Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

turo baki' be Kalli inda take ba yace' kinga Zan zo anjima kadan ki kulamin da kanki.

Nan ya juyo Yana Kallan nijlah kafin yayi Magana ta Koma daki da gudu tana kuka' murmushi mashkur yayi ya tashi yabi bayanta.

Yaci sa'a Bata rufe kofan ba,kai tsaye ya Shiga Dakin ya janyota jikinshi,, a hankali ya dago fuskanta Yana qaremata kallo yace' ' Yar rigimata yafada Yana zagaye hannunsa Duka akan qugunta, bayanta ya Shiga shafawa alaman rarrashinta.
Cikin Salo da birgewa Hade da matsananciyar sha'awanta mashkur yafara magana.

Nijlah ta? Meyasa kikesan wahalan dani' kodai bakisona? Ki gayamin, Dan Allah ki gayamin nasan zuwa yanzu kinsan menene soyayya sabida kema kinajin abinda nake ji' Shiru Nijlah tayi tana mamakin yadda ya zauna gabanta Yana wadannan maganganun beko Duba yarintartaba.

Hannu yasa Yana shafa fuskanta Hade da wuyanta Yana Mata tafiyan tsutsa' lokaci guda suka safke ajiyar zuciya kowanne su da abinda yake saqawa a cikin zuciyarsa.
Kiyi Magana mana nijlah kinajina Har cikin nan Ko? Yafada Yana tafa saitin zuciyarta.

Wani irin Yar nijlah Taji Wanda Bata tabajin irinsaba nan tafara qoqarin kwacewa sedai mashkur be Bata damar Hakan ba Saima cigaba da jagwalgwalata yake Yana rikitama kansa lissafi.

Dakyar nijlah ta Iya Bude baki a hankali tace' Ni Ni ka sakeni' banaso ta fada cikin sarqewar numfashi'
Wannan Abu ba qaramin daurewa mashkur kai yayi ba sedai daya Tina tayi fara period Sai yayi murmushi Yaja hannunta suka fada Kan lafiyayyan gadonsu Wanda yaji Wani hadendan bedsheets..

Suna fadawa ya qara matseta sosai a jikinshi Yana fidda numfashi a hankali' qoqarin yin Magana take yayi saurin Hade bakinsu Yana Mata Wani irin tsotso kama ya Samu Babbar mace..

Lokaci guda ya birkice Mata Yana aika Mata sakonni masu wuyar fassara' Wani irin damqa ya kaiwa boobs dinta Yana shafasu
idansa rufe' qoqarin janye rigar jikinta yake sukayi ana kwankwasa kofa da karfi ana kwala masa Kira..

Mashkur Mashkur mashkur?........





Comments & share







*Momn sultan ce*✍✍✍
💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*'YAR SADAKA FAN'S 1....*



6âƒĢ4âƒĢ&6âƒĢ5âƒĢ


Dan ubanka nace ka Bude kofan kafin Na balleta' ka Bude Nace mashkur Baka jinane? Mummy ta fada cikin fada..

Dakyar mashkur ya Iya tsayawa da abinda yake yayinda kukan nijlah ya qara qarfi Har mummy Na Iya jinsa,, Baze Iya Magana ba Dan haka ya janyota jikinshi Yana qara rumgumeta tare da yimata Magana cikin kunnanta'
Lamo nijlah tayi a jikinsa tana Maida numfashi kafin ta fara qoqarin Tashi a jikinsa.

Ki tsaya yanzu Zan sakeki sonake jikinki ya dawo daidai kidena wannan karkarwan kinji?
Bata Iya Magana ba Sai Daga masa kai tayi tana goge hawayen fuskanta'.

Nijlah kisani banayin wannan abun abida Na Bata ranki sedai soyayya da tsantsar kaunata gareki' nijlah ita soyayya zurfine da ita ga Kuma fadi,,sedai bazaki fahimci Hakan ba Sai nan ba..

To to Nika sakeni' bakaji ana buga kofan ba' nijlah ta fada a shagwabe.

Mummy Ko Banda Kiran mashkur Babu abinda take tana buga qofan Dakin da Iya qarfinta, yayinda takejin baqin ciki Na ruruwa a cikin zuciyanta...

Ka sakeni ka Bude kofan kaji' nijlah ta fada a hankali' be Iya tashiba Saima kafeta da yayi da tsummamun idanunsa Wanda ya canza Kala Daga fari zuwa ja' sabida tsabar tashin hankalin dayake ciki.

Sai da yayi kusan minti 3 ahaka kafin yayi yaqi da zuciyarsa ya Tashi a hankali ya safka Daga Kan gadon Yana kallanta' kasa kallan idanshi nijlah tayi sabida tsabar Kunya nan ta fara gyara riganta tana San zubda hawaye'

Dasauri mashkur yace' shhhhhhiiiitttt Karki soma hawaye kinga Dai mummy na jirana.

Zaro Ido nijlah tayi tace baba fa kace' wayyo Allah Na kado wallahi dukana zatayi kaga saita zube Akan bed tana neman inda zata buya' Duk da halin da mashkur Ke ciki Saida yayi murmushi.

Kinga jeki Shiga toilet Karki Bude indai Bani Nace ki Bude ba kinji' Bata Iya amshiba ta kwasa a guje ta fada jikin toilet da zaninta a hannu,,tana Shiga tasa key ta ciki ta kulle jikinta Na rawa sabida tsabar tashin hankali..

A hankali mashkur ya soma takowa zuwa jikin kofan tamkar Wanda egg ya fashewa a ciki' hannunsa Na rawa yafasa zare key.
Haryanzu mummy Bata Dena fadaba tana Kiran sunansa ahaka harya gama Bude qofan ya sauke idonshi ana mummy.

Tsaye take a falon tana sababi kama Wanda aka bama gasar Cin kofin duniya' Ai tana ganin ya Bude tayi cikin Dakin Ranta a bace tana huci kama kububuwa' Ke kina Ina Dan ubanki ki fito Nace wallahi Yau sainayi maganinki 'Yar masu yawan Jeje da bakin halin tsiya wallahi Baku isaba kurwan Dana tafi karfinku matsiyata banza matsiyatan Wofi kina Ina mummy ta fada cikin ihu da amsa kuwwa, kai kace da sa'arta take fada.

Jikin nijlah ne ya dauka rawa Amma Duk Da haka Bata zauna ba Saida ta tashi ta zo jikin kofan tasa jikinta ta qara turawa yayinda bakinta be bar ambatan Sunan Allah da neman dauki a gurinshi ba..
Sai yanzu take danasanin Qin bin hajiya Khadija da tayi.

Sosai mummy ta Shiga zagaye Dakin tana neman nijlah Amma Bata gantaba.

Takowa mashkur yayi harya qaraso inda mummy Ke tsaye yasa hannu ya riqe nata Yana Magana a hankali' mummy Wai Wa kike nema nifa kadaine a dakinnan Babu kowa..

Be kai Ida maganar ba mummy ta Daga hannu cikin fishi zata daukeshi da Mari'
Dasauri mashkur ya rufe idansa Dan Baze Iya kallan wannan baqar ranar ba sedai jin Shiru yasashi budewa idon a hankali,, itama mummy sauke hannunta tayi Dan bazata taba Iya Marin autan nata ba ta zuba masa Ido cike da bacin Rai..

Mummy kiyi Allah Dan Allah' mummy kidena Daga hankalinki wallahi Babu abinda nakeso fiye da ganin farin cikin ki da kwanciyar hankalinki,,mummy Idan kina irin wannan tashin hankali Zaki dorawa kanki hawan jini kisa mu Shiga uku.

Kaine Zaka doramin hawan jini auta, Sau nawa Zan gayamaka banasan tarayyarka da kusanci ka da wannan aljanar yarinyar?

Cikin sanyin murya yace mummy wacce yarinya kike magana?

Nijlah nake Magana Ko kanaso kace Bata cikin. Dakin nan?

Bakinsa da rawa yace mummy batanan fa tana...
Tana gidan ubanka ko? Kayimin Shiru,,wallahi ka qarasa Magana tam Dinka.
tana Ina Ko kanaso kace ba ita Naji kuka yanzu ba, wato kai Har Zaman aure kakeyi da ita Ko?

Kasa ya safke idonsa Yana cewa' eyyah Mummy bafa haka bane laifi tayimin shine na duketa kikaji kukanta yanzuma dakyar ta Samu Na saketa shine ta boye, mashkur ya qare maganar cikin rashin gaskiya.

A Ina ta Boye Naga Dai ba kofan fita ta Baya?
Mummy bansani bafa,, Dan Allah muje ki zauna kibar tada hankalinki akanta.

To Ya kakeso nayi da rayuwata mashkur? Kodan kaga Na Dora soyayyana akanka shiyasa zakesan Bani wahala?

Ah ah mummy inaso ne Dai ki fahimceni' mummy nijlah Amana aka Bani ita,Kuma matatace ta Sunna Na tabbata Idan Na zalinceta Sai Allah ya sakamata gashi marainiyace.

Kayimin Shiru Ko yaya,,Sai anyi Magana kace marainiya marainiya, shin ni Ina nawa iyayen Ko ita kadai kake tausai?

Ah ah Mummy nidai ki zauna Ko lemo kisha.

Anqi a zauna' kaga mashkur ka kiyayeni, wallahi matuqar kanasan farin ciki saika Maida yarinyarnan garinsu''

Shidai beyi Magana ba Yaja hannunta suka zauna kan daya Daga cikin kujerun dake ajiye a falon' Tashi yayi ya kunna TV tare da daukomata ruwa da lemo masu sanyi yafara tsiyaya Mata a cup.

Mummy amsa wannan Kisha nasan kin debo rana?
Amsa mummy tayi tafara sha tana hararansa,,shidai mashkur hakuri kawai yake bata harta gama sha ta tashi tsaye tana cewa'

Jeka nemomin ita aduk inda ta Shiga Dan wallahi Bazan barta nan ba tazo tana samaka damuwa kaga saura 3 days afara bikin nan kada azo aganka a rame Dan wannan Har jini zata Iya tsotsema..

Zaro Ido yayi cike da tashin hankali yace' mummy kibarta anan Duka zata sha Nifa Ko abincin kirki ba Bata Nike ba shiyasa kikaga ban damu da zamanta anan ba..

Ah ah Dai auta jeka kawomin ita ,,Dan gaskiya hankali Na Baze kwanta ba indai wannan ja' irar tana tare da kai..

Magana zeyi mummy ta katseshi' kaje Nace Ko.

Babu yadda ya Iya haka ya Shiga Dakin Yana Kiran nijlah.zuciyansa na quna.

Nijlah ki Bude nine fa, tana budewa ta saki kuka tana cewa honey ta tafi Ko?
Bata tafi ba,, kinga abinda taurin kanki Yaja Miki Ko nijlah gashinan mummy tace dake zata tafi..

Wani irin takaici da haushine suka cikata tare da Dana Sani mara amfani' nan ta fara hawaye tana cewa' kado Dan Allah kace aunty Khadija ta dawo Allah Zan bita,, wallahi Bazan qara yimata musu ba,,nadena Allah nadena Nijlah ta fada cikin kuka da tausayama Kanta..

Janyota jikinshi yayi Yana cewa' kiyi hakuri Nida kaina zansa a satoki a hannun mummy kedai kawai kiyi biyayya ki bita ki Kuma Nuna Mata bakyasan Zama dani kinji?

Cike da sallamawa farin ciki nijlah ta dagamasa Mai tana goge hawayen fuskanta da gefen rigarta tace' shikenan tinda haka kace, Amma tayaya za'a Iya satoni a wannan gidan naku,, nidai kawai kace mutuwa zanyi..

Kije kawai yafada yana Dagamata kai nan suka fito tare,, hankada qeyarta mummy tayi tana cewa wuce muje dangin Hau irin masifa Wanda Basu San komaiba Sai yawo a dawa.
Nijlah Na kuka suka fita ahaka ta sata cikin Mota ta juyo inda mashkur yake tana cewa.

Kai auta ka Kula da kanka Nina tafi sabida Yau inada manyan baki'

Cikin Dakiya da nuna rashin damuwa mashkur yace' mummy wasu irin baqi kuma?

Wallahi su linda ne zasu zo wadannan nake aikin a NGOs dasu na Hada musu liyafa ta gani ta fada fatan kaima Zaka zo ayi Taran dakai, tinda jiya nake nemanka Sai yanzu danazo da kaina Na ganka.

Murmushi mashkur yayi Danya Samu hanyar ganin nijlah' ya Kuma San yadda su Linda Ke ba mummy mahaukanta kudi sabida aikinsu Nada kyau Kuma mummy ta Iya aiki sosai shiyasa indai suka zo qasar Basa Iya tafiya Sai sun zo gidan mummy..

Shikenan mummy Nima yanzu Zan zo,, wanka kawai zanyi.

Dasauri mummy ta Shiga Mota tana cewa kadai zo da. Wuri nasanka da nawa,, Har mummy ta Shiga Mota ta juyo tana cewa kai auta, kada ka manta ka tahomin da diyata.

Diyarki Kuma mummy?

Kaci gidanku Ina da wata diya data wuce Yasmeen' ka kawota itama su gaisa Ko?

Ciki ciki yace to mummy ya Koma ransa a mugun bace.

Kan gado ya kwanta tare da dafe kansa Yana tinanin halinda nijlah zata Shiga a hannun mummy'
Dasauri ya tashiga Shiga wanka Yana tinanin ta hanyar daze bullowa mummy'
Badan wankan ya Zama Dole ba da Baze yiba..


Suna tafiya nijlah Na kuka ahaka Har suka qarasa gidan Mummy' driver ne ya Bude musu suka fito' nan fa mummy ta Shiga rankwashin nijlah tana zaginta tare da tsintsine mata'
Banda kuka Babu abinda nijlah take tana ba mummy hakuri Dan ba qaramin zafi rankwashin yake Mata.
Sai da mummy ta gashi Dan Kanta kafin ta kyale nijlah ta Shiga ciki..

Kusa da motan nijlah ta kwanta tana birgima tana ihu( ah lallai Yau Nijlah an tuna ruga lolxx)

Mummy Na Shiga falon wayanta ya fara ringing tana dauka Linda take gayamata sun qaraso Aida sauri mummy ta katse Kiran ta amsa Na Mai Gadi sabida ya hanasu Shiga ciki yace yanzu Bakar fatama tsoranta akeji balle farare wadannan ba Yan qasa ba.

Mummy Na dauka get man yace' hajiya wasu masu corona ne suka zo sukesan shigowa gidan Dan gaskiya Ni Ko tsayawa sauraransu banyiba Na gudu cikin lambu'

Kai dallah gafara can shashasha angayama Koma keda corona zaka dakatar dasu to wallahi ka Bude kafin kayi a bakin aikinka' Linda ce Baka Sani ba ko yaya?

Ah hajiya Dama Linda ce Ai ban Sani ba sabida Ni Ina ganin Jan kunne na tafi ta gudu Na boye kinsan....cikin tsawa mummy tace ka Bude musu ba shegen surutu Na tambaya ba..

Nan get man ya bude suka fara shigowa.

Nijlah dake kwance tana kuka ta dago kai' Aiko tayi arba da masu jajayen kunnuwa saita Tashi tsaye tana ihu tana neman dauki'

Wayyo Allah Na baba ta kawoni lahira Allah Na tuba wayyo dodanni ,,nayi gamo da aljanu' nijlah ta fada tana nuna su Linda da abokanka da suka tsaya sukayi cirko cirko Suna kallan Nijlah..

Ganin yadda suke qara tahowa inda suke yasa Nijlah Tashi da gudu tayi cikin falon tana cewa mummy, mummy fito ki gani wadannan abebadan da Ake gani cikin kayan kallo sune suka fasa suka shigo Dan tinda nijlah ta tashi zaune taga inda take ta tabbata ba a lahira take ba a Duniya ne nan ta Tina a inda ta taba ganinsu....

Da gudu mummy ta fito tana gyara daurin dankwalinta yayinda Maryam me aiki Ke biye
da ita a Baya..

Ai Suna zuwa daidai dining kujera ta harde qafan mummy tayi taga taga saiji kake timmmmmm mummy ta wintsila ta fadi kasa dagwash........






Comments & Share.






*Momn sultan ce*✍✍✍
💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘


*STORY & WRITING ...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*R.HUSSAIN....*



*Alhmdllh,,komai yayi farko zaiyi qarshe' kawata mmn amatullah marubuciyar rayuwar zainab' ina tayaki murnar kammalashi da kikayi Allah yabi ladan fadakarwa ya yafemiki laifin da kika aikata a ciki,, haqiqa labari yayi Dadi Babu abinda zamuce dake Sai godiya" Allah ya rayamana yaranmu da albarka ya qaramana Zaman lafiya da kaunar juna,, nagode sosai da karamcinki gareni' momn sultan na Miki San so,,duk da kedin kawar hy hy ne*ðŸĪŠðŸĪŠðŸĪŠ



6âƒĢ6âƒĢ&6âƒĢ7âƒĢ


Tinda mummy ta fadi ta saki Wani qara tana cewa' wayyo Maryam quguna shikenan Na karye wayyo Allah' surutai ta shigayi tana kukan azaba, Maryam Ko bataji faduwan mummy ba ta fita da gudu tanasan Duba nijlah sabida Allah ya doramata San nijlah ba kadan ta,,ita shirmen yarinyar shike qara birgeta da ita.

Shiru Linda da dasauran tawaganta sukayi Suna sauraran shirme da ihun nijlah' tin Suna daukan abin wasa Har tsoro yafara kamasu' bashi suka cire choko chokon takalmansu suka riga kwasa da gudu Suna neman dauki,,anan suka zubda kayan hannunsa Suna rige rigen fita.
Shiko get man dadine ya ishesa Dan Dama yace a wanne dalili zasu shigo gidan Suna Ake zargi da yada wannan cuta' sedai fitansu yanzu ba qaramin haushi abin yabashi ba Dan Yau Ko Sisi Basu bashi ba nan yaqara kulewa da kukan nijlah Wanda Dama ta ishesa hakuri kawai yayi ita kada ta sauke masa wannan dararan idon nata tana hararanshi'
Kallanta yayi ransa a bace yace' Ke dallah tashi' kin zo kinmana baqin ciki 'mitsitsiyar yarinya dake Sai qinjin tsiya.

Turo masa baki Nijlah tayi tana murguda su sakamakon ganin yadda su Linda suka fita a guje yasata yin hamdala ta Tashi tana Kade jikinta,,daidai lokacin Maryam ta qaraso gurin tana tambayan nijlah'

Lafiya Dai nijlah waya tabaki? Bakiji ciwo ba Dai?

Goge hawaye nijlah tayi tana cewa' eh banjiba.

Wai da me aka Miki Nijlah?

Maryam gamo nayi' Kuma wannan mutumin da Baya aski Saina 'yan iska shine ya Bude musu suka shigo Amma dayaga nayi addu'a Suma da gudu suka fita' Sai kuma ta Dafa Maryam tana cewa'

Wai' nafa auna arziqi da Basu daukeni ba.

Ke Dan ubanki ni s'ankine' 'yar kauyen kawai dako kwalliya baki iyaba' gadai Kaya masu kina Sawa Amma a banza.

Murguda masa baki tayi tana cewa' oho dai Kuma Allah ya isana daka tsoratan.. nijlah Bata gama rufe baki ba get man ya kaiwa bakin Duka Yana cewa'
Kujimin mara kunyan yarinya towai Zaman uban me kike a gidannan da Zaki zauna Harda zagina..

Abinka dame jiran kadan Ai tini nijlah tasa kuka tana birgima tare da Kiran kaka' Maryam tayi rarrashin harta gaji' kallan get man tayi tace'
Haba Musa meyasa Zaka biyeta'

Ke banasan munafunci' Ko Ke bakiga abinda tayimin ba?

Naga ita yarinyace be kamata kayi Mata wannan Dukan ba.

Maganar ta safka kunnan mashkur dake qoqarin shigowa cikin gidan da qafafunshi Dan yayi horn harya gaji ba'a Bude get din ba,Dan haka ya fito yaga abinda Ke faruwa..

Kai tsaye gaban nijlah ya isa Yana tambayanta Ke lafiya meke faruwa dake danshi be tsammanin nijlah get man ya dakaba.

Tabe baki nijlah tayi tana nuna Musa dayayi tsuru tsuru da Ido Yana kallansu.

Cike da faduwar gaba mashkur ya Maida kallansa ga musu mai gadi' bakinsa Na rawa yace' meya hadaka da ita..

Dasauri Maryam tace' haka kawai yasa hannunsa me shegen zafi ya bugeta a baki sabida kawai ta.... Ya isa mashkur ya daka Maryam tsawa Wanda tasa hankalin kowa dake gurin tashi' Hatta ita Kanta nijlah Saida ta firgita ta zabura ta miqe tsaye tayi Kan mashkur tana qoqarin riqeshi ya tureta idonshi rufe batare dayasan waya bige ba yayi Kan Musa da zuwa yanzu yafara magana cikin tsoro da tashin hankali.

Maryam kiji tsoran Allah' ranka ya Dade wallahi niba dukanta nayi ba rashin kunya tayimin nasa hannu Na bige b.....

Be Iya qarasawa ba yaji Wani lafiyayyan naushi a bakinsa'

Cikin Daga murya mashkur ya soma magana da zafin zuciya Dan shiyake kama ya cireta ya cillar koze huta da abinda yakeji.

Wallahi sainayi Sharia dakai matata ka doka Har kana Iya maimatawa a gabana.

Ba Musa Mai Gadi ba Hatta Maryam Saida maganar ta girgiza, a tare suka maimata maganar'
Matarkafa kace?

Fuskan mashkur a Hade kama hadari yayi Kan Musa Yana cewa' ka Hada kayanka yanzu basai anjima ba' Dan wallahi bazakayi kwanan farin ciki ba, ka kumayi sa'a bantaba fada Da Wani ba da tau Saina kusa kasheka..

Hannu Musa ya Dora aka Yana cewa' wallahi ban daketaba sharri kawai Maryam tayimin' Ke Maryam Dan iyayenki ki gayamasa Karya kike wayyo Allah Na Ni Musa Ina Zan Samu ogah kamarka me tausai dajin kai' Na tuba ranka Shi Dade nizan Bata hakuri.

Be jira cewan mashkur ba ya rarrafa zuwa ga nijlah Yana kuka da hawaye Yana cewa'
Kiyi hakuri ranki ya dade Banda abinki Ai bayani ake' Ina zanyi tunanin ogah Ze sauri wannan abun,,kiwa Allah ki ceceni.

Nijlah Bata kulashi ba Saima turo masa baki tayi tana fulatanci Wanda nikaina bansan abinda take Gaya ba..

A fusace mashkur ya fuzgo Musa Yana cewa' kai Wai haka be ishekaba saika samin ita a gaba' to Bari nayi maganinka saika dawo cikin Hankalinka tinda Baka dashi.

Tattare hannun Riga mashkur tashiga Yi Yana qoqarin damqar Musa mummy ta saki Wani ihu Wanda yasa suka dawo cikin Hankalinsu' be Iya aikata abinda yayi niyyaba ya Shiga cikin falon da gudu zuciyarsa na bugawa da sauri Dan tinda yake be tabajin kukan da ihun mummy Kamar Na yanzu ba.

Jikinsa a sanyaye ya qarasa Shiga falon sedai abinda ya gani yayi bala'in Daga masa hankali Har besan Sanda ya riqa tsallake kujerun daya Bayan daya ba' ji yayi tamkar Ze Rasa mahaifiyar Tashi sabida Jin sautin bugawan da zuciyarta keyi.

Yana zuwa inda take yayi saurin rungumata jikinshi Yana jera Mata sannu'

Lafiya mummy badai haduwa kikayi ba?

Mummy Bata Iya Magana ba Dan Iya azaftuwa ta azaftu Banda nuna masa cinyanta Babu abinda take tanayi tana kuka.

Shiru yayi Yana Jin kukan nata kama ana diga masa dalma' da kyar ya Iya tashin mummy ya kaita Kan carpet Yana jera Mata sannu'

Mummy Bata Iya amshiba Sai cije lebe take tana Kiran wash wash' sannu mummy Wai garin Yaya Hakan ta faru?

Nijlah ce da Maryam suka shigo suka bar Musa nata zagaye faluwa yana sumbatu cikin tashin hankali.

Cikin wannan Hali Mummy ta dago kai' tana cewa' ku ficemin da wannan shegiyar yarinyar banasan ganinta' Sai kuma tasa kuka tana cewa' Auta kaga abin bake gayama Ko,, gashinan tayi sanadiyyar gurguncewar uwarka Dan banza kawai da Baka Kishina...

Baba ni kuma, menayi Miki Nijlah ta fada tana nuna Kanta?

Ki fita nace, fita Dan ubanki'

Kallan Maryam mashkur yayi bakinsa Na rawa yake tambayanta?

Maryam meke faruwa kiyimin bayani Dan Allah,, mashkur ya qare maganar cikin rauni da tausayama rayuwarsa.

Bakin Maryam Na rawa take gayamsa abinda ya faru ta qare da cewa'
Nidai bansan yadda akayi ta fadi ba' Iya abinda nasani Na gayama.

Bata Ida rufe baki ba mashkur yayi Kan nijlah ya fizgota fada Kan kujera' nan ya zare belt Yana daka Maryam tsawa'
.fita a Dakin nan kafin Na Hada dake..

Sosai jikin nijlah ya Shiga rawa tana bashi hakuri tare da cewa' wallahi Bani bace wasu aljanu nagani inaga itama sune suka Bude Mata Ido kaga Kuma tayi qatuwa da yawa bazata Iya gudu ba shiyasa suka cutar da ita..

Haushi mashkur yawaraji Dan Dama ya tsani ta Kira Mummy da qatuwa gani yake kama raini ne'

Bude baki tayi da niyyan cigaba da bashi hakuri Amma ya rufe Ido ya Daga hannu ya safke Mata belt din a bayanta'

Razananniyar qara nijlah ta saki Dan tinda take ba'a taba yimata irin wannan Duka me Shiga jiki ba Dan Ko Dukan da Yasmeen tayi Mata bekai wannan zafi ba.

Saida tadena Ji Na wasu 'yan lokuta kafin jinta da ganinta su dawo'

Rikice masa tayi ta Kuma Rasa inda zata sa Kanta Taji Dadi Banda juya kai Na azaba Babu abinda nijlah take,,kuka takesanyi sedai kukan yaqi zuwa haka ta kife a gurin tana birgima.

Daga belt din ya kumayi Yana cewa' kin Tashi kin Bata hakuri Ko saina qara miki' nidai banga lokacin da Zaki hankali ba nijlah Anya Ko kinaso mu zauna lafiya?

Bata Iya Magana ba Saima shesheqan kuka ta riqayi numfashinta Na sarqewa' amma Duk da haka be kyaketaba ya dakamata tsawa Yana koranta waje.

Da gudu nijlah ta Tashi ta fita a Dakin cike da tashin hankali ta fita.

Tana fita mashkur yasa hannu ya goge hawayen tausan nijlah Dan ba'a San ranshi yayi Mata haka ba yayine kawai sabida mummy Taji Dadi ta Kuma barshi da nijlah Dan yasan Babu makawa mummy zata Iya cewa saiya saki nijlah adaidai wannan lokacin Duba da halin daya tsinceta a ciki..

Kallan Mummy mashkur yayi Yana cewa'
Mummy kiyi hakuri nizanyi maganinta,, yanzu ki Tashi Na kaiki hospital'

Cike dajin ciwo mummy tace ' Bazan Iya tashiba auta' ka Kira Dr kawai yazo ya dubani anan..

Beyi Magana ba yayi dealing number likitan..

Nijlah na fita ta zauna bakin kofa tana kuka tare da Dana sanin yadda da rabuwa da kaka Ashe dai talauci yafi Wani tashin hankalin sauqi,dama shirme nake danake ganin Zan Samu farin ciki Idan nayi aure ya Allah nijlah ta furta daqarfi tana yarfe hannu sabida Har yanzu bayanta be gama saisaita ba.

Hannu tasa ta shafa gurin aiko tana cirewa taga jini kwance a hannunta' wayyo Allah nijlah saita Tashi da gudu tana zagaye get din tana Kiran kaka da laman'

Dama haka aure a birni yake gashi Na kawo kaina inda za'a kashemini' wallahi Bazan zauna ba gida Zan tafi'

Bata qara neman shawaran zuciyantaba ta tashi,,Bata Ko dauki takalmi ba ta fita da gudu tayi titi' Sai da tayi tafiya mai Nisa kafin taga me napep ta tsayar dashi' .

Qoqarin tsayawa yake nijlah Tasha gabansa Aiko ya bigeta ta fadi gefe' tsoro da tashin hankali suka sa me napep ya gudu Sai wata matashiyar budurwa dake Bayan me napep dince ta tsaya kasan cewar layin ba mutane sosai ta nemi dauki Bata samu ba,,haka ta cire mayafinta ta dauka nijlah tasa a Mota tana mejin tausan yarinyar ta tafi asibiti da ita...


_________


Haba kawata yakamata ace munyi shagali a bikin nan gashi wannan corona tazo tayi kaka gida Har ansa dokan ta bashi a kowanne state kinga Ko Dole a Daga biki suwa Bayan Sallah..

Zaro Ido mubeena tayi tana cewa'haba kawata keda Zaki addu'a ayi bikin nan a gama saiki kawo wata magana' Naga Dai ba dolene ayi chasu a biki ba.

Ke kinga mubeena kibari kawai muyi a lokacin da zafi mana Dadi Ko bakisan ita Yasmeen'yar Gata bace Dan haka yakamata lokacin Duniya tasan da aurenta,, zee ta fada tana kallan yasmeen.

Yatsina fuska Yasmeen tayi tana hararan mubeena' Sai kuma ta Kalli Zainab tana cewa yauwa zee gayamata gaskiya to Idan ba'a Daga biki ba Sai ki gayamin ta inda abokan Abba zasu shigo qasar kinsan abbana bashida abokai dayawa anan yawancinsu ba 'yan qasa bane..

Gaskiya ne kawata suka tafa da zee'

Cikin rauni Yasmeen tace' zee nifa inaga kama mashkur Baze yadda da Hakan ba?

Dan Wallahi ya matsu da maganan auren nan'

Ai Toba Dole ya Daga qafa ba,,nifa Dama gani nake wannan mijin naki zee mugun takura Ke Allah yasa kin tsuma jiki sosai,,dariya suka sa zasu qara Magana mama ta shigo Dakin tana cewa'

Ku Kuma bakijin yinwane kuketa Hira haka Baku neman abinci Yasmeen..

Kuyi hakuri kwana biyu banajin dadi sosai.


Comments & share






*Momn sultan ce*✍✍✍

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya





Please Login or Register in order to submit comment