Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙasusuwa,
To ka ga daimon sai a yashin Maliya.

Kai ɗan gwara bari kwaikwayon shaho sama,
Ko ka cira ba ka isa ga samaniya.

Jifar da tai nisa duka ƙasa za ta yo,
Mai kyautatawa zai ji daɗin dukiya.

Shi ko sukar ko an zuba shi a goruna,
Ɗaci na goran ba ya sa shi maɗaciya.

Ya zauna wanna tsibiri tare da bayinsa, ba a daɗe ba shi ma ya amsa kiran Ubangiji mai girma da ɗaukaka. Suka yi masa wanka suka rufe shi kusa ga abokinsa. Sai aka riƙa kiran wannan tsibiri da suna Abuƙir da Abusir. Amma da aka daɗe, zamunna suka shuɗe, sai sunan tsibirin ya koma Abuƙir kurum saboda taƙaitawa.

Yanzu haka wannan ɗan tsibiri, mai suna Abuƙir, ya zama babban gari, yana nan kamar mil goma sha biyu, Arewa da birnin Iskandariya a ƙasar Masar. An ce kuma har gobe, mutane na kai ziyara garin domin ganin kaburburan waɗannan abokai biyu, suna kuma yi wa kowa addu'a, daidai da abin da ya aikata yayin zamansa na duniya. Watau dai sharrin Marini ya bi shi har cikin kabarinsa.

Wannan shi ne abin da ya zo mana, na daga hikayar Abuƙir Marini da Abusir Wanzami. Muna fatar ma'abota hankali da tunani za su yi duba izuwa ga wannan hikaya, domin su hankalta, su guji yi wa juna sharri, domin shi sharri kare ne, mai shi yake bi!

ƘARSHE.

...

LITTAFIN DARE DUBU DA ƊAYA

Littafi ne da ya ƙunshi labaran soyayya, yaƙi, aljanu, addini, tafiye-tafiye, kimiyya da sauransu. Shi wannan littafi ainihinsa na Larabci ne, an kuma yi ittifaƙin cewa babu wani littafin adabi da ya kai shi shahara a duniya.

Ganin muhimmancin littafin ne ya sa harsunan duniya da dama suka fassara shi cikin harsunansu. Duk harshen da ba a ga fassarar wannan littafi ba a cikinsa, to ana yi wa wannan harshe kallon baƙauyen harshe, watau harshen da bai waye ba ta ɓangaren adabi. An kuma yi fina-finai ba iyaka, tun daga na Indiya, Amerika, Chana da sauransu duka daga labaran wannan littafi.

Ganin shaharar littafin na Larabci a cikin maluman zaure na ƙasar Hausa, ya sa wani Baturen mulkin mallaka mai suna Frank Edgar ya zauna ya fassara shi da Hausa dukkansa, sai dai Hausar da ya yi amfani da ita ba kowa ne zai iya fahimtar ta ba, waɗanda suka karanta littafi na ɗaya da na biyu, bugun NNPC, za su gane haka.

Wannan ya sa muka zauna, ni da Farfesa Malumfashi Ibrahim da Danladi Z. Haruna muka sabunta fassarar da ingattacciyar Hausa da kowane Bahaushe zai fahimta. Muka ƙuƙƙulla da taimakon mutanen da suka yi rijista a Facebook tun daga masu yin ta Naira ɗari biyu har zuwa waɗanda suka zuba dubu goma, muka samu muka fitar da mujalladi na farko a kasuwa daga cikin mujalladai goma da muke sa ran fitarwa.

To sai dai inda gizo ke saƙar shi ne, kamar Hausawa ba su shirya karɓar wannan littafi ba. Cikin kwafi dubu da muka buga na mujalladi na farko, tun a shekarar 2015, har yanzu ba a sayar da kwafi 500 ba, balle a samu kuɗin aikin mujalladi na biyu, kodayake ana kan aikinsa yanzu haka. Burinmu na fitar da cikakken littafin nan ga Hausawa ya fara dusashewa muddin ba gwamnati ta shiga cikin aikin ba ko wani ɗan siyasa ko ɗan kasuwa mai sha'awar aikin adabi.

To, rubutu dai na nan jibge cikin kwamfutocinmu, za mu fitar da wanda muke iya fitarwa, wanda ba mu fitar ba, sai na bayanmu su ci gaba daga inda muka tsaya, kamar yadda muka ci gaba daga inda Frank Edgar ya tsaya shekaru ɗari da suka wuce. Idan kuma an samu masu tallafawa, a shirye muke mu fitar da dukkan littafin.

Bukar Mada
09/11/2022

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment