Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin gari yana cewa, "ya ku bayin Allah, ku zo maza ku yi wanka a wurin da aka keɓe, wanda ake kira Gidan Wankan Sarki."

Mutane suka yi ta tururuwa suna zuwa don yin wanka. Yaran nan suka himmatu wajen hidimta musu. Duk wanda ya yi wanka sai su taje masa kansa kamar yadda Abusir ya koya musu. Mutane suka yi ta zuwa suna yin wanka, tsawon kwana uku ba a karɓi dirhami ko ɗaya daga hannun kowa ba.

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, insha Allah.

Bukar Mada
19/10/2022SHARRI KARE NE 7

HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI

Waziri Aku

Mutane suka yi ta tururuwa suna zuwa don yin wanka. Yaran nan suka himmatu wajen hidimta musu. Duk wanda ya yi wanka sai su taje masa kansa kamar yadda Abusir ya koya musu. Mutane suka yi ta zuwa suna yin wanka, tsawon kwana uku ba a karɓi dirhami ko ɗaya daga hannun kowa ba.

A rana ta huɗu Wanzami ya gayyaci Sarki zuwa ga gidan wanka. Sarki ya yi hawa da tawagarsa duka, suka nufi gidan wanka. Abusir ya tarye su kyakkyawar tariya. Ya kai Sarki wani ɗaki na musamman domin yin wanka.

Sarki ya tuɓe tufafinsa ya shiga cikin kwatarniyar wanka, Abusir ya samu soso da sabulu mai ƙamshi ya riƙa cuɗa bayan Sarki yana fitar masa da dauɗa kaɓaki-kaɓaki. Duk sadda ya kankaro dauɗa sai ya nuna wa Sarki, shi kuwa ya yi ta mamaki.

Wanzami bai gushe ba yana cuɗa Sarki har sai da ya ji fatarsa ta yi santsi kamar ta kifi, dauɗar jikinsa duka ta fita, sa'annan ya samu ruwan wardi ya ɗauraye masa jikinsa, ya tsane masa ruwa da mayafi mai laushi, ya yayyafa masa turare. Ya sa yaran nan suka taje masa gashin kansa. Sarki fa ya ji jikinsa ya yi garas kamar ba nasa ba, sai wani sabon ƙarfi yake ji kamar aholakin jaki. Ya ji ta ko'ina sai iska mai daɗi ke shigar sa. Ya dubi Wanzami ya ce, "ashe haka gidan wanka yake?"

Abusir ya ce, "I, Allah ya taimake ka."

Sarki ya ce, "Wallahi birni kuwa ba ya cika birni muddin babu irin wannan a cikinsa." Ya yi ta mamaki yana tu'ajjibin wannan abu, ashe su zaune kurum suke ba su san daɗin duniya ba. Ya yi wa Allah godiya da ya kawo musu Wanzami wannan gari domin su ɗanɗani daɗin gidan wanka.

Ashe dai tuntuni kallon ƙauyawa baƙin da ke zuwa garin ke yi musu, sai yanzu da wannan baƙo ya zo ya fid da su kunya. Daga nan Sarki ya ce wa Wanzami, "to nawa za ka riƙa karɓa ga duk wanda ya yi wanka?"

Abusir ya ce, "duk abin da ka yanke, shi za a karɓa, ranka ya daɗe."

Saboda santin wanka da Sarki yake yi da kuma daɗin da ya ji, sai ya ce, "in haka ne kuwa duk wanda ya yi wanka ya kamata ya biya dinari dubu, ko ma sun yi kaɗan ne a ƙara."

Abusir ya yi murmushi ya ce, "Allah ya taimake ka, kuɗin sun yi yawa. Ba duka mutane suka zama ɗaya ba, akwai mawadata da talakawa a cikinsu. Idan aka ce kowa ya biya dinari dubu, talakawa ba za su iya biya ba, mawadatan ma ba za su juri biyan wannan kuɗi ba kullum, yau da gobe sai Allah, watarana sai a wayi gari babu mai zuwa wanka a gidan."

Sarki ya ce, "to, nawa kake gani za ka iya karɓa?"

Abusir ya ce, "abin da na ga ya fi shi ne kowa ya biya gwargwadon ƙarfinsa. Mawadata su biya gwargwadon nauyin lalitarsu, su ma talakawa su biya ɗan abin da suke iya biya. Ta haka sai kowa ya amfana da gidan wankan. Amma biyan dinari dubu wannan sai Sarki kaɗai ke iyawa."

Babban Alƙali da ke wurin ya tsolma baki ya goyi bayan Abusir, ya kuma ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara ai wannan karimci na biyan dinari dubu ba wanda ke iya shi sai fa kamar kai Sarkin adalci."

Sarki ya ce wa Alƙali, "ka yi gaskiya. Amma wannan mutum baƙo ne da ya kawo mana abin alherin da ba mu taɓa zato ba a garinmu, ya fid da mu kunyar baƙi da ke zuwa kasuwanci, ai kuwa ya kamata mu nuna masa mun ji daɗin wannan alheri, mu karrama shi iyakar ƙarfinmu, an ce yaba kyuata tukuici."

Fadawa suka karɓa, "gaskiya ne Sarkin duniya. Amma kuma, Allah ya ba ka nasara, ba ƙaramin aikinka ba ne idan ka ɗauke wa talakawanka biyan kuɗin wanka a nan, duk abin da za su biya, kana iya biyan shi cikin arzikinka, albarkacin kaza, kadangare ke shan ruwan kasko."

Sarki ya ce, "to, shi ke nan. Amma duk wanda muka zo tare yau, ya biya dinari ɗari kuɗin wanka, ya kuma ba wannan baƙo kyautar baƙin bawa ɗaya da farin bawa ɗaya da kuyanga ɗaya."

Muƙarraban Sarki suka amsa gaba ɗaya, "mun ji mun amince ya Sarki. Amma muna roƙon alfarma daga yau a bar mu mu riƙa biyan abin da ya sawwaƙa idan mun yi wanka."

Sarki ya ce, "babu laifi ga wannan."

Mutanen nan suka kawo duka abin da Sarki ya ce, suka damƙa wa Abusir. To, tawagar nan da Sarki ya zo da ita, waɗanda suka yi wanka, mutum ɗari huɗu ne. Don haka suka tara masa dinari dubu arba'in da baƙaƙen bayi ɗari huɗu da fararen bayi ɗari huɗu da kuyangi ɗari huɗu. Sarki kuma ya kawo dinari dubu goma ya ba shi, ya ƙara masa da baƙaƙen bayi goma da fararensu goma da kuyangi goma.

Yayin da Abusir ya ga an tara masa wannan dukiya haka, sai ya tafi gaban Sarki ya durƙusa ya ɗauki ƙasa ya ce, "ya Sarkin adalci mai yawan kyauta, ina zan sa waɗan nan bayi haka?"

Sarki ya bushe da dariya, ya ce, "Allah Sarki, talaka dai talaka ne. To ina ƙudan yake balle romonsa? Yanzu waɗan nan 'yan bayin har gani kake sun yi maka yawa? Ka sani mun ba ka su ne ko da wata rana sha'awar garinku ta faɗo maka a rai, sai ka tafi da abinka can, ka zauna da iyalinka cikin wadata."

Abusir ya ce, "Allah ya ɗaukake ka, ni dai da kuɗi ka ba ni maimakon bayin nan da na so. Talaka da ni, ina na ga zarafin ciyar da wannan runduna balle saya musu tufafi, wannan ai sai Sarki."

Sarki ya yi kekkewa ya ce, "gaskiyar ka. To, ka sayar mini da kowane ɗaya dinari ɗari?"

Abusir ya ce, "na sayar maka, Allah ya ba ka nasara."

Sarki ya sa Ma'aji ya je taska, ya ƙidayo kuɗi ya kawo wa Wanzami. Abusir ya karɓa ya yi godiya ga Sarki ya kuma ce masa, "na gode da ka raba ni da wannan gayyar bayi da babu mai iya cishe su sai Sarki, Allah ya ba ka nasara."

Sarki ya bushe da dariya, ya kuma ce wa muƙarrabansa kowa ya ɗauki bayinsa da ya bayar, ya ba su kyauta. Suka shirya suka juya gida, suka bar Abusir yana ta faman ƙidaya kuɗi yana shirya su wuri guda yana ƙullewa cikin jakunkuna. Bai gushe kan haka ba har dare ya raba. Ya tara jakunkunan kuɗi masu yawa, ya kuma riƙe bayi ashirin baƙaƙe da wasu ashirin farare da kuma kuyangi huɗu da za su yi masa hidima.

Kashegari Abusir ya buɗe gidan wanka, ya tura mai shela cikin gari yana cewa, "kowa ya yi wanka yau a gidan wanka, ya ajiye abin da yake iya biya gwargwadon ƙarfinsa, kada wanda ya tsananta wa kansa." Shi kuwa ya samu kujera ya zauna a cikin zauren farko, ya ajiye ƙaton akwati kusa gare shi inda za a riƙa sanya kuɗi.

Mutane suka yi ta zuwa giye-giye suna yin wanka suna saka kuɗi cikin akwati, kafin rana ta faɗi akwati ya cika da kuɗi. Ana nan kuma sai Uwargidan Sarki ta aiko cewa gobe za ta zo ta yi wanka da tawagarta. Don haka sai Abusir ya sa aka sake yin shela cewa, gobe maza za su yi wanka daga safe zuwa tsakiyar rana, sauran yini kuwa na Sarauniya ne da mutanenta.

Washegari da yamma Sarauniya ta zo yin wanka, to da ma Abusir ya zaɓi kuyangi huɗu ya koya musu duk yadda za su cuɗa mutum su fitar masa da dauɗar jikinsa, kuyangin nan suka wanke Saurauniya fes suka feshe ta da turare. Ta ji daɗi, ƙirjinta ya yalwata don farin ciki. Ta ba Wanzami dinari dubu, muƙarrabanta ma suka yi masa ruwan kuɗi, suka tafi.

Haka dai Abusir ya ci gaba da kula da gidan wanka, duk wanda ya zo, talaka ko tajiri, a kan girmama kowa ba tare da nuna fifiko ba. Sarki ya kasance ya kan zo gidan wankan nan duk sati, idan kuma ya zo ya kan saka dinari dubu a cikin akwati. Arziki ya yi ta kwararo masa kullum kamar ruwa. Ya yi abota da manyan fadawan Sarki. Labarin gidan wankan nan ya barbaɗu ko'ina cikin gari, kowa burinsa bai wuce a ce ya yi wanka a cikinsa ba. Wannan ke nan game da Abusir Wanzami.

Amma Abuƙir kuwa sai ya ji kullum ba labarin da mutane ke yi sai na wani sabon gidan wanka da aka gina a garin. Rannan ya ji wasu mutane biyu na hira, ɗaya na ce wa ɗaya, "kai wane, ashe haka gidan wankan nan yake? Wannan gidan wanka ai shi ne aljannar duniya. Wanda ko duk ya yarda ya mutu bai yi wanka cikinsa ba to ya yi wa duniya shiga shantun ƙadangare, a shiga da gudu a fita da gudu."

Ɗaya mutumin ya ce, "ai insha Allahu gobe sai na je na yi wanka cikinsa, kada a kwashe daɗin duniya mutum na nan sake da baki."

Da Marini ya ji haka sai ya ce a ransa, "kai, ya kamata dai in tafi gidan wankan nan, in ga abin da mutane ke ta giɗaɗawa, an ce gani ya kori ji." Ya sanya tufafinsa masu kyau ya hau alfadara, ya tafi tare da bayi, huɗu na yi masa zagi, huɗu na dafe da kuturi har suka isa bakin ƙofar shiga gidan wankan.

Ya ga mutane sai shiga da fita suke yi babu ƙaƙƙautawa, ga kuma ƙamshin turaren wuta ya game ko'ina gwanin daɗi. Ya sauka daga kan alfadara, ya kutsa kai cikin zauren farko, sai ya ga Abusir zaune a kan kujera. Yayin da Abusir ya ƙyalla ido ya gan shi, sai ya miƙe tsaye.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, insha Allah.

Me kuke tsammani zai faru a wannan haɗuwa ta biyu? Ko Abusir zai rama wulaƙancin da Marini ya yi masa?

Bukar Mada
22/10/2022SHARRI KARE NE 8

HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI

Waziri Aku

Ya sauka daga kan alfadara, ya kutsa kai cikin zauren farko, sai ya ga Abusir zaune a kan kujera. Yayin da Abusir ya ƙyalla ido ya gan shi, sai ya miƙe tsaye, ya tarye shi da murna.

Amma Marini kuwa sai ya yi tsaye ƙerere kamar wani gunki, ya buɗe baki, wai shi mamaki. Ya dubi Abusir ya ce, "a'aha, ashe rai kan ga rai? Watau da ma haka halin 'yan duniya yake? Yanzu a ce Sarki ya gina mini Marina a garin nan wadda babu kamar ta, na zama babban marini a cikin garin nan, arziki ya lulluɓe ni ta ko'ina, amma ko dai ka zo inda nake, ko kuma ka ce shin wai ina abokina ya shige ne? Duk ba ka yi wannan ba, babu abin da ya dame ka da halin da nake ciki. Ni kuwa babu inda ban neme ka ba, na je gidan baƙin da muka sauka, aka ce ka bar gidan. Na tura bayi gidajen baƙin da ke garin nan duka wajen neman ka, babu ɗaya da ya zo mini da labarinka. Kullum da tunaninka nake kwana da shi nake tashi."

Abusir ya ce, "a'a, ka dai manta ne. Ai na zo marinarka kwanan baya, ka liƙa mini sata har ka yi mini bulala, ka ci zarafina gaban mutane."

Abuƙir ya riƙe haɓa cikin mamaki ya ce, "da ma kai ne na yi wa bulala?"

Abusir ya ce, "I, ni ne."

Abuƙir ya rantse da abin da zai kashe shi wai bai gane shi ba. Ya ce masa, "wani ɓarawo ne ya dame ni da sata, kamarku ɗaya kamar an tsaga kara, to Wallahi na aza shi ne na yi wa bulala, ashe kai ne." Ya yi ta tafa hannuwa yana sallallami yana cewa, "inna Lillahi wa inna ilaihirraji'un! Tabbas na cutar da kai, na zalunce ka ba da sanina ba. To, amma me ya sa ka ƙi ce mini kai ne wane? Ai da sai ka sanar da ni tun da ka ga aiki ya yi man yawa, mutane sun rufe ni, ban tsaya na dube ka da kyau ba, balle in gane ka."

Abusir ya ce, "ai babu komai, ƙaddara ce, limamin gari da rabon giya. Mu shiga ciki ka yi wanka."

Abuƙir ya ƙara marairaicewa yana cewa, "don Allah ka yafe mini wannan babban zunubi da na aikata maka."

Abusir ya ce, "Wallahi na yafe maka, ai ko Ubangiji ba ya kama bawa da laifin abin da bawan ya aikata cikin rashin sani." Ya kama hannun Marini suka shiga cikin gidan.

Marini ya yi ta raba ido, kamar ɓera a buta, ya saki baki yana kallon abubuwan mamaki da aka ƙawata gidan nan da shi, ko a garinsu, Iskandariya, da suka baro, bai taɓa ganin gidan wankan da aka ƙawata kamar wannan ba. Sai ya tambayi Wanzami, "ya aka yi ka mallaki wannan katafaren gidan wanka haka?"

Abusir ya ce, "wanda ya gina maka marina shi ya gina mini wannan gidan wanka. Na je wajensa ne na bayyana masa alfanun gidan wanka." Ya kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsa da Sarki duk ya gaya wa Marini.

Marini ya ce, "ai kuwa Sarki babban aminina ne, bai kuwa san yadda ni ke da kai ba. Lallai ne gobe in je gare shi in faɗa masa cewa kai babban abokina ne, idan ya ji haka kuwa na tabbata zai so ka ya ƙara girmama ka fiye da yadda kake yanzu."

Abusir ya ce, "a'a, kada ma ka wahal da kanka don wannnan. Mai cusa soyayya a cikin zuciyar bayi yana nan koyaushe, kuma ya rigaya ya sanya soyayyata a cikin zuciyar Sarki da fadawansa, duk abin da ka gani nan, daga wurinsu na same shi." Ya faɗa masa duk irin alherin da Sarki da fadawansa suka yi masa. Daga nan ya ce, "tuɓe tufafinka in cuɗa ka."

Abuƙir ya cire tufafinsa ya shiga cikin kwatarniyar wanka, Wanzami ya sa soso da sabulu ya wanke shi tas, dauɗar jikinsa ta fita duka. Ya ɗauraye shi da ruwan wardi. Ya sa 'yan yaran nan kyawawa suka tsane masa jiki, suka taje masa gashin kai, suka yayyafa masa turare, suka dai shirya shi tsaf. Ya ji jikinsa ya koma kamar ba nasa ba.

Abusir ya dafa shayi da hannunsa, ya sa aka shirya musu shimfiɗa, aka jera akussan abinci iri-iri, suka zauna suna ci suna kurɓar shayi. Mutane suka yi ta mamakin yadda Abusir ya girmama wannan mutum, wanda ba su taɓa ganin ya yi wa kowa haka ba.

Da suka gama cin abinci, sai Abuƙir ya ɗauko lalitarsa ya ƙidaya kuɗi ya ba Abusir, shi kuwa ya rantse ba zai karɓa ba. Ya kuma ce, "haba abokina, ka sani fa ni da kai abu ɗaya ne. Ai abin kunya ne a ce na karɓi kuɗi gare ka don na yi maka hidima. Allah dai ya tsari gatari da saran shuka."

Abuƙir ya nisa sa'annan ya ce, "na rantse da Allah abokina, gidan wankan nan naka ya isa abin kwatance, ya kuma fi duk wani gidan wanka da na sani, sai dai abu ɗaya kurum na lura da babu shi."

Abusir ya ce, "wane abu ne wannan?"

Abuƙir ya ce, "maganin kakkaɓe gashin hamata da na mara. Na tabbata idan ka haɗa wannan magani ka ba Sarki, ka kuma faɗa masa yadda zai yi amfani da shi, idan ya jaraba ya ji daɗinsa, to zai ƙara ɗaukaka matsayinka a cikin ransa."

Abusir ya ce, "af, lallai kuwa na sha'afa, an yi tuya an manta da albasa. Ai duk gidan wankan da babu wannan magani to kuwa ba ya zama cikakken gidan wanka. Yau ɗin nan kuwa zan haɗa shi, ba ko wanda zai fara amfani da shi sai Sarki." Suka yi sallama, Abuƙir ya hau alfadararsa ya tafi.

Aka ce wai ɗan banza yashi ne, ko an dunƙula shi sai ya watse! Duk da irin karimcin nan da Abusir ya yi wa Marini bai sa zuciyarsa ta yi sanyi ba, sai ma ya fara tunanin wani sharrin da zai ƙulla wa Wanzami a cikin zuciyarsa. Don haka da ya hau alfadarsa, bai zame ko'ina ba sai gaban Sarki. Ya faɗi ya yi gaisuwa kana ya ce, "Allah ya ba ka nasara na zo ne domin in gargaɗe ka a kan wani tuggu da na hango magauta na shirya maka."

Sarki ya tambaye shi, "wane tuggu ne ka hango?"

Abuƙir ya ce, "wai na ji an ce ka gina gidan wanka a garin nan?"

Sarki ya amsa, "ba wai ba inke, gaskiya ne. Kwanaki wani baƙo ya zo nan, ya zayyana mini amfanin gidan wanka, na kuma gina masa kamar yadda na gina maka karofi." Sarki ya kwashe duk yadda suka yi da Wanzami ya gaya masa, ya ƙara da cewa, "gidan wankan nan kuwa ya haskaka birninmu ga idanun baƙi fiye da yadda muka yi tsammani. Yana ɗaya daga cikin abubuwa masu daraja a garin nan da muke alfahari da shi."

Abuƙir ya duƙar da kai cikin ladabi ya ce, "ranka ya daɗe ka taɓa yin wanka cikinsa?"

Sarki ya ce, "I."

Da jin haka sai Abuƙir ya buga salati ya ce, "tir! To Allah ya fisshe ka sharrin wannan kafiri kuma maƙiyin addinin Islama. Wannan da ka gina wa gidan wankan."

Sarki ya ce, "iye? Wanene shi?"

Abuƙir ya ce, "Allah ya ba ka nasara, sai mu gode wa Allah da wannan kafiri bai yi galaba a kan ka ba har yanzu. To amma ina mai tabbatar maka da cewa, idan ka sake shiga gidan wankan nan, to kai kuma sai dai labari."

Sarki ya gyara zama ya ce, "ta yaya hakan zai faru?"

Abuƙir ya amsa masa da cewa, "wannan mutum da kake gani maƙiyinka ne kuma maƙiyin addinin Musulunci. Ba da niyyar alheri ya sa ka gina masa gidan wanka ba, sai don wata ɓoyayyar manufa da yake da ita cikin zuciyarsa, ta ya hallaka ka ba tare da kowa ya sani ba. Yanzu haka ya shirya wata guba da zai ba ka idan ka ƙara zuwan gidan wankan nan, zai ce maka wai maganin cire gashi ne, ka shafa wa hamatarka da mararka duk gashin wurin zai zube."

Sarki ya dubi Marini yana wasi-wasin abin da ya gaya masa. Sai ya tambaye shi, "ashe dai? to kai ya aka yi ka san da haka?"

Abuƙir ya gyara zama, ya fara kantara wa Sarki ƙarya.

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, insha Allah.

Shin Sarki zai yarda da ƙarairayin da Marini zai shara masa ko dai korar sa zai yi?

Ayi SHARE domin wasu ma su amfana.

Bukar Mada
26/10/2022SHARRI KARE NE 9

HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI

Waziri Aku

Abuƙir ya gyara zama, ya fara kantara wa Sarki ƙarya, ya ce, "ai bawan Sarkin Turawa ne, shi ya aiko shi nan garin don ya kashe ka. Ya yi masa alkawarin idan ya kashe ka zai 'yanta shi da matarsa da 'ya'yansa da ke bauta wurinsa. Ni ma na taɓa faɗawa hannun wannan Sarki, a can ma muka haɗu da wannan mutum. To ni da Allah ya tashi tarfa wa garina nono, sai na buɗe marina irin wadda ka buɗe man nan garin, na rina wa Sarki tufafinsa da launuka masu ɗaukar hankali. Ya yi farin ciki kwarai, ya ce in faɗi duk abin da nake so ya ba ni. Ni kuwa na ce masa ba na son komai, sai dai ya 'yanta ni. Ya yarda kuwa, ya 'yanta ni. Da dai na ga na samu kaina, sai na ɓalle na yo nan garin."

Abuƙir ya ci gaba da cewa, "yau da na je gidan wanka sai na ga wannan mutum. Na tambaye shi, ko shi ma ya samu 'yancinsa ne daga Sarkin Turawa? Ya ce mini a'a, ai har yanzu shi da iyalinsa suna cikin igiyar bauta. Da na tambaye shi abin da ya kawo shi nan garin, Wallahi ranka ya daɗe kamar abin asiri, kuma da yake bai san yadda nike da kai ba, sai ya buɗe mini cikinsa duka, ya fara ba ni labari yana cewa:

Wai wata rana suna zaune a fadar Sarkin Turawa ana hirar manyan sarakunan duniya, sai wani ya ambaci sunanka. Da dai Sarkin Turawa ya ji an ambaci sunan nan naka, sai ya ɓata rai, ya ƙuta. Ya ce, shi kuwa babu wanda ya tsana a duniyar nan kamarka, ya ce da zai samu wanda zai halaka ka, da ya ba shi duk abin da yake so. Ya ce mini sai ya samu Sarkin ya tambaye shi, idan ya yi dabarar da ya kashe ka zai 'yanta shi da matarsa da 'ya'yansa? Sarki ya yi masa alkawarin zai 'yanta shi da iyalinsa duka, muddin ya kashe ka.

Da na tambaye shi yadda zai yi ya kashe ka? Sai ya yi dariya ya ce mini, zai kashe ka ba tare da kowa ya sani ba. Zai shirya maka wata guba, wadda idan ka ƙara zuwa wanka, zai ba ka ya ce maganin cire gashi ne, ka shafa wa hamatarka da mara. Idan ka shafa, dafin gubar zai riƙa shiga jikinka a hankali, cikin kwana ɗaya da yini, zai isa ga zuciyarka ya dakatar da ita, sai dai a ga ka faɗi matacce, babu wanda zai san abin da ya kashe ka. Shi kuma sai ya koma ya kwashe iyalinsa daga hannun Sarkin Turawa. Daga nan ya ƙyalƙyace da dariya har yana buga ƙafa ƙasa.

Ni kuwa da na ji haka, sai hankalina ya tashi, na tuna irin alherin da ka yi mani, na ga idan na ƙyale aka cuce ka lallai na zama bakin kaza, mai manta alheri. Shi ya sa na zo nan yanzu da hanzarina, domin na faɗa maka halin da ake ciki, ya Sarki."

Yayin da Sarki ya ji wannan labari, sai ya ƙume, ya cika da fushi. Ya ce wa Abuƙir, "kada ka faɗa wa kowa wannan sirri." Sa'annan ya sallame shi ya tafi. Kodayake Sarki ya yarda da wannan magana ta Marini, amma ya yanke shawarar ya fara bincikawa tukuna, kafin ya yanke hukunci, don an ce saurin fushi shi ke kawo da-na-sani.

Da gari ya waye Sarki ya ce a ransa bari dai na gani in maganar Marinin nan gaskiya ce, ba a bori da sanyin jiki. Idan kuwa maganar nan ta tabbata zan kashe wannan ja'iri, muguwar kisa, ai an ce kashe makashinka tun bai kashe ka ba. Sai ya hau tare da askarawa, ya nufi gidan wanka.

Abusir ya tare shi, ya yi masa hidima kamar yadda ya saba. Bayan Sarki ya kammala wanka ya kimtsa, sai Wanzami ya ba shi maganin nan ƙunshe cikin tsumma ya ce, "Allah ya ba ka nasara ga wani magani da na shirya maka. Idan za ka kwanta da dare yau, ka shafa shi ƙarƙashin hamata da mararka, ko da za ka tashi da safe, za ka ga gashin wurin duk ya kakkaɓe."

Sarki ya ce, "mu gani." Ya karɓi tsumma ya sunsuna, ya ji abin yana wani ƙauri da bai taɓa ji ba. Nan take ya gasgata maganar Marini, ba shakka wannan guba ce. Nan take idanunsa suka kaɗa suka yi jawur don tsananin fushi. Ya daka wa askarawa tsawa, "ku kama shi!"

Kafin Sarki ya rufe baki, askarawa sun cafe Wanzami. Sarki ya juya ya koma gida, fuskar nan tasa baƙiƙirin kamar hadarin tsakiyar dare. Mutane suka yi ta mamakin abin da ya haɗa Sarki da Wanzami da suke yi wa kallon mutumin kirki. Shi dai Sarki bai faɗa wa kowa abin da ake ciki ba, su kuwa fadawansa babu damar su tambaye shi ganin irin fushin da ya yi, to wa ma zai yi wannan ganganci, wai haihuwa ga damina. Wasu suka riƙa cewa, idan ka ji gangami to da labari, ai ruwa ba ya tsami banza.

Da Sarki ya koma gida sai ya fito majalisa ya zauna, ya ce a kawo masa Abusir. Aka kawo shi ɗaure cikin igiya. Sarki ya kira shugaban askarawan da ke kula da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment