Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaɓar teku, ya ce masa, "ka tafi da wannan mayaudari, ka sanya shi cikin jaka, tare da ɓuraguzan farar wuta, ka ƙulle bakin jakar. Ka sanyo shi cikin kwale-kwale ka biyo da shi ta gaban wancan gidan nawa da ke bakin kogi, za ka tarar da ni ina jiranka. Idan ka zo sai ka tambaye ni, 'in jefa shi ciki?' Zan ce maka, 'I, jefa shi.' Sai ka jefa shi cikin teku. Ta haka farar wutar za ta tafasa ruwan da ya shiga cikin jakar su dafa shi, ya ɗanɗani azaba biyu kafin ya mutu, azabar wuta da ta nutsewa a ruwa."

Shugaban askarawa ya ce, "an gama, ranka ya daɗe" Ya cakumi Abusir ya yi waje da shi. Ya tafi da shi wani tsibiri, can bayan gari, inda yake zaune, domin ya samu jaka da farar wutar da zai sanya Abusir a ciki, ya tafi da shi cikin kwale-kwale kamar yadda Sarki ya umurce shi. Yayin da suka isa tsibirin nan, sai shugaban askarawa ya tambaye shi, "kai kuwa wane babban laifi ne ka yi wa Sarki har ya yi fushi da kai haka, ya yanke maka wannan irin ɗanyen hukunci?"

Abusir ya ce, "Wallahi ban san laifin da na yi masa ba."

To, shugaban askarawan nan kuwa ya taɓa zuwa wanka, inda Abusir ya yi masa goma sha tara ta arziki, ya kuma rantse ba zai karɓi ko dirhami daga wurinsa ba, sa'adda ya yi niyyar biyan sa. Wannan abu ya yi masa daɗi ya kuma rike abin a ransa, har yana cewa lallai ne wata rana, in na samu dama, in rama masa da wannan alheri da ya yi mini.

Shugaban askarawa ya ce, "ina tsammanin akwai munafukin da ya haɗa ka da Sarki. Domin yadda ka samu shiga ga Sarki haka, har ka fi wasu 'yan gari, ba abin mamaki ba ne a yi maka hassada. Amma babu komai zan taimake ka, kamar yadda ka kyautata mini a baya, ka san an ce mai hankali ke yada alheri baya domin ya tsince shi gaba. Shi kuwa wanda ya yi maka wannan sharri, da sannu sharrin zai koma kansa. Ai shi sharri kare ne, mai shi yake bi. Yanzu sai ka zauna nan tare da ni, har Allah ya kawo jirgin da zai tafi garinku, sai in haɗa ka da shi." Wanzami ya durƙusa ya yi wa Allah godiya da ya kuɓutar da shi daga halaka, ya kuma gode wa shugaban askarawa. Da ma an ce sabo da maza jari.

Shi kuma shugaban askarawa sai ya samu gungumen ice ya ƙulle a cikin jaka tare da farar wuta. A cikin ransa kuma zuciyarsa na ɗar ɗar, yana tsoron kada Sarki ya gane shirinsa. Ya ce, "kai, na dai dogara ga Allah." Ya kawo ragar kamun kifi ya ba Abusir ya ce masa, "riƙi wannan ka jefa cikin ruwa, idan Allah ya nufa ka kama kifaye to ka ɗebi wanda za ka gasa ka ci. Saura kuma ka zuba cikin kwando, ka ajiye shi nan waje. Bayi za su zo daga gidan Sarki su ɗauka. Ka sani cewa kullum ni ke samar da kifayen da ake dafa wa Sarki, to ga shi yau Sarki ya sa ni wani aikin. Idan ka yi mini wannan ka ga ka hutar da ni yau."

Abusir ya karɓi raga ya ce, "ai wannan ba wani aiki ba ne mai wuya. Tafi, kai dai Allah ya sa kada Sarki ya gane shirinmu."

Shugaban askarawa ya kinkimi jaka ya sanya cikin kwale-kwale, ya tuƙa ya nufi gidan da Sarki ya ce ya same shi, gabansa na faduwa. Yayin da ya isa sai ya iske Sarkin saman bene yana jiransa. Ya ɗaga murya ya ce, "in jefa shi, ya Sarki?"

Sarki ya dubi jakar nan da kyau, sai ya nuna ruwan teku da ɗan yatsansa ya ce, "jefa shi ciki!"

Shugaban askarawa ya ingiza jaka cikin ruwa, ƙundum! Sa'adda jakar nan ta faɗa cikin ruwa, sai kuma wani haske, wal, kamar walƙiya ya fita daga yatsan Sarki, ya faɗa cikin ruwan nan tare da jakar.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, insha Allah.

...

Me kuke tsammani zai faru? Shin ko dai Sarki zai yi amfani da wani sihiri ne wajen gane shirin da shugaban askarawa ya yi?

Bukar Mada
29/10/2022SHARRI KARE NE 10

HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI

Waziri Aku

Shugaban askarawa ya ingiza jaka cikin ruwa, ƙundum! Sa'adda jakar nan ta faɗa cikin ruwa, sai kuma wani haske, wal, kamar walƙiya ya fita daga yatsan Sarki, ya faɗa cikin ruwan nan tare da jakar.

Abin nan da ya faɗa cikin ruwa kuwa, wani zoben Sarki ne, ya sulluɓe daga yatsansa. Zoben kuwa na sihiri ne. Duk lokacin da Sarki ya yi nufin hallaka maƙiyinsa, sai kurum ya nuna shi da zoben, haske zai fita daga gare shi kamar walƙiya, ya fille kan mutum, kamar an sare shi da takobi, sai dai a ga ya faɗi shirim, babu rai.

Dukkan fadawan Sarki da askarawansa sun san da wannan zobe. Ba ma komai ya sa suke bin Sarkin nan ba, kamar raƙumi da akala, sai don tsoron zoben nan.

To, yayin da zoben ya faɗa ruwa, sai tsoro ya kama Sarki, maimakon ya yi wa bayin da ke tare da shi tsawa, ya ce musu, "zobena ya faɗa cikin ruwa, ku tsunduma ku nemo shi!" Sai ya yi gum da bakinsa, kamar malam ya ci shirwa, bai yarda ya furta al'amarin ga kowa ba. Kada wani daga cikin fadawansa ya biɗi zoben ya kashe shi, ya gaje mulkinsa. Ya koma gida sukuku, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.

Amma Abusir kuwa, sa'adda ya ga shugaban askarawa ya ɓace daga ganinsa, sai ya ɗauki raga ya jefa ta cikin ruwa. Ba a jima ba, ya jawo ta cike da kifaye, ya zazzage su gefe, ya sake jefawa. Ba a daɗe ba kuma ya sake jawo ta cike da kifaye. Haka ya yi ta yi har sai da ya tara kifaye tsibi gudu kamar, wani ɗan ƙaramin tudu a gabansa.

Da ya ga ya tara kifi da yawa, sai ya ajiye raga, kwaɗayin kifi ya motsa masa. Ya ce a ransa, 'haƙiƙa na daɗe ban ci kifi ba, bari dai yau na fid da kwaɗayi." Sai ya zaɓi kifin da ya fi kowane girma daga cikin kifayen. Ya samu aska ya feɗe cikinsa yadda zai ji daɗin gasa shi. Da farke cikin kifi, sai ga zobe na ƙyalli. Ashe zoben Sarkin ne kifin ya haɗiye, ca yake wani abinci ne. Allah da ikonsa ya koro shi wannan tsibiri ya faɗa cikin ragar Wanzami.

Yayin da Abusir ya ga zobe na ƙyalƙyali, sai ya ɗauka ya sanya shi a yatsan hannunsa na dama, bai san amfaninsa ba. Ya ci gaba da gasa kifinsa. Yana cikin gasa kifin nan sai ga bayi biyu daga madafar Sarki, sun zo domin ɗaukar kifi. Suka tsaya gabansa suka tambaye shi, "ina shugaban askarawa?"

Abusir ya nuna musu inda ya bi da hannu ya ce, "ya tafi inda Sarki ya aike shi." To lokacin da yake nuna musu inda shugaban askarawa ya bi, sai hannunsa ya nune su. Nan take ya ga kawunansu sun yi tsalle sun rabu da jikunnansu, suka faɗi ƙasa matattu.

Abusir ya firgita, ya fara waige-waige wai ko ya ga abin da ya fille wa bayin nan kawuna, amma bai ga komai ba, bai kuma ji motsin kowa ba. Ya riƙa tambayar kansa, "to wa ya kashe waɗannan mutane?" Ya yi ta kakabin abin shi kaɗai.

Yana cikin wannan hali sai ga shugaban askarawa ya komo. Ya ga tarin kifin da Abusir ya kama, ya ga kuma bayi biyu a ƙasa matattu, babu kawuna. Ya dubi Wanzami ya ga yana ta tafa hannu, yana kallon bayin nan yana mamaki. Da ya lura da kyau, sai ya ga zoben Sarki na ƙyalƙyali a hannunsa, nan take ya gane abin da ya faru. Tsoro ya kama shi, ya ɗaga murya ya ce masa, "ya kai ɗan uwana, kada ka motsa hannunka mai zobe, kada kuma ka nuna ni da shi, idan ba haka ba, za ka halaka ni."

Abusir ya ƙara cika da mamaki, ya tsaya sororo, bai yarda ya motsa hannunsa ba har shugaban askarawa ya zo kusa gare shi. Ya tambaye shi, "wa ya kashe waɗannan bayi?"

Abusir ya ce, "na rantse da Allah, ɗan uwana, ban san wanda ya kashe su ba."

Shugaban askarawa ya ce, "na yarda da maganarka." Ya dubi yatsansa ya ce, "ina ka samu wannan zobe?"

Abusir ya nuna masa kifin da yake gasawa ya ce, "a cikin wannan kifi na tsince shi."

Shugaban askarawa ya ce, "ka yi gaskiya. Haƙiƙa zoben Sarki ne, na ga walƙiyar faɗawarsa cikin ruwa sa'adda ya nuna ruwan da hannunsa ya ce in jefa jakar da na tafi da ita. Allah ne ya ƙaddari wannan kifi da haɗiye shi, ya kuma koro kifin gare ka domin ka mallaki zoben a matsayin sakayyar cutar ka da aka yi. Ka kuwa san amfanin wannan zobe?"

Abusir ya ce, "a'a. Yana da wani amfani ne da ya wuce a sanya shi domin ado?"

Shugaban askarawa ya yi murmushi ya ce, "to bari ka ji. Ka ga wannan zobe da kake gani, saboda shi ake yi wa Sarki biyayya. Duk lokacin da aka lura da babu shi a hannun Sarki, askarawansa za su yi masa bore, wataƙila ma su tuɓe shi. Da shi yake kashe duk wanda ya so cikin sauƙi. Idan ya yi nufin kashe mutum, sai kurum ya nuna shi da zoben, wani haske zai fita daga gare shi, kamar ƙibtawar ido, ya sare wuyan wanda aka yi nufi."

Yayin da Abusir ya ji haka, sai ya yi farin ciki, gayar farin ciki. Ya ce wa shugaban askarawa, "mayar da ni birni."

Shugaban askarawa ya duƙar da kai cikin ladabi ya ce, "na ji, na yarda. Ai yanzu babu wata fargaba gare ka da kuma ni. Ko Sarki da kansa, sai yadda ka yi da shi yanzu. Idan ka ga dama sai ka kashe shi ka ɗare karagarsa, ka gaje bayinsa da dukiyarsa duka. Fadawa da askarawa kuma duk za su yi maka mubayi'a, su bi ka kamar bante." Yana gama faɗar haka, suka shiga jirga suka nufi birni.

Yayin da suka isa sai Abusir ya tasar wa fada. Ya iske Sarki zaune bisa karaga, fadawa sun kewaye shi ana ta fadanci. Sarki kuwa babu abin da ke cikin zuciyarsa sai tunanin ɓatan zobensa, yana cike da zulumin kada askarawansa su lura da babu zoben a hannunsa, su yi masa tawaye. Yana cikin wannan tunani kuma sai ya ga Wanzami ya shigo. Ya dube shi cikin tsoro da kuma mamaki ya tambaye shi, "ba kai ba ne muka jefa cikin teku? Yaya aka yi ka fito?"

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, insha Allah.

...

Shin Abusir zai yi wa Sarki juyin mulki ne, ko kuwa dai zai ba shi zobensa?

Bukar Mada
02/11/2022

SHARRI KARE NE 11

HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI

Waziri Aku

Yayin da suka isa sai Abusir ya tasar wa fada. Ya iske Sarki zaune bisa karaga, fadawa sun kewaye shi ana ta fadanci. Sarki kuwa babu abin da ke cikin zuciyarsa sai tunanin ɓatan zobensa, yana cike da zulumin kada askarawansa su lura da babu zoben a hannunsa, su yi masa tawaye. Yana cikin wannan tunani kuma sai ya ga Wanzami ya shigo. Ya dube shi cikin tsoro da kuma mamaki ya tambaye shi, "ba kai ba ne muka jefa cikin teku? Yaya aka yi ka fito?"

Abusir ya durƙusa gaban Sarki ya fara ba shi labari ya ce, "ya kai Sarkin zamunna, ka sani cewa, lokacin da ka yi umurni da a jefa ni cikin teku, sai shugaban askarawa ya tafi da ni tsibirin da yake zaune. Da muka isa can ya tambaye ni, "kai kuwa wane laifi ka yi wa Sarki ya yanke maka wannan mummunan hukunci?"

Na amsa masa, "Wallahi ban san laifin da na yi wa Sarki ba."

Shugaban askarawa ya ce mini, "ina tsammanin akwai munafukin da ya sare ka gun Sarki, domin yadda ka samu fada wajensa, har ka fi wasu 'yan gari, to dole ne a yi maka hassada. Amma kada ka damu, zan taimake ka kamar yadda ka kyautata mini sa'adda na je wanka a gidan wankanka."

Wanzami ya ci gaba da cewa, "shugaban askarawa ya kwance mini ɗauri. Ya ce in zauna nan tsibirin tare da shi, har sadda ya samu jirgin da zai tafi garinmu ya haɗa ni da shi. Ya samu gungumen ice ya sanya cikin jakar da ka ce a sanya ni. Ya ba ni koma ya ce mini, "ka jefa wannan cikin ruwa ka kama kifi da ita. Ka ɗebi wanda za ka ci, ka ajiye sauran cikin kwando, bayi za su zo daga madafar Sarki sai ka ba su."

Na ce masa, "na ji na yarda."

Ya sanya jaka cikin jirgi ya tafi ina yi masa addu'a. Da ya zo inda kake jiransa, ya tambaye ka ya jefa jaka cikin ruwa? Ka yi masa umurni da ya jefa ta ciki, kana mai nuna masa ruwa da yatsanka. Sa'adda ka nuna ruwan sai zobenka ya sumɓule ya faɗa ciki, kifi ya haɗiye shi yana tsammanin abinci ne.

Ni kuma ina cikin tsibirin nan ina su, sai Allah ya jefo da kifin da ya haɗiye zobenka cikin komata. Bayan na tara kifaye da yawa, sai na yi nufin gasa babba daga cikinsu. Ko da na feɗe cikinsa sai na ga zobe na ƙyalli. Na ɗauka na sanya ga yatsana ban san amfaninsa ba. Ina cikin gasa kifi sai ga bayi biyu daga madafar Sarki za su ɗauki kifi. Suka tambaye ni inda shugaban askarawa ya tafi. Na nuna musu inda ya bi da hannu, ashe na nune su da zoben nan, sai kurum na ga kawunansu sun rabu da jikunnansu, sun faɗi matattu. Na yi ta mamaki, ina tunanin abin da ya kashe su, na rasa.

Ina nan cikin wannan hali sai ga shugaban askarawa ya dawo. Yayin da ya ga abin da ya faru, ya kuma ga zoben Sarki ga hannuna, sai ya faɗa mini amfaninsa. Nan take na ce masa ya maido ni wurinka. Ya Sarki, na dawo ne domin in ba ka zobenka, saboda irin alheri da karimcin da ka yi mini a baya."

Ya cire zobe daga yatsansa ya miƙa wa Sarki kana ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ina roƙon ka, da ka faɗa mini laifin da na yi maka kafin a kashe ni."

Sarki ya karɓi zobe, bai gasgata abin da yake gani ba, har sai da ya sanya shi ga hannunsa sa'annan ya tabbata ba mafarki yake yi ba. Ya yi doguwar ajiyar zuciya, hankalinsa ya komo jikinsa. Bai san sadda ya miƙe daga kan karagarsa ba, ya rungume Wanzami don farin ciki yana cewa, "ban taɓa ganin mutumin kirki kamarka ba, haƙiƙa ka cika ɗan halas. Da a ce wani ne ya tsinci zoben nan, na tabbata ba zai maido mini da shi ba. Don Allah ka yafe mini abin da na yi maka bisa ga kuskure."

Abusir ya ce, "ya Sarkin zamunna, idan kana so in yafe maka, to sai ka faɗa mini abin da na yi har ya fusata ka haka, ka ba da umurnin a kashe ni ta hanyar dulmiyarwa a ruwa."

Sarki ya ce, "Na rantse da Allah, abin da ka yi mini yanzu, ya tabbatar mini da cewa ba ka da wani mummunan shiri a kaina. Amma ka sani cewa, Marini ne ya zo nan ya ce mini kaza da kaza a kanka." Ya kwashe duk abin da Abuƙir ya ce game da shi, ya faɗa masa.

Yayin da Abusir ya ji haka sai ya buga salati, ya ce, "Wallahi ni ban san wani Sarkin Turawa ba, ban kuma taɓa jefa ƙafata cikin garuruwan Annasara ba. Kuma ko da mafarki, ban taɓa tunanin cutar da kai ba, balle har in kashe ka, ya Sarki."

"Sai dai shi wannan Marini da kake magana abokina ne," in ji Abusir, ya ci gaba da ba Sarki labari, "garinmu ɗaya da shi, watau birnin Iskandariya, shagunanmu na kallon juna a cikin kasuwa. A kullum yakan zo shagona ya zauna mu yi ta hira. To, Allah ya ba ka nasara, da muka ga gari ya yi mana ɗaurin butar malam, kasuwancinmu ya tsaya har na cefanen gida na gagararmu, duk da kuwa mu gwanaye ne a ɓangaren sana'o'inmu, kodayake an ce idan farauta ta ƙi mutum, sai kunkuru ya tsere wa karensa."

"To, da muka ga haka sai muka yanke shawarar mu shiga duniya mu ga abin da Allah zai ba mu daga sana'oinmu. Muka yi wa juna alkawari wanda duk ya fara samun aiki zai ciyar da wanda bai samu ba. Muka yi addu'a muka shafa Fatiha bisa ga wannan alkawari, muka yi sallama da 'yan uwa, muka shigo jirgi."

Abusir ya faɗa wa Sarki yadda ya yi wa Marini hidima a cikin jirgi har suka iso wannan gari, suka sauka masaukin baƙi. Da yadda ya ci gaba da ciyar da shi yana kwance a gidan baƙi, babu aikin fari balle na baƙi har zuwa lokacin da rashin lafiya ya kwantar da shi, ya kasa fita neman abinci.

Ya faɗa wa Sarki yadda Marini ya kwashe masa kuɗi, ya rufe shi cikin ɗaki ya gudu, ya bar shi cikin tsananin ciwo. Da yadda mai kula da gidan baƙi ya gano shi rufe cikin ɗaki, ya yi ta jiyyarsa har ya murmure.

Ya kuma faɗa wa Sarki yadda ya shiga cikin gari har ya iso ga Marinar Abuƙir yana tsammani ya tare shi da farin ciki, amma sai ya liƙa masa sata, ya sa bayi suka birkice shi, ya yi ta kwaɗa masa bulala. Kai, Wanzami dai ya kwance wa Sarki bakin jaka har zuwan Abuƙir gidan wanka, da yadda ya tarye shi, ya girmama shi, bai manta komai ba.

Abusir ya ci gaba da cewa, "kuma shi ne ya tuna mini da maganin cire gashi da na manta ban haɗa shi a gidan wanka ba. Ya kuma ba ni shawara idan na haɗa maganin kada kowa ya fara amfani da shi sai kai, saboda muhimmancinsa, wannan zai zama wata karramawa gare ka. Na amince da shawararsa. Ya Sarkin zamunna, ka sani cewa wannan magani ba shi da wani aibi, duk gidan wankan da ya amsa sunansa gidan wanka, to dole a samu wannan magani cikinsa."

Daga ƙarshe ya ce, "ya Sarki, ka aika a kira mai kula da gidan baƙi da bayin da ke yi wa Marini hidima a karofinsa, ka tambaye su, ko abin da na faɗa maka gaskiya ne."

Nan da nan kuwa Sarki ya ta da manzanni, ya ce su yi maza su zo masa da bayin Abuƙir da mai kula da gidan baƙi. Da suka hallara Sarki ya tambaye su abin da suka sani game da Wanzami da Marini. Suka faɗi kamar yadda Abusir ya faɗa masa.

Da Sarki ya ji haka sai tausayin Wanzami ya kama shi, har ya fid da ƙwalla bai sani ba. Ya yi fushi da Marini, fushi mai tsanani. Ya daka wa askarawa tsawa, ya ce, "ku je gidan Marini ku kamo shi, ku ɗaure hannuwansa a baya, ku tuɓe masa rawani da takalmi, ku ingizo ƙeyarsa zuwa gare ni." Askarawa suka bazama da gudu domin cika umurnin Sarki.

To, a wannan lokaci kuwa Abuƙir na gidansa cike da murna, Sarki ya hallaka Wanzami. Ba ya da sanannen ciki sai ya ga askarawa kwaram bisa kansa, kamar an jeho su, babu ko sallama balle neman izinin shiga gidan. Suka ɗaure shi da igiya, suka fizge rawanin da ke kansa da takalminsa, suka tasa shi gaba sai fada. Da isarsu ya ga Abusir zaune kusa da Sarki, ya ga bayinsa da kuma mai kula da gidan baƙi, sai idonsa ya raina fata.

Ko da mai kula da gidan baƙi ya gan shi sai ya nuna masa Wanzami ya ce, "ashe wannan ba abokinka ba ne, wanda ka sace wa kuɗi ka rufe shi cikin ɗaki alhali ba shi da lafiya, bayan kuwa ya yi maka abu kaza da kaza na kyuatatawa? Allah dai ya waddan halinka!"

Su ma bayin nan suka ce, "ashe da ma wannan mutumin abokinka ne, ka ce mana ɓarawo ne. Ka sa muka riƙe shi ka yi ta tsala masa bulala? Tir da wannan hali naka!"

Munanan halayen Abuƙir suka bayyana ƙarara ga Sarki. Sarki ya cika, ya cika, kamar zai fashe don tsananin fushi. Ya dubi Abuƙir ya ce, "haƙiƙa ka cancanci azaba fiye da wadda Munkar da Nakir ke yi wa kafiri a cikin kabari!"

Za mu ƙarƙare wannan hikaya idan Allah ya kai mu ranar Laraba mai zuwa, insha Allah.

...

Da a ce ku ne Sarki, wace irin azaba ko hukunci za ku yanke wa Abuƙir Marini?

Bukar Mada
05/11/2022SHARRI KARE NE 12

HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI

Waziri Aku

Munanan halayen Abuƙir suka bayyana ƙarara ga Sarki. Sarki ya cika, ya cika, kamar zai fashe don tsananin fushi. Ya dubi Abuƙir ya ce, "haƙiƙa ka cancanci azaba fiye da wadda Munkar da Nakir ke yi wa kafiri a cikin kabari!"

Sarki ya ce wa askarawa, "ku zagaya da shi cikin gari da kasuwa kuna tsala masa bulala. Idan kuka karaɗe gari da shi, ku sanya shi cikin jaka tare da farar wuta, ku jefa shi cikin teku."

Abusir ya durƙusa gaban Sarki ya ce, "Allah ya ja zamaninka, karɓi cetona gare shi. In don ni za a yi masa wannan hukunci, to na yafe masa duk abin da ya yi mini."

Sarki ya ce, "idan ka yafe masa, to ni ban yafe masa ba. Kuma wanda ya ƙi cin naman kura, ba zai hana wata rana ta ci nasa ba. Idan na yafe masa, ba zai hana wata rana ya ƙulla wani sharrin da zai halaka ka ba." Ya juya ga askarawa ya ce, "ku tafi da shi."

Askarawa suka cakumi Marini suka yi waje da shi. Suka zagaye garin nan kaf da shi suna tsala masa bulala. Duk wanda ya ji abin da ya aikata, sai ya yi ta tsine masa. Daga ƙarshe suka ƙuga shi cikin buhu tare da farar wuta, suka jefa shi cikin teku, ya mutu ta hanyar tafasa da dulmiyewa a ruwa. Da ma an ce, in za ka gina ramin mugunta, to gina shi gajere don wataƙila kai za ka faɗa ciki. Kuma sharri kare ne, mai shi yake bi!

Da wannan ta ƙare Sarki ya juya ga Wanzami ya ce, "ya kai Abusir faɗi duk abin da kake so gare ni, in ba ka shi yanzu."

Abusir ya kalli Sarki, idanunsa cike da hawayen baƙin cikin mutuwar abokinsa ya ce, "ranka ya daɗe ba abin da nake so yanzu face ka mayar da ni garinmu, ba zan iya zama wannan gari ba."

Sarki ya ce, "ni ko so na yi da in naɗa ka ɗaya daga cikin waziraina."

Abusir ya ce ya gode, amma shi dai ya fi so ya koma garinsu inda iyalinsa, tunda ya samu abin da ya fito nema. Sarki ya ce masa, ba laifi, tunda haka ya fi so. Ya sa aka shirya masa babban jirgi, aka maƙare shi da dukiya da bayi da kuyangi.

Abusir ya yi ban kwana da Sarki, kowa na hawaye, ya shiga jirga suka tsunduma cikin teku, iska ta yi musu kyawu. A kwana a tashi har Allah ya kawo su wani ɗan tsibiri, kusa da birnin Iskandariya. Abusir ya ce a tsaya nan a sauke kaya.

Aka ɗaure jirgi bakin gaɓa, bayi suka shiga kici-kucin sauke kaya. Can sai wani daga cikinsu ya ce, "ku duba, ga wani ƙullin kaya can, kamar buhu, a cikin ruwa." Abusir ya ce a tafi a ɗauko shi.

Bayi suka sulmiya cikin ruwa suka yi iyo, nan take sai ga su sun komo da buhu, wanda aka ɗaure bakinsa. Abusir ya kwance bakin buhu, sai ya ga gawar abokinsa, Marina, fatar jikinsa duk ta saɓule kamar kazar da aka jefa cikin ruwan zafi. Ya tuna yadda suka bar gida tare, ga shi kuma sun dawo tare. Ya yi kuka, kuka mai tsanani. Ya sa aka gina kabari, aka bizne Abuƙir. Aka zagaye kabarin kamar ɗaki, aka yi masa ƙubba. Ya rubuta waɗannan baitoci a ƙofar ɗakin:

Shi ɗan Adam duka ayyukansa ka bayyana,
Kyawu na halayensa wannan duniya.

Kai dai guje wa maganganun gulma duka,
Domin suna iya zagayo maka ba wuya.

Kalma ta banza kar ka furta gun wani,
In za ka yo zance ka yi shi da gaskiya.

Sani shi kare na walwala ba takura,
Mugun nufin zaki ya sa shi a igiya.

A saman Sahara za a samu

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment