Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sedai beyi mamakin Hakan ba sabida yasan Kishin Yasmeen tin kafin kaddaran auren nijlah ta fada masa,,dafe kansa yayi yanamejin haushin Hakan dayayi mata' Dan Ko ba'a gayamasa yasan Yau Yasmeen bazata Iya Cin komai ba' Idan kuwa Hakan tafaru to tabbas ya cika Maci Amana Kamar yadda ta kirashi da Sunan.
Rasa mafita yayi Dan haka ya yanke shawaran Shiga ciki koze Iya shawo Kan masoyiyar tasa' dasauri ya kunna Mota yayiwa get man horn, Yana Bude masa ya Shiga ciki Ko kallan inda baba Mai Gadi yake be Kalla ba haka ya tsayar da motan ya fito Yana tafiyansa me daukar hankali.

Tabe Baki get man yayi Yana cewa' oh ikon Allah kuduba yadda nake gaisheda mutuminnan yayi kama be gani ba,,kodan ba abin mamaki bane tinda Yana tare da wannan'yar girman Kan Yasmeen yaqare maganar Yana waiwaye alamun rashin gaskiya.

Masha na Shiga yafara qoqarin Kiran layin Yasmeen sedai wannan Karan wayar a kashe ake gayamasa" Rasa yadda zeyi yayi Dan haka ya qarasa kofan falon Yana sallama"
Mama na daki ta fito da sauri tana cewa'wanene?

Mama nine mashkur'
Murmushi mama tayi tana cewa sannu da zuwa Ka shigomana Ka tsaya a waje' Kan mashkur a qasa ya shiga' be zauna akan kujera ba ya risina Yana gaida mama,,

Mama ina kwana?

Lafiya qlau mashkur' yame jiki?
Dasauri harta Samu lafiya an sallamemu'
Kai alhamdulillah naji dadi sosai,,Allah ya kiyaye gaba.

Ameen mama' mama bata tashiba Saida taqara ba mashkur hakuri akan abinda yafaru nan ta tashi tana cewa ina ita Yasmeen?
Ka Kira wayanta mana' sosai kai mashkur ya shigayi Yana cewa ai mama wayan ne akashe shiyasa ma na shigo..

Dakin Yasmeen mama ta tafi tana Kiran sunanta sedai mama bata iya cigaba da Kiran ba sabida Jin kukanta" dasauri ta Shiga tana cewa ke Yasmeen lafiya me aka Miki?
Cikin kuka Yasmeen tace' mama shine wallahi yadena Sona nijlah yakeso.

Girgiza Kai mama tayi tana cewa inji waye? Waya gayamiki?
Allah mama Baya Sona shikenan nayi asaran dakon soyayyarsa danayi shekara da shekaru' sai yanzu wata Kula baqa Zata zo muyi kasan soyayyarsa da ita.
Ai kinji matsalarki mama ta fada tana Zama a gefen bed tare da janyota a jikinta' kinga Yasmeen ki tashi ki goge wannan hawayen' indai mashkur ne gashican Yana jiranki a falo..

Dan Allah mama da gaske?
Kinci gidanku ina Miki karyane?
Dariya Yasmeen tayi tana goge hawayen fuskanta ta tashi ta fada toilet,,tana Shiga mama ta fito tana cewa gatanan zuwa tana can tana shirmen nata.

Murmushi mashkur yayi yakasa amsawa' har mama takai qofa ta dawo tana cewa'kaga munata magana ban tambaya su mummy ba?

Murmushi mashkur yayi Yana cewa'suna lafiya tace a gaisheki

To alhmdllh mama ta fada tana Shiga daki.

Sosai Yasmeen ta zauna ta tsara kwalliya tare da saka wasu Kaya masu shegen kyau turaruka ta feshe jikinta dasu kafin ta fito tana taku cikin nutsuwa Dan Yasmeen badaga nan ba gurin iya daukar wanka da kalamai masu dadi shiyasa ko sun Sami sabani da mashkur bata Shan wahala gurin janye hankalinsa har yaji ya hakura..

Tinda ta fito ya zuba Mata Ido Yana Yaba kyan surarta' a haka harta qaraso kusa dashi'
Jitayi kama ta rungumeshi sedai bazata iya hakan ba nan ta zauna Kan hannun kujeran da mashkur ke zaune tana kashe masa ido' a hankali tasa hannu ta zagaye jikin kujeran tare da kwantar da kanta Kan hannun kujeran daidai inda hannunsa ke Kai.

Ido ya zuba Mata Yana zancen zuci' wai me yarinyarnan take nufi kadafa ta susutani sabida alokacin yafara Jin wani irin Abu na tsirgawa a cikin jikinshi..

Baby fishi kake dani?

Kallanta mashkur yayi Yana girgiza mata Mai Yana kallanta cike da soyayya' to Amma shine zaka sani kuka,,yanzu Dana hadiye zuciya na mutu ya zakayi?

Hakan ma baze taba faruwa ba,,sedai yanzu kema kin chanza Hali shiyasa Nima nakesan chanza nawa kema kiji inda dadi.

Baby ni kuma me nayi?

Au Bama ki sani ba' ko?

To kayi hakuri bazan qaraba'
Kallanta kawai yake Yana mamakin shagwabanta,,da kyar ya bude baki Yana magana Yana kallanta"

Allah yasa'

Da ameen Yasmeen ta amsa tana qara narke masa.

Babu Wanda ya qara magana kusan minti guda daga Baya Yasmeen tace'
Baby wai har lokacin biki yayi? Ni gaskiya sonake adan qara lokaci kaga'
Kinga dakata banasan wannan shirmen zancen naki,,sai ana magana na arziqi saiki tsiro da shirme, wanne irin daga biki?

Nan fa mashkur ya rikice Mata Yana fada a cikin nutsuwa tare da Nuna Mata bacin ransa.

Murmushi Yasmeen tayi tana dariya tare da yimasa gwalo tace' yeeeeee naji ta bakinsa,,Dama sonake naji kadena dokin bikinmu ko haryanzu kanayi?

Ba qaramin sanyi mashkur yaji ba Dan yau har saida yakai hannu da niyyan bigeta ta goce,,daganan suka cigaba da hira,, mashkur be bar gidansu Yasmeen ba sai bayan sallar magrib yamata sallama ya tafi gidan abokinsa jabeer....

Tinda nijlah ta kwanta bacci ya gagara daukanta Banda juyi babu abinda take,,tin tanajin ciwo kadan kadan harta fara riqe cikinta tana yamutsa fuska,, ahankali a hankali ciwon ya riqa sauka a cikinta tare da riqemata bayanta da mara,,tin tana kuka a hankali harta fara me sauti tana Kiran sunan Allah..

A haka bacci yadan fara daukanta,,tana cikin bacci taji fitsari me shegen zafi na damunta' dakyar nijlah ta tashi zaune tanasan Shiga toilet sedai wani abun mamaki qafan yaqi daguwa ga wani irin ciwo dake damunta'Banda kuka tana kallan kofa babu abinda nijlah take..
Dakyar ta iya safka da rarrafe ta sauko akan gadon tana kuka ta rarrafa ta Shiga toilet..

Mummy dake zaune a falo tana kallo yayinda Maryam me aiki ke tsaye a kitchen tana fere doya taji suka ji kukan nijlah' tsaki mummy tayi tana kwana Kiran Maryam"
Maryam ke Maryam kina ina zoki budemin dakin wannan shegiyar yarinyar Naga abinda take,,aini bansan tana gidanba nake zaune a falo,,to Allah ya kareni daga daukan Corona virus a jikinta,,nasan babu inda qafanta be kaiba' dariya Maryam ta gumtse tana tsoran Kada tayi mummy ta hauta da fada...

Dagowa mummy tayi taga Maryam tsaye tana sunne Kai'

Ke kuma ya haka zaki tsayamin aka saikace mara hankali'
Dasauri Maryam tayi qasa da Kai tana cewa mummy kiyi hakuri..

Niba wannan na tambayeki ba,,jeki duba dakin auta kiga me wannan yarinyar takewa kuka Kada muna nan zaune ta hadamana gobara bamu sani ba,,kafin mummy ta qarasa magana nijlah ta saki wani wahalallan ihu tana Kiran Kaka..

Da gudu Maryam ta qarasa dakin tana cewa ke kina ina'

Nijlah da qarasawanta toilet kenan ta cire pant da niyyan zatayi fitsari taga jini nabin jikinta pant dinta yayi kaca kaca da jini gashi jinin hadda guda guda..

Wayyo Allah na jama'a Ku taimakamin wallahi Bari nake.

Dasauri Maryam ta Shiga toilet tana janyo nijlah jikinta,,jinin data gani ne yasata sakin salati tana cewa' ke dama cikine dake?

Eh wallahi Dan Allah ki taimakamin Bari nake nijlah ta fada a galabaice Dan zuwa yanzu magana ma a hankali takeyinta.

Mummy dake zaune taji nijlah na ambatar bari' bata Ida tsinkewa ba Saida taji Maryam na cewa Dama ciki gareki?mummy bata jira Jin amsar da nijlah Zata ba Maryam ba ta miqe tsaye tana tafa hannu tare da sakin kuka tana cewa.......




Kuyi hakuri inada mara lafiya shiyasa kukaji Shiru...



Comment & share






*Momn sultan ce*✍✍✍
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*MMN MUHMUD...*



5⃣4⃣&5⃣5⃣


Cikin kuka da tashin hankali mummy ke magana"Shikenan auta kajamana abun kunya' mezan gani a gidana ni hauwa?
Da gudu ta qarasa dakin mashkur Bako sallama tana surutai marasa Kan gado.ita ta manta da ciwan kafanta sabida tsabar tashin hankali datake ciki.

Maryam ko ta duqufa gurin yiwa nijlah sannu tare da qoqarin yadda Zata gyara Mata jiki,,sedai duk yadda maryam taso taba nijlah' nijlah taqi bata dama..
Banda kuka da Kiran Kaka babu abinda nijlah take tana riqe mara yayinda taqi Bari Maryam ta taimaka Mata.

Mummy na zuwa ta fara bin jikin nijlah da kallo tana hawaye' turus tayi ganin jinin dake bin kafan nijlah" haushine ya kama mummy tayi kukan kura ta chafki wuyanta tare da zubamata rankwashi akai'
Dan ubanki haka Ake Bari zaki dagamin hankali,shegiyar yarinyar kawai me suffar aljanu.

Turo Baki nijlah tayi,,cikin kuka tafara magana,Allah Baba Bari nayi ki tambaya kado ai dai yace Nima Zan haihu gashi kuma cikin ya zube ta fada tana sakin wani kuka danma zuwa yanzu ciwan maran yafara sakinta.

Saketa mummy tayi tana tsaki' aikin banza yarinya qarama dako kanta bata Gama sani ba yaje ya daukowa mutane wahala,,to wallahi zanga me gyara Miki jiki a gidan nan sedai ki rufe a haka,,Nina godema Allah dayasa bakimin wannan qazantar a falo ba..

Kuka nijlah tasa tana cewa" Dan Baba ki wankemin wallahi bazan iyaba.

Ke Maryam tashi kifita anan kije ki cigaba da aikin Dana saki'
Maryam da karkarwa tace to mummy'
Nan ta fita tana tausan nijlah sedai bata da yadda zatayi,,tana fita ta fada kitchen ta cigaba da aikin ta..

Maryam na fita mummy ta maida hankalinta ga nijlah tana cewa' to ke kuma me Bari saiki jira Wanda yamiki cikin yadawo kinga Saiya wanke miki,, kafin nijlah tayi magana mummy ta fita tana murmushi.

Falo ta dawo ta zauna Kan kujera ta dora qafa daya Kan daya tana dariya Saida tayi me isarta kafin tace' hmmmm gaskiya yaro yarone Banda haka ina wannan yarinyar ta isa ciki har zatayi bari' Banda hauka irin nata' to nidai me aikina bazata taba wannan jinin me shegen qarni ba we dai ta jira idan ya dawo yasan yadda zeyi da ita.

Tinda mummy ta fita nijlah ta kife cikin jinin tana kuka,,Banda karkarwa babu abinda jikinta yake' hakoranta sai haduwa suke da juna suna bada qara kaf kaf kaf,,lokaci guda zazzabi ya sauka a jikinta me zafin gaske....


Gyara Zama mashkur yayi cike da San Jin shawaran da jabeer ze bashi yace' Uhmn jabeer kenan bazaka gane ba'
Haba mashkur kaima kasani dole ran mummy ya baci kama ci sa'a mummy na Sanka na tabbata da kB ne da tintini mummy ta koreshi a gidanta gaba daya..

Ajiyar zuciya mashkur ya safke Yana cewa' jabeer nasan da haka Amma yakamata ace kaima Ka fuskanceni' be kamata mummy tariqayin haka ba duba da yanayin nijlah' yarinyace qarama idan tana Abu zaka fuskanci batasan komai na raguwa ba Amma duk da rashin wayanta Saida ta gane irin qiyayyar da mummy take Mata' wallahi jabeer ina tsaran girman nijlah batare da mummy ta chanza Hali ba, ya qare maganar idansa cike da hawaye..

Ido jabeer ya zuba mashkur Yana nazarinsa kafin ya bude baki a hankali yace' dadina dakai wallahi ragwanta kama mace' Dan Allah duba yadda Ka bude baki kana kuka saikace mace' nifa bawai bangane abinda kake nufiba,,na gane sosai sedai in tambayeka?

Inajinka cewar mashkur' yafada cike dasan tsayar da kukansa!

Yanzu Dama Kai Baka shirya daukar irin wannan tashin hankali ba kaje Ka auro jinsin dakasan mahaifiyarka bata so?

Oh God' jabeer nasani dole mummy tayi fishi Amma yakamata ta sauko haka sabida nabata hakuri' to shikenan kacigaba da rarrashinta Zata hakura cewan jabeer.

Ajiyar zuciya mashkur ya safke Yana cewa' jabeer nifa ba wannan me damuna ba!

Menene kuma cewan jabeer Yana kallan mashkur cike da tausayawa?
Jabeer Yasmeen ce' narasa yadda zanyi na ajiye soyayyanta na hukuntata akan abinda ta aikata' dariya jabeer yasa Yana cewa ai bazaka iyaba,,abokina nasankafa dasan Yasmeen har tinani nake akan soyayyarku' sedai yanzu na kama bakina na rufe tinda gashi kayimata kafi kishiya' Duka mashkur yakai masa Yana cewa' pls jabeer muyi magana Ka ajiye zancen wasa' wallahi Nima banso hakan ba naso raguwa da Yasmeen ita daya kamar yadda take a cikin gidansu sedai kash qaddara ta Riga fata..

Dariya jabeer yayi Yana cewa hhhhhh daga Baya kenan angon nijlah' murmushi mashkur yayi bece komaiba jabeer ya cigaba da magana" abokina abinda kayi kayi daidai Dan be kamata Ka hukunta Yasmeen da hukunci me tsauri ba,,duba da yadda akayimata kishiya tinkafin ta shigo Dan ma kishiyar kwailace.

Murmushi mashkur yayi Yana cewa eh nidai nace yanzu ya zaayi da maganar nijlah?

Shiru jabeer yayi Yana tinani kafin yace' mashkur inaga kawai a nemi makaranta me kyau asakata ciki islamiyya da boko..
Girgiza Kai mashkur yayi' nan jabeer ya Tabe Baki Yana cewa Kai nifa banasan iskanci yazaayi muna magana ta Riga Bani amsa da Kai,, sorry jabeer a gaskiya banasan nijlah tafara haduwa da wasu kawaye tana cikin wannan hali,,nafiso saita fara wayewa kafin ta Shiga cikin mutane'
Sabida me mashkur jabeer ya tambaya?
Sabida ina gudun su hure Mata kunne..

To shikenan kaima kayi magana' toga shawara ta biyu' meze Hana mu kaita makarantar matan aure taje can ta koya Zama da mutane tare da wayewa da girki Kai hadda Kula da miji za'akoyamata a ciki.

Murmushi mashkur yayi yace hakan yayi Amma kafin nan Nima inasanta akusa Dani sedai bayan kwana biyu Zata iya tafiya kaga lokacin Nima na Samu sai kuma yakasa qarasawa.

Baki jabeer ya riqe Yana cewa wai kana nufin har rage zafi kake da wannan yar yarinyar' dasauri mashkur ya zaro Ido waje' Yana cewa' ah haba kaga niba haka nake nufiba nafi so Ka samamin malama dazata riqa zuwa har gida tana koyamata kafin biki kaga da an Gama biki saita wuce makaranta.

Murmushi jabeer yayi Dan ya Riga ya harbo jirgin mashkur yace' to shikenan kwana nawane biki.

3 weeks ya rage Insha Allah' Allah ya kaimu jabeer yafada Yana tsokalan mashkur.

Harsun Gama hira mashkur yace' kaga abokina wai kuwa ina Shi Nasir Ka Bani wayansa inasan magana dashi?

Hannu biyu mashkur yasa ya dafe kansa Yana cewa' Kai Amma ban kyautaba' wallahi jabeer tin bayan dawowana ban qara waya da Nasir ba.
Nasan yanzu hankalinsa a tashe yake'

Tab Amma wannan iyayenta ba qaramin kasada sukayi ba,,wai kana nufin daga Kai sai nijlah kuka Baro kauyen kankan?
Dariya mashkur yayi Yana cewa da Bello suka hadoni Niko na korashi sabida banaso yazo yaga tashin hankalin da mummy Zata man,,Amma yanzu Zan dauko SIM card Dina nasan Nasir duk inda yake hankalinsa a tashe yake'.

Gaskiya Ka gaggauta kiransa Dan Baka kyautaba' hakane jabeer Nima banso daukan lokaci me tsayi har hakaba,,abubuwane kawai da suka sha kaina gashi itama yarinyar ta cika rigima' Kai wallahi har kash.....sai kuma yakasa qarasawa Yana Sosa Kai..

Daga nan suka Dan taba hira mashkur yace' nizan wuce kaga lokaci Yaja gashi nabar nijlah a daki,,sabida nasan Zan Dade shiyasa ban kaita saban gidaba na kaita gidan mummy...

Gidan mummy fa kace mashkur?
Eh wallahi jabeer can na kaita shiyasa kaga inata sauri ban saki jiki na zauna ba ,,yanzu ma sabida dolene zuwan.

Hakane yanzu dai kayi saurin tafiya sauran bayanin Zan Kira Ka sai muyi a waya.
To shikenan jabeer nagode nan ya miqa masa hannu sukayi musabaha,, har mota jabeer ya raka mashkur Yana daga masa hannu...

Sosai Mashkur ya saki gudu a mota Yana yi Yana adduan samun ta lafiya sedai tindaga bakin get yake jiyo hayaniyar mummy..
Dasauri ya fito a motan ko parking ne Ida gyarawaba ya Shiga ciki,,

Assalamu alaikum

Yauwa sannu da zuwa' angon nijlah saika qarasa Shiga ciki,ga matarkacan tayi Bari.

Bari kuma mummy mashkur ya tambaya?

Dan gidanku tambayana kakeyi' Ka wuce kaje Ka gyaramin gida kafin nayi Baki warin jini ya hanasu zama'

Be tsaya jin qarashen zancen ba ya Shiga dakinsa da gudu Yana kwala Kiran nijlah.

Ke Maryam qaramin turaran wuta a dakinan Dan gaskiya yau bazan kwana a wannan gidan ba..

Yana Shiga ya ganta kwance cikin toilet tana fidda numfashi a hankali' dasauri yaqarasa kusa da ita Yana cewa'ke nijlah meke damunki.

Bata iya magana ba yasa hannu ya dagota jikinshi Yana kallan fuskanta'
Langwabewa tayi a jikinsa shiko ya rumgumeta Yana shafa bayanta, beko damu da jinin daya bata Mata jiki ba,,seda yaji tafara sauke ajiyar zuciya yasa hannu ya dago kanta..

Murmushi yayi yace'Dama kin tabayi ko wannan ne na farko?

Cikin kuka nijlah tace Allah bantabayin Bari ba,,kamanta yammata basa Bari sai matan aure.

Mtssss wai Dan Allah yaushe zaki hankali nijlah?
Dasauri nijlah tace gobe..

Bata qarasa rufe bakiba mashkur yasa hannu ya bige bakin Yana cewa' Bana Hana idan ina magana kinayi ba,,koni sa'ankine???





Comment & share






*Momn sultan ce*✍✍✍
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*MY SULTAN...*



*Assalamu alaikum' dan Allah Ina Baran addu'a Daga bakunanku masu albarka Akan Wani Abu dake neman damuna' Allah ya Shiga cikin lamarin.Tare da Duk Wanda yake cikin tashin hankali Ko damuwa Ko neman fita cikin tashin hankali,, nasoyi na gaskiyane kadai zei yasani cikin addu'oinsa,, nagodeπŸ™†πŸ€¦β€β™€πŸ˜₯*

5⃣6⃣&5⃣7⃣


A hankali nijlah tafara girgiza Kai hawaye na qoqarin bin fuskanta' ki hadiye kukan nan Kona barki cikin wannan kazantan.
Dasauri nijlah ta tasa hannu ta rufe Baki tana cewa' Allah nadena Dan Allah kayi hakuri Ka wankemin.
Kai ni mashkur na hadu da aiki' anya kuwa Zan iya wanke wannan abun, yafada Yana kallan yadda jinin ya daskare a qasa gefensa yafara bushewa.
Ganin bashida yadda zeyi yasashi yin ta Maza ya miqe tsaye da nijlah a jikinsa.
Tana hannunsa ya cika ahun wanka da ruwa me zafi bayan ya Gama ya yafara cire Mata kayan jikinta' nan ya sata cikin ruwan zafin Yana cewa' kinga kiyi hakuri ki zauna ciki nasan maranki Yana ciwo ko?

Daga masa Kai tayi tana tashi tsaye a cikin ruwan tace' bazan iya Zama ba da zafi'
Beyi magana ba ya qara ruwan sanyi ciki Amma duk da haka nijlah taqi Shiga tana masa kuka.
Banza yayi da ita ya qarasa gurin data bata yafara sharewa da tsintsiyan kwakwa' bayan jinin ya Ragu ya barbada omo da jik,, Saida ya Gama ya tattara kayanta ya zuba cikin warshing machine.
Nan ya dawo inda nijlah ke tsaye ta zuba masa ido,cikin tsawa yace'
Wallahi kika Bari naqaraso nan Baki gyara jikinki ba Saina sa bulala na Zane Miki jiki' kazama kawai' ke ko San rabuwa da wannan jinin bakiso gashinan ruwan haryayi sanyi.

Nijlah na kuka ta Shiga ciki tana wanke jikinta' kimin Shiru anan' dukanki nayi ko zagi dazaki sani gaba kina kuka' maraji kawai..

Shiru nijlah tayi tana wanke jikinta' harta Gama be qara yimata magana ba ya chanza Mata saban ruwa ya Mata wanka da kanshi' Saida yayimata Sabi 5 kafin ya kyaleta, hakan ma danta fara bashi hakuri ne tana ciwa da ciwo .

Towel ya dauko yasata ciki tare da bude Mata kofa yace' jeki shafa Mai'
Maqale kafata nijlah tayi tana kallan shi' kije nace Nima yanzu Zan fito wanka zanyi naqarasa dauraye Miki kayan.

Tabe Baki nijlah tayi tana magana a shagwabe' ni dai saika daukeni Ka kaini can' ta fada tana Nuna dakin.

Besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba' kallanta yayi yaga bata da niyyan tafiya Dan haka yasa hannu biyu ya dauketa' Kan gado ya ajiyeta tana dariya nan ya dungure Mata Kai Yana cewa'
Kifa nutsu kisan kinyi aure' nan ba a gaban Kaka kikeba.

Turo Baki nijlah tayi tace' toba kace zaka yimin komai ba aidai naji lokacin da kake gayama Kaka da malam.

Zaro Ido yayi Yana kallanta kafin ya bude baki da kyar Yana cewa' au shiyasa kikemin yadda kikeso ko?

Girgiza Kai tayi tana boye fuska' nan ya Barta ya koma toilet, bayan ya Gama wanke kayan ya yi wanka me kyau ya gyara jikinshi,,nan ya fito ya dauka air freshener ya feshe dakin..

Kallanta yayi yaga yadda ta kwanta Kan gadon bacci harya dauketa' kallan bedsheet yayi yaga yadda tafara batashi da jini' kansa ya dafe Yana ambata sunan Allah tare da saurin daukan jallabiyanshi yasa.

Da sauri ya fita Yana kwala Kiran maryam' Maryam ke maryam' da gudu Maryam ta ajiye yanka alayyahun hannunta ta qaraso inda yake' gani auta ta fada kanta a qasa.

Amsa wannan da Allah kiyi sauri ki siyomin pant anan shagon bakin layi' har Maryam ta fara tafiya yace' kinga kiyi sauri ina jiranki anan'

To tace tana tsoran tambayanshi jikin nijlah duk da tasan mashkur bame yawan fada bane kuma bashida zafi haka ta fita tana tausan nijlah.

Bata Jima da fitaba ta dawo da baqar Leda a hannunta' da sauri ya amsa Yana Mata godiya ya koma daki.

Tashinta ya riqayi Amma nijlah taqi tashi sabida bacci yamata dadi ba kadan ba' ganin tana bata masa lokaci yasashi daukanta be direta ko inaba sai cikin toilet' saban wanka ya sake Mata tana kuka tana komai ahaka harya Gama ya dasa Mata pant nan fa nijlah tace bazata Saba sai ya cire shiko Dan haushi be iya magana ba ya dagata Sama yasamata' qoqarin cirewa nijlah take ya bude baki cikin zafi Yana magana'
Wallahi kika sake kika cire wannan abun Saina daukeki da mari, shashasha kawai'wai ya ina Miki Abu kina Neman maidani bawanki ya qare maganar muryanshi na rawa Dan harga Allah yafara gajiya da wannan wahalan Dan be Saba ba...

Ganin yadda ranshi ya baci yasa nijlah Shiga hankalinta nan ta bude baki tana magana a hankali' kayi hakuri honey bazan qaraba'
Wani irin sanyi mashkur yaji ya ratsa zuciyarsa har besan lokacin daya rungumota jikinshi ba Yana cewa'
Keda Baki manta sunan Dana gayamiki ba shine Baki taba gayamin ba sai yau?

Itama murmushi tayi tana boye fuska..
To fita muje nidai Dan Allah kidemin gaddama inba sokike aji kanmu ba Dama gashi masoyanki basa ganin qoqarina.

Tare suka suka fito Yana riqe da hannunta,,nan ya cire bedsheet ya shinfida Mata wani' zoki kwanta anan ki huta kafin na samamiki magani ko' eh nijlah tace tana kwanciya Kan gadon..

Cikin sauri mashkur ya qarasa shiryawa ya dauka mukullin motanshi ya fita'
Pharmacy ya Samu me kyau anan ya tsaya yayi musu bayanin abinda ke damun nijlah' murmushi Dr yayi Yana cewa' ok first period dinta ne shiyasa yazo Mata da wannan yanayin na ciwo Amma idan Ka bata wannan maganin Zata Samu sauqi da yardar Allah.

Godiya mashkur yay ya amsa maganin tare da biyanshi kudin ya fita cikin sauri Yana tsoran Kada ta tashi taga bayanan ta cire pant din jikinta...

Yana dawowa ya sameta zaune takasa bacci Banda ciwo babu abinda ke damunta' nijlah na ganin shigowansa ta tashi da gudu ta fada jikinshi tana cewa'

Dan Allah honey Ka ciremin wannan abun ciwo yasamin a cikina ta qare maganar cikin kuka da tashin hankali.

Sosai Mashkur ya tausaya Mata Dan likitan yayimasa bayanin irin ciwon da Mata ke Samu a wannan lokaci' hannu yasa ya rungume tsam a jikinshi Yana cewa' kiyi hakuri zai dena kinji..

Daga masa Kai tayi sabida tsabar ciwan dake damunta nan ya dauko ruwa ya ballo maganin ya kaimata Baki Amma saitaqi amsa ta rufe bakin.

Be iyamata fadaba ya sa maganin a bakinshi ya zuba ruwa cikin' kallanshi kawai nijlah take taji yasa hannu ya daukota ya Dora Kan cinyarshi' bakinsa yasa yafara lakubar nata bakinta tare da qoqarin budeshi da hannunsa'
Tureshi tafara tana kuka shiko ya yasa kafa ya matseta sosai ya kuma bude bakinta ya hade da nasa' anan ne ya riqa Dura Mata ganin har Saida ta hadiye kafin ya janye bakinsa a nata ya bata ruwa ta sha,, Shi kuma ya zuba ya kuskure bakinsa' sai yanzu yakejin dacin maganin a bakinsa sedai be damu da hakan ba tinda yayi nasara akanta ta shanye gaba daya..

Janyota yayi a jikinsa a hankali Yana shafa bayanta tare da manneta da qirjinsa, ta bayanta yasa hannu ya shafa maranta Yana lumshe ido,lokaci guda shauqinta dasan kasancewa tare da ita' nan ya maida kallansa gareta.

Murya a kasalce yace' ina sanki nijlah' inasan wannan shagwaban naki sedai banisan taurin kai' inaso kidena kinji amaryata?
Shiru tayi masa kama bada ita yake ba daga Baya tafara tinanin wayar dataji yanayi da Yasmeen jiya da dare nan take zuciyarta tafara bugawa da karfin gaske,me wannan mutumin yake nufi Yana nufin yace ni yakeso ba itaba,,bayan naji Yana gayamata itama yanasanta..

Haushine yakamata tafara tureshi tana cewa' ni ni banaso ai ita kadai kace kanaso'

Murmushi yayi yace kema inasanki nijlah kowaccenku tana da gurbi a cikin zuciyana sedai bazaki gane hakan ba sai nan gaba.

Ita dai bata qara magana ba bacci yafara daukanta' har bacci ya dauketa mashkur Yana gayamata kalamai masu dadin sauraro tare da shafa duk inda hannunsa yakai a jikinta.

Ganin tayi bacci ya janyeta a jikinshi ya fito,,dakin mummy ya Shiga Yana cewa' mummy kina ina?

Ganin nan angon qarni mummy ta fada tana dariya' Shima dariya yayi yace wallahi mummy duk na gaji.

Karka kuma gayamin kaifa kaga zaka iya Nika daukemin ita daga gida Ku koma can inda kuka fito.

To mummy Dama abinci nakeso adan Sama mata?

A me ,,to badai a gidannan ba kaga auta ka fita a idona'

Kiyi hakuri Mummy yanzu dare yayi Bazamu Samu abinci yanzu ba'

Yinwan ta kaheta nace' Shiru yayi Yana cewa kiyi hakuri Dan Allah ki tausayawa maraicinta' kujimin Dan Allah

Please Login or Register in order to submit comment