Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida ba,,

Karyar banza cewar aunty lateefah tana nuna nijlah,,wacece wannan?
Hade fuska mashkur yayi,,Zan gayamusu yanzu nagaji da yawa saina huta,,mummy kinajin abinda yake fada kinyi shiru??
Mummy bata iya motsawaba Saida lateefah tayi saurin girgiza ta kafin ta safke nannauyan ajiyar zuciya tana kallan mashkur Daya kafeta da Ido Yana mamakin halinda mummy ta shiga..
Dasauri yayi gurinta Yana cewa,,lafiya sweet mom,,waya tabamana ke"" dasauri ta daga masa hannu alamun karya qaraso inda take,,chak ya tsaya tare da hadiye yawun Daya taru a bakinta,,tinda yake mummy bata taba yimasa irin wannan karbar ba to kodai shima ya shafo abinda take kyama tattare da Fulani,,yayiwa kanshi wannan tambayan..
Bakin mummy na rawa tace,,auta wacece wannan?
Shiru mashkur yayi Yana tinanin amsar dazeba mummy sai ya maida kallansa ga nijlah yanasan yimata magana da ido,,aiko nijlah ta washe Baki tana tinanin amsa mashkur yakesan tabada..
Tace ehhh,,a kankan ya dauko ni kuma Malam ya daura mana" tsawa mashkur ya Daka Mata Yana hararanta tini nijlah ta rufe Baki tana karkarwa tare da komawa bayan aunty lateefah tana boyewa,, da mugun gudu lateefah ta dawo bayan yaya tare da Dora hannu aka..
Dan ubanka kabani amsa kafin yanzu na Saba ma,,yaushe kazama haka mashkur ni nake ma tambaya kana kallona,,,to kodai na chanza ma,, dasauri yace ah ah mummy dama dama.
Dama me,, gaskiya zaka gayamin ko angayama idan zakayi taimako saika kawomin irin jaraba har gidana,,Bama ta tsaya iya get ba shine saida Ka kawomin ita har cikin falona..
Zuciyarsa na dokawa yace mummy kiyi hakuri tare zamu zata zauna da ita"
A ina?mummy ta tambaya..
Batare da fargaba ba mashkur yace anan gidan,,sedai Ka zauna da ita Amma badai mummy ba" shima baze zauna da wannan annobar ba mummy taba lateefah amsa..
Kai Dan birni me suke fada,,Allah dai yasa badani suke ba,,cewan nijlah tana kallan mummy sai kuma ta sunkuya tace sannu ina yini..
Ke tashi anan kafin kimin barbaren kudin cizo Naga alama a wannan jikin naki babu abinda bazaa samu,,Kai mashkur Ka fitamin da ita a falo Ka kuma dawo kayimin bayanin inda Ka daukota..
Mummy marainice shiyasa na kawota ta riqa tayaki aiki,,mummy yarinyar bata da matsala Dan Allah karkice ah ah yafada Yana hada hannu alamun roqo.
A tare mummy da lateefah har ma da yaya suka sa salati suna tafa hannu" lateefah ce tace cewa akayi mummy na buwatar 'yan aiki,,to koma ina buqata saina rasa Wanda Zan dauka sai wannan..
Duk da yarinta da shirme irin na nijlah saida tagane kyamarta suke gashi taji Dan birni Yana maganar aiki zata tayasu,,to wai me suke nufi?
Wanne irin kallo suke min nijlah ta tambayeni kanta,bata dawo daga tinanin ba taji mashkur Yana cewa..
Mummy Dan Allah kiyi hakuri ki tayani riqe amanar da Allah ya doramin,,yarinyarnan marainiyace bata da gata shiyasa na kawomiki ita,,
Karya kake mashkur Idan Zaka fadi gaskiya ka fada ayita ta qare..
Haba Aunty lateefah,,ki tausayamata..

Ya mashkur kodai Suma Suna bakin cikin aurena,,Naga alama Suma irin kakane" Kuma ita wannan qatuwar wacece,,sukaji nijlah Na tambaya???
Ke kimin Shiru Nace dame kikeso Naji,,to wallahi naqara Jin maganarki Saina zaneki anan" turo baki nijlah tayi tana dire diren qafa,,a hankali mashkur yace menene Kuma,,Nina gaji Zama zanyi,,Kuma Dai ka Tina Allah Yana kallanka,,Kuma a wuta yakesa me Karya haka malaminmu ya Gaya a islamiyya,,gwara kawai kace matarkace Ni Kamar yadda ka Gaya Bello..
Gaba daya jikin mashkur yayi sanyi Dan haka ya zauna Kan kafet Yana Kallan mummy...
Mummy kiyi hakuri Nima ba haka naso ba,, mummy ki dauka kaddarace tasa nayi, Sai ya kasa qarasawa..
Qaddara tasa kayi me auta,,ka gayamin Ko hankalina Ze kwanta..
Mummy auren nijlah nayi a,,kafin ya qarasa magana mummy tasa kuka tana cewa..
Shinkenan ka cuci rayuwata ka nuna Kaine da kanka,me kakeso mu Gaya iyayen Yasmeen,,yanzu wannan abun Abar aure ce,,kadubeta kama an daurawa muciya zani..
Kallan jikin nijlah ya riqayi Shima Yana hawaye,,Dan Allah mummy kidena wannan kuka wallahi kukanki masifa ne a gareni da rayuwata mummy na tuba yafada Yana kama qafanta..
Saida mummy tayi kuka me isarta kafin tace ina Baka umarni Daka mayar da yarinyarnan inda Ka daukota kafin..
Mummy kiyi hakuri nijlah amanace agareni nayi alqawarin Zan riqeta duk rintsi,,bazan taba rabuwa da itaba..
Zaro Ido mummy tayi tana kallansu kafin tace a ina zaka zauna da ita?
Mummy Dan Allah ko dakin Baki Kona 'yan aiki ki kaita nasan zata zauna" Kai wallahi ko a dakin Karen gidannan bazan ajiye wannan irin jarabar ba,,gwara tin muna arziqi Ka fita da ita..
Kafin yayi magana aunty lateefah tafara Jan nijlah da niyyar kaita waje,,cikin ihu mummy tace ke lateefah Baki da hankali zaki tana jikin wannan nida Zan iya da tinanin na kaita lahira hannunane bazan iya Sawa a jikinta ba,,Amma zanyi maganinta idan har be fita da ita a gidan nan ba..
Cikin kuka nijlah ta Koma Bayan mashkur tana riqe rigarsa tace,,Dan Allah ka fita Dani zasu kasheni,,Bata sona..
Kiyi hakuri nijlah komai zeyi daidai kinji,,mummy.
Karka qara Kiran sunana saika fara fita da wannan annobar,, mummy Bazan iyaba haqqinta Yana kaina.kiji tausayinmu.
Kaima kasan Bazan taba Zama da ita a gida daya ba Dan haka ka zabamata inda ya dace Kuma a yanzu nakeso ka saketa saki uku.
Mummy kiyi hakuri tinda bazaki Bata gurin Zama ba nizan zauna da ita a dakina,,batin saki Kuma kiyi hakuri Baz...
Lafiyayyun Mari Har guda uku Yaya ya safkewa mashkur Yana nunashi da yatsa,,kayi kadan ka wulaqanta mana uwa,,wallahi sedai kabar gidannan..
Beyi Magana ba ya kama hannun nijlah dake kuka tana Kiran Sunan kaka ya Shiga dakinsa da ita,,a qasa nijlah ta zube tana birgima tana ihu,,shiko bakin gado ya zauna ya dafe kansa Yana Jin Wani irin faduwar gaba..
Cikin kuka lateefah tace,yanzu haka zamu zuba ido mashkur yayi yadda yakeso,, ba Wanda yabata amsa..
Nan mummy ta dauka waya ta Kira daddy tana kuka,tace Alhaji ka dawo gida yanzu,,tana gama fada ta katse Kiran Bata jira amsar Shiba..
Wani layin ta Kira ta miqa lateefah wayar..
Yasmeen dake kwance Kan cinyar mama tana game a waya taga Kiran mummy,,kallan mama tayi jikin Jin Kunya tace,,mama mummyn mashkur ce.
Ki Daga mana cewan mama tana kasa kunne,,Yasmeen Na dauka lateefah tace ..
Sunana lateefah yayar mashkur,,mummy nasan ganinki yanzu....



Wash,, typing da wahala,,mu hadu a page na gaba..

Karku manta da share.



*Momn sultan ce*✍✍✍
💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*MOMN ANSAR*



1⃣9⃣&2⃣0⃣


Mummy kuma,,ke Yasmeen dama kina waya da mahaifiyar yaran nan" gizgiza Kai Yasmeen tayi tana kallan mama data kafeta da ido,,amsa zaki Bani,kinfi kowa Sanin bagane wannan yaran naki nake ba..
Cikin yauqi da yanga Yasmeen tace,,Allah mama bamu waya da ita"
Ok!saiki gayamin ta ina mahaifiyar sa ta dauka number ki??
Mama sau dayane mashkur ya kirani da layinta shine nayi saving,,cike da rashin gamsuwa mama tace,,idan bakwa waya da ita yaya za'ayi ta kiraki???
Mama ba ita bane yayanshine,,sunanta aunty lateefah sedai da wayan mummyn ta Kira kuma tace wai mummy nasan ganina..
Mezaki Mata???
Eyyah mama Nima bansani ba,, Yasmeen ta fada tana turo Baki..
To babu inda zakije"wannan ai shirmene ki dauki qafa kije har gidansu saurayi kina magana da mahaifiyar sa,,mama Allah bantaba zuwa ba sedai jikina Yana Bani kamar akwai matsala..
Wanne irin matsala kinga Yasmeen kidena kawo tinani marasa kyau a cikin zuciyanki...
Mama ba haka bane,,wallahi tin jiya gabana yake faduwa ki abinci ban iya Ciba,,gashi sai Kiran mashkur nake wayanshi kashe,,kuma Shi be Kira ba,,gashi yanzu aunty lateefah ta Kira mummy na nemana,,kinga ko da wani abu.
Babu komai Insha Allahu,,karyar da murya Yasmeen tayi tana hawaye tace,,mama Dan Allah kibani dama naje wallahi bazan zauna ba..
Hmmm Yasmeen ina jiyemiki Abu Amma ke Baki gani,,akullum ina gayamiki ki rage wannan soyayyar da kikewa mashkur,,namiji fa mijin mace hudu ne..
Bata fuska Yasmeen tayi tana kallan gefe tace,,,mama kullum gadanki Baya wuci Kan mashkur,,ba aibu bane Danna nuna kulawa da tsananin soyayya gareshi,,mama mashkur Yana Sona har inaga kama Sanda yakemin ya zarta nawa"" duk da haka ki rage nidai ina gayamiki..
To mama Dan Allah naje???
Ajiyar zuciya mama ta safke tana kallan yadda Yasmeen ta narke Mata kama ance wani Abu ya Samu mashkur tace,, shikenan kije Amma sainayi waya dashi mashkur din naji daga bakinsa yakuma hadani da maman nashi..
Mama kenan,,haba mama na saikace Baki yadda da tarbiyyana ba,,mama kinsani mashkur Baya gari kuma wallahi number mamansane barima nakira saikiji da bakinki..

Number mummy Yasmeen ta Kira sedai wayan akashe Dan haka mama tace babu inda zata fita,,kuka Yasmeen tasa tana Jin wani irin yanayi a dukkan jikinta,,jitake kama qirjinta ze fashe zuciyarta ta fito gaba daya Kota huta da abinda takeji,,koya ta motsa Kota Tina sunan mashkur sai taji kama andora Mata dutse aka,,duk yadda taso hakura takasa haka tasa mama agaba tana kuka..

Yasmeen meyasa kikesan dagamin hankali,,ba Duka ba zagi amma kinsani gaba kina kuka saikace qaramar yarinya..
Mama kibari naje ko hankalina ze kwanta,,wallahi mama akwai matsala,,bantabajin irin wannan yanayin ba sai jiya zuwa yanzu,,Insha Allahu bazan wuci 1 hour ba Zan dawo..
Shikenan Yasmeen tinda haka kikeso saikije daki sani gaba kina wannan kukan ko kunya baji..
Share hawaye Yasmeen tayi tana murmushi tace,, nagode mama..
Mama bata iya bata amsa ba Sai binta da kallo tayi tana mamakin yadda Yasmeen ke nuna damuwanta agaban kowa..

Dago jajayen idanunsa yayi ya zubamata ido Yana kallan yadda take kuka tana Kiran kaka,,wani irin juyawa kanshi yake sabida halin dayake ciki ga kuka dake taba masa zuciya,,ahankali ya riqa Kiran sunanta..
Nijlah. nijlah. Nijlah..
Bata amsaba Saima qarawa kukanta sauti tayi,, ya rasa yadda zeyi da ita,,nan ya miqa hannu Yana Magana da shaqanqiyar murya,,zomana amaryar mashkur,,maqale kafata nijlah tayi ta kuma juya masa baya tana turo baki,,duk da haka ranshi be baci ba ya cigaba da kiranta Yana rarrashinta,,amma duk da haka bata iya shiru da bakinta..
Shiru yayi yana kallanta tare da tinanin ta inda zefara rarrashinta.
Ahankali ya tashi Yana tafiya isa inda take kwance,,kafin ya qarasa nijlah tafara birgima tana juyi a qasa..
Haushine ya kamashi Dan haka ya daka Mata tsawa Wanda tasa hantar cikin nijlah kadawa nan take jikinta yafara karkarwa ta fada jikinsa tana safke ajiyar zuciya..
Rungumeta yayi a karo Na farko Yana shafa bayanta"kukan ya isa haka,,ko kinajin yinwa,,daga masa kai tayi tana qara shigewa jikinsa..
Labensa na qasa ya cije Yana tinanin yadda ze bullowa labarin,,sedai yayi alqawarin baze taba rabuwa da nijlah ba,sabida nijlah amanar Allah ce agurinshi...
Ahankali ya Tashi da ita a jikinshi ya zauna gafen bed Yana qaremata kallo,,qara shigemasa tayi sabida karkarwa da jikinta ya dauka..
Kinaso nazaneki,,saurin girgiza masa kai tayi,,bakinta na rawa tace Dan Allah kayi hakuri..
Zan hakura amma saikin dena wannan birgiman da kike,,koni bakiga halin da nake ciki ba???
Shiru tayi,shiko ya cigaba da Magana,, nijlah indai baso kike zuciyana ta buga ba,toki dena irin wannan kukan Kina birgima a qasa saikace yarinya,,dagowa tayi tana kallansa shiko ya dage Mata gira,,wai ko bakisan kin girmaba??.
Nan ma shiru tayi saida taji ya janye jikinsa anata yana qoqarin Tashi tace..
Kado yinwa nakeji"
Kobata fada ba yasan dole zataji yinwa duba da rabanta da abinci nan yayi murmushi yace jeki falo ki gaya mummy..
Bakinta na karkarwa tace,,Nina qoshi"
Yana niyyan Magana yaji ana buga kofan dakin,,beyi Magana ba yayi shiru Yana sauraran bugun..

Mashkur wai bakajina ina tsaye tin dazu baka bude ba" menene ya fada a hankali" mashkur ni kake tambaya menene??
Cike da qosawa yace,,haba aunty lateefah,,wai me kike nema dani,,Nabar Miki falo nan ma saikin biyoni..

Toka fito mummy na kiranka..
Ina zuwa yabata amsa a ciki,, juyawa aunty lateefah tayi tana tafiya tana tinanin abinda ya chanza mashkur yaran da ko Magana bata dameshiba..
Mummy yace Yana zuwa..
Tinda Yasmeen ta hau titi take gudu kama zata Tashi sama,,ba ita ta rahe gudun motan ba har saida ta shigo layin gidansu mashkur,,Yana zuwa tayi horn get man ya bude mata,,bata iya daidaita parking ba ta fito tana sauri zuciyanta da halbawa da sauri da sauri harta isa kofan falon,,a bude yake Dan haka tayi sallama tana jiran a amsa Mata"
Yaya ne ya iya amsawa Yana kallan kofan,,a hankali Yasmeen ta shiga falon kanta a qasa tana mejin kunya..
Qasan kafet ta zauna tace ina yini,,lafiya qalau suka amsa kafin mummy tace..
Ke lateefah jekice yazo yanzu kafin ranshi ya baci,,kafin lateefah ta Tashi mashkur ya qaraso falon,,nan idansa ya safka kan Na Yasmeen Wanda tayi mamakin ganinsa adaidai wannan lokacin..
Murmushi yamata tare da kashe Mata ido,,duk da yadda zuciyarta ke halbawa saida ta mayar masa na martani,,bakinta a bude a hankali tace lvu..

Kusa da mummy ya zauna Yana niyyan kwantar da kansa jikinta tayi saurin tureshi tana hararanshi,,karka soma wallahi,,shiru yayi yace,,ke kuma daga ina mashkur ya tambaya Yana kallan Yasmeen..

Kafin Yasmeen tayi Magana mummy tace,,Nina sa akiramin ita,,inaga zata fini sanin gaskiyar Magana akan wancan aljanar yarinyar..

Dasauri Yasmeen ta daga kai tana satar kallan mummy,,gabanta Na cigaba da faduwa tace,,
Mashkur wacce yarinya ake Magana,,Dan Allah kada ka hada soyayyana da wata ta qare maganar hawaye cike a idanta..

Daddy dake shigowa ya bisu da kallo Yana mamakin abinda yasa gidan nasa ya zama haka kama anyi mutuwa,,kusa sa mummy ya zauna Yana kallan mashkur,,kai kuma saukar yaushe,,kafin mashkur yayi Magana daddy ya qara wata tambayan?
Hajiya bakuwa kukayi,,eh kawai mummy tace tana hararan mashkur, ka tambayi danka shize gayamaka ko wacece..

Qara yin qasa dakai Yasmeen tayi tana goge hawaye Dan ko Magana bazata iya ba..
Mashkur wacece wannan ya fada Yana nuna yasmeen..

Bakinsa Na rawa yace Yasmeen ce,,budurwata,,budurwarka,,wani abune ya faru Naga tana kuka,,shiru sukayi aka rasa Wanda ze yiwa daddy bayani..
Ganin haka yasa daddy kallan Yasmeen ya Kira sunanta.
Bata iya amsawaba daddy yace Tashi kije gida nizan zo muyi magana da abbanku..

Da gudu Yasmeen ta fita tana kuka..

Tana fita daddy yahau mummy da fada,,haba hajiya akan me Kina kallo yaro ze kawo yarinya har gida bazaki tsawatarba,,Nina rasa meyasa kike daurewa yarannan gindi yake abinda yaga dama..

Daddy kayi hakuri Nima bansan da zuwan Yasmeen ba anan na ganta"kai mashkur har kanada bakin Magana,,daddy aure fa yarannan yayi ga matar can ya sata adaki cewan lateefah tana huci...

Sake da baki daddy yace aure kuma,,aure wanne iri" saika tambayi danka cewar mummy..
Kai mashkur dagaskene abinda suke fada??

Bakin mashkur Na rawa yace" kayi hakuri daddy haka Allah ya qaddaramin badaga ni....
Kayimin shiru mutumin banza saida kasani tambayama aure sannan zakayimin shegan taka,,bada niyya nayi wannan auren ba,,kuma banyi Danna tozar taku ba,,daddy ka fahimceni..

Amma ko kayi wauta mashkur,mena rageka dashi,,koka taba kawomin abu kanaso na hanaka,,cike da nadama mashkur ya girgiza kai..
To meyasa kayimin haka,,da wanne ido Zan kalli iyayen wannan yarinyar?

Shiru mashkur yayi Yana matsar ido nan ran daddy ya baci yayi kanshi da duka,,dasauri mummy ta tare tana girgiza masa kai,,kayi hakuri Alhaji,,ba laifinsa bane,,laifin mugayen mutanan ne dasuka daura masa auren ba saninmu..

Ran daddy a mugun bace yace,,idan su Basu sa hankali shibashi Shi,,ko zaman kansa yake,,daddy kayi hakuri wallahi ban na bata ranku nayi wannan auren ba,kada kuyi fishi dani..
Zama daddy yayi Yana kallan mashkur,,nan mashkur ya safke kashi qasa Yana sauraran daddy..

Mashkur ya akayi tayi wannan auren??

Ahankali mashkur ya bude baki Yana Magana,,daddy bantaba tinanin zanyi wani abu batare da saninkuba,,sedai Hakan yafaru bisa kaddara kuma wallahi bani na nema auren yarinyar ba,,sadaka aka bani..

What what Alhaji kanaji fa wai *yar sadaka* anyako Basu zautarmin da yaro ba?
Wallahi mummy karki yadda saiya saketa ta koma Inda ta fito,,tsawa daddy ya daka lateefah Hakan yasa tayi shiru tana muzurai,,Yaya ko kasa Magana yayi Yana nazari...

Mashkur ka tabbata maganar daka fada gaskiya ne,,eh daddy..

Idan har ka sake Na tambaya naji ba haka ba saina sabama,, dasauri mashkur yace eh Na yadda..


Shikenan yanzu ina yarinyar take,,daddy tana daki,,jeka kawomin ita..

Kambu,,ai wallahi bazata taba sabuwa ba,,wai Alhaji me kake nufi shikenan auren ya dauru"
Kiyi hakuri haka Allah ya qaddara maganar lateefah kuma ba abin damuwa bane,,nizan yiwa iyayenta Magana Sai suma suyi hakuri adaura auren kinga yanzu 2 month ya rage ayi biki..

To ai shikenan amma ku sani daga kai har Dan naka,,wallahi sedai yazabi daya ko nijlah ko Yasmeen..
Mashkur dake zuwa falon nijlah Na biye dashi yaji abinda mummy ke fada nan yaji wani irin tashin hankali,,be iya jiran nijlah ba ya qarasa da sauri ya zube gaban mummy..

Mummy Dan Allah karkice zaki rabani da Yasmeen mummy badan bana santa nayi auren nan ba,,daddy kayi Magana"turesa mummy tayi tana daga murya tace..
Nasan bakinku daya to wallahi bazan taba karbar wannan auren ba,,ka rasa Wanda zaka auro Sai yar matsiyata kuma yar fulani..
Ran daddy bace Shima yace,,amma ko kinji kunya,,kuma ina nan ina jiran yadda zakiyi damu nida Dan nawa,, mashkur ka dauki matarka kuje,,ni Zan baka gida azauna..

Tsiru nijlah tayi tana binsu da ido taji daddy yace,,nace ka kawomin matar taka naji shiru..

Kafin mashkur yayi Magana nijlah ta washe baki tace baba gani' kallan Nijlah daddy yayi kafin ya maida kallansa ga mashkur.......







*Momn sultan ce*✍✍✍
💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*CLASSIC FEEDOR*



*Ayi hakuri da rashin Jina Akan lokaci,,tare da rashin amsa comments naku,,haqiqa Naga comments Iya comments nakuma karanta,,Hakan ya nuna labarin Yana muku Dadi,,sedai Ina me gayama fans Na 'yar sadaka 2&3 daku gyara comments naku Idan ba haka ba........ nagode sosai da kaunarku gareni....🤝😍*




2⃣1⃣&2⃣2⃣



Bakinsa na rawa yace,, mashkur kana nufin wannan jaririyar ka aura???
Sosa kai mashkur yayi Yana kallan Nijlah da haushinta ya gama cikashi yace,,eh daddy itane dan Allah ka....
Ya isa mashkur Ashe dai bakada hankali nida nakeso kayi aure nima Na samu jika,,saika Tashi ka auro wannan yarinyar dako kanta bata gama sani ba,,dariya mummy tayi tana tafa hannu tace...
Au kuma,,kai da kanka zaka gayi haka??
Tini zuciyar mashkur ta gama tsinkewa bamda halbawa Babu abinda take lokaci huda yaji hawaye na neman zubomasa amma saiya riqesu Yana kallan daddy yace ,,
daddy Dan Allah kada kace ah ah,,daddy ka temaka mu inganta rayuwar nijlah,,wallahi bata da kowa..

Kai dallah rufemana baki,,kabari kawai daddy ya yanke hukunci aini nasan indai yaga wannan aljanar yarinyar dole yadawo bayanmu..

Kallan lateefah nijlah tayi tana turo baki,,doke Mata baki lateefah tayi tana cewa to mayya nidai kada ki cinyeni..
Dasauri mummy tace karki qara hada jiki da wannan yarinya kai kuma ka dauketa daga nan inasan Magana da mijina"

Mummy kawai kiyi magananki wannan tatsitsiyar meta sani cewan Yaya Yana hararan mashkur..
Hawayen da mashkur ke dannewa sune suka Sami damar zubomasa,,kallan daddy yayi da ranshi ke bace yace..

Shikenan madogaran Dana jingina da ita,,ta Rushe,,wayyo Allah ni mashkur,, daddy ina kaunar dakuke ikirarin kuna yimin,,kunyi alqawarin San abinda nakeso daddy kaida kanka kakemin maganan tausayi da taimako gashi yanzu nayi kunjuyamin baya..

Tabe baki mummy tayi tana cewa,,haqiqa duk cikin yarana Babu Wanda nakejinshi a Raina sama dakai mashkur tafada tana nunashi,,bawai Dan bana sansu ba kona fi sanka akansu,,ah ah ba haka bane,,kawai dai inajinka fiye da kowannensu..
Kai shaidane amma duk da haka ka rufe ido kayimin abinda nafi tsana da qi arayuwana,,kodan kana ganin yanda nake shagwabaka har banasan bacin ranka,,toka sani akan wannan aljanar yarinyar nijlah take kowa,,Zan iya batawa dakai har zuwa lokacin dazaka mayar musu da tsiyarsu..
Qasa mashkur ya safke kai Yana goge hawaye nijlah ko haryanzu bata iya cewa komai ba ahankali ta rarrafa ta qaraso kusa da mashkur,,hannu biyu tasa tana goge masa hawaye..

Kado kayi hakuri kazo muje can garinmu kaga kaka da Malam Basa yima fada irin hak..Bata rufe baki ba..

Yaya yasa qafa yayi cilli da ita nan ta zube jikin kujera tare da riqe bayanta ta saki wani marayan kuka..

Kasa dagowa mashkur yayi yanajin ze iya daukan komai Banda dukan nijlah,,sedai a yanzu bashida yadda zeyi haka ya kallo ya barta ta cigaba da kukanta Badan bayajin zafin kukan nata ba sedan ba yadda zeyi..


Kai babban Yaya Ashe baka da hankali,,matar kanin naka kayiwa haka,,Ashe bazaka iya hada zumunchinku anan gaba ba,,kana babba kana zubda girmanka,,to wallahi ku bude kunnanku da kyau kujini..

Ni din nan bana jayayya da lamarin ubangiji duk abinda tafaru Dani murna nake ina godewa Allah,,se yanzu danya ba Dana kyauta mafi muhimmamci da qima Zan qi gode masa,,Toni ba haka nakeba,, Abu guda yasa kukaga nayi shiru harna kasa magana..

Shine ganin yarinyar Karama da ita,, mashkur ta Yaya zaka iya zaman aure da wannan???

Dasauri mashkur ya dago Yana kallan daddy,,yace daddy Zan iya,,, goyan bayanku kawai nake buqata..

Kaji ko Alhaji shiyasa nake gayama yaran nan bashida lafiya Dan Allah mukaishi hospital aduba lafiyarshi,,yaro shekara 34 amma baya San aure mummy tafada tana kallan Daddy..

Mummy lafiya na qalau,,namiki alqawarin auren yarinyar da kikeso,,mummy kinsani nima inasan Yasmeen sedai ina tsoran halinta Na kyamar talaka,,nikuma gashi Allah ya hadani dasu.


Hadiye kukan nijlah tayi tana kallan mashkur daga inda take tace kambu kana sontafa kace" ara ta kaddani bamemin kishiya daga zuwana,, tana gama fada ta cigaba da kukanta ..

Ba mashkur ba ita kanta mummy saida tayi mamakin nijlah..
Ke Dan ubanki harkinsan wani Abu wai Kishi,,turo baki nijlah tayi tace,,
Aidai malaminmu yace ba kyau zagi kuma duk Wanda ya zagi wani kan....ke rufemana baki bakida kunya,, wannan fa mahaifiyatace mashkur ya fada,, idan tana Magana kiriqa yin shiru,,Ko bakiga yadda nake ba???

Ahankali nijlah tace nagani.

Ah ah ka Barta ta nuna mana halinta kafin ka fice a gidan,kinci sa'a mummy ta hanani tabaki da yanzu kingane dawa kike shegiya 'yar sadaka..

Runtse ido mashkur yayi kafin ya bude a hankali yace haba aunty lateefah,,zaro ido lateefah tayi tana kallan mummy..

Barshi lateefah,ki barshi ta gama zagina tinda Shima ya nuna ta fini daraja agurinsa..

Mummy ba haka bane kiyi hakuri,,

Daddy ne yace,kaga mashkur Tashi kaje daki da ita anjima zanyi Magana dakai..
Har mashkur ya Tashi yaji daddy Na cewa..
Taci abinci kuwa??

Badai a gidana ba,, wallahi ko ruwa bazata shaba..
Girgiza kai daddy yayi yana kallan mashkur..

Kafin yace,, Mashkur zaka iya zama da matarka a saban gidana.
Kanshi a qasa yace eh daddy..

Daddy be qara Magana ba ya shiga dakinsa,, cikin minti biyu ya fito da key a hannunsa,, mashkur ya miqawa Yana murmushi..

Hannun mashkur Na karkarwa ya amsa,,daddy nagode,,karka damu Dana duk abinda kake buqata ka sanar Dani,,harya fara tafiya ya juyo yace..
Ka kula da yarinyar mutane..


To yace a hankali Yana kallan mummy data hade fuska tana tinanin abinyi.

Tashi yayi hannunsa Na karkarwa ya kama hannun nijlah ya miqar suka fara tafiya..

Karka sake bakina ya furta kalma mara Dadi akanka,,bazan zuba ido ka tare da wannan yarinyar ba,,tsayawa mashkur yayi yana sauraran mummy yaji daddy yace..
Kaje abinka Nina baka umarni.

Daddy na gama fada ya fito a falon,,Mota ya dauka zuciyansa na quna ya tafi gurin mahaifin Yasmeen..


Tinda Yasmeen ta fito take sharara gudu a titi tana driving tana kuka akaha harta kai gida,,a fAlo ta Sami mama sedai bata Biya ta kantaba ta shiga dakinta da gudu hannunta aka,,
Kan gadonta ta fada tana kuka tare dajin mahaukacin Kishin mashkur Na taso Mata..

Wacece wannan taji ana Magana da Wanda takesa ran yazama mijinta nan da wata biyu kachal,,idan ko San mashkur take tabbas itace ajalin ta.

Tana cikin tinani taji mama Na Magana akanta,,ke Yasmeen lafiya kika dawo Kina kuka badai wani abu ya samu mashkur ba..
Da gudu Yasmeen ta Tashi ta fada jikin mama tana cewa mama,,

Watace watace,,kimin magana kin zauna Sai Kiran wata kike,,kodai mutuwa yayi,, girgiza kai Yasmeen tayi tana cigaba da kuka,,to kodai cewa yayi yafasa aurenki????






Comments &share









Momn sultan ce
💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*HANNATU GALADIMA...*


*Dan Allah aqara yawan pages,Dan Allah aqara yawan pages,,,Kalmar da mutane dayawa Ke ambato batare da sun tambaya abinda Ke hanani typing dayawa ba,,kusani Nida kaina Ina ganin qoqarina,,Duba da ayyukan dake gabana Amma natsaya Ina farantamuku Rai Duk Dan kuji Dadi..*
*Dan Allah masu kirana a waya kusan irin abinda zaku gayamin Ko tambayana,,niba Matan aure nake fadakarwaba,,sedai Ina rubuta labari Wanda Zaki dauki darasin Zaman takewar aure da al'umma tare da gyara kuskuren da muke aikatawa,,masu min chogen Kira Dan Allah kudena kibari saikin cika waya da kudi kafin ki Kirani,,momn sultan data kawai take ajiyewa a waya Bana ajiye kudin kiranku,, nagode*



2⃣3⃣&2⃣4⃣


Cikin kuka Yasmeen ta Bude baki da kyar tana Magana"
Mama mashkur ne ya kawo wata gidansu Sai kuka ya qara zuwa Mata takasa qarasa,,nan da nan hankalin mummy yaqara Tashi,,jikinta ta janyo Yasmeen tana gogemata hawaye..
Kinga Yasmeen kibude baki kigayamin abinda Ke faruwa kafin abbanki dayawo ya safkemin kwandan masifa akaina..
Mekika ji a gidan Basu?Ko Wani ya gayamiki Magana mara Dadi??
Mama ba haka bane,,tinda naje gidan Naga hankalinsu a tashe musamman ma Shi mashkur,,mama Seda daddynsu ya dawo mummy tace Wai kirana tayi koni zefi gayamin gaskiyar Magana,,Sai kuma tayi Shiru takasa qarasawa Jin Wani qatan Abu ya maqale Mata

Please Login or Register in order to submit comment