Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tagaya mini sai nayi
shiru na dan wani lokaci ban cemata komai ba,
sannan daga baya sai nacemata : kiyi abunda
kike ganin ya dace, ni bazan hanaki ba.. To tun
daga wannan rana, matar tawa bata gushe ba
tana cikin wani yanayi na bakin ciki da damuwa,
tana kuka har tsawon shekara 1….

To ananan haka, Bayan ta cika shekara tana
kuka, watara sai tacemini : ya dan uwana ! ina
neman alfarma a wurinka, inaso ka bani dama in
gina kabari ( gidan makoki ) a cikin fadarka
saboda inkadaita a ciki da bakin cikina, kuma zan
sanyawa wannan wuri suna : ( gidan bakin ciki )
ko gidan makoki.. sai nacemata : babu komai kiyi
duk abunda kikaga yadace. To sai ta gina gidan
makoki da kabari mai girma a cikin fadartawa,
sannan sai ta kaurar da wannan BAWA ta
kawoshi ta ajiyeshi cikin wannan makoki da ta
gina. shikuma wannan BAWA – masoyinta matar
tawa – tun daga wannan rana da naso na
halakashi amma banyi nasara ba, ya kasance
yana cikin tsananin rauni da rashin lafiya ko
matsi baya iya yi, baya iya anfanar da ita da
komai, shi dai kawai yana iya shan ruwa da
sauransu.. tun daga wannan rana da na masa
rauni baya iya magana shi dai kawai yana raye
ne, saboda ajlinsa bai kareba.
To Sai matar tawa ta kasance cikin kullum a
cikin dawainiyar wannan BAWA, A kullum- safe
da yamma - sai ta shiga wurinsa a daki ta zauna
tayi ta kuka tana zubar da hawaye. Kuma tana
bashi duk abunda yake bukata na abubuwan sha.

bata gushe ba tana cikin wanna yanayi na
dawainiyar wannan BAWA - safe da yamma - har
A ka shiga shekara ta biyu. Nikuma na cigaba da
hakuri da ita, na kai zuciyata nesa na zura mata
ido ina kallon abunda takeyi..
Ananan Bamu gushe ba muna cikin wannan
yanayi, har saida watarana na shiga wannan daki
namakoki da ta gina ta ajiye BAWAN a ciki, - ba
tare da saninta ba -.. Bayan na shiga cikin
wannan daki sai na sameta a ciki ta daura
hannunta akanata tana kuka saboda tsananin
bakin ciki, tana raira wadannan baitoci kamar haka.

((Na kasa samun kaina a rayuwa bayan na
rasaka))
((Hakika zuciyata bata kaunar wani in ba kai ba))
((Ka dauki gangar jikina nama kyauta duk inda
zaka))
((Duk inda ka mutu a ka bunneka abunneni kusa
da kai))
((Idan ka kira sunana a kusa da kabarina To ))
(( Sautin motsin kasussuwata zasu amsa
kiranka.

Bayan ta gama raira wannan waka, nikuma in
tseye a bayanta bata sani ba, sai na zaro
takobina nacemata :Ai daama wannan shine irin
zancen da mata mayaudara masu cin amana
sukeyi, wadanda suka ki kusantar mazajensu,
suka tauye hakkin Aure.. Bayan na fadamata
wannan magana, sai ta fahimci cewa tabbas nine
na raunata wannan BAWA da takeso. kafin ta
juyo sai nayi yunkurin daga hannuna sama
saboda in halakata da wukar dake hannuna..
kawai sai ta tashi ta tseya daram da kafafunta ta
kalleni – cikin fishi da bacin rai – nikuma na
daga hannuna sama ina rike da wuka, amma na
kasa yin komai.. bayan ta tashi sai ta furuta
wasu kalmomi (maganganu) da bana fahimta,
bayan haka sai tace : Don darajan furucin da nayi
ALLAH ya zamar da rabin jikinka dutse rabinka
kuma DAN ADAM, Atake sai halittata ta canza na
zama kamar yadda ka ganni, sai na kasance a
cikin wannan yanayi bana iya tashi balle in
zauna, nidai kawai ganinan ba macecce ba kuma
ba rayayyeba. ( saurayin yake bawa wannan sarki
labari )
To sai ya cigaba da cemasa : bayan na zama
kamar yadda ka ganni, sai wannan matar tawa ta
tsafe wannan gari nawa da kasuwanni da gonaki
dake ciki gabadaya.. kuma daama a garin nawa
Akoi al’umma – daban daban – har guda 4.. Akoi
MUSULMAI, da NASARA (kirista) da YAHUDAWA
da MAJUSAWA ( masu bautawa rana da wuta)
duk a cikin wannan gari nawa.. to sai matar tawa
ta sihirce (tsafe) su gabadaya ta zamar da su
kifaye. fararen kifayen sune MUSULMAI, jajayen
kuma sune MAJUSAWA, warawara (blue) sune
NASARA, sudin kuma sune YAHUDAWA..

Bayan haka, sai ta sihirtar da sauran garurruwan
baqaqen fata guda 4 da suke cikin masarutata ta
zamar da su manyan duwatsu, sai ta zagaye
wadannan duwatsu da wannan tapki da kagani..
sannan kuma kowane rana sai ta zo ta azabtar
da ni tayi mini bulala 100, da bulalar irin ta fata,
har sai jini ya koraro daga jikina.. sannan sai ta
sakamini rigar da aka saaqa (dinka) da gashi ta
lullubeni da shi saboda ya kara mini radadi…
To a nan sai wannan surayi yayi ta kuka, hawaye
suna korarawa daga idanunsa, ya raira wannan
wakar kamar haka"

(Ya ALLAH Nayi hakuri da qaddara da
hukuncinka)
(Ni mai ahkurine idan har Akoi yardanka a ciki)
Hakika na ina cikin kunci na abunda ya sameni
(Amma nayi ta wassuli da zuri’ar annabi
yardajje.

Da saurayin ya gama wannan waka, sai idanunsa
suka koraro da hawaye ya fashe da kuka.. haka
shima sarkin idanunsa suka koraro da hawaye
saboda tausayawa halin da saurayin yake ciki..
sai wannan sarki ya daga kansa ya kalli saurayi
yacemasa : ya kai samari ! hakika ka kara mini
bakin ciki da damuwa a cikin zuciyata. Sannan
sai ya tambayesa yacemasa : yanzu a ina
wannan matar taka take ? sai saurayin yacemasa
: tana tare da wannan BAWA (masoyinta) a cikin
wannan gidana makoki da tagina, a kullum tana
ziyartarsa sau daya a rana, kuma kafin taje
wurinsa sai tazo wurina ta tube mini rigana tayi
mini bulala 100, inyi ta I’hu ina kuka har ingaji,
kuma gashi bana iya motsi balle inkare kaina
daga radadin bulalarta,sannan bayan ta gama
azabtar da ni, sai ta wuce ta tafi wurin wannan
BAWA ta biyamasa bukatunsa tabashi abun sha
ya sha, saboda baya iya cin abinci tun lokacin da
na raunatashi.
Da wannan sarki yaji wannan magana daga wurin
saurayin sai yacemasa :wallahi na rantse da
ALLAH sai na taimaka maka nayi maka irin
alherin da za’a tuna da ni ko bayan raina, sai na
maka abun alfahari wanda zai zama tarihi bayan
raina. Sannan sai sarkin ya zauna tare da
wannan saurayi yana hira tare da shi yana dauke
masa kewa har zuwa dare.Sannan da dare yayi,
al fijir ta kusa ketowa, sai sarkin ya tashi ya tube
kayansa ya dauki takobinsa ya rataya a wuyarsa,
ya nufi wurin da wannan BAWA yake kwance
(makoki).
Bayan ya shiga wannan wuri sai ya ga pitila da
kendir a kunne. a wani gefen kuma, sai ya ga
turaren wuta da magunguna da sauransu….

Sannan sai ya ga wannan BAWA a kwance . To
da yaga haka, baiyyi wata wata ba, kawai sai ya
zaroo takobinsa ya lumawa wannan BAWA ya
karasashi ya kasheshi, sannan sai ya daukeshi
yanufi rijiya da shi ya jefashi a ciki. bayan haka
sai ya dawo ya dauki rigar wannan BAWA ya
saka. sai ya koma ya shiga dakin BAWAN
(makokin) da takobinsa a hannusa ya zauna cikin
shiri..
Bai gushe ba yana zaune, bayan kamar Awa 1,
sai ga matar ta shigo cikin fadar, isowarta ke
dawuya sai ta shiga dakin da wannan saurayi
(mijinta) yake, sai ta dauki bulala tayi ta zabga
masa, shikuma sai I’hu yake yana – wayyo
wayyo – yana I’hu yanacewa : dan ALLAH kibarni
da abunda nake ji, kiyi min afuwa, ki rahamceni,
sai tacemasa : shin kai ka rahamci masoyina
ne ? sannan da ta gama sai ta sakamasa riga
(wanda aka saqa da gashi ) ta yadda zai kara
masa radadin ciwo. Sannan sai ta nufi dakin
masoyinta BAWA da abinci a hannunta.
To shikuma sarkin da yaga tanufi dakin da yake,
sai ya kwanta akan gadon BAWAN ya lullube
jikinsa yayi kamar yana bacci. sai matar ta shigo
cikin dakin, da shigarta kawai sai ta zauna ta
soma kuka tace : ya masoyina dan ALLAH kayi
mini magana, dan ALLAH kayi min zance mana
inji dadi a raina.. Sai ta cigaba da kuka tana
cewa dan ALLAH kayi magana inji sanyi a raina.
To sai sarkin ya kankatar da muriyarsa ya
karkatar da hashensa yayi irin muriyar baqin fata
(BAWA) yayi nishi irin ta marasa lafiya yace :
AA’h, LA HAULA WA LA QUWWATA….
Da matar taji yayi magana sai tayi I’hu saboda
tsananin murna har sai da tasuma dan farinciki..

bayan ta farka sai tace : - cikin murna - watakila
masoyina ya samu lafiya ? . sai sarkin ya
kankantar da muriyasa yace : ya ke fitsararriyar
mata, baki cancanci inyi miki magana ba, sai
tacemasa : menene dalilin haka ? me nayi maka
ne ? sai yacemata : a kullum da rana kina
azabtar da mijinki yana ta I’hu yana rokonki har
yana hanani bacci da daddare, kuma bayan kin
tafi sai mijin naki yayi ta qasqantar da kansa ga
ubangiji yana ADDU’A yana kai kukarsa ga ALLAH
yana kararki har sai da sautin muriyarsa ta
hanani nitsuwa ta samini damuwa a cikin
zuciyata, da ba don haka ba, da tuni na samu
sauki na warke.. Shi yasa naki nayi miki mgagna
dazu. To Sai tacemasa : ya masoyina idan ka
amince zan warware masa wannan sihiri saboda
kasamu kwanciyar hankali da nitsuwa da
isheshen lafiya. Sai yacemata : kije ki
warwaremasa wannan sihiri ki hutar damu mu
samu nitsuwa a ranmu. sai tace : to ranka ya
dade kamar yadda kakeso haka za’a yi.
Sai ta tashi cikin sauri ta fita ta nufidakin da
mijin nata yake (saurayi), shigarta dakin sai ta
samesa a zaune yana kuka. sai ta dauko kwano
ta cikashi da ruwa ta yi wasu maganganu
(furuci)da ba fahimata, sai ta tofa a cikin
wannan ruwa, sai ruwan ya soma tafasa, bayan
haka sai ta yayyafawa mijin nata tece : don
darajan furcin da nayi (tofi) ka fita daga wannan
halittar ka koma halittarka ta farko, To sai
saurayin ya kumbra ya canza kamanni ya koma
halittarsa ta farko - cikekken DAN ADAM –To sai
ya tashi ya tseya da kafafunsa yayi farin ciki
sosai ya godewa ALLAH yayi salati ga ANNABI
(S.A.W) sannna sai matar tasa tacemasa : ka
fita daga wannan wurin ka bar garinnan kar ka
kara dawowa, idan ka dawo zan kasheka, sai ta
daka masa tsawa tace ya fita yabata wuri,
shikuma bai ce komai ba, sai ya kama hanya ya
fita abunsa.

Bayan haka sai wannan mata to koma daki wajen
wannan sarki, ta samesa yana kwance akan gado
jikinsa a lullube. Da shigarta sai tacemasa"
ranka ya dade na Aiwatar da abunda kakeso, dan
ALLAH ka bude fuskarka inganga. Sai ya
kankantar da muriyarsa yacemata : wani irin abu
ne kike ganinizakiyi ki kwantar mini da hankalina
ki cire mini damuwar da ke cikin zuciyata.?? Ai
abunda kikayi bakiyi komai, saboda baki aiwatar
da asalin abunda nakeso ba. Sai tace masa"

menene asalin abunda kake so ya masoyina? sai
yace : mutanen wannan garin da kuma garurruwa
da suke hade da wannan garin da kika shiratar
da su. kullm idan dare yayi sai wadannan kifayen
su ke daga kawunanasu sama suna ADDU’A suna
rokon ALLAH tare da tsinemana dani da ke.
Kuma wannan shine dalilin rashin samun sauki
da lafiya a gareni, saboda haka inaso ki je ki
warware musu wannan sihiri sannan sai kizo ki
kama hannuna ki tseyar da ni saboda yanzu na
samu lafiya.

Da wannan mata taji abunda sarkin ya fada,
kuma ta dauka wannan BAWAN ne, sai tacemasa
– a cikin farin ciki - : to ranka ya dade kamar
yadda kake so haka za’a yi. Sai ta tashi ta mike
cikin farin ciki ta fita a guje ta nufi inda wannan
tapki yake. isowarta ke da wuya (wurin tapkin),
sai ta dibi kadan daga cikin ruwan wannan tafki.

Ranar lahadi zan daura wanda insha Allahu nake sa ran gama labarin duka

Yusuf abdullahi A jibaga07 HIKAYAN MASUNCI DA IFRITU.
KARSHE,
wannan sarki dake kwance akan gadon ( BAWA )
– mara lafiya - ya umurci wannan fitsararriyar
matar (matsafiya) SAI yacemata : yanzu inaso ki
je ki warware wannan sihiri, sannan sai kizo ki
kama hannuna ki tseyar da ni saboda na samu
lafiya.

To Da wannan mata taji abunda sarkin ya fada,
kuma ta dauka wannan BAWAN ne, - masoyinta -
sai tacemasa – cikin farin ciki - : to ranka ya
dade kamar yadda kake so haka za’a yi. Sai ta
tashi ta mike - cikin farin ciki - ta fita a guje ta
nufi inda wannan tapki yake.
Bayan ta iso wurin wannan tapki sai ta dibi
kadan daga cikin ruwan tapkin, ta yi wani furuci
(maganganu – ko lafuza) da baa’a fahimta, ta
tofa a ciki, jim kadan sai wadannan kifaye suka
motsa suka daga kawunansu, sannan atake sai
halittarsu ta canza suka zama ‘yan ADAM –
kamar yadda suke da farko – sihirn ya warware
wa mutanenn wannan gari , sai garin ya koma
kamar yadda yake da farko – agine – kasuwanni
a bude, kowa yana harkarsa, ana ta hadahada,
kamar babu a bunda yafaru, kuma wadannan
duwatsu guda 4 suma suka koma kamar yadda
suke ( daama sune qasashe baqaqen fata da ta
tsafe su suka zama manyan duwatsu gudu 4 da
suka zagaye tapkin ) to sai suma duwatsun suka
koma kamar yadda suke da farko yan ADAM.
To bayan haka, atake sai wannan mata – makira
ma tsafiya – ta juya ta koma wurin wannan
sarki, kuma ta dauka cewa wannan BAWAN ne
wanda take so. Da isowarta wurinsa sai
tacemasa : ya masoyina ! na aiwatar da abunda
kakeso, ka miko mini hannunka mai al-barka in
tsunbata inji dadi a raina. Sai sarkin ya kankantar
da muriyarsa yace : to ki matso kusa dani,
motsowarta ke da wuya kenan sai ya zaro
takobinsa ya luma mata a kirji har sai da takobin
ya fito ta bayanta sannan sai ya tsagata ya raba
gangan jikinta biyu ya aikata lahira, a nan
kwananta ya kare..
Sannan sai sarkin yafito waje ya sami wannan
saurayi – mijin matar – yana tseye yana jiran
fitowarsa, sai sarkin ya taya saurayin murnar
kubuta daga halin da yake ciki - na wannan mata
-, kuma sai saurayin ya rungumi wanna sarki ya
gode masa, sai sarkin yacemasa : zaka zauna a
wannan gari naka ko kuma zamu tafi tare zuwa
masarutata (garisa) ? sai saurayin yacemasa :
ranka ya dade sarki ! shin kasan tsawon tafiyar
da ke tsakaninka da masarautarka kuwa ? sai
sarkin yace : kwana biyu da rabi ne kawai.. . sai
saurayin yayi dariya yacemasa : ya mai
martaba ! idan bacci kake to ka farka, tafiyar da
ke tsakaninka da masauratarka tafiyar shekara
daya ne cib ga mai tafiya da sauri kenan,..

abunda yasa ka iso wannan gari nawa a cikin
kwana biyu da rabi, saboda wannan fitsararriyar
matar tawa ta tsafe garin ne shi ya sa. Amma
yanzu dunda komai ya koma daidaita, to babu
makawa zakayi tafiyar shekara daya cib kafin ka
iso masarautar ka, sai wannan sarki yayi mamaki
matuqa da jin wanna maga. Sannan bayan haka
sai saurayin yacemasa : ya mai martaba wallahi
ina qaunarka bazan taba rabuwa da kai ba,
saboda kayimini abunda bazan taba mantawaba.
Sannan sai suka rungumi juna suka yi farin ciki
matuqa.. sannan sai sarkin yace : godiya ta
tabbata ga ALLAH wanda yayi mini Ni’ima ya
hadani da kai, yanzu ka zama 'dana, saboda
ALLAH bai arzuqtani da (‘DA ) ba duk tsawon
rayuwata, sannan sai suka kara runguman juna
sukayi farin ciki, sai suka nufi cikin fadar
masarautar wannan saurayi, sai saurayin ya tara
muqarrabansa da fadwansa ya gabatar musu da
wannansarki.
Washe gari sai saurayin ya sanar da jama’ar
garinsa cewar yana so ya yi tafiaya zuwa qasa
mai tsarki saboda yiyi aikin HAJJI, sai aka
shiryama abunda yake bukata gabadaya. Sannan
suka kama hanaya da shi da wannan sarki,.. a
wannan lokaci. shikuma sarkin zuciyarsa tana
cike da begen masarautarsa, saboda yayi
shekara cib da barin gari nasa.

To basu gusheba suna ta tafiya dare da rana
kwana da kwanaki har sai da sukayi shekara 1
cur suna tafiya, tare da askarawa, har sai da
watara suka iso kofar shiga wannan masarauta
ta wannan sarki. Sannan sai wazirin wannan sarki
ya fito tare da askarawa saboda tarbar sarki
bayan sun cire tsamanin dawowarsa, sai fadawa
da askarawa suka zo sukayiwa sarki marhaba
suka girmamashi.
Da komai ya daidaita, sai sarki ya shiga fadarsa,
jama’a da mukarraban sarki da fadawa suka taru,
sannan sai sarkin ya gabatar da wannan saurayi,
yayi musu bayanin a bunda yafaru gabadaya
daga farko zuwa karshe.
Sannan bayan haka, sai sarki ya ‘umurci waziri
da ya kirawo masa (masunci) mai kamun kifi,
wanda shine dalilin kubutar da wannan saurayi da
mutanen masarautarsa gabadaya. To atake sai
waziri ya zo da mai kamun kifi, sai sarki yayi
masa gagarumin kyauta, kuma ya tambayeshi irin
rayuwar da yake ciki, ya tambayeshi shin yana da
yara ne ? sai mai kamun kifi ya gayamasa cewar
yana da yara uku, daya na miji biyu kuma mata.

To sai sarkin ya Auri daya daga cikin ‘ya yan mai
kamun kifi, sannan sai shi kuma wannan saurayi
ya auri dayar, sai sarkin ya dauki dan mai kamun
kifi na mijin ya bashi mukami mai girma (mai lura
da baitul mali) a masarautarsa. Sannan sai sarkin
ya aika wazirin nasa zuwa masarautar wannan
saurayi, ya nada shi a matsayin sarkin wannan
gari. To daga wannan lokacin ne rayuwa ta
kasance madaidaiciya ga wannan sarki da kuma
saurayin.. suka rayu cikin wadata da annashwa,
shima mai kamun kifi ya wayi gari yana daga
cikin mafiya arzikin wannan zamani gabadaya,
‘ya yan sa kuma sune matan sarakuna....

Basu gusheba suna cikin wadatacciyar rayuwa
har sai da mai raba tsakanin ‘yan uwa da masoya
ya zo ya daukesu ( mutuwa)..

A NAN LABARIN MAI KAMUN KIFI ( MASUNCI)
YA KARE.

Wanda ni yusuf abdullahi A jibaga' na jagoranci kawo muku.
Sai bayan kwana biyu idan munsake haduwa awani labari,

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment