Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

01 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU

Allah shi ne Sarki mafi daukaka daga dukkan
sarakuna. Shi ne mafi tsarki daga dukkan
abubuwa. Tsira da aminci su tabbata ga
Manzonsa kuma Annabinsa, Muhammadu dan
Amina (SAW).
: Akwai wani mutum tsoho masunci, yana da mata
d'aya da 'ya'ya uku, ya kasance talaka ne, bai
ajiye abincin yau ba ballantana na gobe. Kullum
yakan je kogi ya kamo kifi ya kai kasuwa ya
sayar ya sayo abin da za su ci. Yana da wata
al'ada mai ban mamaki, duk lokacin da ya tafi su,
yakan jefa komarsa sau hud'u ne kawai, daga
nan sai ya nad'e ta ya tafi da kifin da ya kama
ya sayar, idan ma bai kama komai ba a jefawa
hud'un nan, to ba zai yi ta biyar ba, sai dai ya
koma gida haka nan, ranar su kwana da yunwa.
Wata rana ya fita da Azuhur zuwa ga yankin
bahar domin yin su, da ya isa ya shiga cikin ruwa
daga bakin gaba, ya jefa komarsa ciki, ya juya
ta, ya kuma juyawa, sa'annan ya jawo ta, ya ji ta
da nauyi, ya fitar da ita daga cikin ruwa. Ya juye
abin da ke ciki, bai ga komai ba face ciyawa. Ya
kakkab'e ta ya sake jefawa karo na biyu cikin
ruwa, jim kad'an ya jawo ta da kyar saboda
nauyi, har rigarsa ta bi ruwa. Koda ya juye abin
da komarsa ta d'ebo, bai ga komai na daga kifi
ba face mataccen jaki. Da ya ga haka ya yi
bak'in ciki, ya ce a ransa babu tsimi babu dabara
face daga Allah mai girma da d'aukaka, neman
wannan abinci nawa da ban al'ajabi yake, yayin
nan ya waka wad'annan baitoci:

"Ya mai bayarwa a cikin duhun dare,
Ba da dabara ko wayo ba,
Na dogara gare ka ya Razzak'u,
Kai ke azurta mu ba don k'ok'arinmu ba."

Bayan ya gama rera wannan wak'a, ya jefar da
mataccen jakin, ya wanke komarsa ya shanya ta,
ta sha iska, ya d'auke ta ya shiga cikin ruwa
sosai sannan ya jefa ta kashi na uku yana mai
cewa Bismillahi. Koma ta nutse cikin ruwa, ya
hak'ura har ta nutse sosai. Ya jirkita ta, sannan
ya fara jawo ta zuwa tudu, ya ji ta nannauya fiye
da jefawar farko da ta biyu, ya yi farin ciki domin
ya zaci kifi ne.
Koda ya juye abin da ke cikin koma, sai ya tarar
da karafuna da matattun tangaram da duwatsu
da yashi da laka, babu komai na daga kifi. Yayin
da ya ga haka ya yi bak'in ciki mai yawa, ya rera
wannan wak'ar:

"Ya rayuwar zamanina ki fahimta,
Idan ba ki fahimta ba ki yafe ni,
Har yanzu ba a ba ni rabona ba,
Har yanzu ba a yi hukunci a kaina ba,
Na fita bid'ar arzikina na ishe ya k'are,
Sau da yawa jahili yakan ga abin b'oye,
Sau da yawa ilimi kan b'ace wa Malami."
Masunci ya zubar da tarkacen da komarsa ta
kwaso, ya wanke ta, ya nemi gafara ga Allah
bisa wannan wak'a da ya yi. Da komar ta sha
iska ya d'auke ta ya shiga cikin ruwa, wannan
karon ya kutsa nesa cikin ruwa, ya d'aga kansa
sama ya ce, ya Ubangiji ka sani cewa ba ni jefa
komata fiye da sau hud'u a rana, na jefa sau uku
ban sami komai ba, Allah ga ta hud'u kuma ta
k'arshe zan jefa, ka nufe ni da samun abin da
zan ci, ni da iyalina. Ya ambaci sunan Allah, ya
jefa komarsa karo na hud'u.
Bayan ya dad'e yana juya ta, sai ya jawo ta
zuwa tudu, wannan karon ta fi koyaushe nauyi.
Da ya fito da ita da kyar, ya juye abin da ke ciki,
babu komai face yashi da wata yar batta
(kwalba) k'arama, ta farin k'arfe, girmanta bai
wuce a saka ta a cikin aljihu ba, an lik'e bakinta
da darma, an buga hatimin Annabi Sulaimanu a
saman murfin.

Yayin da masunci ya ga wannan batta, ya yi farin
ciki ya ce wannan na sayar da ita a kasuwar
farin karfe dinari goma, in sayi abin da za mu ci.

Ya sa hannu d'aya zai d'auki batta, ya ji ta da
nauyi, hannunsa d'aya ya kasa d'aukar ta. Ya yi
mamaki da wannan abu, ya ce babu makawa in
bude ta in ga abin da ke ciki, in zazzage shi cikin
jaka, sannan in sayar da battar a kasuwa. ya
zare wuk'a, ya b'amb'are murfin darma daga
batta, ya ajiye shi gefe a kan k'asa.

Ya girgiza batta domin ya ji abin da ke ciki ko
yana motsi, sai ya ga hayak'i na fitowa yana yin
sama. Masunci ya cika da mamaki, ya yi tsaye
yana kallon ikon Allah. Da hayak'i ya gama fita,
ya tattaru wuri d'aya a sama, sai ya juye ya
zama Ifiritu, kansa yana cikin gajimare,
k'afafunsa cikin k'asa. Girman kansa kamar d'aki,
bakinsa tamkar kogo, hak'oransa kamar duwatsu,
k'ofofin hancinsa tamkar ibirik', idanunsa ja wur
kamar garwashin wuta, damuttsan hannuwansa
kamar ginshik'i, k'afafunsa kuwa tamkar
bishiyoyin kuka. Wannan Ifiritu ya kasance mafi
daud'a da k'ura cikin halittu.
Yayin da masunci ya ga wannan irin halitta,
gab'ob'insa suka yi sanyi, yawun bakinsa ya
k'afe, ya kasa motsawa daga inda yake. Da Ifiritu
ya ga masunci sai ya ce, babu Sarki madawwami
sai Allah, na shaida Sulaimanu Annabin Allah ne
kuma Manzonsa. Ya Annabin Allah kada ka
kashe ni, na rantse da Allah ba ni koma sab'a wa
umurninka.

Muryar masunci na rawa don tsoro ya ce, "Ya kai
wannan maridi, kana tsammanin a gaban Annabi
Sulaimanu kake? Bayan ya rasu da shekara dubu
d'aya da d'ari takwas, ka sani yanzu muna
k'arshen zamani ne. Ka labarta mini wanene kai?
Menene sanadiyyar shigarka wannan batta?"

Koda Ifiritu ya ji zance masunci sai ya ce, "Babu
Sarki sai Allah, hak'ik'a ka faranta mini ciki ya
kai wannan dan Adam, da sannu zan saka maka
da abin da ka yi mini." Masunci ya fara murna ya
ce, "Da me za ka saka mini?" Aljani ya ce "Da
kashe ka a cikin wannan sa'a, muguwar kisa."

muyutumin yace " yanzu wannan shine abunda zakamini
albishir dashi, kuma menene nayi dazan
chanchanci kisa ? me nayi dazaka kasheni ? NI
da nataimaka maka nafito dakai daga cikin
wannan kogi, kuma naciroka daga cikin wannan
tulu natsirar dakai daga halaka wannan shine
sakamakona ?... sai aljani (almaridu) yacemasa :
kazabi kalar kisanda zanma saboda kana
batamini lokaci… sai mutumin yace : wani
zunubine na aikata da zaka sakamini da wannan
mumunan sakayya ? sai (Almaridu) yacemasa :
kafin inkasheka bari inbaka labarina tukuna… sai
maikamun kifin yacemasa : inasauraranka kuma
kataqai labarinnaka saboda yanzu zuciyata
tabuga…

sai aljani (almaridu) yace : kasani cewa : ni
nakasance dagacikin aljanu (ma’riqai) wato -
masu taurin kai - wadanda sukabijirewa umurnin
ALLAH da manzonsa kuma suka kafircewa
ALLAH.. kuma nasabawa annabi (sulaimana) dan
annabi (da’wuda) dani da aljani maisuna (sakhru)
To sai annabi (sulaimana) ya aikamini wazirinsa
maisuna (a’sifu dan barkhiya) yakamani adole
yakawoni wajan (annabi sulaimana) ya
tsayardani agabansa aqasqance.. da (annabi
sulaimana) yaganni sai yarazana yace : (A uzu
billahi) saboda munin halittata.. daganan sai
(annabi sulaimana) umurceni da inyi I’MANI da
ALLAH kuma inshiga qarqashin ikonsa, (wato –
inyiwa annabi sulaimana DA’A) To nikuma sai
nayi taurin kai naqi amincewa… To sai (annabi
sulaimana) yasa aka kawomasa wannan tulun
yasakani aciki yamanne bakin tulun, yabuga
tambarinsa da suna maigirma, sannan sai yasa
akajefani cikin (teku) kogi, nikuma sai nakasance
acikin kogin har tsawon shekara 100, sai nace -
acikin zuciyata - : duk wanda yazo yafitardani
daga cikin wannan kogin acikin shekaru 100 to
zan arzuqtashi har abada..

amma babu wanda
yazo yafitardani dagacikin wannan kogi, sai
nacigaba da zama aciki har nakai shekaru 200
bangusheba inaciki, to anan sai nace : duk
wanda yazo ya fitardani zan budemasa taskokin
duniya gabadaya.. amma babu wanda yafitar
dani, sai nacigaba dazama aciki har shekaru 400
suka shude bangusheba inaciki.. bayan haka sai
wasu shekaru 400 daban sukazo sukashude sai
nace : duk wanda ya fitardani a wannan lokacin
to zan biyamasa buqatu guda 3… amma babu
wanda yafitar dani daga cikin wannan teku.. To
daganan kawai sai nayi fishi mai tsanani nace : -
acikin zuciyata - duk wanda yazo a wannan
lokacin to zan yimasa mumunan kisa, kuma zan
bashi dama yazabi kalar kisanda zanmasa.. To
yau gashi kazo kafitar dani saboda haka zan
kasheka kamar yadda nayi alqawari..

da wannan maikamun kifin yaji wannan labari sai
yacemasa : to ai ni ALLAH baibani damarda zan
fitardakai daga wannan kogi ba sai a wannan
lokacin… saboda haka kayi hakuri kar kasheni
ALLAH zaimaka afuwa, idankuma ka kasheni to
ALLAH zaikawo wanda zai halakaka kaima..

amma sai (almaridu) yace karka batamini lokaci
kasheka babu makawa.. kawai kazabi kalar
kisanda zanmaka…
Da maikamun kifin yatabbatar cewa (almaridu)
zai halakashi, sai yaqara durqusawa yaroqeshi
yacemasa : kayimini afuwa saboda karamcin
tsirar dakai danayi.. sai (almaridu) yace : To ai
nima zan kashekane saboda tsirardani da
kayine… sai mutumin yacewa (almaridu) ya
dattijon aljanu shin zan maka alheri kaikuma
kasakamini da sharri ? sai (almaridu) yacemasa :
karkasa tsammanin zaka rayu inajiranka kazabi
kalar kinsanda zan maka ..

To anan sai mai kamun kafin yatseya yaiy tunani
- acikin zuciyarsa – yace : wannan aljanine, niku
DAN ADAM ne, kuma ALLAH yabani hankali
cikekke, saboda haka zanshirya wata dabara
saboda inhalaka wannan aljanin kafin ya
halakani.. bayan yagama tunaninsa sai yacewa
(almaridu) : shin bakagusheba har yanzu kanada
ra’ayin kasheni ? sai (almaridu) yace : e’h inakan
ra’ayina.. sai mutumin yace : dan darajar suna
maigirma wanda aka rubuta akan zoben (annabi
sulaimana) inason inyimaka wata tambaya kuma
inafata zakabani amsa daidai.. da (almaridu) yaji
an ambaci ( suna mai daraja ) sai yaji dadi ya
girgiza kanshi yace : kayi tambayarka kuma
kataqaita zan amsamaka.. sai mutumin yace :
taya ka kasance cikin wannan dan karamin tulu,
bayan kuma ko hannunkama bazai iya shiga cikin
wannan tulu ba ballema kafafunka ?.. yaya akayi
tulun ya daukeka ?... sai (aljani almaridu) yace :

shin baka yardabane daga cikin wannan tulu
nafito ? sai mutumin yace : bazan taba yardaba
sai nagani da idona quru quru..

MUHADU RANAR LARABA MISALIN 9 PM DONCI GABA INSHA ALLAHU02 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU

wannan mai kamun kifi (masunci) yacewa
ALJANI ALMA'RIDU : ba zan taba yarda da
maganarka ba, har sai nagani - quru quru – da
idanuna ka koma cikin wannan tulu kamar yadda
ka kasance a ciki da farko...
Atake sai (alma'ridu) ya kumbura ya cika, sai
yazama hayaqi, kuma hayaqin yanufi sararin
samaniya, sannan sai ya shiga cikin tulun kamar
yadda ya kasance a ciki dafarko.
. To da mai kamun kifi yaga haka sai yayi sauri
ya daukko murfin wannan tulu – wanda aka
manna tambarin (annabi sulaimana) ajiki - sai
yarufeta (kirip).. sai yaqira sunana aljani
(alma’ridu) yacemasa : ya kai matsiyaci la’nanne
kazabi kalar kisan da zan maka… zan jefaka cikin
wannan kogin..., kuma daga yau dinnan zan gina
gidana anan wurin, duk wanda yazo wannan
kogin zai kama kifi zan hanashi, kuma zan sanar
dashi cewa : acikin wannan kogin akoi wani aljani
la’nanne (ALMA'RIDU) duk wanda ya fitar dashi
daga cikin wannan kogin sakamakonsa shine : zai
bashi zabi ya fadi kalar kisan da zai masa.. -inji
mai kamun kifi yake gayawa ALJANI
ALMA’RIDU..

Da ALMARIDU yaji abunda mai kamun kifi
yafadamasa, sai yayi qoqarin fitowa daga cikin
tulun, amma sai yaji – inaa – bazai iyaba,
saboda an rufeta da murfi mai tambarin zoben
(annabi sulaimana).. Anan sai ya tabbatar da
cewa wannan mai kamun kifin ya shiryamasa
tarkon da bazai iya kubuta daga cikintaba..
shikuma mai kamun kifi sai ya dauki wannan tulu
ya nufi kogi da ita, daniyyar zai jefata a ciki.. sai
ALMARIDU yayi I’hu yace : A’A dan ALLAH kar
ka aikata haka !! .. sai mai kamun kifi yace : ai
babu makawa sai na maidaka inda kafito da
farko… da ALMARIDU yaji haka sai ya yafirgita ya
zama abun tausayi, ya qasqantar da kansa, ya
soma lallabar mai kamun kifi.. sai mai kamun
kifin yacemasa : zan jefaka cikin wannan kogi..
idan har kakasance ka zauna a ciki har tsawon
shekaru 1800 To yanzu zan mayar da kai ka
cigaba da zama a ciki har zuwa ranar da za’a
buusa qaho - tashin qiyama -.. kuma koda na
mutu zanbar wasiya ga mutanen da zasu zo
nangaba..

Mai kamun kifin yacigaba da cewa : kuma shin
dazu ban rokekaba nacemaka : kayimini afuwa
kar ka kasheni kaima ALLAH zai maka rahama ?,
amma sai kaqi saurarata, kayi kunnene uwar
shegu kaso ka ha’inceni ? sai gashi ALLAH yasa
yanzu ka fada a hannuna…? sai ALMARIDU yace :
dan ALLAH ka yimin rai, ka fitar dani, wallahi
idan ka fitar dani to zan kyautata maka.. sai mai
kamun kifi yacemasa : karya kake tsinanne… Ai
irin abunda yafaru tsakanina da kai, kamar irin
abunda yafaru da wazirin wani sarki da ake kira
(SARKI YUUNA’N) da kuma wani mutum da ake
kira (HAKIM DAUYAN) sai ALMARIDU yace :
manene yafaru tsakanin wazirin sarki da HAKIM
DAUYAN ? sai mai kamun kifi yacemasa : kasani
cewa : a zamanin da yagabata, antaba samun
wani sarki a qasashen FARISAWA (iran) da
ROMAWA (italy) mai suna sarki (YUUNA’N)..
kuma wannan sarki yakasance yanada dukiya mai
dunbin yawa, dakuma rundunoni na soji masu
yawan gaske.. kuma masarautarsa tana da fadin
gaske, kuma yanada muqarrabai da sauransu…
A wani bangaren kuma.. wannan sarki ALLAH ya
jarrabeshi da cutar BARAS (zabya) wanda likitoci
da masu hikma suka kasa warkardashi… dukiyar
da sarautarsa basu iya sun anafanar dashi ba…

haka kuma magunguna da yaka anfani dasu basu
tsinana masa komaiba aka… babu wani daga
cikin lilitocin wannan gari dama wasu qasashen
daban da ya iya warkar dashi..
To ananan.. wata rana sai wani mutum – tsoho
– da ake kira (HAKIM DAUYA’N) ya shigo
wannan gari – wato garin sarki yuunan – kuma
wannan mutumi ya kasance yanada ilimi sosai..
ya karanta litatafai na al’ummomi da dama, ya
karanta littatafan mutanen YUUNAN (girka) da
FARISA (iran) da RUUM (italy) da LARABAWA da
sauransu.. kuma yayi fice afannin likitanci da
ilimin taurari da abinda yashafi ‘ya’yan itatu masu
anfani da masu cutarwa, kuma shehun malamine
abangaren falsafa, (philosophy).. a taqaice dai,
babu wani bangare na ilimi da bayyi fice aciki
ba..
To bayan wannan mutumi ya shigo wannan gari,
sai yaji labarin wannan sarki, da kuma irin
matsalarr dake damunsa - na cutar BARASI -
( zabiya ) kuma babu wani daga cikin likitaci da
ya iya warkar da shi..
Da wannan mutumi yaji wannan labari, sai ya
soma lissafi da tunanin yadda zai samu damar
isa wurin wannan sarki saboda ya jarraba
iliminsa da qorewarsa ta likitanci kuma ya samu
karbuwa a wurin wannan sarki..
Wayewar gari kedawuya, sai HAKIMU ya sanya
kayansa, ya kama hanya yanufi gidan sarki, kuma
ya samu damar shiga cikin fada.. bayan ya shiga
sai ya gaishe da sarki ya girmama shi, yayi masa
ADDU’A da fasahar harshe, sannan sai ya
gabatar da kansa yace : ya mai martaba naji
labarin irin abunda ke damunka - na cutar
BARASI - (zabiya), kuma naji labari cewa likitoci
sun kasa warkar da kai, basu san yadda zasu
rabaka wannan cutarba, shiyasa yau nazo saboda
in warkar da kai, ba tareda na baka magani
kasha ba, ko ka shafa ba…
Da sarki YUUNA’N yaji abunda wannan mutumi
yafada, sai yayi mamaki matuqa kuma yacemasa
: ta yaya zaka iya warkar dani.. ?? wallahi idan
ka warkar dani zan baka dukiyar da zaka anfana
da ita dakai da jikokinka.. kuma zan yimaka
ni’ima, kuma duk abunda kakeso zan baka shi,
kuma zaka kasance daga cikin mafi kusa dani,
masu cin abinci tare dani, zan nunamaka so da
qauna…

Daganan sai sarkin ya dauko wata kyauta ya
miqawa HAKIMU saboda jindadin abunda ya zo
dashi.. kuma sai sarkin ya qara tambayarsa
yacemasa : shin zaka iya warkar dani daga
wannan cutar ba tareda na sha magani ko na
shafa ba… ?? sai HAKIMU yace : tabbas babu
shakka zan iya warkar da kai, batare da wata
wahala ba… sai sarki yayi mamaki matuqa, kuma
yacemasa : To yanzu da yaushe zaka soma
wannan aiki.. ? sai HAKIMU yacemasa : gobe zan
soma aiki ya mai martaba…
Daganan sai HAKIMU yafice daga fadar sarki,
yaje yakama gidan haya, yazuba littatafansa da
kayan aikinsa da sauransu... sannan sai yaciro
kayan aikinnasa da magungunasa.. bayan haka
sai yaqera wata sanda ‘yar karama irin ta
sarakuna, yayi mata mariqi… sannan a wani
bangaren kuma yaqera qollo - kamar qollon (ball)
- … bayan ya gama, washe gari sai yanufi gidan
sarki, yaje ya masa bayanin yadda zayyi… ya
‘umurceshi da yashiga babban fili, wanda
dawakai suke tsukuwa a ciki, sannan sai ya
soma wasa da wannan qollo, yana bin qollon
yana dukansa yana gudu batareda ya tseyaba…

A lokacin da HAKIMU yashigo fadar sarki, ya
sameshi tare da waziriransa da manyan gari
gabadaya suna shawarwari gameda al’amura da
suka shafi masarauta.. amma duk da haka, da
sarki YUUNA’N yaga HAKIMU yashigo ya miqa
masa sanda da qollo, sai yatashi yabar abunda
yakeyi..

To sai HAKIMU yacemasa : kashiga babban fili,
sannan sai ka wurga wannan qollon, kayita
tabinsa kana duukansa da sandar daqarfi, kuma
koda kagaji kar ka tsaya har sai kayi gumi, tafin
hannunka ya jiqe da gumi, idan kayi haka to
maginin da yake jikin sandar zai shiga cikin
jikinka ya soma aiki.. bayan haka sai ka koma
gida kayi wanka, ka kwanta kayi bacci, daganan
zaka warke..

Sai sarki yayi dukkan abinda HAKIMU ya
gayamasa… bayan yagama sai ya sanar da
HAKIMU, sai HAKIMU ya ‘umurceshi da ya koma
fadarsa yayi wanka batareda bata lokaciba.. To
sai sarki ya koma yayi wanka ya chanza
tufafinsa… wannan shine halin da sarki YUUNA’N
ya kasance a ciki…
Amma shikuma HAKIMU DAUYA”N bayan yakoma
gida ya kwanta, washegari sai ya nufi gidan
sarki, da isarsa sai yanemi izinin shiga fada,
bayan yashiga sai ya tsunkuyar da kansa yayi
gaisuwa, kuma ya yabi sarki YUUNA’N da
baitoci.. bayan yagama yabon sarkin, sai shikuma
sarkin yatashi ya tseya da kafafunsa ya rungumi
HAKIMU kuma ya zaunardashi akusa da
kujerarsa ta sarauta, kuma yayi masa kyautar
alkebba da wasu keututtukan daban..
Bayan sarki yafito daga wanka, kawai sai yaga
fatar jikinsa takoma kamar ta kowa, babu sauran
BARASI (zabya) ajikinsa,, yayi matuqar farin ciki
da haka, hankalinsa yakwanta… Da gari ya waye,
sai sarki YUUNA’N yashiga fadarsa yazauna,
waziransa da muqarrabansa sun bayyana a fada,
sai ga HAKIMU ya shigo, da sarki ya gansa sai
ya tashi cikin sauri yarungumeshi ya zaunardashi
agefensa,, sannan sai ya bada ‘umurni aka kawo
abinci sukaci tare.. shikuma HAKIMU yana cike
da farin ciki saboda yadda sarki yake karramashi
fiye da kowa acikin fadar..

HAKIMU baigusheba yana tare da sarki har zuwa
faduwar rana… sannan sai sarki yabashi DINARI
2000 da wasu keututtuka daban, sannan da
HAKIMU ya tashi tafiya sarki ya rakashi ya
daurashi kan dokinsa,, sannan sai sarki ya dawo
gida yana matuqar mamakin irirn yadda HAKIMU
ya warkar dashi,, kuma yace : (acikin zuciyarsa)
wannan mutumin ya warkar dani daga cutar dake
damuna batareda ya shafamini magani ba,
wallahi wannan ba karamin baiwa bace, kuma ya
zama wajibi akaina in keutatawa wannan
mutumin in daukeshi in kusato dashi, in daukeshi
abokin hirana har tsawon rawuta.. sannan sai
sarki ya kwana cikin farin ciki ..

Da gari ya wa’ye… sarki yafito fada, wazirai da
hakimai dakuma manayn gari kowa yabayyana a
fada.. sai sarki yasa aka kirawo HAKIMU.. To
bayan HAKIMU ya shigo, sai ya gaida sarki,,
shima sarkiN ya tashi saboda girmama HAKIMU..
ya zaunar da shi yasa aka kawo abinci sukaci
tare kuma sarkin ya keutatata masa.. sannan da
yamma tayi sai yabashi keututtuka daban daban
har guda 5 ya hadamasa da DINARI 5000 sai
HAKIMU yakoma gida abunsa yana mai farin ciki
da godiya.. Washegari sarki ya taho fadarsa..
wazirai da ha’kimai da manyangari sun
kewayeshi..

To daga cikin waziran sarki YU’NAN akoi wani
waziri da ya kasance bashida hali mai kyau,
yanada matuqar muuni, bashida kyan gani, mai
yawan tsangoma da zargi, kuma mai hassada,
marowaci, annamimi, dasauransu….
Da wannan waziri yaga cewa sarki yana
kyautatawa HAKIMU, kuma ya kusantar dashi ya
daukeshi tamkar aboki fiye dasu, sai yasoma
HASADA, ya shirya masa makirci da mugunta..

To anan sai wata rana wannan waziri ya gabato
ya matso kusa da sarki YUUNA’N ya yayi
gaisuwa ya yabi sarki, sannan sai yace : ya mai
martaba idan ka amince inada NASIHA da nakeso
inyi maka, saboda idan nayi shiru ban gayamaka
wannan nasihar ba, to babu shakka zan kasance
munafiki, kuma kamar (‘DAN) da aka haifa daga
zina… idan ka amince inbayyana maka nasihar to
zan bayyana… sai sarki yacemasa ( tareda
mamakin irirn kalaman da suke fita daga bakin
wannan waziri ) : menene nasihar da kakeso
kayi ? kafada inasauraronka ? sai wazirin yace :
ya mai martaba : masu magana sukace : duk
wanda bayyi nazari yayi tunani ya hankalta acini
duk abunda yakeyiba, to duniya ba abokiyarsa
bace… saboda nalura naga sarki yana kan
kuskure, saboda irin kyautatawa da yakewa dan
adawarsa, kuma wanda yake qoqarin qwace
masa sarautarsa… hakika ka kyautatamasa sosai
har ya wuce iyaka.. kuma ka kusantar da shi
sosai ya wuce misali.. Ni ina fargabar kar yayi
maka juyin mulki…
Da sarki yaji wannan maganar daga wajen
wannan waziri, atake sai yafirgita launinsa ya
chanza yamike tseye yace".

wacce irin magana
kake fada ne ? wanene kake ganin zai zama
abokin adawata? kuma na kyautatamasa har na
wuce gona da iri ? sai wazirin yacemasa : ya mai
martaba idan bacci kake to ka farka.. ba kowa
nake zargi ba sai HAKIMU DAUYAN… sai sarki
yace : A’A wannan abokina ne, kuma yafi kowa
mutunci a idona… sabodamutum ne mai ilimi da
hikma sosai, kuma ya warkar dani daga cutar da
babu wani likitan da ya iya warkar dani, ba
tareda ya bani magani na sha ko shafa ba, babu
mutum kamarsa a wannan zamani – gabar da
yamma – saboda haka banga dalilin da yasa
kake fadin wannan magana gameda wannan
bawan ALLAH, kuma - bugu daqari ma – daga
yau dinnan na yanke shawar sanyamasa albashi,
a qarshen kowani wata yanada DINARI 1000…

kuma abunda wannan bawan ALLAH yamini koda
ace na raba masarautata kashi biyu na basa
kashi daya, to ban biyashi ba, abunda nabashi
yayi kadan… Ni dai kawai inganin HASADA kake
masa,, kamar yadda labarin wani sarki mai suna
( sindi bado ) ya iso mini… sai waziri yace :
wanene kuma sarki ( sindi bado ) kuma menene
labarinsa ?? sai sarki yace : an rawaito wani
labari cewa……..

Akoi wani sarki
daga cikin sarakunan FARISAWA (iran) wanda ya
kasance yana matuqar son shaqatawa da yin
farauta adaji, kuma wannan sarki yakasance
yanada wani TSUNTSU da ya horarar dashi kan
al’amuran farauta kuma baya rabuwa da wannan
TSUTSU dare da rana ya saba da shi, kuma koda
zai kwanta bacci ma tare suke suke kwana, da
rana kuma yana yawo dashi a hannunsa duk inda
zai je, yasaba dashi kamar dan uwansa, kuma ya
ratayamasa wani dan qarmin qorya na goal a
wuyarsa, kuma wannan TSUNTSU yana taimaka
masa sosai wajen farautar namun daji..

Toh ananan watara sai lokacin tafiya farauta
yayi, sai sarikin ya shirya ya dauki wannan
TSUNTSU a hannunsa suka fita suka nufi daji, da
shi da muqarrabansa masu tayashi farauta, to
bayan sun isa.. sai suka dana (suka shirya)
tarkonsu na farautar namun daji…

(kuma tarkon nasu ya kasance kamar wata
igiyace aka daura a jikin sanduna,, sai aka zagaya
ta yadda idan dabba ta shiga ciki ba zata iya fita
ba,, sai dai idan tayi tsalle ta tsallaka wannan
igiya to sai tasumu kubuta,, kuma duk da haka
mutane zasu kewaye wannan wuri da aka sa
igiya aka killace )
to jim kadan sai ga wata BAREWA ta danno kai,
sai ta fada cikin wannan tarko,, sai suka tashi
suka kewaye ta,, sai sarkin yacewa wadanda
suke tare dashi suke tayashi farauta : duk wanda
wannan BAREWAR ta gudu ta bangarensa to za’a
kashe shi, har ma dani sarki.. sai suka amince
da haka.. to sai kowa ya dau damara saboda kar
BAREWAR ta gudu ta bangarens a kashe shi… to
sai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment