Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ya dauki
wannan kifi ya nufi gidan sarki kamar yadda
ALMA’RIDU ya ‘umurceshi,,, isowarsa gidan sarki
keda wuya sai ya samu damar shiga fada ya isa
wajen sarki yayi gaisu sai ya gabatarwa sarki
kifin nasa ya bashi kyauta, sai sarkin yayi farin
ciki,, kuma yayi mamaki sosai saboda a
rayuwarsa bai taba ganin kifi mai launi - kala kala
- daban daban ba,, sai sarkni yayi ‘umurni da a
mikawa mai girki wannan kifi ta dafamasa…
sai wazirin sarki ya kira buduruwa (kuyanga) mai
giri ya ‘umurceta da ta dafa wa sarki wannan
kifi… Kuma dama wannan ‘yar buduruwa ta
kasance kuyangace wanda sarkin RUM (italy) ya
aikawa wannan sarki HADAYA tun shekaru 3 da
suka wuce, to sai a wannan rana sarkin yabada
‘umurni a bawa wannan budurur kifin ta dafa shi
saboda ya jarraba korewaeta a girki …
To bayan waziri ya ‘umurci mai girki da ta dafa
kifi, sai yacemata : ya ke ‘yan mata : mai
martaba yace : ba’a yin tanadi sai don gaba,
saboda haka yau sarki ya tanadeki don wannan
rana irin ta yau,, kuma yanaso ya jarraba
korewarki ne a girki yanaso ki girkashi yayi dadi
sosai…sai wazirin yacigaba da gayamata :
wannan kifi wani bawan ALLAH ne ya kawawo
sarki … bayan haka sai waziri ya koma cikin fada
abunsa.

Bayan waziri ya koma cikin fadar sarki, sai sarki
ya ‘ umurcesa da ya bawa mai kamun kifi DINARI
400… sai waziri ya aiwatar da umurnin sarki…. Da
mai kamun kifi ya karbi DINARI 400 sai yayi farin
ciki sosai saboda bai taba riqe irin wannan kudi
ba,, sai ya wuce kasuwa ya sayi duk abunda
yake buqata da shi da iyalinsa.. wannan shine
halin da mai lamun kifi ke ciki…
Amma ita kuma mai girki,, bayan ta karbi kifin
daga waje waziri sai ta wanke ta tsabtace shi ta
gyara ta saka a cikin tukunya ta soma dafawa,,
jim kadan kifin ya soma dafuwa, yana tafasa sai
ta juya daya bagaren saboda ya nuna..
To juya kifin ke da wuya.. kawai sai ga bangon
kicin din ya tsage, sai ga wata BUDURUWA
kyakkyawa sosai ta bullo daga jikin wannan
bango tana riqe da sanda a hannunta,, sai ta
saka sandar a cikin tukunyar da kifin yaka ciki
sai tace : ya ku wadannan kifaye, !! ya ku
wadannan kifaye !! shin har yanzu baku gushe ba
kuna kan bakar ku ??...wato (kuna kan ra’ayinku)
… da mai girkin taga abunda ya faru atake kawai
sai ta suma…

To sai wannan BUDURUWA da ta bulla ajikin
bango ta kara maimaita abunda ta fa darko har
sau 3 .. To sai kifayen suka daga kansu daga
cikin tukunyan sukace : E’h, E’h, E’h muna kan
bakrmu.. to sai BUDURUWAR ta kifar da tukunyar
kuma sai ta koma jikin bangon ta shiga wurin da
ta bullo da farko sai ta bace…
jim kadan sai mai girki ta farfado daga sumar da
tayi,, sai taga wannan kifi ya zama toka baqi
kamar gawayi…. To Tana cikin wannan hali sai
ga waziri ya shigo ya tseya akanta yacemata :
ya ke ‘yan mata ki kawo kifin da kika dafa sarki
yana jira tun dazu…. Sai mai girki tayi kuka ta
bawa waziri labarin abunda ya faru gabadaya…

da waziri ya ji wannan labari sai yayi mamaki
qorai da gaske yace : kai wannan al amrine mai
ban mamaki sosai…. To bayan haka sai waziri ya
aika a kirawo mai kamun kifi,,
da mai kamun kifi yazo sai waziri yacemasa : ya
kai wane, munaso ka qara kawo mana irin
wadannan kifaye guda 4 da ka kawo wa sarki
rannan muna bukata… sai mai kamun kifi ya
kama hanya ya nufi wurin da ALMARIDU ya kaisa
sai jefa shingensa ya kamo kifi 4 kamar irin na
farko ya kawo wa waziri aka bashi DINARI 400
ya juya ya tafi abunasa
To bayan haka, sai waziri ya dauki kifin ya baiwa
mai girki yacemata : yau ki dafa wannan kifin a
gabana saboda inaso in gani da idona abunda zai
faru.. sai mai girki ta karbi kifi ta wanke ta
tsabtace ta saka a cikin tukunya…

jim kadan da
kifi ya soma dafuwa yana tafasa , kawai sai ga
bangon kicin din ya tsage sai ga kyakkyawar
BUDURUWA ta fito daga ciki, da sanda a
hannunta sai ta taba kifin da sandar tace : ya ku
kifaye shin baku gusheba har yanzu kuna kan
bakarku ne ?... sai kifayen suka daga kansu
sama sukace :
(( ﺇﻥ ﻋﺪﺕ ﻋﺪﻧﺎ ﻭﺇﻥ ﻭﺍﻓﻴﺖ ﻭﺍﻓﻴﻨﺎ = ﻭﺇﻥ ﻫﺠﺮﺕ ﻓﺈﻧﺎ
ﻗﺪ ﺗﻜﺎﻓﻴﻨﺎ ))
Idan kika maimaita muma zamu maimaita (wato
iadan kika kara tambayarmu muma zamu baki
amsa irin ta farko) idan kuma kika cika alkawari
muma zamu cika, idan kuma kika kaurace to
muma mun isa komai

A lokacin da wadannan kifaye suka daga
kawunansu sama suka mayar wa wannan ‘yar
BUDURUWA amsa cewar suna kan bakarsu, ita
kuma BUDURUWAR sai ta kifar da wannan
tukunya da sandar da ke hannunta, bayan haka,,
sai bangon kicin din ya budu – ya tsage - sai ta
koma ta shiga jikin bangon kamar yadda ta fito,

sai bangon ya kara rufuwa ya hade.
To da wazirin yaga abunda ya faru a idonsa –
quru quru – sai ya tashi tseye yace : wannan
al’amri ne mai ban mamaki, kuma ya zama dole
in sanar da sarki abunda ake ciki… sannan sai ya
shiga wurin sarki ya sanar da shi abunda ya faru
a idonsa… sai sarki yace bazan yarda ba sai na
gani da idona – quru quru.

To sai sarki ya bada umurni aka akirawo mai
kamun kifi,,

RANAR LARABA ZAN DAURA INSHA ALLAHU.

Wannan labari na zuwa Muku ne daga ==>Yusuf Addullahi A jibaga05 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU

quru quru – sai ya tashi tseye yace : wannan
al’amri ne mai ban mamaki, kuma ya zama dole
in sanar da sarki abunda ake ciki… sannan sai ya
shiga wurin sarki ya sanar da shi abunda ya faru
a idonsa… sai sarki yace bazan yarda ba sai na
gani da idona – quru quru –
To sai sarki ya bada umurni aka akirawo mai
kamun kifi,, bayan mai kamun kifi ya iso fadar
sarki, sai sarkin ya umurceshi da ya kawo masa
kifaye guda 4 kamar yadda ya saba,, atake ba
tare da wata wata ba,, sai mai kamun ya kama
hanya ya nufi wannan tapki dake bayan gari yaje
kamo kifaye guda 4 masu launi daban daban ya
kawo wa sarki, sai sarki ya bada umurnin a
baiwa mai kamun kifi DINARI 400.
To Bayan haka sai sarki ya dauki kifin ya mikawa
waziri yace masa : ka dauki wannan kifin ka
wanke ka gyara ka dafashi a anan a gabana
saboda ingani da idanuna – quru quru – sai
waziri yace : ranka ya dade ! kamar yadda kaso
haka za’ayi… atake sai waziri yaje ya kawo
murhu da tukunya ya hura wuta, ya hada komai
da komai, ya wanke kifi ya gyara, sannan sai ya
zubashi a cikin tukunyar sai ya dan saurara, jim
kadan bayan tukunyar ta soma tafasa kawai sai
ga bangon fadar sarki ta ya tsage kuma sai ga
wani baqin BAWA mai muumunar halitta mai
tsoratarwa ya bayyana a gabansu da ganye a
hannunsa, sai ya daga muriyarsa da karfi yace :
ya ku wadannan kifaye ! shin har yanzu baku
gushe ba kuna kan bakarku ?.. wato (kuna kan
ra’ayinku ?.) sai kifayen suka daga kansu daga
cikin tukunyar sukace : E’h, Eh, Eh, bamu gushe
ba muna kan bakarmu, sannan sai suka rai raya
wannan baiti"

idan ka kara tambayarmu zamu ba amsa irin ta
farko, idan kuma ka cika alkawari muma zamu
cika, idan kuma ka kaurace to muma mun isa
komai - bama bukatar wani
. (sai labarin ya qare za’a fahimci wannan
maganr)
Sannan bayan haka sai wannan baqin BAWA ya
kifar da tukunyar a cikin murhun, kifayen suka
qone kurmus suka zama toka baqi, sannan sai
wannan BAWA ya juya ya koma daga inda yafito
ya bace..
To a nan sai sarkin yayi mamaki matuqa yace"

kaai ! wannan Al amarine mai ban al’ajabi, babu
shakka akoi wani sirri boyeyye game da wannan
kifi, kuma ba’zaiyyu muyi shiru a kai ba, dole
muyi bincike akai musan me ke faruwa..
To sai sarki ya bada umurni da aje akawo masa
mai kamun kifi, atake akaje aka cincimo mai
kamun kifi aka kawo gaban sarki, shikuma mai
kamun kifi yana cikin wani hali na tsoro da firgita
saboda bai san me ke faruwa ba…

To bayan mai kamun kifi ya bayyana a gaban
sarki, sai sarkin yacemasa : ya kai mai kamun
kifi ! A wani wuri ne kake kawo wannan kifi ??..
sai mai kamun kifi yace : ya mai martaba ina
kawo wannan kifin ne daga wani dan karamin
tapki ( kogi) da yake tsakanin wasu duwatsu
guda 4 da suke bayan wani babban dutse a
bayan wannan gari naka, To sai sarkin ya matso
kusa da mai kamun kifin yacemasa : tafiyan
miniti nawa ne za’a yi kafin a iso wannan tapki –
kogi- . .? sai mai kamun kifi yace : tafiyar minti
30 ne kawai ya mai martaba..

Da sarki yaji wannan magana daga wurin mai
kamun kifi sai ya kara mamaki matuqa, kuma
atake ya bada umurnin a fitar da rundunar sojoji
( askarawa) a shiryasu kuma a dauki mai kamun
kifi a saka shi a gaba yaje ya nuna inda yake
kamo wadannan kifaye masu launi daban daban,,
da mai kamun kifi yaga kansa a gaban rundunar
soja ana tafiya dashi sai ya tsorata yana kuka
yana La’antar ALMA’RIDU yana tsine masa yace :
daa ma ya barni a cikin talaucina…

To sai sarkin wannan gari da rundunarsa ta soji
sukayi ta tafiya a cikin daji, mai kamun kifi yana
gaba yana nuna musu hanya har sai da suka iso
wurin wannan dutse suka hau kansa suka sauqa,
sannan sai suka tarar da wani daji mai fadin
gaske wanda basu taba ganisaba, basu sanda
zaman wannan wuri ba duk tsawon rawuwarsu a
wannan gari da su da kakanninsu,, sai sarkin yayi
matuqar mamaki, haka ma sauran jama’a da
askarawa da suke tare da sarki sukayi mamakin
ganin wannan daji da basu taba ganinsa a baya
ba, basu taba jin labarinsa ba..

To Bayan haka, sai suka cigaba da tafiya, jim
kadan sai suka ga wasu duwatsu guda 4, kuma a
tsakiyan wadannan duwatsun akoi wani dan
karamin tapki – kogi - wanda a ciki akoi kefaye
masu (nau’i) da launi - daban daban – har kala
hudu.. akoi : FARI JAA SHUDI da kuma KORE
duk acikin wannan dan karamin tapki da yake
tsakanin duwatsu guda 4.. da sarki yaga haka sai
ya qara matuqar mamaki da ganin irin wannan
abun al ajabi da bai taba gani ba a rawuwarsa..
To sai sarki ya juya ya kalii ASKARAWANSA da
sauran jama’a dake tare da shi, tare da mamaki
ya tabayesu yace : shin a cikinku akoi wanda ya
taba ganin wannan wuri ko yaji labarinsa ??
gabadayansu suka hada baki sukace : A’ A’ ko
kadan.. sai sarkin yace : To wallahi na rantse
bazan koma masarauta ta ba har sai nasan
hakikanin abunda yake faruwa game da wannan
dan qaramin tapi (kogi) da kuma kifayen da suke
ciki.. sannan sai sarkin ya umurci jama’a da su
koma gefe suyi nesa da dutsen..

To Bayan haka, sai sarkin ya kira wazirinsa suka
koma gefe, sai yacewa wazirin nasa : Akoi wani
Abu da nakeso inyi shiyasa nakira ingayamaka…
sai sarkin yacigaba da gayawa wazirin nasa yace
: nayi tunani naga cewa yakamata in zauna anan
wurin har zuwa dare – inkwana annan - saboda
inaso in gudanar da bincike gameda wannan dan
karamin tapki da kifayan da ke ciki, saboda haka
ka kawomini KHAIMATA ( kamar daki ko rumfa )
ka kafa mini ita anan, kuma kasanar da dukkan
faadawa da hakimai da sauran wazirai cewa sarki
yana cikin wani yanayi na damuwa bayaso kowa
ya shiga wurinsa, kuma ya umurceni da kar inbar
kowa ya shiga wurinsa kuma kar ka sanar da
kowa abunda nayi niyyar aiwatarwa…( abunda
sarkin ya gawa waziri kenan )
Da waziri yaji wannan magana daga wajen sarki
bai iya ya saba umurnin sarki ba, sai ya aiwatar
da dukkan abunda sarkin ya bukata… sannan
bayan haka sai sarkin ya canza tufafinsa ya
badda kamaninsa ya dauki takobinsa ya rataya a
kafadarsa ya sulale a tsakanin jama’arsa ya fita
batare da kowa daga cikinsu ya sani ba, sai ya
kutsa ya shiga daji abunsa …

To sai sarkin ya cigaba da tafiya a cikin dajin
ALLAH har sai da dare yayi sarki baigusheba
yana tafiya har gari ya waye aka shiga dare na 2
gari ya waye sarki baigushe ba yana ta tafiya
acikin dajin ALLAH batare da ya hadu da wani
mahluuqi ba – ko dabba ko mutum – a cikin
kwana na 3 bayan gari ya soma haske sarki bai
gusheba yana ta tafiya a cikin daji… jim kadan
sai sarki ya hango wani baqin abu daga nesa, sai
yayi farin ciki da ganin wannan abun duk da
cewa baaisan ko menene ba, To sai yace – a
zuciyarsa - : yawwa ! yanzu wataqila ko zan
samu wanda zai bani labarin wannan dan
karamin tapki (kogi) da kifaye masu launi daban
daban da ke ciki !!! to bayan haka, sai ya matso
kusa wannan baqin abu da ya gani daga nesa,,
bayan ya matso kawai sai ya tarar da wani
baban masaurata da aka gina da baqaqen
duwatsu da karafuna,, kuma sai yaga kofar
wannan masarasuta a bude yake, sai yayi
matuqar farin ciki da ganin haka, sannan sai ya
matso kusa da kofar ya tseya ya konkosa a
hankali, amma babu wanda ya amsa masa,
sannan sai ya qara konkosawa karo na 2 da na 3,
duk da haka dai bai ji alamun amsa ba, to anan
sai ya qara konkosawa da karfi a karo na 4
amma duk da haka bai ji alamun akoi wani aciki
ba, babu motsin komai… To sai yace : babu
shakka wannan gida babu kowa a ciki, to kawai
sai ya kutsa ya shiga ciki yayi ta tafiya har ya
iso cikin zaure, sannan sai ya kolla I’hu yace : ya
ku masu wannan masarauta ni mutum ne, kuma
matafiyi, ina neman taimako, shin za’a samu
abinci a wurinku ne ?? ya maimaita wannan
magana har sau 3 amma baiji motsin kowa ba..
to sai ya kutsa ya shiga can ciki har sai da ya
isa tsakiyar wannan fadar amma baiga kowa ba,
amma kuma sai yaga wurin gabadaya anyi
shimfida mai kyau, kuma gashi aniyiwa wurin ado
da gwalagolai da wasu abubuwan daban na ado..
sai yayi mamaki kuma yaji takaicin rashi samun
kowa a ciki wannan fada da zai bashi labarin
wancan tapki da kifayen da ke ciki da kuma
duwatsun da suka zagaye tapkin,, to kawai sai ya
zauna ya rasa abun yi yana tunani, kawai can sai
yaji karar nishin mutum daga nesa, kuma a bisa
dukkan alamu mai wannan nishi yana ciki wani
yanayi na bakin ciki da muwa,, to da yasa hankali
ya saurara sai yaji mai wannan nishi ya rairai
wannan waka kamar haka.
((Na boye halin da nake ciki na wahala amma ya
bayyana))
((bacci a idona ya juya ya zama rashi bacci))
((Nayi I’hu na kira bakin cikin da yake ta karuwa
da tunani))
(( nace : ya bakin ciki na rokeka kar ka kasance
a tareda ni))
((Yau ga rayuwata tana tsakanin wahala da kuma
hadari))

Da sarkin yaji wannan waka atake ya mike tseye
ya nufi inda wannan mai waka yake… bayan ya
iso wannan wuri sai yaga wata kofa anyi mata
sutura da labule, sai ya bude wannan labule,
budewarsa ke dawuya sai yaga wani saurayi mai
matukar kyawun sura da kamala da jamala yana
zaune akan wani gado kuma yana sanye da hula
irin ta sarauta yana kuka yana zubar da qolla,
kuma akoi alamun damuwa da bakin ciki atare da
wannan saurayii.
To sai sarkin yayi farin cikin samun wannan
saurayi, sai yayi sallama, sai saurayin ya amsa
kuma yacewa sarikin : kayi mini uzuri saboda ban
tashi na tseya dan girmamaka ba !.. amma sai
sarkin ya nuna rashi damuwa. sai sarkin ya
tambayi saurayin yacemasa : ya kai saurayi !
kabani labarin wannan dan karamin tapki (kogi)
da kifaye masu launi – daban daban - da ke ciki
da kuma wannan masarauta mai girma da
nasameka a ciki da kuma dalilin da yasa na
sameka kai kadai kuma me yasa naga kana kuka
kana zubar da hawaye.
Da wannan saurayi yaji wannan magana daga
wurin wannan sarki sai hawaye suka zubo daga
idanunsa suka cika kumatunsa kuma yayi ta yin
kuka sosai har saida wannan saki yaji tausayinsa
kuma yayi mamaki sosai, to bayan haka sai
sarkin ya tambayesa yace : ya kai saurayi me
yasa kake kuka ? sai saurayin yace : me yasa
bazanyi kukaba ? irin wannan hali da nake ciki ?..
sai saurayin ya mika hannunsa ya daga rigarsa,
kawai sai sarkin yaga rabin jikin wannan saurayi
gabadaya dutse ne ( daga konkoso zuwa
kafarsa ) abunda ya kama daga cibiyarsa zuwa
kansa kuma siffar (DAN ADAM) ne.
To sai saurayin yacemasa : kasani cewa wannan
tapki da kagani yana da labari mai ban al ajabi
sosai, kuma akoi darasi ga wanda ya lura. Kuma
sai yace : kasani cewa mahaifina shine sarkin
wannan babban masarauta da ka gani, kuma
sunansa MAHMUD wanda yake mulkar wasu
kasashen baqin fata, kuma wannan tapki mai
kifaye da duwatsu guda 4 suna cikin
masarautarsa ne. kumu yayi mulkain wannan
masarauta kimanin shekara 70 sannan sai ya
rasu. sai nikuma na gaaji sarautar mahaifina
bayan rasuwarsa, sai na auri ‘yar bappa na
(kanin baba) kuma takasance tana matuqar sona
sosai ta yadda idan na tafi nabarta ita kadai bata
iya cin abinci har sai ta ganni, To sai nakasance
tare da ita har tsawon shekaru 5, to ananan
watarana sai wannan matar tawa – kuma ‘yar
bappana – ta fita ta tafi zuwa shagon da ake yin
kwalliya (saloon) ta barni a gida, kuma ta umurci
mai girki da ya shirya mana abincin dare, to
nikuma sai na shigo ciki na kwanta akan wannan
gado da ka ganni akai yanzu na yi bacci.
To daama matar tawa ta umurci ‘yan mata
(kuyangu) guda 2 da suzo wajene suyi mini
tausar jiki suke shafar fuskata kafin ta dawo. To
sai daya daga cikin yan matan ta zauna akusa da
kafafuna, dayar kuma ta zauna kusa da kaina,
nikuma a wannan lokaci inacikin matuqar
damuwa saboda kasancewar matata batanan ta
fita waje, a dalilin haka sai na kasa yin bacci,
amma kuma idanuna a rufe suke nayi kamar nayi
bacci zuciyata a farke take, wadannan ‘yan mata
suna mini tausar jiki sun dauka nayi zurfi a
bacci..

To sai naji daya daga cikin ‘yan matan – wanda
take zaune a kusa da kaina – tana gayawa ‘yar
uwarta – wanda take zaune akusa da kafafuna –
cikin kakkausar muriya : ya ke MAS’U’DATU : sai
dayar ta juya ta kalli wanda ta kira sunan nata.
sai wanda tayi kiran tace : umh mai martaba
(sarkin da yake bacci kenan) abun tausayi ne,
kuma asararre ne, saboda bai san abunda
wannan fitsararriyar matar tashi takeyi ba idan
tafita, sai dayar tace : ALLAH ya tsinewa matan
aure mazinata, kuma mutum mai daraja da
halaye masu kyau kamar mai martaba baidace da
wannan mata fitsararriya mazinaciya ba, wanda
kullum take zuwa ta kwana da wani kato a waje
amma shikuma mai martaba baisani ba, sai
wanda take kusa da kansa tace : ai mai martaba
baya cikin hankalinsa saboda kinga baya
tambayar ina take zuwa.. sai dayar tace : to ai
shi baisan abunda yake faruwa ba kuma baisan
halinta ba, saboda wannan tsinanniyar matar
tashi a kullum da daddare tana saka masa
magani a cikin ruwan da yake sha kullum kafin
yayi bacci, da zarar ya sha wannan ruwa baya
iya sanin abunda yake faruwa, koda yanke
naman jikinsa akayi bazai iya saniba, shi yasa
bazai san ina take zuwa da daddare ba kuma me
takeyi, saboda bayan ta bashi wannan magani
yayi bacci sai tayi kwalliya abunta tasaka kaya
mai kyau ta fita ta tafi abunta ta je ta kwana da
wani kato bazata dawo ba sai bayan sallar
asubahi, idan ta dawo saita hada masa wani
turaren wuta mai karfi sosai wanda idan hayakin
ya shiga hancinsa to sai ya farka, baisan wainar
da aka tauna a wannan dare ba, saboda karfin
wannan magani da ta bashi ya sha a ruwa.
Sai saurayin ya cigaba da bawa wannan sarki
labari yace : To bayan na saurari abunda
wadannan ‘yan mata suak fada, kawai sai naji
duniyar gabadayanta tayi mini matsi, haske ya
zama duhu a idanuna saboda tsananin bakin ciki,
bansan lokacin da dare yayi ba, kawai sai ga
matartawa ta dawo daga shagon da ake yin
kwalliya ( beauty saloon).
To bayan ta dawo, sai aka kawo mana abincin
dare mukaci dani da ita, sai muka zauna muna
hira, jim kadan sai aka kawo ruwan da nake sha
kafin inyi bacci, kuma daama tariga ta saka
magani a ciki kamar yadda ta saba, sai ta dauki
wannan ruwa ta mika mini, nikuma sai na karba
na dan juya gefe nayi kamar inasha amma
bansha ba, jim kadan sai na kwanta nayi kamar
nayi bacci mai nauyi, itama ta dauka nayi bacci,
sai naji tace : umh kayi bacci sosai kuma wallahi
bazaka farka ba har sai gari ya waye, wallahi na
tsaneka na tsani mai sonka na tsani ganin
siffarka, kuma na tsani kusantarka.
To Bayan haka, sai ta dauki rigarta ta saka, ta
fesa turare ta dauki takobinta ta rataya a
wuyanta ta bude kofar fada ta fita. To niku sai
na tashi na bita a baya bata saniba, bata
gusheba tana tafiya nikuma ina binta a baya har
sai da tashige ta cikin kasuwa ta fita nima ina
binta duk inda ta shiga tana ta tafiya har saida ta
iso kofar fita daga gari. Bayan ta iso wannan
kofa sai tayi wasu maganganu da bana
fahimtarsu, sai kofar ta budu, nikuma ina bayanta
bata sani ba har sai da ta iso wani gini mai
tsawo sannan sai ta shige ta wannan gini,
nikuma sai na hau saman ginin ina kallonta daga
nesa, kawai sai naga taje tasamu wani (bakin
bawa) mai muumunar halitta, bakinsa kamar
murfin kwano, duk jikinsa a jike yake, yana
kwance akan wasu itatuwa da ciyayi.

To Bayan ta iso gabansa sai ta tsunkuyar da
kanta ta durkusa ta gaisheshi ta gimamashi, sai
shi kuma ya bata rai, ya daka mata tsawa
yacemata - cikin fishi da bacin rai - : kaiton ki !..
me yasa kika bata lokaci baki fito da wuriba ?
gashi duk abokanaina gabadaya sun hallara a
wannan wuri, kowa yana tare da masoyiyarsa
amma ni inzaune ni kadai naki naci komai. sai
tacemasa : ranka ya dade mosiyana rabin raina,
shin bakasan cewa ni matar Aurebane ? kuma
dan bappana nake Aure (sarki) ? kuma kaima
kasan cewa babu wanda na tsana kamar wannan
mijin nawa, ina kyamar ganin mai kama da
surarsa, ina nisantar da kai a gareshi, da ba don
ina tsoron fishinka ba da na tsafe wannan garin
gabadaya, na tarwatsasa, ta yadda zai zamanto
babu komai a ciki sai hankaki da tsuntsaye, kuma
in kaurar da duwatsun dake cikin wannan gari in
kaisu bangon duniya.
Sai masoyin nata (wannan bakin bawan.)

yacemata -cikin fishi - : ke fitsararriya kariya kike
mini, wallahi na rantse daga yau idan kika kara
yin jinkiri baki fita da wuri, to ba zan kara
abokanta da ke ba, bazan kara hada jikin da
jikinki ba, mayaudariyar mace kawai.
Sai saurayin (sarkin) ya cigaba da bawa dayan
sarkin labari yacemasa : wallahi da naji maganr
da matata tayi da wannan bakin bawa kuma ina
kallo da idanuna – quru quru – kawai gabadaya
sai naga duniyar tazama duhu a idanuna, bansan
inda ruhina yake ba. Kuma bayan haka sai naga
matar tawa ta tsunkuya tana kuka ta qasqantar
da kanta tana rokon wannan baqin bawa tana
rarrashinsa akan ya yafemata tana cemasa : ya
masoyina rabin raina kayi hakuri, saboda banida
wani inba kai ba idan narasaka zan mutu, idan ka
koreni to ina zan je ? ya hasken idona dan ALLAH
kayi hakuri ! . bata gusheba tana ta kuka tana
kasqantar da kanta tana rokonsa har saida ya
yarda ya yafemata sannan sai tayi farin ciki ta ji
dadi.
To bayan haka, sai matar tawa ta tashi tseye ta
tube kayanta, tacewa wannan baqin bawa
(masoyinta) : ranka ya dade mosoyina ! shin akoi
abinci a wurinka ne wanda masoyiyarka zata ci ?

sai ya nunamata wani wuri yacemata taje akoi
dafaffen qasussuwan beraye ta dauka taci.
Bayan ta gama cin abici ta wanke hannu, sai
tazo ta kwanta tare da masoyin nata – baqin
bawa - a wani lungu, nikuma da naga abunda ‘yar
uwata kuma mata takeyi na cin amana a gabana
sai nakasa hakuri nayi yunkurin kashesu, su biyu
gabadaya. Sai na zaro takobina na soma da
wannan bawa da farko, na doke wuyarsa da
takobi.

To Alokacin da na bugeshi da takobina, sai nayi
tsammanin cewar ya mutu…..

Naga kamar wasu sungaji da karatu" sai ran juma,a idan Allah yakaimu.

Yusuf abdullahi A jibaga. Shike kawo muku wannan lbr dafatan mu kwana lafiya.
06 HIKAYAN MASUNCI DA IFRITU

wannan saurayi da aka tsafe – wanda kuma
shima sarki ne – ya cigaba da bawa dayan sarkin
labari, sai yace masa"

A lokacin da na zaro takobi na doke wuyar
wannan lalataccen BAWAN saboda in pille masa
kayi.sai na yanke fatar wuyarsa da makokoronsa,
amma ban raba kayinsa da gangar jikinsa ba, sai
yayi gurnani ya numfasa yayi nishi irin ta fitar
rai, ya daina motsi, to nikuma sai na zaci cewar
ya mutu.. To sai matarwa – ‘yar uwata – tafarka
daga bacci, - bayan ni nagudu na barwajaen –
kawai sai taga an sare wuyar BAWAN, sai ta
dauki wannan takobi da na pille wuyar BAWAN
dashi ta boyashi, bayan haka sai ta kama hanya
ta shigo gari ta dawo gida a cikin wani yanayi.
To Bayan matar tawa ta dawo ta shigo fada
jikinta amace, kawai sai ta kwanta akan gadona
har zuwa wayewar gari. Daga wannan rana, sai
matar tawa ta aske gashin kanta gabadaya
tasanya tufafin bakin ciki ( bakin tufafi ) ta soma
zaman makokin rashin wannan BAWA da takeso.
To bayan haka Sai matar tawa tacemini : ya ‘dan
uwana ! kar ka zargeni a bisa abunda kaga
nakeyi na zaman makoki, saboda labari ya iso
mini cewar mahaifiyata ta rasu, mahaifina ma an
kashe shi a wurin JIHADI ( yaki ) haka kuma ‘yan
uwana guda 2 daya anyi masa rauni a kayi,
dayan kuma gini ya ruso a kansa. saboda haka
na cancanci inshga wannan yanayi insanya
tufafin bakin ciki, kuma naga ya kamata inyi
zaman makoki inyi ta kuka in sanarwa duniya
bakin cikin da nake ciki.
Da naji abunda matar tawa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment