Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BAREWAR ta fuskanci bangaren sarki ta kalle
shi ta zuramasa idanu, sai ta durqusa qasa ta
tsunkuyar da kanta kamar tana gaisheda sarki
tana bashi girma,, kawai atake sai tayi tsalle ta
tsallaka wuyar sarki, ta arce a 100 ta gudu
abunta ta shiga daji… to da sarki yaga haka sai
yajuya wurin mutanen ( abokanen farautansa )
sai yaji suna qananan magan ganu a tsakaninsu
game dashi, sai yacewa wazirinsa : ya kai
waziri.. menene mutanen nan suke fada a
kaina ?? sai wazirin yace masa : wai sukace"

dazu kacemusu duk wanda BAREWA ta kubuce
ta gudu ta bangarensa to babu shakka za’a
kashe shi…. Da sarki yaji haka sai yace : wallahi
na rantse da ALLAH sai nabi wannan BAREWAR
na kamota na zo da ita…

kawai sai ya shiga daji
saboda ya kamo BAREWAR,, baigusheba yana
tatafiya a cikin daji yana bin wannan BAREWA
kuma TSUTSUN nasa yana bin BAREWAR yana
caccakar idanunsa har sai da ta yamanto baya
iya gani baya iya gudu… to sai sarkin yaciro
kibiyarsa ya harbeta.. bayan tafadi sai yaciro
WUQA ya yankata yafede ya ratayata a jikin
dokinsa ya kama hanya zai koma…

naga wasu sungaji da karatu.
RANAR ASABAR ZAMU DAURA INSHA ALLAHU DAFATAN KUN WUNI LAFIYA03 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU

Da sarki yaji haka sai yace : wallahi
na rantse da ALLAH sai nabi wannan BAREWAR
na kamota na zo da ita… kawai sai ya shiga daji
saboda ya kamo BAREWAR,, baigusheba yana
tatafiya a cikin daji yana bin wannan BAREWA
kuma TSUTSUN nasa yana bin BAREWAR yana
caccakar idanunsa har sai da ta yamanto baya
iya gani baya iya gudu… to sai sarkin yaciro
kibiyarsa ya harbeta.. bayan tafadi sai yaciro
WUQA ya yankata yafede ya ratayata a jikin
dokinsa ya kama hanya zai koma…
To a a lokaci da sarkin yake kokarin komawa
wurin abokanen farautarsa, ana zafin rana sosai..
to sai ishiruwa ta dameshi kuma yaga alamar
dokinsa ma yana matuqar jin ishiruwa.. sai sarkin
yajuya yaga wata bishiya mai inuwa sai ya zauna
a qarqashinta,, kuma sai yaga ruwa yana tsiyaya
daga saman wannan bishiya,, to sai ya dauko
kwariya ya ajiye a inda ruwan yake tsiyaya
saboda ya tari ruwan ya sha.. jim kadan sai
kwariyar ta cika, sai sarkin ya dauki kwariyar ya
ajiyeta a gabansa saboda ya sha,, kawai sai
wannan TSUNTSU ya zo a guje ya buge kwariyar
da qafarsa ya kifar da ita ruwan ya zube
gabadaya a qasa.. To sai sarkin ya dauki
kwariyar ya qara ajiyeta a inda ruwan yake
tsiyaya,, jim kadan sai kwariyar ta cika, sai ya
daukota ya ajiyeta a gaban wannan TSUNTSU
saboda ya dauka TSUNTSUN yana jin ishiruwa
ne, sai ya a jiye agabansa saboda ya soma sha
tukuna , amma duk da hakan sai TSUNTSU ya
qara buge kwariyar ya kifar da ita… To sai sarkin
yaji haushin wannan TSUNTSU… sai ya dauki
kwariyar a karo na uku ya qara a jiyeta har sai da
tacika sannan sai ya dauketa ya ajiyeta a gaban
dokinsa saboda dokin ya sha, sai ga wannan
TSUTSU ya qara zuwa ya buge kwariyar yakifar
da ita… sai sarkin yaji haushi yacewa TSUNTSUN
: amma anyi la’anannen TSUNTSU anan.. ka
hanani shan wannan ruwan, ka hana kanka sha,
ka hanawa dokina sha… me kake nufi ne ? kawai
sai ya zaro takobinsa ya buge TSUNTSUN ya cire
mata fikafikinta ! sai TSUNTSUN ya fadi gefe ya
numfashin fitan rai, jini na zuba daga jikinsa yana
motsi kadan kadan !! To bayan haka sai
TSUNTSUN ya soma daga kanasa sama yana
kallon sarkin yana masa nuni (ishara) da
idanunsa, yana gayamasa cewa : ka daga kanka
sama ka kalli saman wannan bishiya, sai sarkin
ya fahimci a bunda TSUNTSUN yake nufi,, sai ya
daga kansa sama ya kalli wannan bishiya, kawai
sai yaga wani katon maciji, wanda kuma wannan
ruwa dake zubowa daga saman bishiyar ashe
guban wannan macijinne ( wanda sarkin yake
kokarin tara saboda ya sha amma TSUNTSUN ya
hana shi ) da sarkin yaga haka sai yayi I’hu yayi
kuka saboda matuqar nadamar abunda yayiwa
wannan TSUNTSU na zalunci… bayan sarkin
yagama kukarsa sai ya dauki TSUNTSUN ya hau
dokinsa ya kama hanya ya koma wajen ‘yan
uwansa… TSUNTSUN kuma yana hannunsa, rai a
hannun ALLAH..

bayan ya isa wurin ‘yan uwansa sai yamiqa musu
wannan BAREWA da ya kamo, yace musu : ku
dauki wannan BAREWAR ku dafata.. sannan sai
sarkin ya zauna a kan kujera a gefe yana riqe da
TSUNTSUN … jim kadan sai TSUNTSUN yayi
dogon nishi ya mutu !! sai sarkin yayi I’huu mai
qarfin gaske saboda nadamar kashe wannan
TSUNTSU da ya tsirar da shi daga halaka….
Wannan shine labarin abunda yafaru da sarki
SINDI BADO..
To anan sai sarki YU’NAN yacewa wazrinnasa :
To ka gani kar inkashe wannan mutumi –
HAKIMU – inyi nadama kamar yadda sarki SINDI
BADO yayi nadama… da waziri yaji abunda sarki
YU’NAN ya fada sai yace : ya sarki mai martaba
mai daraja.. wannan qoqari da kaga nakeyi
saboda in rabaka da HAKIMU koda ya zamanto
akoi laifi a ciki ko cutarwa ai saboda kai nakeyi !!
kuma saboda ina tausaya makane kar ka hala…

idan kaji shawarata to ka tsira, idan kuma kaqi
zaka halaka kamar yadda wani waziri da ya yiwa
dan sarki wayo da dabara saboda ya halakar da
shi,, amma sai shi wazirin ya halaka… sai sarki
YU’NAN yace menene labarin wazirin da kuma
dan sarki ??
Sai waziri yacemasa : akoi wani sarki da ya
kasance yana da wani dansa da yake matuqar
son farauta a daji… to sai wannan sarki ya
‘umurci wazirinnasa da ya kasance tare da dan
nasa duk inda zai je.. to anan sai wata rana dan
sarkin ya fita zuwa daji, kuma wannan wazirin
yana tare da shi.. To bayan sun shiga cikin daji"
sai wazirin yaga wata dabba, sai yacewa dan sarki.

kabi wannan dabbar ka kamota nasan kai
jarumine .. shikuma dan sarkin da yaji haka sai
yasoma bin wannan dabbar ,, bai gusheba yana
ta binta ita kuma tana qara shiga cikin daji har
sai da tajanyo shi cikin duhun daji sannan sai
daga baya ya daina ganin wannan dabba atake
ta bacemasa… sai dan sarkin ya tseya ya juya
gaba da baya bai ga kowa, kuma bai san hanyar
da zai bi ya koma ba.. ya bata a cikin wannan
daji, sai ya rikice ya rude ya dimauce ya tsorata
bai san ina zai nufa ba… jim kadan sai ga wata
‘yar buduruwa ta bullo a gabansa tana kuka.. sai
ya tambayeta yacemata : daga ina kike ? sai
tacemasa : Ni ‘yar wani sarkine daga cikin
sarakunan qasar (INDIA) kuma nakasance
inatafiya ne a kan dokina sai gyengedi (bacci) ya
kamani sai na fado daga kan dokina, bayan na
farka sai na nemi dokin na rasa, to sai narasa
yadda zanyi, shine na kama hanya ina tafiya a
qafa har na iso wannan wurin…
da dan sarkin yaji haka sai ya tausaya mata ya
dauketa a kan dokinsa ya daurata a baya
shikuma yana gaba… sai suka cigaba da tafiya
har sai da suka iso kusa da wani TAPKI
( qaramin kogi ) sai yarinyar tacemasa : ranka ya
dade inaso ka sauqar dani anan saboda in biya
buqatata (fitsari) sai dan sarkin ya sauqar da ita,,
sai ta shiga.. bayan wani lungu ta yadda baza’a
iya ganinta ba,, sai shikuma ya tseya yana
jiranta.... kuma ta dau lokaci mai tsawo bata fito
ba… To jim kadan sai yace bari ya bita ya duba
ya gani me ya hana ta fitowa… ita kuma batasan
cewa yana binta a baya ba… kawai da ya shiga
wannan lungu sai leqa sai yaga wannan
buduruwa ta zama ALJANA (a surar dabba) kuma
yaji tanacewa : ‘ya‘yanta : ya ku ‘ya’yana kuna
ina ne ? kufito yau na nazo muku da wani saurayi
mai qwari mai nama.. sai yaran sukacewa
uwartasu ALJANAN : yawwa mama, dan ALLAH
ki kawo mana shi muci, dama yunwa mukeji,
cikinmu babu komai, ke muke jira…. Da wannan
dan sarkin yaji haka sai zuciyarsa ta buga, kuma
ya tabbatar da cewa kwanarsa ta qare babu
shakka zai zama nama ga wannan ALJANA..
bayan haka sai ya dawo baya hankalinsa atashe
idanunsa sun yi hawaye yana karkarwa.. jim
kadan sai ga wannan ALJANA ta dawo sai taga
dan sarkin yana cikin wani hali na tsoro yana
karkarwa… sai tace masa "

me yasameka ne naga
kamar kana cikin tsoro ? sai yacemata : akoi
wani da nake tare dashi, kuma ya kasance
maqiyina ne, kuma ina tsoron sa… sai ALJANAN
tacemasa : shin dazu bakacemini kai dan sarki
bane ? sai yacemata E’h tabbas ni dan sarki… sai
tacemasa : me yasa bazaka bawa wannan
maqiyin naka kudi ba saboda kasamu yardarsa ?
sai yacemata : Ai wannan maqiyin nawa baya
buqatan dukiya, ba’a samun yardarsa da kudi, shi
raina kawai yakeso.. Nikuma tsoronsa nakeji
sosai, kuma ni mutum ne wanda aka zalunta… sai
tacemasa : idan ka kasance mutum ne wanda
aka zalunta me yasa bazaka nemi taimakon
ALLAH ka yi tawakkali ka dogara da shi zai iya
kareka daga sharrin duk abunda kake tsoro….
Tosai dan sarki ya daga hannunsa sama yayi
addu’a yace : ya wanda yake amsa addu’ar
wanda yake cikin tsoro da matsi da fargaba idan
ya roqesa kuma yake kawar da muunan abubuwa
ya ALLAH ka bani nasara akan wannan maqiyi
nawa kuma ka kawarmini da shi,, sadoba kaine
mai iko akan duk abunda kakeso kayi… da
wannan ALJANA taji wannan addu’ar kawai sai
ta juya ta tafi abunta… sai shima dan sarkin ya
kama hanya ya koma gida abunsa… bayan dan
sarkin ya koma gida sai yasanar da mahaifinsa
sarki abunda wannan wazirin yamasa.. (wato
wazirin yamasa dabara ya turashi cikin daji idan
yamutu, sannan idan sarkin ya mutu sai wazirin
ya gaji sarauar sarkin) a daliln haka sai wazirin
ya rasa ranasa……
To sai wzirin sarki YU’NAN yacewa sarki YU’NAN
: ya mai martaba kaga kaima idan ka ciga da
yiwa HAKIMU DAUYAN alheri to babu makawa
zai kashe ka, saboda ya gaji sarautarka, kuma a
duk lokacin da ka kyautata masa ka kusantar
dashi ka sashi ajiki, to zai samu damar da zai
halaka ka... shin bakaga yadda ya warkar dakai
batare da ya baka magani ka sha kokuma ka
shafa ba ? kawai wata ‘yar sanda ya baka ka
riqeta ahannunka kawai sai ka warke ? To kar
kayi mamaki a nan gaba ma zai iya baka wani
abun kariqe da hannun kuma ka mutu ? …. To A
nan sai sarki YU’NAN yacewa wazirin nasa"

haqiqa kayi gaskiya.. wataqila abunda ka fada
zai zama gaskiya… ya kai waziri wanda ya iya
bada shawara da nasiha… wataqila wannan
mutumin - HAKIMU – dan leqen asiri ne,, ya zo
garinnan ne kawai saboda ya halakani.. kuma
haqiqa idan wannan mutumi zai iya warkar dani
daga cutar dake damuna da wani abu da zai bani
in riqe da hannuna,, to babu makawa zai iya
kasheni da wani abu da zai bani in shaqa ta
hanci…

To sai sarki YU’NAN yacewa wazirin : to yanzu
menene abun yi ? wace hanya zanbi in kashe
HAKIMU DAUYAN ? sai wazirin yacemasa : ka
Aika a kirawoshi yanzu, idan ya zo sai ka kashe
shi kawai ka huta da sharrinsa... ka kasheshi tun
kafin shi ya kasheka… sai sarki YU’NAN yacewa
wazirin nasa : kayi daidai ya waziri…

To bayan haka sai sarki YU’NAN ya Aika aka qira
HAKIMU… sai HAKIMU kuma yazo kamar yadda
ya saba batare da bata lokaci… bayan ya shiga
sai ya gaida sarki kuma ya yabeshi ya karanta
masa baitoci da qasidu na yabo da godiya kamar
yadda yasaba a kullum.. bayan gama sai sarki
yacemasa : kasan meyasa nasa aka kiraka a
wannan lokacin ? sai HAKIMU yace : babu wanda
ya san GAIBU sai ALLAH.. sai sarkin yacemasa :
na kirawokane saboda in kasheka in kawar dakai
a bayan qasa !! sai HAKIMU yayi matuqar
mamaki da jin wannan maganar kuma sai
yacewa sarkin : ya mai martaba me yasa zaka
kasheni ? wani laifi nayi da za’a kasheni ? sai
sarkin yacemasa : Naji labarin cewa kai dan
leqen asirine, ka zone saboda ka kasheni,,
shiyasa nace bari in kashe kafin ka kasheni..

kawai atake sai sarki YU’NAN yayi I’hu ya kira
mai pille kan mutane,, jim kadan sai ga wani
gardi ya shigo da takobi a hannunsa,, sai sarki
YU’NAN yacewa gardin : ka dauki wannan
makirin ka sare kansa ka hutar dani daga
sharrinsa.. sai HAKIMU ya zama abun tausayi ya
rasa abunda zaiyyi.. sai ya durqusa ya soma
roqon sarki YU’NAN ya cemasa : dan ALLAH kayi
min rai ! kaima ALLAH zai rahamaceka !.. kar ka
kasheni kaima ALLAH zai kashe ka… sannan sai
HAKIMU yayi ta maimaita masa yana roqonsa
kamar yadda nima nayi ta maimaita maka naroqe
ya ALJANI ALMA’RIDU akan kar ka kasheni
amma sai kaqi jin maganata…
To sai sarki YU’NAN yacewa HAKIMU DAUYAN :
NI hankalina bazai kwantaba sai na kasheka
tukuna.. saboda ka warkar dani da wani abu da
kabani na riqe a hannuna – sanda – To babu
makawa zaka iya kasheni da wani abu da zaka
bani in shaqa – in shishina- in mutu kokuma kayi
wata dabarar daban dan ka kasheni… sai
HAKIMU yace : ya mai martaba : yanzu wannan
shine sakayyar da zaka saka mini da ita ?? nayi
maka abu mai kyau kai kuma zaka sakamini da
muumuna ? sai sarkin yacemasa : babu makawa
sai na kasheka batareda bata lokaciba… To da
HAKIMU ya tabba cewa sarki YU’NAN zai
kasheshi babu makawa,, sai yayi ta kuka yana
zubar da hawaye, kuma ya zargi kansa saboda
irin abunda yayiwa sarkin amma sarkin kuma ya
saka masa da wannan sakayar..
To bayan haka sai wannan gardin - mai pille
kayin mutane – ya zaro takobinsa yacewa sarki :
ya mai martaba ina jiran izininka ne… shikuma
HAKIMU sai kuka yakeyi yana zubar da hawaye
yanacewa sarki : kayi mini rai kaima ALLAH zai
maka rahama, kar ka kasheni kaima ALLAH zai
kasheka… sai HAKIMU ya soma karanta wasu
baitici yace :

Nayi nasiha ban bandace ba, su kuma sunyi
zamba sai suka dace … to yau gashi nasihata ta
shigar dani gidan wulaqanci
Idan ALLAH ya rayar dani to bazan qara yin
nasiha ba, idan kuma namutu to ku isar da
saqona zuwa ga masu yin nasiha a bayana
dukkan abuna nafada
To sai. Bayan ya gama wakarsa sai"

HAKIMU yacewa sarki YU’NAN : yanzu
wannan shine sakamakona daga gareka ? zakayi
mini sakayyay irin sakayyar da akayiwa wata
KADA.. sai sarki YU’NAN yace : menene labarin
wannan KADAR sai HAKIMU yace : Ai yanzu
bazan iya baka wannan labari ba saboda irin
halin da nake ciki... sai yace : dan ALLAH kayi
mini rai, ALLAH zayyi maka rahama! Sai HAKIMU
yayi tazubar da hawaye yana kuka..
sai wasu daga cikin muqarraban sarki YU’NAN
suka tashi sukatashi sukacewa sarki YU’NAN : ya
mai martaba ! ka yafe mana jinin wannan
mutumi HAKIMU saboda bamu taba ganinsa yayi
wani abu na laifi da zai sa a kashe shi ba, kuma
mu dai bamu taba ganin yayi wani abu na laifi
ba, saidai ma gashi yazo ya warkar da kai daga
cutar da ta dukkan likitoci, babu wanda ya iya
warkar da kai daga cikin likitacin qasanan
gabadaya sai shi.. saboda haka bai kamata ka
kasheshi ba, sai sarki YU’NAN yacemusu :
bakusan dalilin da yasa nakeso na halaka
HAKIMU ba… saboda idan na barshi ya rayu, to ni
zan halaka babu makawa..

mutumin da ya warkar
dani daga cutar dake damuna da wani abu da
yabani na riqe da hannuna, ai babu shakka zai
iya kashe da wani abu da zai bani da zan shaqa
in mutu.. shi yasa yanzu nake tsoron kar ya
halakani bari Ni insoma halakashi
da HAKIMU ya tabbar da cewa sarki YU’NAN zai
halakashi babu makawa, sai yacewa sarki
YU’NAN : ya mai martaba ! idan har ya kasance
babu nakawa sai ka kasheni, ina neman alfaram
ka dan sauraramini ka bani dama inkoma gidana
inbiya buqatuna kuma inyi WASIYYA ga iyalina da
maqotana kuma in sanardasu warin da zasu
bunne ni idan ka kasheni,... sannan kuma !! Akoi
wani littafi na likitanci da nakeso inbaka wanda
zai anfaneka bayan mutuwana, kuma Akoi wani
littafin daban kebabbe wanda ba kowa nake
bawa ba, inason inyi maka kyautar wannan littafi
ka ajiye sa a wajenka saboda zai anfaneka
sosai…
sai sarki YU’NAN yace masa : wannan wani irin
littafine kuma menene a ciki ?? sai HAKIMU yace
: wannan littafi yana dauke da a bubuwa masu
dimbin yawa sosai wanda baza’a iya irgawa ba,,
kadan daga cikin abubuwan dake cikin wannan
littafi na sirri shine kamr haka : bayan ka sare
(pille) kaina sai ka bude wannan littafi kuma sai
ka bude shafuka guda 3, sannan sai ka karanta
layi 3 daga shafin farko daga hannunka na hagu,
idan kayi haka to (KA'YIN NAWA) da ka sare
zayyi maka magana, kuma duk tambayar da
kamasa zai amsa maka…

da sarki YU’NAN yaji
wannan magana sai yayi mamaki matuqa.. ya
girgiza kansa saboda mamaki.. yacewa HAKIMU
: yanzu idan na sare kanka zayyi mini magana ??
sai HAKIMU yace : tabbas hakane.. sai sarkin
yace : wannan abun mamakine ! sannan sai sarki
YU’NAN ya amince masa da yaje gida ya biya
buqa tunsa ya dawo kuma ya turashi tare da
masu tsaronsa…
bayan HAKIMU ya koma gida ya biya buqatunsa,
a rana na 2 sai ya dawo wajen sarki YU’NAN…
bayan ya shiga fadar sarki sai ya samu wazirai
da hakimai da dukkan muqarraban sarki sun
bayyana a fada… fada ta cika makil manyan gari
kowa ya hallara…

To sai HAKIMU ya tashi ya tseya a gaban sarki
YU,NAN yana riqe da wani tsohon littafi, kuma a
cikin wannan littafi akoi wani abu kamar kwalli
(gaari-gaari) da wani sinadari da kuma abun
rubutu (alqalami)… To jim kadan, sai HAKIMU ya
zauna akan kujera yace "a kawomini faranti
(plate) sai aka zo da faraniti,, sai yayi rubutu a
cikin wannan farani .. sannan yacewa sarki
YU,NAN : ya mai martaba ka dauki wannan
littafin,, kuma kar kayi anfani da shi sai bayan ka
sare kaina tukuna,, idan ka sare ka'yin nawa sai
ka saka a cikin shi wanna farantin, sannan sai ka
bada umurnin a danne kayin nawa ackin wannan
faranti, bayan nan jinin dake tsiyaya zai yanke ya
tsya.. sannan sai ka bude littafin…

Da sarki YU’NAN yaji haka atake sai ya soma
bude shafin littafi tun kafin ya aiwatar da abunda
HAKIMU ya gayamasa, ya qosa yayi gaggawa
saboda ya tabbatar da abunda HAKIMU ke fada
gaskiyane ? …. Tosai sarki YU’NAN ya bude shafi
(page) na farko sai yaga shafin ya mannu da
shafi na biyu kuma ya yaqi buduwa, To sai ya
saka ‘yar yatsarsa a cikin bakinsa saboda ya
jiqata da nyawu saboda ya samu sauqin bude
wannan shafi da yaqi buduwa .. bayan ya saka
‘yar yatsarsa a cikin bakinsa ya jiqata,, sai ya
bude shafi na 1 da na 2 da na 3 kuma ko wanne
shafi yana bashi wahala wajen budewa.. a haka
har ya bude shafuka guda 6 amma bai ga rubutu
a ciki ba, ko harafi daya babu…sai sarkin yace :
ya HAKIMU : ni ban samu komai a cikin wannan
littafi ba ?… sai HAKIMU yace : ya mai martaba
ka cigaba da budewa zaka samu abun mamaki a
ciki wannan littafi… sa sarki YU’NAN yacigaba da
budewa… To ana cikin haka bayan wasu ‘yan
mintuna.. sai guba ta shiga jikin sarki YU’NAN ta
yadu a jikinsa (wato wannan abu mai kama da
kwalii na cikin littafin gubane) To sai sarki ya
soma juye juye yana kar karwa, kawai sai yayi
I’hu yace : ya jama’a ! guba ta shiga jikina !
kawai sai ya fadi qasa ya mutu nan kwanarsa ta
qare….

Sai mai kamun kifi yacewa ALMA’RIDU : ya
ALMA’RIDU kasani cewa : da sarki YU’NAN bayyi
qoqarin kashe HAKIMU ba, to da ALLAH ba zai
halaka shi ba, amma sai sarki YU,NAN ya yarda
da zugar wazirinsa yaso ya zalunci HAKIMU ba
tare da wani haqqi ba (laifi) sai ALLAH ya kawar
masa da basirarsa,, HAKIMU yayi nasara a kansa
da hikimarsa da dabararsa…

To kaga kaima da bakayi qoqrin halakani ba, da
ALLAH ba zai mayarda kai haka ba.. yanzu gashi
kana cikin qasqanci sai yadda nayi da kai.. kuma
babu makawa sai na maka abun HAKIMU yayiwa
sarki YU’NAN …..

RANAR LITININ ZAN DORA INSHA ALLAHU".

By Yusuf abdullahi A jibaga

What'sapp
0807105113804 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU

Wannan bawan ALLAH mai kamun kifi yacewa ALJANI
ALMA’RIDU : ya ALMA’RIDU... kaga yanzu daa
sarki YU’NAN bayyi qoqarin kashe HAKIMU ba, to
da ALLAH bai halaka shi ba.. to amma sai sarki
YU,NAN ya amince da shawarar wazirinsa, yaso
ya zalunci HAKIMU ba tare da wani haqqi ba
(laifi).. sai ubangijin ALLAH ya kawar da
basirarsar sarki YU’NAN… HAKIMU yayi nasara a
kansa…
To kaga kaima da bakayi qoqrin halakani ba, da
ALLAH ba zai mayar da kai haka ba.. yanzu gashi
kana cikin qasqanci sai yadda nayi da kai.. kuma
babu makawa kaima sai na maka irin abun
HAKIMU yayiwa sarki, zan rufeka a cikin wannan
tulun sannan injefaka cikin wannan kogin har
zuwa tashin Qiyamah …

Da ALMA’RIDU yaji maganar da mai kamun kifi
ya fada sai ya qolla I’hu yace : dan girman
ALLAH kar kayi haka,, kayi mini halacci kar ka
halakani.... kar ka dubi halina,, idan NI na
kasance mai mugun haline, to kai kuma ka
kasance mai kyautatawa,, saboda masu magana
sukace : ( ya mai kyautatawa wanda yayi masa
mugunta… kabar mugu da halinda ) kar irin
abunda AMAMATU yayi wa A’TIQA… sai mai
kamun kifi yace : menene ya faru tsakaninsu ?
sai ALMARIDU yace : wannan lokacin ba lokacin
bada labari bane,, yanzu ni inacikin kurkukune,
bazan iya baka wannan labari ba, yanzu
hankalina a tashe yake,, bazan iya yin komai ba
har sai ka fitar dani daga cikin wannan tulu,, idan
ka fitar da ni to zanbaka wannan labari…
sai mai kamun kifi yace : Ai yanzu babu makawa
sai na jefaka cikin wannan kogi, kuma babu wata
hanya da zaka iya bi dan ka fita daga ciki…shin
ka manta cewar dazu na rarrasheka na lallabeka
na durqusa a gabanka saboda kar ka kasheni,
amma kaqi, kace sai ka halakani babu makawa
batareda wani laifi da na aikata ba ?, kuma babu
abunda na maka sai alheri kasancewata na
fitarda kai daga cikin kogi…

Alokacin da kace sai ka kasheni sai na fahici
cewar kai kana daga ciki asalin mugayen
ALJANU la’anannu… kuma ka sani, zan jefaka
cikin wannan kogi, duk wanda yazo saboda ya
ceceka ciroka zan bashi labarin irin halayenka
kuma in gargadeshi saboda koda ya ciroka a
cikin rashin sani to zai mayar da kai kayi tazama
a ciki har zuwa qarshen zamani, saboda kayi ta
ganin azaba kala kala kafin tashin qiyamah….
Sai ALMA’RIDU yacemasa : dan ALLAH ka fitar
dani kar ka halakani, saboda nalura naga kai
mutumne mai mutunci mai halacci kuma yanzu
lokacine na afuwa, namaka alqawari bazan cutar
da kai ba idan ka fitar dani daga cikin wannan
tulun, kuma zan baka wani abu da zai anfaneka
ya arzuktaka har abada.. sai mai kamun kifi yaji
haka sai ya tausayawa ALMARIDU.
To Anan sai ALMA’RIDU da mai kamun kifi suka
kulla yarjejeniya sukayi alqawari akan cewa idan
ya yafitar da shi - ALMARIDU - ba zai cutar da
shiba, kuma ALMA’RIDU zai kyautata masa har
abada,, To sai ALMA’RIDU ya rantse da sunan
ALLAH mai girma… sai mai kamun kifi ya bude
tulun,, sai ga hayaqi ya fito daga cikin tulun,
kuma ya nufi sama, sannan sai ya hadu a wuri
daya, kawai sai ALMA’RIDU ya bayyana a cikin
mumunan halitta..

bayan ya fito sai ya buge wannan tulun da
kafarsa (yayi ball da ita ) sai ta fashe ta watse
ta shiga cikin kogi… da mai kamun kifi yaga
ALMA’RIDU ya buge wannan tulu ya fasata sai
ya tsorata ya firgita zuciyar ta buga har sai da
yayi fitsari a wandonsa, kuma ya tabbatar da
cewa babu shakka kwanarsa ta kare, kuma yace
- azuciyarsa - : wannan alamun ba na alkairi
bane,, sannan sai ya nuna jarunta ya cire tsoro
yacewa ALMA’RIDU : ya ALMA’RIDU ka sani
cewa ALLAH yace : (KU CIKA ALQAWARI
SABODA ALQAWARI ABUN TAMBAYA NE)
kuma dazu
kayi mini alqawari kayi rantsuwa akan ba zaka
cutar da ni ba,, yanzu idan ka cutar da ni,, To
ALLAH zai nuna maka, kuma dazu idan baka
manta ba na baka labarin irin abunda ya faru
tsakanin sarki YU’NAAN da HAKIMU DAUYAN da
irin rokon da HAKIMU yayi wa sarki YU’NAN aka
kar ya kashe shi…
. Da (ALJANI ALMA’RIDU) yaji abunda mai
kamun kifi ya fada sai ya kyal kyale da dariya
saboda ganin yadda mai kamun kifi ya tsorata ya
razana.. To bayan haka sai ALMARIDU ya soma
taku yana tafiya har yawuce taga gaban mai
kamun kifi,, sai yacewa mai kamun kifin : ya kai
mai kamun kifi ! ka biyoni a baya,, sai mai kamun
kifi ya bi ALMARIDU a baya yana cikin wani
yanayi na tsoro da tashin hankali dakuma rashin
yarda,, saboda yana ganin kamar ALMARIDU zai
hallakashi….

Sai suka cigaba da afiya har sai da suka bar
bayan gari,, bayan wani dan lokaci sai suka iso
wurin wani babban dutse, sannan suka hau
saman wannan dutse suka sauko,, sannan sai
suka ga wani dan tapki (karamin kogi) mai fadi
kuma a tsakiyansa akoi wani tapkin daban - dan
qarami -,,
To anan sai ALMARIDU ya tseya a wurin wannan
kogi, sai ya ‘umurci mai kamun kifi da ya jefa
shingensa saboda ya kama kifi,, sai mai kamun
kifi ya qura idanunsa ya kalli wannan tapki (kogi)
na ruwa sai yaga kifaye masu launi daban daban,
- Akoi launi (kala) FARI akoi JAA akoi BLUE da
kuma YELLO, To sai mai kamun kifi yayi mamaki
matuqa…
bayan haka sai ya jefa shingensa, bayan ya
saurara zuwa wani dan lokaci, sai ya janyo
shingen nasa,, sai ya samu kifaya guda 4 a
ciki,... kowani daya daga cikin kifayen launinsa
daban yake ( FARI - JAA - BLUE - YELLO )…
. Da mai kamun kifi yaga haka sai yayi farin ciki
sosai…To sai ALMARIDU yacemasa : ka dauki
wadannan kifayen ka kaiwa sarki,, ka bashi
kyauta,, shi kuma zai baka dukiya mai yawa
wadda zata wadatar da kai…
sannan sai ALMA’RIDU yacewa mai kamun kifi :
dan ALLAH kayi mini uziri ! saboda ni na kasance
cikin wannan kogi har tsawon shekara 1800 ban
taba ganin dunuya ba sai yau, saboda haka zan
tafi, zan barka anan,, kuma inaso inyi maka
WASIYYAH dacewa : kar ka kama kifi a cikin
wannan kogi a kowani rana,, a sati sau daya
kawai zaka kama kifi,, sannan inamaka ban
kwana… sai ALMA’RIDU ya bugi qasa da kafarsa
sai qasar ta budu sai ALMA’RIDU ya lume ciki ya
bace abunsa ya tafi…
To sai shima mai kamun kifi ya kama hanya ya
koma gida abunsa yana matuqar farin ciki da
mamakin abunda ya faru da shi tare da
ALMA’RIDU..

Bayan mai kamun kifi ya isa gida,,

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment