Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da abinda ya faru"
Kanta a qasa tace to..

Tashi daddy yayi Yana Kallan Mashkur"auta kuna buqatar Wani abu?
Ah ah daddy Dama likita yace zuwa dare Ze sallamemu sabida jikinn nata yayi sauqi sosai" to shikenan Allah ya qiyaye gaba..

Tare da suka fito mashkur yayima daddy rakiya Har jikin Mota" Har mashkur ya juyo daddy ya Kira sunansa"a hankali ya juyo Yana Kallan daddy" daddy yace,,,
Mashkur yazama Dole kasa Ido Akan yarinyar mutane,,Idan Kuma ka Bari Wani Abu yaqara faruwa da ita Saina sabamaka sabida itama 'yace kama Yasmeen..

Jinjina kai mashkur yayi yanaba daddy hakuri kafin suyi sallama ya Koma Dakin...


Kwance Yasmeen take ta zuba wayarta Ido tana kallan yadda kiranta ke Shiga Amma baby yaqi amsata,,time yake nufi dani? Badai haushin dukan nijlah yake jiba?

Indai ko hakane na Shiga uku"

Kai wallahi babu abinda ya gagari Yasmeen wannan ma baze taba zamemin matsala ba,,da gudu ta tashi ta fita falo tana kuka,,ganin ba kowa a falon ta shige dakin abba tana kuka sosai...

Tin kafin ta Shiga abba ya fito Yana tambayana"
Wanne shege ya tabaki 'yar Lele?
Cikin kuka Yasmeen tace abba mashkur ne yaqi amsa kirana,,wallahi abba kusan kwana nayi ina kiransa yaqi amsani abba nashiga uku shikenan zasu rabani dashi..

Zasu rabaki dashi ko dai zaki raba kanki dashi,,Dan wannan halin kadai ya isa yasa mashkur dena kulaki tinda kin Nuna keba me hankali bace...

Turo Baki Yasmeen tayi tana kallan abba tace,,abba kaga mama ko...

Tsakin mama taja ta dauka basket din ta tana kallan abba,,nizan wuce asibiti Naga Rana tayi..

Wallahi babu inda zakije indai nine gaba dake kuma ni nake Baki umarni" akan me zaki dauki abincin gidana ki kaiwa wancan yarinyar,,
Yarinyar data Zama silar kuka da baqin cikin 'yar Lele...

Amma abba Yasmeen" Amma me? kinga banasan Jin komai daga gareki kifita kawai kibani guri...

Rawa Yasmeen tayi tana cewa yau abbana,,Dama Kai kadai kake Sona nasan mama.

Hararan da mama take matane ya hanata qarasa fadar abinda tayi niyya..

Fita daga dakinan kafin yanzu jikinki ya gayamiki, da kuka Yasmeen ta fita tana qunquni....





Comment & share








*Momn sultan ce*✍✍✍
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*.....*



4⃣8⃣&4⃣9⃣


Yasmeen na fita abba ya maida hankalinsa kan mama"ransa a bace yake kallanta,,kauda fuska mama tayi tana mejin haushin hanata zuwa hospital dubiyan nijlah..
A gefenshi ta zauna tana magana a hankali" yanzu abban Yasmeen kana ganin rayuwar daka Dora Yasmeen ita ta dace da ita?
Nasan kana da ilimi na boko Dana addiniya Ka kuma San amanarta Allah yabamu,,be kamata mu zuba Mata Ido tana Abu Yadda takeso ba"Dan Allah kayi tinina Ka kuma tinani 'ya'ya da dukiya amanar Allah ce,,ze tambayemu akansu ranar da gata ko dukiya bazasu mana amfanin komai ba...

Ajiyar zuciya abba ya safke Yana kallan mama" kafin ya iya bude baki yace"
Yanzu ya kikeso nayi?
Sokike na fifita 'yar wasu akan tawa?

Ba haka nake nufiba sedai inaso kagane Yasmeen tayi laifi Ka kuma hukuntata akan abinda ta aikata..

Cike da zafi abba yace" haba hajiya yanzu duk irin hukuncin da kikayimata be ISA haka ba,,to to to yanzu na gane hausarki,,sabida ke bakisan zafin Zama da kishiyaba shiyasa kike gayar irin wannan maganar,,to wallahi Bari ingayamiki,,daga yanzu ko kallan banza kika qara yimata akan wannan maganar Saina Saba Miki,,Wanda batasan ciwan nata ba,,mtssss abba Yaja tsaki Yana fita a dakin..

Harya fita ya juyo Yana cewa" ban kuma yarda ki qara zuwa hospital ba,,idan ma mutuwa tayi ita da iyayenta sukayi asara Bani ba..

Bakin cikine ya Hana mama magana har abba ya Kada Mata kura ya fita" Yana fita tasa hannu biyu ta zuba tagumi tana girgiza Kai...
Yasmeen ce ta shigo ta zauna jikin mama tana shafa fuskan mama"
Sweet mamana,,waya tabamana ke?

Murmushi mama tayi tana shafa Kan Yasmeen tare da janyota zuwa jikinta tana qare Mata kallo,,zuwa wani lokaci ta bude baki da kyar tana Mata magana cikin nasiha dajan hankali..

Yasmeen yakamat kisan kin girma kidena daukomana magana" kodan kinga mahaifinki be damu da abinda kikeba,,saima goyamiki Baya yake"
Bata jira amsartaba ta cigaba da magana"
Yakamat ace kingane abinda kika aikata ba daidai bane,,kiduba girmanki da shekarunki ki kuma duba na yarinyar da kika buga.
Kinsani ko baa gayamiki ba nijlah ba sa'arki bace,,ko kina tunanin mashkur ze aureki da haka??

Turo Baki Yasmeen tayi tana cewa to Amma ita tasan yarinyace ta auremin miji.

Mijinki ko mijinta Yasmeen kokin manta yanzu nijlah matar mashkur ce,,ko kuwa fa har yanzu kina matsayin budurwanshi a yanzu yace yafasa shikenan aurenki ya fasu kinga shikenan sai abbanki yaje kasuwa ya siyomiki miji kama mashkur ko?? Mama ta qare maganar ta sigar tambaya...

Shiru Yasmeen tayi zuciyarta na halbawa da sauri dasauri,lokaci daya jikinta ya dauki rawa,,babu abinda take hangowa sai tashin hankali game da rabuwanta da mashkur,,bakinta na rawa tace"
Yanzu mashkur sai yace yafasa aurena?
Sosai ma,,tinda kin Nuna bazaki zauna da matarsa lafiya ba.

Mama Shifa ba Santa yake ba.

Ummmm Yasmeen kenan, haryanzu ke yarinyace kina tinanin namiji ze zauna da mace alhalin Baya santa?

Shiru Yasmeen tayi tana zubda hawaye tana kallan mama sai kuma ta rungume mama tana cewa"
Dan Allah mama ki bashi hakuri bazan qara dukantaba kinga tin dare nake Kiran wayarshi yaqi amsani..

Ya zaayi ya amsaki kodan bake akama wannan dukan ba?

Cikin kuka Yasmeen tace Allah mama nadena ni haushina daya danaga yarinya nada mugun kyau,,wallahi mama duk kyau nijlah ta Fini kyau wannan dalili yasani bugunta..

Dariya mama tayi tana kallan Yasmeen tace" kaji shirmen naki ba,,waya gayamiki yanzu kyau Yana tasiri gurin Maza?

Cike da shagwaba Yasmeen tace toba Naga yanzu kowa man saka fari yake shafawa..

Badai kowa ba kuma a yanzu duk namijin dayasan kanshi Baya zaben kyau,, kyankyawar tarbiyya Ake Zabe gashi ke kin Nuna Baki da ita..

Bakin Yasmeen a gaba tace toba nadena ba" Allah yasa cewar mama.
Yanzu saiki tura masa text message ki bashi hakuri, nasan ze karanta.

To Yasmeen tace ta tashi tana murna Dan ita ta manta da wani text massage"

Zazzafan sako Yasmeen ta tsara tare da turama mashkur.

Zaune yake ya dawo daga restaurant Yana qoqarin hadama nijlah abinci yaji qaran zuwan sako cikin wayarsa..

Be duba ba ya cigaba da abinda yake,,Saida ya Gama hada Mata tea ya dauko ya dawo kusa da ita Yana miqa mata...
Nina koshi nijlah tafada cikin shagwaba"
Amsa kisha banasan musu"
To tace ta amsa tana sha badan taso ba,,ki dauka wannan abincin Shima ki cinye inba so kike likita yaqi bamu sallama ba..

Batayi magana ba tafara cin abinci tana ci tana yinqurin amai Shi kuma Yana shafa bayanta ahaka harya Samu taci da yawa.

Gefe ya koma Yana qare Mata kallo tare da tinanin ta inda ze dauki matakin daya dace Kan Yasmeen..
Wayarsace tafara ruru nan yasa hannu a hankali yayi picking wayar ta hanyar kaita kunne Hade da sallama..

Daga daya bangaren mummy ta amsa da kyar tace" Auta kana da hankali kuwa,,ko kanaso kace jinyar matarka yafi zuwa Ka gaisheni??

Bakinsa na rawa yace' kiyi hakuri mummy anjima Zan zo idan ta fito babu Wanda ze zauna da ita,,mummy nijlah na buqatar kulawa sos....

Bata Bari yaqarasa ba tace" rufemin Baki kafin na bigemaka Shi ta cikin wayan" kazo Ka sameni yanzu base anjima ba inasan ganinka,,Ko ita ta haifamin kai dazata riqeka yarinyar da Ko haqqinka bazata Iya saukewa ba Amma kake rawar kai akanta..

Shiru mashkur yayi be qara Magana ba Har Saida mummy ta gama yafara Bata hakuri"mummy kiyi hakuri insha Allahu yanzu Zan zo"kadama kazo auta kadai zauna kana jinyar banza Naga ita tafi karbanka Akan kazo muyi shirye shiryen bikinka...

To kawai yace yana sauraran mummy tagama fada ta katse wayar' tinda yafara waya nijlah ta kafeshi da Ido tana sauraran abinda yake fada' Ko Bata tambayaba tasan fada akemasa Wanda Waze wuci akanta Ake abin ba,,Yana gama wayar Shima ya zuba Mata Ido tare da cewa' Ke Kuma wannan kallan fa?

Dauke Kanta nijlah tayi tana mejin tausan halin da tasashi ciki,,haka nan Taji tanasan ganin kaka,,koba komai Zata rungumeta a jikinta ta rarrasheta yanzu ki bata dame yimata haka sai Wanda Zena mulmula Mata nono Wanda ta dauka hakan a matsayin wahalarwa da hukunci me tsaurin gaske..

Ganin Yadda ta zurfafa cikin tinani yasa mashkur qarasawa kusa da ita Yana cewa" amarya tinanin me amaryana take?

Boye fuska nijlah tayi taqi dagowa,,duk yadda yayi nasan ganin fuskanta taqi yadda yamata wasan harya gaji ahaka wani sakon ya sake shigowa cikin wayarsa...

My baby ya gani nan yayi murmushi tare da duba sakon,,Yana karantawa Yana dariya harya Gama ya rungume wayar a qirjinshi Yana cewa"
Allah yasa haka babyna naji dadi kalamanki sedai bazan iya Baki reply ba har sai matata ta Samu sauqi keda kika dariyana..

Dagowa nijlah tayi tana sauraransa harya Gama magana Dan a fili yake magana" haushi da takaicine suka kamata Dan idan bata mantaba sunan dataji Yana Kiran Yasmeen kenan dashi a lokacin datake kwance Kan ruwan cikinta"mtssss yaji anja tsaki Wanda besan daga inda ya fito ba,,dasauri ya dago kansa Yana kallan nijlah da zuwa yanzu hawaye suka fara cika Mata Ido..

Kasa magana yayi sabida tsabar mamaki wai me wannan yarinyar take nufi Dani,,badai kishi take da baby ba?
Tabdijan indai ko hakane zanga irin zaman da zanyi dasu ahaka,,gashi Bani dasan raba Iyalina...

Yana cikin tinani nurse ta kwankwasa dakin,,firgigit ya dawo daga tinanin tare da bata umarnin shigowa" da sallama nurse ta shigo ta Basu ta kaddatar sallama tare da yiwa nijlah fatan samune lafiya,,da ameen Mashkur ya amsa nijlah ko bata iya magana ba sabida abinda ya tokare Mata maqogwaro..

Nurse na fita mashkur yafara hada musu kayansu,,Saida ya Gama ya juyo Yana Yana cewa,,zaki iya tashi mu tafi idan kuma anan zaki zauna to?

Nijlah bata amsashi ba ta tashi a hankali tana sa takalminta" dasauri ya fita yakai kayan mota ya dawo ya riqe hannunta suka fara tafiya" duk inda suka gifta kallansu Ake kowa na fadar albarkacin bakinsa ahaka har suka Kai mota nijlah na yimasa shagwaba wai ta gaji da tafiya,,be kulata ba ya zagaya ya Bude Mata mota Yana cewa"

Wai Bana gayamiki ki koya yadda Ake Bude Moto ba,,koni driver kine?
Murmushi nijlah tayi tace,Toba gashi can Wani ma Yana budewa matarsa Mota ba,,

Kallan inda nijlah ta Nuna mashkur yayi nan yaga wasu Mata da miji,,mijin ya budewa matar mota ta fito hannunta dauke da baby girl Yar qarama..

Murmushi yayi Dan Shima mutanan sun birgeshi" beyi Magana ba ya zagaya bangaren driver ya Bude,,Yana Shiga itama ta Shiga nan ya tada motan suka fara tafiya..

Seda sukayi Nisa ya juyo Yana kallanta" a hankali yace,,amarya Nima Zaki Iya Bani irin wancan babyn,,Naga kema yarinyar ta burgeki Ko?

Cike dajin Dadi nijlah tace" eh mana Zan Iya" cike da farin ciki Mashkur yasa hannu ya janyota jikinsa Yana shafata yace" yaushe Zaki Bani?
Kai tsaye nijlah tace" Abu me sauqi Duk lokacin da kakeso Allah Zan Baka,,ba ance ana bacci Ake haihuwa ba..

Tinda mashkur yaji abinda nijlah tace haushi ya kamashi anan ya gane batamasan abinda yake fada ba..

Ahaka Har suka qaraso gidan mummy"

Sai da ya daidaita parking motan kafin ya Bude ya fito,,itama ya Bude Mata.
Hannunta ya riqe suna tafiya a hankali Yana aiki yimata sannu" kai tsaye falon mummy ya nufa da ita...



Yawan comments yawan typing.




*Momn sultan ce*✍✍✍
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*Dr JANAN.....*



5⃣0⃣&5⃣1⃣


Mummy na ganin shigowar mashkur hannunsa riqe Dana nijlah ta Mike tsaye"jikinta Har kyarma yake gurin finciko nijlah ta cillata Baya tana nuna mashkur da dan yatsa'wallahi Karya kake mashkur nadena zubamaka Ido kana yadda kaso" kwana fa kayi tare da wannan shegiyar yarinyar,mummy ta fada tana nuna nijlah dake rabe jikin bed tana hawaye'

Nan take zuciyar mashkur tafara bugawa da qarfin gaske Babu abinda yake kallo Sai nijlah data daskare tsaye tana mamakin halin mutanan da Allah ya hadata Zama dasu"
Yanzu shikenan ahaka zanyi rayuwa? Adakeni lokacin da akaso,,a zageni Duka Ni daya?
Nijlah ta tambaya Kanta tana sakin kuka meban tausai..

Girgiza Mata kai mashkur ya shigayi yanasan hanata kukan,,da yanada Iko jikinsa ze janyota ya rarrasheta koya rage Jin abinda yakeji a cikin zuciyarsa..

Dan gidanku auta Bada kai nake Magana ba,,kodai kurma ka Zama?

Fuskar mashkur sake yake kallan mummy Amma a can cikin zuciyarsa bacin raine chinkuye a ciki sedai bashida damar nunawa mummy Hakan..
Ka tsareni da ido Ko bakaji tambayan danayi Maka ba?

Murmushi yayi Wanda yafi kuka ciwo ya Bude baki ahankali zuciyarsa na bugawa yace'mummy bafa a gurinta Na kwana ba,,inacan muna tsara yadda za'a gudanar da bikinmu da Yasmeen to shine dare yayi,Saina zauna Na kwana acan..
Yanzu dazan dawo shine Na biya Na taho da ita Ko nijlah mashkur ya qare maganar cikin bugawar zuciya da zillimin Baran baramar da nijlah zata Iya yimasa..

Dasauri nijlah tashiga Daga kai tana cewa eh.

Kaga auta banisan qarya?
Cike da shagwaba Mashkur ya fada jikin mummy Yana cewa' Toba ga yarinyar nan tsayeba Ai saiki tamabayeta" to to shikenan yanzu a Ina kuka tsaya Kan batin shagalin bikin?

Dariya mashkur yayi Yana Kallan nijlah da tinda ya ambaci aurensa ta hadiye kukan tana kallansa" nan ya kashe Mata Ido Yana cewa' Ai mummy ki kwantar da Hankalinki Dan munriga mungama Hada komai kedai kawai ki jira lokaci..

Dariyar farin ciki mummy tayi tana shafa Kan mashkur tace' Yau Dan albarka kaga shikenan Nima zanga auren auta Na" sosaima yafada Yana janye jikinsa.

Mummy nizan Shiga daki inasan watsa ruwa a jikina' Yana dakyau Ai,,Amma Dai Idan ka shirya gurin mutuniyar zakaje?

Sosa kai mashkur yayi Yana cewa' eh Mummy

Shiru nijlah tayi tare tare da yin tsuru tsuru da Ido tana kallansu daya Bayan daya yayinda hawaye suka riqa zirya a idonta,, ganin yadda gaba daya mashkur ya manta da ita tsaye Saima maganar aurensa yake,,
To waima yaushe aka bashi aurena dahar yafara maganar Wani auren?
Nijlah ta tambaya Kanta..

Sedai abinda Bata Sani ba shine" Duk abinda mashkur yake Yana kallanta tare dajin matsanancin tausanta bashida yadda zeyi shiyasa ya zuba ido akemata yadda akaso..

Mashkur Na satar kallan nijlah ya fita a Dakin Yana addu'a Allah yasa nijlah ta biyo bayansa,, harya fita Beji alaman tahowantana Dan haka ya tsaya Daga kofa Yana leqenta...

Nijlah Na ganin tafiyan mashkur ta Daga qafa a hankali tanasan binshi Taji mummy tace"dawo Nace,,
Dan ubanki Ina Zaki bishi?
Muryar nijlah Na rawa tace" uhmn Zan"

Uhmn uhmn me" wato Kan ansaba bin Maza a gindi a gandi kuna yawo da shanu shine Zaki bishi kuyi wankan tare Ko?

Shiru nijlah tayi tana wasa da hannunta..
Kibani amsa" nasan Dai babu abinda Zaki Iya a bed dadai yawan jejeni nasan anan kikafi kauri..

Tsuru tsuru nijlah tayi tana tsoran kada mummy ta doketa,,bakinta Na rawa tace"
Dan Allah baba kiyi hakuri Bazan qaraba"

Ah ah Wallahi Zaki qara,,indai shawan jejine Dan baki Samu gurin Zama anan ba..

Ita Dai nijlah Bata qara Magana ba Banda rawa Babu abinda jikinta yake" akankali Takai kallanta ga kofa Aiko taci sa'a idanta ya safka Kanna mashkur" hannu yasa ya yaficeta dashi tare da yimata alamar Kira..

Aida sauri nijlah tayi hanyar fita tana tafiya tana Hada hanya.
Ke dawo Dan ubanki Ina zakije" hannu yasa ya rufe bakinsa Yana Mata alama da kada tayi magana nan itama tasa hannu ta rufe bakinta tana kuka a hankali"

Duk abinda mashkur yake daddy Na tsaye a bayansa sedai yarasa abinda yakewa hakan danshi ba cikin Dakin yake kallo ba" hakanan jikin mashkur ya dauki rawa nan daddy yasa hannu ya janyeshi Daga jikin qofar ya Kuma sa kai ciki..

Mummy bataji zuwan daddy ba ta shigaba da zazzaga Mata masifa" sabida Ke mayyace kinkasa gane cewa ba'a sanki,,Sai liqewa yaro kike Yana guduwa,,Ni wallahi naso ace mutuwa kikayi da tinin Na huta da damuwa..

Tana leqewa yaranki Koshi Yana liqe Mata" kinga hajiya ki kiyayi kanki" Idan baso kike rabo ya kasheki ba daddy ya fada cikin daure fuska,,
Kina nan kinsa masa Mata gaba kinacin zarafi Shi Kuma ya labe Yana Kiran matarsa Amma sabida tsabar San zuciya kinkasa ganewa..

Tabe baki mummy tayi tana cewa' to Wai Alhaji me nayi kawai sabida Na hanata zuwa dakinsa saika hauni da fada,,Ko Dai sokake gaba daya yarinyarnan ta tare masa a Daki Sai Abu mara Dadi yafaru azo ana zance da karkata kai?

Nauyayyen ajiyar zuciya daddy ya safke Yana cewa'wanne irin Abu mara Dadi?Naga Dai matarsace ta Sunna Dan haka kibarsu suyi rayuwarsu yadda sukeso..

Hhhhhh wacce irin rayuwace za'ayi da wannan jaririyar yarinyar Ko bakaga yadda take ba" Ni wallahi bansan meyasa auta ya kwaso wannan ba,, ka dubetafa kama an daura muciya zani.

Ke Tashi kije gurin mijinki,aikinsan Dakin nasa Ko?

A hankali nijlah ta Daga kai Duk Da batasan ta inda zata fara neman Dakin mashkur ba.

Jeki can Yana jiranki' nijlah Bata qara Magana ba ta fita da gudu tana waiwayen mummy" Harara mummy ta riqa binta dashi Har Saida nijlah ta nacewa ganinta...

Kusan Cin Karo nijlah tayi da mashkur Dan tinda yaga tahowanta ya Bude Mata hannu Yana jiran zuwanta" Kamar tasan abinda yake nufi ta fada faffadan qirjinsa tana safke ajiyar zuciya.

Nan ya riqa shafa bayanta Yana hura Mata iska a kunne" kiyi hakuri kinji nijlah ta,,komai yayi farko zaiyi karshe,,anjima zanje gurin abokina Naji yadda zamu bullowa lamarin..

To tace tana kuma tana qara shigewa jikinshi" ahaka har suka Shiga dakinsa nan yasa key ya rufe kofan ya kwantar da ita Kan hado Yana Mata sannu'

Nijlah bata iya amsawa ba sai lumshe ido take tana kuma busheshi" ganin haka yasa mashkur tashi ya fada toilet..

Bayan yayi wanka itama ya hadamata nan ya dawo Yana kallan yadda ta harde kafa tana tinani" Kobe tambaya ba yasan abinda take tinani Dan haka yasa hannu biyu ya ciccibeta Yana cewa'
Muje kiyi wanka ko kya dena warin asibiti' turo Baki nijlah tayi tana cewa Allah Bana wari sedai Kaine kakeyi.

Kece dai kike nida ban kwana a gadon asibiti ba" dariya nijlah tayi mara sauti tace' Naga dai tare Muka kwana katina har kana shamin nan tafada tana Nuna boob's dinta" murmushi mashkur yayi yakai hannu Yana qara shafasu tare da cewa' ni yanzuma idan zaki Bani sonake Dama naji daddy Yana Miki huduba tazu ko ke Baki gane abinda yake nufi ba??

Dukan Wasa takai masa tana cewa ni Allah banaso Nika Bari,,kuma yau hadda kaina zaka wankemin kaga yayi datti,,tafada tana shafa yalolan gashinan kanta daya kwanta kama babu komai..
Shima hannu yasa Yana shafawa yace'saloon Zan kaiki acan Ake gyaran kai" Dan gaskiya niban iyaba.

Kai kado kuma Ka iya wanka,, Naga Kaka harda wankin Kai take yimin?
To idanma Baka iyaba nizan koyama..

Ah inye yarinyar dako wanka bata iyaba shine Zata koyamin wankin Kai?
Rufe fuska nijlah tayi tana boyewa a jikinsa tace' ai dai yanzu na iya Kaine Baka Bani..

To so shikenan yanzu saiki tashi mu Shiga toilet ga ruwan wankanki can anan Zan gane kin iya ko Baki iyaba.

Ba musu nijlah ta tashi suka fada toilet" brush yabata tayi,,Saida ta Gama yabata sosa da sabulu ya koma gefe Yana kallanta.
Sosai nijlah tayi wanka takuma fita tanayi tana dariya tana cewa kado na iya ko?

Eh babu laifi bayankine da kawai Baki iya wankewa ba kinga ko Baki iyaba" kukan shagwaba ta saki masa tana cewa ni Allah na iya aidai kaima Baka iya wanke nakaba..

Yana dariya Yana tsokalanta yaqarasa Mata wankan suka fito..

Kado nizan shafa Mai da kaina kaji Dan birni?

Naji' Amma daga yau kada naqarajin kin kirani da kado kinaji ko?
Turo Baki nijlah tayi yasa hannu ya doke bakin Yana cewa Bana hanaki wannan abun ba..

A hankali nijlah tace mantawa nayi" kuma Baka gayamin sunan dazan kiraka dashiba,,kaga mu a ruga Mai gida Ake cewa ko malam.

Toni ba malam bane kawo kunnaki kiji sunan danake so,,kuma so nake a gaban kowa ki kirani dashi kinji amaryata..

Nijlah na dariya tace to tare da Kai masa kunnata daidai bakinsa" maimakon ya gayamata sunan sai ya bige da hura Mata iskar bakinsa yanayi Yana qara janyota jikinshi" wani irin yarrrrr nijlah taji a cikin jikinta Wanda bata tabajin irinsaba aiko ta gantsare tana qoqarin janye jikinta a nashi" dariya yayi ya dena hura Mata iska itako bata dena yinqurin kwatar kantaba..
Cikin kasala da mutuwar jiki yace ki tsaya mana yanzu Zan gayamiki,,nan ya rada Mata sunanta Yana dariya.

Kamar tasan abinda sunan yake nufi ta rufe Ido tana cewa to..

Dakyar ya iya tashi ya daukomata doguwar Riga abaya tasa,,Shifa kansa ya shafa Mai da powder tare da lipstick,,kafin Shima ya shirya jikinsa ..

Yanzu saiki tashi muje saloon a gyara Miki kai,,ko, to Tashi bakinta Na rawa tace Amma saika Duba Idan baba Bata nan Saina fito nijlah tafada cikin tsoro..

Dingurinta yayi Yana cewa kedai wallahi anyi matsoraciya ,,fakar idansa tayi ta murguda masa baki..

Hannunta ya kama ya kaita Har cikin Mota kafin ya dawo ya Shiga Dakin mummy"
Zaune ya Ganta ta idar da Sallah tana Jan charbi,, mashkur ya Dan risina Yana cewa'mummy zanje Naga Yasmeen ba lallai nadawo da wuri ba..

Kai kawai ta Daga masa sabida haushin fadan da daddy yayi Mata gashi yanzu aunty lateefah ta tafi Babu me tayata hira..

Be Wani damuwa ba ya fita Yana addu'ar samun daidaito tsakaninsa da mummy..

Hadandan salon yakai nijlah aka wanke Mata kai tare da tsara Mata kwalliya" sosai matar ta Yaba da Kyan nijlah gami da nutuwarta nan ta Nuna mashkur wasu a tamfofi dake maqale jikin shagon tana saidawa..
Ranka ya Dade gafa Kaya irin Baku Na manya" nasan zasuyiwa ' yar Kanwar tamu kyau?

Murmushi mashkur yayi Yana Duba kayan nan Shima ya Yaba da kyansu" bakomai ki bazamin set 50 a ki gwadata a Dinka,,Amma fa kaloli nakeso less da atamfa da material,,hadda shadda Idan ansamu Daga Sai a qaramin wasu"
Sosai aunty zee tayi godiya tafara zabar kayan tana nuna masa,, nijlah Ko sabida Dadi batasan lokacin data rungumeshi ba tana cewa yeeee Nima Na Zama Yar birni" hannu yasa ya lakuce Mata hanci Yana cewa wuce muje kafin kimin halin naki anan..

Suna fita ya Wani sakon ya qara shigowa cikin wayarsa' Yana karantawa Yana murmushi harya gama"
Allah ya Sani Yana mugun San Yasmeen Har besan yadda Ze kwatantawa me karatu ba,,Duk Da itama nijlah Yana jinta Har a cikin jininsa tana ninqaya..

Sosai yaji kewar Yasmeen ta kamashi musamman Idan ya Tina kwalliyar data yimasa ranar da abin Ze faru" hakanan ya riqa tuqi Yana murmushi.

Nijlah Ko Bata Wani Kula dashi ba,,Banda murnar an Sai Mata Kaya Babu abinda take, a haka harya kawota gidan mummy,,a Dakin Shi ya ajiyeta Yana shafa bayanta,

Ki kwanta nan ki huta nizanje Wani guri Na dawo" to tace tana gyara kwanciyarsa Dan Dama cikinta ciwo yafara tin a saloon,,daurewa kawai take..

Mashkur be Koma Dakin mummy ba ya fita Yana murna,,Wani katafaren gurin Saida kayan ciye ciye ya shiga,,nan ya Saima Yar Lele Kaya iri iri,, be je gurin Yasmeen ba Saida yasai Mata kayan da Duk yasan Yana burgeta kafin ya qarasa kofar gidansu Yana mejin dadi..

Waya ya dauka yayi dealing number ta" Yasmeen Na kwance abin Duniya Duk yabi ya isheta musamman Idan ta Tina rabanta da Jin muryar mashkur,,Sai Taji Duk Babu Dadi a jikinta ga Wani irin faduwa da gabanta yake Idan ta Tina da Sunan nijlah,, Taji wayanta Na ringin dasauri ta dauka ta karata a kunne tana murna tana komai..

Saida ya saita nutuwarsa kafin yace' ki fito Ina waje" shagwabe fuska tayi tana cewa' pls baby kashigo ciki,,kaida gidanku..

No a hanya nake akwai abinda ya kawoni Zan gayamiki ba Zama nazo ba.

Rasss rasss gaban Yasmeen ya fadi Har Saida tasa hannu ta dafe" mashkur beyi Aune ba yaji ta sakar masa kuka tana bashi hakuri..

Dan Allah bebi kayi hakuri ka shigo,,kwalliya nasan nayima shiyasa'
Cikin tsawa mashkur yace Ke niba ba kwalliya nazo gani ba,,sabida yanzu Na dawo Daga kai matata gurin kwalliya........................





Comments & share







*Momn sultan ce*✍✍✍
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SMALL GIFT TO...*
*MY DALAπŸ€ͺ.....*



5⃣2⃣&5⃣3⃣


Cike da mamaki Yasmeen ta Bude baki a hankali tana maimaita Kalmar matata' matata.
Yanzu nadawo Daga kai matata gurin kwalliya' Yasmeen ta maimaita maganar a fili"
Eh haka nace daidai kikaji' kinga kidena batamin lokaci Idan bazaki fitoba nizan wuce' mashkur ya Bata amsa sedai wannan Karan cikin sanyin murya ya fada ganin yadda ta Shiga Wani Hali Dan kawai ya Kira nijlah da matarsa...

Yasmeen Bata qara Magana ba ta saki wayar ta fadi qasa' nan take wayar ta ragargaje"
Bata bi takantaba ta kife a gurin tana sakin kuka'
Tajima tanayi kafin Daga bisani ta Tashi ta fada toilet.

Tinda mashkur yaji tsinkewar wayar yasan abinda yafaru

Please Login or Register in order to submit comment