwar dare ya yi domin ta keɓance da abin ƙaunarta. Yayin da duhu ya yi sai ta kwanta a wurin barcinta, ta yi kamar tana barci bayinta suka tsammaci haka domin idan lokacin barcinta ya yi ba ta bari kowa ya tsaya kusa da ita sai ‘yan ƙananan kuyangi biyu masu kunna fitila.

Bayan ta gama kintsawa ta aika a kirawo abin ƙaunarta, ya taso ya same ta kwance bisa gado da fitila na haske a daidai kanta da ƙafafunta. Daga can gefe kuma fitilun zinariya ne ke haske kamar rana lokacin fitowarta.

Yayin da jama’a suka ji cewar sarki ya aiko a tafi da Ali Sharu wajensa a wannan daren, sai suka riƙa zance a junansu. Wani daga cikinsu ya ce, “duk yadda aka yi sarki ya yi nufin ya ja shi a jikinsa ne kuma ya naɗa shi babban askar a washegari.”

Da suka zo da shi ya sunkuya ya sumbaci ƙasa a gabanta sannan ya yi addu’ar ɗorewar mulki da ƙaruwar arziki ga sarki. Ita kuma tana cewa a ranta, “babu makawa sai na gara shi, na yi wasa da shi sa’a ɗaya kafin ya gane ko wacece ni.”

Ta tambaye shi, “shin ka je gidan wanka kuwa?”

Ya amsa, “eh na je.”

Ta ce, “tunda ka wahala ga kaza can da nama soyayye da halawa da ruwan wardi ka ci ka ƙoshi sannan ka zo nan.”

Ya amsa, “na ji na amsa.” Ya aikata kamar yadda ta umarce shi, sannan ta ce masa, “hawo nan bisa gadona ka yi min tausa.”

Ya hau ya zauna bisa gadon ya ji shi mai matuƙar taushi irin na alharini, ƙamshi na tashi daga kai. Ya shiga yi mata tausa, ya ji fatarta laushi tamkar siliki.

Ta ce masa, “yiwo sama da tausar taka.”

Ya ce, “afuwa dai ya shugabana. Daga gwiwa ba zan iya matsawa gaba ba.”

Ta ce, “kana son ka saɓa umarnina ne? Daren nan kana so ya zame maka shu’umi?”

Aliyu Sharu ya ce, “me zan aikata domin cika umarninka ya sarkin zamani?”

Ta ce, cire tufafinka ka kwanta bisa fuskarka, ruf-da-ciki.”

Ya ce, “wannan abu ne da ban taɓa aikata shi a rayuwata ba, ko da kuwa da mace balle namiji, idan kuma ka matsa min da sai na aikata, to kuwa zan tsaya da kai a wajen Ubangiji ranar gobe ƙiyama. Ɗauki duk abin da ka ba ni ba na so, kuma a yanzun nan zan bar maka birninka.” Ya fashe da kuka yana mai nadama.

Duk da haka ta kanne, ta sake kaurara murya ta ce, “tuɓe ka kwanta kusa da ni ko yanzun nan na sa a fille maka kai.”

Da ya ga babu mafita sai ya fara tuɓe tufafinsa, jikinsa na rawa. Wannan abu sai ya ba ta dariya har ta kasa daurewa. Ta yi ta dariya har ta faɗi bisa ga ƙeyarta, sa'annan ta ce wa Alisharu, "ya shugabana, shin kai ma har yanzu ba ka shaida ni ba, kamar yadda mutanen birnin nan suka kasa gane ni?"

Ali Sharu ya ce, “wanene ya sarki?”

Ta ce, “ni ce kuyangarka Zumarrazi.”

Ta yaye fuskarta ya gan ta. Yayin da ya gane ta, bai san lokacin da ya rungume ta ba kamar zaki mai jin yunwa yayin da ya yi ido huɗu da nama. Ya sakankance kuyangarsa ce babu saɓani. Ya riƙa sumbatarta kamar zai haɗiye ta, ita ma haka. Suka ba juna labarin bayan rabuwa, da abin da ya faru ga kowannensu, daga nan suka hau gado suka kwanta abinsu.

To duk bidirin da masoyan nan biyu suka kwana suna yi a kunnuwan 'yan kuyangin nan biyu ne. Sai suka riƙa yin gulma a tsakaninsu suna cewa, "wanna dariya kamar akwai mace a ciki." Ɗaya ta dubi ɗaya ta ce, "ai ni tuni na gane sarkin nan namu mace ce, na dai yi shiru da bakina ne." Suka yi shiru da bakinsu domin tsoron ransu ba su faɗa wa kowa ba.

Da gari ya waye Zumarrazi ta tara askarawanta da manyan fada ta ce da su, “na yi niyyar zan bi wannan mutumin domin na gano garinsu. Ina so ku naɗa na’ibi a cikinku wanda zai mulke ku kafin na dawo gare ku.”

Suka amsa, “mun ji, mun yi biyayya.”

Ta shiga shirin tafiya, ta ɗebi kayan guzuri masu yawa, sannan ta ɗebi dukiya da kuɗi mai yawan gaske ta lafta wa raƙumma da alfadarai da jakuna akwatuna da yawa na dukiya. Suka shirya suka tafi tare da Ali Sharu. Ba su gushe suna tafiya ba har suka sadu da birnin Ali Sharu, ya shiga gidansa tare da ita, ya riƙa fitar da kaya yana yiwa ‘yan uwa da abokan arziki kyautuka.

Ya yi ta sadaka da dukiya ga marasa ƙarfi. Suka zauna cikin soyayya har Allah ya ba ta haihuwa da shi suka hayayyafa. Suka zauna cikin jin daɗi da annashuwa har mai rusa jin daɗi, mai rarraba jama’a ta zaike musu.

Tsarki ya tabbata ga Wanzajje, wanda ba ya mutuwa har abada.

ƘARSHE

Idan Allah ya ba ni dama, zan sake zaƙulo muku wata hikayar mai daɗi, ba da jimawa ba.

Sai kun ji ni, in sha Allah.

Bukar Mada
28/12/2022

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment